Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yanzu shi ne silar komai, ba dan haka ba da duk abubuwan da suka faru ta san Aliyu zai iya yafe mata su zauna domin tana son mijinta, amman yadda Ummi ta dauki zafi ta san zata sha wahala kamin ta samu kanta. Balle kuma Emily tana gidan ta dauke masa hankali da kyaunta ta san ba zai tsaya tunaninta ba, daman tun farko kyaun ne ya dauki hankalinsa ba komai ba. "Ni ban san ma san miyasa wannan Mama Baraka ta hadu da bature ba har aka haifo wannan yarinyar, kuma abu ya zo ya zama kamar na gida ni na shiga uku, shiyasa na ki ya rabu da ita, ashe ita wannan Mama Barkatar tana nan tana shirya masa soyayyar Emily ni aka maida mahaukaci" Ta kwanta ta tashi ta rasa ma wane irin tunani zata yi, kuma ta san idan ta yi sake bata hankara ba zata ji an daura musu aure domin ba a banza aka bar mijinta ba, kamar yadda aka yi ma Babansu. Ta zauna tana ta cizon baki, babu wanda ta fado mata a rai a yanzu kamar Tasmia zuciyarta ta raya mata babu inda zata samu mafita sai a gurinta. Ta janyo wayarta ta duba sai ta tuna bata da number Tasmia ta goge tun a wacan lokacin da suka samu matsala. Sai dai abu mai sauki ta can gidansu, bata da tabbacin zata iya samunta a gidan amman saboda neman mafita ta dauki key din sabuwar motar da Momynta ta siya mata ya fita ba tare da sanin kowa ba ta dauki kafa zuwa gidansu Tasmia. Ta isa gidan tana ta sake sake kuma tana dan jin kunya da nauyin Tasmia na abun da ya faru tsakaninsu, be ma kamata ace ta je neman taimakon Tasmia ba amman saboda bata da wata mafita sai wannan ya saka ta aje komai a gefe ta faka harabar gidan na masu rufin asibiti bayan mai gadi ya bude mata gate. Ta rufe motarta ta nufi cikin gidan tana rike da key ta a hannu da green din hijab dinta idan ka ganta ba saka yi zaton zata yi fitina ba. Ta shiga da sallama a tsakar gidansu Tasmia jikokin da suka nan suka amsa mata suna wasa da ruwa. Su ta tambaya ko tasmiya na ciki suka ce mata tana cik sai ta nufi kofar falon ta shiga da sallama. Suka amsa mata da mamaki domin Tasmia ta fada musu sun samu matsala da Kameela sai dai bata labarta musu gaskiya maganar ba kawai ta ce saboda Kameela tana da zafin kishi ne. Mamasu ta amsa mata da far'a kanen kam sai kallonta suke. Ta kai har kasa ta gaishe da mamansu sannan ta tambaya Tasmia ko tana ciki, maman ta tambaya ko lafiya ta amsa da babu komai tana dariya. Sai aka nuna mata dakin da Tasmia take, ta nufi dakin ta shiga da sallama tana yaye labule. Ita kanta Tasmia ta yi mamakin ganinta har tana tsoro domin bata san da me ta zo mata ba. "Yan bautar kasa wato kun gama babu ko labari babu ziyara?" "Ke da wacce kika zo? Ni da ke fa kai ta san kar ne" Tasmia ta fada sannan ta tashi zaune da kyau kar a shammace ta. Kameela ta tabe baki. "Ni da alheri na zo miki, ba sheri ba" "Koma da wacce kika zo ni daidai nake da ke" Kameela ta zauna ba tare da an mata tayin zaman ba. "Ke dan Allah ki bar abin da ya wuce ya wuce mana, ni ma yanzu ina cikin tawa matsalar mafita nake nema shiyasa na rugo a guje na zo gurinki" Tasmia dai kallonta kawai take. "Dan Allah ki ba ni aron hankalinki kuma ki natsu sannan kuma ki fahimce ne" "Ina jinki" Kameela ta yi shiru na lokaci can kuma sai ta ce. "Emily ce matsalar, amman ba zan fada miki komai ba sai idan zaki taimaki kanki ki taimake ni" "Zan taimake ki ba tare da sanin me ya kawo ki? Hajiya ki fada min damuwarki kawai ba wani noke noke" Kameela ta rage murya ta marairaice ta fara karanta mata damuwarta sannan ta koro da labarin Emily. Tasmia dai sai saurarenta take har ta kai aya. Kameela ta juya makullin motar dake hannunta tana kallon Tasmiya bayan ta gama bata duk labarin Emily da kuma abun da ya faru. "Tohm yanzu ni miye nawa a ciki? Har kike ba ni wannan labarin?" "Tasmiya aurena fa ya mutu?" "Na san aurenki ya mutu mana, abun duniya ai baya boyuwa na ji tun kamin na dawo garin nan kuma yanzu gashi kin kara fada min, dalilin da zai kawo ni cikin matsalar ne ban sani ba" "So nake ki taimaka min, ni biyanki ne ma zan yi Wallahi, na san da can kina son Aliyu ai ki yi duk yadda zaki iya ki dauke hankalinsa daga gurin kafirar nan, ni da ta aure shi Wallahi gara ke ki aure shi" Tasmia ta yi dariya "Wato Kameela kin dauke ni marar hankali marar wayo ko? Ke ce mai wayo? Bayan duk abubuwan da suka faru yanzu