Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 2 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a duniyar yanzu ba.

Dikkansu ya zuba masu idanu yana kallo har jirgin ta yi leading, wasu
zaƙwaƙuran manya manyan Robbot ne suka fara kutsawa izuwa gaban jirgin, sai kuma
wasu jiga jigan motoci masu ɗauke da sunan Black Tiger irin masu container a
bayansun nan suka ɗan matso kusa da jirgin.

Wasu Robbot ɗin ne suka zo suka hau bubbuɗe bayan containers ɗin, empty suke babu
komai a ciki.

Ana buɗe Fp na jirgin Robbot da suka matsa kusa da shi suka kutsa ciki. Wasu jiga
jigan manya manyan caton masu ɗauke da hoton motoci a jikinsu waɗan nan Robbot ɗin
suka fara fitowa da su daga cikin jirgin. Girman waɗan nan kwalaye sun wuci mutane
su iya ɗauka sai dai Robbot ɗin. Yanzu fa kusan manya manyan ayyukan Black world
dikka Robbot ne suke yi.

Wanna jirgi maƙare yake da kayan billions of dollars, gabaɗaya kayan kyara sabbin
motoci masu rai da lafiya ne. INA MASU CEWA BLACK TIGER YANA BURGESU TA ƁANGAREN
GYARA KASARSA DA TAIMAKAWA WAJEN GANIN YA KAWO DIK WASU SABBIN TSARE TSARE DA ZATA
KAWO MASHI CIGABA? TO A NAN DAI KUN YI GASKIYA, BAKU FAƊI BA DAN KUN SO SHI TA NAN,
DAN FA BA KARYA YANA IYA ƘOƘARINSA WAJEN GANIN YA GINA KASARSA, BURINSA SU FI
KOWACE KASA CIGABA DA KOMAI DA KOMAI, MATSALARSA DAI WANNAN BAKAR ZUCIYAR TASA TA
ZALINCI NE KAWAI, BAREMA RABA UWA DA ƳAƳA DA YAKE YI, ABIN AKWAI TAƁA ZUCIYA.

Kafataren companynsa na kyara motoci za'a kai waɗan nan kaya domin a fara haɗa
motoci sabbi wanda babu irinsu a duniya, a kullun yana son yaga shi ya fara kirkiro
abu in ya so daga baya saura ƙasashe su kwaikwayesa, wannan yasa ya yi dogon nazari
kafin ya fito da tsarin motocin nasa.

A kallah containers sun kai 50 a wajen, amma sai da suka cika tab da kayan nan
da Black Tiger aircraft ta ɗauko.

Wani irin ajiyar zuciya ya sauke ganin dik abin da ya buƙata sun sauka lafiya, a
hankali ya mayar da kallonsa a kan masu hakar gold, yadda yake kallonsu ya ɗan zare
sharp eyes ɗin nan nasa sai ya baku tsoro, kamar ba idanun mutum ba, da alama magic
eyes ɗinsa ya juyo ba na ainahin ba.

Wani daga cikin warriors dake hakar gold ɗin ne ya miƙe tsaye tare da ihu yana
faɗin.

"Red gold, red gold!!".

Ɗan kara zaro idanun Black Tiger ya yi. "Red gold!". Ya maimaita kalmar.

Ga dikkan alamu ya ji daɗin samun red gold a karkashin kasan kasarsa da suka yi,
red gold shi ne abu na biyu a tsada a duniya cikin Precious stones and mentals,
yana da bala'in tsada fiye da tunaninku, ga balai'n daraja, ya fi normal gold tsada
nesa ba kusa ba, samun wanna red gold ɗin a karkashin kasar birnin Black Tiger ba
karamar nasara bace, a yanzu haka suna da dukiyar iya karawa da kowace kasa bare
kuma ace sun kara samun arzikin red gold? Me kuke tunanin zai faru? Wani irin
arziki kuke tunanin Black world ko in ce Black Tiger zai kara samu?. Duniya iya
duniya wa Black Tiger fa my people's.

Sosai ya ji daɗin wanna karuwa da suka samu, sai dai babu ko ɗikon alamar
canji daga face ɗinsa da zai sa ka fahimci ya ji daɗi, yana nan yadda yake kamar
hadari.

