Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta kama hannun Emily suka fice daga falon, kamin su isa gate Aliyu ya iso gurinsu da mota suka shiga ya kai su unguwarsu Tasmia, sannan ya juya ya koma, suna shiga ciki Tasmia ta hada ma Emily ruwan tea Emily ta sha kadan ta kwanta akan gadon Tasmia, tana ta kallon sama hawaye na mata zuba. Misalin karfe biyu na rana Aliyu ya dawo gidan domin babu wayar da zai iya jin Emily kuma yana son ya san halin da take ciki, ya kwankwasa kofar dakin Tasmia ta bude be shigo ba ya tsaya daga bakin kofa. "Na zo na duba Emily" A lokacin Emily ta samu yin bachi dan haka Tasmia ta amsa masa da. "Bachi take, ka shigo ciki" Ya girgiza mata kai ya juya zai wuce Tasmia ta ce. "Karka damu ba zan fadawa Kameela komai ba, ban san a ina kuka hadu ba, ban gama saninta ba, amman alamu na nuna ta sha wahalar rayuwa ina tausayinta sosai" "Wata kila da zaki saurari labarinta da zaki fi tausaya mata sosai, dan Allah ki zama jekadiyar musulunci ki canja rayuwar yarinyar nan tun da har ta yarda da ke" "In Shaa Allah" Ta juya yayi tafiyarsa ta bishi da kallo tana murmushi sai da ta ga zai shiga mota sannan ta rufe kofar gudun kar ya ga tana kallonsa ta koma tana lekensa ta windows. Bayan ya tafi ta dawo falon ta zauna after like 5 minutes ta ji an kwankwasa kofar ta tashi tana mamaki Aliyun ne ya dawo ko kuma wanene. Ta fara lekawa ta hango mutumen da annuri be samu gurin zama a fuskarsa ba, gabanta ya fadi ta matsa baya. "Waye wannan?" Bata samu amsar tambayarta ta aka sake buga kofar dakin. "Waye" Yaki magana sai kwankwasawa yake, sai a lokacin take dana sanin yin magana da tayi domin bata san waye ba gashi ta yi magana ya ji cewar akwai mutum a ciki. "Bude..." Ta juyo ta kalli Emily dake tsaye bakin kofar bedroom dinta. "Wani ne mai kama da marasa imani" "Na san waye bude" Ta bude ta yi baya tana kallon kofar Vito ya turo kofar ya shigo hannunsa daya a aljihu. "Ina tunanin mun kai karshe da ke cewar babu ke babu alaka da kowa? Amman gashi kin tafi gurin wani kato ya rufe danki yanzu kuma kin zo nan, Emily kina manta waye ni ko? Duk wani motsi naki akan idona yake" "Bayan wannan bana da wata kawa ko yar'uwa da nake alaka da ita, dan Allah ka bar min wannan ita kadai" Ta fada ta sigar magiya, ya kalli Tasmia da tuni mararta ta cika da fitsari ya ciro hannunsa ya nuna mata wata yar mitsitsiyar bindiga dake aljihu mai kama da ta wasan yara. "Ki yi taka tsantsan" Tasmia ta zube kasa "Wallahi har taka tsaki da tsakuwa ma sai na yi idan baka son alaka da ita ba zan sake ba, kai ni ban ma santa ba" Ta juya gurin Emily. "Ke na sanki? Kin san ni, ka gani ba mu san juna ba" Sai kuma ta fashe da kuka. "Wallahi ba ni da kowa a garin nan dan Allah ka rufe min asiri, bautar kasa na zo amman idan kace yau na kama hanyar garinmu Wallahi zan tafi..." Vito ya mikawa Hannu. Emily taka ta isa gurin da yake ta rika hannunsa tana kallon Tasmia ya jata suka fice daga falon. Motarsa ya bude mata ta shiga sannan ya shiga yaja motar be zame da ita ko'ina ba sai gidansa. Yana yin fakin ta kalleshi. "Me zamu yi a nan?" "A nan zaki zauna for now" Ya fita ya zaya ya bude mata, fitowarsa ta yi daidai ta fitowar mahaifiyarsa ta nufo inda take. _____________________________ Sannu ‘yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe ɗinki da kaya masu kyau, masu ƙima daga Khadeeja Candy Store Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sauƙin sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing. Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taɓawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet ɗinmu sun dace da ke Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sauƙi ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko’ina! Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame. Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ƙayatarwa duk a farashi mai sauƙi. Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu! Baki da lokaci? Muna da sauƙin oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina! To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haɗuwa. [5/17, 1:00 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ FOLLOW ME ON 👇🏻 FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914 TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Page 2️⃣5️⃣ After like 2 hours da tafiyar Emily Aliyu ya dawo gidan Tasmia ya kwankwasa ta bude masa a tsorace. "Ta farka?" Shi ya fara tambayarta domin damuwarsa a yanzu bata wuce ya san halin da take ciki ba. "Ai kana tafiya ina jin ko minti talatin ba ayi ba, wani mutum mai ban tsoro ya zo ya tafi da ita, har da yi min gargadi wai na yi hankali, ka ga kayana can duk na hada gobe ni barin garin ma zan yi" Tana maganar jikinta na rawa. "Saboda me?" "Da bindiga fa ya zo nan kuma daga ganinsa ba shi da imani kafiri ne ga Cross a wuyansa fuska babu annuri, ita kanta daga gani tsoronsa take" "Shi ya kawo ki da zai ce ki bar gari? A wane dalili? Ku daina sakawa kanku tsoro da yawa shi yake bawa mai cuta damar cutar da ku, karki je ko ina ki yi zamanki babu abun da zai same ki sai abun da aka rubuta ya kasance gareki" "Wato ba ka ga bindiga ba ne shiyasa kake fadin haka kuma baka ga fuskarsa ba" "Zaman a nan ra'ayinki ne, tafiyar ma ra'ayinki ce idan kin so" Ya fada mata sannan ya juya ya shiga motarsa ya bar gurin. A wunin ranar da darenta Aliyu ya wuni ya kwana da tunanin halin da Emily take a zuciyarsa, wata kila mutumen yana can yana dukanta saboda ta yi ma danta abun da take jin ya fi zama kwanciyar hankali da natsuwa a gurinta, zuciyarsa na raya masa wata kila yanzu ya canja mata kamanin fuska saboda duka, bakinciki zai zame mata biyu ga rashin danta ga duka. Ya busar da iskar bakinsa ya shafa kansa hannunta rike da mug yana sanye da kayan bachi. Sai da ya kira sahibarsa suka gaisa ya ji tashinta ya kira mahaifiyarsa, sannan ya sake gwada number Emily da har cikin dare yayi ta kira saboda ya ji halin da take ciki sai ya ji wayar a kashe. "Ki kirani idan kin riski sakona, ina son na san halin da kike ciki" Ya aika mata sako sannan ya zauna ya aje Mug din yana kallon harabar gidansa kamar wani bako. Can zuciyarsa ta raya masa zai iya zuwa ba tare da ta kira shi kamar yadda ta yi a wacan karon, waya sani ma ko Viton ya karbe mata waya ya hanata kiran kowa. Ya tashi ya koma ciki yayi wanka yayi shirin office na kananan kaya ya fito yana ta kamshi ya shiga motarsa ya dauki hanyar office dinsa, yadda yayi zato ba haka ya samu ba, domin be samu Emily na jiransa a office ba, har tambaya yayi ko akwai wanda ta zo nemansa aka ce aa. Ya wuni a office da damuwa kamar wanda shi ne yayi silar shigarta a wani hali, nishadin aikin ma ya