Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da wata mata da be san waye ba sai rusar kuka take. Da takunsa na kasaita ya karasa gurin ya tsaya, sallama ce kawai ya gagara yi amman ya gabatar ma da Ummi gaisuwa domin har lokacin safiya ce. "Barka da Safiya" Ya kalli Takardar Hannun Ummi da kallonsa kawai ta yi ta dauke kai zata sauka Entrance din. "Na zo gurin Aisha ne?" "Me kake nema a gurinta? To muma nemanta muke ba mu san inda take ba" Yayi murmushi jin yadda Ummi take son raina masa wayo, calmly ya ce. "Haba Ummi ko na saki Aisha ai har duniya ta nade ita uwar yata ce kuma har yanzu ban gama sauke nauyin hakkin da musulunci ya dora min ba akanta, dan Allah ina son ganinta" Ummi ta juyo ta kalleshi. "Fitsare marar kunya, fita ka bar min gida ko na saka a yi maka wulakanci yanzu nan, an fada maka yarinya ta bata kana fadawa mutane maganar banza" "Taya zata bata bayan daga gidan ta tafi can direban kuma ya dawo da ita..?" Ummi ta sauka Entrance din tana sauraren mai fadin wani yace ya ganta a hanya a kasa dazun amman be san inda take ba a yanzu. "Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un ina yarinyar ta tafi? Ko dai ta ji maganar da muke ne? Bari na dauko wayata" Ummi ta juya da sauri ta koma ciki, a nan Turhan ya fara fahimtar da gaske Emily bata gidan domin tashin hankalin da ya gani a fuskar Ummi da kuma kukan da matar nan take yayi yawa, ya juya ya nufi motarsa ya bude ya shiga yana mamakin taya zata bata? Ba gidan ta dawo ba ne ko kuma yaya? No ta dawo gidan mana ba gashi har ya ga takardar da ya bata ba a hannun Ummi, hakan yana nufin fita ta yi daga gidan ko kuma me? Yaja motarsa shi ma ya shiga nemanta na dan ya san inda zai ganta ba sai dan ya gwada sa'arsa, ya san abu ne mai wahala ace ta gudu daga garin gaba daya saboda Fatima, amman hakan be hana shi tafiya har tasha nemanta ba, tun yana jin natsuwa da abun har hankalinsq ya fara tashi sosai gashi ba shi da layinta balle ya kira. Amman saboda me zata tafi? Bayan Ummi da Aliyu sun rike ta, ko kuma dai su ma suna cutata mata ne? Ko kuma cilasta mata karbar fatima suka yi da hakan ya gagara ta ji suna maganar wani abun ta gudu? Tun da har ga shi Ummi da kanta fadi cewar ko dai ta ji abin da suke tattaunawa ne? Ko kuma so take ta koma gida ta dauke Fatima what if duk wannan shiri ne? Ya juya motarsa ya kama hanyar gida be samu natsuwa ba sai da ya faka harabar gidan ya fita da hanzari ya shiga falon ya nufi stairs kamin ya karasa ya ji muryar Ammy a kitchen tare da Fatima, ya juyo ya da sauri ya nufi kitchen din sai da yayi arba da sanyin idaniyarsa sannan hankalinsa ya kwanta, ya sauke numfashi a hankali har da shafa kirjinsa, ya kalli Ammy Ammy ta kalleshi tana karantar yanayinsa alamar ba lafiya ba, domin idonsa ma sun sauya. Fatima ta zo da gudu ta rumgume shi tana masa oyoyo, sai ya duka ya dauke ta ya rumgume ya lumshe ido yana jin wani irin kaunarta a ransa, da ace zuwan da yayi yanzu ya tarar bata gidan wata kila da sai yayi karamar hauka, domin ya san idan Emily ta dauke ta abu ne mai wahala kamin ya sake ganinta ko sanin inda take, wata kila ma zata iya barin kasar gaba daya. Ya fito Kitchen din ya dawo falon ya zauna rumgume da yar gudaliyarsa, Ammy ta biyo bayansa ta zauna a dayar kujerar sannan ta tambayeshi. "Me yake faru? Ya ka shigo haka a rikice" "Wai Aisha ta bata" "Ta bata kamar ya?" "Haka suka fada min, daga gidan nake na bi bayanta ne sai na samu