https://chat.whatsapp.com/FdvabUKwybz6ogMKtgx02w
*🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
Page 1️⃣1️⃣
Ta kalli Fatima ta sake kallon Aliyu dake zube a gaban wayarta. Amman ta kasa magana.
“My bad”
Ya furta sannan ya kashe wayar, hotunan da Fatima ta tura masa ta duba a lokacin ne ta sake kallon Fatima cikin tsawa ta ce.
“Me ma'anar hakan? Ina kika san shi? Ina kika samu number shi?”
A nan kuma ta kwashe labarin komai ta fadawa mahaifiyarta, babu abun da ta boye ko ta manta tun daga farkon haduwarsu har zuwa yau.
“Amman na fada miki ki daina magana da mutanen da baki sani ba, miye amfanin abun da kika yi, baki san manufarsa akanmu ba, bayan ganinsa da nake a kamfanin nan ban san waye shi ba, ban san halinsa ba”
“Cewa yayi ya sanki”
“Meyasa baki bari na gabatar miki da shi ba? Kin taba ganin na nuna miki shi ko na masa magana? Kin taba ganina tare da shi...”
Ta sake daka mata tsawa har tana mikewa tsaye kamar zata dake ta, Fatima ta razana sosai ta matsa baya tana fashewa da kuka.
“Sorry Momy”
Ta dafa kanta ya juya ta juyo gaba daya ta tsoro kamar wata marar gaskiya, can kuma ta koma ta zauna ta dauki wayarta ta aika masa da sako.
“Me kake nufi da abun da ka saka yata ta aikata? Me kake nema a yanzu? Bayan korar da kuka min yanzu kuma wani sherin kuke neman bina da shi?”
Ya duba sakon amman be bata amsa ba, kuma da alama be shirya yin hakan ba.
“Kana wasa da rayuwarka ne yaro, baka san waye ni ba, kuma bari na fada maka idan wani abu ya same ni ko ya samu yata sai ka yi nadamar zuwanka duniya”
“Boy? Huh? Hmm”
Ya rubuto mata as reply. Kana ya rubuto mata.
“Mutumen da ya fada min halinki ya fada min babu ruwanki da fitina, amman naga akasin haka, bana nufinki cutar da ke, mu musulmai bama cutar da kowa, kawai ina nemi yarinyarki ta turo min hotunanki ne saboda tantance Aisha da Emily, ina son na san banbancin wacan mai kibar da ke, ina son na gane banbancin wacan marar masifa da kuma ke”
“Waye kai?”
Ta mike tsaye tana kallon wayar gabanta na bugawa da mugun karfi. Hoton Turhan ya turo mata.
“Kin san waye wannan?”
“Aa”
Ta amsa da sauri gumi na karyo mata, sai ta kashe data ta goge chat din ta jefar da wayar akan gado, ta fara safa da marwa cikin dakin kamin hawaye su samu matsugunni a fuskarta. A nan ta fara tambayar kanta? Waye wannan mutumen tun farko? Meyasa yake bibiyar yarta da ita kanta? Yanzu kuma da ya turo mata hoton Turhan me yake nema a gareta? A kokarin samun amsoshinta ta sake daukar wayar ta bude data sai kuwa ta ci karo da sakonsa.
“Meyasa kike boya? Meyasa kika boyewa yarki gaskiyar cewar tana da uba? Why?”
Ta kasa bashi amsa jikinta rawa yake kamar yadda zuciyarta ma take rawa.
“Baki san yarki ta yi farincikin ganin mahaifinta? Baki taba tunanin samarwa yarki iyali ba? Kiran sunanta da ake da Fatima Aisha Emily be taba damunki ba? Idan yarki ta girma ta mallaki hankalin kanta wane irin amsa zaki bata?”
Nan ma bata amsa masa ba.