nemeshi ya rasa, bayan ko wace awa sai ya gwada kiran number ta sai ta ji a kashe. Be tashi aikin da wuri ba sai 4pm duk kuwa da kasancewar da wuri ya shigo office saboda son sanin halin da Emily take ciki. Daga Office dinsa kai tsaye ya wuce gidan Tasmia ya dade yana knocking sannan ta bude, be shiga ba ya tsaya daga bakin kofar ba tare da ya kalleta ba ya ce "Ko kin ji daga gurin Emily?" "Aa" "Kin gwada kiranta?" Ta kalleshi tana magana a hankali. "Eh amman ban same ta ba" Ya juya ba tare da yace komai ba, Tasmia ya rufe kofar ta koma ta gurin windows tana lakensa har ya wuce. Haka yayi ta jera mata ranaku kusan kullum idan ya taso daga office sai ya biyo ya tambaya ko ta ji daga gurin Emily, sai ta amsa masa da aa, ko yayi kamar ba zai je ba, sai wata zuciyar ta raya masa wata kila yau ta je ko kuma ita Tasmia ta samu waya da ita. A wani zuwa da yayi neman Emily Tasmia ta bukaci ya bata number shi so that idan ta zo ko ta ji daga gareta sai ta kira shi, be bata ba kawai yayi tafiyarsa. Sai da ya kwana biyu be sake zuwa ba, sai kuma gashi ya dawo neman Emily da har mafarkinta yake saboda ya damu da halin da take ciki, a zuwan da yayi ya tambayi Tasmia ko ta ji wani abu daga gurin Emily ta fada masa har lokacin babu labari, a ranar ya zabi ba zai sake zuwa ba saboda ya hutar da kansa zuwa neman Emily domin ba mutuncinsa bane zuwa gurinta, duk da yake dai be taba tarar da namiji ko wata macen da bata dace ba a gurin, dan haka ya yaba da hankalin Tasmia, domin har zuwa lokacin matarsa bata san wainar da ake toyawa ba. Da Aliyu ya ga an doshi sati na hudu babu Emily babu labarinta sai ya zabi tafiya gidanta kai tsaye, faka motarsa a waje ya bude ya fita ya doshi gate din gidan yana isa ya kwankwasa, mai gadin ya bude yana tambayar abun da yake bukata, sai ya fada masa yana son ganin Emily ne, ya fada mashi bata gidan ya koma ciki ya rufe Aliyu ya busar da iskar bakinsa ya koma motarsa, ya dade a haka kamin ya ja motar ya koma gida. Immediately after gama sallah isha'i ya tuko motarsa ya shiga unguwar Emily ya faka nesa da gidan ta Inda ba za a ganshi ba ya kashe hasken fitilar motarsa yana kallon gate din gidan, so yake ya gane idan da gaske bata gidan ko kuma tana ciki. Be bar gurin ba sai 11pm na dare, ya isa gida tare da yanke shawarar zai dagawa kansa kafa daga neman Emily duk kuwa da ya san zuciyarsa ba zata bar shi ya samu sukuni ba domin be san halin da take ciki. A tunaninsa ya iya abun da zai iya a yanzu, idan ma tana bukatar taimakonsa zata iya nemansa ko mayar masa da amsar sakonnin daya tura mata. Sai da ya fito wanka sannan ya kira Kameela a waya, sun dade suna waya har yake fada mata a satin nan zai shigo domin yayi missing dinta kuma ta yi arba ta kusa dawowa. Suna yin sallama sai ga kiran Ummi ya shigo wayarsa ya amsa yana murmushi. "Hajiyata barka da dare baku kwanta ba" "Yanzu dai nake ta shirye shiryen kwantawar, mahaifinka kuma be ma shigo ba, yana can falonsa da baki" "Oh Ummi siyasa sai ku, karfe kusan sha biyu dare zan tsaya da baki? Kai ni bana iya wannan" "Bata kama ka ba ne kawai malam idan ta kama ai dole ayi" "Haka ne kuma, amman dai Allah ya bar ni a haka bana iya wannan" "Ameen idan shi ne alheri, ya matarka kasan ta gama wanka ko? Ta yi arba'in fa ko da yake ka ma fini sani ai" Yayi murmushi mai sauti. "Eh ba mu dade da gama waya