Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 40 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da tare wa kishi
faɗa, tab abin babba ne.

Harara Mammie ta wurgawa Akka ba tare da kowa ya lura ba, a cikin ranta ta ce
shegiyar tsohuwa idan baki yi hankali ba ni ce nan ajalinki. A fili kuma sai ta
sunkuyar da kanta ƙasa tare da cewa mummy. "Kiyi hakuri".

Wato akwai iyashege a kingdom ɗin nan, wlh matan King sun san kan duniya.

Jiki ba kwari Sarina ta bar gaban Akka ta koma mazauninta zuciyarta na tafasa,
mammie ta ƙara jin ranta ya ɓaci, ta kara jin lallai dole ta mallaki kujerar
kingdom of power ko ta halin yaya ne, da yanzu ita take da mulki a hannunta ai wane
kaniyarsu su yi mata abin da suke yi mata ɗin nan.

Akka kuwa hankalinta gabaɗaya ta mayar a kan Mahnoor, like wow, she was so
surprised seen her beautiful face, abin ta bata yi expecting ba, ita kanta ta
shaida Mahnoor kyakkyawa ce, ga gyaran da ta sha, skin ɗinta har wani yellow yellow
ya yi yana wani glowing, wlh komai sanin da ka yi wa Mahnoor ba zaka taɓa ganeta a
yanzu ba, dan ta haɗu iya haɗuwa, ko makiyi sai ya jinjinawa haɗuwar da ta yi sai
dai idan ba zai faɗi gaskiya ba saboda kiyayya.

Gabaɗaya su King zuba mata idanu suka yi suna kallanta, a cikin zuciyarsa King ya
ce. Dama shi yasan dik abin da Rahilarh zata zaɓa ba abin yasarwa bane, lallai ba
shakka wannan yarinya ta dace da jaish.

Cike da matsuwa da san jin amsarsu momma ta ce. "Gwaggo (Akka) ya kuka ganta? Ta
yi?".

Shiru Akka ta yi tana cigaba da karewa Mahnoor kallo, baiwar Allah mai innocent
face. Kun san Akka fa babu ɓoye ɓoye, dan haka sai ta ce. "Wannan yarinya anya ba
zata iya zama green snake under green grass ba kuwa?".
Ɗan zaro idanu suka yi gabaɗayansu, sai dai babu wanda ya iya tambayar Akka
dalilinta.

Cigaba ta yi da cewa. "Yanayin fuskarta ya nuna shiru shiru sosai ce ita, kun san
masu irin wannan fuskar munafikai sun fi yawa a cikinsu".......... Akka tamu ta
amana.

Shiru parlourn suka yi, dan idan Queen mother tana magana ba'a katseta sai ta
gama.

Hannu ta kai ta ɗan ɗago haɓar Mahnoor, abinku da kaka, ko kunya bata ji ta fara yi
wa Mahnoor leke leke har da gane mata girman tula tulanta, tana yi tana magana
kamar haka. "Ni jikokina dik lafiyayyu ne, dan haka suna da buƙatar cikakkun mata,
sannan suna san komai ya ciko sosai, saboda gujewa zinace zinace dole mu bincika da
kyau mu samo wadda zata iya ɗaukarsu, dole na bincika masu komai".

(Nace yanzu kun gane qualities ɗin da King ya zage yake ta cewa sai mace tana da su
sannan zai aurawa ƴaƴansa ita? Kun gane irin qualities ɗin ko sai an maku karin
bayani? Su kansu sun san abin nasu na gado ne, to dai ga Akka ta buɗe komai mun ji
irin qualities da ake nema😅)

Tana magana tana sassaukewa Mahnoor alkyabbarta izuwa saman shoulder ɗinta.

(Kam bala'i, jama'a Akka duniya ce, a lallai gara ta duba masu, kai aima dole ta
duba dan tasan sun yi gadon abin,🤭 tasan wanenen King Abdul Malik kakansu kenan, e
dole ta duba aga Mahnoor zata iya ɗaukan Jaish ne ko yaya? Kai wlh wannan tsohuwa
duniya ce.)

"Shekarunki nawa?". Ta jefawa Mahnoor tambaya. Momma ce ta yunkura zata yi magana,
hannu ta ɗaga mata alamar ta yi mata shiru.

