Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ne saboda gujewa Ummi ko Aliyu su fadawa Emily ko su shirya wani abun da zai zama laifi a gurin Turhan. Dan haka ya zabi shiru da bakinsa ba tare da ya fada musu dalilin dawowarsa ba. Mahaifin Aliyu ya sauka Kaduna on Saturday, Sarkin Sudan ya sauka Abuja on Saturday tare da Turhan da yan rakiyarsa masu fassara masa daga hausa ko turanci zuwa larabci, a gidan abokinsa Bulama, sun samu kyakkyawar tarba a daya daga cikin manyan masaukan baki da Bulama yake da su, abinci aka kawo musu kala kala tun daga kan na Nigeria har zuwa na kasar Sudan. The following day suka suka shiga private jet na Alhaji Bulama zuwa garin kaduna, Dr A-B be fadawa Emily za su zo ba, duk kuwa da kasancewar tana kiransa akai kai da sabon layinta da Mama Baraka ta bata. Sai yayi tunanin ko Mahaifin Aliyu ya sanar musu da zuwan, sai dai duk da haka be yi mata maganar ba saboda yana son ta ganshi as surprise kamar wacan karon. Even Mama Baraka bata san wainar da ake toyawa ba. Domin mijinta baya magana da ita, balle ya labarta mata cewar mai gidansa Alhaji Bulama zai sauka garin a ranar ta Lahadi ba, shi ne mutum na farko da ya fara isa filin jirgin ya tarbe bakin da aka sanar masa da zuwansu amman ba a fada masa dalili ba. Alhaji Bulama ya sanar masa ne saboda shi ne babban yaronsa kuma indai har za su sauka a garin Kaduna babu wanda yake tarbarsa kamar shi, balle kuma wannan da suke ganin ya alakantu da shi. Ya tarbosu tare da yi ma maigidansa tayin sauka a a gidansa ko masaukin baki, amman ba su amsa gayyatar ba domin uzurin da ya kawo su dabam. Hankali be tashi ba sai da ya ji ana zancen makiyinsa kuma surukinsa, suka dunguma gaba daya suka dauki hanyar gidan. Ba zai iya zare kansa yace ba zai je ba, saboda yana tare da mai gidansa, kuma siyasa ta gaji haka idan aka hadu a rumgume juna ana wasa da dariya kamar babu komai. Ba su fada dalilin tafiya gidan ba sai da suka kusa isa, be yi mamaki ba domin ya hararo haka ganin Turhan a karon farko da Alhaji Bulama ya gabatar masa da shi har yana fadar ga surukinka. EMILY POV. Tun a daren Assabar Daddy ya sanar da matarsa cewa yana da baki gobe ta shirya abinci mai kyau da wuri, duk yadda Ummi ta so ta ji ko su waye be bata dama ba sai kawai ya fake da cewar abokan siyasa ne. Sannan ya bukaci ta fadawa Aliyu kar ya shigo gidan gobe sai idan ya kira shi. "Bakin da za su zo suna da alaka da shi ne?" "Aa kin san ita harkar siyasa akan boye wasu abubuwan saboda gaba, shi Aliyu ba mutum ne mai son siyasa ba, to be kamata ace kowa ya san da shi ba, hakan kan iya haifar da matsala wani lokacin a cutar maka da naka" "Haka ne kuma, zan fada masa Allah ya kaimu lafiya." "Ameen Uwargida kuma Amarya" Daddy ya fada yana murmushin manyan mutane. "Ka ji da shi, idan ka tashi auro min yar yarinya dadin bakinka ba zai hana ba ai" "Ni yanzu ke ma ba hakuri kike da ni ba? Ina na ga lokacin kara miki wani aure? Wahalar ma ai sai ta yi min yawa" "Uhmm" Haka dai suka cigaba da hirarsu sama sama har kusan tara na dare, shigowar sirri Daddy yayi amman haka be hana makusantansa da masu saka idon unguwa su fahimci ya sauka garin ba domin dan siyasa ba a boye yake ba, A ranar be kwana ba da ya sallami kowa da abun da ya kamata. Da Aliyu ya zo yi ma Daddy sallama Ummi take fada masa gobe ya zauna ya huta kar ya shigo gidan sai an kira shi domin ba su san saukar yaushe baki za su yi da safe ko rana ko yamma. To him it's