Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ba kamar Fatima ba dake nuna masa kiyaya da rashin kunya, kuma ta ki yarda da sunan Lisa da ya saka mata, haka kuma har gobe idan ibadar ta tsikareta sai ta yi sallah ko taje Islamiyar da mahaifiyarta ta sakata. Chidimma na shigowa falon ita ma ta fashe da kuka, kusan idan aka cire Vito London ya fi sabo da ita fiye da mahaifiyarsa musamman a yan kwanakin nan da baya yarda da Emily. KAMEELA POV. "Hhmmm sai yau kika tuna da ni?" "Ke tunawa kike, ke da ba kira kike ba sai dai a kira ki?" "Baki san na haihu ba halam?" "Tohm yaushe?" "Yau kwana takwas, amman abun da na haifa be zo da rai ba, ina gida" "Allah sarki Allah ya bada rayayye" "Ameen kina PH har yanzu" "Eh mana kin san sai na yi shekara a nan ai" "Okay Allah ya taimaka" "Ameen, shi mijinki yana nan kenan?" "Tasmia ina ruwanki da mijina da har zaki tambayi mijina bana fa son haka" Tasmia ta kalkale da dariya "Kameela kina bani mamaki, wai ke lafiya kike kar kishi ya haukata ki fa" "Ke ya haukata ni din ina ruwanki? Toh miye na tambayar mijina" "To ai na ga yadda kike da kishi ne na yi zaton ko ba zaki iya barinsa a can ba tare kuka zo wanka gidan" "Mtssschesssss" Ta yanke kiran. Tasmia ta kyalkyale da dariyar mugunta. "Yau da kin san abun da mijinki yayi da sai kin kusa kashe kanki dan kishi, gashi nan daga tafiyarki ya tsallaka gurin wata da ba addinmu daya ba" Ta sake fashewa da dariya. "Ko da yake gayen ya hadu dole ki yi kishi ki yi taka tsantsan ai" Ta fada tana murmushi kamin ta tashi daga kwancen da take ruf da ciki ta yango Food flask dinta mai two set da ya siya gurin Khadeeja Candy ta bude ta zubawa kanta tsemo da miyar agutsi. Ta sake daukar wayarta ta kira layin Emily sau biyu tana maka miss calls sai a uku aka daga. "Hello..." "Wacece wannan" "Kawar tace" Dip ta ji an kashe wayar ta duba wayar tana mamakin waya daga? Ta sake jira sai ta ji wayar kashe. Ta tabe baki ta aje wayar kusa da ita ta cigaba da cin abincinta. ALIYU POV. Ya kalli harabar gidan da iska mai dadi ke kadawa sannan ya amsa. "Ina gida" "Gida a ina?" "Compound" "Me kake yi a nan toh?" Yayi murmushi. "Wai ke me kika dauke ni ne? A harabar gida gidan dai ba aljannu ne za su tsallako su shigo nan ba ina zan ga mata?" "Baka kallon mata amman ai akwai social media kuma wasu ma za su iya samun numberka su kiraka" "Saboda ni kadai ne namiji a duniyar nan? Kameela wai wane irin kishi ne yake damunki? Ke har alkawarin da na yi miki ba ki yarda da ni ba" Ta yi shiru. "Na san kowa da yadda Allah ya halicce shi, amman ya kamata ace muna damuwa da wasu abubuwan ba wai kishi ba a koda yaushe, already kin aure ni, ina sonki kina sona kina da kishi wannan abu ne da na sani tun kamin na aure ki kuma na aureki na miki alkawari ba zan miki kishiya ba, toh miye kuma abun daga hankali da bin diddigina?" " Mata shedanu ne wata zata iya sakawa ka karya alkawarin da ka yi min" "Akwai abubuwan da ya kamata ace mun damu da su, wata ma kokarin ganin ta samu kwanciyar hankali take, wata bata da iyaye bata da yan'uwa bata da kowa, damuwarta na samun canjin rayuwa ne, bata ta kishi take ba, be kamata muna damuwa da wasu abubuwan Kameela" "Damuwar wasu ba tamu bace, kowa ai da kalar kaddararsa, ni tawa kaddarar kishi ne da kaunarka yaushe zaka zo?" "Sai idan zaki koma zan zo na tafi da ke" "Saboda me? Yanzu baka yi marmari na ba?" "na yi idan na zo mi zan yi? Aiki nake a nan fa Kin sani, zan