“Turhan yana ta nemanki babu dare babu rana, yana ta neman hanyar haduwa dake, wata kila baki san da hakan ba, amman yana da kyau ki hadu da shi ko dan yarki”
“Ba kasan komai akan rayuwata ba, baka rayu a cikin duhun da na rayu ba, har yanzu ban gama warkewa daga ciwon da zan bukaci kowane namiji a kusa da ni ba, balle kuma Turhan, ba ni da alaka da shi, alakarsa da yata kuma na yanketa, daman be san da ita, idan ya saka shiga rayuwata da rayuwar yata ne saboda ya san halin da nake ciki, to ka fada masa Aisha da ya sani a da ba ita ce a yanzu ba, kuma kar ya kuskura ya tunkaro gurin da nake”
“Ban riga na sanar masa ba, amman zan sanar masa a yau?”
“Sanar da shi zai jefa rayuwarka da tawa da tasa a matsala ne kawai, karka aikata hakan, karka jefa ni a matsala, ina da yara har biyu yanzu, kokarin gina rayuwa nake, karka maida ni a kangin da na fito, ina da kudi enough zan biyaka ko nawa kake so, zan nika maka abun da ya baka dan Allah karka sanar masa, ina son yata ina son rayuwata, farincikina kankane karka barar da shi”
Tana rubuta masa sakon tana hawaye.
“Na miki kama da mutumen da za a biya kudi a aikata wani abu? Ke kina ganina kin na girmi talauci, duk abun da kike takamar kina da shi, ina takama da ninsa sau dari”
“Amman kace kai musulmi ne?”
“Yes haka ne, babu shakka”
“Ina hada da Ubangijinka Ubangijin gaskiya, da Manzon Allah ( S A W) yace ranar tashin alkiyama Allah baya magana da mutum uku har da wanda aka hada shi da Allah be aikata ba, na roke ka dan Allah dan Allah karka fadawa Turhan komai akaina, idan kuma har ka fada masa to ka canja, dan darajar Manzon Allah S A W na san indai kai musulmin kwarai ne ba zaka aikata ba!!!”
Bayan wannan sakon bata sake aika masa wani ba, shi ma be sake cewa komai ba, ta aje wayar ta mike tsaye hawaye na cika mata ido har suna zuba ta fice daga dakin ta nufi dakin Fatima da tunin ta fice daga dakin na mahaifiyarta bayan ta fahimci nufinsa abun da ta aikata babban laifi ne.
Emily ta tura kofar dakin sai ta tsaya daga bakin kofa tana kallon Fatima dake kwance akan gadonta tana kuka, ta fara takawa tana tafiya jiki babu karfi, wayen da suke zubo mata a yanzu sun sha banban da na farkon. Jinjirar yarta take jangowa tana tuna lokacin da farinciki da kuma kishiyarsa suka lullube a rana daya, ranar da ta haifi Fatima, ta dauki cikin yarta ta yi rainon cikin ba tare da sanin Turhan ko danginsa ba, ta raini yarta irin rainon da bata fatan ko makiyinta ya fuskanci rayuwar data fuskanta, ta tuna lokacin da Nurses suke fadar a kawo kayan jaririya, kuma aka rasa abun da za a lulluba mata sai da wata ta taimaka mata da zane daya, ta tuna tsawon kwanakin da Fatima ta dauka a hannunta tana lullubeta da zane saboda babu tufafi.
Ta tuna yadda ruwan nononta yake kafewa saboda yunwa har sai da ta saci nonon akuya ta shayar da yarta, ta tuna yadda ruwa yake dukanta a rumfar wani bakanike da take fakewa idan dare yayi, ta tuna yadda take bin gidajen masu hali tana neman abun da zata kai a ciki, taya rana tsaka a yanzu Turhan zai bayyana yace nemanta yake me yake nema a gareta? Ya rabata da yarta kamar yadda ya rabata da sauran farincikin da ya rage mata a wacan lokacin? Ya sake dawowa rayuwarta ya haifar mata da matsala? A yanzu ta samu mai bata komai yayi mata ginshiki shi ne yake neman rusawa?
