Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da shi sai na ji burgeni ba, wata kila saboda kyau ya daina rudata tun daga kan Khaleefa, ba ma akasin kuma ya zama dalili na banbanci al'ada da kalar halshe. Ya shigo da far'asarsa Ammy tana ta guɗa, kowa yana murna da zuwa ni ma sai na yi yake na yi masa sannu da zuwa kamar kowa, sai da ya fara shiga falon sannan kowa ya shiga ya zauna Ammy na watsa masa fulawa tana masa marhabun da zuwa, shi ma dai ba laifi yana da far'a da sakin fuska a farkon ganina da shi, amman yana da jin kai sosai a kallonsa kadai zaka iya fahimtar hakan. Bayan an gama murnar zuwansa na koma dakina shi ma ya shiga dakinsa yayi wanka ya shirya cikin wasu tufafin sannan yayi sallah, sai da kowa ya hallara falon sannan Ammy ta aiko a kira wai na sauko mu ci abinci, daman babu wanda ya ci komai duk shi muke jiran ya iso. Cikin rashin sakewa na sauko na zauna a dinning din na fara zuba nawa abinci ina sauraren yadda yake taba hira da hausarsa mai harshen larabci yana yi yana hadawa da larabci, sai yaba abincin yake. Tun da na zauna be kalli inda nake ba ni ma ban kalleshi ba, haka nan kawai babu dalili nake jin be yi min ba. Sai da yayi rabin plate sannan ya kalleni ya ce. "Ammy ina kuka samo wannan katuwar mace? Mai kama da orange cat" Na ji gabana ya fadi domin ya aybanta hallitatta tun gabanin ya san wacece ni. Ban ce komai ba na cigaba da cin abincina. Sai Ammy tace. "Kasan orange cat fa kyakkyawar mage ce kowa yana sonta, kuma orange cat din ita ta shirya maka komai da yake nan har kake santi, kuma ita ta gyara maka daki ta saka turare" Ya dan tabe baki yayi murmushi. "Yayi kyau" Daga haka be sake cewa komai ba, ni kuma ban sake kallo inda yake ba, ba karya ya fada ba na yi kiba da yawa na wuce kimar shekaruna, domin a lokacin ban kai shekara ashirin ba, amman kumburin da na yi na haihuwar London sai ya shige min a jiki ya zame min kiba, sai dai ban taba jin muzancin kibar ba sai a ranar da Turhan ya kira da big fat, kuma orange cat, a take na ji abincin ya fita raina gudun Ammy ta gane raina ya bace ya saka na yi karya. "Na ji kamar Ibrahim yana kuka bari na duba shi" Ina fadar hakan kan na mike tsaye kan kujera Turhan ya maido da abincin dake bakinsa a plate din dake gabansa. "Haba Ammy kin san tana da yara kika bari ta girka min abinci? Kin san bana son yara kyamarsu nake" Na kalleshi kawai ya dauke kai na nufi hanyar da zata sadani da stairs, kamin na shiga dakin na cika kaina fal da tambayoyi kala kala. Anya abun da Ammy take kokarin aikatawa mai yiyuwa ne kuwa, ni dai tun ganin farko be kwanta min a rana ba, da alama ni ma ban burge shi ba da va zai furta wannan kalamin a yanzu ba, baya ga haka kuma ya fadi cewar baya son yara kazantarsu yake gani, har yana kyamar abincin da na girka masa to ta iya zai iya zama da ni ma? Ko dai minene ni dai na yi alkawarin ba zan taba furtawa Ammy cewar bana son danta ko kuma ba zan amince da kudurinta ba, domin ta yi min hallaci a lokacin kuma idan na ki danta ina zan koma na zauna. Na yi tunanin Ammy zata duba dan abun da ya faru a tsakaninmu gurin cin abincin nan ta tsagaita wasu abubuwa amman babu abun da ta fasa, gaba daya idonta ya rufe saboda tana son danta yayi aure daga bangarenta ya samu nasa iyalin tana son danta ya dawo kusa