zo amman dole sai na dauki hutu" "Toh ka dauki hutu mana" "Okay, zan dauka shikenan" "Eh i love you" "I love you more, ki kula min da kanki" "I will sai da safe" "Okay" Ya aje wayar yana daga kansa ya kalli sama, labarin Emily halin da ta shiga kawai yake hangowa, ya kan ji labari kala kala na ban tausayi amman be taba jin kalar nata ba, be taba arba ido da ido da wata mata da ta sha wahalar rayuwa kamar ita ba. Duk kuma labarin da ta bashi na rabin wahalar da ta sha ne na rayuwar da Khaleepa, be san wane irin zama suka yi da abokinsa ba, be san ya ya riketa ba, da alama shi ma bata sha da dadi ba shiyasa har take guje masa kuma ta biyowa yarsa cewar tana da uba a raye. Ya sauka daga bayan boot din motar da yake zaune yana mamakin yadda zuciyar wasu mazan take bushewa su saka rashin tausayi a ciki har su cutar da abokiyar zamansu, ba su yarda ana hisabi ba ne ko kuma dai gani suke kamar matan ba su da hakki su kadai ne suke da hakki akan matansu? Abun takaici ne kuma abun haushi ace Khaleefa ya juya mata baya ya san wacece ita kuma ya amince ya aureta. A yadda taba shi labarinsa mutum mai addini amman ya take saninsa ya rufe ido ya zalinci wanda bata da kowa sai shi. Bata da uwa ba uba sai shi ko da yake har a yanzu a cikin wahala take a ganinsa saboda Vito ya mata duka a gabansa ranar da yaje gidan, shi ma yayi mata hakan ne saboda ya san bata da kowa. Ya tabbatar da ace tana da iyaye a raye wannan kangi da wahalar rayuwar da cin zafin ba za a yi mata shi ba. "Rashin iyaye masifa ne" Yana maganar yana danna kiran mahaifinsa bayan sun gaisa ya nemi ya ba shi Ummi ita ma suka gaisa sannan yayi musu sallama ya kashe wayar. Ya gwada kiran number Emily har sau biyu ya ji ta a kashe sai ya ji duk ya damu ya san halin da take ciki domin ya aje ta gidanta a dazu a wani yanayi marar dadi, yanzu kuma ya ji wayarta a kashe, waya sani ko mutumen dake nuna mata fin karfi ya ga lokacin da aja aje ta a dazun ko kuma wani ya fada masa, waya sani ko ma ya mata duka akan haka saboda kowa ya maida ita baiwa saboda bata da gata. Gashi ya tuna mata da baya ya san yanzu damuwar zata mata yawa, a yanzu ya gamsu da hujjarta na son gina rayuwarta ita kadai da take ba tare da neman taimakon kowa ba. "Idan kin ga wannan sakon ki kira ni, ina son na san halin da kike ciki" Ya aika mata sakon yana jin zafin yadda suka cutar da ita har cutarwa ta yi nasarar sauya tunaninta akan musulunci da musulmai. Ya dan jima a tsaye a waje, labarin da ta ba shi kawai yake ta hararowa yadda ta yi zaman. Sai kuma ya ji ya kagu ya ji irin zaman da ta yi da Turhan yadda ta hadu da Vito kuma taya halittar jikinta ta canja zuwa siririya bayan Turhan ya fada masa tana da jiki sosai a labarin da ta bashi a yanzu kuma ta fada masa ta yi rama sosai a gidan Khaleefa saboda wahalar data sha. Ya bude motarsa ya zauna a ciki yana kai dubansa gurin agogon da ta aje masa dazun a office. Ya kai hannu ya dauko agogon yana ta juya shi a hannunsa. "Kai wasu mazan akwai bakar zuciya" Ya fada yana mamakin yadda wani zai aikata abun da shi ba zai iya kusantar makamancinsa ba me balle ya aikata. "Waya sani shi ma ko yana can yana nemanta" Ya ayyana da nufin Khaleefa a ransa kuma yana jin haushin Turhan tun gabanin ya san wane irin zama suka yi. EMILY POV. Ya aje wayar a hankali kusa da ita bayan ya kashe wayar gaba daya. Ya zauna kusa da Emily da bata iya daga ido saboda kukan da ta sha idon ya rufe mata