zan iya kallonta ta shiga wani hali ba ba zura ido"
Cikin natsuwa Aliyu ya kalli Hajiya Asma'u.
"Hajiya maganganun da kike min kamar kina nufin by fire by force ban isa na yi ma Kameela kishiya ba?"
"Ba zan ba ka isa ka yi mata kishiya ba, ko kuma na hana abun da ka yi nufi ko aka saka ka abun da ka yi niya ba, Ummi take da wannan ikon ba ni ba, amman dai ni a matsayina na mahaifiyar Kameela ina mai tabbatar maka Kameela ba zata zauna da kishiya ba, a yanayin zuciyar Kameela ba zan bari a kashe min ya ba"
Aliyu yayi murmushi a bayaninta na yanzu ya fahimci har yanzu bata dauke shi a matsayin danta ba, if not ba zata fada masa magana haka ba, calmly ya fara magana.
"Na gode da wannan bayanin da kika min a yanzu Hajiya, kuma na gode da kika fahimci Ummi ce kadai ta isa ta saka ni abun da ban yi niya ba, ko kuma ta hana ni abun da na yi kuduri, wannan sharadin kuma tun farko ya kamata a fada min kamin na auri Kameela ba yanzu ba, amman duk da haka na gode zan kiyaye a huta lafiya"
Ya mike tsaye ya ciro 500k aljihunsa ya dora akan center table din dake falon.
"Anty Shafa a siyawa yaran wani abu"
Daga Hajiya har Anty Shafa babu wanda ya sake cewa wani abu binsa suka yi da kallo har ya fice. Yana sauka entrance din Hajiya Asma'u ya nufi bangaren Mama Barakat sai da yayi knocking sannan ya tura ya shiga, ta amsa masa da far'a tana masa maraba har da dauko masa ruwa.
"Mama Kameela tana nan ko?"
"Eh tana dakina na ce ta shiga ta kwanta na ganta sai a hankali, Allah yasa dai lafiya"
"Lafiya kalau Mama"
"Maa Shaa Allah haka muke son ji, Dan Allah Aliyu ayi hakuri, shi zaman aure dole sai da hakuri, ba zaman aure kadai ba gaba daya rayuwar duniyar ma sai anyi hakuri, kuma kowa da inda Allah yake masa jarrabawa wani ta bangaren aure, wani ta iyaye, wani ta yaya, wani ta abokiyar zama, wani ta surukai, dan'adam baya taba zama hakan nan dole sai da jarrabawa, kaf duniya babu wanda zai zauna 💯 percent babu damuwa, dan haka ka yi hakuri kuma ka danne zuciya"
"In Shaa Allahu, Mama na gode sosai"
"Ba komai, kai ai ko da yaushe ɗana a gurinmu, dole idan muka ga za'a kuskure sai mu lurar, tun da ku yara ne mu kuma manya, bari na kira maka ita"
Ta mike tsaye ta nufi staircase, shi kuma ya sauke kansa kasa, be dago ba sai da Kameela ta sauko, sannan ya kalleta fuska a hade.
"Zauna"
"Ba zan zauna ba"
Ta daka masa tsawa tana hararasa idonta har sun kumbura tsabar fitinar kuka.
"Ba ni mamaki Aliyu ashe jira kawai kake na daga ka fara soyayya da wata, har kana tambayar lafiya, ita kuma ta samu Audacity kiran ka kai tsaye"
"Ban taba sanin baki da hankali sai yau, ban san rashin tunaninki ya kai haka ba sai yau"
Ta nuna kanta.
"Ni kake kira mahaukaciya?"
"Idan ba rashin tunani ba yaushe wannan maganar ta kai ki kaita a gaban iyayenki? Idan ba hauka ba yaushe zaki kira matar da baki san me take Going through ba ki zageta ki kirata da karuwa?"
Ya mike tsaye rai a bace.
