Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 70 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗaya kada ace mashi ta ji mummunar rauni ko
wani abin makamancin haka, shi kwata kwata ma bai kaita ga batun mutuwa ba tukun
nan. tashin hankali. Bai ma san har iyayen nata dik babu su ba.

Kallan yayan nasa ya yi, faɗuwar gabansa tsananta ya yi sosai, saboda yasan yayansa
na ganin komai dake faruwa a birnin, tabbas yaga abin da ya samu Floris, amma yasan
ko ya tambayesa ba zai sanar da shi ba. Dan dolensa ya dawo cikin room ɗin, saman
chair ya zauna tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki, murya a raunace ya ce. "To big
bro da safe zan iya zuwa nemanta?"...... Jinjina mashi kai Black Tiger ya yi alamar
e, sannan ya cigaba da cin abincinsa. Umartar robbot ɗin shi ma Ronnien ya yi da ya
yi serving ɗinsa. Cikin gaggawa kuwa ya yi, hankalinsa ya ɗan kwanta tun da yayan
nasa ya ce da safe ya je nemanta.

"Sweetie ki zo ki ci abinci". Ya faɗa yana ɗaukar chopping stick, cikin natsuwa ya
yi bismillah can cikin zuciyarsa kafin ya fara cin abinci. Kai ta girgiza mashi
alamar ita ba zata ci ba, sannan ta miƙe ta dawo saman chair ɗin zuciyarta cike da
tinanin ina Floris take? Tabbas akwai abin da ya saɓa haka take ji a ranta. Zama ta
yi suka sanya Black Tiger a tsakiyansu, shi da Ronnie suna cin abinci ita kuma ta
buga uban tagumi tana binsu da kallo.

🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥

Washegari da misalin karfe 9, shirye cikin ƙananan kaya masu kyau ya fito daga
cikin bedroom ɗinsa, wata irin trouser ce mai kama da army one, sai shirt milk
color ya sanya daga ta sama, yau har da black glass and p-cap milk color ya sanya a
kansa, sannan ya sanya ankle boots masu shegen kyau da tsada suma milk color, ya yi
kyau matiƙa.

Hannunsa rike da wayarsa. Kai tsaye bedroom ɗinta ya nufa, yana tafiya cikin
natsuwa da kamala. Bakinsa a ɗauke da siririyar sallama ya tura kofar bedroom ɗin
ya shiga ba tare da ya jira izininta ba. A wani irin miliyan ta juyo da kallanta a
kan kofar, tana ɗaure da towel a kirji ta fito daga wanka, gabaɗaya jikinta ruwa. A
maimakon ya juya ya bata waje, sai ya ɗan shagala da kallanta irin kallan kasan ido
ɗin nan, ita kuwa tana ganin shi ne da gudu ta bar wajen ta shiga dressing room na
ɗakin, ajiyar zuciya ya sauke yana mai ɗago kansa sama kaɗan, kamar wanda yake
magana da wani ya ɗan jinjina kansa kafin ya ƙarisa shigewa cikin ɗakin. A saman
side bed ya zauna yana bin ɗakin da kallo, a ransa ya hayyana yaushe ta tashi daga
barci har ta yi wannan gyara, ta ko'ina kamshi ne yake tashi, yarinya mai tsabta
kamar dai shi.

Can a cikin tinanin nasa surar jikinta ya ratso mashi ta cikin kwakwalwarsa, ajiyar
zuciya ya sauke kamar wanda ya gamsu da abu, sannan ya ciro wayarsa domin ta ɗebe
mashi kewa kafin ta fito, dan baya san yawan tunane tunanen nan da yake yi,
ƙwaƙwalwarsa tana da abin ɗauka mai mahimmancin da ya fi wasu tinane tinanen.
Almost 10 mins yana zaune a haka kafin ta fito sanye cikin ɗaya daga cikin abayas
da ya saya mata, ta yi matuƙar kyau kasancewar abayar milk color ita kuma chocolate
color, ta fita sosai, yadda ta yi rolling veil ɗin sai ya baka sha'awa, ga wani
kyakkyawan fashion flat shoe a kafafunta, launin kayan jikinta, sai tashin kamshi
take yi sosai. Wucesa ta zo ta yi ba tare da ta yi mashi magana ba ta nufi waje,
sai satar kallansa ta witsiyar ido take yi.

