hannu dama shi ne nata”
“Na sani, ina son na kai ki office dina ne mu gaisa”
Ya shiga office din yana rike da hannunta, ta bude ido tana ta kallon office din.
“Amman kai ya sunanka?”
“Aliyu”
“Okay Mr Aliyu are you Muslim or Christen?”
“Muslim amman Momy na Christen ce, but her name is the Aysha”
Ya bude fridge dinsa ya dauko mata lemu ya bata.
“Taya kika zama musulma mamarki ba musulma ba?”
Ta nufi kujera ta zauna ba tare da ta jira ya mata izini ba.
“Okay, Momy na tace babana musulmi ne shiyasa ta saka min suna Fatima kuma na tashi ta ga ina son musulunci shi ne take barina ina yi, ta koya min sallah, ta fada min ita ma ta taba yin musulunci, amman yanzu ta daina”
Ya zauna a kujerar dake facing din wanda take zaune.
“Kin fada min baki da baba? Taya kuma zaki ce babanki musulmi ne?”
“Ni ma haka Momy na ta fada min, shiyasa nake son ta samu new boyfriend ya zama daddy na, amman kai kana da mata?”
“huh-?”
Ya bude baki not knowing what to say. Ta yatsina fuska.
“Kana da ita?”
“Uhhhh No”
Ya amsa mata saboda ta saki jiki da shi ya samu abun da yake so.
“Okay Good”
Ta masa thumb up ta fara shan lemun da ya karba ya bude mata ya bata, ya ciro wayarsa ya dauketa hoto.
“Hoto kake daukata?”
Ya juyar da wayarsa ya kalli wayar ya manta flashlight din wayarsa a kunne yake.
“Kin min kyau ne shiyasa nake daukarki hoto, kina da kyau, zan so haihuwar kyakkyawar yarinya irinki, so ina son na dauko hotonki ne na aje ina kallo a wayana, saboda mamanki tana min rowarki ba zata tura min hotonki ba”
Ya fada mata haka ne saboda ya wanke kansa.
“Why? Ko zaka sace ni ne?”
“Nooooo ta fada min akwai hotunanki masu yawa a wayarta, nace ta tura min tace aa ba zata tura ba”
“Idan kana so zan tura maka”
“Taya?”
“Zan karbo wayar Momy na tura maka”
“Aa ai ba zata yarda ba, amman ina son ki yi a boye, zan rubuta miki number na sai ki saka a wayar Momynki ki duba whatsapp dinta ki tura min hotunan ta can idan kika tura sai ki goge karki bari ta sani, kin iya turawa ai ko?”
Ta daga mishi kai.
“Na iya, amman ban iya gogewa ba”
Ya bude whatsapp din wayarsa ya nuna mata yadda zata goge.
“Kin gane?”
“Yes”
Ya tashi ya bude karamar durowa ya dauko katinsa ya bata.
“Idan kika gama sai ki jefar da katin a inda ba za a gani ba”
“Okay”
Samun hotonta da hoton mahaifiyarta zai taimaka masa sosai gurin samawa abokinsa mafita cikin sauki.
Ya matsa kusa da ita ya rumgume ya sumbanci kanta, sai ta lafe a jikinsa ta yi shiruuuuu kamin ta dago ta kalleshi ta yi murmushi.
“Muje gurin Momy ki kar ta nemi ki bata ganki ba, amman wannan sirrinmu ne ba zaki fadawa kowa ba haka ne”
“Yes”
‘Yanzu na san dalilin Mamankin na cewa kar ki yi magana da wanda baki sani ba, you're talkative’
Ya fada a ransa domin samu abun da yake so cikin sauki, ya kama hannunta.
“Mu tafi”
Ya rike hannunta suka fita office tana kara masa wasu labarunka da be sani ba, amman hankali ya tafi wani guri he just can't wait ya nunawa abokinsa hoton yarinyar nan da kuma mahaifiyarta, ya san ba karamin dadi Turhan zai ji ba na samun Aysha kawai balle kuma ace ya ga yar nan mai kama da shi.
