Reading RAWANIN ZALINCI STEP 3 NA FATEEMA ZAHRA MUSA Chapter 65 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mashi birninsa dan baya san ganin datti ko wani jini
jini or gawarwaki ko kaɗan, dik gawarwakin da suka mutu a jefasu cikin ramin da
za'a haƙa dan kona waɗan da suka juya mashi baya, daga karshe ya ce yana da buƙatar
mutanen birnin waɗan da ba su juya mashi baya ba da su hallara a gaban fada nan da
kwana uku!!!.

Wani irin zabura Ronnie ya yi ganin wannan umarni da yayan nasa ya kaddamar,
hankalinsa ne ya yi mummynar tashi, da umarni ɗaya Black Tiger zai sa a kona mutane
sama da dubu biyar? Kuma a konasu da ransu, kai wannan hukunci ta munana sosai, kun
san yanzu musulunci ta ratsa zuciyar Ronnie sosa, da a baya ne ko mutane nawa Black
Tiger zai sa a kashe baya damuwa, da kalma ɗaya Black Tiger yake sawa a tashi kauye
guda daga cikin kauyukan birnin, a gaban Ronnien an sha bada umarnin kashe mutum
sama da dubu kuma baya wani damuwa, amma yanzu sai ya ji ina wlh ba zai iya ɗauka
ba, hankalinsa a tsakanin tashe ya ce.
"Yaya please ka yi masu afuwa tun da babu yadda zasu yi da kai, kasan ba zasu
yi nasara a kan ka ba, ka yi hakuri ka kyalesu kawai". Muryarsa na rawa ya yi
maganar.

Sweetie ce ta bi Ronnie da kallo tana san karin bayani, dan bata fahimci komai
ba. Kallanta shi ma Ronnie ya yi, cike da tashin hankali matuƙa ya kora mata
bayanin abin da Black Tiger ya yanke. Innalillahi wa inna ilahir rajiun, shi ne
abin da ta furta kafin nan cikin fitar hayyaci ta ce. "Saboda me zaka kashe rayuka
masu tarin yawa haka? Saboda sun bijire umarninka? Ko dan saboda suna neman ƴancin
kansu? Saboda suna ƙoƙarin gujewa mulkin injustice ɗinka?! Saboda suna nemanwa
kansu sauki? Shi ne zaka sanya a konasu da ransu? Shin waye ya baka izinin kashe
rai? Ko baka san cewa ba kai ka haliccesu bane? Ko baka san cewa mahaliccin waɗan
nan rayuka ya yi hani da kashesu ba ne? Ko baka san cewa kai ma ka bijirewa
mahaliccin bane shiyasa suma suka bijire maka? Kana tinanin kashesu shi ne mafita a
gareka? To ka saurara ka ji hukuncin dik wanda ya kashe rai daga nan sai ka san a
wani matsayi kake. Allah maɗaukakin sarki a cikin suratul Hijr surata 15 aya ta 29
ya bayyana yadda ya halicci mutum daga turɓaya kuma ya busa mashi rai, ka je ka
karanta wajen dan kasan menene ma rai da kuma yadda aka samar da shi. Haka zalika
cikin suratul tin sura ta 95 aya ta 4 Allah maɗaukakin sarki ya ce. Lalle ne mun
halicci mutum cikin mafi kyawun sura daga halittuna, darajan ɗan adam ya fi dikkan
sauran halittun Allah!! Allah ya bayyana a bayyane cewa kashe rai ba tare da
dalilin da ya cancanci kisa ba haramun ne, cikin suratul isra'i Allah ya ce kada ku
kashe rai wanda Allah ya haramta, sai dai bisa haqqi. Wanda aka kashe ba bisa hakki
ba, hakika mun ba wa magajinsa iko na neman hakkin ransa, amma kada ya wuce gona da
iri a kisan, domin hakika wanda aka kashe ba bisa haqqi ba shi an taimake shi ne"

Kazalika a cikin Suratul Ma’ida sura ta biyar 5 aya ta 32 Allah ya sake yin magana
a kan haramcin kashe rai. Allah ya yi gargaɗi mai tsanani ga al’umma da suke kashe
juna da zalunci, a cikin Suratul Baqara sura ta 2 aya ta 195, manzan Allah ya ce
kisa yana ɗaya daga cikin manyan zunubai".