da ita, bata duba halin da ni zan kasance ba. Tun daga wacan ranar ban sake shiga Kitchen ba ita take girka masa abun da zai ci ko ya sha, sai dai a kullum teburi daya muke zama gaban dayanmu mu ci abinci, na safe ko rana ko dare, idan ya riga ni zama na iso zai daure fuska ya daina dariyar da yake idan na gaishe shi ya amsa min kamar an masa dole. Idan kuma ni na fara zama baya sake fuska yayi hira da Ammy sai idan na bar gurin. Sai da ya kwana bakwai a gidan a gidan sannan ya shigo dakina, bayan Ammy ta shigo ta sanar min zata je dubiya marar lafiya ta dawo. Ina zaune ina yi ma London wasa yana dariya a cikin yanayinsa, kamin ya zabura ya kwalla ihu saboda shigowar da Turhan yayi yanayin bude kofar sai ya firgitashi a take ya saka kwallowa yana wani birkicewa ni kuwa na kama shi na rumgume ina rarrashinsa. "Me ya same shi?" "Shigowarka ce ta firgita shi" "Shigowa ta kuma? Dodo ne ni?" "Aa haka yake idan ya tsoro ta, komai a sannu ake masa saboda autism ne" Ya maida kofar ya rufe. "Kice mahaukaci kika haifa kenan?" Ita ce magana ta biyu da ya furta a gareni mai daci tun bayan zuwansa gidan, abun da ban sani ba ashe shi din gwanin cin fuska da bakar magana ne. "Aa ba mahaukaci ba ne, ba shi da lafiya ne dai" Ya zauna a nesa da ni jikin wata kujera dake kusa da kofar dakin. "Yana daya daga cikin dalilin da ya saka bana son yara, wannan hayaniyar da kazantar ni ba zan iya dauka ba" Yana maganar yana yatsina fuska kamar wanda yayi arba da wani abun kazanta, sai kuma ya bi dakin da kallo. "Ammy ta ba ni labarinki, ta fada min musulunta kika yi ko? Ke tubabbiya ce? Kuma na tausaya miki matuka, amman abun da ban gamsu da shi ba shi ne, miyasa mijinki be tashi wulakantaki ba sai da kika haihu?" "Wata kila ta manta bata fada maka ba, da cikin ya kore ni a hanya na haihu" "Yeah what i mean is, Allah yasa da gaske mijin ne ya koreni ba irin abun nan kika yi ba na yan matan zamani, kin san akwai wadanda kunyar haifar yaron ke saka su barin gari sai su tare a wani gurin su yi karya saboda su samu mafaka" Na yi shiru bance masa komai ba, zuciyata kuma bata fasa sosuwa da kalamansa ba. "Ke ruwa biyu ce? Ko kuma zabaya ce ke? (irin mutanen da ake haihuwa masu fari sosai)" Na fi kyautata zaton ruwa biyu ce ni, domin zabaya ba haka suke ba" "Eh na ga kuna da dan banbanci, maganar gaskiya ba wai na zo ne saboda na muzantaki ba, duk wani abu da zan fada miki gaskiya nake fada miki zahirinta, ban sani ba ko Ammy ta yi miki maganata?" Nan ma ban ce masa uffan ba. "Ke ba wata macen arziki ba sai shegen jinka, baki san waye ni ba? Ko kuma saboda Ammy ta kawo ki a nan gidan kika jin wata ce ke? Har ina tambayarki ki yi min shiru? Kina fama da jiki kamar uwar mata" "Wa can lokacin bana iya maida magana dan haka na danne zuciyata ina jin yana aybanta ni amman bana iya ce masa komai" "Ammy ta so ma yi min maganarki, duk da yake bata fito min a fili ba, amman na san karshen zagayen zai dawo akan ki ne" Ya ciro wayarsa yana tabawa. "Kamin ke Ammy ta hada ni da mata da yawa na fada mata ba su min ba, amman ke na ga alamar da gaske take, dan haka ina son idan ta tunkare ki da maganar ki fada mata na fi karfinki kina tsoron aurena, domin na fi karfinki din ina sa matata kyakkyawa marar jiki, ke kuma kin zama wata uwar mata mace mai kiba