Ummi ta fada min wai su ma nemanta suke, hankalinsu a tashe yake kuma har wani na cewa ya ganta a hanya amman be san inda take ba a yanzu, ni kuma na tafi tashar da na sani na bincika sun ce ba su ga wata mace mai kamanin taba, daga baya sai na ji tsoron ko ta zo ta tafi da Fatima ne" "Ai Fatima ta dawo gida kenan Turhan da yardar Allah, ita kanta Emily zata dawo ai uwa bata iya rabo da danta, kawai dai tana son ta tashi hankalin mutane ne gaba daya rayuwar yarinyar nan ya canja" "Wata kila kuma wani abun suka shirya ita da Aliyun, ita kanta Ummi bata sani ba, ko kuma dai ta sani amman..." Ya mike tsaye ya sauke Fatima daga jikinsa. "Ina zaka je? Karka koma gidan nan Turhan karka kuskura ka ce zaka je ka yi ma Ummi rashin mutunci" "Ba gidan zan koma ba, ba da ita zan yi magana ba, ba zai yayu na zauna hakan nan ba tare da ni nemanta ko sanin halin da take ciki ba, What if taje ta shiga wani hali again? Saboda Fatima bata kusa da ita, kuma sun zugata ke kuma kin cilasta min na sake ta, sakin nan fa bata shirya masa ba" "Kai da ba wani sanin gari ka yi sosai ba ina zaka je nemanta?" "Duk inda zan shiga dai ba zan bata ba Ammy, gashi Abie ya kira ni dazun yace na bar duk abin da nake na dawo gobe, ba ni da enough time dole na nemeta a yau, dan Allah ki kula min da Fatima" Ya nufi kofa Ammy ta bishi da kallo for the first time ta ji tausayin danta tausayi na hakika ya kamata, Fatima ta tambaye ta me yake faruwa da halshe turanci, Ammy ta bata amsa da babu komai ta rika hannunta suka koma kitchen din, Fatima na bata labarin makarantar su da zamansu da Vito. Hanyar gidansu Aliyu, Turhan ya sake komawa yana tafiya yana kallon gefe da gefe ko zai ga Emily amman ko mai kama da ita be gani ba, sai zuciyarsa ta raya masa wata kila ba guduwa ta yi ba, ko ta tafi gurin Aliyu ne sai suka yi tunanin ko ta gudu, ba mamaki ta tafi ta fada masa abun da ya faru ne, ya juya kai yana jin kamar ya shafe tarihin Aliyun nan ya huta, Aliyun nan ya masa kaya, a take ya juya motar ya daga wayarsa ya kira Ammy ya tambaya ko a wace asibiti aka kai Aliyu, Ammy ta fada masa kuma ta kwatanta masa yadda zai gane amman duk da haka sai da ya hada da tambaya sannan ya samu isa asibitin ya tambaya aka nuna masa jerin rukunan da dakin Aliyu da ire irensa suka, yayi mamaki na ganin police a bakin kofar ya dan tabe baki wato har wani tsoro ake ba shi kamar wani dan sarki. Da fari hana shi shiga suka yi, sai ya bukaci su fadawa Aliyun cewar Turhan ne da kansa ya zo ganinsa kuma magana yake son yi da shi, bayan mai aikan ya shiga Turhan ya matsa baya yana dan shan kamshi daman kuma daka ganshi kasan ya fi karfin rainin wayo, zuwansa a nan ma ba dan Emily ba, domin Aliyu ne ya kamata ace ya kawo kansa gareshi ya nemi yafiyarsa kuma ya wanke kasa, sai ga shi shi ne ya zo da kansa, but saboda Emily ne if not because of her be jin ko sawunsa zai bari ya biyo bayan Aliyu balle kuma shi da kansa. "Bismillahi ka shiga ciki" Sai da yayi musu wani kallo na rainin wayo sannan ya doshi kofar ya murda ya tura ya shiga ciki. UMMI POV. Ummi ta shiga ciki ta dauki wayarta ta kira Aliyu ba dan ta labarta masa halin da ake ciki ba sai dan ta bukaci number Emily a gurinsa. A ka'ida idan Ummi ta bukaci abu gurin Aliyu baya musa mata baya kuma mata tambaya har sai ya aiwatar, dan haka be tambayi me ya faru ba sai bayan ya tura mata number. "Na turo, amnan me yasa kike neman number ta Ummi ba tana gidan ba?" "Aa