ne Emily ta san wasu al'adu na jego da haihuwa, domin a baya ita kadai take haihuwarta cikin wahala a yanzu kuma tari da yan'uwa da mijinta a kusa da ita.
Ana sauran kwana biyu ayi suna Ummi ta dira a Kaduna a gidanta, abun ka da yan siyasa har abun da be kai ya kawo na yi ake, sai barka ta koma gurin Ummi ana hadawa da abubuwan alheri, daman kuma wani abun biki ne dole ita ma zata rama musu. Kusan ita ta tsara yadda komai zai guna na cikin saboda Emily bata da kawaye, sai sababin makota da kuma yan'uwan miji da yan'uwanta da suka zame mata kawaye.
Ranar suna yaro ya ci sunan mahaifin Aliyu Mudallab aka yi masa alkunya da Abulkhary. A ranar Emily ta ga biki ba ji ba, ta san miyen dadin yan'uwa miye yan'uwa da kuma abokan arzikin, ta san dadin haihuwa a cikin dangi ba a gurin bare ba. Ta samu alheri sosai kusan duk abun da aka bawa Ummi na biki tun daga tufafi da kayan jarirai sai da ta kawo mata su, bayan ta yi mata nata kayan barka irin wanda take yi ma matar yayan Aliyu a duk lokacin da ta haihu. Mama Baraka ma ta yi mata nata domin Abulkhary ne jikanta na farko gashi kuma tana kokarin kyautatawa Emily.
Dr A-B ma be yarda an barshi a baya ba, duk kuwa da kasancewar be samu zuwa ba saboda shi ma yana ta shirye shiryen nasa auren ne, amman ya saka wata online vendor ta shirya ma Emily kayan barka daga Kano aka aika mata Kada. Uban yaro kam daman tun kamin a haihu yayi booking kayan barka gurin wata cousin dinsa dake siyar da kayan yara, da sharadin idan mace ce ga budget dinsa da zai biya haka ma namiji yayi payment tuntuni ana haihuwarta da kwana uku aka kawo kayan har sai da Emily ta rasa bakin yi ma Aliyu godiya.
A haihuwar Abulkhary Emily ta san ta ci naman sunan ɗanta, ta san a aje mata nama mai uban yawa ace nata ne ita kadai bayan an bawa mutane, duk abubuwan da aka yi babu wanda ya fi burge ta kamar taron suna, saboda ta ga mutane sosai wasu ma bata san su ba sai a lokacin, wasu kuma sai a lokacin suka san Aliyu ya sake mata ba Kameela ba, kuma ya sauya gida. Ammy bata zo mata barka ba, amman ta aiko mata da Fatima an yi komai da ita kamar yadda aka yi na aurenta.
TURHAN POV.
Saboda hankalin Emily dana mahaifiyarsa ya kwanta ya yarda ya bar Fatima a gurin Ammy, ba dan baya son zamanta a kusa da shi ba, ga kuma karatunta da baya son ya rabu biyu idan bata zauna gu daya ba. Yakan ziyarce ta a duk karshen wata, wani lokacin ma ba'ayin wata idan yayi marmarin ganinta zai zo ya ganta.
Yana yawan zuwa ne saboda yana tsammanin jin kyakkyawan labari daga rayuwar Aliyu da Emily, tun a wacan ranar da yar'uwar Ammy taje daukar Fatima ta fada masa ta ga Emily na kuka da alama sun samu matsala da Aliyu ne ko sun fara samu.
Sai zuciyarsa ta masa dadi yana jin kamar amanar sa da Aliyu ya ci zata fita, yana jiran ranar da Emily zata fito ta dawo masa. Be taba yarda ya tambayi yarsa labarin Emily ba saboda be son ta yi subutar baki ta fadawa Emily cewar Turhan yana tambayarta. Haka kuma yana tsoron ya tambaya ya ji wani labarin da ba haka ba. Be tana tsinkewa ba sai da Fatima take fada masa momynta tana da ciki, a waya suka yi maganar da Fatima amman a ranar be iya kwana ba, sai juyi yake yana tunanin yadda abokinsa zai zauna da matarsa har ta samu ciki.
