Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
jikina sai yake ba ni kamar aje yarinyar nan suka yi a can na tsawon lokacin nan" "Ni ma jikina ya ba ni haka, wata kila kuma daman ya san inda take ko da shi ya boye ta ba, ko kuma ya nemota ne, tun da ya fi ni sanin mutane a Kasar nan, yanzu kuma ita sai ta yu tunanin ko ban yi kokarin nemanta ba ne, Aliyu be kyauta min ba, na rasa gane me na yi masa, babu yadda za'ayi ta fahimce ni" Ya dafe kanta kansa idonsa na cika da kwalla damuwa ta matsa tsaye a rai. "Ban san dalilin Aliyu na yi min haka ba, amman ni ba zan iya yi ma Aliyu abun da yayi min ba, abota bata ce haka ba, aminci be cancani wannan sakamako ba" Ammy ta tashi ta dawo kusa da shi ta zauna ta dafa kafadarsa. "Haka butulci yake da ciwo, amman ka yi hakuri kuma ka yi addu'a idan kuma ta nuna bata son kasancewa da kai, dan Allah ka saka musu ido, mutum be taba cin amana ya ga daidai ba a rayuwarsa" "Ko ba zata dawo gareni ba, na aminta amman kar ta auri Aliyu, gayen nan ya gama da rayuwata, kuma idan ya sameta hakan ya nuna ya ci ribar abun da ya aikata kenan" "Idan bera da sata daddawa ma tana da wari ai, idan da can kamin ka bayyana a rayuwarta tana kula Aliyu a yanzu be kamata Aisha ta yi haka ba ko dan yarinyar nan, matukar tana da hankali da tunani yadda dai ka dawo mata ka nuna mata kauna be kamata ka saurari kowa ba sai kai, ita uwa koda yaushe tana son abun da danta yake so ne ko dan farincikinsa" "Ammy Aisha bata da laifi, Aliyun nan dai shi ne shege, ita ai daman fansa take son dauka shi ne be dace yayi min haka ba, Ammy ko dai naje na taro ta?" "Ai baka san yaushe zata sauka ba, kuma karamin aikin yarinyar nan ne ta disgaka a gaban mutane, kuma kasan har Aliyu yana gurin sai ya ji dadi ai" Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi. "Turhan idan Aisha ta zabi Aliyu ko wani ba kai ba, ka yi hakuri dan Allah ka bi a hankali, kai fa namiji ne kuma kai ka fara wulakanta ta, na san ka yi nadama amman ka kara da hakuri idan ka yi hakuri ita kanta zata dawo maka, ko kuma ja ga Allah ya musanya maka da wanda ta fita alheri, ko kuma Allah ya baka zuri'a da matar da kake aure yanzu, tun da ba cewa aka yi ba zaka haihu ko kuma ita ba zata haihu ba" Ya mike tsaye cikin rashin jindadin maganar. Ammy ta bishi da kallon tausayi har ya fice, saukowa yayi kasa ya nufi dan karamin dinning din daya siyawa yarsa take zama ta ci abinci ya durkusa a gurin ya dauki spoon din da take cin abinci ya cigaba da bata abincin tana ci data gama ya bata ruwa ta sha sannan ya rumgumeta. "Fatima ina sonki, kuma ina son mahaifiyarki Allah shi ne shaidata, yanzu ku ne farincikina" Ta yi murmushi domin ta san ina sonki da hausa Ammy ta koya mata. "Daddy ina sonki" Ta yi kwance jikinsa tana jindadi ga babanta kusa kuma ga mamanta zata dawo. [8/1, 6:32โ€ฏPM] ๐—ž๐—ต๐—ฎ๐—ฑ๐—ฒ๐—ฒ๐—ท๐—ฎ ๐—–๐—ฎ๐—ป๐—ฑ๐˜†: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL?mode=ac_t *๐Ÿ’ ABOKIN