sai ciwo yake. "Za a maida shi mutuware su aje shi a can kamin ki samu salama a shirya bikin mutuwarsa" "London Musulmi ne, musulmi na haife shi please ka bari a birne shi a makamartar Musulmi, ina jin kamar ban masa adalci ba idan na masa haka, ban bashi kulawa data dace ba, da ace na san zai mutu da na zauna da shi a kowane second da minute" Vito ya rumgume ta. "Ai kin bashi kulawa, shi ne yake kyamarki ba laifinki ba ne" "Amman ai shi ba shi da lafiya ya kamata na masa uzuri" "Baki da laifi a gurin kowa Emily, lokaci yayi da ya kamata ke ma ki so kanki ki dagawa kanki kafa ki yi ma kanki uzuri, kin bashi rayuwa mai kyau ki tuna shi ya rayu da uwa da yar'uwa hakan ma abun farinciki ne a gareki" Ta daga kanta daga jikinsa ta kalleshi duk da kasancewar bata iya bude kwayar idon. "Na gode Vito na gode daka taimaka min gurin bashi gata da rayuwa mai kyau, na gode da baka taba gajiyawa da shi ko maganinsa ba, baka taba kyamarsa ba" Ya maida ita kirjinsa. "Ba zan taba kyamar abun da ya fito daga jikinki ba" Ya shafa bayanta a hankali alamar rarrashi. _______________________ Slowly slowly🥺 VITO is my favorite 🤭 Team VITO iya wuya🫶 [5/10, 7:12 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ FOLLOW ME ON 👇🏻 FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914 TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Page 2️⃣4️⃣ "Har yanzu zuciyarki tana sha'awar musulunci ko Emily? Har yanzu baki dauki darasi daga azabar da muslmai suka koya miki ba? Da biyu kike zaune a cikin addinin kiristiyaniti ko?" Ta dago ta kalleta inda take kyautata zaton fuskarsa take domin bata iya gani da kyau. "A yanzu kake son mu yi wannan maganar?" "idan har babu wata manufa a zuciyarki a wane dalili zaki ce a kai shi makabartar musulmai? Ina ruwanki da kasancewarsa a baya musulmi? Ai kin canja masa addini ko? Ubansa da yake a cikin addinin be damu ba sai ke da kika haura kika leka ciki?" Ta rasa abun cewa, domin ta san ya fita gaskiya, Ubansa be damu ya san halin da take ciki ba balle abun da ta haifa gashi har London ya bar duniya be taba ganin ubansa ba. "Ba ni da alaka da musulmi ta kusa ko ta nesa, ba zan iya tafiya makabarta na tambayi wani yadda za a binne London ba, ina son kin Emily ina son yaranki, amman hakan ba zai saka na kusanci addinin da ba ni da makiyi irinsa ba" Ya mike tsaye ya dauki wayarta ya saka aljibu, ba tare da ta gani ba domin idonta a rufe suke. "Ka bar min dana bana son ka masa biki" Be juyo ba kuma be ce mata komai ba ya fice daga dakin, ko da ya sauko ya samu Chidimma zaune a falon har lokacin tana kuka sosai ita ma idonta ya kumbura domin mutuwar London ta zo mata a bazata. Wayar Emily ya ciro ya mika mata. "Ki aje wannan a gurinki karki bata har sai idan na bukata" "Okay Sir" Ta fada cikin kuka sannan ta karbi wayar ta tashi ta fice daga falon zuwa bangaren da dakinta yake ta boye wayar sannan ta dawo ta shiga dakin da Fatima take. Cikin karfin hali Emily ta tashi tana lalabe har ta isa bandaki ta kunna fanfo ta jika kanta da jikinta ta dauki karamin tawul ta zuba ruwan zafi ta gasa idonta, sannan tana iya daga su ta kalli abu but still tana jin ciwo. Ta fito bandakin ta nufi wardrobe dinta ta sauko short gown ta saka ta nufi gurin da makullin motar yake ta ga baya gurin, sai ta tuna yana cikin aljihun gown din data cire motar kuma tana can asibiti, gashi dare ne yanzu idan ta fita ba lallai ta samu abun hawa in time ba, haka kuma ba