bata burge ni, kuma ni sarauta ne idan Ammy bata duba wannan ba ke ya kamata ki duba, kaskanci ne a gurina na auri wacce ba yar sarauta ba balle kuma tubabbiya macen da musulunta ta yi ba wai ta tashi a cikin addinin ba ne, and you're not my type, kuma ga ki da yaron da da Allah kadai ya san gaskiyarsa, and Aisha baki da dangi ba ki da kowa, ni kuma dan dangi ne jinin sarauta mai asali kuma musulmi gaba da baya, irinku sai dai kawai su zo mana a matsayin masu aiki ko kuma bayi, amman ba saɗaka ko matar aure ba, mahaifina ma ba zai aminta ba, ba zan iya tunkararsa da magana irin wannan ba, Ammy ma dai ta kasa ganewa ne shiyasa har take kokarin hada kifi da kaska" Na daga kai na kalleshi. "Dan haka ina son idan ta miki magana karki amince mata, kuma karki ce mata baki so na domin ta san karya ne wata mace ta kalleni tace bata so na, kawai dai ki fada mata na fi karfinki ba zaki iya cusa kanki a rigima ba, kuma kina da ɗa ke kin san ko haihuwa na yi da ke Allah ya kiyayye ba zan taba son abun da na haifa da ke ba balle kuma dan da kika zo da shi, na zo garin nan da niyar na yi wata biyu ko uku gurin Ammy amman saboda ke next week zan koma, i hate your face, idan aka cire Ammy ni bana ganin kimar ko wace mace bakar fata, iyakarmu da su su mana bauta mu ba su kudi" Yana kaiwa nan ya mike tsaye ya fice daga dakin kofar dakin ma a bude ya bar min ita. Aiko a take hawaye suka ce min Emily yau ma dai zamu ziyarce ki, suka fara sauko min wasu na bin wasu babu tsayawa. Wai fa Turhan yana min haka ne saboda ina zaune a karkashin mahaifiyarsa, kowa yana juya ni ne saboda ina karkashinsa, da ace ina da gurin dazan raba Turhan ko dan Sarkin aljannu ne be isa ya fada min abun da ya fada min a yau ba. A ranar na daukarwa kaina alkawarin ba zan taba yafe musu abun da suka min na wufintar da ni, kuma na dauki alkawarin kasancewa da nawa Yaya a kowane irin hali. Daga ranar sai ya saka min tsoron sa bana ko son fitowa falon saboda kar na ganshi, domin gabana faduwa yake da zarar na ji kamshin turarensa balle kuma ace na yi arba da shi. Da aka kwana biyu Ammy ta ga haka daga gareni sai ta shigo dakina ta same ni tana lallabani wai kar na lalata mata shiri gashi ta fada masa abun da take buri kuma amince sai kuma ni na kirkiro wannan halin a yanzu. "Aisha ko dai baki son shi?" "Sai na kasa amsawa, amsawa bana son sa yana nufin fasa auren da take nufin hadawa amsawar bana son shi yana nufin butulcewa hallacin da ta yi min na tsawon shekaru biyu, yana nufin rusa burinta na son samun danta a kusa da ita, taya ya zan iya mata haka? Wannan dalilin ya saka na boye nawa kunci na so farincikinta fiye da nawa, abun da ban sani ba ashe ina dabawa kaina wuka ne a kahon zuciyata da kaina" "Ki kwantar da hankali, kar wani abu yasa ki fara tunanin Turhan zai zo miki kamar Khaleepa sam ba haka ba ne, yanzu haka na yi magana da shi ya nuna min tausayinki sosai kuma amince zai aureki, kuma zai rike ki amana, amman ya ce na fara tambayarki idan kin amince saboda kar ya zama an cilasta miki, na fada masa tun kamin ya dawo na yi magana da ke amman zan sake samunki da maganar" "Allah ya ba mu zaman lafiya" Shi ne kawai abun da na fada ta amsa da amin ta rumgume tana farinciki da jindadi. "Ya fada min wata biyu yake son yi, amman mahaifinsa ya kira