Cikin sanyin murya ya ce. "Aesh come here, wajenki na zo"........... Kamar ba zata
tsaya ba, sai ta tina dik in da ta je a cikin gidan ma yana iya biyota, so is
better for her to stay with him hare. Dakatawa ta yi ba tare da ta juyo garesa ba,
ta yi ƙasa da kanta dan ita kunyar haɗa idanu da shi ma take yi. Miƙewa tsaye ya
yi, cikin kamala ya kariso in da take tsaye. "Wani waje nike san mu je". Ya faɗa
idanunsa a kan face ɗinta. Bata da bakin tsayawa yi mashi gardama ko ja in ja da
shi, dan haka sai ta jinjina mashi kai kawa ba tare da yin magana ba.
"Zamu iya tafiya?". Ya tambaya yana mai da kallansa kan yatsun hannunta da ta
haɗesu waje guda. Jinjina mashi kai ta yi alamar e zasu iya tafiya. Nuni ya yi mata
da hannu a kan ta wuce su je. Ba musu ta yi gaba ya rufa mata baya cike da tausayi
da kulawa. Kai tsaye harabar gidan zuka nufa, mai gardi guda ɗaya ne a wannan
gidan, dan haka ya umarcesa da ya buɗe masu gate bari su je unguwa, dik tinanin mai
gadin Leesharh matarsa ce, ya yi aure kenan, amma abin da ya bashi mamaki shi ne ya
aka yi ogan nasu ya yi aure maganar bata fita ba? Sam bai ji zancen a hukumansu ba.
Wani zuciya ce ta amsa mashi da ai auren sirri ya yi tun da ga shi ya ce ko su
Bilal sun zo gateman ɗin ya ce masu babu kowa a gidan, dik yadda aka yi auren sirri
aka yi, saboda bai taɓa sanyawa ransa Ramish zai kawo mace haka nan ya ajiye a
gidansa ba, ya kullaceta ba tare da suna da aure ba, saboda kowa dai yasan Ramish
ɗan wani family ne, ba zai yi wannan shashancin ba.

Sosai gateman ɗin nan yake ƙara shan mamaki a dik lokacin da ya kalli
Leesharh, saboda yadda take chocolate color, abin yana bashi mamaki yadda aka yi
Ramish ya aminta ya aureta, sai dai kuma sun yi matuƙar dacewa da juna sosai. Gate
ya wangale masu, cikin natsuwa ya umarceta da ta shiga gaban motarsa, babu musu ta
shiga ta zauna kanta a ƙasa bata san meyake yi mata ciwo ba ita da kanta.

Cikin motar ya shigo shi ma, a natse ya tada ita ya danna waje. Suna fita can ƙasa
ƙasa cikin natsuwa ta ce. "Meyasa kake san fita kai kaɗai ba tare da tsaro ba bayan
kasan aikin da ya kawoni gidanku a kanka? Kasan masu farautar rayuwar kusan sun fi
masu kaunarka yawa". Tana damuwa sosai a dik lokacin da ya fita shi kaɗai, sai taga
kamar ba zai dawo ba, kamar za'a kashe shi a hanya, dan tasan haɗarin masu nikaf.
Yana driving a natse ya ce. "Kin damu da ni ne?"....... Shiru ta yi bata amsa mashi
ba, bata ma da niyar amsa mashi ɗin.
"Aesh meyasa kike shiga damuwa a kan rayuwata?". Ya sake jefa mata tambaya.
Dogon numfashi ta ja tare da saukewa a hankali kafin ta amsa mashi da. "Babu komai,
kawai dai dan nasan ana farautanka ne, and masu nemanka ɗin da alama sun fi yawa a
kewaye da kai"......... "Ba gaskiya bane Aesh, dole kina da dalilin damuwa da
rayuwata, meyasa zaki ɓoye mun?".......... Ya yi maganar dai'dai zai fita daga
ainahin main gate na arear tsadaddiyar unguwar tasu ya sake ce mata. "Allah kuma
yana kewaye da mu gabaɗaya daga ni har masu farautar rayuwar tawa".