Da alama tashin hankali ya rufe mata idanu da take zazzaga mashi waɗan nan karatun,
ta mance a in da take, a wannan karon shi ma Ronnie sam bai yi gigin hanata ba, dan
burinsa ta kowacce hanya su dakatar da Black Tiger daga kashe waɗan nan mutane,
shiyasa ya kyaleta ta faɗa mashi girman Allah ko zai saduda ya hakura zuciyarsa ta
sanyaya.

Sai dai kash, kamar babu alamar saduda a tattare da shi, dan kuwa babu alamar
zatukanta sun ratsa ƙwaƙwalwarsa, sai ma juyawa da ya yi ya cigaba da yin abin da
yake yi, babu alamar mutanen birnin zamu samu koda kwayar zarra na sassauci daga
garesa.
Ganin hakan yasa suka kara shiga tashin hankali matuƙa, Ronnie ya shiga damuwar da
har idanunsa sai da suka ciko da kwallah, ita kuma Sweetie a cikin zuciyarta ta sha
alwashin yau ko mutuwa zata yi sai da ta mutu amma ba zata barshi ya cigaba da
wannan bakin zalinci na CROWN OF INJUSTICE ɗin ba, yanzu ne lokacin da zasu rinƙa
fito na fito da shi dan faɗa mashi gaskiya sai dai komai zai faru ya faru, dik wata
rufa rufa da tsoro yanzu zasu ajiye a gefe su yi shahada su yi fito na fito.

Dan haka tana ganin bai wani saurareta ba ya cigaba da yin aikinsa a matsayin ta
shiga tsakaninsa da laptop ɗin, hannayensa dikka biyu ta riko cikin nata, tsabar
tsoro sai kerma jikinta yake yi, amma tausayin mutanen birnin ya rufe mata idanu a
in da ta zaɓi mutuwa dan cetonsu. Cikin dakiya ta ce. "A gaskiya ba zaka kashe kowa
ba big bro, ya isa haka nan, zunubin da ka kwasanwa kanka a baya shi muke ƙoƙarin
ganin ka tsarkaka daga shi, dan haka Allah ba zaka sake kwasanwa kanka wani zunubi
ba, dan muna kaunarka!". A wannan karan cikin sanyin murya ta yi maganar, dan ta
lura dik wasu tada jijiyoyin wuyarta a banza yake tafiya, shi Black Tiger ma wlh
idan ka yi mashi magana cikin natsuwa da tausasa kalamai ka fi cin riba a kansa
sama da idan ka ɗaga murya, in ka ɗaga murya ma ai sai dai ka ci azaba a hannunsa
ba dai riba ba.

My people's me kuke tinanin zai faru? Black Tiger zai janye kudurinsa a kan
mutanen birninsa kuwa? Zai yafe masu? Shi da Sweetie da Ronnie waye zai yi nasara?.
Muje zuwa.

🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥

Washegari da safe, sai almost karfe 8 Ramish ya iya farfaɗowa daga sumar da ya yi
bayan wannan aika aika da ya aikata, yana gama samun natsuwa dama ya sume kwance
kusa da ita. Bilal ya buga wayarsa tun da daɗin rai har ya fara shiga tashin
hankali, ya ƙasa zaune ya kasa tsaye, dan haka gari na wayewa ya fita gidan da
sunan ya je nemansa, ko kaɗan bai kawowa ransa cewa Ramish na sama ba, sai ya yi
waje nemansa.

A lokacin da ya farfaɗo ji ya yi jikinsa tamkar ba nasa ba, gabaɗaya ya canza,
kansa ne take sara mashi tamkar zata fashe, wani irin jiri yake gani sosai, da
alama har yanzu maganin nan bata gama sakinsa gabaɗaya ba bawan Allah, idanunsa
tamkar wuta saboda ja, har lokacin jijiyoyin jikinsa a tsaitsaye basu koma sun
kwanta ba, arab hairnsa tamkar wanda aka kwato daga bakin kura, gabaɗaya a hargitse
yake, idan ka gansa sai ka tausaya mashi, shi ma kenan, to ina ga Leesharh kuma? Ya
kuke tinanin zata kasance?.

