Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
jin sunan Turhan sai ta mike tsaye da sauri ta zagayo gaban Aliyu ta tsaya cikin tashin hankali tana girgiza masa kai. "Babu amfanin fada, zamantakewa ce ta aure ka auri wanda ba type dinka ba, ba ka sonta dole za a samu wannan, balantana lokacin tunani be tsaya kamar yanzu ba, and Aliyu you will never know what is arranged marriage saboda kai da Kameela auren soyayya kuka yi, komai zan fada maka ba zaka fahimta ba, yanzu dai Maneer ya ba ni shawarar cewar na saka kudi da tsohon hotonta akan duk wanda ya ganta zan ba shi wannan kudin, ya kake ganin abun?" Aliyu ya ji gabansa ya fadi gumi ya keto masa, be taba aikata wani abu ya ji kansa mai laifi ba irin boyewa Turhan Emily da yayi, anya zai iya bari Abokinsa ya bata kudi akan abun da zai iya masa kai tsaye. "Hello.." Turhan ya fada a dayan bangaren, Aliyu ya amsa a rikice yana dawowa daga duniyar tunanin da yake. "Ehm Hello, Turhan yanzu ina Office bari idan na samu natsuwa na koma gida sai na yi tunanin abun da ya kamata mu yi" "Okay" Ya yanke wayar ya kalli Emily. "Ban san me kuke tattauna ba, amman dai ba zaka fada masa ina nan ba, i trust you" Ta fada idonta tab da hawaye. "Turhan Trust me, ke kin yarda da ni to yardar wa zan karya? Kun saka ni a tsakiya I'm feeling guilty, wadanda ban sani ba ma suna magana da ke like likitan nan na yau? Shi kuma a ina kika san shi? Kina zaune a tare da shi har kina masa dariya bayan abokina yana can cikin damuwa saboda nemanki? Anya na yi adalci" "Ka riga ka karya nasa tun da har ka kasa fada masa inda nake duk tsawon lokacin ne, hakan yana nufin nawa ya fi karfi a gurinka dan Allah karka karya, idan ya sani ba zai bar ni da yata ba ita kadai ta rage min, kuma baka san iya abun da mutumen yayi min ba i don't need him" Damuwa karara a fuskar Aliyu, ya nufi kujera ya zauna ya dafe kansa. "There is something about you Emily, kin saka na yi abubuwa da ba halina ba, like boyewa abokina gaskiya, kamar saka mahaifina ya saka NDLEA su bincike gidan Vito kai tsaye daga Abuja, so that idan an same shi da laifi a dauke shi ki samu yanci, amman kika ci mutunci akan haka, and na kyale haka be bata min rai ba, like sitting here in your office talking to you?" Ya dago ya kalli Office din sannan ya kalleta. Hawaye ya sauko mata. "I understand, na yi fada da kai ne akan Vito saboda idan wani abu ya same shi ba ni da mai kula da ni, kuma idan ya gane kai ne ba zai kyale ka ba, ba zan so wani abu ya sake ka saboda ni ba. About Turhan kuma idan kana son fada masa gaskiya amman ka sani cikin rai biyu za a rasa daya ne, nawa ko nasa, domin zan yi duk yadda zan iya na saka Vito ya hana shi raba ni da Fatima, idan kuma har yayi nasarar raba ni da ita, to ni tawa rayuwar bata da sauran amfani, babu abun da zan tsaya yi, ko kuma so kake na dauketa mu yi ta gudu muna boya?" Tana maganar tana hawaye sosai. " Daga kai sai Tasmia sai Vito ne abokan rayuwar da nake sa ran idan ina cikin wata damuwa za ku taimaka min" "Ki cire Tasmia, kuma ki aje Vito a gefe" Ya amsa mata yana kallonta ita ma kallonsa take kamin ta nufi kofa zata bude. "Emily dawo ki zauna" Ta tsaya a gurin na tsawon minti uku sannan ta koma ta zauna kamar yadda ya bukata. "Fada min irin zamantakewar da kuka yi da Turhan, wata kila hakan zai kara min kwarin guiwar kara boyeki a gurinsa, i