Lokaci guda ta sauke ajiyar zuciya, ai shikenan ya gama magana tin da ya ce Allah
kuma babu wani sauran gyara ko ja in ja, dole a yi shiru. Securitys dake tsaran
main gate ɗin nasu ne suka dakatar da motarsa, saboda basu san motar ba, sabuwa ce
ba normal motocinsu da ya saba shiga unguwar da su ba, sannan basu ga face ɗinsa
ba, sai suka dakatar da shi dan bincikarsa, sai da ya saukar da glass ɗin motar
sannan suka gansa. Cikin girmamawa suka sara mashi haɗe da tambayar dama shi ne?.
Kai ya jinjina masu tare da mayar da glass ɗin ya rufe, dama tinted ce, ya ja
motarsa kawai suka cigaba da tafiya yana dannawa securitys ɗin horn alamar gaisuwa
kenan.

Sai satar kallan juna ta kasan idanu suke yi dikkansu biyu, gabaɗayansu suna
yunwar san kallan juna, saboda su kansu sun san sun yi kyau matuƙa, suna san bawa
idanunsu abinci amma kamar suna tsoron haɗa idanu da juna.

"Aesh yaushe zaki bani haɗin kai wajen bincikena? Ki bani cikakken bayani dan
kama mutanen can". Ya jefa mata tambayar tare da dawo da kallansa a kanta........
"Anytime". Ta faɗa tana sauke ajiyar zuciya. "Are you sure and are you
serious?"........ Kai ta jinjina mashi alamar e ta tabbatar. Sosai ya ji daɗin
amsarta, dan yana san cigaba da abin da yake yi, yana burin kama masu nikaf, and
yana san tambayarta wasu tambayoyi a kan abin da ya faru a tsakaninsu a wancan
ranar, amma yana shakkar tambayarta saboda har yanzu bata yarda ba da gangan ya yi
mata ba, da ta aminta da shi ne he has a lot of question for her, amma babu dama,
dan haka sai ya shanye wannan tambayoyi a ransa zuwa time da zai samu dama.

Shiru motar ta kasance na ɗan wani lokaci, yana tuki yana tunanin abin da
yakamata ya fara yi. Da yake yana sharara gudu sai cikin ƙanƙani lokaci suka isa
wani haɗaɗɗen wajen cin abinci na masoya mai bala'in tsari, tsada da kuma haɗuwa,
gabaɗaya yankin wajen ice ne kewaye. Ya lura in dai a gida ne Leesharh ba zata taɓa
cin abinci ba, amma in suka fito waje ko dan idanun jama'a ba zata kunyata shi ba,
komai ya ce ta yi a waje yana da yakinin zata yi dan kada ta bashi kunya, shiyasa
dik da baya cin abincin waje yau ya daure zai jarraba saboda ita ta ci ta ƙoshi. A
katafaren parking space ɗinsu ya tsaida motar tasa, cike da kulawa ya ce. "Muje
ko?".
Ai ta shagala da kallan kyau da tsaruwar wajen, kai Dubai ba dai kyau ba wlh, ga
komai nasu cikin tsari, bata taɓa kallan irin wannan gidan cin abincin ba ko a
mafarki, ba abin da ya fi ɗaukar hankali ma irin abubuwa sky blue da suka yi amfani
da shi a wajen, ga golden da ya ji light mai haske, gaskiya ne wannan gidan cin
abincin ya ci sunansa paradise ɗin kamar yadda yake a rubuce da manyan baki. Buɗe
motar ya yi ya fito, ganin ya fita yasa ta yi gaggawar bin bayansa, dakatawa ya yi
yana jiranta, tana ƙarisowa in da yake yasa hannu ya riƙo hannunta, ai a miliyan ta
ɗago da kallanta a kansa, sai taga sam ba ita yake kallo ba, da gangan kuma yaki
kallan nata, dan baya san ta hana shi yin abin da ya fito da shi, ya fito da ita ne
domin ya samu ta rage damuwar da yake a ranta, yau dai ɗaya ta yi farinciki sosai.