A hankali ya juyar da idanunsa daga magic eyes izuwa ainahin sharp eyes ɗinsa.
Kamar walkiya haka ya ƙarisa bakin wanna daular bed ɗin nasa duniya guda. Zama ya
yi da alamar nazari ya shiga a kan yadda zai kara bunƙasa kasarsa, yadda zasu ci
moriyar wannan red gold ɗin.

P-R-I-N-C-E-S-S T-E-E-M-A💘🔥
___________💘🔥______________

A bangaren Sweetie and Ronnie kuwa, yana jan ta bai dakata a ko'ina ba sai a room
ɗinsa.

Suna shiga ya saki hannunta yana sauke ajiyar zuciya kamar wanda ya sha da kyar, ko
da yake kusan hakance da kyar suka sha.
Ita kuwa room ɗin nasa ta fara bi da kallo tana mamaki ganin kusan komai dake
room na Black Tiger irinsa ne a nan, hakan na nufin Ronnie fa ɗan gata ne na
karshen kasasheshe.

Ganin ba shi take kallo bane yasa ya miƙa hannu ya janyota ta faɗo jikinsa yana
sauke ajiyar zuciya. Da sauri ta ɗago kai tana kallon face ɗinsa, while shi ma ita
yake kallo babu ko kyaftawa, an jima ba'a haɗu ba, ya sha kewarta matuƙa.

"Ronnie meyasa baka je wannan ɗaki da yayankan nan ya ajiyeni ka dubani ba? Ka
barni ni kaɗai sai wani mugun mutum da yake zuwa tambayata wai ina Spender? Idan
ban gaya mashi ba sai ya yi ta azabtar da ni yana bani wahala, ranar har maciji ya
saka mun........".
Ta dakata da yin maganar tana sauke numfashi tana ƙoƙarin fara kuka.

Bai iya ce mata ko uppan ba saboda har lokacin yana ganin kamar Black Tiger bai
kyaleta bane, yana ganin kamar zai zo ya rabasu.

"Wani ɗaki wannan mugun ya kaini, ɗakin babu hanya kuma dik in da ka juya sai
kaga kanka, (kewaye yake da mirror kenan) a wannan ɗaki ya sakani sai ya turo mun
wani bakin maciji mugu, dik ta in da zan gudu sai in ga babu hanya sai dai hoton
fuska zan gani, ga macijin shi kuma yasan hanyan sai ya yi ta bina, ina ta ihun
sunanka kuma baka zo ba.............".
Tana kai karshen maganar ta fara ruwan hawaye masu ɗumi, wato kenan
dama azabtar da ita Black Tiger ya rinƙa yi da ya ɗauketa, ya yi ta razanata, Allah
sarki wlh razana tafi zahirin mugunta cutarwa da wahalar da zuciya, wani ma idan
yana da karamar zuciya mutuwa zai yi idan aka razanar da shi, Allah gara a maka
azaba direct a kan ayi ta razanaka da ababen ban tsoro. Wato Black Tiger ainahin
bakin mugu ne da babi mix wlh, yasan sirrin mugunta da azabtarwa.

Hannu Ronnie ya kai ya fara goge mata kwallar dake idanunta ba tare da ya yi
magana ba, saboda shi dai yasan Black Tiger baya yafiya, bai taɓa yafewa kowa ba a
rayuwarsa, ya kware wajen yi wa mutane azaba da wuta, so sai yake ganin kamar zai
zo ya raba shi da ita.

"Ronnie ka yi magana mana". Ta faɗa yanayin voice ɗinta a shagwaɓe sak na
PRETTY yau kuma.

Jinjina mata kai ya yi, can kasan makoshinsa ya furta. "Zan yi magana Sweetie, amma
ba yanzu ba, for now dai kyaleni ki yi shiru".

"To yunwa nike ji fa". Ta faɗa tana ɗan kwantar da kanta a wannan faffaɗar
kirjin nasa na ƴan Wrestling ɗin.

Da sauri ya ɗago kansa haɗe da kallonsa a kanta.
"To hau saman bed ɗina ki zauna bari in kawo maki abincin ko?". Da kyar ya
iya furta hakan.