EMILY POV.
Ta kalli wayarta dake ringing ganin sunan driver Fatima ya saka ta mika hannunta da yayi tsami saboda typing din da take tun safe ta dauki wayar cike da gajiya.
“Hello”
“Ranki ya dade gani na iso gurin tare da Fatima”
“Bata wayar”
Ya mika mata kamar yadda ta umarce shi.
“Hi Momy”
“Hi Baby ki shigo ciki zaki ga Elevator irin wanda muke hawa a New York da Abuja kin tuna? Sai ki taba number 4 idan ya iso office na biyu hannun dama shi ne nawa”
“Okay Momy”
Ya aje wayar yana mika ji take kamar ta gudu saboda wahalar typing din da take amman babu saboda muradun dake zuciyarta. Kamin ta kalli kofar office din wata matashiyar yarinya ta turo ta shigo.
“Hi”
“Hi how can i help you?”
Matashiyar ta karaso kusa da ita.
“Sunana Raheenatu, ni ce sabuwar Assistant ta Miss Amal da aka dauka”
Emily ta gyara zama tana kallonta with little bit of confused.
“O... Ka..y.... Congratulations”
“Thank you, am an fada min nan ne office dina, na yi tafiya ne yau na dawo shiyasa ban samu shigowa da wuri ba sai yanzu”
“No wata kila sun yi kuskure ko kuma ke din baki gane wane office ba, domin ni ce a wannan office din kuma ni ma Assistant din Amal ce”
“I don't think so, but bari na tambaya”
“Okay”
Ta juya ta fice, Emily ta bita da kallo har lokacin mamaki take, ana daukar masu taimakar har biyu ne ko kuma dai kuskuren ta yi kamar yadda take zargi? Can kuma wani tunanin ya zo mata, kar dai ace mutumen da ta yi ma magana dazun babba ne a gurin ya saka aka koreta, bata gama raba dayan biyu ba Amal ta turo kofar ta shigo.
“Emily kika ce ba a nan office din ba ne?”
Emily ta mike tsaye da sauri domin girmamawa ga Amal.
“Yes saboda Ni nake nan, sai dan za a kara wata ne, amman na fi tunanin ko ta yi kuskure ne shiyasa nace ba a nan ba ne, maybe office din gaba ne”
Amal ta yi murmushin rainon wayo.
“Nan ne, ita sabuwar Assistant dinta”
Emily ta wara ido irin na mai mamaki
“Ni kuma fa?”
“Ke ai da ke da babu duk daya, kamfanin nan be san da zamanki ba?”
“Kamar?”
“Kamar yadda na fada miki, tun da aka dauke ki aiki baki sign idan zaki fita ko kuma idan kika shigo, saboda haka ke da babu duk daya a kamfanin nan, shiyasa aka daukar min sabuwar ma'aikaciya, dan haka ki hannata mata komai ki bata office”
Wani abu da bata yi tsammani ba ne ya zo mata a zuciya ya raunatata yayi nasarar saka ta tara ruwan gishi idonta wato hawaye. Emily ta bude baki ta fara magana a daidai lokacin da Aliyu ya shigo office din da Amal ta bari bude yana rike da hannun Fatima.
“Ban san ana sign in and out idan za a fita ba?”
“Ni zan fada miki? Ban baki dokokin kamfani kika karanta ba?”
Kamin Emily ta amsa Amal ta kalli Aliyu cikin girmamawa ta gaisheshi.
“Good Afternoon Sir?”
Ya kalleta ya kalli Emily dake hawaye ya kalli matashiyar yarinyar sannan ya kalli Amal with seriousness.
“Me ke faruwa a nan?”