"Kada na ji bakin kowa a nan, bincike nike yi tukun nan"........ Tsit suka yi suna
sauraronta.

Baiwar Allah kanta a ƙasa cikin sanyin murya ta ce. "Ban san takamaiman shekaruna
ba, amma dai tsakanin 15 da 16 ne". Larabcin Mahnoor yana gargada,.bata kware sosai
ba.

Jinjina kai Akka ta yi, sannan ta sake cewa. "Mahaifiyarki ta sanar dake abin da
ake nufi da aure ko kuma ta barki a sake tana jiran ni in sanar dake? Kin san
menene aure? Kin san yadda ake kula da miji? Kin san kalan mijinki kuwa? Kin shirya
iya ɗaukarsa?". ........ Yau ga ikon god wajen Akka, tsohuwa zata buɗe komai fa.

"A'a bani da mama, babu kuma wanda ya taɓa faɗa mun menene aure". Tamkar
zata yi kuka ta bada wannan amsa.

Cak Akka ta dakata da ƙoƙari cire mata alkyabba da take yi, da sauri ta dawo da
kallonta a kan face ɗinta. "Ke marainiyace?". Murya cike da tausayawa ta jefa mata
tambayar.

Da e ta amsa mata idanunta suna cikowa da kwallah, nan take Akka ta ji jikinta ya
yi sanyi, Allah sarki suna da jin tausayin marayu sosai, haka zuciyarsu take,
janyota jikinta Akka ta yi, sannan ta ce. "Ya sunanki?".

Mahnoor ta bata amsa. Kwnatar mata da kanta a saman gwiwowinta Akka ta yi tana ɗan
shafa bayanta, da ɗan ɗaga murya ta ce. "Princess Mahnoor mata ga Prince Jaish
barkanki da shigowa familyn King Abdul Malik".

Haba wani irin ajiyar zuciya su King suka sauke, barema momma da ta fi kowa matsuwa
da san jin amsar Akka, tun da ta kira Mahnoor da princess shikenan ta yi na'am da
ita kenan.

Mummyn Chuchu ce ta rangaɗa masu guɗa, nan take suka hau farinciki mara misiltuwa.
Sarina and Mammie bakinciki kamar zai kashesu, barema da suka ga fuskar Mahnoor,
babu abin kushewa a tattare da ita, ga kyau kamar ita ta yi kanta, uwa uba ta fi
Fanan kyau da komai nesa ba kusa ba, kai in short basu da wani abin da zasu nuna
mata da shi, ta fi su komai, kamar Sarina zata haɗiyi zuciya saboda taya Fanan
kishi.

Wato akwai cakwakiya wlh sosai.

Kallan su King Akka ta yi, cike da bada umarni ta sanar da su ta aminta da Mahnoor,
suma tana basu umarni da su karɓeta a matsayin sirika. Cike da gimamawa suka amsa
mata da sun karɓeta hannu bibbiyu ma kuwa.

Akka ce ta buƙaci jin yadda aka yi Jaish ya haɗu da marainiyar Allah da kuma me ya
kaisa Nigeria?. Babu ɓoye ɓoye momma ta zayyana masu dik yadda aka yi. Sosai suka
kara jin tausayin Mahnoor yakamasu, nan take ran Akka ya ɓaci ta ce wlh ita ba zata
yafewa Nenne ba, dole su hukuntata azabar da ta ganawa Mahnoor, kun san basa yafe
zalinci su ato.

A fili Sarina ta yi suɓul da baka wajen cewa. "Ashe ƴan gidan matsiyata ƴan kauye
mara galihu ne ma". Bata san ta yi maganar ba har sai da taga kowa yana kallanta,
sannan ne ta farga, da sauri ta miƙe ta nufi waje tana ɓata ran wai ta ɓata
lokacinta a kallan ƴar gidan matsiyata.

Da kallo suka bita har ta fita, a nan ne King ya fahimci lallai akwai matsala idan
har basu yi da gaske ba, dole ya zauna shi da momma su tsara yadda zasu kula da
Mahnoor ba tare da wani abin ya sameta ba, idan ba haka ba zata fiskanci barazanar
kanne miji.