Da okey ta amsa mashi tare da wucewa ta nufi saman luntsumemen bed ɗin nasa, har
tsoron haurawa taji ya kamata, gani take kamar idan ta hau zata jita a sama.

Idanunsa a kanta, bai fita ba yana jiran ta haura bed ɗin sannan ya fice. Da
yaga kamar ba zata iya hawa ba sai ya ce. "Ki hau babu abin da zai faru".

Da sauri ta juyo da idanunta a kansa, kai ya jinjina mata alamar tabbatarwa da babu
abin da zai faru. Da sauri ta haye ta zauna, sai da ta ɗan lumshe idanunta ta sake
buɗewa saboda daɗi da laushin mattress na bed ɗin, ga wani kamshi na musamman mai
kwantar da hankali dake tashi a arear wajen.

Juyawa ya yi ya fice daga room ɗin, ita kuma ta fara bin ko'ina da kallo tana
mamakin yadda komai yake a shirye tsab gwanin ban sha'awa da ɗaukar hankali, ga
fitinannen kamshi mai sanya nutsuwa a zuciya, lallai yanzu ta yarda da zancen
Floris da take ce mata Ronnie shi kaɗai ne kanin Black Tiger, kuma ɗan gata ne, a
yanzu ta gasgata hakan matuƙa.

Shiru ta zauna tana sakawa da warwarewa a cikin kwakwalwarta har ya dawo cikin room
ɗin hannunsa ɗauke da katon glass tray mai shake da kayan abinci tab a ciki,
abubuwa kala kala wanda bata taɓa ganin makamantansu ba.

Saman glass center table dake tsakiyar wasu egg chair a can gefe ya ɗaura kayan
abincin, a ɗakin Black Tiger swan sofa chairs ne, a ɗakin Ronnie kuwa egg chairs
ne, sunanan kamar design na kwai ne a ka fafake cikinsu aka yi wajen zama, sun yi
matuƙar tsaruwa sosai.

"Zo in baki ki ci sai ki yi wanka mu je ki rakani". Ya yi maganar yana kai
kallonsa a kanta.

While ita ma shi take ta kallo, sai yanzu ta lura da ya rame kaɗan ya kuma kara
hasken fata, kamar wanda ya jera kwanaki yana zazzaɓin dare.

"Ina Floris?".
Ta jefa mashi tambayar tana saukowa daga saman bed ɗin.

Sai a lokacin ya tuna yau bai haɗu da ita ba, ya je school ya rubuta last exams
ɗinsa ya dawo, yana dawowa kuma wajen yayansa ya wuce domin ya gaya mashi ina
Sweetie take, a kan haka suka samu matsala ya fita ɗakin a fusace, zaman da ya yi a
cikin cineman part ɗin yasa ya samu sanyi a zuciyarsa da har yasa ya miƙe ya dawo
wajen Black Tiger domin ya bashi hakuri sai ya sameta a ciki.

"Ya ka yi shiru baka bani amsa ba?".

Ta yi tambayar ne a kusa da shi, bai ga lokacin da ta sauka bed ɗin ba, saboda
ya afaka duniyar tunani.

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "I don't know where's she, amma nasan ba zai
wuce she's in her room or Delisha room ba".

Yana kai karshen maganar ya miƙo mata hannunsa a kan ta kama.

Ba musu ta saka ƴan hannayenta saman tafukansa, har ga Allah tana jin daɗin
kasancewa a tare da shi.

Kamata ya yi ya zaunar da ita saman lallausan duma dake shinfiɗe a wajen, sannan ya
sauko mata da trayn haɗe da tambayarta me zata ci.

Zubawa abincin idanu ta yi tana kallonsu, bata ma san menene bane bare har ta iya
zaɓa, nama kawai ta sani wannan ma dan wanda yake taimaka masu a forest yana kawo
masu nama sosai, so tun kafin ta makance tasan ya kamannin namar yake.

"Ko dai in zaɓa maki ne?".
Ya yi magana idanunsa a kanta.

Ɗago kai ta yi suka kalli juna. "Ni fa Ronnie ban san waɗan nan abubuwan ba, amma
dai ka bani naman ya fi tun da shi nasani".