“Ranka ya dade tana cikin sabin ma'aikatan da aka dauka ne, amman bata zuwa tun da aka dauke ta yau kwana uku, shiyasa kamfani ya dauki wata”
“What-... Wallahi ba gaskiya ba ne, ina zuwa tun da aka dauke ni, kawai bana sign in and out ne shi ma ban sani ba, bata fada min ba”
“Ba a baki file mai dauki da dokokin kamfanin nan ba? Baki karanta ba?”
“An bani amman Wallahi babu gurin a ciki, ban ganshi ba ban sani ba, kuma bata fada min ba, abun da kawai ta fada min idan na shigo na goge mata office dinta na gyara, kuma na rika shigowa karfe 6:30am na safe, jiya ma na yi typing har na 4pm sai da na gama na tafi, gashi a Systems dita, and yau ma gashi ka ga ina yi”
Cikin kuka Emily take maganar ta juyar masa da system din. Aliyu ya kalli Amal.
“Cire takardar kika yi a dokokin kamfani?”
“Aa Sir karya take min sheri ne kawai”
“Amman a dokarmu babu aikin saka ma'aikanmu aiki, idan za'ayi gyara ko wani abun akwai masu yi, har sai idan mutum yafi sha'awar aikatawa da kansa zai aikata, muna da masu aika da zasu siya muna abu, muna da clearness masu gyara guri kullum da safe, and time din shigowa kamfanin nan ga ma'aikanta mu is 8am, masu shara ne suke shigowa 6:30am haka ne?”
Jikinta ya fara rawa.
“Haka amman karya take min, daman tun da aka dauke ta na lura haushina take ji so take kawai ta kulla min sheri”
Emily ta share hawayenta.
“Na kulla miki sheri? Saboda me? Ina da wata alaka da ke ni bayan ta aikin da ya hada mu kwana biyu zuwa uku? Aikin ne baki son na yi shiyasa kika ce na rika shigowa karfe 6 na safe? Kika sakawa ina goge miki office alhalin ba haka dokar take ba? Kika sakawa ina tafiya mai nisa na siyo miki abun da zaki ci? Kuma baki taba fada min ana sign ba? Aikin ne baki son na yi? To na bari daga yau, ni ban shirya tarwatsa rayuwar kowa ba, daman tun da na ganki na san ba za mu jitu da juna ba, saboda ke musulma ce, musulmai ba su da halin kirki sai karya alkawari sai wulakanci sai kyama da nuna banbanci, daman ai ba zaki taba abun kirki ba saboda ke musulma ce, musulmi be taba min abun kirki ba, sai zalinci shiyasa na tsane ku na tsani addininku”
Ta karasa cikin kuka da tsawa sannan ta cire id din da yake wuyanta ta jefar kasa ta dauki jakarta ta nufi yarta da Aliyu ke rike da hannunta ta fisge ta fice daga office din. Aliyu ya kalli Amal a tsanake ya fara mata magana.
“Ba iya suturarmu ce take walkiltar addininmu ba, har da mu'alama da kalamai da dabi'u, kasancewarmu musulmai kawai ta hanyar shigarmu ko sunanmu ba zai wadatar ba, har sai dabi'unmu da mu'amalarmu ta banbanta da ta kowa, ta hanyar kyautata, tausayawa, adalci da kuma bawa kowa hakkinsa, ni musulmi ne ke ma haka, addini ya koyar da mu yadda zamu zauna da wanda ba musulmai ba mu ba su hakkinsu, idan musulmi yayi mummunan aiki, to yana wakiltar duka musulman duniya ne a idon wanda ba musulmai ba, su basa banbance akwai na gari akwai bata gari a cikin addininmu, haka kuma idan musulmi daya yayi abun kirki to a idonsu duk musulmi na gari ne, sai su ji suna sha'awar koyarwar addininmu da dabi'unmu, ban jidadin abun da kika yi ba, ya kamata mu zama jekadu na gari ko'ina”
“I'm sorry Sir, amman sheri take min ba gaskiya ta fada ba”
Be sake ce mata komai ba ya fice daga office din, office dinsa ya nufa kalaman Emily na masa yawo, ya tsinci na tsinta ya watsar da wasu, abun da ya fi tsaya masa a rai kuma ya sosa masa zuciya furucinta na cewar musulmi ba su taba yi mata abun kirki ba, musulmi ba su da tausayi, kuma ta tsani musulunci. Ya yarda da kalamanta ne sama da na Amal saboda ya ganta sau biyu a kamfani ta siyo abu kuma ya ga shigowarta a yau da sassafen nan kamar yadda ta fada.