In short a nan aka yi komai aka gama, momma ta buƙaci iznin zuwa Jimeta a kai kayan
aure da komai da ake yi wa mace kafin a aureta. Akka da kanta ta bata izini. Suka
gama tsara komai, sannan mummyn Chuchu da momma suka miƙe suka kama Mahnoor suka
fita da ita, mama ma miƙewa ta yi ta basu waje. Mammie ce ta yi fitar karshe.

Parlourn ya rage daga King, uncle Abbas, uncle Jahiz sai Akka, tattauna suka fara
yi a kan batun, dan su san ta yadda zasu tsara komai.

Mahnoor kuwa part ɗin momma suka wuce da ita dan su kara shiryata yau za'a kaita
ɓangaren Jaish. Mahreen dai an barota a ɗakin gyara.

🔥🔥🔥BABY AND AMMO🔥🔥🔥

Zaune take a saman sofa tana fuskantar Ammo dake zaune a saman nata sofar, Ammo na
kallan Tv ita kuma tana rike da cup mai ɗauke da cappuccino tana sha, center table
dake gabanta wani ɗan madaidaicin laptop ɗinta mai shegen kyau da tsada ne a kai,
daga gefensa wasu takardunta ne tana karatun exams, na faɗa maku tana bala'in san
karatu, kuma Allah ya bata ilimin both side.

Sanye take da kayan barci masu kyau, rigace mai laushi sosai mai karamar hannu,
sai wani ɗan madaidaicin wando da bai wuce singalalin kafafunta ba, bai kai har
kasa ba. Wandan dai'dai da jikinta yake, shi kuma rigan yana da ɗan faɗi kaɗan,
tana da dirarren jiki sosai kamar dai su Pretty tamu, sai dai bata da wani tsawo
sosai, tsayinta dai'dai da shekarunta.

Tana sipping cappuccino a hankali hankali tana duba takardunta, kanta na sanye da
hular kayan barcin jikinta.
"Baby ni zan shiga in kwanta, karfe 9 ta yi, yakamata kema ki kammala karatun
nan da wuri ki je ki kwanta tun da gobe exam kuke da shi kuma da wuri zaku rubuta
ko?". Cewar Ammo.

"E exam muke da, yanzu zan kammala, saura kaɗan ne". Ta kai karshen maganar
tana ɗaura cup ɗin cappuccinonta a saman table ɗin kusa da laptop ɗinta, sannan ta
ɗauki takardanta ɗaya da take dubawa ɗin, ƙwaƙwalwarta ya ɗan ɗauki zafi, ta ƙasa
gane wannan karatu, tinani take yi ko dai ta kira babynta a waya ta ce ya koyar da
ita ne, in ya so su yi karatun ta Whatsapp kamar yadda suke yi a dik sanda wani
karatu ya gagara mata.

Ita kuwa Ammo miƙewa ta yi ta nufi dakinta tana yi mata sai da safe, da yake
ɗakinsu daban daban, sai idan baby ta yi ra'ayi ne ta je ɗakin Ammo su kwana.

Wayarta baby ta ɗauko da nufin ta kira numbersa ta sanar da shi ya hau
Whatsapp su yi karatu, sai dai bata kai ga kiranba kofofin hancinta suka jiyo mata
kamshin perfume ɗinsa, hakan yasa ta yi saurin kai kallanta a bakin kofar shigowa.

Yana tsaye ya harɗe hannayensa a saman kirjinsa, kallanta kawai yake yi, sanye yake
da wando three quter jeans white color, sai round neck polo shirts sky blue mai
shegen kyau, ya yi kyau matuƙa, da alama fitan ba shiri ya yi, duba da yanayin
dressing ɗinsa.

Zaro idanu ta yi, cike da mamaki mai ɗauke da farinciki ta miƙe tsaye, wani
ƙayataccen murmushi ne ya kubce mata kafin ta ambaci baby.
Shiru bai amsa mata ba, ya dai kafeta da idanu, idan ka gansa zaka yi zaton
gabaɗayanta yake kallah, amma bahaka bane, hankalinsa yana a kan kirjinta, da yake
bata sa bra ba, and gasu masha Allah suna tsole idanun mai kallo.......... Anya
baby ba barci ya ƙasa yi ba da ya biyo dare kuwa? To mutum dai shi ba karfe ba,
kuma shi lafiyayyen namiji, ya kai 30 years, ya zayyi ba zai ƙasa barci ba ɗazun
yaga kaya iya kaya? Kada ku ce na ce, tom gaskiya dai na faɗa.