Tun da ta fara magana ya kafe ɗan bakinta da idanu yana jin wani irin shaukin yadda
take motsa laɓɓanta wajen furta word, har ji ya yi baya son ta dakata da yin
magana.
"Namar jimmina ce da ta ɗawisu, sannan akwai ta ɓauna, wanne zaki ci".

Yadda ya yi maganar sai ya burgeku, saboda idanunsa a kan lips ɗinta ya yi, kuma ya
yi maganar kamar wanda bakinsa yake ciwo.

"Dik abin da ka lissafan nan ban sansu ba, ni dai nama kawai na sani".

Hannu ya kai saman tray ɗin ya ciro mata wani haɗaɗɗe tsadadden plate mai shake da
namar ɗawisu wanda ya ji gashi mai kyau, sai tashin daddaɗar kamshi yake yi ya ji
kayan haɗi.

"Kin ki ki faɗa mun sunanki na ainahi ko Sweetie?"
Yana magana yana ɗauko kananan wukake haɗe da fork domin ya taimaka mata wajen
yanka namar ta samu ta ci.

Ɗan siririn murmushi ta saki har sai da dimples ɗinta suka lotsa kafin ta ce.
"Sunana na ainahi Sweetie".

"Ba gaskiya bane! Sweetie ba suna bane".

Shiru ta ɗan yi, wani zuciya yana ce mata ta faɗa mashi gaskiya, ta yarda da shi,
shi ɗin ba mugu bane, wani zuciya kuma yana gaya mata kada ta yarda da shi, dan mom
ɗinsu ta gargaɗesu a kan kada su yarda da kowa a duniya idan ba Kamran ba!.

"Don't restrict yourself, in baki son gaya mun ba sai kin sha wahalar tuna abin
faɗa mun dan in ji daɗi ba, don't worry, a dik yadda kike zan ji daɗin kasancewa
dake, so forget about the name, yanzu karɓi abinci ki ci".

Ya yi maganar ne bayan ya saita mata fork mai ɗauke da gasashen namar ɗawisu a
saitin ɗan bakinta.

Sosai ta ji wani irin a jikinta na jin furucinsa, jikinta ya yi sanyi, bai kamata
ace ya nemi sanin wani abin dangane da ita ta ɓoye mashi ba, amma ya zata yi to?
Dole ta bi umarnin mom ɗinsu.

Buɗe ɗan bakin nata ta yi ya saka mata namar, suna aikin ganin juna ido cikin ido.

"Ka yi rashin lafiya ne Ronnie?".

Kai ya girgiza mata alamar a'a, sannan ya ɗaura da cewa. "Me kika gani?"

B komai ta bashi amsa tana ƙoƙarin ɗauko ruwan roba dake cikin tray ɗin. Hannu yasa
ya karɓi ruwan tare da ɓalle mata bakinsa, sannan ya zuba mata a tsadadden glass
cup da ya zo da shi.

"Yau zaki bini church ko?".
Ya yi magana yana miƙa mata ruwan.

Karɓa ta yi ta kafa a bakinta, kusan rabi ta sha kafin ta cire, tana ƙoƙarin
ajiyewa a kasa ya kai hannu ya karɓa, bakinsa ya kai ya shanye ragowar tare da
ajiye cup ɗin ya zuba mata idanu tana taunar namar da ya bata bayan ta cire cup
daga bakinta.

"Mu bama zuwa church ai".

"Why?". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce. "Coz I am a Muslim".

"Komai nace maki sai ki ce mun baki sani ba, to ya aka yi kika san church kika kuma
san banbancin addininmu?".
Ya jefa mata tambayar yana ɗaga mata gera ɗaya, har lokacin idanunsu a kan
face ɗin juna.

"Saboda shi abu ne wanda ya shafi addini, ko ban san church a ido ba na karanta
labarinsa a litattafanmu na addini".

Ɗan zaro idanu kaɗan ya yi kafin ya ce. "Okey kenan in na fahimta addininku ya yi
magana a kan namu?".

Jinjina mashi kai ta yi haɗe da cewa. "Kamar yadda ainahin littafin addininku yake
magana a kan musulunci ba".

Ɗan girgiza kai ya yi. "Ban gane ainahin littafinmu ba? Ko so kike ki ce yanzu ba
na ainahi muke amfani da shi ba?!".