RAYUWA ๐Ÿ’* *ยฉ Khadeeja Candy* Page 6๏ธโƒฃ1๏ธโƒฃ Suna sauka Airport Aliyu ya kira wayar direba ya sanar masa. Kamin ya iso Aliyu ya nuna Emily gurin zama. "Zauna a can yanzu zai zo ya dauke mu" Ta kalli gurin ta fara takawa ta isa ta zauna, sai ya shiga ciki ya siyo mata ruwa ya kawo mata da dan abun tabawa ba, ruwan kawai ta karba ta rike bata kallon sai Mama Barakat data kasa hada ido da Emily. "Daure ki sha ruwa kuma ki share hawayenki" Ta fara share hawayen sai ya karษ“i ruwan ya bude mata ya mika mata ta karba ta sha kadan, ta mika masa. "Thank you" Ya fada da murmushi sai ta dube shi, wai shi yake mata godiya saboda ta karbi ruwa ta sha kuma ta share hawayenta. "Ina kike son tafiya? Gurin Ummi ko gurin Mama Barakat? Tana son ki zauna kusa da ita" "Ban taba samun abun da nake so ba, duk abun da kuka zaba min yayi" "Inda ina raye abun da kike so shi zaki samu Emily, dan haka zaki bi mu zuwa gurin Ummi hakan yayi?" Ta daga mishi kai tana ta kallonshi kamar yau ta fara ganinsa. Ya kai goran ruwan dake hannunsa bakinsa ya sha har lokacin kallonsa Emily take bata ko motsa ido, daya sha ya sauke gorar sai ya sska yatsansa cikin ruwan ya cire ya tsarka mata dogon ruwan a fuska yana murmushi, daman shi yana daga tsaye ne tana zaune, sai ta lumshe ido tana murmushi. Hakan ya ba shi damar kallon fuskarta ya koreta ta kallo har ya gano ramar da ta yi ta kara mata kyau ne madadin ragewa. Tana bude idon sai yayi hanzarin dauke kansa ya kawar da fuskarsa, a nan ita ma ta samu damar maida biki wato ta dasa masa nata idon tana kallonsa, sai dai ita ba kyaunsa kawai take kallo ba, duk kuwa da kasancewar yana da siffa mai kyau da kwarjini, sai dai ita a gurinta yanzu kyau bashi da value domin kyaun ta bi Khaleefa ya cutar da ita, haka kuma Turhan ma yana da kyau amman kyaun dan maciji, ita a gurin hali shi ne komai kuma zata iya fahimta a yanzu Aliyu yana da banbanci da sauran, sai dai bata san gaba ba. "Gashi ya zo tashi mu tafi" Ta mike tsaye tana kallonsa kamar babu wani abun kallo a gurin sai shi. Suka jera a tare suna tafiya har suka isa gurin motar ya bude mata baya ta shiga, Direban kuma ya dauki kayan ya saka a bayan mota Mama Barakat ma ta shiga baya Aliyu ya shiga gaba direban yaja motar suka fara tafiya. A harabar gidan direban ya faka Aliyu ya fara fita ta gefen daya fita Mama Barakat take sai ya bude mata kofa sannan ya zagayaya budewa Emily dake zaune tana jiran ya zo ya bude mata, ta kalleshi sannan ta fito ta ya rufe suka jera shi da ita suka shiga cikin falon da Ummi take tsaye tana jiran isowarta. "Maraba Maraba da yata, yar dake guduwa ta bar yarta" Ummi ta rumgume Emily cike da farinciki, sannan ta kama hannunta suka zauna Aliyu ma ya zauna haka Mama Barakat. Direban ya shigo da manyan akwatunan Emily sai Ummi ta kalli mai aikinta ta ce. "Kulu a dauki kayan nan a shigar da su dakina, daga yau dakina Emily zata zauna" "Dakinki kuma Ummi" Aliyu ya tambaya da mamaki. Ummi