ta fita ne tace zata je ta yi magana da Turhan ne, shi ne nake son sani ko ta isa kuma sun yi magana ko kuma yaya?" "Ummi kika barta ta tafi?" "Ita ta bukaci zuwan kaga kuma idan aka hanata sai ta ji ba dadi ai, amman ba ita kadai ta tafi ba na hadata da direban da zai maidota idan ta gama" "Okay" Ya kashe wayar, Ummi ta gwada kiran Number Emily da Aliyu ya turo mata, ta kuma aka yi sa'a wayar da shiga har ta fara ringing, Mama Barakat na jin wayar ta shiga ta mike tsaye kamar zata shige cikin wayar daman ta ci kuka na labarin da ta bawa Ammy ga kuma kukan yadda zata fuskanci Emily, ga na tashin hankalin batan Emily na rashin ganinta ba ba su ba a yanzu, ita kanta bata raba dayan biyu ko dai Emily ta ji abin da suke tattaunawa kai ko kuma sakin ne be mata dadi ba, domin Ummi ta kira direbanta ne ta tambaya halin da ake ciki bayan tafiyarsu gidansu Turhan sai ya fada mata ai har sun ta dawo Emily ta sake fita, a nan suka fito falon a rikice sai suka yi arba da takardar mai dauke da rubutun Larabci, Ummi ta dauka ta karanta bata gane larabci gaba daya ba, amman dai ta karanta sunan Aisha da Turhan dake jiki ga kuma kwanan wata. A nan ta saka masu aikin gidan su fita dubo mata Emily, a wannan halin ne Turhan ya shigo ya same su. [7/19, 5:10โ€ฏPM] ๐—ž๐—ต๐—ฎ๐—ฑ๐—ฒ๐—ฒ๐—ท๐—ฎ ๐—–๐—ฎ๐—ป๐—ฑ๐˜†: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=KhadeejaCandy ๐Ÿ’ ABOKIN RAYUWA ๐Ÿ’* *ยฉ Khadeeja Candy* Page 5๏ธโƒฃ5๏ธโƒฃ Kwantawa ta yi a kasa har gashin ta chudanya da kasa ta lumshe ido kanta na mata nauyi yana juyawa har lokacin bata iya fadin mafarki take ko akasin haka, can ciki kamar daga nesa take jin muryar Dr AB yana magana a wayar data saki ta fadi kasa har ta tsaga. Kamar jira ake ta rufe idon sai wani bachi mai nauyi yayi gaba da ita duk maganar da Dr AB yake a wayar bata amsa ba bata ma sake sanin yana yi ba, shi kuma baya son ya katse kiran be san ko idan ya kira zai samu ta shiga ba kar ya yanke wannan kiran kuma ya zama be sake jinta ba, dan haka ya cigaba da maganar yana fatan wani ya dauki wayar ya amsa masa ko kuma ita da kanta ta amsa. Da ya ga abun ba na yi ba ne sai ya yanke kiran ya sake kiranta shigowar da kiransa yayi a wayarta tare da ringing ya saka Emily ta farka da mugun karfi, idonta ta fara budewa taja numfashi da karfi sai kuma ta yi hanzarin saka hannunta ta tare rana dake hasken fuskarta, ta tashi zaune ta dauki wayar ta duba. Sunan Dr AB ne a jikin screen din wayar data fashe, a take abubuwan da suka faru suka dawo mata, sai ta fahimci ba mafarki take ba kenan duk abun da take gani da ji a dazun matsayin mafarki ba mafarki ba ne zahiri ne. Ranar yau ta kama ta zame mata ranar farinciki amman abun da yarta ta aikata da kuma maganar da ta ji ta rushe duk wannan. Kiran ya katse ya sake kiranta a nan bata daga ba, sai ta mike tsaye ta kama hanya ta cigaba da tafiya, a yanzu kuma ina zata je? Wani guduwar zata sake yi? Haka rayuwa zata kare mata a tsuguno da guduwa, naman gurin zama da mutane? Ta shiga wata kwarkwada tada hango sai ta bulla ta wata hanyar har lokacin Dr AB kiranta yake amman ta ki ta daga. Guri ta samu ta zauna ta cire dankwalin data daure gashinta da shi ta aje gurin ta jingina tana jin ringing din wayarta da ya zame mata kamar wata wakar da zata taimaka mata gurin tausayawa kanta. Wayar ta sake kara wannan karon bakuwar number ce, sai dai ta san ba zata wuce Dr AB yake kira dan ya ji daga gareta ba, ta amsa