Be kara tsanar Aliyu ba sai da yayi waya da Ammy ta fada masa Fatima na gurin Mamanta saboda ta haihu. A ranar ji yayi kamar ace Aliyu yana kusa da shi ya daba masa wuka ya mutu, domin ya fahimci Aliyu ba shi da niyar sakin Emily ko da yake ai yayi wuri yanzu, ya ba su lokaci zuwa gaba mana idan ta canja.
KAMEELA POV.
"Kin san fa yau ba girkinki ba ne, ki bari sai girkinki ya juyo sai mu tafi tare, saboda yanzu dare yayi kar mu shiga hakkin madam"
Ta dauke hannunta daga jikin angon nata tana murmushin karfin hali.
"Shikenan Allah ya tsare"
"Ameen"
Ya juya ba tare da ya damu da ya sumbance ba kamar yadda Aliyu yake ya shiga motarsa ya daga mata hannu ta daga masa ya fice. Falonta ta dawo ta zauna tana hawaye, wai yau ita ce take son fita wani Namiji ya kalli kwayar idonta ya fada mata yau ba kwananta ba ne, ita take sharing miji da wata a yau, ita take raba girki da kwana da kwana da wata, a yanzu su biyu ne a zuciyar mijinta ba ita kadai ba.
Lallai mace yar gaba da baya ce, hakika ta yi aure amman ba ga wadda take so ba, ba ga wanda zuciyarta ta natsu da shi ba, ta yi ne kawai saboda yan'uwanta da kawaye da kuma zuciyata suna zugata ta manta da Aliyu, kuma ta auri wanda ya fishi kudi kamar yadda aka so da farko.
Ta yi auren, amman ta rasa soyayya da kulawa da kauna irin wanda Aliyu yake nuna mata, a nan ta san banbancin ba ko wane mai kudi ba ne yake da lokacin iyalinsa lallai irin Aliyu daya ne cikin dari, ya bata dama ta san shi ciki da waje, ta dauki wayarsa ta bincika duk abun da take ra'ayi, wannan kuma ko kusa da wayarsa be yarda taje ba, ga shi yana masifar tsoron uwargidansa fiye da ita. Gaba daya irin zaman da ta yi da Aliyu ya sha banban da wannan da take aure. Sosai da sosai take marmarin mijinta take kewarsa da rayuwarsu, take nadamar abun da ta aika a baya, wata kila ta bata biye zugar zuciya data yan'uwa ba ta tsaya jira wata kila Aliyu zai iya sake zama da ita a matsayin mata ta biyu har ma ya saki Emily tun da ta san yana kaunarta.
Ganin kamar zaman ba zai mata dadi ba, tsarin rayuwata be dace da nashi ba ya saka ta fara shirye shiryen barin gidan ko ta halin yaya domin komawa tsohon mijinta, kwatsam sai ga ciki ya bayyana a dole ta zubar da makamanta ta maida hankalin gurin rainon cikinta ta kuma kai zuciya nesa akan kishiryarta if not zata iya mutuwa lokacin be yi ba. Ba laifi da ta haihu ya nuna mata kulawa sosai domin kusan wannan ce haihuwar farko a gurinta saboda wacan ɗan be rayu ba, da yanzu ita ma tana da jini da Aliyu. A yanzu kuma idan ta tuna wata ce ta haihu da shi ba ita ba sai ta ji kamar zata mutu, ga shi ta bangaren mijinta ma ba ita ta fara tara masa yara ba.