ta ce "Eh dakin uwa ai na yarta ne, ba zan sake yin wannan saken da na yi ba kika gudu kika barmu, kika daga mana hankali na fi son kina kusa da ni ina jin motsinki, idan muka tashi komawa Abuja ma dake zan tattara mu tafi, idan ma kin zabi sake buguwa ki fada sai na hada kayana mu tafi kin ga neman zai fi dadi" Aliyu yayi murmushi Emily ma ta yi murmushi tana kallon Ummi. "Ba zan sake guduwa ba" "Zamu gani dai, amman ni dai ba zan sake bari ki gudu ba" Ummi ta tabe baki tana yi ma Aliyu kallon zolaya. Emily ta kalli Aliyu suka sakar ma junansu murmushi mai laushi da sanyaya zuciya sannan ta sauke kanta kasa, Aliyu kuma suna hada ido da Ummi ya ga irin kallon da take masa sai ya girgiza mata kai alamar ba abun da take tunani ba ne domin ya san hasashenta, ya mike tsaye yana murmushi mai sauti. "Bari naje na yi sallah" Ya fice daga falon, Ummi ta kalli Mama Barakat. "Ki shigo dakin kasa sai ki yi sallah ko" "Dare yayi Hajiya zan tafi gida dai, gobe sai na dawo" "Toh ba matsala direba yana waje sai ya sauke ki gida" Mama Barakat ta mike tsaye. "Mu kwana lafiya Hajiya na gode" Bayan Ummi ta amsa mata ta juya ta fara tafiya kamar daga sama ta ji muryar Emily. "Sai da safe" Ta juyo jiki a sanyaye ta kalli Emily. "Na yi tunanin ba zaki amsa ni ba ne, shiyasa ban miki sallama ba, ki gafarce ni" "Zuciyata ta saba da karbar ko wane kalar sako na bakinciki, kaddara ta sunnanta min haka, shiyasa na fahimci rayuwar da nake ciki, ni ce nake son mutane ba wai mutane ne suke so na ba, kuma na yarda zan cigaba da rayuwa a haka" Mama Barakat ta fashe da kuka. "Wallahi ba haka ba ne, karki yi zaton bana kaunarki, ina sonki fiye da tunaninki" Ummi ta kwantar da Emily dake kuka a fadarta sai ta yi ma Mama Barakat alama ta tafi da hannu. Mama Barakat ta fice tana kuka. "Toh miye amfanin kuka? Abun da ya wuce ai ya wuce, ni uwa ce a gareki Emily, kuma ki daina wannan tunanin na cewa babu mai sonki, da kin san tashin hankalin da muka shiga ni da Aliyu da mai gidana na rashinki sai kin tausaya mana" Ummi ta dagata daga kan kafadarta. "Muje ciki ki yi wanka ki ci abinci ki huta na baki labarin yadda aka yi muka gano ki, ko Aliyu ya fada miki?" Ta girgiza yau. "Yauwa aikuwa ni zan baki wannan labarin, daman duk ya bi ya ishe ni komai ya tattare baya barin ma wani ya shiga balle ya kyautata miki, shiyasa ma ya fara ba ni haushi sai ka ce shi kadai yake da ke" Cikin yanayin rarrashi da son faranta rai Ummi take maganar da Emily kamar mai magana da yar yarinya karama sa'ar Fatima. Ummi ta rika ta ta kwantaa fadarta ta rike hannayenta suka fara haurawa sama. "Kudi ya zuba can gurin Office din kamfanin sadarwa, bayan mahaifinsa ya saka baki aka duba wayoyin da kika kira, aka ga layina da na Aliyu da kuma na wannan likitan, aka ce wunin ranar da su kawai kika yi waya, Aliyu na jin haka ya ce duk yadda aka yi kina gurin Dr, ya fara bibiyar layin, amman da yake likitan nan baya son mu da alheri da Aliyu