Ya sha madarar mamakin ganin babu tufafi a jikinsa, ɗan waige waige gefensa ya
fara yi, ai a miliyan ya zaro idanunsa waje lokacin da ya ga Leesharh kwance a
gefensa cikin jini, ga sofar da suke kai ɗin fara ce tas, hakan yasa gabaɗaya jini
ya yi kaca kaca da waje. Dafe kansa dake barazanar tarwatse mashi ya yi, idanunsa
ya datse gam, take ƙwaƙwalwarsa ta fara tariyo mashi abubuwan da suka faru daren
jiya. Tsab ya tina komai, innalilahi wa inna ilahir rajiun shi ne kalmar da ya
rinƙa maimaitawa a ransa, ya maimaitata ya fi sau hamsin a in da yake zaune, tamkar
wanda ya yi mangaribar jemage, lokacin guda jikinsa ta yi mugun sanyi, da karfi ya
dafe forehead ɗinsa, wani irin ihu ya kurma da karfi wanda bai san dalilin yinta
ba, ga dikkan alamu zafin da zuciyarsa ta ɗauka ne yasa hakan.

Dama na faɗa maku dik ihun da za'ayi a cikin wannan ɗaki na waje ba zai iya ji ba,
bangon wajen tamkar soundproof yake. Miƙewa tsaye ya yi, yana tangal tangal tamkar
wanda ya sha barasa ya bugu ya nufi gaban computers dake wajen, da kyar ya iya
ƙarisawa wajen, hannayensa dikka biyu yasa ya dafe dest ɗin, wani irin huci ya fara
fitarwa da karfi karfi, numfashinsa na fita da wani irin ɗumi mai ban tausayi.

(Abin akwai ciwo gaskiya, ace tin da ka taso baka taɓa zina ba, baka taɓa sha'awar
yinta ba, hasalima kyamatarta kuke yi, rana tsaka ka tsinci kanka da aikatata! Wlh
dole ya ji zafin hakan, yanzu ya zai yi? Da wani ido zai ganta? Shin zai iya gane
me ya janyo mashi aikata hakan? Idan ya gane wani mataki zai ɗauka? Shin zata yi
mashi uzuri ta yarda ba halinsa bane?.)

Ƙwaƙwalwarsa ce ta sake tariyo mashi yadda ya haikewa yar mutane a daren jiya,
take ya tuno kalamanta da take faɗin. "Yah Ramish kada ka yi mun irin wannan
hukunci, ka yi mun dik abin da kake so da ya danganci azabtarwa, amma dan Allah
kada ka rabani da mutumcina, wlh ni marainiya ce da bani da kowa, bani da iyaye,
mutuncina shi ne kawai abin da ya rage mun mai daraja a tattare da ni, ka dubi
girman Allah kada ka lalata mun rayuwa, ni ban karɓi wannan aiki saboda na cutar da
kai ko wani abin makamancin hakan da gangan ba".

Tana kuka hawaye sharɓa sharɓa tana kora mashi waɗan nan jawabin. Ai hankalinsa ne
ya kara tashi, ransa ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, cikin fitar hayyaci yana huci ya
sake kurma ihu da karfin gaske, cikin zafa yasa hannun da karfi ya fara watsi da
gabaɗaya computers dake wajen, da karfi ya ɗaga dest ɗin mai gabaɗaya ya yi watsi
da shi komai dake kai suka zube ƙasa suka tarwatse watsa watsa, dunkule hannunsa ya
yi ya fara bugun jikin bangon wajen da karfi karfi yana huci har sai da ya yi raga
raga da yatsun hannunsa ya jiwa kansa ciwo, gwanin ban tausayi ya zube gwiwowinsa a
kasa a wajen tare da haɗe kansa da jikin bango, a dik lokacin da ƙwaƙwalwarsa ta
tina mashi cewa Leesharh ta gansa tsirara kuma har ya yi abinga da ita sai ya ji
tamkar ya rataye kansa, ya ji kamar ya yi ta buga kansa da bango har sai rai ya yi
halinsa, zuciyarsa na azalzala mashi da ya yi ajalin kansa kawai, sai dai shi ɗin
mai addini ne yasan hukuncin wanda ya kashe kansa.