Cikin natsuwa ya fara takawa ya nufi cikin wajen, ga mamakinta sai gani ta yi
ƴan'mata da samari masu class da ji da kansu sun tsaya sai ɗaukarsa hoto a
wayoyinsu suke yi, saboda kyan da Allah ya yi mashi, kun san su kyawawa dik in da
suka shiga ko sun shirya ko basu shirya ba sai mutane sun yi ta ɗaukarsu hoto, wai
a hakan ma ya sanya p-cap a kansa fa, basu wani ga face ɗinsa da kyau ba, amma haka
suka rinƙa kashe mashi hotuna ta ko'ina babu kakkautawa. A nan ne wasu suka ɗauketa
ita da shi a tare, and a media suka ɗaura hotunan, shi ko a jikinsa, in da yasa kai
kawai yake tafiya cikin natsuwa, ita kuma ta damu sosai, dan tana tsoron abin da
zai iya faruwa, tana tsoron masu nikaf su gani saboda suna bibiyarsa ta kowacce
hanya.

My people's me kuke tinanin waɗan nan hotuna zasu haifar?.

Sosai ta waro idanu tana kallan yadda cikin wajen ya yi bala'in haɗuwa, sofas masu
bala'in kyau, laushi da kuma tsada, waje ne na manyan kai. Zama suka yi saman sofar
da ya zaɓa masu, sannan ya saka oder abin da yake ganin zasu iya ci, online oder
ake yi, sannan sai ka biya ta online ɗin ka yi komai za'a kawo maka, sp kana ci
zaka tashi ka tafi babu wani tsayawa yin payment, haka tsarinsu yake. Yana oder bai
fi da mintuna uku ba sai ga shi an fara shirga masu abin da ya buƙata a gabansu
saman table, dik a takure take saboda kallansu da jama'a suke yi, dik ta in da ta
juya idanun jama'a a kansu, ga uban hotuna da ake kashe masu light ta ko'ina. Zuba
mata idanu na ƴan sakanni ya yi kafin ya ce. "Ɗauki chopping stick or spoon mu ci
abinci".

Ɗago kai ta yi ta kallesa da nufin ta yi mashi gardama, amma sai ta gagara yin
hakan saboda idanun jama'a dake a kansu, kuma ya yi mata wani irin kwarjini, yau
idanunsa a kaifafe suke sosai, dan dole ta ɗauki spoon dan da shi ta saba, shi kuwa
sai ya ciro wayarsa ya fara latse latse dan baya jin kamar zai iya cin wannan
abinci, bai saba da waje ba. Tana jin yunwa over to over, dan haka sai ta fara cin
abincin a natse, sai dai kaɗan kaɗan take ci. Dik abin da take yi attention ɗinsa
yana a kanta, bcoz ta ci ta koshi ya zo da ita tun da taki ci a gida.

Ya lura ɓata masu lokaci zata yi, dan sai su wuni a wannan waje bata gama cin
wannan ɗan abinci ba, ɗan kaɗan kaɗan take ɗebowa kamar bakinta na ciwo, sai ya
ajiye wayarsa a saman table ɗin ya kai hannu ya karɓi spoon ɗin nata, cikin natsuwa
ya ɗebo abincin mai ɗan yawa ya kai mata saitin bakinta. Ɗago kai ta yi ta kallesa,
while shi ma ita yake kallah ta cikin glass ɗin nasa, bata san disga shi a cikin
mutane sai ta buɗe baki ya fara bata dai'dai san ransa, har lokacin hotuna ake
ɗaukarsu.