lallai ne ta tafi inda take nufin tafiya ta samu mutane a gurin ba. A nan ta fara neman wayarta ita ta rasa ina ta aje wayar, ta dafe kanta ta busar da numfashi sannan ta bude gurin da Vito yake aje mata kudi ta dauka ta fito daga dakin ta sauka kasa. Har ta nufi kofar fita sai kuma ta dawo ta sake haurawa sama zuwa dakin Fatima ta tura kofar a hankali ta leka sai ta hango Fatima kwance a jikin Chidimma, jan kofar ta yi ta rufe ta sauko ta fice daga gidan gaba daya. Ta yi tafiya mai nisa sannan ta samu abun hawa, ta kwatanta masa inda zai kaita wato gidan Tasmia, domin bata manta inda suka hadu ba har ta yi mata tayin shiga gidanta bata yarda ta shiga ba a wacan karon, da suka isa ta sauka ta bashi kudin da bata san nawa ba ne ta doshi gurin da kofar gidan mai kama da BQ yake ta kwankwasa, babu jimawa aka bude mata bayan Tasmia ta tambayi waye tace mata ita ce. Da maimaki take kallonta. "Lafiya? Me ya same ki?" "Zan iya shigowa?" Emily ta furta muryarta na rawa. Tasmia ta matsa jikin kofar ta bata hanya kana ra leka waje ta ga ko tana tare da wani ne. Ta shiga ta zauna sai wani sabon kuka ya zo mata. "Lafiya?" Tasmia ta tambaya tana dafata cikin tashin hankali. "I lost my Son" "Subhanallahi yaushe? Me ya faru?" Cikin kuka Emily ta fada mata yadda London ya mutu. "Na fi son yaron nan fiye da komai na duniya, saboda lalurar da take tare da shi, ina matukar tausayinsa" Tasmia ta kwantar da Emily jikinta tana hawaye. "Ki yi hakuri Emily amman na tausaya miki" Sai da ta yi kukanta ta koshi sannan ta fada mata dalilinta na zuwa gidan a cikin daren. "Gaskiya ban san wani makabarta ta musulmai ba, ban san inda za a iya binne shi ba, kin ga ni ma bakuwa ce a garin, ban da gidan yar'uwa da kuma wata kawata ban san kowa a nan ba sai ke, ita kuma kawar tawa bata nan ma kuma ba zata yarda ba, yar'uwa ta ma bana saka ran haka, saboda ba jini daya muke ba, cousin dita ce, kuma kin ga a yanayinki nan ba kowa zai yarda danki musulmi ba ne" "Ni ina jin kamar be dace a rufe shi a makabarta da ba ta musulmi ba, domin na san ni kaina ba a daidai nake ba" "Toh yanzu ya zamu yi?" Emily ta share hawayenta. "Akwai wanda nake saka ran zai iya taimaka min amman yanzu ban san inda zan same shi ba, saboda dare ne ya bar gurin aikinsa kuma ban san gidansa ba" "Wanene?" "Mutumen da ya kawo ni dazun ogana ne a gurin aiki, kuma mun taba haduwa da shi tun da dadewa, yana da kirki da zuciya mai kyau wata kila zai iya taimaka min" "Aliyu..?" Emily ta kalleta "kin san shi?" "Ba wanda na tambayi me yayi miki ya min bakar magana ba?" "Eh" "Mijin kawata ne, na san gidansa amman da gaske ba wani abun yayi miki ba?" "Be min komai ba, tuna rayuwarta ta baya ne da kuma mutuwar da London zai yi, ya taba ni yasa na zama yadda kika gan ni, kina da number wayarsa?" "Aa ke baki da ita?" "Ban san inda wayata taka ba, ina zan same shi yanzu" "Muje na kai ki gidansa, daman kuma matarsa bata nan" Sai da ta mike tsaye sai kuma ta fara tunanin inda za su samu abun hawa. "Amman anya zamu samu abun hawa yanzu?" "Ina motarki?" "Ba motata bace ta yar'uwa tace nake karbowa ina zuba mai sai na yi yawo da ita, amman muje wata kila ba zamu rasa samun abun hawa ba" A tare suka fito Tasmia na sanye da abaya da mayafi Emily kuma da tufafin jiki, sun yi tafiya mai nisa sannan suka samu texi suka shiga, Tasmia ce ta yi jagora har suka isa kofar gidan. Emily zata bawa mai motar kudi Tasmia ta hana ta biya kudin