awkward and something new, why dan za ayi baki za ace kar ya shigo gidan? Be musa wa Ummi ba domin ta ba shi hujjojinta kamar yadda Daddy ya bata. Shi dai ya amsa musu ne kawai amman ba dan ya gamsu ba, da ya zafafa tunani sai ya fahimci Turhan ne zai ko ko mahaifinsa, a take jikinsa yayi sanyi wani bangare na zuciyarsa ya raya masa titsiye Emily za su yi, su cilasta mata abun da ba shi take da niya ba, wannan bangaren da ya raya masa haka shi ya sake raya masa kowa baya wuce kaddararsa kuma be zama lallai idan ta koma gidan Turhan ya sake cutar da ita ba a yanzu domin ga dukan alama yayi nadama kuma ya fahimci tana da tsada. Haka ya fito bangaren na mahaifinsa yana ta sake sake har ya nufi motarsa sai kuma ya juyo ya sake turo kofar falon ta Ummi ya shiga. Nafeesa da Emily ne zaune a falon sai masu aikin Ummi dake zaune kasa. Tun da ya shigo Emily take kallonsa har ya nufi dinning ya dauki cup ya fara auna madara yana zubawa, ba dan ya sha ba sai dan ya saci kallon Emily din, jin yake yana kewarta fiye da ko yaushe, ya san ba zata iya kaunarta a zuciyarta amman idan aka mata dole ba lallai ta tsallake wannan ba, ya gama satar kallon nata sai ya maida madarar a mazubinta ya fice yana bata wani silent look tana karba cike da kauna. Washe gari da wuri Ummi ta hau aiki tare da masu tayata, innocent her bata fahimci komai ba, har suka kammala hada komai ta shiga ta shirya kowa ya shirya. Emily na ta bude ido ta ga Aliyu ya shigo gidan da safe bata ga ya zo ba, bayan su gama aikin ta ji ba zata iya hakura ba sai ta aika masa da sakon kar ta kwana. "Yau lafiya baka shigo ba?" In few seconds ya maida mata amsa. "Wani uzurin ne ya rike ni?" "Akwai uzurin da ya fi ganina muhimmanci ne? Wuni yau zai min babu dadi" "Ke kenan, balle kuma ni da nake jin awanin da nake a gidan a kullum suna min kadan, Ayusher i miss you more life itself, zan zo soon" Ta aika amsa da sakon Heart emoji ya maido mata smiley face emoji. After like one hours suka ji shigowar motoci a gidan. Emily tana dakinta tana lasa waya, Ummi kuma ta fita tare da Daddy cikin lullubinta domin tarbon bakin da yace mata za su zo. Ganin Turhan da mahaifinsa ya matukar ba ma Ummi mamaki ga kuma Mahaifin kameela a tare da su, sai dai bata yarda ta nuna ba, aka shigo da su babban Falon Daddy ana musu sannu da zuwa. Masu aiki suka shiga jera musu abun da aka shirya musu. Tambayayi suka cika cikin Ummi sai a yanzu ta fahimci dalilin Daddy na hana Aliyu zuwa gidan a yau. Alhaji Bulama da Dr A-B ne kadai sukq sha ruwan da aka jera, Turhan da mahaifinsa ba su taba komai ba daman sarakuna ba ko'ina suke ci ko sha abu ba, balle kuma Mahaifin Kameela, da yaken dole na kawai yake. Turhan na zaune shiru zuciyarsa na raya masa nasara da rashinta. "ina ganin kamata yayi mu yi abun da ya kawo mu? Domin ni yau zan bar garin nan, kasan yadda abubuwan suke ba koda yaushe muke samu lokaci ba, amman abun da yake da muhimmanci kamar na abokina kuma abokin kasuwancina dole na bashi time dina" "Haka ne ranka ya dade, da na so ku fara cin abinci, amman bari a kira yarinyar" Ummi ta yunkura zata tashi Daddy ya hana ta, dugun kar ta tafi ta yi ma ɗanta kamfai, ya daga wayarsa ya kira Nafeesa ya ce ta shigo masa da Emily. Emily na zaune dakinta Nafeesa ta shigo ta ce ta saka Hijab dinta ta fito Daddy yana nemanta. "Lafiya?" Emily ta tambaya domin tun da ya zo ta je ta gaishe shi bata sake shiga bangaren ba. "Wallahi ban sani ba, amman dai na san