Ya zauna a kujerarsa yana mamakin wani abu.
‘Anya wanda ya tsani musulunci zai iya bari yarsa ta yi addinin musuluncin har ta koya mata sallah? Kuma ta sakawa yarta sunan Fatima? Ita ya aka yi ta samu suna Aysha? Ta tsani musulunci ta tsani musulmai ko kuma dai mu'alamar wasu daga cikin batan garin musulman ne ya saka ta tsani musuluncin?’
Yana ta sake sake a zuciyarsa, for the first time ya ji yana sha'awar jin full dalilin rabuwar Turhan da matar da yake ta nema yanzu, domin ya tabbatar ita ce wannan duk kan wata alama ta bayyana hakan, dole akwai wani babban dalilin da ya saka ta boyewa yarinyar cewar tana da uba, and dole akwai dalilin da ya saka ta tsani musulunci. Har yanzu dai ba zai karyata ba tana da masifar kyau fuskarta ta tsaya masa a ido, and when ever idanuwansa suka sauka a fuskarta sai ya ji kamar ya santa, wadannan blue eyes din nata suna raya masa saninsu but be san a ina ba, maybe kyaunta ne yake rudarsa. Har ya daga wayarsa zai kira Sahibar tasa sai kuma ya tuna horo yake mata saboda ta gane girman laifinta, kuma ya ladaftarta ita da abun da bata saba ba saboda ta kiyaye a gaba.
________________
Masu karatu ya kuke ganin Turhan zai yi idan ya samu Aysha? Kamar dai Aliyu Ni ma ina son sanin dalilin Emily na tsanar musulmai kuma ina son sanin a ina sunan Aishar nan ya samu asali?
[4/20, 9:59 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/FdvabUKwybz6ogMKtgx02w
*🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
Page 9️⃣
EMILY POV.
Suna isa gate Fatima ta fisge hannunta daga na Emily.
“Bana son tafiya gida yanzu”
“An koreni a kamfanin ko baki gani ba? Asibiti zamu tafi yanzu”
Emily ta sake kama hannunta da karfi ta jata. Sai ta fisge tana daka mata tsawa.
“Bana son zuwa”
Ta nufi titi da gudu zata tsallaka ba tare da ta tsaya dubawa ba, Emily ta yi hanzarin bin bayanta, motar dake dafe da gudu ta taka burge domin kadan ya rage ta buge Fatima. Emily ta kamo Fatima ta riketa da karfi gabanta na dubawa, gilashin motar aka sauke wata matashiyar yarinya ta leko tana kallon Emily.
“Allah yasa ban taba ta ba”
“No”
Emily ta girgiza mata kai, ta matsa gefe, hakan be gamsar da matar ba har sai da ta faka motarta kusa da gurin da Emily take tsaye tare da Fatima ta bude motar ta fito.
“Kin tabbata bata ji ciwo ba? Ban kula ba ne, ina amsa waya”
Cewar matashiyar budurwar dake sanye da gown din atamfa sai fashion cap a kanta, tana jin babu dadi a tunanin kokarin amsa wayar da take a lokacin da take tukin motar ne ya haddasa matsalar.
“Ba laifinki ba ne, karki damu ita ta fisge hannunta a nawa zata gudu”
Matashiyar ta kalli Fatima dake ta huci kamar wani karamin zaki ta sake kallon Emily.