Lokaci guda mugu mugun tausayin Leesharh ya rufesa, kalamanta dake yawo a cikin
kansa shi ne cewa da ta yi marainiya ce ita, hakan yasa ya ji wani irin kululun
bakinciki ya tokare mashi maƙoshi, da kyar ya miƙe tsaye hannunsa na zubar da jini,
in da take ya nufa har lokacin yana tangal tangal kamar zai faɗi.

Kallo ɗaya ya yi mata ya yi saurin kawar da kansa, kasancewar babu tufafi a jikinta
sannan gata cikin jini. Gabaɗaya ya ji ya tsani kansa, Innalillahi wa inna ilahir
rajiun. Shiru ya yi ya rasa madogara, dan kuwa ko kayan da zai saka a cikin wannan
ɗaki babu, wancan kayan nasa kuma ya yagesu gabaɗaya ya zubar. Ya jima tsaye a
wajen saboda rashin madogara, daga karshe dai ya laluɓo wayarsa can kusa da
computers da ya farfasa, Allah ya cecesa wayar bata yi komai ba.

Uban tilin miss calls ya samu wanda ciki na Bilal ya fi na kowa yawa, ga na Ummie
da ta yi ta kiransa daren jiya dan jaraba, wai so take ta tambayi ina yake sai ta
je ta same shi, bata san a lokacin baya duniyar nan ba, yana can duniyar mercury.
Sam bai bi ta kan miss calls ɗin ba, number Sharifat kawai ya laluɓo ya dannawa
kira. Bugu ɗaya ta ɗauka, cikin kuka ta yi mashi sallama, yau karon farko a
rayuwarsa ya ji faɗuwar gaba ta riskesa, tamkar yasan me Sharifat take yi wa kuka,
wato ta nemi Leesharh bata ganta ba, kun san tun daren jiya take nemanta.

Daurewa ya yi ya yi ta maza wajen cewa. "Ki je bedroom ɗina ki ɗauko mun pjs set
biyu ki kawo mun wajen stair case na ɗakin bincikenmu dake sama, ki ajiye mun a
wajen ki tafi". Yana kai karshen maganar ya yi gaggawar katse kiran dan ma kada ta
kawo mashi zancen dalilin kukanta, dan yasan kwanar zancen.

So ba karya ba, tana bala'in sonsa hakan yasa ta iya gane baya cikin kwanciyar
hankali da natsuwarsa, ta tabbatar yana cikin tashin hankali daga jin voice ɗinsa,
dan haka ita ma nata hankalin ne ya kara tsananta tashi, ta rasa ina zata sanya
ranta ta ji daɗi, ga shi ta tambayi Ummie ko taga Leesharh Ummie ta ce mata kada ta
sake yi mata batu kan Leesharh, gabaɗaya ta rasa wanda zata je wajensa ta ji sanyi
a ranta, Abbie baya nan ya fita. Miƙewa ta yi jiki ba kwari ta fito waje, da yake
tana cikin tashin hankali sai bata wani damu da ta yi tinani a kan me Ramish zai yi
da pjs har set biyu ba, kawai ta nufi bedroom ɗin nasa.
Shi kuma wurgi ya yi da wayarsa tare da kifa kansa da jikin sofar da Leesharh ke
kwance tamkar gawa, sai wani irin zufa ce take keto mashi, gabaɗaya face ɗinsa
tamkar wanda aka watsawa ruwa......... 10 mins tsakaninsa da kiran da ya yi wa
Sharifat ya miƙe ya ɗauki short ɗinsa ya maida jikinsa, sannan ya nufi wajen romote
na stair case ɗin. Jikinsa dik rashin kuzari, da kyar ma ya iya danna romote ɗin
stair ɗin ta yi ƙasa. Allah sarki yau sai ga Ramish da leƙa waje wai dan zai sauko
ƙasa, leƙawa ya yi domin ya duba akwai mutane ko babu, jikinsa har tana ɗan kerma.

Ganin babu kowa yasa ya yi zafin namar saukowa kasa ya ɗauki kayan da ta ajiye
mashi kamar yadda ya buƙata, a gaggauce ya koma sama kirjinsa na harbawa da sauri
sauri. Yana haurawa ya naɗe stair case ɗin sama, sannan ya hau ware set ɗaya ya
sanya a jikinsa, jikin nasa ma ta wani sassa dikka jininta ya yi mashi wanka. Yana
gamawa ya wuce da set ɗaya zuwa in da take. Dan dole ya ɗaura idanunsa a kan aika
aikan da ya yi domin ya sanya mata kayansa. Dik da sun yi mata yawa haka ya sanya
mata, sauri sauri ya kai hannunsa saitin bugawar zuciyarta ya ji tana raye ne ko
dai ba'a iya fyaɗe abin ya tsaya ba har da kisan kai ya yi?.