Tsoron kar ta fita gidan mijin ta sake afkawa wani wanda ya fi shi munin hali, gashi bata da tabbacin ko Aliyu be zai maida ita, ko kuma aa ya saka ta hakura ta zauna gidan sabon mijinta ta rumgume yarta data haifa to her it's not an easy thing ta bar gidan ta bar yarta, bayan kuma bata fuskantar wata matsala a gurin mijinta sai kishiya, sai kuma rashin kulawa kamar Aliyu da yake nuna mata, dadin dadawa kuma tana zargin kamar wani auren yake son karawa su zama su uku, kuma bata isa ta hana ba, domin ba ita ce ta farko ba. Daman hausawa sun ce idan baka yi sharar masallaci ba sai ka yi ta kasuwa ko gidan giya.
EMILY POV.
"Yace idan an yi hutun karshen shekarar nan zai tafi, daga nan ya nuna masa matarsa"
Ta fada tana kwance kan ciyarsa yana wasa da gashin girarta.
"Ba za ki bari sai Abulkhary yayi wayo ba?"
"Wayo na nawa kuma? Wannan yaron ko kai ya tsofeka"
"Eh tun da kakana ya haife shi ba"
Ta yi dariya.
"Amman za mu je tare da kai ko?"
"I don't know kin san yayanki nan ba wani, yi na yake ba, ya kusan sakawa na rasa ki fa, kuma na lura kamar baya son ina shigar masa lamurra tun da yake kira be taba cewa a ba ni mu gaisa ba"
Emily ta bude ido.
"Kai kasan shi fa rayuwar turawa ce da shi ba wani damuwa yake da mutane ba, shi ne kawai, auren nan ma ban dauka zai yi ba, shi kansa yace be dauka zai yi aure ba sai gashi ya hadu da wanda ta yi masa"
"Dan ta kife ne wannan yayan naki, Allah ya so ni aka gano dan'uwanki ne da na sha wuya a hannunsa"
Emily ta sake bushewa da dariya har da kyalkyatawa Aliyu sai kallonta yake with affection yana murmushi.
"Wallahi ba shi da matsala, ka ga ko bikin nan da aka yi, shi yayi ta gabatar da ni a gurin mutane a komai baya bari a bar ni baya, na jidadin yadda ya nuna min kulawa, shiyasa ban wani damu da yadda mahaifiyarsa ta nuna min bata son ganina ba, saboda naje saboda Dr A-B ne da kuma zaton mahaifinsa zai zo bikin sai gashi be samu zuwa ba"
Ya ja mata kunne.
"Mahaifinsa ke ba da ke ba?"
"I don't know ko ya karbe ni ko be karbe ni ba yet"
"Mun gaisa, na gan shi ta system din Dr A-B ya gabatar masa da ni, ya karɓi numberta amman ai har yau be kira ni ba"
"Amman da ya ji cewar ke yarsa yayi mamaki?"
"Eh Dr A-B yace yayi mamaki sosai, yace shi be yarda ba, da farko har yayi denying cewar ya taba zama da Mama Baraka sai da Dr ya gabatar masa da hujoji sannan ya yarda, amman da muka gaiwa na ga dai kamar damuwa a fuskarsa sosai, amman har yanzu be kira ni wata kila baya so na"
"Aa ko dai yana jin kunya ne ba, ko kuma be san yadda zai kalli abun ba, amman yanzu idan muka je zamu gani ai, kawai abun da nake so da ke duk wani abu da zai biyo baya na rashin dadi ba za ki damu ba ki min alkawari"
Ta dago ido ta kalleshi a shagwabe.
"Ina da kai a yanzu Aliyu me zai saka na damu"
Ya kama bakinta ya matse.
"Aliyu ko?"
"Nooo My Soul Mate"
Ya saki bakin ya kai mata rankwashi a kai. Ta da ga jikinsa.
"Ka yi na kudinka"
Ya san me take nufi dan haka ya kalleta da sauri.
"Yi hakuri, zo ki rama"
Ya kai hannu zai rikota ta matsa da sauri ta tashi a guje ta bar masa gurin tana dariya. Murmushi ya mike tsaye ya bi bayanta.