da ita ba, kika kira ina tunanin weekend din nan zan shiga In Shaa Allahu" "Toh Allah ya taimaka, zamu aika ayi bikonta" "Idan mace zata dawo har bikonta ake?" "Eh amana" "lallai mata yan gata, okay zan fada mata" "Aa ba kai zaka fada mata ba, kai dai na fada maka ne saboda na baka naka hakki wannan aikin nawa ne ka bar ni na yi" "Na bari Ummi, akwai abun da ake bukata" "Eh kamar dala dari biyar haka" Ya kyalyale da dariya har yana shafa kansa. "Ummi kun shiga cikin kasar nan har da ni za a daki hancina?" Ta yi murmushi mai sauti. "idan ba iskaci ba duk abun da ake akwai wanda ka taba bada sisinka? Zaka ce akwai abun da ake bukata ko kudin ne suke maka kaikayi?" "Allah ya huci zuciyarki matar dan majalisa ni dai yanzu sai yadda aka yi da ni" Ta girgiza kai tana hamma. Haka suke wani lokacin ita da shi kamar yaya da kanenta ba uwa da ɗa ba. "Mu kwana lafiya ranka ya dade dan masu govnati" "Good Night Ummi Allah ya kara miki lafiya" "Ameen Ya Rabbi" Ya aje wayar yana murmushi. Satin da Emily ta cika sati biyar be ji daga gareta ba ya shirya ya tafi Kaduna gurin masoyiyarta sai dai ko a ranar kamin ya wuce sai da tafi gidan Emily ya tambayi mai gadinta ko tana nan yace masa a a. Shi dai kawai ya damu ya san halin da take ciki ne, wata kila zai iya taimaka mata ko cetota daga wani abun. Ya san ba lafiya ba domin har yanzu bata kira shi ba bata mayar masa da amsar sakon da daya tura mata ba, kuma bata zo ko ta aiko an dauki motarta dake gurin aikinsu ba. EMILY POV. 5 Weeks Later.... Hannayensa ya saka ya rufe windows din da iska ki shigowa da karfi ya ja curtains din, sai ta juyo ta kalleshi. "Kin ci abincin dare?" Ta daga mishi kai, sai ya riko hannunta ya nufi suka zauna kan kujerar dake dakin. "Emily zamanki a nan takura ne? Kina jin kamar na takura miki ne?" Ta girgiza kai alamar aa. "Tun da kika zo kin kasa sakewa, not even me or my mother" Ta sauke kanta kasa. "Zuciyata ta kasa sakewa, yanzu kuma bayan London wa zan sake rasawa? Fatima? Ko kuma Fatima zata rasa ni ta rayu ita kadai, tunani da hankali ya tattara ya koma a kan gobena" Ya shafa kanta. "Ba zaki sake rasa kowa ba, zamu rayu tare zaki samu soyayya da kulawa zaki samu wani iyalin" Ya kwantar da ita jikinsa. "Bani da wani buri a duniyar sai naki, bana jin akwai wanda ya zame min wajibi na kula da shi sai ke, ina son ki Emily ko a ina nake tunaninki nake, duk wani abu da nake kauna a duniya bayanki yake" Ta lumshe ido tana maida numfashi a hankali. "Baki tunanin lokaci yayi da ya kamata mu bawa junanmu farin ciki? Ya kamata ki bude zuciyarki ki manta da baya da rayuwar baya, a ganina lokaci yayi da ya kamata ace jira ya kare tsakanina da ke" Ta dago daga jikinsa ta kalleshi. "Emily lokaci yayi da ya kamata mu yi aure" Ta ji gabanta ya fadi ba tare da dalili ba. "Kin san ni kin san waye ni, na san ki kuma na so ki, kuma kin san cewa har kasa ta nade wani be isa ya so ki ba sai ni, toh bata lokaci na miye? Har zuwa yaushe zan yi ta jiranki?" Ya kama hannunta. "Na lura baki son na taba ki a yanzu, shiyasa nake daga miki kafa, a yadda nake sonki na fi son mu yi komai cikin farin ciki, kuma auren ki kadai ne zai tabbatar da hakan" Ta zare hannunta daga rikon da yayi mata ta mike tsaya ba tare da ta ce komai ba. "Kina jiran mutanen da suka wulakantaki ne su dawo miki? Ko kuma wani kike dako a gaba? Mutanen