Yana tsaka da bata abincin ne gabaɗaya yankin gidan cin abincin nan ya karaɗe da
jiniya ta ko'ina, tamkar za'a tashi garin. Yana zaune bai motsa ba, ita kuwa
hankalinta ya tashi sosai, dan idan ba a gidan Abu Abdussalam ba bata taɓa jin
jiniya irin haka ba, a gidan Abbie kawai tasan idan za'a fita ko za'a shiga wannan
jiniya yake tashi, to waye ne kuma ya zo a yanzu?. Bata kammala tambayar kanta ba
sai ganin wasu jiga jigan jami'ai sun danno cikin restaurant ɗin a guje ta yi, ba
dan tana tare da shi kuma taga bai motsa ba da ba abin da zai hanata tashi ta gudu.
Gabaɗaya big girls and big boys dake wajen babu wanda hankalinsa bai tashi ba, babu
wanda bai ji tamkar ya tashi ta gudu ba, bare ma yanda jami'an nan suke muzurai
tamkar zasu ɗauki rayuka nan take.

Ko'ina tsit kake ji, jami'an gabaɗaya sun yi tsayuwa jarumta sun kewaye wajen
gabaɗaya, shi dai Ramish tamkar bai san da zuwansu ba, yana cigaba da bata abinci a
baki, ya lura ta tsorata sosai, dan haka sai ya yi ƙoƙarin ɗauke mata hankali daga
kansu ta hanyar tambayarta a ina ta haɗu da masu nikaf har suka bata contacts na
kashe shi?.

Tana ƙoƙarin bashi amsa wani very handsome jami'i ya danno kai ciki, he was so
cute, handsome and gorgeous, sai dai shi chocolate color ne ba balarabe bane, and
zubin Nigerians ke garesa, cikakken namiji ne mai rai da lafiya, kyakkyawa ajin
farko, very hot guy, yana da tsawo dai'dai misali, Ramish ya fisa tsawo da kaɗan.
Sanye yake cikin kakinsa, wasu zaratan jami'ai guda huɗu suna take mashi baya, kai
tsaye in da su Ramish suke ya nufo. Yana isa wajen waɗan nan jami'an da suka rakosa
suka yi gaggawar kewaye kowani angle na table ɗin da su Ramish ke kai, shi kuwa guy
ɗin haɗe kafafunsa ya yi cike da jarumta ya ɗaga hannu ya sarawa Ramish. Ajiye
spoon na hannunsa Ramish ɗin ya yi tare da miƙewa tsaye, hannu ya bashi suka yi
musaba cike da kulawa yana faɗin. "Saukar yaushe my guy?".

Sai a lokacin Leesharh ta ɗago kai cike da tsoro dan taga wanenne?. Ai bata san
lokacin da ta zabura ta zaro idanunta tana kallansa ba, kamannin dake kan face
ɗinsu har ya ɓaci, sun yi kama sosai tamkar ƴan uwa na jini, sai dai kowa da yadda
yake kallan mutum, shi ma Ramish yaga kamanninta da friend ɗin nasa, sai dai ba can
sosai ba, shi kuma friend ɗin nasa bai ma bi ta kanta ba bare har yaga ko suna kama
or akasin hakan.

Izini Ramish ya bashi a kan ya zauna mana, kun san sofas na table ɗin irin two
seater ɗin nan, ɗaya ta side ɗin nan ɗaya ta side ɗin can, table yana tsakiya, so
shi da Leesharh suna saman sofa guda, abokin nasa sai ya zauna a ɗayan shi
kaɗai. ...... Cike da mamaki guy ɗin ya ce. "My Man yaushe ka fara cin abinci a
restaurans kuma?". Cewar jami'in kenan ba.

Zama Ramish ya koma ya yi kafin ya amsa mashi da. "Ba ni zanci ba, ga wadda na
kawo ta ci nan". Ya kai karshen maganar yana nuna Leesharh da hannunsa. Sai a
lokacin guy ɗin ya lura da ita a wajen, cike da mamaki ya yi mata kallo ɗaya kafin
ya mayar da kallansa a kan Ramish, sannan ya ce. "My man wacece wannan ɗin? And I
was so surprised ganinka tare da mace, the thing looks some how to me, i never
expect that for now, amma dai nasan gaba kila in yi expecting ganinka da mace, but
now kai I was so surprised". Ya kai karshen maganar yana sake dawo da kallansa a
kan Leesharh, dan shi kansa yaga kamannin dake tsakanin fuskokinsu. Ita kam ba iya
kamanni kawai ba, gabanta ne yake faɗuwa idan ta gansa, ji take yi kamar ta san
shi? Sai dai a ina? Ita da bata san kowa ba bayan iyayenta da suka tsinceta sai
mutanen gidan AAJ, gidan aikinta ita da mamarta yanzu kuma ƴan gidan Abu
Abdussalam, su kawai ta sani.