Ta kai hannu ta dago yarta, wani mummunan furuci da yayi mata a wani lokaci da farinciki ya juya mata baya ya dawo mata.
“Karki sake nuna kin san ni, akwai banbanci tsakanina dake”
Ta lumshe ido tana tuna wata rana da matarsa ta saka bayinta suka yi mata bulala yana kallo be yi kokarin hanawa ba har sai da suka bar mata tabo a jiki. Ta rumgume Fatima, wani kalar ruwan hawaye ne yake mata zuba mai zafi da dacin zuciya, ashe duk bayan wannan zai dawo nemanta?
“Momy me yasa kike kuka? I'm sorry”
Tambayar Fatima ta dawo da ita hanyacinta, sai ta bude idon ta share hawayen tana murmushi.
“Ina sonki Fatima, no matter what happen, daga ke sai London ne Iyalina, na wahala na yi sadaukarwa kamin ku kawo inda kuke a yanzu, a yanzu ma ban gama ba dan Allah kar wata rana ta zo ki fifita wani akaina”
Ta rumgumeta, sun dade a haka sannan ta sake ta tashi ta fice daga dakin, kasa ta sauka ta zauna a falo zuciyarta cike fal da tunani. Vito be dawo gidan ba sai after 8pm, ya shigo falon tare da Chidimma dake rike da leda tana biye da shi a baya. Emily ta kalleshi ta kalleta.
“Ina London?”
“Bachi yake, na zo na dauki wasu abubuwan ne na yi wanka”
Ta maida dubanta gurin Vito, ya san abun da take bukatar ji tun kamin ta gabatar masa da tambayar ya bata amsa.
“Ya sauko ya daina fushi, na yi magana da shi”
“Thank you”
Ta gyada mata kai kawai, sannan ya kalli Chidimma.
“Ki shirya da wuri direba zai maida ke asibitin kar a barshi shi kadai”
“Okay Sir”
Ta amsa tana wani karairaya daman idan shi ya bada umarni ba ta bata lokaci take aikatawa. Sai da ta fice Emily ta maida dubanta gurin Vito da idanuwansa suka dade a fuskarta.
“Zan tafi na kwana can”
Ya amsa mata kawai da ido sannan ya nufi kujera ya zauna, ita kuma ta haura sama ta shirya ta fito ta shiga dakin Fatima ta yi mata sallama sannan ta sauko suka fice a tare, ya rigata isa gurin motar ya bude mata ta shiga ya rufe sannan ya nufi bangaren da Chidimma take ya fada mata an samu sauyi zata kwana da Fatima saboda Emily zata kwana da London a asibiti, ya dawo motar ya ke kunne tun a lokacin da ya faka a harabar, daman a ka'ida baya kashe mota sai idan ya gama fita gaba daya a wunin ranar. Yana tukin yana karantar yanayinta har suka isa asibitin.
“Aikin fa?”
“Na aje”
Ya kalli irin kallon mai cike da tambaya, sai ta sauke kanta kasa tana taba yatsun hannunta.
“Saboda na bawa yarana lokacina”
“Ko dai sun koreki?”
Ya tambaya ne kawai ba dan hana da tabbacin haka din ba, domin ya san yadda ta kwalla fa rai da son aikin kuma har ta fara zuwa ba karamin abu zai saka ta aje aikin ba. Ta bude motar ta fice ba tare da tace masa komai ba, yana daga cikin motar yana kallonta har ta shige ciki sannan ya ciro wayarsa ya duba time, sai kuma yaja motar ya fice daga asibitin.
ALIYU POV.