lafiya kam In Shaa Allahu" Emily ta dauki bakin mayafin abayar dake jikinta ta rufe kanta ta saka talkaminta sannan suka fita tare da Nafeesa, suna tafe gabanta na faduwa musamman da suka doshi falon, tsayawa ta yi cak cike da faragaba kamar tace ba zata shiga ba, ganin haka ya saka Nafeesa ta kama hannunta suka shiga cikin falo, Emily kanta na kasa har ta zauna inda Daddy ya nuna ma Nafeesa. Sannan yayi ma Nafeesa alama da ta tashi ta fita, Emily ta dan dago kai kadan ta kalli mutanen da suka falon gabanta ya buga da karfi, ba dan arba da Turhan kadai ba har dan ganin mahaifinsa da kuma Alhaji Bulama ga kuma mahaifin Kameela a falon. Daddy ya gabatar mata da kowa daya bayan daya, sannan ya fada mata dalilin zuwansu neman gafararta ne na abubuwan da suka faru. "Dukanmu nan har ni mu zauna ne saboda neman yafiyarki ga dan mu, yayi kuskure mun sani kuma yayi nadama shiyasa takanas ta Kano ya dauko mahaifinsa da abokan mahaifansa da ni kaina da yake jin zan iya shige masa gaba mu roka masa yafiyarki, kuma muna fatan za ki dube mu da hurhurar dake kan mu ki yafe masa" Emily ta yi shiru na tsawon lokaci. "Ki bude baki ki yi magana muna saurarenki, kuma ba wai muna cilasta ki ba ne, kuma ba muna son ki ga kamar mun tsareki ba ne, aa yafiyace muke nema ga Turhan kowa yana kuskure abu ne da kika sani, kowa ya sani" Cewar Alhaji Bulama. Emily ta dago kai a hankali ta fara magana ba tare da ta kalli kowa ba. "Na yi tunanin mun wuce wannan gabar, tun kamin na yi magana da shi, na yi da Ammy kuma na fada na yafe masa, gaba daya ni na zubar da abun da ya faru, yanzu ai wata rayuwa muke yi bata baya ba, kuma Turhan uba ne ga Fatima ya cancanci girmamawa ta da yafiya, har a gurin Allah ni na yafe masa" "Maa Shaa Allah" Haka kowa ke fadi fuska a sake cike da far'a. Mai Martaba da kansa ya soma magana ana fassara mata. "Na jidadi da jin wannan maganar, kuma na yaba da hankalin ki da tarbiyarki, a rayuwa ana son mutum ya zama mai yafiya, kuma kin nuna mana ke mai hankali ce ba ki watsa mana kasa a ido ba, mun gode sosai, akwai tsaraba da muka so miki da ita fatan ba zaki raina ba" Mai fassarar na rufe baki aka shigo da manyan akwatuna biyu aka aje a gefen da Emily take zaune. "Sai dai kuma ba yafiya kawai na zo nemawa ɗana ba, ko da yake tafiyar daya ce ai, amman dai haka ba zai hana mu fada ba, Emily muna rokon alfarma, ki duba yadda muka zo nan dukanmu kuma da irin yadda yayi nadama yake ta kai da kawo akanki, kuma ki duba yarki da zuri'ar da za ku samu nan gaba, indai har da gaske kin yafe masa kuma kin manta komai toh ki amince ki koma karkashin kulawarsa da igiyar aurensa, kusan shi ne makasudi zuwanmu a nan" Ummi ta ji abun kamar daga sama, amman babu damar magana saboda Daddy yana gurin zaune, dan haka ta mike tsaye kawai ta fice daga falon. Daddy be wani yi mamaki sosai ba saboda ya hango hakan tun farkon zuwansu gidan. Emily ta kalli Alhaji Bulama wanda shi ne yayi maganar sai ta ji nauyi ba shi amsa. Dr A-B ya ciro daurin dollars a aljihunsa ya aje kasa. "Zan fi kowa farinciki idan ta amince, kuma ace ni na biya sadakin kanwar nan tawa" Emily ta sake daga kai cikin tsananin damuwa. "Dan Allah ku gafarce ni, kuma ku fahimce ni, bana nufin bata ran kowa, bana nufin zubar da kimar kowa, na yafewa Turhan amman hakan baya nufin na yarda na aure shi, Wallahi ba zan iya zaman aure da shi ba, akwai wanda na so" "Wake kike so?" Alhaji Bulama ya tambaya, sai ta yi shiru. "Ki bude