da suka rasa ki sun rasa ki kenan har abada, wanda kuma yake zuwa nemanki idan wani abu ne a zuciyar sa toh yana wahalar da kansa ne kawai domin ke mallakina ce kamar dai haka" Ya cire zobe hannunsa ya nuna mata sannan ya maida zoben a dan yatsansa. Ya mike tsaye ya fice daga dakin ya barta tsaya tana mamaki da tambayar kanta wa ke zuwa nemanta? Wata kila Tasmia ce, amman namiji yace, bayan Aliyu bata san wani namiji da zai zo nemanta ba, ko kuma Turhan ne? Ta tambayi kanta, for the first time bayan dawowarta gidan ta ji tana bukatar wayarta, wayar da tun a ranar da London ya mutu bata sake bi ta kan wayar ba, a zamanta nan kuma tunaninta ya tafi a gurin danta da ta rasa bata damu ta nemi wayar ba. Tun da ya dawo da ita gidansa bata fita ko'ina daga cikin gidan sai harabar gida, ya dauko Chidimma da Fatima ya dawo da su gidan a tare da ita ga kuma mahaifiyarsa. Sai dai ko kadan Fatima bata son zaman gidan saboda mahaifiyar Vito da take ganin ta takura mata, kuma ga shi bata so bata masa biyayya Vito. Emily ta nufi kofar dakin ta fito ta sauko hawa na biyu a zatonta Vito yana gurin domin ya fi yawan zaman a falon dake hawa na biyu, a gurin ta zauna tana tunanin ko dai Aliyu ya bawa Turhan addireshinta ne ya zo nemanta? Ko kuma Aliyun ne da kansan yake nemanta.? Kamar an tsikare ta mike tsaye ta sauka falon na farko bata karasa sauka ba ta ji muryar Fatima tana ihu da fadin "I hate you... I hate you" Ta sauka da sauri ta nufi gurin da Fatima take tsaye Chidimma na gefenta tana rike da cups din da aka fasa, Vito na zaune kan kujera ya dora kafa daya kan daya yana kallon Fatima fuska babu annuri. "Me ya faru?" "Me yake sabu a ciki? Rashin kunyar da yarki take yi ko kuma fadar bata son Vito a gaban kowa? Gaba daya yarinyarki bata da tarbiya, taya zata kalli idon mutumen da akarkashinsa kuke tana zaginsa?" "Ki yi hakuri Momy ina iyakar kokari gurin ganin na gyara halayyar Fatima na san abun da take ba shi da kyau amman ita yarinya ce" "Ina kokarin da kike yi nuna min na gani. yara nawa ne sa'ainta basa abun da take? Yarinya karama amman ta iya shiga idon manya? Idan ba Vito ba wa zai iya zama dake ko yarki?" Sai a lokacin Vito ya mike tsaye domin ya ji mahaifiyarsa ta fara saka Emily. "Okay that's enough" Yaja Emily ya maida ita bayansa. "Ba laifinta ba ne, wannan yarinyar da kika gani ga dukan alamu bakin halin mahaifinta ta dauko shiyasa bata kama da Emily ko kadan, saboda babu halin ta ko daya a tare da ita" Fatima ta sake kallonsa "I hate you i hatee youuuuuuuuu" Ta kalli mahaifiyarta. "Momi na ce miki bana son nan gida nake son tafiya bana son nan" "Okay zamu je" Emily ta amsa da sauri kana ta kalli Vito. "Ina son zan koma gida" Momin ta Vito ta yi dariya. "Baki da ra'ayin kanki kenan sai na yarki? Karamar yarinya zata juyaki tana fada miki yadda zaki yi? Shiyasa kike kyale ta tana abun da ta ga dama?" Emily ta daka mata tsawa. "Yata ita kadai ta rage min a yanzu ba ni da wata bayan ita, abun da take so shi nake so, ki cire idonki akan yarinyata, tun da muka zo gidan nan kullum sai kin ce ga laifinta" Momynta ta mike tsaye tana kallon Vito. "Kajinta ko?" Vito ya kalli Emily calmly yace "Je ki jirani gurin mota, Chidimma zata hado kayanku yanzu zan kaiki gida" Emily ta kama hannun Fatima suka fice daga falon, Chidimma ta sauke numfashi ta nufi Kitchen