"Miye a cikin kanki Kameela? Wannan ba kishi ba ne hauka ne, matar da kika zaga bata miki komai ba, baki san komai akanta ba, matar dake kokarin picking kanta Piece by piece, abun da kika yi kin nuna baki ma yarda da ni ba kenan, idan wani ya zo ya fada miki wata magana akaina zaki yarda. Ba tsoron ki nake ba duk abun da nake miki ina biyewa miki ina daga miki kafa ina yi ne saboda mu zamu zaman lafiya, na miki alkawarin ba zan kara aure ba saboda ba ni da ra'ayin auren mace fiye da daya, kuma saboda hankalinki ya kwanta, not because of kin fi karfina ko ina tsoronki, ke kin san waye ni kamin ki aure ni bana daukar rainin wayo bana daukar wulakanci, saka miki idon da na yi yana kokarin saka ki raina ni? Idan ba raini ba yaushe zaki zafi matar da ni na fara neman number ta kamin ta nemi number ba, kin yi min magana be isa ba? Duk wata number mace dake cikin wayata ta yan'uwan da kika san akwai aure tsakaninmu ko abokan aiki kin bi kin goge kin yi blocking, kullum cikin bincike wayata kike, mazinaci ne ni? Ni ya kamata na bincike numberki saboda ni ne mijinki, a cikin cousins dina baki shiri da kowa saboda tunanin wata zata aure. Abun da kike kina nuna ban isa da gidana ba kenan ko kuma kin fi karfi. Toh wannan ya zama na farko kuma ya zama na karshe idan Emily tace kin sake kiranta kin ci mutuncin kin kaɗe....!"
Tun da ya fara fadan bata komai sai kuka, Mama Barakat data sauko tana kallonsu saboda daga muryar da Aliyu yake ta matsa ta rike Kameela.
"Lafiya Aliyu?"
"Karamin abu ne da ya faru da be ma kamata ka ji ba, amman yarinyar ta bi ta lalata komai"
"Meyasa ba zaka fada mata saboda wata karuwa kake ci min mutunci ba, wata banza yau kake min abun da baka taba yi ba, saboda kana ganin ita fara ce mai kyau baturiya saboda kana ganin kamar ta fini kyaun? Abun kunya ma matar abokinka, yarinyar da ba a san su waye iyayenta ba, yarinyar da tsintarta akayi a Lagos, yarinyar da ba ma musulma bace, ai ko aure zaka yi ko soyayya zaka yi ka yi da mai ma'ana mana"
Aliyu ya dube ya sake dubanta ya kuma ya dubeta sannan ya dauke kai ya fice daga falon. Da wani irin kufura da fushi ya isa motarsa, da ace halinsa ne saki ko dukan mata a yau ba zai ragawa Kameela da ko daya ba, domin kalamanta na yanzu sun fi abun da ta aikata zafi, yana barin gidan ya daga waya ya kira Umminsa tana dagawa be tsaya gaisuwa ba ya ce.
"Ummi karki aika bikon Kameela a yanzu"
"Me ya faru?"
"Yar hatsaniya muka samu, kuma na san Hajiya Asma'u zata iya yin wani abun da zai bata miki rai ko ni, ni kuwa a yadda nake jin kaina a yanzu idan ta kuskura ta furta wata kalma marar dadi a gareki ko Daddy, na rantse da Allah sai na nuna mata ta fi kowa rashin sa'ar suruki a duk fadin garin Kaduna...!"
"Toh Allah ya kyauta, shiyasa ake son idan mutum zai yi aure ya auro yar gidan mutumci, ba tarbiyar yarinyar kadai ba ta iyayenta ma ya kamata a duba, Hajiya Asma'u fa hankalinta ba zai kwanta ba sai taga Kameela bata gidanka, saboda ta dauke mu makiyansu. Ko da yake ma komai ya faru ai kai ka janyo, babu yadda ba mu yi ba ka nace sai ita, abun da duk iyaye suka ce a bari barin shi yafi alheri ko da babu dadi, idan riba ce yanzu ai ka fara ci"
Tana fadar hakan ta kashe wayar. Aliyu ya cigaba da tukin motar sai huci yake har ya isa gidansa.
_______________________
Sannu ‘yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe ɗinki da kaya masu kyau, masu ƙima daga Khadeeja Candy Store
Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sauƙin sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing.
Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taɓawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet ɗinmu sun dace da ke
Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sauƙi ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko’ina!
Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1
da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0
Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame.
Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ƙayatarwa duk a farashi mai sauƙi.
Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu!
Baki da lokaci? Muna da sauƙin oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina!
To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08
Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store.
Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haɗuwa.