baki ki amsa mana, ko a addinin musulunci bazawara amsawarta ake amfani ba shirunta ba, shiru na budurwa ne, haka Annabi S. A. W ya fada" Daddy ya ji kamar yace kar ta fada. "Aliyu..." Ta furta a hankali, falon yayi tsit na tsawon lokaci, kamar babu wani abu mai rai a ciki, tsabar jin nauyi Daddy ya ji kamar kasa ta tsage ya shige ciki. Turhan ya mike tsaye ya fice falon ba tare da ya kalli inda Emily take ba zaune ba. Sarkin Sudan ya tsare ta da ido. "Kin san mutanen da suke zaune a gabanki kuwa yarinya?" Emily ta fashe da kuka ita kanta bata nufin watsa musu kasa a ido. "Ku gafarce ni dan Allah? Ku fahimce ni ku taimaki rayuwata, ku bar ni ni ma na yaki iskar yanci" Sarkin ya mike tsaye bayan an fassara masa abun da ta fada ya fice tare masu rakiyarsa. "Amman baki yi kyauta ba, kuma ba mu tsammaci haka ba" Cewar Alhaji Bulama sannan ya mike tsaye ya fice, tare da rakiyar Mahaifin Kameela. Dr A-B ya kalli Emily dake ta kuka ya sakar mata murmushi. "Aliyu kike so?" Ta daga mishi kai. "Share hawayenki na miki alkawari ba zan bar garin nan ba sai an daura aurenku, ni ma kamar uba ne a gurinki ai zan iya bada aurenki, na nufin biyan sadaki ba zan fasa ba" Ya juya ya kalli Daddy ya tura masa kudin. "A rike wannan a matsayin sadakin Emily, a sanarwa duk wanda ya kamata a sanarwa, zan tafi na dawo daga can zan sanar da Madam Baraka, anjima kadan zan dawo za a daura aurenta da wanda take so, ni dai burina ta kasance cikin farin ciki, amman a tabbatar da shi ma yana sonta gudun abun da zai je ya dawo kar ya cutar mana da ita" Ya tashi shi ma ya fice, Daddy ma mikewa yayi tsaye ba farinciki ba bakinciki domin shi ma be ga dalilin da zai saka ayi ma Emily dole ga abun da bata so ba. Emily kadai aka bari a falon tana rusar kuka, bata sani ba ko shi ma Aliyun ya juya mata bayan ta watsa ma manyan mutane kasa a ido. Ummi ce ta shigo da kanta ta kama Emily ta fita da ita bayan Daddy ya fada mata abun da ya faru. Daddy ya sanar duk wanda ya kamata ya sani cikin kankanen lokaci, Dr A-B ya tafi kai tsaye yayi magana da Madam Baraka ya fada mata abun da ya faru, sai ta daga waya ta kira Emily ta sake tambayarta da gaske Aliyu take so Emily ta amsa mata da eh. Kamin a daura auren sai da Daddy ya jira Aliyu ya tambaye shi ko yana son Emily. "Eh ina sonta Daddy?" Ya amsa kai tsaye babu boye boye babu kwankwanto, gabansa sai faduwa yake ba kamar ya san wainar da ake toyawa. "Tohm za a a daura aurenku, daga baya abubuwa za su biyo baya" "Na gode Daddy Allah ya ba ni ikon sauke nauyin da za a dora min" Daddy ya kashe wayar ba tare da ya sake cewa komai ba. Sannan ya sanar da Ummi yadda suka yi, Ummi ta shigo ta ta sanar da Emily halin da ake ciki yan'uwan Daddy da nata duk sun hallara gidan. "Anjima idan an fito sallah La'asar za a daura aurenku da wanda kike so Aisha" Emily ta kalli Ummi tana kuka. "Allah kasa ya rike ni amana..." Ummi ta kama hannayen Emily tana hawaye. "Wallahi ko ba ni da rai Aliyu ya ci amanarki, ban yafe masa ba..." Emily ta kwantar da kanta jikin Ummi, Ummi ta rungumeta tana amsa sallamar Mama Baraka. [8/21, 10:14 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 7️⃣0️⃣ 🌟✨ TALIYAR HAUSA – YAR MURJI ✨🌟 🥘 “Abinci na gargajiya, ɗanɗano na musamman, jin daɗin iyali!” 