Kai tsaye Ramish ya amsa mashi da. "She's my wife to be In Sha Allah"......
Dum!!! Dum!!! Zaro idanu guy ɗin ya yi yana kallan Ramish, sai kuma ya ɗan saki
murmushi kaɗan kafin ya ce. "Amma baka taɓa yi mun wasa ba, meyasa yau kake san yi
mun? Ka manta ka ce kai babu abin da zaka yi da mace a rayuwarka ne?". .......
Harara Ramish ya bisa da shi kafin ya ɗan saci kallan Leesharh ta wutsiyar ido,
take ya ga face ɗinta ya sauya saboda ta ji ya ce babu abin da zai yi da mace a
rayuwarsa, wato kenan dama abin banza suka ɗauki mata kenan?. Shi kuma wannan guy
ɗin bin Ramish da kallo yake yi yana jiran amsa, bai san da cewa Ramish neman
amincewanta ma yake yi taki ba, yanzu ba batu ake yi na me zai yi da mace ba tukun
nan, batu ake yi na yana neman hanyar da Leesharh zata aminta da shi.

Spoon ya ɗauka tare da fara ɗebo abincin yana kai mata ɗan bakinta ba tare da ya
sake bi ta kan abokin nasa ba, dan ya lura idan ya biye mashi zai cigaba da faɗar
maganganunsa da ya rinƙa faɗa a baya wanda kuma zai sa Leesharh ta ƙara arzuƙa ta
ki yafe mashi, zata ce dama a banza ya ɗauki mata shiyasa ya yi mata abin da ya yi
mata kenan, dan haka gara ya fiske kawai. Abokin nasa ya lura da baya san
maganganun da suka wuce, dan haka sai ya yi mashi fatan alkhairi tare da juyowa ga
Leesharh ya hau tsokanarta da sunan amaryarsu.

Ƙasa da kai ta yi tana jin gabanta na faɗuwa, har ga Allah tana jin kamar jini na
fusgarta idan ta ga face na guy ɗin.

Lokaci guda Ramish ya ji kishi sosai a kan maganan da guy yake yi mata tana amsawa,
ransa ta sosu, sai ya ce ta tashi su tafi cin abincin ya isa haka, kun san mutanen
da kishin bala'i, ya ce wa guy ɗin kuma ya wuce gida zasu haɗu zuwa dare...........
TO WANENEN WANNAN GUY ƊIN KUMA?.

Yana kai karshen maganarsa ya miƙe tsaye tare da riko hannunta, kamar zata kwace
kanta sai kuma ta daure ganin jami'ai a wajen, ta san kuma shi ba ƙaramin jami'i
bane, kada ta ja mashi raini, dan haka sai ta hakura ta biye mashi har suka fice
daga wajen, haƙiƙa ya jinjinawa halaccin da ta yi mashi, ta daure ko sau ɗaya bata
kunyata shi a idanun mutane ba, abin ya yi mashi daɗi sosai!.

Suna fita cikin wajen ta kwace hannunta, bai ce mata ko uppan ba ya shiga gaban
mota, kafin ma guy ɗin ya fito sun bar gidan cin abincin da gudu gaske.

A maimakon ya zame da ita gida, sai ya wuce da ita wajen shakatawa da wasanni dik
dan ya samu ta sauko ta yafe mashi, ranar yau gabaɗaya ya sadaukar mata, ya sanya a
ransa ba zai mayar da ita gida ba sai can tsakiyar dare, watakila zata ji sanyi a
ranta. Amma fa yasa a ransa tana yafe mashi zai mayar da ita gidan Abbie ya cigaba
da aikinsa.