ya tura masa sako be ba shi amsa ba, muka rika sama da kasa sai da muka hada da Hajiya Baraka ta sama mana Information din mahaifiyarsa Aliyu ya dage, amman ni nake taya shi da addu'a fa dan kar ki yi zaton kamar ban yi komai ba, ke daga karshe sai da mahaifinsa ya shiga kuma ita ma Hajiya Barakat ta yi magana da roko da komai aka samu ta amsa mana tace su zo wannan satin Aliyu ya saka date suka tafi, kamar a mafarki sai na ga sun dawo min da ke, na ma yi zaton za ku tsaya ku kwana Abuja, ashe ya damu da halin da nake ciki sai ga shi be tsaya kwana ba ya dawo" Emily tana kwance kafadar Ummi tana bata labarin har suka shiga dakin. "Kin ji yadda aka yi, amman fa mum shiga tashin hankali sosai, ba dan ni ba dan Allah Emily karki sake guduwa ko minene kamata yayi ace kin tsaya kin fuskance shi ba wai ki gudu ba" "Na rasa ya zan yi ne, abubuwan suka hade min ko'ina ba dadi" "Har da gidana? Ko kadan ni fa ban bi bayan Hajiya Barakat ba dama ta ba ni labarin abubuwan da suka faru ke na fi tausayawa, to kin ga ni miye nawa da zaki dora min laifi?" Emily ta dago da sauri. "Ban dora miki laifi ba, ko kadan baki min komai ba" "To miye na duguwa ki bar gidan? Na yi tunanin ko ba zaki iya zama ko'ina ba zaki zauna a gurina, har tambayar kaina nake wai ko dai na miki ba daidai ba?" "Baki min komai ba, kuma ba zan sake guduwa ba" "Alhamdulillah Allah yasa haka" Ummi ta rumgume har ga Allah Ummi tana jin tausayin Emily sosai. Bayan Emily ta yi wanka ta canja tufafi sai ta dauki abaya ta dora saman kananan kayan da suke jikinta domin suturta jikinta, na ci abinci ta kwanta kan gado, babu jimawa Nafeesa ta shigo kiranta wai Ummi ta ce ta sauko kasa idan ba bachi take ba. Babu musu ta fito a dakin na Ummi ta sauko kasa tana jin kamar ta samu gata a yanzu ko da yake bata san me gobe zata haifar ba, amman dukanin wani kulawa da uwa zata nunawa yarta Ummi ta nuna mata a yanzu. Ta sauko a hankali ta karaso ganin kowa yana zaune kasa sai ta zauna ita ma, kusa da Aliyu sosai a gurinta ita ba komai ba ne dan jikinta ya taba na wani wanda ba Muharraminta ba, a addinin data samu kanta ciki hakan ba laifi ba ne, kuma ta saba. A kokarin Aliyu na bin umarni Allah sai ya matsa kadan dan kar jikinsa na taba nata, domin ya san ita din ba halalinsa ba ce. "Muna ta fira muna shan tsamiyar dila baki kusa na ce a kira ki sauka mana cikin dangi, amman na fada mata idan bachi kike ta barki ki huta" "Ba bachi nake ba" "To ga abun da muke ci idan zaki iya ci, saka hannunki ki dauka sai an balle ake ci" Ummi ta fada, kamin ta saka hannunta sai Aliyu ya dauki karamin plate ya aje gabata ya zuba mata wanda ya banbanra. "Sha ki ji ko zaki iya ci" Ta dauka ta kai baki sai ta ji abun wani iri domin bata taba ci amman dan tsami tsamin da ta ji ya karbi bakinta dan haka ta cigaba da sha. Kwankwasa kofar falon aka yi kadan kadan kamar bugun yaro, Emily ta kalli kofar da sauri zuciyarta na bugawa da gudu kuma tana raya mata