“Amman lafiya”
“Haka take min, bata jin magana”
Emily na rufe baki Fatima da saka ihu tana son fisge hannunta a na mahaifiyarta.
“Ki kyale ni Momy ki sake min hannu, akwai ciwo ina son na tafi gida yanzu”
Matashiyar ta dan zaro ido tana kallon Fatima da mamaki, ganinta karamar yarinya amman da take yi ma mahaifiyarta ihu.
“Ya sunanta?”
“Fatima”
Emily ta amsa mata idonta na cika da kwalla. Matashiyar ta rage tsayinta tana kallon Fatima.
“Sunana Tasmia, please Fatima ki daina yi ma mahaifiyarki rashin kunya da tsawa kin ji babu kyau, ba ayi ma iyaye tsawa da uwa da uba dukansu abun girmamawa ne”
A madadin Fatima ta amsa mata da OK sai ta fada mata abun da ba kowa ya kamata ya sani ba.
“Ni ba ni da uba haka nan aka haife ni babu uba, can you imagine?”
Matahsiyar ta kalli Emily sannan ta mike tsaye ta yi mata sallama.
“Allah ya tsare gaba bye”
Ta juya ta fara tafiya Emily ma ta fara takawa tana kokarin ganin hawayen dake idonta basu zubo ba.
“Can you take us home?”
Cewar Fatima tana kallon Tasmia da already ta bude motarta zata shiga.
“Yes darling ku shigo sai na sauke ku”
“No mun gode zamu hau okada”
“Ni ba zan hau okada ba ni mota nake son ta kai ni gida”
Ta fada a tsawa.
“Is okay Fatima ba sai kin yi tsawa ba, zan sauke ku, please ki shigo ko dan masalahar yarki”
Tasmia ta karasa tana kallon Emily, Emily bata da sauran tace bayan abun da yarta ta take so kuma ta zartar, dan haka ta nufi motar ta bude gidan baya suka shiga ita da Fatima, Tasmia ta shiga mazaunin direba ta ja motar.
“Ina zan sauke ku?”
Fatima ta fada mata unguwar da Number gidan, Emily kuma ta maida fuskarta gefen titi tana kallon ababen hawa, sai dai a badini, zuciyarta zafi take mata tunanin rayuwarta na baya ya dawo mata, damuwa ta baibaiye mata zuciya. Har suka isa unguwar Emily bata ce komai ba haka ma Tasmia Fatima ce kawai ke nuna inda za'a bi har suka isa kofar gidan. Bata jira komai ba ta bude motar ta fita ta rufe gambun da karfe ta doshi gate din gidan ta fara kwankwasawa.
Emily ta bude dayan gefen ta sauke kafafuwanta.
“Mun gode, ki yi hakuri da abun da ta yi miki, haka take bata jin magana, yaran yanzu sai a hankali”
“Haka ne amman yana da kyau mu rika tsawatar musu, idan har bata tsoronki ko ki hada da wanda take tsoro yayi mata hukunci ko yayi mata fada, kamar yayanki ko kanenki ko mijinki ko saurayinki, su yara wani lokacin sai da mai tsawatawa, amman fa ki yi hakuri na shiga abun da babu ruwana”
Tun da Tasmia take magana Emily ke jin wani abu na mata yawo a zuciya, har ya saka ta kasa rike hawayenta sai da suka zubo.
“Wata kila ke kina da duk abubuwan da kika lissafa saboda haka ba zaki gane komai ba, na gode sai anjima”
Ta share hawayen sannan ta karasa fita ta rufe mata motar a hankali. Tasmia bata wuce ba sai da Emily ta shiga gidan, sannan ta ja motarta. Emily na shiga falon ta jefar da jakarta a saman kujera ta zauna ta dafe kanta sai hawaye.
