a yau ta dandanin miye auren so da masoyin gaskiya.
"Meyasa ban hadu da kai ba tuntuni?"
Ta tambaya tana murza kanta a kirjinsa kamar zata tsaga kirjinsa ta shige cikin zuciyarsa. Sai ya bata amsa cikin rada shi ma idonsa a lumshe cike da kwalla, auren soyayya suka yi da Kameela amman ko ita bata nuna masa kaunar haka a ranar aurensu ba kamar Emily.
"Ita ce tambayar da na dade ina yi ma kaddara, miyasa bata hada ni da ke, tun farkon da ta bude miki shafi"
"Aliyu ina ƙaunarka"
Ya bude ido ya sauketa ya rika fuskarta yana kallon cikin kwayar idonta.
"Duk wata kauna ta furuci ko ta aiki, ko wanda take zaune a zukanta masoya, Ayusher na fi kauna, kaunarki, na fi numfashinki son kasancewa da ke, ni da ke ABOKAN RAYUWA ne, sai da mutuwa"
Ta yi sauke wani sanyayen numfashi ya lumshe ido tana murmushi.
“Madalla da kasancewarka cikin rayuwata, ka zamo min tauraro mai haske. Madallah da ABOKIN RAYUWA irinka"
Ya kai goshinsa ya hade da nata, hancinsa a saman nata, ya saka yatsunsa na dama cikin nata, na hagu ma haka suka tsarkafe yan yatsunsu cikin juna.
"Abokiyar tafiyata, har tsawon rayuwa, Madalla da ABOKIYAR RAYUWA irinki"
Sun dade a haka sannan ya sake ta ya matsa baya. Ta kalleshi tana murmushi a yau ta san yadda rumgumar masoyi take mantar da damuwa, ya sameta tana kuka ya maye mata gurbin hakan da murmushi.
"Idan akwai abun da kike son aikatawa, ni halalinki ne just do it"
Ta taka one step forward kamar ya san manufarta sai ya maida hannayensa baya ya duko da fuskansa ta sumbanci gefen fuskansa da sauri, ta juya baya tana jin kunya. Murmushin dake fuskarsa ya fadada har ya bayyana hakoransa. Ya nufi kofar fita har ya kusa isa sai kuma ya yanke tafiyar ya juyo ya dawo gurin masoyiyyarsa ya rumgumeta ta baya, sai kuma ya juyo da ita, da sauri ta saka hannayensa ta rufe fuskarta. Hannayen dake fuskarta ya sumbanta ya goga fuskarsa yana dariya sannan ya saketa ya fice dakin ya rufe mata kofa yana jin kamar kar ya tafi ya barta.
TURHAN POV.
A lokacin da ya fito daga falon na Daddy waje ya tsaya jikin motar da suka zo, ya ji duniyar kamar tana juya masa, ko da wasa be yi tsammanin Emily zata juya masa baya har haba ba, kuma a gaban iyayensa. Dadin dadawa kuma ta furta sunan wanda take kaunar a gabansa cikin kunnensa.
Miya yayi ma Aliyu? Ita ce tambayar data fara zuwa masa a rai. Miyasa ya dauki bata masa ta wannan hanyar? Wace irin kiyayya Emily take masa har haka? Be samu amsoshin tambayayinsa ba Sarkin ya fito, kamin ya shiga motarsa Alhaji Bulama ya fito tare da Mahaifin Kameela, shi dai ya san ya shiga mota, yadda aka yi suka kama hanya har suka isa gidansu Ammy shi ne abun da be san yadda aka yi ba.
Ya zauna cikin falon yana sauraren yadda Alhaji Bulama yake labarta mata abubuwan da suka faru, yana jin mahaifinsa yana magana da ita amman be fahimce me suke magana kai ba, a yau ne karo na farko da yaren larabci ya subuce masa a kai.
"Aliyu... Aliyu... Aliyu..."