Fatima ce. Aliyu ya mike tsaye ya nufi kofar ya rufe sai ga Fatima ta shigo da gudu. "Uncle..." Har ta rike shi zata rumgume shi sai kuma ta sake shi ta nufo gurin Emily da gudu, Emily ma kasa rike kanta ta yi sai ta zabura da sauri ta rumgume yarta ta fashe da kuka, zata iya yafe komai da kowa amman ban da yarta, ko kadan bata son Fatima ta dandana rashinta domin ta san yadda ta rayu saboda uwarta bata kusa da ita, cikin kuka Fatima ta ce. "Momy ina kika je? Kin dade baki zo ba" "Saboda kin ce baki so na" Sai ta kara rumgume Emily. "Ina sonki ke da daddy ina sonki,. Karki sake tafiya ki bar ni bana son ki tafi" Emily ta rumgume. "Idan baki son na tafi ki daina zabar Mahaifinki kina barina, ko gobe kika ce shi kike so to zan tafi na kyale ki" Sai Fatima ta kara fashewa da kuka. "Amman ina son shi Momy, yana so na" "Who do you love the most? Ni ko Dady?" "You" "Good" Emily ta rumgume ta sosai a kirjinta kamar zata maida ita ciki. Fatima na shiga cikin falon Aliyu ya kalli Turhan dake tsaye bakin balcony din be tako ba, sai ma dukawa da yayi yaje masa wayarsa a kasa. Ya saka hannayensa duka biyu aljihu. Aliyu na ganin hakan ya fita ya karasa gurin da wayar take ya duka zai dauka. "Ka ji kunya Aliyu, ka ci amanata" "Ban ji kunya ba, kuma ban ci amanarka ba, akwai tsarin da na yi sai dai Allah be ba ni ikon cika wannan burin ba har Kameela ta yi abun da ta yi" "Ai baka da bakin kare kanka" "Ba kokarin kare kai nake ba, kuma ba so nake ka fahimta ba, ina fada maka abun da yake gaskiyarsa ne" "Har abada... Ba zan taba barin yata ta kira wani katon banza da sunan Baba ba, yata ba zata yi agolanci ba yana da kyau ka san wannan" "Kai yanzu baka ji kunyar fadar hakan ba? Kai yanzu abun da ya dame ka wa Emily zata aura? Ko wa take so? Baka damu ka san lafiyarta ko samun farincikinta ba? Kana da son kanka Turhan... Kuma har gobe ban yi nadamar taimakin Emily ko kuma boye mata kai ba, saboda ta fada kai ne wanda bata son ganin kuma zaka karbe mata yarta ga shi ka aikata, kai yanzu iyakar burinka Emily ta dawo gareka, idan ta dawo zata dawo ta yi farinciki ko aa ba shi ne a gabanka ba, kaico da zuciyar dake take kirjinka" "Kai kuma Tirrrr da aboki irinki mai fuska biyu, zan baka mamaki Aliyu, kuma ina gargadinka da shiga tsabgar matata da yata, baka da alaka da dukkansu" Aliyu yayi murmushi kawai ya juya ya shiga ciki, Turhan ya tofar da yawu yana jin zuciyarsa tana kuna. Aliyu na shiga falon Fatima ta juya ta kalleshi. "Ka ce Dady ya tafi sai gobe zan koma tare da Momy" "Already ya tafi ai, ni ba zaki min oyoyo ba?" Ya ware hannayensa, sai ta taso tana dariya ta nufe shi da gudu ta rumgume shi ya daga ta sama ya jefa ya chabe yana dariya ita ma sai datiya take tana farinciki domin ta yi marmarinsa da Momynta. Emily tana ta kallonsu tana murmushi. " Kin yi missing din Momy?" "Sosai" Ta fada tana kallon Emily, sai Aliyu ya dauke ta haura sama da ita suna tafe yana mata hira. A ranar Emily