trust you ba zan so wani abu marar kyau ya shafe ki ta dalilina ba" Ya cire agogon hannunsa ya mika mata. "You can keep this" Ba zallar agogon yake bata ba, yana tuna mata da rayuwar baya ne, dan gutun lokacin da yayi sanadiyar agogon ya zauna hannunta, what he need is ta fada masa gaskiya kuma ta tuna yadda ya taimake ta kar ta boye masa komai. Ta tara hannunta ya zuba mata agogon ta jimke...! KAMEELA POV. Mama Baraka ta dafa ta. "Kameela ba ni na haife ki ba abu ne da kika sani na sani, na san kuna kallona a matsayin kishiyar uwa wacce bata son ku alhalin ba haka ba ne, yadda ba zan so wani abu ya samu Aleeya ba haka ba zan so wani abu ya same ki ba, da na kowa ne ba mu san inda na mu yayan za su samu kansu ba, dan haka nake rike yayan wasu da amana" Kameela ta kalleta. "Me ya kawo wannan maganar yanzu?" "Ina son zan baki shawara ne a matsayin na uwa, ina son ki kalle wannan ta fuskar uwa ba kishiyar uwa ko matar uba ba" Kameela ta dan share hawayenta ta natsu. "Da farko na so na ga hoton yadda yarinyar take, na ga shim me ta fiki da shi da har kike tunanin ta dauke hankalin Aliyu akanki, wata kila ke kika ganin haka amman bata fiki komai ba, kin san wani lokacin mu mata mu muke bada kofar da wasu suke gani har su samu damar juya mu, tsakaninki da mijinki kin fi kowa sanin waye shi me ya fi so me ya fi tsana sai ki kiyaye ita kuma wanda ta dauke masa hankali sai ki duba ki ga dame ta dauke hankalin nasa yawan kyalliya ko kalamai, ko biyayya duk yadda take da shi na san kin fita kusanci da mijinki, kuma ke da kanki ke kika kawo Aliyu kika ce kina so, babu wanda ya muku dole, kuma a yadda na fahimta idan har zan fadi tsakani da Allah Kameela na san ke ce mai laifi duk da ban san abun da ya shiga tsakaninku ba, iya wannan ne ko akwai wani, amman a yadda na fahimta Aliyu mutum ne mai hakuri mai juriya" Kameela ta yi shiru tana sauraren maganar hankali da mahaifiyarta bata zaunar da ita ta lurar da ita ba. "Shi zaman aure dan hakuri ne, kuma kowa da kalar jarrabawarsa, wani a gidan mijin ne da wasu abokan zama wasu kuma iyayen miji, wasu mazan ne ba na kwarai ba, wasu iyayensu ne fitina wasu yara, wasu ma shiga gidan miji ko samun mijin aure ya gagara, kaddara rayuwa gata nan birjik an raba an bawa kowa tasa, amman ke baki samu muguwar suruka ba, kuma mijinki yana sonki, toh me zai saka ba zaki yi hakuri da dan abun da aka jarrabe ke da shi ba? Kaddara ma Aliyu neman matan yake ai be yi ba sai da baki kusa ko?" Ta daga kai. "Kin gani, wata kila rashin ki ya saka shi aikata hakan, a yanzu kuma da kika dawo madadin ki gyara sai kika kara lalata lamarin, kin ga kin bude masa kofa kenan kuma ita wacan kin bata galaba, ita na kawarki da kike zance kar yi mamaki ace son take ta cire ki a gidan ta saka kanta ma gaba daya, na san baki rasa komai a gidan nan ba, mahaifina yana da kudi zai iya miki komai, amman karki duba wannan shi aure Rahama ne daraja ce kwanciyar hankali, ki yi hakuri ki jure ki danna komai ki koma dakin mijinki, iya mai turo miki sakon tana yi ne saboda tana son ki bar gidan ita ta shiga" "Mama Baraka shi da kansa fa yace na dawo" "Eh wata kila akwai abun da kika masa ne, ni zan kira shi, zan yi magana da shi duk abun da za ayi karki biye kanenki da yayyenki domin su ba son Aliyu suke ba, ke kuma kina son mijinki, duk yadda za'ayi ki daina bari ana jin kanku, ita