motar sannan suka fara kwankwasa gate din gida. Mai gadin ya bude yana musu kallon rashin sani. "Mai gidan yana ciki?" Tasmia ta tambaya da turanci be amsa mata ba sai ya tambayi lafiya. "Ka fada masa Emily tana nan waje tana son magana da shi" Ya juya ya koma ciki, babu jimawa ya dawo ya bude musu gate din suka shiga, Tamia ta wuce gaba domin ita ta taba zuwa gidan sai da suka isa gurin kofar shiga sannan ta koma baya ta bar Emily a gaba, Emily ta tura kofar falon ta shiga Aliyu na tsaye sanye da jallabiya yana raga volume din wa'azin da African Tv suka saka, sannan ya juyo ya kalli kofar yana amsa sallamar da Tasmia ta yi domin Emily bata yi sallama ba ta shiga. Be gama mamakin zuwansu gidan cikin dare nan ba, yayi arba da Fuskar Emily da idonta da suka kumbura. A take zuciyarsa ta raya masa mutumen nan ne yayi mata duka wata kila saboda ya kaita gida. "Me ya same ki? Ko dukanki yayi?" "Danta ne ya mutu" Tasmia ta amsa masa sai yayi kalmar shahada ya zauna ya dafe kansa cike da tausayinta, yaron data gama bashi labarin wahalar da ta sha akansa shi ne kuma ya mutu a yanzu. "Mun zo nan ne saboda tana son ayi masa jina'iza irin ta musulunci, ni ma kuma bakuwa ce a garin nan ban san kowa ba amman ita tace...." Tasmia ta fada masa abun da yake tafe da su domin Emily bata komai sai hawaye. Aliyu ya sauke ajiyar zuciya. "Yaron yana ina yanzu?" Sai a nan Emily ta iya amsawa muryarta na rawa. "Yana can dakinsa yana gida" Aliyu ya dubeta duban da ya dauke shi tsawon dakika 120 yana kallonta. "Emily" Ta dago ta kalleshi ba tareda ta amsa ba, a zatonta zai ce mata ba zai samu damar aiwatar da kudirinta ba ne. "Mu a musulunci akwai shika shikan imani da akan gindawa kowane musulmi, ina kyautata zaton lokacin da kika musulunta an fada miki su? A ciki akwai imani da kaddara mai kyau da marar kyau, na san kin tsani musulmi kin tsani musulunci amman ni ina ji a jikina wannan imanin da kika yi da Allah har yanzu yana nan cikin zuciyarki, kuma ban kara tabbatar da hakan ba sai a yanzu, dan haka ki yi hakuri da wannan rashin Emily, kuma na jidadin shawarar da kika yanke na yi masa sutura irin ta musulunci, shi kanshi da ace zai dawo yanzu zai miki godiya na abun da kika yi masa, kuma ina tabbatar miki zan yi masa duk wani abu da ake yi ma musulmi In Shaa Allahu" Ta amsa masa da kai tana matse jikinta wani yanayi take ji marar dadi. Aliyu ya shiga dakinsa sai gashi ya sauko sanye da kananan kaya. "Zan tafi da mai gadi na mu dauko gawarsa, zan masa wanka a yau da duk abun da ya dace In Shaa Allahu, da safe sai ayi masa sallah a kai shi makwancinsa" Ta mike tsaye. "Idan ba mu je tare ba, ban san iya abun da zai faru tsakaninka da Vito ba idan ka tarar da shi a gidan ba" "Karki damu ina addu'a aljani ma be isa ya cutar sa ni ba sai da izinin Allah balle Vito" "Baka sanshi ba ne, baka san irin hadarin da yake da shi ba" Ta fada tana kuka. "Idan na je na tarar yana gidan ba zan dauko ba zan dawo sai mu tafi da ke" Sam bata yarda ba, saboda ta san Aliyu be san aikin Vito ba, kuma be san hatsarinsa ba. "Zamu tafi tare, mai gadin ma ba zai bari ka shiga ba" Aliyu ya kalli Tasmia. "Kin iya mota? Ko?" Ta daga mishi kai, sai ya shiga ya dauko makullin wata motar ya bata, shi kuma ya shiga motarsa tare da mai gadinsa, ya rigasu isa gidan amman ya tsaya har sai da Emily ta shiga ciki ta yi ma mai gadin magana sannan Aliyu ya shiga har dakin da London yake ya cire shi a cikin