ta yi bachin farinciki irin wanda ta kwana biyu bata yi irinsa ba, ta kwanata rumgume da yarta a dayan dakin da Ummi ta bata saboda ta ki yarda ta hau gadon Ummi ta kwanta sai dai kasa, Ummi kuma ba zata iya jurar kallon ta kwana a kasa ba, dan haka ta bata wani dakin ita da yarta. Kamin Fatima ta yi bachi sai da ta yi ta bata labarin abubuwan da Ammy take mata da kuma Dadyta. Washe gari Emily na cikin bachi ta ji an taba ta sai ta bude ido, ta yi zaton Fatima na dakin sai ta yi arba da Mama Barakat ga kayan abinci an jere a gurin kamar dai wacan karon. "Ki yi hakuri na tashe ki kina bachi" Emily ta murza ido ta tashi zaune tana duba gadon har tana kokarin sauka sai ga Aliyu ya kwankwasa kofar dakin, sannan ya turo ya shigo yana dauke da Fatima. "Mama Ummi tace min kin shigo yanzu" Ya fada yana kallon Mama Barakat. "Eh ku yi hakuri na yi muku sammako, bana son Emily ta karya da komai ne sai abun da na dafa" "Wacece wannan?" Fatima ta tambaya tana nuna Mama Barakat. "Kakarki ce, ita ce ta haifi Emily" Fatima ta wara ido kamar wata babba tana mamaki. "Muna da kowa a nan ina farinciki da zama a nan ba za mu koma can ba ko Momy? Ashe ke ma kina da Momy" Emily ta daga mata kai. Aliyu yayi murmushi. "Karki yi zaton ko na shigo na same ki a yanayi marar kyau ne, ita ce ta farka da kanta ta fito tana bin daki har ta same ni, wai ta yi zaton ko na tafi ne" "Momy mun yi sallah mun yi sallah da shi kina bachi" Emily ta yi murmushi tana kallonsu. "Aci dadi lafiya ni zan sauka, Emily idan kin gama da wannan sai ki sauko na mu breakfast din yana jiranki, Ummi ma sai fada take wai Mama Baraka ta dako sakko baki farka ba kuma ta san zata shirya miki abun karyawa" Mama Barakat ta yi murmushi. "Ka bata hakuri, na tashi tun karfe uku na fara shirya komai saboda kar na makara, zan yi farinciki idan ta ci" "Zata ci, ai Emily bata da matsala ko kadan kamar ruwa haka take, kifi ce musulmi nama" Ta fada sannan ya juya ya fita yana dauke da Fatima dake tambayarsa miyasa Emily bata kama da Mama Barakat? Bayan ita tana kama da Turhan. Emily ta shiga bandaki ta wanke bakinta da sabon brush da ta gani ta yi fitsari ta fito ta zauna bakin gado, sai Mama Barakat ta sauka kasa ta bude abincin gaba daya tana tambayar wane zata ci. "Ina son na kira ki da Aisha ban san ko kina son haka ba, Ummi ta fada min ana kira Aisha amman Emily ya fi karfi, amman sunan da na saka miki Aisha ne ba Emily ba, musulma na haife ki ba kirista ba" Emily ta dube ta. "Kina so na haka kika bar ni? Har yanzu na gagara gane wane laifi na aikata miki, na wahala an wulakanta saboda ba ni da kowa, anyi min gori, abubuwa na suka banbanta da na sauran masu iyaye, ban san gata ba ban iya komai sai guduwa daga wannan gurin zuwa wani, fada da kika yi cewar da saninki kika jefar da ni kuma baki taba tunanin ki waiwaye ni ba ya tsaya min a rai, mu ma yaya muna da hakki akan iyaye, baki yi adalci tsakanina da sauran yayanki ba, su kika zabi