kiran da nufin fada masa bata bukatar taimakonsa a yanzu, sai ta ji muryar Ummi tana magana cikin rawar murya da hanzari irin na wanda ya zaku ya ji daga wani da aka rasa. "Emily? Kina ina? Direba yace kin dawo amman baki shigo ba kin fita ina kika je? Ga kuma takardar mun gani Turhan ya sake ki ko?" "Eeh ya sake ni" "Kina ina kin daga mana hankali?" Ta kalli gurin da take zaune. "Ummi na shigo na tarar kuna wani zance kuma na ji, matar da na bari a gidanki muryarta na ji kamar tana ikiraran ita ce Mahaifiyata ko kuma ta san inda mahaifiyata take dan Allah ki fada min da gaske ne?" Ummi ta yi shiru ta rasa ta ina zata fara, can kuma sai ta nisa. "Yanzu dai kina ina? Idan wani abu kike son ji ko sani ai gida ya kamata ki taho, ba wai ki tafi wani gurin ba, kin daga mana hankali, ke da ya kamata ki yi farinciki Turhan ya sake ki?" "Dan Allah Ummi ki amsa min, abun da na ji gaskiya ne?" Ummi ta dauke wayar daga kunnenta ta mikawa Mama Barakat. 'Tana son sani idan ke ce mahaifiyarta ko akasin haka, ban san amsar da zan bata ba" Mama Barakat ta karbi wayar ta kara a kunne. "Hello... Emi... Eim...emi...emilllllyyy lyyyyy" Ta amsa murya can kasa. "Na'am" Sai kuma ta yi shiru. "Kina ina dan ki dawo" "Da gaske ke ce mahaifiyata?" Mama Barakat ta fashe da kuka. "Ni na haife ki da cikina... Ni ce uwarki... Mahaifiya..." Emily ta yi murmushi mai hade da hawaye da kuka. "Waya raba ni da ke? Miyasa ban tashi tare da ke ba? Taya zan yarda ke kika haife ni ma?" "Ba magana ce da za'ayi ta ta waya ba, magana ce da ya kamata ace ina kusa da ke kina kusa da ni" "Ki amsa min dan Allah, tsawon rayuwata na karar da ita ne akan nema da son sanin su waye iyayena su waye dangina, dan Allah ki fada min waya raba ni da kowa? Ko kuma dai kina nufin kin san inda iyayena suke?" Mama Barakat ta fashe da wani irin kuka. "Ni ce...." Emily taja numfashi, tana mamakin wace irin uwa ce zata raba yarta da kowa. "Bari na canka, saboda kin haife ni ba ta hanyar aure ba ne ko?....." Mama Barakat ta fashe da sabon kuka mai karfi ta kasa amsawa na tsawon lokaci. "Dan Allah ki yafe min Emily ki zo mu yi magana ki fahimce ni, zan fada miki komai" Emily ta dauke numfashi na wucin gadi, a take duk wani farinciki da ta taba sani ya rushe, ko ba ta amsa mata da eh lallai ba ta hanyar aure ta haife ta, ta fahimci amsar domin shirun da tayi kamin ta amsa da kuma kukan da ya kwace mata sun tabbatar da hakan gashi kuma tana neman gafararta. "Sanin wannan amsar da dade ina tambaya, ya fi duk wani furuci da halin kunci da na taba shiga a rayuwata" Ta katse kiran ta share hawayenta, sauran da suka rage a ramen idonta suka kafe a nan take, kukan ya yanke zuciyarta ta kafe, ashe akwai ranar da bakinciki zai ninku hawaye su tsaya. Wayarta ta sake ruri wannan karon data duba sai ta ga number Aliyu ta daga jiran ta kara a kunne. "Assalamu Alaikum" Ta yi shiru. "Emily" "Aliyu... Ka gafarce ni dan Allah, na shiga rayuwar ka na rusa farinciki da amincin dake tsakaninka da matarka, na yi sanadin kwanciyarka Asibiti" "Me kuma ya kawo wannan maganar? Ni na kira ne saboda Ummi ta fada min kin tafi gidansu Turhan kuma har yanzu baki dawo ba ta ce na turo mata number ki tana son ta ji ko lafiya, Emily me yasa kika tafi? Already mun yi magana da Daddy kuma ya fada min yayi magana da mahafin Turhan komai zai zo karshe cikin lokaci, amman ban so kika tafi gidan ba" "Ba amfani Aliyu... Turhan ya riga ya sake ni, ranar da ya