Haɗiye namar dake bakinta ta yi kafin ta amsa mashi da. "Kusan hakance, ainahin
littafinku ai annabinmu ne ya zo da ita, kuma magana take a akan musulunci da
dokokin Allah da dai sauransu, amma yanzu gabaɗaya an canza littafin da rubutun
cikinsa, masu son zuciya tun tsawon shekaru da suka gabata sun canza wasu abubuwa,
a hankali hankali suka rinƙa zare wasu shafuka masu muhimmanci daga ciki, suna
shigo da na san zuciyarsu dan su ɓatar da alumma, haka mom ɗinmu ta ce mana".

Tun da ta fara magana idanunsa yake a saman laɓbanta babu ko kyaftawa, sai dai
kunnuwansa suna saurarenta da kyau, ƙwaƙwalwarsa kuma yana jujjuya mashi zantukan
nata, lallai ba shakka ta zo da babban al'amari, ya za'ayi ta ce an canza masu
littafi? Ƴar karama da ita da wanna zancen, lallai so take ta jawa kanta bala'i,
dan kuwa ba zata iya wanna faɗar ba!!.

Sai da ta dasa aya a maganar ne ya sauke ajiyar zuciya tare da ajiye fork na
hannunsa, sannan ya ɗan gyara zama kaɗan.

"Addininki ne ya ce maki an canza wasu shafuka cikin littafinmu ko kuma littafinku
ne ya ce hakan?". Ya jefa mata tambaya.

"Ko ɗaya daga ciki, ba addinina bane, hasalima ni addinina kyakkyawar zato yake yi
wa kowa".

"To ya akayi kika san and canza littafinmu domin a cigaba da gusar mana da hankali
muna tafiya a kan ɓata?".

A gaskiya Ronnie yana da saukin kai sosai, kuma ga dikkan alamu yana bala'in jinta
har cikin ransa sosai ne yasa har ya iya jure maganganunta, kun san ba kowa zai
yarda acewa da littafinsa da kuma malaman da yake bi haka ba, ba wanda zai yarda a
ƙaryata malamansa ko kuma ace suna cutar da mutane wajen canza maganar gaskiya
izuwa ta karya, amma shi cikin kwanciyar hankali yake yi mata tambayoyi ta hikima
haɗe da ilimi, gaskiya ilimi ta yi a rayuwa, tana sanya iya magana da zama da kowa
lafiya sosai, jahili yake faɗace faɗace ba mai ilimi ba!.

"Zan gaya maka yadda aka yi na sani, zan kuma baka hujoji masu karfi da zaka
yarda dani, amma sai na koma wajen mu tukun nan, dan dik hujojin suna forest
ɗinmu".

Shiru ya ɗan yi yana tunanin yadda za'ayi ta bar empeir ɗin nan har ta je ta bashi
hujojin, ga shi yana son waɗan nan hujoji ko dan ya gani da ido, to me abin yi? Dan
dai Black Tiger ba barinta zai yi ta tafi ba tare da ta bada Spender ba!.

"Zaka taimaka mun na bar nan?".

Tambayarta da ya ji takmar saukar aradu kenan, har sai da ya ji kansa ta ɗan juya
mashi tana wani sarawa.

Idanunsa a cikin nata bai iya bada amsa ba, dan bashi da ta cewa.

"Ronnie ina kewar ƴar uwata sosai, ina son komawa forest domin in je in ganta,
please ka taimaka mun na bar nan ka ji?".

Tamkar zata sanya kuka ta kai karshen maganar.

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ɗan jinjina mata kai haɗe da cewa.
"Zan taimaka maki ki bar nan kamar yadda kika buƙata, amma da sharaɗi guda biyu,
idan kika mun abubuwa guda biyun nan tabbas zan fitar dake daga nan koda kuwa hakan
zai zama sanadiyyar mutuwata!!"....... BABBAR MAGANA!!.

A hanzarce ta ce. "Menene sharaɗin? Ka gaya mun kome ne zan yi".

Cigaba da yanka mata namar ya yi yana faɗin. "Zuwa dare zamu yi wanna magana,
zan gaya maki sharaɗin, yanzu dai ci abinci ki je ki yi wanka".