Ya hade yawu a hankali yana mamakin yadda aka yi ta san hadisin da ta kafa masa hujja da shi, ta san addinin musulunci ne har haka? Ta yi nisa a ciki? Me yasa ma ta bar addinin tun farkon fari. Ya sake karanta sakon ta dayan bangaren yana nisa tunanin a wani bangare na labarin da ta gutsura masa, gashi kuma ta daure shi da kalamanta, be rabi Turhan a zamanin da suka yi rayuwa a Emily ne, dan haka ba zai iya shaidar kyautata ko kishiyarsa a tsakaninsu ba, amman a neman da Turhan yake mata a yanzu da kuma gudunsa da take zai iya fahimta daga rayuwarsu.
Sama yayi kadan ya sake kallon hotunan da Fatima ta turo masa, Emily ta kai mace har ta wuce, and ya yaba da yadda hotunan duka basu bayyana tsiraicinta ba duk kuwa da kasancewar ba musulma ba.
Ya fita daga chat dinsa da ita ya shiga na Turhan, ya sake karanta sakon da ya aiko masa a dazun.
“Na aureta ne a bisa cilastawar Ammy ba dan ina sonta ba, she's not my type at all, kuma adadin na ji ina sonta sai ma kiyayya ce ta ginu a tsakaninmu, har dai shedan yafi karfina na rabu da ita, amman ban cutar da ita ba”
Kana ta karanta dayan sakon dake biye da shi, a take jikinsa yayi sanyi zuciyarta ta karaya, ya san abokinsa yana neman Emily, and yes ya samu Emily da kuma tabbacin ita din ce, amman yana tsoron kar haifar mata da matsala, ka ya sakata a wani hali kamar yadda ta fada, ta dayan bangaren kuma yana tunanin ya zai yi da abokinsa, idan yayi shiru anya ya kyauta masa kuwa? Ya sani idan Turhan ko mahaifiyarsa suka san da Fatima ba za su bar mata ita ba.
“Lafiya kuwa?”
Aisha ta tambaya tana aje Bowl ta kunna tap ta wanke hannunta tana kallonsa irin kallon nan na jiransa.
“Tun da ka amsa wayar dazun na ga yanayinka gaba daya ya canja”
“Ba komai”
“Ko dai akan yarinyar da aka kora ne?”
Yayi murmushi ya dago daga jikin fridge.
“Ba ita ba ne”
Ya saka wayar aljihu ya nufeta ta rikata suka fice daga kitchen din tana masa zancen business din da take son ta fara.
“Watan cin kudin nawa ya tsaya kenan?”
Ta kyalkyale da dariya.
“Kasan ai kana cewa na rika sana'a”
“Ke da baki san kowa a nan ba, taya zaki fara sana'a, kuma kin san ina binki kudi fa”
“Namiji idan namiji ya rantawa matarsa kudi daman ai bata biya, amman shi idan ya ranta sai ya biya”
“Saboda shi namiji be san zafin kudinsa ba ko?”
Ta saka dariya a tare suka zauna ta kwanta jikinsa tana taba jira kadan bachi yayi gaba da ita, a hankali ya zaro wayarsa wani abun na cizon zuciyarsa ya sake bude sakonta ya karanta a karo na biyar, abu ne da yake bayyana a gurin kowa, zuciyar kowace mace kyakkyawa ce, sai dai wanda ta bar shaidan ya rinjayeta, ko kuma wanda wasu gurbatatun mazan suka yi ma illa.
Akwai tambayoyin da yake bukatar amsarsu a gurin Emily, yana son ya ji kadan daga dalilinta na hana yarta da ita kanwata zuwa ga abokinsa dake nemanta kamar zai salwantar da rayuwarsa wata kila hakan ya taimaka masa gurin karfafa rokon da ta yi masa.
Sai dai kuma ba lallai ta saurare shi ba, ba lallai ta yarda ta maida shi duniyarta ta baya ba, yana bukatar ganinta face to face domin amsa masa tambayoyin da ita kadai take da amsarsu. Amman kuma? Anya zata yarda su hadu? Zata yarda ta fada masa a inda zai same ta ko ta same shi? Ya shiga contact list dinsa ya tabo William ya aika masa da sako.