“Duk abun da nake kokarin yi a yanzu, ina yi ne saboda ku da kuma rayuwarku ta gaba, kin ce baki son zama a gidan nan baki son Vito, ina ta kokarin ganin na tsaya da kafafuwana saboda ku, yau kina kallon yadda aka koremu gurin aikin nan kuma mun kama hanyar gida kina min tsawa kina neman ki daga min hankali, dole sai kin fadawa kowa baki da uba?”
Fatima dake zaune a kujera rumgume da hannayenta ta kalleta tana turo baki gaba irin na fitsararun yara.
“Toh ai bani da uba, ba karya na yi ba”
Emily ta dago ta kalleta cikin bacin rai ta daka mata tsawa.
“Kar bakinki ya sake furta haka ga kowa, baki san zafina ba ne shiyasa kike fadar hakan, lokacin da nake kamar ke da ace na samu wata macen a matsayin uwa ko yaya take zan rike ta”
“Toh miyasa baki da uwa? Ni ina ruwana da hakan?”
Ta fada tare da mike tsaye ta dauki remote dake gefenta ta jefar a kasa sannan ta nufi upstairs tana tafiya da karfi kamar wata babbar mace. Emily ta bita da kallo hawaye na sauko mata zuciyata na zafi sosai, ko da damba ne kake wahala da shi kake kokarin ganin ka faranta masa, idan ka fahimci ba kai ne a gabansa ba dole hakan zai maka zafi, balle kuma ace mutum ne, mutum ma yarka jininka. Ta girgiza kai ta share hawayenta ta mike tsaye nufi dakinta, keys din mota ta dauko ta sauko ta sake daukar jakarta ta fice daga falon.
Tafi minti goma a motar zaune tana sauke ajiyar zuciya sannan ta murza key ta yi warming dinta ta juyar da ita mai gadin ya bude mata ta fice, restaurant din dake kusa da su ta fara biyawa ta yi takeaway sannan ta karasa asibitin da danta yake, dukanin abun da take tana kokarin ganin ta boye damuwarta ne, so take ta zama jajirtacciya, wannan dalilin ne ya saka take tare hawayenta a duk lokacin da suka so zuba. Ta shiga dakin da danta yake tana murmushi kamar babu damuwa a zuciyarta, Chidimma ta gaisheta ta amsa tana kallon danta daya dauke fuska alamar baya son ganinta.
“My Boy how are you”
Ya sake juyar da fuskar dayan gafen, bata damu ba ta aje takeaway dake hannunta ta juya gefen da fuskarsa take ta zauna tana masa murmushi sai ya sake juyar da fuska ya matsa gefe.
“Tun da ya tashi yake kiran sunanki”
Chidimma ta fada mata.
“Baki fada masa ina gurin aiki ba?”
“Na fada masa, maybe yana son ganinki ne a lokacin be samu damar hakan ba, saboda baki kusa”
Emily ta sauke dogon numfashi sannan ta dawo gabansa ta tsuguna ta rike kunnuwanta, tana neman yafiyarsa kamar yadda ta saba yi idan ta bata masa rai.
“Okay I'm sorry, Momy ta bata maka rai ka yafe min I'm sorry”
“No i hate you”
A take yanayinta da fuskarta suka sauya, ta kalli Chidimma ta sake kallonsa, sai dai wannan karon bata sake cewa komai ba ta mike tsaye tana jin zuciyarta kamar zata rufe, domin be taba furta mata kalmar i hate you ba sai a yau, ta fice daga dakin ta sake komawa cikin motarta ta zauna tana ta hade wani abu da ya tsaya mata a zuciya.
Bata yarda ta yi kuka ba sai shafa fuskarta take tana kokarin kwantar ma da kanta hankali. Ta sake yi ma motar key ta fice daga asibitin tana tukin motar zuciyarta na kara yin nauyi har ta iso gida, ta faka motar a gun da ta dauke ta, sannan ta bude ta fito tana rike da jakarta har ta isa balcony din kofar falonta ta zauna a gurin ta sauko da kafafuwanta kan interlock tana kallon harabar gidan kamar wata bakuwa.