To bari mu je Paris mu dawo mu bisu wajen shakatawar mu ga me zai faru a can kuma,
amma kuma tinanin Leesharh zata yafe mashi kuwa? Zai kama masu nikaf? Wani irin
hukunci zai yi wa Ummie a lokacin da zai gane ita ta cutar da rayuwarsu?.

🔥🔥🔥🔥🔥PARIS🔥🔥🔥🔥🔥

Washegari da safe babu yadda Auta bata yi da Pretty a kan ta zo su sauka kasa ba,
amma taki, ta ce wlh babu ita babu batun sauka kasa akwai damisa a wajen. Dan dole
Auta ta rabu da ita a saman ta sauka, wunin ranar dai a ɗaki Pretty ta wuni har
dare, ko abinci a ɗaki Auta ta kawo mata. Sai can dare bayan sun yi sallar
mangariba da isha'i ne Auta ta shiga toilet dan ta yi wanka, a lokacin ita kuma
Pretty ta yi wankarta, ta shirya cikin wani sleeping dress mai shegen kyau, launin
purple color, ta yi kyau matiƙa.

Yunwar dare take ji yana addabawa cikinta, ga Auta tana cikin toilet, tinai ta fara
yi a kan mafitarta, dai'dai da second ɗaya ba zata iya jurar yunwa ba. Saukowa
kasan bed ɗinsu ta yi, cike da tsoro ta nufo parlourn sama. Sai wani lallaɓawa take
yi kamar wata ɓarauniya, wai dik dan kada damisan nan ya ji sautin takunta, a
hankali ta turo kofar bedroom ɗinsu, kanta ta sako waje ta leƙo dan ta duba. Watam
parlourn babu kowa, ƙarisa buɗe kofar ta yi ta kara fito da jikinta waje da kyau ta
leƙa. Da gaske dai babu kowa babu komai, ai a miliyan ta yanka da gudu sai ɗakin
Smart.

Babu ko excuse ta afka mashi cikin ɗaki. Yana tsaye a tsakiyar bedroom ɗin rike da
wayarsa, sanye yake da haɗaɗɗen bathrobe launin up white a jikinsa, kamar sako yake
typing a cikin wayar. Da gudu ta tafi ta faɗa jikinsa tana sauke ajiyar zuciya, kun
san ta saba yi wa Kamran haka, so bata wani damu da waye shi ba. Har sai da ta buge
mashi waya ya faɗi ƙasa, dan bai yi tsammanin wani zai shigo ba, sao gata ta shigo
har da faɗawa jikinsa. Cak ya tsaya, slowly ya dawo da kallansa a kanta.
Kun san halinta da shegen shagwaɓa, tamkar zata yi kuka ta ce. "Yah Omerish yunwa
nike ji, kuma ina tsoron wannan damisan naka, ka je ka kawo mun abin da zanci dan
Auta tana toilet"....... Ai rasa abin faɗe Smart ya yi, wai shi ne zai je ya kawo
mata abin da zata ci, kai sai kace a mafarki, tab lallai wannan yarinya ta zo da
sububa a lamuranta, tana da buƙatar gyara.
Ya luluƙa duniyar tinanin me zai yi mata sai ji ya yi ya fashe mashi da kuka,
kun san halin mutuniyar, yo ita ina ruwanta da yana da izza? Ai shi ya jiyo shi da
sarautar tasu, ita dai abinci ta sani sai shagwaɓa, dan haka yunwa take ji dole a
bata abinci in ba haka ba ta yi ta kuka daga nan har wayewan gari.


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬




49




🔥🔥🔥🔥PARIS🔥🔥🔥🔥

Wani irin ratsa mashi zuciya kukanta ya yi, amma sai ya yi ƙoƙarin dannewa haɗe da
ƙoƙarin daka mata tsawa, sai dai kash, ya gagara iya rabata da jikinsa, dan ta
ƙanƙame shi gam tana kukan ita dai lallai ya samo mata abin da zata ci tin da shi
ya ajiye Tiger and Lion a gidan.
Dan dole ta tilasta mashi ya sassauta muryarsa tare da sanya hannu ya ɗan rungumeta
kaɗan, already

Please Login or Register in order to submit comment