[5/20, 10:17 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
FOLLOW ME ON 👇🏻
FACEBOOK
https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914
TIKTOK
https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1
INSTAGRAM
https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0
CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01
KHADEEJA CANDY STORE
https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08
Page 2️⃣7️⃣
The following day ya shirya ya wuce Abuja gurin mahaifiyarsa daman zuwansa kaduna saboda Kameela ne, ya fara sauka a nan idan ya ganta suka gaisa aka masa binkonta zuwa gidansu dake Kaduna sai ya dauke ta su tafi Abuja gurin Ummi su mata kwana biyu sannan su sannu dawo garin da yake aiki a yanzu wato Part hartcour, sai dai a yanzu ta yi nasarar ɓata masa rai yayi tafiyar da be shirya ba.
Ya sauka Abuja around 12pm Ummi ta aiko sabon direbansu ya dauki Aliyu daga Airport zuwa gidansu dake Wuse II, kamin su karasa gidan Kiran Kameela ya shigo wayarsa a karo na 32 bayan sako goma sha daya da ta aiko masa, be amsa kiranta ko daya ba haka kuma be mayar mata da amsar sakonta na Sms ko WhatsApp ba, har Instagram dinsa sai da ta bishi tana masa be amsa ba, domin a duka sakwaninta babu wanda ya nuna ta yi nadamar abun da ta yi sai dai ta bashi hakurin bata masa rai da tayi wani gurin kuma tace wai yanzu saboda wata banza yake mata wulakanci, wani sakon kuma tace ya bata mamaki, a na karshen kuma nanatawa take wai zai jawa Emily bala'i idan be rabu da ita ba.
A katafaren gidan Direban ya faka ya fito ya budewa Aliyu mota, Aliyu ya fito yana kallon yadda aka kara gidan na mahaifinsa kamar ba za a mutu ba. Sannan ya wuce ciki, falo biyu ya wuce sannan ya isa wani madaidacin falo wanda be kai na farkon sa na biyun girma ba, kanwarshi ta zo da gudu ta tarbe shi ita da wata cousin dinsa, Aqeel kuma ya mika masa hannu suka yi chop knuckle, Ummi ta dan tabe baki kadan tana kallonsa.
"Yaushe rabonka da gidan nan?"
Ya nufeta ta zauna kusa da ita yana dariya.
"Irin Welcome din nan ma na uwa da ɗa ba zan samu ba? Ina shigowa sai a fara min da tambayoyi"
Ummi ta yi murmushi kadan, tayi ma direban da ya shigo da akwatin Aliyu sannu.
"Hajiya ga wannan ina za a aje?"
"Bar shi a nan Khaleepa Ladi zata shigar masa da shi ciki"
"Toh Hajiya"
Ya amsa sannan ya juya ya fice.
"Ummi haka aka kara gyara gidan nan, wato ku babu ruwanku duniya ta muku dadi ko?"
Ummi ta watsa masa wani kallo har tana karkatawa dan ta samu ganinsa da kyau.
"Ahhh Toh so kake ta yi mana zafi? Ɗan hamayya! Ko ka bi jam'iyar matarka? Kasan fa kai yanzu ruwa biyu ne, kana nan kana can ba gane kanka ake ba, karka mana zagon kasa"
Duk suka fashe da dariya har Aliyun, daman haka yake da mahaifiyarsa idan suka hadu ita da shi kamar abokan wasa ko yaya da kanenta, sam ba zaka ce ɗa da uwa ba ne. Sai da suka gama wasa da dariya da Ummi sannan ya shiga ciki yayi wanka ya fito ya dawo dakin Ummi, already ya samu Ramla ya kawo masa abinci a dakin Ummi, abu ne da suka sani idan zai ci abinci duk inda Ummi take zaune a nan yake ci, a daki ne ko falo ko bangaren mahaifinsa, shi dai burinsa ya ci abinci kusa da mahaifiyarsa yana ci yana hira da ita.
"Sai yaushe Daddy zai dawo?"
Ya tambaya bayan ya kai spoon biyu bakinsa.