Before time din da Dr A-B ya tsara yayi, Aliyu yayi nasa tsare tsaren ta yadda zai samu damar raka matarsa, sai kuma aka yi sa'a a lokacin ana hutun karshen sabuwar shekara ne.
Ana gobe za su tafi Abuja, Aliyu ya kaita da ɗanta gurin Mama Baraka gurin mata bakwana, ta zaren labari yayi tsawo Emily ta bayyana mata fargabarta na tafiya tana ganin kamar ba zai karbe ta ba.
"A gurin Bature haihuwa babu aure ba illa ba ce, kusan ma sun fi yin haka, ina da yakinin zai karbe ki"
"Idan ya tambayi labarinki fa?"
"Ki fada masa komai, amman ban da mutuwar aurena"
"Why? Za ki komawa mahaifinsu Kameela ne?"
"Ba lallai ba, na lura kamar ya dauki abun da zafi sosai, ni kuma ban shirya auren kowa a yanzu har sai na aurar da duka yarana, by that time kuma na san aure ya fita kaina"
"Amman da yanzu ace Mahaifinsu Kameela zai dawo zaki koma masa"
"To me zai hana?"
Ta amsa tana murmushi, Emily ta kalleta ta sauke kai ga dukan alamu tana son tsohon mijinta, sai dai kuma zama ya kare a tsakani. Sai dare Aliyu ya zo ya dauke ta bayan ya ajewa Mama Baraka siyaya kamar yadda ya saba.
Abuja suka fara tafiya sai da suka kwana a gidan Dr A-B da ya bukaci su kwana a gidan amman Aliyu be yarda ba, sai ya kwana a gidansu gurin Ummi. Emily kuma ta kwana a gidan ɗan'uwanta.
Matarsa wayayyiya ce kamar shi, tana da son mutane da nuna kulawa Emily ta yaba da yadda aka tarbe ta. Alhaji Bulama na da na shi uzurin haka ya saka Dr A-B ba samu alfarma tafiya a jirgin mahaifinsa ba sai na kasuwa.
Ba a cika samun direct flight daga Nigeria zuwa Scotland kai tsaye ba. Yawanci Ana tashi daga Lagos (Murtala Muhammed International Airport LOS) ko Abuja, kasancewar a Abuja suka kwana a nan jirginsu ya daga sai ya sauka a London Heathrow, sai da suka huta a wani hotel dake kusa da airport din sannan suka dawo suka shiga wani jirgin ya ɗaga zuwa Scotland. Tafiyar daga Abuja zuwa London ta ɗauke su kusan 6–7 hours.
[9/7, 7:58 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08?mode=ac_t
*🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
Page 7️⃣7️⃣
Kin dade kina sha’awar sayen kaya a wajen Khadeeja Candy amma ba ki samu dama ba?
Kin shirya fara tanadin kayan Sallah ko na azumi tun yanzu? Ko kuma tanadin kayan auranki ko na ’yarki? To, ga sauƙi ya iso!
ADASHE NE NA GATA!
Ki zuba kuɗi, ki ɗauki abin da kike so daga:
Sutura da zannuwan gado
Kayan kitchen
Kayan electronics (fridge, freezer, washing machine, gas cooker, da sauransu)
Talkami da jaka
Zanen gado
Frames (flowers decoration ko standing ones)
Console mirror
Boxes na Lefe ko na traveling.
Warmers iri-iri
Food flask iri daban-daban
Jugs da flask. Kai abin fa sai wanda rai ya so!
Sauƙi ya zo, za ki mallaki duk abin da kike so a wajen Khadeeja Candy cikin aminci da kwanciyar hankali, babu cuta babu cutarwa.
📌 Tsarin: Zubi ne wata-wata da kuma sati-sati.
📌 Akwai sharudda da ka’idoji.