mace gona ce ga namiji ka yi gina ka rufe duk abun da kake so babu wanda ya sai idan ta fitar, shi kuma namiji sutura ne ga mace babu mai ganin tsiraicinta sai idan ta bayyana ko ya bayyana, karki nuna masa ma kin fadi abun da ke tsakaninku, kina son komawa dakin mijinki?" Ta daga kai. "Ina son Aliyu sosai Wallahi" "Indai har kina sonshi to ki shirya fuskantar duk wani kalubale akansa, ni zan kira shi da kaina zan yi magana ta fahimta daga ni sai shi, idan ya kama har mahaifiyarsa zan yi magana da ita, amman bana son ki bar Hajiya ta sani" "Ba zan fada mata ba" "Yauwa yanzu na gamsu kina son mijinki, saka min number sa a nan zan kira shi mu yi magana ba zan ma nuna masa kin san na kira ba" Mama Baraka ta mika mata wayarta Kameela ta karba ta saka mata number Aliyu. "Amman fa sai kin taya ni yakin, domin idan ya zo ya nuna yana son ki koma toh ki nuna kina son mijinki kuma kina son komawa idan ba haka ba yan dakinku za su kara bata abun ne kawai" "Na fahimta Mama Baraka" Na fada tana duba dp Emily dake whatsapp ta nunawa Mama Baraka hoton Emily saboda ta ji dadin shawara da karfafa guiwar da ta yi mata. "Kin ga hoton yar iskar yarinyar nan" Mama Baraka ta yi saving number Aliyu sannan ta karbi wayar Kameela tana duba hoton. "Tsohuwar Matar Abokinsa ce fa Turhan har da ya a tsakanin su yanzu haka Turhan din nemanta yake sosai, wai mahaifiyarsa ta yi fushi da shi saboda ita, ni ban gamsu ba wata kila dai ta gudu masa da ya ne, ko da yake Aliyu yace wai be san yana da yar ba, kuma ban san miyasa ya ki ya fada masa ya ganta ba, wata kila saboda sonta yake ko? Idan ba haka ba ai zai fada masa, wata kila kuma ya boye min ne, amman ko minene dai sai na bincika, yanzu ma bake jin karfin guiwar komawa dakin mijina" Duk dogon rattaba zancen da Kameela take Mama Barakat bata ji ko daya ba, gaba daya hankalinta ya tafi gurin kallon hoton Emily kamar mai son tantance wani abu. "Ya sunanta" "Emily amman Aisha ake ce mata" "Tana PH ne tare da shi?" "Eh yanzu tana PH amman yar Lagos ce a wani gidan marayu ta tashi a can ta girma aka ce, kamin ta auri Turhan din ko a ina suka hadu ma Oho" Mama Baraka ta hade abu da karfi yanayinta gaba daya ya canja, ta kurawa hoton ido kai kace ranar ta fara ganin mutane. "Bata fiki da komai ba, hasken fata kawai zata nuna miki, wannan ai bata kai ta kwace miki miji ba, karki daga hankalinki akanta, kuma ita ai ba musulma bace da alama ga Cross a wuyanta" Tana maganar idonta ya cika da kwalla sai dai bata bar Kameela ta gani ba. "Eh kafira ce" "Wata kila ma duk abun da kike zato ba shi ba ne, Aliyu da hankalinsa ai ba zai yarda ya rabi kafira ba, zan yi magana da shi na san zai saurare ki kwantar da hankali" Ta mika mata wayar. "Tashi ki koma bangarenku kar ayi zaton wani abun muka shirya ma" "Tohm" Ta mike tsaye ta fice daga falon tana jin bakinciki dake zuciyarta yana raguwa saboda shawarar da Mama Barakat ta bata da kuma matakin da tace zata dauka, a yanzu kuma tsoron ta daya kar ya fada mata ko mahaifinta cewar ta saka masa guba a abinci, idan kuma har Ummi taji ta san auren ta da Aliyu ya kare har abada, ta san bata kyauta ba, be kamata ta aikata hakan ba kuma ta yi kuskure, da yanzu ta kashe shi wa gari ya waya? Ai ko mahaifiyarsa ba zata fita jin zafin mutuwarsa ba, haka dai ta yi ta sake sakenta har ta shiga bangarensu ta shige dakinta ta