Furucin Emily nata dawo masa, be san yaushe aka mahaifinsa ya fita ya dai ji Alhaji Bulama ya dafa shi yana fadar maganar da be gane ba, yana zaune a falon kowa ya fice be san an yi ba sai da Ammy ta girgiza shi.
"Turhan nan?"
"Ammy me na yi ma Aliyu? Ina ta kokarin tariyo rayuwarmu ta baya zaman da muka yi, me na masa? Ashe ko ba ni da rai bancanci yayi min hallaci ba?"
Ammy dake tsaye ta zauna idonta cike da kwalla.
"Ka yi hakuri Turhan, ba a taba cin amana aka yi nasara ba, muna nan da kai hakki zai bayyana"
"Miyasa ita ma ba zata fahimce ni ba? Ko. Kalaman ne nawa ba su kai ba? Wallahi ina sonta ina kaunarta Ammy, kuma ba zan sake cutar da ita ba, Wallahi na yi alkawari ba zata sake zubar da hawaye akaina ba"
Hawaye ya sauko ma Ammy, ko wace uwa bata son ganin danta cikin damuwa balle kuma Ammy da Turhan kadai take da shi, bata tana ganin tsananin damuwa a tsare da shi data gusar masa da hankali ba irin yau.
"Tashi ka tafi ka yi sallah"
Be haura sama ba sai ya fice falon a masallacin yayi alwala yayi sallah, suna fitowa masallacin mahaifinsa ya kira shi akan ya shirya, jirginsu zai tashi karfe 5pm, daga shi sai DR A-B ake jira saboda Dr A-B yace ba zai bar garin ba sai an daura auren Emily da Aliyu kuma karfe 4:30pm za a daura. A nan ya ji wani labari da yafi furta sunan Aliyu azaba a zuciyarsa. Daker ya iya kawo kansa falon Ammy. Yana shigowa ya nufi agogon dakin ya tsaya yana kallo yadda dakika take juyawa ta zama minti. Jikinsa yayi ma kafafuwansa nauyi yana ta lilo jiri na dibansa kamar zai fadi.
Yana ta kallon agogon da second din ke dis da bugawar zuciyarsa yana jin wani dubu na haye masa kai. Har agogon ya nuna karfe 4:30pm. Turhan ya rufe ido, Ammy dake tsaye bayansa tana kallonsa ta karaso ta rike ɗanta tana jansa baya a hankali har ya zauna kan kujerar dinning.
"Ammy a yau na san rashi, na san miye kiyayya, na kuma san miye soyayya, da na sani ƙeya, tsanar da Aisha take min ta kai har ta auri abokina ta bar ni? Shin ita bata tafiya ne? Ammy ina son yarinyar nan miyasa kika cilasta na sake ta? Ammy ma rasa Aisha, uwar ƴata na rasa ta, cikon farincikina na rasa shi a yau....!"
Hawaye ne masu zafi suke sauko masa, ko Ammy sai da tsoro da tausayin ɗanta suka kamata, domin bata taba ganinsa cikin wannan yanayin na gasawa da rudani irin wannan ba.
" Dady?"
Ya ji muryar yarsa da sai a yanzu ta filo daga dakinta ta sauko kasa duk abun da ake bata sani ba. Turhan ya saka hannayensa biyu ya dafe kansa baya son yarsa ta ga hawayensa. Fatima ta zo da gudu ta rumgume shi.
"I miss you... Dady ka dawo? Ina Momy kace tare za ku zo ba?"
"Momy ki ta zabi Aliyu Fatima, ta barki ke da Dady, Momy ki ta auri Aliyu bata auri Dady ki ba, tace Aliyu take so ba Dady ki ba"
Ammy ta fada mata tana hawayen tausayin danta gaba daya ta rikice. Cikin tsoro Fatima ta bude hannayen Turhan babu hawaye a fuskarsa amman suna kwance a cikin idonsa, sai kawai ta fashe da kuka sosai ta rumgume. Ya dauke ta ta dora saman jikinsa ya hade duk wani abu da yake ji ya fara rarrashinta. Wayarsa ta yi kara alamar shigowa sako, ya ciro wayar ya duba Dr A-B ne ya aiko masa da sako cewar za su tafi shi ya tsaya sai next week, ya aje wayar ya kalli mahaifiyarsa sai ya sakar mata murmushin karfin hali.