coffin ya saka bedsheet ya lullube shi ya fito da shi Chidimma na ta kallonsa Fatima kam ta dade da yin bachi a lokacin. A gidan suka dawo ya fada a musulumci idan mutum ya rasu ana masa wanka sannan ayi masa sutura ayi masa sallah. Tun a cikin daren Aliyu yayi masa wanka na aje gawarsa a wani dakin na dabam. Tasmia na zaune falo tare da Emily, Tamia ce kawai ta iya angaje Emily kam idonta biyu har safe. Misalin karfe shida da rabi Aliyu yayi waya da wani daga cikin yaran da yake sakawa aiki idan yana bukatar wani abu, suka kawo masa likkafani ya shirya London a ciki sannan ya sauko falon Emily na ta kallonsa ya ce. "Kina son ki ganshi?" Ta daga mishi kai. Sai Tasmia ta hana. "Ba lallai ne ta iya rike kanta ba" Aliyu ya kalli Emily. "Ba zaki ihu ba? Kin yi alkawari?" Ta daga mishi kai. "Shiga ki ganshi, kina da hakkin ganinsa ko a musulunci ana son iyalin mamaci su yi bankwana da shi" Tasmia ta ki shiga Emily kam ta taka ta isa har kofar dakin ta tura ta shiga. Ta hango shi kan tabarma an nade shi da zane ta cikin zanen kuma an masa sutura da farin kyalle wato likkafani. Ta karasa ta zauna kasa inda yake ta bude zagen ta bude likkafani har ta kai ga fuskarsa, tana ta kallonsa. "Mun wahala ni da kai, amman kai ka fini wahala saboda kai baka gane komai a cikin duniya, na dauki cikinka da yunwa da wahala na haife ka daker, kuma sai ka zo ba a lafiyayye ba, ammam a yau komai ya zama labari, rashin farinciki da samuwarka da mahaifinka be yi ba, rashin son sanin kana raye ko a mace yau duk ya zama tarihi, yau an rufe babin rayuwarka Ibraheem, ka tafi kana fushi da ni saboda cutar dake damunka bata barka ka fahimci ina kaunarka ba, kuma zan yi ta kewarka har karshen rayuwata" Ta kai bakinta ta sumbanci goshinsa hawayenta na sauka a fuskarsa. Sannan ta rufe masa fuska ta gyara komai kamar yadda ta tararda shi. Ta taso ya fito daga dakin Aliyu yana ta kallonta har ta iso gurin da yake tsaye, sai ya ji ta burgeshi, a iya saninsa wadanda ba musulmai ba idan aka musu mutuwa ihu suke suna faduwa suna tashi suna burgina da tambayar ubangijinsu Meyasa ya aikata hakan? Amman a gurinta ya ga banbancin haka. Misalin karfe tara yayi waya a gurin aikinsa duk wanda yake musulmi ya saka aka dauko shi aka kawo shi gidansa wasu suka suka zo da kansu, Emily tana tsaye jikin window falon Kameela tana kallo suka yi sahu Aliyu yayi jagoranci yi masa sallah sannan suka dauki gawar yaron suka fita da shi. Ta zauna a falon shiruuuuu tana ta tunani kala kala, Tasmia ta kwantar da ita a kafadarta. Suna haka Aliyu ya dawo tare da mai gadinsa domin sauran mutane daga makabarta suka wuce gurin aiki. Da ya shigo sai ta tambaye shi nawa aka kashe mutanen da ya kira suka yi masa sallah da kuma tafiya kai gawar makabarta ma nawa aka kashe. Yayi murmushi yana kallonta. "Mu a musulunci idan aka yi ma gawa sallah kana da lada mai yawa balle kuma ace ka raka gawa zuwa gidanta na gaskiya, ladar suke kwadayi ba biya ake ba, abubuwan da aka siya kuma ni na dauke ladar" "Na yi zatona akan daidai, kai kadai ne namiji mutumen kirki musulmi, na gade Aliyu" "Ina rokon Allah yasa ki samu musulmai fiye da yadda kike kyautata min zato, Allah ya sanyaya zuciyarki Aisha" Tasmia ta amsa da Ameen tana jin dadin abun da Aliyu yayi har cikin ranta ta ji ya burgeta. Emily ta kalleta. "Ban takura ki ba idan na biki zuwa gidanki?" "Aa babu takura haba Emily ni da ke ai mun zama kawaye" Tasmia

Chapter 19 of 63