"Baby daman zaka zo ne baka faɗa mun ba?". Cikin wannan shagwaɓa tata kamar
ta Prettynmu dai ta yi maganar.

Ɗan gyaran murya ya yi saboda ya ga kaya har muryarsa ta sarkafe taki fita. "Babu
zuwan a lissafina, dole ce ta sa unexpect ya shiga lissafina". Ya faɗa ba tare da
ya motsa daga in da yake ba.

"Dole kuma baby?". Kai ya jinjina mata alamar e........ "To waye ya yi maka
dole ka zo ɗin?". Nisawa ya yi tare da ɗan kawar da kallansa daga kan dukiyan
fulaninta, (yau dai ban ce tula tula ba saboda an saka mun ido da wannan suna nawa
mai albarka 😅)

"Kece kika tilasta zuciyata zuwa, na koma na kasa samun sukini, zuciyata ta
damu da san zuwa in ganki".

Wani irin murmushi ta saki. "Yes that is my baby, dama nima ina san
ganinka"......... A ɗan takaice ya ce. "Meyafaru kike san ganina?".

Turɓe fuaka na shagwaɓa ta yi, kamar zata saka mashi kuka ta amsa da. "Wannan
karatun ne yake bani wahala, na kasa gane komai, please kazo ka duba
mun"............. Tin da ta fara magana ya dawo da kallansa a kan wannan ɗan bakin
nata da take turowa, gabaɗaya sai ya ji shi a network, wani irin kasala ne ya
saukan mashi lokaci guda. Da kyar ya daure ya tako izuwa in da take.

Yana zuwa bai wani ɓata lokaci ba ya zauna a saman sofa yana sauke ajiyar zuciya.
Zama ita ma ta yi kusa da shi, sai a lokacin ta ce. "Ina wuni baby?"...........
"Sai yanzu za'a gaisheni my ƴan'mata?". Cikin zolaya ya yi maganar.

"To zumuɗin ganinka ya ja na manta da gaisuwar, amma yanzu na tina". Ta kai
karshen maganar tare da ɗaukar cap ɗin cappuccinonta ta cigaba da kaiwa baki tana
ɗan sipping....... Hannu ya kai ya ɗan ɗauki littafin nata ya fara dubawa.

Wani irin daɗin cappuccino nan take ji yau, dan baby ya zo. Unexpext ta ga ya sanya
hannu ya karɓi cappuccino, a hankali ya kai bakinsa ya ɗan yi sipping, sannan ya
cire, cikin nitsuwa ya fara kora mata bayani a kan karatun da bata gane ɗin ba,
yana yi yana shan cappuccinon ɗin.

Sosai take fahimtar abin da yake faɗe, dan tana san karatun. Sai da ya
tabbatar ta fahimci karatun sosai, sannan ya rufe littafin ya cigaba da ɗan sipping
na cpn ɗin.

"Baby in kawo maka wani cappuccinon ne?". Ta jefa mashi tambayar tana dawo da
kallanta a kansa. Kai ya girgiza mata tare da miƙa mata cup ɗin yana faɗin. "Wannan
ma saboda ke na sha"....... Hannu ta kai zata karɓa hannunsu ya gogi na juna, nan
take wani shock ta ratsa jinin jikinsa, har sai da ya ɗan furta ash ba tare da ya
san ya faɗa ba, sai jin shagwaɓaɓɓiyar voice ɗinta ya yi tana faɗin.

"Sorry baby". Kai ya jinjina, ta wutsiyar idanunsa yake kallanta, kallansa kuma dik
a kan tula tulanta da suka yi mugun tafiya da imaninsa. Sam bata fahimci yana
kallanta ba, sai shagwaɓa ta hau zuba mashi tana kara jefa shi cikin
saukin................