[8/25, 8:41 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
Page 7️⃣1️⃣
KAMEELA POV.
Sosai ta natsu tana sauraren labarin da Hajiya take bata kamar yadda Alhajin ya fada mata yadda abubuwan suka faru.
"Wai kawai sai ta bude baki tace Aliyu... Na ce daman dai hadin baki aka yi da uwarko?"
Kameela ta kai tsaye.
"Hajiya dan Allah karku bari a yi auren nan, Wallahi ina son mijina, kuma na san yana so na, kawai makircin yarinyar nan da uwarta"
"Zancen banza, aure ai tuni aka daura, babanku yace mai gidansa da dansa ba su bar garin nan ba sai da aka daura auren, wai da la'asar sai kace auren kauye"
Anty Shafa ta karba mata.
"Auren kauye ai yafi na wannan arniyar daraja, kuma shegiya ce shiyasa suka daura auren kar ya subuce, dadin dadawa kuma Mama Baraka ai zata iya yin komai saboda ace yarta ta auri Aliyu kin ga ai ta yi gasa da ke"
Kameela ta dora hannu a kai.
"Na shiga uku, Innalillahi... Hajiya ina son mijina ina son Aliyu"
Hajiya ta daka mata tsawa.
"Ke dalla gafara can mahaukaciya, Aliyu autan maza ne halam? Tun da kika aure shi wani farinciki kika samu? Kuma ke da kike ikirarin ba zaki zauna da mai mata ba? To yanzu ai yayi aure, kuma shi be damu dake ba sai ke? Ko kuma mu mahaukata ne da za mu bar ki yi kishi da marar uba? Yarinyar da bata kai rabin matsayinki ba? Daman can ba son auren nan muke ba, shi kuma be shirya rike amana ba, aure be jimawa daga dawowa haihuwa an fara samun matsala"
Ta fashe da kuka tana jin duniyar ta juye mata mijin da take so ya juya mata baya, dakunsa da take kuma ya kare a yau saboda yayi auri abun da bata taba zato ba, gashi iyayenta sun kasa fahimtarta.
"Ki duba ba fa Hajiya, ko irin ya dawo yana bada hakuri din nan be yi ba, gaba daya ya nuna shi daman ba sonta yake ba, kawai iyayensa da shi sun shirya wulakanta zuri'armu ne, idan har yana sonki kuma yayi nadama ai kamata yayi ya kawo kansa yana kuka yana faduwa kasa yana tuba, amman ba ko da ya, sai ma tafiya ya auri marar asali ko dai ya manta waye shi ne? Kuma iyayenwai suka bar shi? Tab"
Anty Shafa ta fada tana tabe baki da jinjina lamarin. Kameela ta tashi ta bar su a falon, dakinta ta shige ta kwanta kasa tana kuka kamar an yi mata mutuwa, bata taba jin zafin azabar kishi da bakincikinsa ba irin yau. Aliyunta ne dai yayi aure? Ta rarraba ta isa bakin gadonta ta kai hannu zata dauki wayarta kuka ya ci karfinta.
" Aliyu ka yi aure? Ina alkawarin da ka yi min Aliyu? Ina soyayyar da na nuna maka?"
Ta kai hannu daker ta dauki wayar ta da sabon layin da take aika masa sako ta gwada kiransa tana kuka, ringing daya ya daga, ba dan be san mai kiran ba sai dan ya shiryawa kiran.
"Sallamu Alaikum"
"Aliyu ina alkawarin da ka yi min? Cewar ba zaka min kishiya ba?"