🥘 Idan kina/kanason abinci mai ɗanɗano na musamman wanda zai tunatar da kai daɗin gargajiya, to babu kamar Taliyar Hausa – Yar Murji! Wannan taliya ba wai kawai abinci bace, al’ada ce mai haɗa iyali, ƙauna da jin daɗi a teburin gida. ✨ Me yasa za ka zaɓi Taliyar Hausa – Yar Murji? • ✅ An yi ta da tsafta da inganci • ✅ Ta dace da kowanne irin miya: miya mai ƙwai, miya taushe, ko miya mai ƙyauƙyau • ✅ Sauƙin dafawa – cikin mintuna ka samu abinci mai gamsarwa • ✅ Lafiyayye, mai sauƙin narkewa, kuma ya dace ga kowa cikin gida • ✅ Za ka iya amfani da ita wajen girki na yau da kullum ko kuma na musamman 📍 Muna a Kaduna – amma ɗanɗanonmu ya zarce iyaka! 🚚 Ana kawo muku duk inda kuke a Najeriya (delivery guaranteed). 💛 Idan kana son jin daɗin abinci na gida wanda ke haɗa zuciya da iyali, to ka gwada Taliyar Hausa – Yar Murji yau! 📞 wa.me/+2347071821482 tuntube mu yanzu domin yin odar ku. 👉 Ka more ɗanɗanon gargajiya mai tsafta, mai daɗi, mai ɗorewa! _________ Karfe 4:30pm aka daura auren Aliyu da Aisha, bayan sauke sallah farilla ta La'asar. Daddy da yan'uwansa suna gurin, yan'uwan Ummi ma wasu daga ciki suna gurin. Dr A-B ne ya bada auren Daddy da kansa ya karbawa dansa auren Emily, masu shaidu suka shaida aka yi addu'a sannan masu tafiya suka tafi, Daddy da Dr A-B suka nufo cikin gidan da ragowar goro da dabino. Daddy ya nufi bangarensa Dr A-B kuma ya shiga falon Ummi ya tambaya ina Aliyu yake. "Baya gidan, amman yanzu zan kira shi ya zo" "Emily fa?" "Tana sama, Nafeesa tashi ki kai shi" Ummi ta umarce ta, Nafeesa ta mike tsaye ta wuce gaba Dr A-B na bayanta har suka shiga cikin dakin da Emily take zaune tare da Mama Baraka. Nafeesa ta juya ta fice, Dr A-B ya zauna kusa da Emily sai ta dube shi idonta a kumbure ta yi kuka sosai har ta gode Allah. "An daura aurenki da wanda kike so yau, ina miki addu'ar Allah ya ba ku zaman lafiya, kuma ya saka mutuwa ce za ta raba" Ta kara matsawa kusa da shi ta rumgume shi tana jin sanyi. "Na gode, wannan karo na farko da jinina ya bada aurena..." Ta furta murya na rawa tana kuka, ita kadai ta san me take ji, tana son Aliyu kuma tana tsaron abun da gaba zata haifar, gashi ta watsa kasa a idon manyan mutane babu wanda ya fahimce ta, shi kansa Dr A-B ganin take yayi mata abun da take so ne kawai ba dan ya gamsu da zabinta ba. Ta dago kanta amman ta kasa kallon kowa. "Allah ya ba ku zama lafiya" Cewar Mama Baraka tana share hawayenta. Sun kusa rabin awa a dakin har aka fara kiran Dr A-B saboda Alhaji Bulama zai bar gari kuma tare za su tafi. Ya mike tsaye kenan sai ga Aliyu ya turo kofar dakin ya shigo da sallama duk suka amsa masa ban da Emily da kanta yake kasa, tana ta lissafin rayuwa. Idan Aliyu ya juya mata baya shi kan ita kam ta gama rayuwa kuma makiya za su mata dariya. Dr A-B ya kama hannun Emily ya mikar da ita tsaye ya kama hannunta ya kama hannun Aliyu ya saka hannunta cikin na Aliyu. "Ga amana an baka, ta wahala ka sani, muna fatan daga kanka ta dace, a gaban iyayenmu ta zabe ka ta bar wanda shi ya so ya aureta a yau, dan Allah karka bata kunya. Sannan zan tunatar maka a yanzu Emily tana da uwa, dan'uwa da kuma uban da zata sani nan gaba kadan, karka kuskura ka ce zaka taba ta. Ta fada kai take so kuma na tsaya har yanzu ne saboda na tabbatar da cikar burinta, na sauke nawa nauyin, ni zan tafi ina muku addu'ar Allah ya baku zaman lafiya na bar ku lafiya" Ya dauke hannunsa daga kan na su ya nufi kofa ya fice daga dakin, Mama Baraka ta mike tsaye ta bi bayansa. Aliyu ya kama hannaye Emily duka biyu ya rike yana kallon yadda take hawaye. "Na san nisar tafiyar da kika yi, a hanya kin taka kaya, kin tsallake rame, kin yi