Kasa jura ya yi, out of control ya kai hannu ya janyota jikinsa, a take ya sauke
nannauyar ajiyar zuciya. Ita kuwa ta zaci abin da ya saba yi mata ne na zaman da
take yi a jikinsa suna hira, sai ta saki jiki har da ɗan ɗaura hannunta a saman
kirjinsa ta sama kusa da shoulder ɗinsa.

A hankali ya sanya hannunsa a saman bayanta, dik bata kawo tinanin komai a ranta
ba. Slowly ya zame mata hular kayan barci dake kanta ya ajiye a gefe, a hankali ya
shiga shafa lallausan black hairnta. A wannan karan ji ta yi gabanta ya faɗi, amma
bata yi ƙoƙarin hanashi ba, dan bata san ma me zata ce da shi ba.

Cikin dabara ya dawo da hannunsa saman........


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A
PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
======🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬



26




Cikin dabara ya dawo da hannunsa saman wuyarta. Wani irin al'amari ta fara ji yana
ratsata, zata tashi ya yi saurin maida ita ya kwantar, sai ya gyara mata kwanciya
ma da kyau.

"Baby dare ya yi ba zaka koma bane?". Ta faɗa tana ɗago kanta. Bai yi mamakin
jin maganar tata ba, saboda yaga tsoron abin da yake yi mata a cikin idanunta,
shiyasa ma ta nemi ya koma bayan a baya kullum ita take damuwa da ya zo.

Rinannun idanunsa da suka rikiɗe izuwa jajir ya sauke a kan face ɗinta. Ta ɗan
tsorata ganin idanunsa sun sauya launi, hakan yasa ta kara jin tana san raba
jikinta da nasa.

Ƙasa bata amsar maganarta ya yi, tamkar an ɗaɗɗaure mashi tongue ɗinsa, sai
kawai ya bita da kallo. Unexpext Ammo ta shigo cikin parlon tana faɗin. "Baby ba
zaki hakura da karatun nan sai da safe ba kuwa? Dare ya yi yaushe zaki yi barci
ba.............."

Bata iya ƙarisar da maganar ba ganin su biyu a parlon, ta yi mamakin ganinsa, da
tasan yana nan ba zata fito ba. Kunyarsa ne ya kamata.
Sannu da zuwa ta yi mashi tana ɗan ja da baya. Kallo ɗaya ya yi mata ya kawar
da kallansa, jinjin kansa kawai ya yi bai iya amsa mata ba, wai yana ɓoye halin da
yake ciki kada ta gane.

Juyawa ta yi ta koma ciki tana mamakin yaushe ya zo gidan nan? Ko karar motarsa
bata ji ba.

Ɗagowa daga jikinsa baby ta yi, a ɗan tsorace ta ce. "Baby zan je in kwanta dare
ya yi"......... Lumshe idanunsa ya yi, wannan shagwaɓa tata ta kara ratsa shi
sosai, sai ya ji ya zo har wuya.

Kasa shanyewa ya yi, a hankali ya matsar da face ɗinsa dab da ita. Zaro mashi
idanu ya yi tana kallansa da mamaki. Can ƙasan maƙoshinsa ya furta. "Can i kiss you
my baby?".

Wani irin zaro idanu da ta yi tamkar kwayar idanunta zasu faɗi ƙasa. A rikice
ta ce. "Baby kiss kuma?". Muryarta na rawa ta yi maganar.

Kai ya gyaɗa mata alamar e kiss yake nufi. A wani irin zabure ta miƙe daga jikinsa,
kafin ya yi wani yunkuri tuni ta watsa da gudu sai cikin ɗakin Ammo, tana shiga ta
tura kofa tana sauke haki da sauri sauri. Sai da ta tsorata Ammo dake kwance a
saman bed, a razane ta tashi zaune, dama bata yi barci ba, tana kwance tana tinanin
wanda za'a iya alƙanta shi da lamarin su baby ɗin.
Ganin ta gudu yasa ya yi saurin miƙewa ya bi bayanta, dan ya santa da shiririta
tsab zata faɗawa Ammo abin da ya ce mata. Yana turo kofar yasa kai ya shigo. Tana
ganinsa ta saka yar kara tare da kwasawa a guje ta haye gadan Ammo tana riko Ammo
da karfi.