Bata yi mashi musu ba, dan ta lura musu yana ɗaya daga cikin abin da baya so, tun
zuwanta empeir ɗin ta fahimci hakan a tsakaninsa da su Floris, dan haka sai ta yi
shiru tana karɓar namar da yake bata har sai da ta ƙoshi.

Sannan ya rakata toilet ɗinsa da kansa ya fito ya barta a ciki, ta yi tsaye tana
ganin ikon god, duniya guda kamar ba za'a mutu ba.

Shi kuwa ya dawo ya kwashi kayan abincin ya nufi waje da su.

Yana fitowa babban parlourn kasa ya isko Floris ta ci kwalliyar sexy dress, ta yi
kyau sosai, ɗan rigarta a iya cibiya ya tsaya mata, sai sket da bai gama rufe
gwiwanta ba black color, rigar kuma white, da yake in baku manta ba mutanen birnin
Black world suna da yelwar tsawon gashi sosai kamar turawa, haka ta sake dark brown
hair nan nata har baya, sai sheki yake yi yana curlyn.

Ɗan bakin nan nata ya sha lips balm sosai sai sheki yake yi, ta ɗaura kafa ɗaya
bisa ɗaya tana rike da wayar Ronnie tana latsawa, ta yi kyau irin sosai ɗin nan.

Tun da ya sako kafarsa a saman stair case ɗin yake binta da kallo har ya karisa
saukowa. Jin motsin mutum yasa ta yi saurin ɗago kanta da kallonta a kansa.

Ganin shi ne yasa ta mike har da haɗawa da ɗan gudunta ta nufesa. Buɗe mata hannu
ya yi ta faɗa saman Wrestling chest ɗinsa.

Tana faɗawa jikinsa wani Robbot ya kariso wajen ya karɓi kayan abincin dake
hannunsa ya juya ya nufi hanyar kitchen da shi.

Shi kuwa kamar wata ƴar tsana haka ya ɗagata sama sai saman shoulder ɗinsa suka
juya izuwa sama.

"I really missed u mine". Ta faɗa tana saƙalo wuyarsa.

Yau yana cikin farinciki ya ga Sweetie kuma Black Tiger ya barsu a tare, hakan ba
ƙaramin farinciki ya haifar mashi ba, cikin sanyin murya ya amsa mata da.

"Missed u too babydoll".

Ɗan bakinta ta kai saman lallausan kumatunsa ta fara sumbata tana goge mashi lips
balm dake saman lips ɗinta.
"Zaki fara ko?".
A shagwaɓe ya yi maganar.

"Ba kai ne ka barni sai da na yi missed ɗinka sosai sanna ka waiwayeni ba?".

Yana cigaba da tafiya ya nufi room ɗinsa ya gangaro da ita izuwa saitin wrestling
chest ɗinsa, ya zama suna kallon juna. Fingerprint ya sanyawa door room ɗinsa ta
buɗe ya shige ciki da ita yana ta kallon face ɗinta.

Saman bed ya sauƙeta, kamar mai jin barci ya furta. "Ki taya Sweetie ta sanya kaya
ta shirya ina zuwa".

Ta ɗan yi mamakin jin yadda ya yi maga a kasale sosai, ta san shi ɗin shagwaɓaɓɓe
ne idan ya yi ra'ayi, sannan tasan riƙaƙƙene ta ɓangaren iya kalaman soyayya, amma
bata taɓa jin ya yi magana a irin wannan yanayi ba, bata san cewa yanzu ya fara
girma yana jin feeling sosai bane, da ai sai dai ya yi dik abin da zai yi na
shagwaɓarsa baya jin komai, amma yanzu girma ta fara zuwa, ya fara amsar sako.

Bai jira amsarta ba ya juya ya fita. Bai zame ko'ina ba sai room ɗin Black
Tiger.