kamata ta zama ta farinciki a gareni wata mata daga dangin Kameela mai ikirarin ita Mahaifiyata ce da kuma yata sun rusa duk wannan, Fatima ta zabi ubanta ta ce ta tsane ni Turhan take so, a yau kuma na gane da wacece ni, tambayar da na dade ina yi a yau na samu amsarta, na gano inda tabarbarewar rayuwar ta samo asali ba ni da sa'a tun gurin haihuwa shiyasa kowa yake taka ni yake guduna, indai har uwa zata haifi ya kuma ta jefar da ita saboda gudun jin kunyar duniya ko shiga wani hali, ta zabi farinciki akan na yarta, ta fifita mutumcin akan na yarta, toh taya kake tunanin wani zai ga yar nan akan hanya kuma ya bata farinciki? Ashe har da uwar data haife ni bata bukata ta" "Ban fahimci me kike magana kai ba Emily amman dai ko minene ni ina da bukatarki, kuma ke ma kina bukatar kanki, karki damu da abunda Fatima ta yi daman na hango from miles away, ita ai yarinya ce wacce ta dade tana mafarkin samun uba, kowa yace zai tsaya a matsayin ubanta karba zata yi balle kuma ta hadu da ubanta na gaskiya, shiyasa data tambaya ni ban musa mata ba, sai na fada mata kin yi zaton baya raye ne shiyasa kika fada mata cewar bata da uba, idan kuma kin hadu da wata tace ita mahaifiyarki ce baki san uzurinta ba" "Wane irin uzuri ne zai saka uwa ta jefar da yarta? Shin bata yi tunanin ya rayuwa zata kasance min ba bayan babu ita babu kowa a kusa da ni? Shim bata damu ta san a wane hannu na fada ba? Saboda ta haife ni bata aure ba ni miye laifina ne? Miyasa bata yi tunani ba kamin ta aikata?, na girma cikin tsangwama da rashin daidai da abokin tafiyarsa, da kowane faruwa tambayar kaina nake ina iyayena suke? Ta san bata bukatata miyasa ta haifo ni? Ashe uwa zata iya jefar da yarta ko danta saboda jin kunyar duniya?" "Ita ta fada miki bata hanyar aure ta haife ki ba Emily ko kuma dai baki saurareta ba na fa san halinki, dan Allah karki jefa kanki a wata matsala, ki daina tunanin babu mai bukatarki ni ina da bukatarki ina son farincikinki" "Ni da kai kamar mafitar rana ne da mafadarta, dukanmu muna fuskantar mabanbanta hanyiyi ne. Baka bukatata a rayuwarka Aliyu, indai har mahaifiyata zata ji cewar ni illa ce a rayuwarta, yar da raina da azaba da damuwa ta zabi mahaifinta sama da ni to babu mai bukatata a rayuwarsa. Ni dai yau gaji na yi yaki har karfina ya kare, na yi iya yadda zan iya na kasa cin ma muraduna, an rusa rayuwata da farinciki tun ina karamata, a yau na haka rame na binne burina zan bar wannan shafi famko ba tare da digon tawada ko zanen alkalami ba, na ga rayuwa rayuwa ta gan ni, na wahala iya wahala daga karshe kuma na hadu da bakin labari, ni dai na fahimce wacece ni yau, tambayar dake yawan yi ma kaina na samu amsarta a yau. Na yi ta kokarin ganin kaiwa ga hasken farin wata, da na isa kusa da shi, sai kuma na fahimci daga nesa ya fi kyaun kallo, duk yakin da nake na samun kwanciyar hankali ne" "Kar idonki ya rufe ki aikata abun da za ki sake dawowa kina nadama, ni dai bana nufin komai a gareki sai alheri, ina son na same miki wani tsanin hawa ne a duk lokacin da kasar da kike taku ta yi miki zafi, ina son na zama wata igiya da zaki rika ki cimma burikanki, na so na zama kamar uba ko dan'uwa a gareki a duk lokacin da ruwan sama ya sauka akanki, na so in kasance wanda zai kawo miki laima, a duk Lokacin da hawaye suka zubo daga idonki, na so in kasance wanda zai share su, a duk Lokacin da kika ji kadaici na so in kasance wanda zai rarrashe ranki kuma ya