Jin kamar kirjin nata na bugawa can kasa kasa ya sa ya yi gaggawar miƙewa tsaye ya
saɓata a saman shoulder ɗinsa, kai tsaye ya nufo ƙasa da ita, har lokacin hannunsa
na zubar da jini, da kyar ya iya naɗe stair case ɗin sama. Kai tsaye bedroom ɗinsa
ya nufa da ita, yana shiga ya mayar da kofar ya rufe tare da murza key, dan ko
Bilal bai yarda ya san abin da ya faru ba, shiyasa ma bai kaita A&E ɗinsu ba ya
wuce da ita bedroom ɗinsa kai tsaye, a cewarsa zai rufe kayansa shi kaɗai, a cikin
kwakwalwarsa ya fara tinanin ko dai ya yi mata allura manta komai ya shafe mata
kwakwalwarta ne?. Wani zuciya ce ta ce mashi zai tabka manyan laifuka guda biyu
kenan, idan ya yi mata hakan ya gama cutarta duniya da lahira, zata manta kowa ta
manta komai, dik wasu mutane masu mahimmanci a rayuwarta zata manta su? Kai ina
wanna babban zalinci ne, wani ɓangare na zuciyarsa ce ta amsa mashi da kai tin da
asirinka zai rufu ai kawai kada ka wani damu da dik abin da zai faru, dama ai
marainiya ce bata da kowa, dan haka kayi mata alluran kawai.

My people's kuna ganin yiwa Leesharh allura da zai yi shi ne mafita a garesa? Shi
ne zai sa asirinsa ya rufu? Ko shi ne zai sa komai ya wuce? Idan ya yi hakan kuna
gani ya kyauta mata kuwa? Ya yi mata adalci? To muje dai zuwa.

A saman bed ɗinsa ya shinfiɗe ta tare da ɗauko remote ya kashe A.c, a
gaggauce ya fito ya rufota a cikin ɗakin, kai tsaye ya wuce A&E, dik wasu abin da
yasan zai buƙata ya haɗa a cikin A box sannan ya ɗauko ya dawo bedroom ɗinsa, sake
kulle kofar ya yi, a gaggauce ya hau yi mata aiki dan kada a rasata.

A lokacin da yake yin wannan aiki a lokacin shi kuma Bilal ya dawo daga yawon
nemansa, sai ya nufi ɗakin binciken nasu domin ya shigar da number Ramish ɗin a
cikin computers ɗinsu ya yi traking na number dan ya ga in da ɗan uwan nasa yake.
Ya sha madarar mamakin ganin yadda ɗakin ta yi watsa watsa, computers ɗin dik anyi
raga raga da su, sai dai bai damu da fashesu da aka yi ba, dan yasan babu wanda zai
yi wannan aiki sai Ramish, damuwarsa ɗaya shi ne meyasami ɗan uwansa har ya fashe
masu kayan aiki haka?. A gaggauce ya juya ya nufi bedroom na Ramish.

A dai'dai lokacin Ramish yana kan yi wa Leesharh allura, turo kofar ya yi da nufin
ya shigo sai jinta ya yi a datse, hankalinsa ne ya tashi sosai, knocking ya fara yi
dan yasan akwai mutum a ciki, idan ba ku manta ba shi ne ya yi na karshen fita
ɗakin daren jiya, so yasan bai rufe da key ba, dole Ramish ya dawo yana ciki kenan.
Cike da tashin hankali yake knocking, amma shiru Ramish bai ko ɗago ya kalli
door ɗin ba. Bilal na ƙoƙari juyawa ya bar wajen dan ya je ya tambayi Abbie ko
yasan wani abin dangane da Ramish daga jiya zuwa yau kwatsam kallansa ya sauka a
kan jinin hannun Ramish da ya ɗiga a wajen, ai hankalinsa ne ya kara tashi, take ya
kara tabbatarwa da kansa ba lafiya ba, dole yasan me yake faruwa, sake sake daban
daban ne cike a cikin ransa a kan Ramish.
Baya ya koma da karfi yasa karfi zai ɓalle kofar, wata iriyar duka ya kaimata,
jijjiga kofar ta yi amma bata ruguje ba, sake yin baya ya yi ya zo da karfi ya daki
kofar da shoulder ɗinsa, nan ma jijjiga ta yi bata ruguje ba. Sai a karo na uku ne
kofar ta ruguje ƙasa, cikin zafa ya afka cikin ɗakin kirjinsa na harbawa da sauri
sauri, yana ta raba idanu game da zarosu yana tinanin ta ina zai kalli ɗan uwansa.