kama hoton Aliyu tana kallo da wasu videos da suka yi a tare tana ta jin kewar mijinta da kuma nadamar abun da ta aikata domin ta fi kowa sanin Aliyu yana sonta, ta san ba dan yana sonta ba wata kila da sakinta zai yi gaba daya ba zai tsaya cewa za a duba kwakwalwarta ba ko ya turata gidansu. *** *** *** Mama Barakat ta bi bayan Kameela da kallo har ta fice fuska a raunace, ta yunkura zata tashi kafarta ta hagu ta yi mata nauyi sosai ta gagara daga kafar, zuciyarta ma ta yi nauyi sosai kamar an dora mata dutse. "Aleeya Aleeya Aleeya... Samira Samira..." Ta kwalawa yaranta kira Sameera ta sauko da saurinta tana dariya hannunta rike da waya da alama wani abun take kallo a wayar. "Mama gani zuwa, Aleeya bachi take" Mama Baraka ta daga kai tana kallonta har ta sauko. "Rika ni ina son zan shiga dakina na" Ta fada mata da yaren yarbanci daman da yarenta take magana da yaranta idan su kadai ne a gidan wannan ya saka suke jin yaren sosai. Sameera ta yi hanzarin aje wayarta tana kallon Mama Baraka. "Mama Lafiya?" "Kafata ce ta rike, ina son na tashi na kasa" Sameera ta rika ta cikin karfin hali domin bata iya dagata gaba daya, Mama Baraka mace ce mai jiki, ta mike tsaye daker ta cije baki ta taka dayar kafar dayan kuma ta daga ta, da taimako Sameera suka haura sama suka shiga dakinta Sameera ta dora ta kan gadonta. "Mama ko asibiti za mu je?" "Aa zai saki, ai bata taba min haka ba sai yanzu, tafi dakinku zan kwana na huta" "Okay" Ta fice daga dakin, Mama Baraka ta kwanta saman gadon ta yi ruf da ciki ta danne zuciyarta take mata nauyi ta lumshe ido tana maida numfashi a hankali. [6/16, 2:18 PM] null: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_writing 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ Page 3️⃣5️⃣ Ta hade yawun bakinta tana kallon agogon da Aliyu ya bata. *** ***. ***. "Matar da na faɗa gidanta neman taimako, har aka ba ni abinci ita ce mahaifiyar Turhan, a lokacin da na bashi shinkafa sai ya dauke numfashi, hankalina ya tashi sosai na yi zaton London ya mutu a wacan lokacin a take na fara girgiza shi ina ihu, matashiyar yarinyar da ta kawo min shimkafar ta fito da sauri tana tambayar lafiya, ya mutu shimkafa na ba shi sai ya dauke numfashi, na shiga uku na mutu ba ni da kowa sai shi. Shi ne abun da nake ta fada ina hargowa, sai ga Hajiyar ta fito tana tambayar me ya faru? Bana iya amsawa sai sambatu nake ina ihu, sai tace a kira direba ta shiga da kanta ta dauko mayafinta ta karbi Yaron ta shiga mota na shiga direban yaja mu zuwa wata babbar asibiti, muka zuwa aka karbi Ibrahim suka bude nasa file suka masa duk abun da ya kamata, likitar data karbe shi mace ce a take ta rufe ni da fada a wane dalili zaki ba shi shimkafa jariri kamar wannan, baki da hankali? "Ba ni da ruwan nono ne kuma ba ni da wani abun ba shi" "idan baki da abun bashi sai ki bashi abinci yaushe kika taba ganin an bawa jariri abinci? Haka kika ga ana rainon jarirai" Na girgiza mata kai ina hawaye. "Ban san yadda ake ba, ba a taba haihuwa a gabana ba, ba a taba rainon jariri a gabana ba" Na bata amsa, sai Hajiyar ta dube ni. "Daga wace duniyar kike?" "A gidan marayu na taso, ban san duka wadannan abubuwa ba" Na durkusa kasa ina mata godiya "Na gode Hajiya na gode" Sai ta rika ni ta mikar da ni tsaye. "Sunana Ammy karki damu ki kula dai ko ruwa karki sake ba shi" "Amman idan be ci