Shiru ya ɗan yi yana kallanta, ita kam Ammo ta gama fahimtar komai, sai ta tuna
kamar bata fahimta ba, ta riko jikar tata tana tambayar lafiyarta kuwa. Cike da
shiririta ta fara ƙoƙarin faɗawa Ammon abin da baby ya ce mata. Sai dai bai bari ta
faɗa ba ya yi saurin cewa Ammo.

"Ɗan bamu waje bari in yi magana da ita". Ba musu Ammo ta saketa tare da saukowa
kasa. Da sauri ita ma ta sauko ta ƙanƙame Ammo tana faɗin sai dai su fita wajen a
tare.

Ɗan jinjina kai ya yi tare da cewa Ammo ta je kawai kada ta damu. Wucewa Ammo ta yi
da sauri ta rufa mata baya dan bata san tsayawa. Sun zo zasu fita ya damko baby ita
kuma Ammo ta fice. Kuka ta saka mashi mai sauti tana faɗin ya saketa bata so.

Shiru ya yi bai saketa ɗin ba, kuma bai yi magana ba har tsawon mintina 5, sannan
ne ya rungumota da kyau a jikinsa, murya ƙasa ƙasa ya ce. "Saboda na ce zan yi
kissing ɗinki ne kike wannan kukan?".

Cigaba da yin kukanta ta yi bata yi magana ba, sai dai ta kwanta luf a saman
kirjinsa....................... "To am so so sorry, ba zan sake faɗin hakan ba,
saboda ba zan so hawayenki su sake zuba ba, ya isa haka kin ji?".
Stilll shiru bata kulasa ba, sai ma ƙara kukan nata da ta yi. Ɗan rage tsawonsa
ya yi ya ɗauketa can suka fito daga ɗakin, yana jin wani irin azabbabben yanayi a
tattare da shi, amma ya daure saboda ya fin san farincikinta fiye da komai. A
tinaninsa zasu samu Ammo a parlour, sai kuma yaga akasin hakan, saman sofa ya koma
da ita a jikinsa ya zauna, rarrashinta ta cigaba da yi babu kakkautawa, tin yana
jiyo sautin kukanta a hankali hankali har ya dai'na ji, a hankali saukar
numfashinta irin na mai barci ya fara dokan dodan kunnesa, alamar ta yi barci
kenan. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗaga kansa sama ya jingina da jikin
head na sofar, a hankali ya lumshe idanunsa yana sauke ajiyar zuciya.

Ya ɗauki 20 mins a haka kafin ya dawo da kallansa a kanta haɗe da sauko da kansa.
Ai ina, ta jima da yin barci har barin ya yi nauyi. Nisawa ya yi tare da miƙewa da
ita cikin dabara, ya ɗauketa cak sai bedroom ɗinta. A saman kyakkyawar bed ɗinta ya
kwantar da ita, ya janyo mata bargo ya lulluɓeta izuwa dai'dai cikinta, a gaban bed
ɗin ya tsuggun dai'dai saitin face ɗinta, kasa kasa kamar mai raɗa ya ce.
"Rigimamma kawai, to yanzu ba ga shi kin yi barci ba?". Ya yi maganar yana kallan
ɗan bakin nata.

A hankali ya dawo da kallonsa a saman kirjinta da gabaɗaya tudunsu suke a waje
saboda yanayin kayan jikinta da yanayin kwanciyar da ta yi. A hankali ya ɗan haɗiyi
yawu kamar wani da ya ga abin kwaɗa yi. Ajiyar zuciya ya sauke, a hankali ya kai
hannunsa jikinta, hannun nasa sai wani kerma yake yi. Wuyar rigar tata ya ɗan ja
mata sama, sannan ya ɗan sunkuyo da kansa a kanta. Sumbata ya manna mata a baki.
Ɗan motsawa ta yi kamar tana san farkawa.

A hanzarce ya miƙe kaman maras gaskiya, da sauri ya nufi switch na ɗakin, kashe
mata wutar ɗakin ya yi, da sauri ya fice kamar zai kifa ƙasa. Bai zame ko'ina ba
sai cikin motarsa, ko da ya shiga ya kasa jan motar ya tafi, ya ɗauki good 30 mins
a wajen yana ƙoƙarin controlling na feeling ɗinsa kafin ya iya driving.