Shi kuwa Ramish da iskanci ya gama cika mashi kai dik abin da Bilal yake yi yana
jinsa, bai taka mashi birki ba kuma bai yi niyyar buɗe kofar ba, dan haka ko da ya
rugujeta ya shigo ma ko ɗagowa ya kallesa Ramish ɗin bai yi ba, ya cigaba da abin
da yake yi kawai.

Me kuke tinanin zai faru kenan? Shikenan Bilal ya gansu? Asirin Ramish zai tonu
kenan ko yaya? Shin Bilal zai fahimcesa ya yi mashi uzuri ya rufa mashi asiri
kuwa?............. To azimi ya zo ina gab da tafiya hutu, shiyasa nike san leƙa
maku kowani part dan kusan halin da ko'ina suke ciki kafin mu tafi hutu, dan haka
mu leƙa kingdom of power mu dawo.


🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥

Tafiya take yi tana ɗan ɗingisa kafafunta zata je part ɗin mama, bata gama warkewa
daga jibgar da Smart ya yi mata ba, cikin daren ta fito dan ta je wajen maman Yah
Ramish, kun san Sarina da mama suna shiri sosai, tana tafiya tana latsa wayarta
tana ɗan turo baki, still dai tana cikin wannan karuwan shigar nata na sleeping
dress. Alamar bata daku da kyau ba, dan babu alamar nadama a tattare da ita.

Dai'dai zata shiga part ɗin mama ita kuma Mahreen tana fitowa daga part ɗin
momma zata je wajen mama Haulat a part ɗin Jaish. Tana fitowa suka ci karo da
Sarina. Baya kaɗan ta yi tare da bankawa Sarina wani irin matsiyacin kallo na uku
saura kwata kafin ta ce.
"Amma ke dai dabba ce ko? Dan naga dabobi ne suke tafiya basa ganin gabansu,
suna sukuwa dik in da kansu ya nufa". Ta yi maganar tare da riko waist ɗinta da
hannu bibbiyu, irin dai yadda take cin uwar sabada a kauye idan aka taɓota. Yanzu
larabci ya fara zama sosai a bakinta, rashin mutum sabo take karowa, dan ta fara
wayewa, infact kallan kauyawa marasa hankali ma take yi wa Aneesa and Fanan, gani
take basu san me suke yi ba tun da basa kwalliya.

Amma kuma tana matuƙar girmama Chuchu saboda ɗaukar wankarta, kun san
mutuniyar da shegen san kwalliya, idan kana kwalliya ai biyayya zata yi maka sau da
kafa ku zauna lafiya ka koya mata yadda ake yi, akasin haka kuwa ka gurji rashin
kunya da rashin mutunci daga wajenta.

Mamaki ya hana Sarina yin magana, kallonta ta fara yi from head to toe, yau
rashin kunya da fitsara ne suka haɗu waje guda. Wani irin faɗuwar gaba Sarina ta ji
a lokacin da taga face ɗin Mahreen, dan ta ganta kyakkyawar gaske, gata yar
siririya zubin turawa, komai dai masha Allah, ta sako kayan barcinta masu kyau, a
daren ma sai da aka yi kwalliya, ai yanzu tun da ta iya kwalliyar nan kowa sai ya
sarara mata, dan na safe daban na rana daban da dare daban, yanzu ta zama mace mai
class kamar Chuchu tamu ta amana.

Ita kuwa Mahreen tana wannan girgiza tana binta da harara, wai a hakan ma ta
raga mata ne dan ta ɗan yi simple make up a face ɗinta, shi ne ta samu rangwame, ba
dan haka na masifar da Mahreen zata yi mata sai ya fi hakan.