Domin ƙarin bayani, ki/ka
tuntube ni ta wannan lamba: 08036126660
Ko ta hanyar WhatsApp 👉 Danna nan https://wa.me/message/2Y7RIJEODZO2K1
Ko kuma ku yi join WhatsApp Group https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08?mode=ac_t
Thank you 😍 🙏
Daga London zuwa Edinburgh/Glasgow kusan 1 hour flight ne. Jimilla tafiyar ta zame musu ta 10 - 12 hours bisa layin jirgin da suka bi. Scottish, Scotland tana cikin United Kingdom (UK) ne, arewacin Ingila take. Tana da manyan birane kamar Edinburgh (babban birni), Glasgow, Aberdeen, Dundee. Yanayin can yawanci sanyi ne sosai, musamman lokacin hunturu (November–March), akwai ruwan sama da iska mai ƙarfi, balle kuma yanzu da yake January. Shiyasa suna sauka filing jirgin Edinburgh Airport (EDI) dake garin Edinburgh, Aliyu ya rufe matarsa da rigar sanyi da ya riko mata, dan kam tun a jirgi yayi masa tanadi daman shi yake kula da abunsa..
Tun da suka sauka kasar Emily ta tabbatar sun zo garin yan'uwanta domin yawan mutane kasar kowa zaka gani jan gashi ne irin nata, tana ta kallon manyan gine ginen da kawar gari ta zo inda bata sani ba. New Town, wata sabuwar unguwa ce da mai taxi ya kaisu bayan Dr A-B Ya Fada masa domin a unguwar mahaifinsu yake.
Aliyu ya fara fita motar yana rike da Abulkhary dake bachi sannan ya bude mata ta fito tana kallon gaban gidan da suka tsaya wanda tsarinsa ya sha banban da na mu na hausawa.
Karamin gate ne ba mai tsawo sosai ba an saka flower gefe gefen na gida ga haske normal ba. Gidan sama ne mai fadi amman ba mai ado da lankwashe lankwashe kamar na mu ba.
Aliyu ya tsaya a gabanta ya saka hannunsa daya ya gyara mata fuskarta,.ya cire mata hullar kanta gashinta ya bayyana sai ya baza mata gashin ko'ina, sannan ya rika hannunta suka nufi kofar shiga gidan.
Dr A-B ne a gaba tare da matarsa Emily tana daga baya tare da Aliyu. Door bell ya taba sannan ya kara fuskar sa gaban ring camera yayi magana kasancewar sun shigo da dare ne a lokacin da sawu ya fara daukewa. Wata kyakkyawar matashiyar yarinya ce ta fara bude kofar tana ganin Dr A-B ta saka ihu ta rumgume shi shi ma ya rumgumeta yana murmushi.
Aliyu ya kara matse hannun Emily take hannunsa domin ya lura fargaba ta cikata ta ko'ina.
Da suka shiga ciki kowa kallon Emily yake saboda an labarta musu ita tun kamin ta zo, kuma sun ga zahiri domin bata rage komai daga kammanin mutumen dake tsaye gabanta yana kallonta ba.
"Dad wannan ce Emily yarka, Emily wannan shi ne mahaifinki"
Ya dade yana kallonta kamar ya rasa abun yi, bata bar komai daga kammaninsa ba, shi kasan da ya ganta sai da yayi rabin mutuwar tsaye, domin duk yayansa babu wanda yake kama da shi sosai da sosai kamar yadda ita take yi. ita ma tana ta kallonsa sai hawaye take.
"Dare yayi ya kamata kowa ya kwanta gobe za mu yi abun da ya kamata domin tabbatarwa"
"Dad baka ga kamammi ba?"
"Kammanin kawai ba su isa su wadatar ba ya kamata mu bi ka'idodi"
Kamar wanda be san taya zai karbe ta ba, haka ya tarbe ta sai duk kuzarinta ya gushe. Sai dai Aliyu da Dr A-B sun kafarara mata guiwa, a dokar kasar be isa ya amsa cewar shi ne mahaifinta kai tsaye ba ta hanyar kammani ko sheidu sai da takardun shedai gwajin jini kuma sai ya zama tana bin sunansa ne.