kwantar da zuciyarki..." "Na gode amman ni a yanzu bana da bukatar ABOKIN RAYUWA, ko wane iri ne na nesa ko na kusa, zan nisanci kowa zan rayu kamar yadda aka bar ni, har zuwa lokacin da da rayuwar ita ma zata gaji da ni ta bar ni.. Sai wata rana Aliyu..." Aliyu ya lumshe idonsa yana jin kamar ya sauka kan gadon, ina ma ace tana kusa da shi a yanzu ya kwantar mata da hankali... "Wata ranar da bata da rana..." Ta sake maimaitawa sannan ta katse kiran ta cire dankunnenta ta juya wayar ta cire layin ta saka a bakinta ta tauna har ta raba shi biyu ta jefar a gurin, sannan ta mike tsaye ta fara tafiya sai da ta fita kwararon sannan ta jefar da wayar. ALIYU POV. "Emily..." Ya furta a hankali idonsa a lumshe, kamin ya bude idon ya sake gwada number wayarta sai ya jita a kashe. Tun da yake a rayuwarsa be taba jin tausayin wani yadda ya ji tausayin Emily a yanzu ba, duk halin da take shiga be taba jin tausayinta irin tausayin da ya rasa ma'aunin dora shi balle ya auna ba irin yau. Emily ta wahala har a yanzu bata samu gatan daya dace ta samu ba, gashi kuma abu ta dade tana nema ya zo mata a ษ“aragurbi, da wanne zata ji? Be samu amsar tambayarsa ba, daya daga cikin masu tsoronsa ya kwankwasa ya leko kofar dakin ya sanar masa wai wani Turhan yana son ganinsa. "Ce ya shigo" Aliyu ya fada ba tare da ya kalli kofar ba ma balle kuma mutumen dake tsaye yana sanar masa isowar Turhan. After 3 min Turhan ya turo kofar dakin ya shigo cikin takun sarauta da da martaba. Sai da ya karewa dakin kallo kaf sannan ya kalli Aliyu. "Na biyo sawun Aisha, sai Ummi ta fada min ta bata, wai nemanta suke... Na yi kyautata zaton tana nan ko kusa da nan, zuwan kuma ba na iya nemanta ne kawai ba har da na gargadi" "Da nine kai, ba zan taba bibiyar matar da na nake ganin ba ajina ba ce, ba zan taba bibiyar matar da na rusa mata ragowar farinciki ba, ban ga dalilin da zai saka na yi amai kuma na bibiyi aman na lasa ba, kazanta ai ta kazanta" Aliyu ya fada ba tare da ya kalleshi ba. "Toh ai ba ni ne kai ba Aliyu, ban iya cin amana ba" "Har abada, Turhan ba sai taba zama kamar Aliyu ba, namiji yana cika namiji ne da karfin tunana da hakuri da adalci da kyautata, ba da izza ko nuna isa ba, da kai wani mai wayo ne tun a lokacin da mahaifiyarka ta yi maka kyauta da ka riketa da hakuri wata kila da duk ba mu kawo a wannan ba" "Turhan ya fi karfin Aliyu, shiyasa Aliyu ba zai taba zama kamar Turhan ba, ta ko'ina na damaka na shanye Aliyu" Aliyu ya juya ya kalleshi. "Da ko wace dakika idan na yi maganarka Emily rokon take na boye maka sirrin saninta, saboda tana jin zaka rusa ragowar farincikinta, da ko wane numfashi idan na tuna na boye maka sai na ji cewar ban kyauta ba, daga lokacin da ka gane gaskiya sai na gagara samun salama na abun da nake zaton cin amana ce na aikata, amman a yau na gane abun da na aikata daidaine, na fahimci karatun da Emily take karanta min a yanzu biye da lokacin da take min bitarsa, yanzu a haka sai ka kira kanka namiji? Ka cutar da yarinyar iyakar cutarwa ta raini yarta da dadi babu dadi har ta yi wayo, rana daya ja dira a rayuwarta ka raba ta da yarinyar da ita kadaice ta rage farincikinta? A haka kuma kake neman yafiyarta? Wallahi....! Da ace zan iya sake rubuta farkon faruwar wasu abubuwa da na goge shafinku a tarihin rayuwar Emily...! Zaka gane kana sonta kawai idan ka rasa ta, kuma ka rasata...!" "Ka iya bakinka, karka sake ka sake aikata kuskuren

Chapter 44 of 63