"Daddynka yanzu ganinsa sai da ticket, ko ya shigo ba samun ganinsa zaka yi ba"
Yayi murmushi
"Ummi wai ni korata kika yi a gidan nan ko sadakata aka ba da, na ga tun da na so kike min wulakanci"
"Daman kai dan gidan nan ne? Ai mun yafe ka tun da muka aurawa Kameela, yaushe rabonka da gidan nan, babu ruwanka da labarin mu komai ake kai baka ma sani ba, yanzu ma ba dan ka samu matsala da Kameela ba ba zaka zo ba"
"Yanayin aikin ne ai Ummi kin san ba mu da hutu kullum, kuma daman na yi nufin daga Kd na dauko Kameela mu zo nan mu kwana biyu wannan mu koma, sai gashi notin kanta daya ya cire"
Ummi ta tabe baki.
"Allah dai ya kyauta, dazun ma ta kira ni tana fadin wai ka mata fada kamar zaka daketa, saboda wata matar abokinka Turhan kuma matar ma kafira ce miye miye... Ni ban ma gane kan zancen ba, wai yanzu kuma fushi kake da ita"
"Shareta kawai Ummi ba zaki ganin kan zancen ba"
"Kishin yarinyar nan yayi yawa, kuma ba komai ya sa yayi yawa ba sai damar da ka bata, akwai abubuwan da ake takawa mace burki a kansu, amman kai komai ta yi sai ka biye mata saboda kana sonta, wannan ba so ba ne, abun da kake mata yanzu tana wuce gona da iri shi iyayenta suke mata da sunan so alhalin ba soyayya bace lalata mata tarbiya ne suke yi"
"Ummi da kin tashi magana sai ki ce Kameela bata da tarbiya, Kameela tana da tarbiya kawai dai zafin kishi ne yake damunta"
"Na ji tana da tarbiya, iyayenta fa? Ai komai kyaun farin tuwo a ɓakar tukunya ya fito, kuma kamar kumbo ne kamar korensa duk yadda za'ayi dole Kameela sai ta samu matsala domin barewa bata gudu danta yayi rarrafe, idan bata maka abun haushi ba iyayenta za su maka, kuma duk yadda aka yi sai ta dauki hudubarsu, uwa ba wasa ba ce Aliyu, idan za'ayi aure ba tarbiyar yarinya kawai ake dubawa ba har da iyayenta ana son a duba su waye iyayenta"
Be sake cewa komai ba har ya gama cin abinci, domin abun da be yarda da shi ba shi ne mahaifiyarsa ta zauna tana zagin matarsa, hakan zai dasa kiyayyarta a zuciyar mahaifiyarsa, wanda ba zai so haka ba, even though dai Ummi ba wani yin Kameela take cancan ba, amman ya san bata tsaneta ba, haka kuma ko da wasa ba zai yarda ya budewa matarsa damar maganar mahaifiyarsa ba, kowa matsayinsa dabam. Ya gama cin abinci a daidai lokacin da motar Daddynsa ta faka harabar gidan, sai dai be san shigowarsa ba domin gidan ba irin gidan da ake jin fita ko shigowarsa mota ba ne, musamman dakin Ummi da baka sanin wainar da ake toyawa idan kana ciki sai ka fito.
Aliyu ya aje spoon din da ya gama cin abinci da shi kenan, kiran Daddy ya shigo masa ya sanar masa ya dawo.
"OK Daddy gani nan zuwa"
Ummi ta kalleshi.
"Wato na yan siyasa mahaifinka yayi min ko? Daga ganin sabuwar jam'iya sai ya tsalleke ya koma can ko? Ai tafiya zaka yi a bar ni da shi"
Aliyu ya kai tsaye yana dariya.
"Allah ya bar mana ke Ummi, yanzu miye laifin Daddy dan ya nemi ganin dansa?"
Ummi ta yi murmushi. Aliyu ya fice shi ma yana murmushin. Wani abun da ya kara bata masa rai a game da Kameela shi ne sanar da Daddy da ta yi bayan Ummi, kuma ko kadan hakan be masa dadi ba, domin a ganinsa abun be kai ace iyaye sun ji ba, ta sanar da iyayenta hakan be mata ba sai ta sanar da na shi. Nasiha Daddy yayi masa akan zamankewar aure ya fada masa wai sai yayi hakuri da matarsa kowa hakuri yake. A tare suka yi Sallah Isha'i a harabar katon gidan dake da matsakaicin masallaci a ciki, Aliyu ya jagoranci Sallah daya daga cikin jami'an tsaron da suke gadin gidan yayi masa ladanci, Daddy da sauran ma'aikatan gidan kuma suka shiga sahun mamu, bayan an gama sallah ne Aliyu ya juyo yana gaisawa da kowa yana musu alherin da abun da ke aljihunsa, har ya kai gurin sabon direban da aka dauka domin shi dai be taba ganinsa cikin ma'aikatan gidan ba, ko da yake gidansu kullum cikin canje canjen ma'aikata yake ba shi kadai ya gani bakuwar fuska ba, amman rabin fuskarsa ta fi tsaya masa a rai, domin rabin kawai ake iya gani dayan gefen a kone yake har zuwa hannunsa na hagu, yayi baki sosai ya alamar wuta ko mai ta kone jikinsa domin fatar kafadarsa ra hagu zuwa wuyansa a hade take, jikinsa ya zama two color.