Emily ta kwana da tunani, washe gari da suka hadu teburin cin abinci sai ta lura babu mahaifinta a gurin sai yan'uwnta maza biyu da mace biyu da kuma matarsa da tun jiya suke rigima saboda abun da ya aikata shekaru da yawa da suka wuce.
Kusan kowa be saki jiki da ita a gidan ba, saboda dokar bata tabbatar ba, har sai da suja tafi Asibiti aka yi musu gwajin kwayoyin halitta ita da mutumen da take ikirarin ɗanta ne results din ya fito at 98% sannan mahaifinta ya yarda. Tana zaune wajen asibitin ita da Aliyu dake rike da hannunta ta dora kanta a kafadarsa. Mahaifinta ya fito daga cikin asibitin yana rike da takardun gwajin.
Emily na ganinsa ya mike tsaye tana kallonsa ya nufo inda yake with so much emotional tana jiran ya fada mata results din dake hannunsa sai ta ga kawai ya rumgumeta.
Aliyu ya sauke sanyayar ajiyar zuciya yana murmushi tare da yi ma Allah godiya. Shi kansa abun da ya faru jiya ya ba shi tsoro. Ya dagota daga jikinsa ya duba fuskarta ya taba ya sake maida ita jikinsa.
"Na san kin zo da tari tambayoyi da suka bukatar amsa.."
Ya sunbance saman kanta.
"No na riga na san amsar komai, na san duk abum da na ke son sani, komai ya faru ne ba da son ran kowa ba"
"Yeah ki yafe min, da ace na san tana dauke da cikinki ba zan juya baya ba, dukan mu muna kuskure na yi kuskure na sani I'm sorry"
Emily ta rike hannayensa.
"Mu daina tuna baya, na zo nan ne saboda samun karin farinciki da kuma sanin asalina, ba amfanin tuna abun da ya wuce"
Ta juya ta nuna Aliyu.
"Wannan mijina ne, wannan kuma yarona"
Ya mikawa Aliyu hannu suka gaisawa, da ya tara hannu zai karbi Abulkhary sai yaki zuwa saboda kewa yake yi baya yarda da kowa sai iyayensa.
Duk yadda Dr A-B zai yi ya fahimtar da Step Mom dinsa mahaifinsa ya aikata kuskure kuma yayi nadama sai da yayi, domin a gurinsu kamin abu ne ta maka shi a kotu ta nemi a raba auren, kuma a raba har ma da ganimar daukar dukiyarsa a damka mata kuma a bata ragamar yayanta. Ta inda ta saurara masa be aikata hakan a lokacin da yake aurenta ba. Ya aikata ne kamin ya hadu da ita.
Sam ita kam baya yarda ta karbi Emily ba, sai ya zama ma. Kamar tana kishinta saboda Emily ta fi kama da mahaifinta fiye da yayanta, ga shakuwa da ta shiga tsakaninsu na dan zaman da ta yi a gidan, yaran ma sun sake jiki maza da mata amman ita bata yarda da Emily ba. Mahaifinta ya kaita gurare da yawa, ya nuna mata abubuwa wasu daga tarihinsu wasu kuma daga tarihin garin.
Mutumen mai kaunar karensa sosai duk inda yaje yana tafiya da su domin rakiya, tun tana tsoro har ta daina. Wata rana da ya tafi da ita gurin da yake kamun kifi ne yake tambaya labarin Mama Baraka, ta fada masa kuma ta labarta masa yadda abubuwa suka faru da ita. Ya tausaya mata matuka, ta nuna masa hoton Fatima a wayarta.