"Na cika miki, tun da ban miki kishiya da igiyar aurena ba"
"Ina ladar soyayyar da na nuna maka?"
"Na miki sakamako iya yadda zan iya, fadi tashi a tare muka yi har iyaye suka amince muka yi aure, yanayin rayuwar aurenki da zafin kishinki, rashin nazari kamin yanke hukunci sune abubuwan da suka hana zaman aurenmu, kuma ba zan miki Karya ba, kowane namiji yana son kwanciyar hankali da farinciki a gidansa, iyakar hakkinki na baki, har wanda ba naki ba na baki, kin wuce gona da iri Kameela, idan ma na ce zan cigaba da zama dake ba ni da kwanciyar hankali, kuma mahaifiyarta ba zata yarda ba, gashi kuma iyayenki ba so na suke ba"
"Munafiki azzalumi maci amana, can da baka ganin komai sai a yanzu da ka auri karuwa? Yar titi marar uba? Yar zina? Matar da aka haifa na da aure ba? Ai baka yi aure ba Aliyu tun da baka auro yar gidan mutumcin ba"
"Zaki iya zagina ki ci mutumci, amman ban da matata, dan an haife ta ba da aure ba, miye laifinta? Ko kina tunanin dan'adam yana iya tsallake kaddara ce ne? Ko daga sama ta fado ina sonta a haka, dan haka karki sake fadin wata magana marar dadi akan matata, kamar yadda ban yarda a taba mutumci lokacin da nake aurenki ba, ba zan yarda a taba mutumcinta ba"
Ya yanke wayar, Kameela ta ji kamar ta haukace tsabar bakinciki na jin kalaman Aliyu. A daren da bakinciki ta kwana tunani be barta ta runtse ido da sunan bachi ba, ganin abun take kamar mafarki, wai Aliyu yayi aure, a tunanin zai gama kewaye kewayensa ne ya dawo mata. Idan ta tuna yadda take rayuwa da mu'alama da mijinta, ta hango yanzu Emily ce a makwafinta, sai ta ji kamar zata haukace, wani karin bakin cikin ma Emily daga tsatson Mama Baraka take ba, da ace daga wani gurin ne dabam wata kila zata fin saukin kishi.
Yanzu kenan Emily ta yi nasa? Bayan ta shiga tsakaninta da mijinta tun a PH gashi kuma ta aureshi, babbar matsalar ta ma babu mai rataya kishin ita kadai take yakin, tun da yan'uwanta sun gagara fahimtarta. Haushinta da Hajiya ta ji ya saka bata damu ta cilasta mata fitowa ta ci abincin ba, a ganinta akwai mazan da suka fi Aliyu komai nesa ba kusa ba, amman tana wahalar da kanta ta wanda tun tashin farko ba su so auren da shi ba, a yanzu ma taki ta bawa wasu kofa ne amman ana nuna mata kauna, gata kyakkyawar bazawara sakin Wawa, babu ɗa balle abu ya dame ta.
Sai da ta bari kowa ya gama karyawa sannan ta sauko ta nufi dinning kanta na tsarawa kamar zai fashe, ta zuba madara da suga a cup ta zuba ruwan zafi sai kuma ta ji ba zata iya sha ba.
Ta zauna a kujerar tana kallon Anty Shafa dake kwashe kayan wasan yaranta.
EMILY POV.
Kusan wannan ne karon farko da aka daura aurenta ta kwana da cikakke farinciki. Wacan auren nata na farko anyi shi ne a lokacin da iyayen mijinta basa so, kuma bata da wanda ya tsaya mata, tsabanin yanzu da komai kishiyarsa ne, na biyun kuma an daura da wanda bata so be san darajarta ba...
But Aliyu ya zama wani na dabam a gareta, ya nuna mata farinciki da jindadin data kasance matarsa, gashi mahaifiyarsa tana sonta, ga shi yan'uwanta sun shaida. A yau ta kara sanin darajar yan'uwa da dadinsu. Ta farka cike da farinciki, da kuzari tana gama Sallah asuba sakon Aliyu ya shigo wayarta.