“Please kana da wani information na gurin da Emily Aisha take zama”
William ya masa reply Immediately.
“Wace Aisha?”
“Yarinyar da ka zo kana ta santi, wata half Cast haka mai jan gashi da blue eyes”
“No wani abu ne ya faru?”
“Yeah sun yi fada da Amal ne, har ta bar aikin ina bukatar ganinta face to face na bata hakuri kuma na mata bayanin yadda abubuwan suke”
“Meyasa ka tambaye ni? Sau daya na ganta ban sake sakata a ido ba”
“Saboda baka shigowa Office ne a yanzu, na dauka ko kuna gaisawa da juna ne, na ga ta sace maka zuciya ne”
“Ta sace mana zuciya dai”
“Nooo sam ba abun da kake tunani ba ne, idan ma kishi kake ka daina, ni ai musulmi ne, kuma ni bata cikin tsarin matan da nake so ma?”
“Bata maka kyau ba”
“Bana son macen da ta cika kyau sosai, kyaun idan yayi yawa yana zama illa, kuma ni bari da burin kara aure yanzu ko nan gaba”
Ya dauki William tsawon mintuna talatin kamin ya aiko masa da address din har da number gidan da take zaune.
“Thanks”
Aliyu ya rubuta masa a as reply.
“Me ya hada ta da Amal?”
“Idan mun hadu zaka ji”
Ya amsa masa sannan ya saka wayar alijhu cikin jindadi, ya rika matarsa zuwa bedrooms dinsu bayan ya kashe komai na falon.
#TeamTurhan
#TeamVito
A ina kuke?
#KhadeejaCandy
[4/20, 10:00 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/Dfp3nf5JwbA22eFdvKklyG
🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
Page 1️⃣2️⃣
Assalamu Alaikum.
Barka mu da Sallah.
Allah ya karbi ibada ya maimaita mana.
*** ***. ***.
Ta tura kofar dakin ta shiga fuskarta dauke da murmushi.
"Hello my beautiful boy"
Ya kalleta kawai ya dauke kai ba murmushi babu far'a kuma babu fushi, ta karasa kusa da shi cike da karfin guiwa ta zauna a kan gadon, hannu ta kai zata shafa shi a take ya saka mata ihu. Da sauri ta janye hannun, ta mike tsaye ta matsa gefe.
“Ka yi hakuri London I'm sorry”
Ta hade yawu tana kallonsa rashin jindadin dake zuciyarta ya bayyana a fuskarta. Hannu ta saka a aljihu jean din dake jikinta ta ciro wayarsta ta yi dialing din number Vito. Ta juyawa London baya hannunta daya a kan lebenta tana cizon akaifarta idonta tab da hawaye.
“Na dauka ka yi magana da London kace min ya hakura fa”
“Yeah na masa magana kuma ya hakura”
“Amman na zo yanzu yana min ihu, baya son na taba shi”
Vito yayi shiru for few seconds yana karantar yanayinta
"Kuka kike yi?"
"To me zan yi"
Ta fada a tsawa tana shessheka kuka kai kace shi yayi mata laifin. Daker ta iya hade yawu sannan ta kashe wayar ta juyo tana fuskantar London, rasa makamar yadda zata ba shi hakuri ya sakata ta zauna a gurin tana cigaba da kallonsa har lokacin hawaye sauko mata suke, tunanin rayuwar da ta yi kamin ta haifi London da kuma wanda ta yi bayan haihuwarsa, da yadda rayuwarsa ta zo mata, halin da ta shiga fargabar matsalar saninta da Aliyu yayi a yanzu duk suka taru suka mata tsaye a cikin kai.