Honeymoon din da Aliyu be samu tafiya yayi da matarsa ba lokacin da suka yi aure shi yayi da ita a nan. Ya jata sun shiga gari sun yi yawa har makotan garin sun ziyarci gurare dabam dabam. Sati daya ta yi a gidan ya dauke matarsa suka tafi yawon amarci. Dr A-B daga can wata kasar ya bulla. Mahaifinta ya saka ta gaba suka tafi aka ayi komai a rubuce da ka'ida cewar shi ne mahaifinta a doka.
Da za su tafi Emily ta yi kuka sosai tana ta kewar mahaifinta, ta rumgumi yan'uwanta ta yi musu bankwana tare da jaddda musu za ta dawo a duk lokacin da ta bukaci haka. ya rumgume yarsa ya saka mata wata sarka tashi mai tarihi ya dauko kudi mai yawa ya bawa Emily amman bata karba daman bata zo domin kudinsa ba sai dan ta san waye ubanta shi ma kuma ya san wacece ita, amman ta karbi kyautar agogo da hotuna da yayi mata...
Karfe bakwai na safe suka bar kasar ita da Aliyu, sai da suka sake daukar awanin da suka dauka da farko sannan jirginsu ya isa Nigeria suka sauka da dare saboda awaninin ba daya ba. Ummi ta aika da mota aka dauko su daga Airport, zuwa gidan inda suka samu tarba ta musamman.
Washe gari suka sha hira da Ummi na abubuwan da suka faru da kuma yanayin garin da guraren da suka ziyarta, hotunan da suka dauka da sauransu.
Satinsu daya Abuja sannan suka dawo Kaduna, rayuwa ta cigaba kamar yadda aka saba. Da Fatima ta yi arba da hotunan da aka dauka a wayar Emily ta sha kuka sosai ba a tafi da ita, Emily ta mata alkawarin idan zata koma da ita zata tafi. Har a lokacin Ammy bata yarda Fatima ta zauna a hannun Emily sai dai ta rika zuwa tana dawowa, sai kuma idan fitsarar Fatima ya tashi ta nace sai ta kwana a gidan.
Emily na yaye Abulkhary Aliyu ya biya mata Ummara ta tafi tare da Fatima da shi, da Abulkhary, a can suka yi sallah karama ba su dawo na sai bayan Sallah. Da lokacin hajji yayi kuma ya cika mata kawarin da ya daukar mata tun tana da cikin ɗansa. Ita kadai ta tafi ta yi hajji ba da shi ba saboda yanayin aikinsa.
TURHAN POV.
A shekarar da Emily ta tafi hajji a shekarar Turhan ya yafi, shi da matarsa sai dai har kowa yai ibadarsa ya gama be hadu da dan'uwansa ba saboda jirginsa kasar da masaukin kowa dabam.
Turhan yana zaune yana waya da Fatima yana fada mata abubuwan da ya tara mata a dakinta dake gidan. Matarsa ta shigo, ta zauna can nesa da shi ta zauna, haka take a duk lokacin da yake magana da yarsa saboda tana kishin Fatima ba yarta ba ce, kuma tana kishin duk wani abu da zai dauke hankalin mijinta daga gareta. Ta jira har sai da ya gama wayar sannan ta koma kusa da shi ta tsaya tana murmushi.
"Rufe idonka"
Ya kalleta cike da shauki, yayi murmushi ya rufe idon kamar yadda ta bukata. Ta kama hannunsa ta saka masa abu a hannu, ya lakaba abun sannan ya bude idon. Wasu yan mitsitsinan kayan yara ne irin na yar tsana amman na jarirai.
"Da leek.. laken testanna tisʿa shuhur."
"Wannan domin kai ne, amman ka jira sai nan da wata tara"
Turhan ya kalleta ya sake kallon kayan, kamin tunaninsa ya ba shi abun da ya dade yana tsammani daga gareta. Wani irin tsalle Turhan yayi ya dauke matarsa yayi sama da ita yana juyawa. Kamin ya sauke ta tambayeta.
"Kina ciki da gaske?"
Ta daga mishi kai tana
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 62 Chapter of 63