"Barka da safiya matata mine and mine only, farar mace mai farar zuciya"
"Barka da safiya Aliyu?"
"Wato Aliyu ko? Idan na zo sai na horar da bakin nan sai na masa hukunci"
Ta yi dariya.
"I'm sorry"
Ta rubuta masa.
"I love you"
Ta maida masa amsa da heart Emoji guda biyu. Sannan ta dauko karatun da suke fara karantawa, sai ga kiransa ya shigo ta amsa tare da amsa sallamarsa.
"Amince ya tabbata ga kyakkyawar yan mata ne mai zazzakar murya, da tattausar zuciya"
Ta yi murmushi mai sauki.
"Tare da jarumin da ya tare komai ya wanzar da farinciki a zuciyata"
"Zai wanzar dai, yanzu ne zai fara aikin, ina nan kwance ina ta tunaninki, kuma na san idan na dako sammako Ummi zata gan ni, dan haka na jira na ji muryarki"
"Na gode da ka kira ni"
"Aa ranki ya dade na gode da kika amsa, za mu iya karatu ta waya? Ko sai na zo?"
"Zaka iya?"
"Ta ina zuciyarki ta samu kwarin guiwar tambayar abun da ba zan iya ba saboda ke?"
"Ina sonka Aliyu"
Ta fada da kwalla a idonta.
"Ni kam kaunarki nake Amaryata wacce ta fi ta kowa, bude littafinki ki fada min abun da kika iya"
"Ni ba na gane komai idan baka kusa da ni"
"Ki sassauta kalamanki, inda ba son kike zuciyata ta fashe da kaunarki ba, da kuma kewarki da na yi a yau fiye da kullum"
Ta yi dariya. Sannan ta fara karatun bakin inda ta iya ya dora matada wani. Bayan sun yi sallama ya aiko mata da sakon.
"I love you"
Ta aika masa da sakon heart.
"No ki ko yi fada min I love you, yana kara damkon kauna kuma ni mijinki ne"
"Okay" as reply
"Okay??"
I love you ta tura amsa.
"I love you more"
Ya maido mata da amsa. Ta kwanta a gurin tana ta kalmomin cike da kaunarsa. Misalin karfe takwas na safe ta fito dakinta ta sauko kasa cike da kunya ta shiga Kitchen domin ta ya Ummi aiki kamar yadda ta saba.
"Yanzu nake kokarin cewa a kiraki, ki shigo ko kara koyar abubuwan da mijinki yake so"
"Ummi ina kwana"
"Lafiya ƙalau, an tashi lafiya?"
"Alhamdulillah"
Ta amsa tana jin tsananin kunya abun da bata saba ba. Suna tsaka da girkin ne, daya daga cikin ma'aikatan gidan ya kwankwaso kofar ya sanar da Kulu dake mopping din falon cewar ana sallama da Emily. Kulu ta shiga kitchen ta sanar da Ummi.
"Wake sallama da ita?"
"Ban tambaya ba Hajiya"
"To ki tambaya mu ji, yana ina?"
Kulu ta juya, bata jima ba ta dawo.
"Wai Hajiya Baraka ce"
"Ah ah tana ina?"
"Can wajen gate"
Daga Ummi har Emily fuskar mamaki suka yi.
"Bata shigo ba?"
Emily ta tambaya.
"Eh haka yace tana can waje"
Ummi ta dan yi shiru sannan ta amsa.
"Toh gata nan zuwa"
Sai da Kulu ta fice sannan Ummi ta kalli Emily ta ce.