Da kyar ya iya tada motar da gudun gaske ya nufi gate, da yake gate ce mai amfani
da na'ura, da kanta ta buɗe kanta ya danna waje da gudun gaske. Ammo tana tsaye a
windown bedroom ɗinta dake fuskantar harabar gidan tana kallansa har ya tafi,
sannan ta nufo ɗakin baby. Kamar yadda ya barta haka ta sameta, addu'ar barci ta zo
ta yi mata dik da tana da yakinin ya yi mata, dan ya saba yi, sai dai bata san yau
kansa ya ɗauki zafi bai yarda ba ya tafi.

Bayan ta gama yi mata addu'ar ne ta fito ta wuce nata bedroom ɗin, ta koma saman
bed ɗinta ta kwanta cike da tinanika kala kala a ranta.......... ASUBA TA GARI.

🔥🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥🔥

"Haulat bani waje bari in yi magana da ita". Cewar Momma kenan, tana san ganawa da
Mahnoor wanda bata yi hakan ba ko sau ɗaya, so yanzu tana san su gana. Zaune suke a
bakin bed ita da Mahnoor ɗin, Mahnoor kanta a ƙasa.

Miƙewa mama Haulat ta yi cikin girmamawa ta ansa da to tare da nufar hanyar fita.
Har ta kai tsakiyar ɗakin sai ta tsinkayo muryar momma tana faɗin. "Nan da 2 hours
ki turo mun Mahreen".

Da okey mama Haulat ta amsa sannan ta fice waje. Dawo da kallanta a kan Mahnoor
momma ta yi, hawaye bibbiyu ne a face ɗinta, da alama ta tina maraicinta yasa take
wannan kuka. Janyota jiki momma ta yi ta hau rarrashinta, cike da kauna ta ce.
"Kada ki ɗaukeni matsayin sirika, ki ɗaukeni matsayin uwa". Ta kai karshen maganar
tana goge mata hawaye.

Shiru Mahnoor ta yi tana jinjina halacci irin na momma, zamanta da mama Haulat
na satin ɗayan nan har ta koyi wasu abubuwa masu muhimmanci.

"A matsayina na uwa a gareki zan yi maki nasihar zaman gidan miji, ki nitsu ki
saurareni da kyau, dan a bisa dokarmu a ɓangaren mijinki zaki kwana yau, nan da
sati biyu masu zuwa zamu je jimeta, da naso mu je gobe, amma akwai wasu dalilan da
yasa sai next two weeks, akwai saye saye da za'a kawo daga Dubai, sai mun haɗa
komai zamu tafi, gobe ya yi kusa".

Jinjina kai Mahnoor ta yi tana sauke ajiyar zuciya, tabbas tana jin momma
tamkar mahaifiyarta, tana kaunarta sosai ita ma.

Cikin sanyin murya momma ta fara magana kamar haka. "Ki dage da hakuri da biyayya.
Aure yana buƙatar hakuri da juriya. Ki kasance mai biyayya ga mijinki, kuma ki guji
nuna rashin kunya ko rashin girmamawa gare shi. Ki kula da addua da ibada. Ki dage
da addu'o'i don neman zaman lafiya da albarka a gidanku. Ibada za ta taimaka muku
wajen samun kwanciyar hankali. Ki zama mai tsafta da ƙyalli, Haulat zata koya maki
kwalliya sosai. Ki kula da tsaftar jikinki, gidanki, da tufafinki. Mijinki mutum ne
mai jin daɗi idan ya ga matar da ke da tsafta kuma tana jan hankalinsa, yana da
kyankyani ya tsani ƙazanta, a kan kanwarsa ƴar autarsu ya fahimci hakan, dan in ta
yi kwalliya wuni yake yi yana yabonta baya gajiya, so yana san kwalliya sosai. Ki
koyi maganar mai daɗi da ta dace da shi, dan yana san magana cikin kulawa. Ki guji
faɗar kalamai masu zafi ko cin fuska. Kalaman kirki suna gina soyayya kuma suna
rage duk wani rashin fahimta. Kula da sirrin gidanki da mijinki. Kada

Please Login or Register in order to submit comment