komai ba ai zai iya mutuwa ko?" "Za a kawo abincin da zakiba shi, yanzu zaki zauna ki yi jinyarsa har zuwa lokacin da za su sallame shi, akwai wanda kika sani nan?" Na girgiza mata kai. "Ban san kowa ba" "Labarin yana da tsaye kuma idan na fada miki ba lallai ki yarda ba" "Zan yarda, saboda na yarda Ubangijina ba zai bari a cutar da ni ba, amman tun da kin ce labarin yana da tsayi ki aje har zuwa lokacin da za mu samu zama" Na amsa mata da tohm sai ta tafi tare da likitar aka bar ni a gurin, can kuma sai ga likitar ta dawo tace na tafi Ammy tana jirana gurin mota wai zan bita mu koma gida saboda jariri zai zauna a hannunsu ne har ya samu sauki, zuciyata bata gamsu da haka ba dan haka na ki yarda saboda ina tunanin kamar sace min yaro suke son yi, ganin haka ya saka dole aka bar ni a asibiti, Ammy tasa aka kawo min abun shimfida da abinci, aka kawo madara ta jarirai ana bawa yaron, kullum za a kawo min abinci, amman bana iya ci saboda hankalina yana gurin yarona, aka kwana biyu sai Ammy ta dawo duba ni a lokacin ne take tambayata ko na san yarona yana da wata rashin lafiya nace aa, sai tace min likitoci sun fada mata yarona yana da sickle, ban ma fahimci ciwon ba sai da ta yi min bayanin cewar jinina da jinin mahaifin yaron ne ya zo daya, tace min kar na damu zata dauki nauyin maganin yaron, haka kuwa aka yi naira biyar ban taba kashewa ba a tsawon zaman da na yi na asibiti na wata daya, a tsawon watan da na yi asibitin nono be kawo ba saboda bana iya cin abincin kirki kullum cikin tunanin butulci da Khaleefa yayi min da kuma makomar yarona, ban san ina da hawan jini ba sai a lokacin kuma ashe idan mace ta haihu wanka ake mata da ruwan zafi ko kuma a bata magani ban sani ba hakan ya saka na yi ta kumbura, ina jin akwai canji a jikina amman saboda babu mai kula da ni ban damu da lafiyata ba, har sai da Ammy ta same ni ta tambaye ni ina da wani ciwo ne da yake saka ni kumbura haka domin na zama wata babba uwar mata, nace mata aa sai idan abun ya same ni ban sani ba, sai saka aka bude min file aka bincika ni, a nan aka gane hawan jinin da na samu da cikin dana be sauka ba, kuma ba a gasa min jiki ba shiyasa nake ta wannan ciwon. Ni ma gadon suka ba ni ana kula da ni, a tsawon wata daya da na kara a asibitin Ammy ce take kula da ni ni da dana, ta saka mai aikinta tana jinyata har na samu lafiya amman jiki be sauka ba. Da aka sallamo ni sai na amince na dawo na gidanta na bar London a asibitin, ta ba ni daki daya a cikin dakunan da suke cikin gidanta kuma suke kusa da dakinta, daman tun ina asibiti ta kawo min tufafi sai ta kara min wasu tace idan ina son abinci na sauka na ci kuma na sake jiki kamar gidana. Na jidadi ta karammani a lokacin ba tare da sanin wacece ni ko daga ina nake fito ba. Kwana biyu da dawowata aka sallamo London sai aka dawo da shi gida, sai ta siya masa tufafi kusan kala goma sha biyu bayan pampers da madara da ta karo ta siya masa gadon yara da tawul, mai aikinta take masa wanka ta goya shi wani lokacin kuma ita da kanta zata dauke shi ya wuni a hannunta. A haka na kwashe wata uku a gidanta, kuma a tsawon lokacin nan bata taba tambayar labarina ba, bata tana nuna min banbanci ba, idan ta ga ina ja baya gurin shiga lamuran gidan sai ta rufe ni da fada, wai na kasa sakin jiki, ita ta lura da wani bangare na ibada ta daya kamata na gyara sai ta fara koya