dingishi kin karaya, na san zafin wutar data kona ki, na san buri da mafarkinki, ka karanci zuciyarki na san kudurinki, kin yi rayuwar kadaici. A yau ni da ke mun zama iyali, zan zame miki mijin da baki taba tsammanin samu ba, zan cika duniyarki da farinciki har sai kin manta da damuwarki, kuka ya kare hawaye, ba zaki sake zubar da hawaye akan ɗa namiji ba, fargaba ba zata sake kusantarki ba, kin zama jinina, farincikina, kaunarki ce rayuwarta, ina mai tabbatar miki baki yi kuskuren zabe ba" Ya sake hannunta ya matsa baya kadan ya zube kasan guiwoyinsa ya hade hayyansa. "Na gode da kika yarda da cewar zan iya! Na gode da kika ba ni wannan damar, na gode da kika yarda a dora min wannan nauyin na gode da kika yarda na zama silar warakar duk wani ciwo naki, na gode da kika so ni, na gode da kika aminta da ni, na gode da kika aure ni, na gode Saruniyar mata, mace mai hakuri da kyakkyawar zuciya, na gode Ayusher na gode... Na gode... Na gode na gode..." Ta kasa komai wasu hawaye na dabam suna sauko mata, sai ta lumshe ido tana maida numfashi. Aliyu ya mike tsaye ya matsa daf da ita har yana jin fitar numfashinta. "Bude idonki ki kalli mijinki, mijin da be san komai sai ƙaunarki, mijin da samunki ya zama babbar kyauta da rahama a gareshi" Ta bude idon ta kalleshi ido cikin ido daf da daf gab da gab das da das... "Ayusher ina ƙaunarki, ke tawa ce ni ne ABOKIN RAYUWARKI" Ya rada mata cikin wata murya da be san yana da ita ba, furucin yana fitowa ne har can kasan kasan kogon zuciyarsa. Ya kai bakinsa ya sumbanci goshinta. Sannan ya ware hannayenta. "Ina tsarin Allah daga shedan la'ananen, duk wani abun kin, ko na cutarwa da zai shiga tsakanina dake, ina neman tsari Allah daga duk wani abun da zai saka na bata miki rai, kuma ina rokon duk wani alheri da zai kara mana zaman lafiya da kaunarnan junanmu, ina neman rahamar Allah a duk inda za mu saka gaba, ina neman rahama daga Ubangijin da shi ya hada mu, ya kawo mu a nan kuma ya nuna mana wannan ranar mai muhimmanci a rayuwarmu, Allah na gode da wannan kyauta da ka yi mini, da sunan Allah mai rahama mai jinkai" Ya rumgumeta halal hug ya saka a kirjinsa, wani irin rumguma yayi mata sosai kamar za a kwace masa ita, ya yi squeezing dinta har sai da abayar dake jikinta ta dage, yayi sama da ita kafafuwanta suka dage. Emily ta yi shiru..... Hawayen suka yanke mata, numfashinta na fita a hankali yana shiga da kamshin turaren jikin mijinta, ba a taba rumgumarta ta ji damuwarta da fargaba sun gushe mata ba sai a yau. Babu wanda ya taba rumgumarta ta ji hankalinta ya kwanta ya samu sukuni ba irin Aliyu. Yanzu ta san me ta rasa, sai a yanzu ta san what truly halal hug means, ka so a so ka so na hakika dabam yake, auren wanda yake kaunarka kaunar ta gaskiya ta hakika a dabam take, son wanda yake sonka so na hakika dabam yake, lallai akwai wata irin rahama da farinciki, jindadi da cikar buri a auren soyayya. Ranar yau kadai ya nuna mata tana da muhimmanci, wunin yau kadai ya shafe duk wani fargaba da take, ta share duk wata damuwa da ta fuskanta. Lallai macen da miji yake so Sarauniya ce, a yau Aliyu ya furta mata kalaman da babu wanda ya taba yi mata su a ranar aurenta, shi da kanshi yake gode mata, a yau ta shaida soyayyar gaskiya marar algussu. Aliyu be kalleta a matsayin mace da ta taba aure biyu ba, be kalleta a matsayin ta haihuwa biyu ba, ya kalleta a matsayin macen da yake so, lallai mai son be ganin ramarka,

Chapter 56 of 63