ta zuba cups din hannunta a shara sannan ta fito ta haura sama inda dakin Fatima da Emily yake. "Kana ji tana fadar abun da yarta take so shi take so? Daman ina tunanin bata lokacinka kake yi a kan yarinyar nan baka yarda ba" "Bana bukatar Emily ta so ni, tun da ni ina sonta hakan ya wadatar, na sani tuntuni ban gama shiga zuciyarta ba, amman da sannu zata gane kuma zata gode min ta kaunace ni, zuwa lokacin da ta rasa Lisa (Fatima) za ta gane bata da kowa sai ni" "Idan kuma hakan bata faru ba fa?" "Abun da yake nawa nawa ne har abada ke kin sani, dole zan yi ma Emily uzuri saboda ta sha wahalar rayuwa, kuma ta tashi bata da kowa bata yan 'uwan bata san kowa a jininta ba sai yaran da ta haifa, daya ya mutu sauran daya to me zai saka ba zata ki abun da yarta take ki ba?" "Wai miye a wannan yarinyar da lekewa haka ne? Kana da kudi zaka iya samun kowace mace kake so a duniyar nan, idan ma fari ne akwai fararen mata, idan kana ganin kamar ita baturiya ce zaka iya tsallakawa ka auro wanda kake so wanda ta fita kyau da komai, ita wannan fa har ta haihu kana ta wahala da yaran da ba naka ba" Ta nufi windows din falon ya daga curtains din yana kallon Emily dake tsaye jikin motarsa tana cizon hannunta. "Abun ba daga kyau ba ne kawai, wani abu ne ya hada zuciyata da kaunarta ya daure, kamin ita ai na ga mata da yawa ban so kowa ba sai ita, bayan ita ban ga wata wanda zan iya so ba, yarinyar da dukiyata bata dame ta, sanin tana da damar da zata iya sakawa na wulakanta kowa akanta be taba burgeta ba, ita kadai ce macen da ta saka na ji ina sha'awar tara iyali, mutuwar danta nan tana da damar ta tuhume ni saboda ni na barshi na fita alhalin ba a barinsa shi kadai, amman bata tana ce min komai akan haka ba bata taba nuna min bacin ranta ba, a yanzu zuciyarta a bushe take, nakasassun mazan da suka rayu da ita basu gwada mata komai ba sai azaba shiyasa har yanzu bata san yadda zata so kowa ba" Ya juyo ya kalli Mahaifiyarta. "Akwai mata da yawa, amman masu irin halinta kadan ne, a idona kuma ita kadai ce, kuma baki fahimce ta, karki sake fadin wata magana marar dadi akan Emily indai kina so, ki so Emily...!" Yana kawai nan ya nufi kofar falon ya bude ya fita, Emily na hango shi yana saukowa ta nufo shi da sauri tana hawaye. "Vito I'm sorry kasan be kamata na yi magana da mahaifiyarka haka ba, raina ne ya bace kuma..." Be bari ta karasa ba ya rumgume. "Na fahimta" "Zaka iya bata hakuri?" "Eh, shiga mota muje" Ya sake ta sai ta zagaya ta shiga motar Fatima daman ta dade a ciki zaune sai cika take tana batsewa kamar wata babba. Be jira Chidimma ta zo ba yayi ma motar key. "Chidimma bata zo ba" Be ce mata komai ba yaja motar suka fita daga gidan. Har suka isa gidan da ya tanadar ma be ce mata komai ba ita ma bata ce masa ba, amman hannunsa na rike da nata yana tuki da dayan hannun. Be gama farkin ba Fatima ta bude motar ta fita ta bar masa gambun a bude, fita yayi ya zagaya ya rufe motar ya budewa Emily ta fito tana kallonsa, ta kai hannu ta taba fuskarsa sai ya matsa baya ya bata hanya ta ratsa shi ta nufi cikin gidan shi kuma ya koma motar yaja ya fice gidan. Ta samu gidan yayi kura yayi gummm irin na gidan da aka dade ba a shiga ba, guri ta samu kusa da Fatima ta zauna tana jin kewar danta London yana dawo mata. "Kin ce zaki nemi kudi zaki yi gida mu bar

Chapter 20 of 63