shi akwai wani buki da suke a can duk shekara zai tafi a satin nan albashi idan sun gama sai ya dawo, dan haka nake son a daura aurenku a satin nan, sai ku tafi tare, abar min Ibrahim har sai kun dawo tukuna" "Tohm Ammy" "Allah ya miki albarka" Jindadin da na gani a fuskarta yasa ni jindadi duk da ina fargabar abun da zan tarar. Turhan ya so gyara kansa a gurin mahaifiyarsa ne ta hanyar nuna masa ya amince da kudurinta ni kuma ya buga da kasa ta hanyar amfani da ni na fadawa Ammy ba zan aure shi ba, daga nan zata fahimci na mata butulci wata kila ma ta kore ni ko kuma ya karyata labarina. Washe garin ranar da aka yi haka Ammy ta bukaci dole sai na fito na yi karin kummalo a falon wai saboda ni da Turhan mu kara fahimtar juna. A dole na fito na karya a gurin muna cikin karyawar ne take mana addu'a da fatan alheri tare da nuna jindadinta na yadda muka bata hadin kai. "Allah ya hada kanku ya ba ku zaman lafiya, sa na yi nufin a hade aurenku da na kanwarka (yarinyar da Ammy take riko) amman saboda uzurin da ya same ka yanzu zan tafi family house a yau na yi magana da su na abun da ya kamata, sai a daura auren albashi a bar bikin sai idan kun dawo sai ayi komai cikin natsuwa da kwanciyar hankali" "Eh haka yayi Ammy" Ya amsa mata yana murmushin dole. "Bari na barku ku ci abincinku, zan tafi na shirya na tafi gurinsu Hajiya" Ta mike tsaye ta fice daga dinning din, fitarta ke da wuya Turhan ya kalleni ya ce. "Ba dai kin amince da wannan auren ba? Sai kin ci ubanki" Ya wurgar da spoon dinsa ya fice a fusace, ban san lokacin da na fashe da kuka ba, domin na shiga tsaka mai wuya idan na fasa auren nan Ammy zata ga laifina, idan kuma na amince ba dadinsa zan ji ba. Ta bangaren iyayen Ammy ma murna suka yi suna nuna farincikinsu, ba a fara shirye shiryen komai ba sai da Turhan ya bukaci ayi min gwaji, aka gwada jinina da na shi dukanmu bama dauke da kowace kalar cuta da zata dakatar da aurenmu. Haka bi dare ina raya shi da kuka da tunani kala kala har zuwa ranar da Ammy ta shigo min da kaya masu dubin yawa akwaiti goma sha biyu a matsayin lefe na, lefen da aka hada gurin Khadeeja Candy Store, sannan ta danka min dubu dari biyar a matsayin sadakina, ko bata fada min ba na san ita ta biya sadakin ko wani nata, domin bani da kima da martabar da Turhan zai siye da ni da sadaki mai tsada haka, a dan kankanen lokacin Ammy ta saka aka fara min gyaran jiki. Ranar Jumma’ah aka daura mana aure bayan saukowa daga Sallah Jumma’ar mai raka'a biyu, ina zaune garden din gidan tare da mai kunshin da Ammy ta kira ta bukaci ta yi min lalle mai kyau. Mai aikin Ammy ta shigo tana rangwada guda da murna ta sanar min an daura aurena da Turhan, a take na ji gabana ya fadi wani abu mai kauri da zugi ya tunkari zuciyata ya tsaya, tun daga wannan ranar har yau wannan abun be sauka ba. Kusan zan iya cewa auren dole Ammy ta yi min da Turhan domin bana son shi tsarin rayuwarsa gaba daya be yi min ba. _______________________ Sannu ‘yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe ɗinki da kaya masu kyau, masu ƙima daga Khadeeja Candy Store Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sauƙin sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing. Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taɓawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet ɗinmu sun dace da ke Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sauƙi ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko’ina! Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame. Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ƙayatarwa duk a farashi mai sauƙi. Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu! Baki da lokaci? Muna da sauƙin oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina! To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haɗuwa. [6/25, 9:02 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ FOLLOW ME ON 👇🏻 FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914 TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Page 4️⃣0️⃣ Aliyu ya dago yana sauke numfashi ya kalli Fatima dake rike dayar wayarsa tana kallo, ita yake kallo ammam Emily yake tunani wahalar data sha a gidan Khaleefa be gamsar da alkalamin kaddararta ba har sai da ta sake zana mata wani shafin mai daci a tsakaninta da abokinsa. A yanzu ya fahimci duk abun da Ammy ta yi ma Turhan na juya masa baya ta yi daidai, ga kuma rashin samun haihuwa da be yi ba a yanzu sai kuma Allah ya jarrabe shi da son yaran ashe shi ya fara butulcewa tun farko. Ya kai hannunsa ya shafa Fatima sai ta kalleshi ta yi murmushi, shi ma yayi mata murmushi sannan ya maida hankali gurin wayar ya kunna dayan voice note din ya cigaba da saurare. ***. ***. *** A ranar da aka daura mana auren, Turhan be dawo gidan ba sai dare, ina dakina a lokacin da ya shigo tare da Ammy tana ta murmushi sai addu'a take zuba mana, shi ma yana murmushi kamar gaske, ni kuma na kasa ko daya kallonsu ko yin murmushi, London yana hannuna Ammy ta karbe shi ta fice aka bar mana dakin daga ni sai shi, kaina a kasa shi kuma ya nemi guri ya zauna ya dora kafa daya kan daya, sai a lokacin na iya dagowa na kalleshi farar shadda ce a jikinsa sai kamshi yake kamar angon kirki. Mun dauki minti talatin a haka babu wanda yace da wani uffan, sannan ya taso ya karaso kusani da ni. "Wani mummunan abu be taba faruwa da ni ba kamar aurenki" Furucinsa ya tsari kaina, na dago na kalleshi sai ya tofa min yawu da karfi a fuska ya daki kafata dake da lalle da karfi sannan ya sa kai ya fice. A daren ban yi bachi ba, kuma ban yi kuka ba tunani ma na rasa wane zan yi, ina ta sake sake idan na kulla wannan na kulla wacan ta ko'ina zaren warware min yake na rasa gane inda zan raba na fake. A daren Ammy ta kawo min international passport din da ta saka aka yi min saboda barin kasar zamu yi. Washe gari Assabar Ammy ta fara shirya min kayan da zan tafi da su, ita ta hada min komai nawa ido ne kawai sai kuma ɗana sa nake ta rumguma ina jin kewar rabuwa da shi, a daren Ammy ta yi min nasiha sosai kuma ta kara tabbatar min ɗanta ba zai taba cin amanata ba, kana ta yi min godiya na yadda na amince da kudurinta har aka kulla auren, ta ce na toshe kunnuwana daga kananan maganganu ko kuma abun da zan gani da be kai ya dawo ba, na kwantarwa da mijina hankali, ba can zamu zauna ba zamu je ne kawai mu dawo. Ranar Lahadi da safe aka fito mana da akwatinanmu ni ma na fito cikin shirina ina rumgume da ɗana, Turhan ma ya fito cikin nasa shirin yana ta far'a kamar gaske, Ammy ta so ta rakamu Airport amman ya hana wai idan ta bimu har can zan fi kowa