Takaici yasa Sarina ta cire hannu ta zabga mata dalleliyar mari mai tsada, dan a
cewarta bata da lokaci ɓata baki a kan yarinyar da bata wuce tasa bulala ta yi mata
dukan mutuwa ba, dama ga takaicin Mahnoor ta kwacewa Fanan Jaish ya cika masu
zuciya, sai ta nemi sauke hakan a kan Mahreen.
Aikuwa tana saukewa Mahreen wannan mari ta yi tsalle ta dira ta ce idan Sarina ta
isa Allah ya kasheta, wlh bata ga mai hanata rama marin nan ba, Sarina bata yi
zatan zata yi yunƙurin rama marin ba shiyasa bata wani kauce daga gabanta ko ta yi
wani yunƙurin ba, unexpext ta ji saukar hannun Mahreen a face ɗinta ta dalla mata
mari mai tsadar gaske, ji kake tass da karfin tsiya, kai tsabar Mahreen ta kware a
faɗa ma sai da ta daka tsalle ta buɗe hannunta da kyau kafin ta dalla mata marin.

Ai wani irin baya baya Sarina ta yi tamkar zata faɗi kasa ta yi gaggawar dafa
bango, har wani jiri ta gani yana ɗebanta, ta maru ba karya, lokaci guda ta ji
kamar wadda aka ɗaura a saman fanka yana juyawa da ita. Mahreen kuwa ko da ta rama
marin bata tsaya a iya nan ba, cikin jajjagen masifa ta ce. "Waye ubanki da har
zaki mareni in kyaleki? Wlh kin yi kaɗan, kin ci karya kin kwana da yunwa, shegiya
mai kirar akuyoyin Nenne".

Kunsan a kauye haka suke cewa idan suna faɗa, sai su ce waye uban mutun da zai
dakesu ba zasu rama ba? So kalaman bala'inta na kauye ta yi amfani da shi a kan
Sarina, dan ita bata ɗauka ma wani kalmar azo a gani bane, kawai faɗarsu na yara
take faɗen hakan, ita kuwa Sarina wani irin mugun zafi kalmar ta yi mata, wai waye
ubanta, lallai yana da kyau ta gwada mata uban nata kuwa.

A fusace ta cakumo wuyar kayan barcin jikinta da nufin ta naɗa mata ɗan banzan
duka, to kun san a ɓangaren faɗa kam dai su Sarina kifin rijiya ne, babu wayon
faɗa, basu iya faɗa da hannu ba dan ba yi suke yi ba, a barsu dai da faɗa da baki
nan suka fi kauri, ita kuwa Mahreen ta yi dambe da mazan kauye ma bare wata Sarina,
dan haka tana cakumo mata wuyar riga Mahreen ta yi kasa kamar wadda zata yi sujjada
kawai ta finciko kafar Sarina da karfi, kan kace me sai ga Sarina ta zube ƙasa
wanwar kafafu a buɗe, ɗaya ya yi can ɗaya ya yi can.
Tana ganin ta faɗi kasa ta yi gaggawar haye ruwan cikinta, yadda dai ta yi
wa ƴaƴan ɓoɗejo bogaza, haka ta haye kan Sarina ta hau kai mata duka a kirji kan
tula tulanta. Ba shiri Sarina ta fara ihun neman taimako, yau ga wadda ta fita hau
ai.

Ai tana wannan ihu kamar tana kara ingiza Mahreen ne, hular kayan barcin dake kanta
Mahreen ɗin ta ciro ta cusawa Sarina a cikin bakinta da ta wage take ihun, wai dan
ma kada ta tara mata jama'ar gidan bata gama cin ubanta ba a zo a rabasu, dama
Sarina ba karfi ba, yanzu kuma ga rashin lafiyar dukan da tasha bata gama warwarewa
ba, hakan yasa ta gaza iya kwatar kanta, Mahreen ta rinƙa kaiwa tula tula naushi
abinta, ga shi ta tura mata hula a cikin baki ba halin yin ihu.

A dai'dai wannan lokacin guyson ya zo giftawa zai je part na Mommarsa dan yaga
Mahreen ɗin, yau

Please Login or Register in order to submit comment