min a lokacin take tambayar a gidan marayun da nake ba a koya mana ibada ni. A ranar na fayyace mata komai na yadda kaddara ta tsara min rayuwa. Ta yi kuka ta tausaya min kuma ta yi min alkawarin zata zame min uwa, itace ta fara saka ni a makarantar islamiya na fara koyon addini. Sannu a hankali na sake jiki na zama kamar yar gidan, wata rana ina zaune falo ta same ni tace Aisha ina jinki kamar yata daman ina sha'awar ya mace Allah be bani ba, samunki a yanzu ya saka na ji kamar Allah ya maye min gurbinki da wanda ban samu ba ne, fadar hakan da tayi sai ya kara karfafa min guiwa na jidadi, ta fada min yaro daya ta haifa amman baya hannunta matashiyar da na gani a lokacin mai suna Nana rikonta take, yanayin yadda take mu'amalantar danta abun sha'awar ba dan na gani ba sai dan labarin da ta ba ni da kuma yadda take idan ya kirata ko ta kira shi, na fahimci tana matukar kaunarsa ne ta yadda take fada min hallayensa da dabi'unsa, har ta fada min idan ya kan shekara biyu kamin ya zo gurin, amman wnnan karon idan ya zo akwai shirin da ta yi masa, ban fahimci me take nufi ba ashe aurena da shi take son ta hada amman bata fada min ba. Sai dai tana yawan ce min musulmai suna da dadin zama kuma Allah zai min sakamako da miji na gari. A haka har yarona ya shekara daya ina kula da shi, Ammy kuma tana siya masa magani da madara, sai dai ni kam jiki be sauka ba, duk kuwa da kasancewarsa na samu lafiya sosai ga wadata ta abinci, na zama kamar wata babbar mace fari ya fito jan gashina yayi kyau saboda yana samun gyara a yanzu komai a wadace. Wata rana na yi wanka na shirya cikin shudiyar atamfa wanda ta yi mjn kyau sosai, na fito harabar gidan na zauna ina shan iska, da kuma mamakin yadda har zuwa lokacin Khaleefa ba neme ni ba, ba dan ina da bukatarsa ko wani abu daga gareshi ba sai dan cikin da ya sake ni da shi, da kuma irin halin da ya bar ni, amman be biyo sawuna ba. Da ace ban hadu da Ammy ba wata kila da ina nan cikin gararin rayuwa amman be damu ba. Be yi tunanin alhakina ba ko na dansa. Ban san ba, ashe ina tunanin hawaye suna saukowa min amman ban jin ba saboda zuciyar ta yi nisa gurin tunani har sai da Ammy ta fito ta zauna kusa da ni tana fadin. "Me kika tuna? Domin na san kin samu lafiya yanzu ballantana nace ciwo kike ji" "Bana tunanin komai" "Ga hawaye a fuskarki Aisha karki cutar da kanki mana, ki dauke ni a matsayin uwa bana son kina boye min komai" Na kai hannu na taba fuskar sai na ji hawaye. "Kawai ina tunanin yadda Khaleefa ya juya min baya ne, kuma yadda be waiwaye ni ba har yanzu, be damu ta sanin halin da dansa yake ciki ba" Sai ta yi murmushi. "Yarinya ce ke shiyasa baki fahimci rayuwa ba, ai a yanzu ne yake cikin shauki da jindadin yaudara, ba zai neme ki a yanzu ba, sai a lokacin da nemanki ba shi da amfani a gurinsa, kuma ina baki shawarar idan ya dawo miki karki saurareshi ban ce karki yafe masa ba, amman karki yarda ki sake saka kafarki a gurin da aka wulakanta ki aka nuna baki da daraja. Aisha maza na gari suna tsada, ba kowa ne yake iya aure ya rike amana ba, amman ina mai tabbatar miki nan gaba kadan zaki samu samu wanda zai mantar da ke komai zai so ki ke da danki, ni ma na sha wahalar rayuwa a aurena na farko kuma banbanci abun da aka miki da nawa kadan ne, ke kin yi ma arziki an barki da yaron, ni nawa karbe yaron yayi kuma ya hana

Chapter 28 of 63