kewarta. Kuka be zo min ba sai da Ammy ta kai hannu ta karbi London dake hannuna sai ya fashe da kuka ni ma na fashe da kuka na karbe shi na rumgume, abun mamaki sai ga Turhan ya zo ya karbi yaron ya dankashi hannun Ammy ni kuma ya ciro handkerchief ya share min hawayena. "Ki kwantar da hankalinki mana, ba wani dadewa zamu yi ba, muna gamawa zan dawo tare da ke, kuma a can zamu zauna ba anan kusa da Ammy" Ya kama hannuna ya saka ni mota da kansa Ammy na ta saka masa albarka har sau uku sannan ta yi mana addu'ar Allah ya tsare. Direba ya ja mota muka kama hanya, ba mu zame ko'ina ba sai Airport aka yi mana duk wani check in da ya kamata har muka kai gurin jirgin, sai da muka shiga na gane ba guri daya za mu zauna ba, shi yana Business class ni kuma a economy, na zauna shiru ga damuwa na barin ɗana, ga fargabar abun da zan je na tarar ga kuma tsoron jirgin domin shi ne karona na farko da na hau jirgi. A Lagos muka fara sauka da na fito sai na tsaya sai da ya fito sannan muka kama hanyar Hotel a taxi, a hotel din ma babban daki ya kama ni kuma ya fada min zan zauna a karamin daki daidai ne, haka na karasa dan wunin daya rage na kwana babu wanda ya kwankwaso min yace ga abinci, tun bayan dan abun da na ci a jirgi da be rike cikina ba. Sai 11am ya buga mun dakin hotel din na bude yace na fito zamu kama hanya, na fito da akwatina muka sake shiga taxi ta kai mu air airport aka yi mana screening aka auna kayanmu da duk wani abun da ya kamata sannan muka hau jirgin da zai dauke mu zuwa Sudan, a nan ma business class ya shiga ya bar ni a Economy, dan abun mutsa baki da aka kawo min a jirgin da shi na samu na karya bayan tafiya ta yi nisa suka kawo mana shinkafa na cinye tas da ruwan shayin kai tsabar yunwa ko ruwan sha ban raga ba komai sai da na cinye har ina bukatar kari. Na yi bachi ban farka ba sai da muka jirgin ya fara jijjigar sauka. Yanayin kasar da garin, mutanen da yarensu dabam ne da na kasar mu, tun a Airport din na kara tabbatar dan sarauta ne, saboda motoci da suka zo daukarsa da kuma yanayin mutanen da suke tuka motar. Mota daya muka shiga da shi a motar yayi min gargadin da ban zan taba mantawa ba. "Karki sake ki yi magana, kin ga hausar mutanen nan da na can ba iri daya ba, kuma za ki je ne a matsayin baiwa, zan sanar da kowa cewar ke baiwa da mahaifin Ammy ya bani, kuma zan sanar musu ke kurma ce, dan haka duk tsanani kar ki kuskura ki yi magana, kuma bayan nan karki nuna kin san ni" Bance komai ba, a lokacin ma kuka baya zuwa min wata kila saboda damuwar ta yi min yawa ne ko kuma dai kukan ya gaji da zirarta idanuwana ne. Masarauta ce babba ko da yake ban san komai akan sarauta da fada ba, amman tabbas mahaifin Turhan babban Sarki ne a garin, ayi masa tarba ta girma, ni kuma aka kaini wani daki na daban aka sauya min tufafi zuwa aka ba ni na wasu masu kamar lafaya, wadanda ma'aikatan gidan suka sakawa. Masarauta ce mai matukar fadi da girma, ba Turhan ne kadai dan da Sarkin ya haifa ba amman kowa da bangarensa da kuma nasa bayin. Nidai tun daga ranar ban sake saka Turhan a ido ba sai da na yi sati biyu, a kullum zuciyata tana gurin ɗana, aiki kam babu hutu musamman da ya kasance ni a karkashin matarsa aka barni, domin bangaren mahaifinsa dabam tun da naje ban taba ganin Sarkin ba,

Chapter 32 of 63