Sai da ta yi da gaske sannan ta iya runtse ido tana maida numfashi a hankali, sai kuma ta kai hannu ta shafa sarkar cross din dake wuyanta. Wayarta ta fara ringing alamar kira, tana kallon kiran har sai da ya kusa yankewa sannan ta amsa ta kara a kunne ba tare da ta yi magana ba.
"I have to take care of something, ba zan iya zuwa ba, amman na yi magana da wani abokina yace akwai wani abokinsa kwararen likitan kwakwalwa, kuma ya shigo garin nan yin wani abu, zai shigo ya duba London kamin ya wuce"
“Dana ba mahaukaci ba ne Vito, ciwo ne kawai yake damunsa”
Ta rufe da fada zuciyarta na bugawa da karfi tsabar bacin rai, ya san yadda zai tafi da ita dan haka yayi shiru be ce komai ba sai na tsawon lokaci.
"Zan aje wayar"
Ta fada jin be ce komai ba har na tsawon minti biyar.
"Na sani, kawai zai duba shi ne ya bashi ya bamu shawarwari wata kila za su taimaka mana"
Tare da ta sake cewa komai ba ta kashe wayar, daga inda take zaune take kallon danta har bachi ya fara daukarta tana angaje har ta kai ta kwanta a gurin, bachi mai nauyi yayi gaba da ita, bata farka ba sai kusan asuba, ta bude idon tana hamma ba tare da ta rufe baki ba, dagowa ta yi kadan ta leki London, ganin yana bachi ya bata karfin guiwar mikewa tsaye ta karasa kusa da gadon da yake kwance ta zauna, ta mika hannunta a hankali ta shafa fuskarsa zuwa kansa, tausayi yake bata sosai saboda lalurar da yake dauke da ita, ba zabin mutun bane ya kasance a yadda yake so, ko kuma waninsa ya kasance a wani hali na dabam marar dadi, abu ne sa yake tsare tun gabanin halittar rayuwa, an rubuta yadda dan'adam da rayuwarsa zata kasance.
Knocking aka yi sau biyu da two fingers, da sauri ta dago ta kalli kofar dakin hakan yayi daidai ta turo kofar dakin da aka yi aka shigo. Cak ta tsaya tana kallon mutumen da ya kasance bakuwar fuska a gurinta, kamar yadda shi ma yake tsaye yana kallonta.
“Lafiya?”
Ta tambaya ganin ya gagara karaso, haka kuma ya gagara cewa komai. Takawa yayi baya ya ja mata kofar ya rufe, bata gama mamakin waye shi da kuma dalilinsa na aikata hakan ba, ya sake turo kofar dakin ya shigo with full confidence...
Kallonsa take har ya karaso kusa da ita idonsa cikin na ta.
"Sunana Doctor Adam Bello amman an fi sanina da Dr A-B kwararen likitan kwakwalwa, ina aiki a asibitin Special Care Hospital dake Abuja, abokina ya fada min akwai wani yaro da zan duba a dakin nan, wanda nake kyautata zaton kanenki ne..."
Ya karasa yana kallon London dake bachi, zuciyarsa na raya masa kanenta, a yanayin halittar jikinta da kuma kurciyar dake fuskarta ba su bar masa alamar da zai aje London a matsayin danta ba.
"London ba mahaukaci ba ne"
Ya daga girarsa biyu kadan ba tare da ya kalleta ba.
“Ni ma ban ce ni likitan mahaukata ba ne, mutane ne suke kuskuren fahimtar ciwon sai suke ganin kamar hauka ce”
Ya kai hannu ya kama hannun London yana taba tsatsunsa a hankali.
“Fada min idan kanenki ya farka yana farkawa a firgice? Idan babu kowa a kusa da shi?”
Ta daga masa kai alamar eh.
“Wane kalar turare ya fi so?"
Har lokacin be kalleta ba.
"Ban taba lura da wannan ba"
"Uhm, da wa yake yarda? Bayan mahaifiyarsa da Babansa da kuma ke?”