"Wata kila tana son ta yi wata magana da ke bata son mu ji ko mu gani, ki tafi ki same ta"
"Okay"
Ta amsa sannan ta bude kofar baya ta kitchen din ta fice daman jikinta a lullube yake da Hijab. Ta nufi gate din ta bude a hankali ta fita, ta yi zaton ganin Mama Baraka ne, sai ta yi arba da Turhan tsaye kusa da motarsa. Da ta duba ko'ina bata ga alamar Mama Baraka ba sai ta juya zata koma.
"Ba zan samu damar da za ki saurare ni ba Aisha?"
"Wata kila zaka fada min magana marar dadi ne"
"Aa dan Allah ki saurare ni"
Ta juyo ta matsa kadan ta tsaya tana rumgume da hannayenta. Da ya kalleta sai ya ji kamar be san miye so ba sai a ranar. Cikin yanayi na sanyi jiki da damuwa ya soma magana.
"Na san idan na ce ni ne, ba za a barki ki fito ba, saboda ke da mutanen gidan kuna kallona a matsayin makiyinku ne, shiyasa na yi amfani da sunan Mama Baraka"
Ba ta dai ce masa komai ba har ya dora.
"Aisha zan kara da kara baki hakuri na abubuwan da suka faru tsakaninmu, kasancewarki a rayuwata ya koya min darasi mai yawa, na san zafin so, na san zafin rashi, kuma na san zafin da kika ji lokacin da na juya miki baya, saboda a yanxu ina jin fiye da abun da kika ji, ke kin ji zafi ne kawai amman ba dan kina so na ba, ni kuma yanzu ina fama da tsabanin haka ne. Jiya da dare ban yi bachi ba, ina ganin abubuwan da suka faru kamar a mafarki, amman yau da safe sai na fahimci wani abu, idan kana son mutum ai zaka so farincikinsa ko? In har zaki yi samu farinciki da ni na kasa baki a gidan wani ne, me zai saka ba zan so haka a gareki ba? Idan na ce miki ban yi bakinciki ba na yi karya, ban kuma ce zan warke ba, amman sannu a hankali zan samu salama"
Ya hade yawu.
"Na gode Aisha, da kiyayyata ko tunanin abun da na miki, da wahala bata saka kin zubar da cikina ko jefar da yata ba, na gode da kika kula da Fatima, na gode da kika yi ma Ammy biyayya gurin aurena, a yayin da ni na kasa yi mata biyayya gurin rike amanarki, kuma ina fatar a duk lokacin da wani abu ya taso na Fatima idan na sanar miki za ki shiga ki tsaya mata kamar yadda kika saba, na kawo ne saboda anjima kadan jirgimu zai daga, zata zauna gurinki na dan lokaci, idan na dawo zan dauketa zan tafi Sudan da ita, na yi magana da Ammy ta amince kuma ina fatan ke ma ba za ki, ki yarda ba, ki yi hakuri amman ba zan iya barin yata ta zauna a gidan wani ba"
Hankalin Emily ya tashi.
"Fatima ta yi kankanta ka tafi da ita masarautarku, har yanzu bata san ta banbance daidai da rashin daidai ba, ta yi kankanta ta fuskanci kalubale"
"Kina tunanin zan iya bari a wulakanta ke da kike mahaifiyarta, balle kuma ita? No babu abun da zai faru"
Yana rufe baki Aliyu ya iso kusa da gate din gidan da motarsa. Ya bude motarsa ya fito ya tsaya inda suke, yana kallon Emily da karantar yanayinta sai dai be ce komai ba, ba shi da nufin zafafa domin Turhan uban yarta ne matukar ba yayi kokarin wuce gona da iri ba ne, dole zai bar wata karamar kofa a tsakani. Turhan yayi murmushi yana kallon Aliyu.