After some minutes. Ya fito sanye da sport wears ya nufi room ɗinsa.
==========🔥🔥🔥===========




ALKALAMIN

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️




‫ ِإَّنَك َحِميٌد‬،‫ َكَما َصَّلْيَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫الَّلُهَّم َصِّل َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬
‫ ِإَّنَك‬،‫ َكَما َباَرْكَت َعَلى ِإْبَراِهيَم َوَعَلى آِل ِإْبَراِهيَم‬،‫ الَّلُهَّم َباِرْك َعَلى ُمَحَّمٍد َوَعَلى آِل ُمَحَّمٍد‬،‫َمِجيٌد‬
‫️❤َحِميٌد َمِجيٌد‬




*Ina yi wa ɗaukacin al'ummar musulmi murnar shiga sabuwar shekara ta 2025, Ubangiji
Allah ya sadamu da alkhairan dake cikinta, Allah ya nisantamu da sharrin dake
cikinta, Ubangiji Allah ya shiga lamuranmu ya kawo mana zaman lafiya da kwanciyar
hankali a kasarmu da ma dikkanin in da musulmi suke, ya Allah yasa mu cika da kyau
da imani ya kuma kara mana kaunar manzon rahma manzon tsira.*




Wani birki ya ja a bakin kofar room ɗin ta ciki, idanu ya zaro waje yana kallonta,
tamkar kwayar idanunsa zasu faɗi ƙasa. Sam bai san lokacin da bakinsa ya furta wow
ba.

Like wow, ni ma dai sai da na furta wannan wow ɗin a lokacin da idanuna suka sauka
a kan Sweetie sanye da kayansa na sport, kun san shi mayen wasanni ne, yana da dik
sport wears na wasanni kala daban daban.

Floris da iya tsiya sai ta bata riga da wandonsa na football ta saka, wandon ya yi
mata tsawo sosai, rigar kuma da yake roba ce kuma sababbi ne bai sakasu ba bare
faffaɗar wrestling chest ɗin nan nasa ya buɗesu sai ya ɗan kamata kaɗan. Floris ta
gyara mata golden white hairnta tare da sanya mata mayukan gyaran kansa, gashin ya
yi bala'in kyau sai sheki yake yi, yanzu ne ma tsantsar kyan gashin ya kara bayyana
da ya samu gyara, wlh kamar ka kwace gashin dan kyansa, dole ashe ya zama mafi
tsada a duniya, ashe haka yake da balai'n kyau, gyara ne dama bai samu ba.

Kasa ƙarisowa cikin ɗakin ya yi, kawai ya harɗe hannu saman kirji yana binta da
ido, dik sai ya ji wani irin wahalallen kasala ya kama shi.....................

"My ka shigo mana".
Cewar Floris dake dake mashi saman bed kamar wata matarsa, ita kuma Sweetie
tana tsaye gaban mirrorsa tana ganin kayan yadda ya dace da ita, sai a yau ta
tabbatar da ashe kyakkyawa ce ita fa, ta mace da kallon kanta.

Jin Floris ta yi magana ne yasa Sweetie juyo da kallonta izuwa door room. Ganin shi
ne yasa ta saki cool murmushi har sai da dimple ɗinta suka lotsa.

Hakan ba ƙaramin kara jan hankalinsa ya yi ba, sai ya ji shi a wata duniya.

"Ronnie na yi kyau?". Cikin sanyin murya ta yi maganar.

Jinjina kai kawai ya yi bai iya furta uppan ba, saboda ta yi mugun tafiya da
tunaninsa, yama rasa me zai ce.

Kara faɗaɗa murmushinta ta yi, ta ji daɗin ya ce ta yi kyau. Floris dai binsu da
kallo take yi tana ta sakin uban murmushi abinta, da alama ta ji daɗin kasancewarsu
a tare.

"Sweetie wai ke bakya shiga damuwa ne?".
Cewar Ronnie, bai yi zaton zai ga murmushi a kan face ɗinta ba, saboda a
tunaninsa wannan wahala da ta sha zai sa dik wani sauran farinciki da ya rage mata
ya kau daga fuskarta.

"Meyasa zan shiga damuwa Ronnie?". Still akwai murmushi a saman face ɗinta ta
bada amsar. Ta yi maganar tana jingina bayanta da jikin mirror.

"Naga kin sha wahala ne shiyasa, a tinanina zaki shiga damuwa a kan hakan, kuma
ga ƴar uwarki bata a tare dake, dik da haka baki shiga damuwa a kan hakan ba!".


Please Login or Register in order to submit comment