“Dana ne ni na haife shi”
Sai a lokacin ya sake kallonta, ya dauke shi tsawon dakika biyar kamin ya iya dauke idonsa daga kyakyawar fuskarta mai matukar daukar hankali.
"Ya kamata ki san kalar turaren da yake so, his favorite color, wane kalar cartoon yake so, wane kalar wasa yake so, wane yanayi yake shiga idan yana kuka, su waye mutanen da yake so, ki fahimci idan yayi bachi wane kalar mafarki yake? Ya yanayin sakewarsa da mutane yake?"
"Na san wasu daga ciki, amman dai shi ba mahaukaci ba ne”
Yayi murmushi ya kalleta.
“Da alama zaki sha wahalar rayuwa kamin ki fahimci duniya da mutanen cikinta, ni dai ina baki shawara ne kawai na yadda abubuwa za su miki da sauki tsakanin ke da... Danki...”
Ya fada tare da jan zaren furta kalmar danta kamar mai jin nauyin alakantata da jininta. Sannan ya ciro katinsa a aljihunsa ya mika mata.
"Bana kallon marar lafiya a free ma, balle kuma magana da shi, sai an yi min biya mai kyau, amman da yake ke tafe kike da sa'a, sai ga shi an lallaba ni na zo har asibitin da kike na duba danki kuma na baki shawarwari a free, so hare is my card idan kina son wanin hakikanin waye danki, taya zaki zauna da shi, wane mataki zaki bi har ki yi nasarar sauya rayuwarsa, da kuma yadda zai samu lafiya, sai ki bi matakin da yake kan card din”
Ya aje mata card din ya juya ya fara tafiya.
“Bama bukata daman ka zo nan ne dan ka ci kudinmu ko? Toh ni na san waye ďana kuma shi ba mahaukaci ba ne”
Juyowa yayi yana murmushi.
“Halinku daya sak da matar direban direban Babanmu, amman kuma da ta bi shawarwarin da na dora ta a kai da magani, sai ga shi ta dawo tana min godiya”
A kokarinsa na fahimtar da ita kudi ba matsalarsa ba ce kamar yadda take zato ya ambato mata direban direban babansu.
Da farko she was confused kamar ya Direban direban babansu kamin ta sake kallonsa cike da mamaki.
“Direban Babanku?"
"Nope Direban Direban Babanmu"
Ya furta yana hade lips dinsa.
"Direban Babanku yana da Direba kenan.?"
“Uhm”
'Wane irin kudi babanku yake da shi haka ne? Da har direbansa yake da direba?'
Kamar ya san tambayar da ta yi ma kanta a zuciyarta sai ya taka ya matsa kusa da ita, yana kallon kwayar idonta.
“Babanmu na da kudin sosai, kwatankwacin yadda kike da kyau sosai mai jan hankali”
Ya fada cikin wata murya na irin mutumen da kuzari ya bar jikinsa, gaba daya kyauta ya gama rudashi. Ta hade yawu da karfi tana kallonsa.
“Akwai wata tambayar ne?”
Ta kasa cewa komai, ya kalli agogon hannunsa.
“Lokacin sallah yayi, duk lokacin da kika shirya bata kudinki, zaki iya nema till then good bye”
Ta matsa baya ya fara tafiya.
"To miye amfanin zuwanka? Baka duba yaron ba baka fada min komai ba taya zan tabbatar da kwarewarka ko akasin haka?”
Tana maganar tana daga kafadunta.
“Ko ba komai ai na auna nauyin kyaunki na fada miki matakinsa, yanzu kin san darajarsa”
Ya fada sannan ya juya ya cigaba da tafiyarsa, ta bi bayansa da kallo har ya fice, sannan ta sauke numfashi ta kalli card din da ya bar mata, ta kalli danta, sai kuma ta dago wayarta ta shiga camera tana
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 63