"Ina taya murna, ka yi nasara, amman ka sani, ba a cin amana kuma a zauna cikin salama, kai ma nadama zata tambaye ka kamar yadda ta tambaye ni a yanzu"
"Ba zaka fahimce ni ba, amman Wallahi ban tsare wani abu daga gareka ko daga Emily da nufin na raba tsakaninku ba, kuma ban boye komai da nufin na mallaketa ba, ni da kai da ita, muna zagaye ne da kaddara, a jiya da iyayenka suka zo, Wallahi ban tsammaci zan same ta ba, indai har zan iya cutar da kaina to zan iya cutar da kai Turhan"
Turhan ya kalleshi sama da kasa kawai yayi murmushi, ya juya ya bude motarsa ya riko hannun Fatima ya fito da ita, yayi mata alama da ta tafi gurin Mamanta, ta kalli Emily da ke miko mata hannu tana mata murmushi.
A gurin Fatima ta murje ido ta rike rigar Babanta da hannu biyu ta juyawa Emily baya.
"Fatima sweetheart, za ki zauna gurin Momy yanzu kin ji?"
Ta girgiza masa kai ya kara rike rigarsa. Ta kalli Aliyu ta shige da fuskarta a jikin mahaifinta.
"Wani abun ka fada mata?"
Emily ta tambaya tana jin babu dadi. Turhan ya girgiza kai.
"Ban fada mata komai da zai saka ta tsane ki ko ta juya miki baya ba, kina kallona a matsayin makiyinki ne kawai, amman abun ba haka yake ba."
Emily ta matsa ta kai hannu ta riko sai Fatima ta buga hannun Emily tana hawaye ta kara rike Babanta.
"Tun da bata son zama, zan koma da ita idan ta bukaci ganinki direba zai kawota, ina miki fatan alheri ke da sabon ABOKIN RAYUWA"
Emily ta kasa cewa komai idonta ya cika da hawaye bata yi zaton haka daga gurin yarta ba. Turhan ya bude mata mota ta koma ciki ta zauna, ya rufe sannan ya zagaya ta shiga yaja motar ya bar su a gurin tsaye, yana jin wani irin bakinciki da be taba ji ba, amman idan ya juya ya kalli yarsa sai ta ji sassauci.
Emily ta bi motar da kallo tana hawaye har ta daina hangota.
"Kowa na zauna da shi sai ya juya min baya, har da ya..."
Aliyu ya rufe mata baki da sauri, ya juyo da ita ya sakata a kirjinsa ya rumgume, yana shafa bayanta a hankali, babu kalma ki yi hakuri rumgumar kadai sai ta ji hawayenta ya yanke, ta haka take iya gane Aliyu ne ABOKIN RAYUWARTA...
Ta dago kai ta kalleshi sai ya sake ta ya saka hannayensa biyu ya share hawayenta.
"Kuka be miki wahala ko? Zai na zane hawayen nan da suke bata fuskar matata"
Ya bude mata gate yana rike da hannunta.
"Shiga gida"
Ya saki hannunta ta shiga ciki sannan ya koma motarsa ya yi horn aka bude masa ya shiga ciki. Da ya faka harabar gidan sai da ya tsaya ya jira Emily ta iso ta shiga falon sannan ya bi bayanta. A lokacin da ya shiga falon ya ga babu kowa sai ya jidadi yayi hanzarin kamo hannunta ta baya ya juyo da ita.
"Hajiya ba ki gaishe ni ba fa"
"Mun gaisa dazun"
Ta amsa cikin rada kamar yadda yayi mata. Ya rufe baki ya kashe mata ido.
"Aw haka na tuna"
Ta cire hannunta da sauri ta nufi hanyar kitchen. Shi kuma ya nufi stairs yana murmushi. Dakin mahaifiyarsa ya shiga ya same tana daura dankwali.
"Ummi ina kwana"
"Lafiya kalau an shigo?"
"Eh, Ummi sai na samu Ayusher a waje"
"Eh Hajiya Baraka ce ta zo tana sallama da ita"
"Waye yace Mama Baraka ce? Ba ita na samu a waje ba Turhan ne"
Ummi ta kalleshi da sauri.
"Turhan? Wanda aka aiko ce mana yayi Baraka ce"
"Ummi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 57 Chapter of 63