A lokacin da wayarta ta fara ringing sai ta saka hannunta a jakar dake bude ta dauko wayar ta duba, V ne rubuce a jikin screen din. Ta amsa wayar ta kara a kunnenta ba tare da tace komai ba.
“How are you?”
Kamar jira take sai kawai ta fasa masa da kuka, kuka sosai mai dauke da ihu kai kace yayi mata bushara da mutuwa ne, har sai da mai gadin da mai sharan harabar gidan suka mike tsaye suna kallonta. Be sake furta komai ba ya kashe wayar, ita kuma ta cigaba da kuka da karfi har numfashinta na rawa tana shafa sarkar Cross din dake wuyanta. Da sauri Mai gadin ya karaso kusa da ita yana tambayar lafiya, bata amsa masa ba ta mike tsaye ta shige falonta a kan kujerar falon ta jefar da wayarta da jakar ta haura sama ta shiga dakinta ta kwanta saman gado tare da jan filo ta rumgume tana cigaba da kuka sai dai wannan karon babu kururuwa...
VITO POV.
Ya aje bottle din Hennessy XO dake hannunsa that's Worth 430k, ya gayen dake kusa da shi.
“A siya min ticket din tafiya ina Port Harcourt yanzu nan”
“Okay Sir”
Ya jingina da kujerar da yake zaune gaba daya ransa ya bace jin kukan Emily da yayi, after like 10m gayen ya dawo ya sanar masa babu flight din da zai tashi daga Lagos to Port Harcourt yanzu sai gobe. Ya dago ya kalleshi.
“Ka fadawa manager Happy Home Hotel ya siya min ticket din tafiya Port Harcourt, a siye tickets din duka ina son tafiya yanzu nan”
“Okay Sir”
Ya sake komawa ya kwanta jikin kujerar da tunani biyu, mutumen da ya gani dazun da kuma kukan da Emily take, kokarin hada biyun yake yaga yadda za su zame masa daya ko zai samu amsar kukanta, sai dai zuciyarsa bata natsu da hakan ba. Yadda ya bukata haka maganer hotel din ya aiwatar aka daukar masa shatar jirgi private jet shi kadai daga Lagos to Port harcourt, tun kamin ya bar Lagos ya turawa direbansa dake port Harcourt sakon lokacin da zai sauka, so that ya zama cikin shiri. In less then awa biyu ya sauka Lagos daman daga Lagos to Port Harcourt 1hr 10m ne to nonstop flight. Yana sauka direbansa ya dauke shi a cikin 2022 -BMW X3 baka mai bakin gilashi.
Be sauka ko'ina ba sai gidan Emily, yana fitowa motar be tsaya rufewa ba ya nufi kofar shiga falonta da saurinsa irin saurin dake ake hadawa da guda, a falo ya fara cin karo da Fatima tana zaune a dinning tana shan cornflakes, kallonta kawai yayi ya dauke kai ya kalli wayar Emily dake aje kan kujera da jakarta, be taba komai ba ya haura sama ya tura kofar dakinta a hankali ya shiga. Talkaminsa ya fara cirewa sannan ya taka ya karasa bakin gadon yana kallon fuskarta a take zuciyarsa ta fara rawa ganin yadda fuskarta ta yi ja ta kumbura saboda kukan da ta yi, idanuwanta a lumshe tana bachi sai sauke ajiyar zuciya take irin na yaran da suka gaji da kuka suka yi bachi.
Zaunawa ya fara yi a hankali sannan ya kai hannunsa ya dagota ya kwanto da ita a jikinsa a hankali ya kai hannunsa yana shafa fuskarta, jira kawai yake ta farka ta fada masa wanda ya saka kyakkyawar sarauniyarsa kuka. Jin ana shafa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 63