Kwanan Aliyu biyu a gidan kullum suna haduwa gurin sallah gidan, kuma a kullum sai yayi musu alheri, daman duk lokacin da ya zo a gidan ko gidansu na Kd haka yake da kowa har ya koma, a ranar da zai koma Ramla ta fito masa da akwatinsa falonsa dai daga cikin masu aikin gidan ta dauki akwatin ta fitar da shi waje sai direban ya karba ya saka mota. Aliyu na zaune falonsa yana duba agogo hannunsa Ummi ta sauko rike da cup tana sanye da Filafil Swiss Lace dan 530,000 da ta siya gurin Khadeeja Candy. Cup din hannunta ta mika masa ya dago daga kishimgiden da yake ya karbi kofin ya leka ciki sai ya ga ruwa kadan, be tsaya komai ba ya kai kofin baki ya shanye addu'ar dake ciki.
"Ita wannan addu'ar idan an sha ana shafawa ko sha kawai ake? Na shanye duka da"
Ummi ta yi murmushi irin na su na manya hakwaranta biyu na makka na bayyana.
"Baka tsaya ka ji yadda ake shan ba ka shanye"
"Ai na san ba saki ba ni abun da zai cutar da ni ba, kuma kin saba min Ummi tun ina yaro kullum sai kin tofa min addu'a a ruwa kin ba ni, kamar dan siyasa"
"Ba sai dan siyasa yake da makiya ba, wani baka sanin makiyinka sai ranar da girkin yaƙi dadi, wani ma sai an hadu gaban Allah gurin rabawa kowa abun da ya aikata zaka ga wani ashe ya ci da guminka ko ya cutar da kai kai baka ma sani ba, dan haka ka rike addu'a da addu'a zaka fi karfin komai, kullum idan zaka iya kamin ka ci komai ka karanta fatiha da ayatul kursiyu ka tofa a ruwa ka sha, Allah ya tsare min kai ɗana, ko baka siyasa ai kai dan masu siyasa ne"
Ya kwanta jikin mahaifiyarsa yana jin tsananin kaunarta.
"Sai ni Aliyu dan Ummi nan gani nan bari adashe manya"
Ummi ta shafa kansa ta saka masa albarka sannan ta kai masa rankwashi.
"Dan Allah daga min katon banza da kai ka zo ka haye min a jiki"
Ya tashi yana dariya. Ramla tana ta daukarsu hoto har da short video. Aliyu ya fito tare da rankiyar mahaifiyarsa har gurin motar da Direban ya bude masa. Aliyu yana ta kallon direban da biyu domin zuciyarsa na raya masa kamar wani abu kamar ba haka ba.
"Ya sunanka?"
"Khaleepa ranka ya dade"
Ya juyo ya kalli Ummi.
"Kun canja direba ne?"
"aa dayan dai yaje ganin gida, dayan kuma shi yake kai yara Ramla school kasan tsoro ya hana ta iya mota har yanzu, Daddynku yace a karo daya saboda zirga zirga ya zama idan biyun basa nan daya yana nan, shi Daddy kasan ai yana da nasa na musamman ko da wasa baya ara mana shi"
"Okay"
Ya shiga motar suka yi sallama da Ummi Ramla na daga masa hannu da Aziza, sai da suka yi nisa sannan Aliyu ya ce.
"Khaleefa ai ba suna ba ne ko?"
"Eh ranka ya dade sunana na ainihi shi ne Hamza"
Aliyu ya sake dubansa ta madubin motar, har ya bude baki zai sake wata magana sai kuma ya fasa ya sauke numfashi. Da suka isa Airport din direban ya fito da akwatin Aliyu bayan ya bude masa, sai Aliyu ya sake masa duba na tsanaki ya ce.