haifarsu da aure kuma kika zauna tare da su, ni kuma kika watsar da ni, baki yi tunanin waca kalar rayuwa zan yi ba, wane kalubale zan fuskanta ba, kin yi komai saboda gujewa kunyar duniya, shin ba na ji ku musulmai kuna cewa lahira akwai hisabi ba? Saboda kin haife ni ba da aure ba ni miye laifina? Ba shawara aka yi da ni kamin a haife ni ba, ya kamata ki yi tunanin idan kika jefar da ni wace kalar rayuwa zan yi? Zan rayu ko kuma zan mutu ne? Baki tunanin ni ma ina da hakki akanki? Taya kika iya kwantawa ki yi bachi alhalin kin san kina da ya a wani gurin da baki san wane hali take ciki ba? Wace irin uwa ce ke? Taya zaka sha wahalar ciki wata tara da nakuda kuma ka jefar da yaron? Shi ma fa rai ne? Uwa tausayi aka sani da ita ke da iyayen da suke haka ba ku kyauta ba, miye laifin wanda aka haife? Wai illar kawai saboda ba shi da uba, kuma ba da aure aka haife shi ba, miyasa baki yi tunani ba kamin ki haife? Wallahi na Wahala na wahala na wahala, ni kadai na san yadda na yi na Wahala na wahala na wahala na wahala na wahala........... Ahk ahk ahk..." Ta fashe da wani irin kuka mai taba zuciya da ฦ™oฦ™on rai. Mama Baraka ta bar inda take ta dawo kusa da Emily ta zauna ta rumgume ta tana kuka. "Ki gafarce ni, ki yafe ni na yi kuskure na sani, ki yi hakuri Emily ki yafe min..." Emily kuka Mama Baraka kuka babu mai iya rarrashin wani... ______________________ Ga iyayen da suke haifar yara ba da aure ba su jefar, shin kun san kuna daukarwa kanku hakki ne? Hakkin zina hakkin haihuwa ba da aure ba hakkin jefar da yaro, ba ku san wane hali zai fada ba wace rayuwa zai yi a wane hali zai girma ko ya samu kansa ya rayuwa zata kasance, wasu yaran ba za su taba haduwa da iyayensu ba sai Alkiyama. Allah ya tsaremu, ka tsarkake zuciyarmu.๐Ÿคฒ [8/4, 9:55โ€ฏPM] ๐—ž๐—ต๐—ฎ๐—ฑ๐—ฒ๐—ฒ๐—ท๐—ฎ ๐—–๐—ฎ๐—ป๐—ฑ๐˜†: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL?mode=ac_t *๐Ÿ’ ABOKIN RAYUWA ๐Ÿ’* *ยฉ Khadeeja Candy* Page 6๏ธโƒฃ2๏ธโƒฃ Na tashi a wani ฦ™aramin gida a Beere, cikin unguwar da ruwa ke ta faman gudu daga bututun da babu mai kulawa da shi, cikin amo da hayaniyar kasuwa, da ฦ™amshin ewedu da ata rodo na mahaifiyata. Baraka suke kirana ษ—iya ga wani tsohon malamin addinin. A cikin al'adun Yarbawa, mata suna da 'yancin yin kasuwanci, sana'a ko aiki tun da dadewa. Wannan ya bambanta da wasu al'ummomi da ke takaita mata ga aikin gida kawai. A yawancin biranen Yarbawa, musamman kamar Legas, Ibadan, da Abeokuta, za ki ga mata masu kasuwanci ko aiki a hukumomi. Iyayen Yarbawa suna koyar da 'ya'yansu mace da wuri cewa ta rike kanta Yana daga dabi'unsu su karantar da 'ya mace ta nemi ilimi ko sana'a domin ta rike kanta, ba tare da dogaro da namiji ba. Wannan ya sa da yawa daga cikin matan su ke da ฦ™warin gwiwa wajen kokarin ciyar da kansu ko tallafa wa iyalansu. Na koyi juriya daga rayuwa, ba daga littafi ba. Na girma ina kallon mahaifiyata tana dafa abinci a kan itace, tana kula

Chapter 49 of 63