"Kai dan wane gari ne?"
"Kaduna, ranka ya dade"
Daga haka Aliyu be sake cewa komai ba Direban ya ja masa akwaitin Aliyu yana gaba yana biye.
EMILY POV.
A ranar da Kameela ta kirata ta yi mata cin mutunci ta kira da suna kala kala marasa dadi Emily ta kwana da bakinciki da damuwa. Washe gari da ta tashi sai ta tashi jiki babu kwari mood dinta kuma ya canja domin ta kwana da tunani kalakala a ranta. Ko da ta sauko already Chidimma ta gama shirya komai, Fatima har ta wuce school, Vito kuma yana zaune a dinning din falon tare da Chidimma suna karyawa at the same time the same table. To her it's a new thing domin Vito be taba hada table da wata mace ba a gaban idonta balle har ya ci abinci a tare da ita.
Kallonsa kawai ta yi ta kalli Chidimma ta dauke kai ta nufi kitchen ta shirya nata breakfast din dabam ta dauko ta fito, a lokacin ne Vito ya mike tsaye.
"Good Morning Bae"
Bata amsa ba kuma bata kalleshi ba ta haura sama zuciyarta tana mata babu dadi, domin bata gane ma'anar abun da yayi ba a yanzu. Saboda ta yi fushi ne jiya har ta watsa masa ruwa ta mari Chidimma? Ko kuma saboda bata nuna interest dinta akan aurensa ba ne? Ko kuma dai saboda ta yi fada da mahaifiyarsa ne.? Ba zata ce tana kishin karyarwa da yayi a tare da Chidimma ma, amman aikata hakan kamar ya budewa Chidimma din kofar raina ta ne domin a kasan ta take zaune.
Ta kasa kai komai bakinta ta mike tsaye ta nufi backyard ta tsaya a gurin tana kallon itacen da suke nan, duk wani abu da yake samuwarta ko kuma ya sameta yana faruwa da ita ne saboda bata da ikon kanta kuma bata da gata, da ace kaddararta bata zo a haka ba, wata kila da salon labarinta ba a haka zai kasance ba.
Sai da ta shaki iskar da take jin ta wadatar da ita sannan ta koma ciki ta zauna a one seater ta kai hannunta ta dauki wayarta, sai ta ci karo da sakon Kameela daga wata number dabam ba wacan da ta yi blocking ba saboda yawan sakon da take turo mata da kira. "Idan baki rabu da mijina ba sai na kashe ki, akan mijina bana ji bana gani kuma ban ragawa kowa"
"Uhffff"
Ta busar da iskar bakinta ta daga kanta sama ta sauke ta shafa kanta ta shafa jikinta gaba daya ta rasa me ke mata dadi. Kamar wasa Vito ya fara shareta kuma ya maida rabin al'amurransa a cikin gidan idan zai ci abinci zai ci tare da Chidimma on the same table, ko da kuwa Emily tana zaune a falon ne, da zarar ya nufi dinning ya zauna sai Chidimma ta tashi ta yi Serving dinsa, idan ta gama sai ya ce ta zauna a nan ta ci abinci ita ma, ya kan tambayi Emily ko zata ci sai ta amsa masa da aa, idan ya shigo ma yana tambayar lafiyarta ko ya rika hannunta, amman ba kamar da ba, hakan kuma yana kona mata rai kuma ya jefata a tunani, a yanzu bata san matsayinta ba, replacing dinta zai yi da Chidimma ko kuma dai yana yi ne saboda ya bata haushi.
Da zarar sun fara cin abinci zata tashi ta ba su guri domin bata ita zama tana kallon bakinciki ba, ga Chidimma din sai daukar wanka take tana ta nishadi a yan kwana biyun nan. Ranar Laraba tana zaune a dakinta Fatima ta shigo sanye da uniform ta jefar da Jakarta a gurin haka ma lunch box dinta.
"Yunwa naka ji"
Emily ta dago ta dube ta kamin ta sake maida dubanta gurin wayarta dake hannunta tana karanta sakon da ya shigo mata.
"Kina da Sako a wajen gate ki fito kamin mai gadinki ya hana shiga da sakon"
Ta karanta sakon da aka turo da wata bakuwar number.
"Momy I'm starving
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 63