ni kike son na zame miki tsanin hawa? Miyasa ke ba zaki yi yakin da kanki ba?" "ba zaki gane ba ne, gaba daya baya saurare ni yanzu ya juya min baya kamar ba Aliyuna ba, daukar yarinyar da na yi na kaita gurin Turhan har Aliyu ya sake ni ni sai nake ganin kamar ba banza aka bar ni ba, Wallahi idan Aliyu ya auri kafirar nan an gama da ni gaba daya, uwarta ta yi kishi da uwata ni kuma na yi kishi da ita? Da dai ita ta aure shi kara ke" Tasmia ta tabe baki. "Ni yanzu ina da wanda zan aura masa Kameela, kuma mijinki mai wuyar sha'ani da shegen wayon tsiya" "Ai mataki zamu dauka ko ta halin yaya, idan kika ba ni hadin kai ma har acit sai mu watsa mata fuskar ta lalace daman ai kyau ne yake jansa" Tasmia ta yi murmushi a nan ta gane Kameela so take ta jefata a matsala. "Ki yi kishi da ita taya? Ai ke ba Aliyu kike aure ba, kuma tun da kika ga ya sake ki saboda ita ya nuna miki ta fiki muhimmanci kenan, haka ya buga min warning lokacin da muke can fa saboda ita, kin san mijinki dan duniya ne duk inda aka juya sai ya gane mutum, dama kin hakura domin yadda kika cika idda abu ne mai wahala ya maida ke, balle kuma kin ce har mahaifiyarsa bata sonki a yanzu, yo daman Kameela uban waye zai so ki? Kin ga yanzu ni dake ai mun zama daya, wai ke uwar gori kin ce ban da aure ko? To yanzu ni da ke waye shegen? Ni Wallahi Emily ma tausayi ta ba ni da kika ba ni labarinta, daman tun da na ganta ganin farko na fahimci tana cikin damuwa, kuma na kulla abota da ita, sai gashi son zuciya ya dauke ni na so cutar da ita ashe da na shiga uku, ni yanzu na bibiye mijinki kamar wata karuwa? Ko an fada miki karuwanci naje can ba bautar kasa ba? Kuma ni yanzu na samu wanda zan aura, kuma idan ba ki bi a hankali ba duk abun da kika fada min sai na fadawa Emily da Aliyu" Kameela ta fusata. "Tasmia idan ke ba karuwa ba ce wacece ke? Dan ubanki nan kika bar garin nan kika tafi har Ph bautar kasa da kika je kuma kika kama hanyar gida baki zauna inda kowa ke zama ba, kika dinga bibiyar mijina wai saboda kin yi kwantain, yanzu saboda kin samu damata na zo har shegen gidanku neman shawara zaki fada min magana, kutumar ubanki Tasmia, idan kin fasa tausayin Emily ko fada mata abun da na fada Allah ya tsine miki albarka" Tasmia ta yi mata sowa da baki.... "Oohhhhhhhhh an dai ji kunya, ke da kika takama kin fi karfin mijinki yau ke ce namiji ya gagareki, kike raba ni saboda ki samu shiga, ke yanzu dan Allah baki ji haushin kanki ba ma? Kim san kina Aliyun uban waye ya saka ki hauka? Kanki farau kishi mahaukaciya yar marasa tarbiya.." "Ubanki ne shegiya mai warin talauci, kuma muna nan dake zaki gan ni da Aliyu, ni da shi mutu ka raba ne takalmin kaza dan ubaki Zubairu" Tasmia ta rufeta da duka suka fara kaiwa juna naushi sai da kanen Tasmia da mamansu ta shigo aka raba su. "Lafiya" "Mama ki bar ni na ci uban yarinyar can, ganin take saboda suna da kudi zata iya taka kowa? Muma na ao muna da rufin asiri yar iska, daman ina rike da ita a zuciyata, idan ba ke wawuya ba yaushe zaki yi fada ni kuma yanzu ki wanko kafa ki zo wai na taimaka miki ke dakikiya ko.? Kara da Aliyun ya sake ki ai, kuma da yardar Allah sai ya auri Emily ke kishiya uwarki kishiya" "Ke ce yar iska marar tarbiya, mai bibiyar mazajen mutane, ko yanzu wa san mijin wa kika kwato? Muna nan da ke Aliyu ba zai auri Kafira ba, haka kuma ba zai auri yar iska irinki ba" Mama ta rufe baki. "Aa ahhhhh kin ga wannan.... Amm... Kameela kike da suna ko? dan Allah kama hanya ki tafi bana son fitina, ba alfahari ba ni dai yarana ba su da abokin fada, kuma ba zan su ki yi abun da zai saka mu da ke mu yi ta nadama ba, dan Allah yafi kin ga karfi ma ba daya ba, daman tun farko na ganki na san ba lafiya ba" Ta dauki makullin ta dake can karshen kofa ta fice tana ya huci sai zagi take jefowa Tasmia idan ta yi yunkurin ramawa Allah Mamanta ta hana. Kameela ta fito rai a bace ta shiga motarta ta juya kamin mai gadin ya bude mata gate ya daga masa hankali da horn kamar zata tashi gidan. [8/8, 9:58โ€ฏPM] ๐—ž๐—ต๐—ฎ๐—ฑ๐—ฒ๐—ฒ๐—ท๐—ฎ ๐—–๐—ฎ๐—ป๐—ฑ๐˜†: *๐Ÿ’ ABOKIN RAYUWA ๐Ÿ’* *ยฉ Khadeeja Candy* Page 6๏ธโƒฃ5๏ธโƒฃ "Idan Hajiya Baraka ta yarda mun tafi dake kuma Ammy ta amince toh wannan makarantar ya kamata a sakata, daman ina jin ana fadar suna karatu sosai" Emily ta yi murmushi kadan. "Na manta ban tambaye ki ba, ko kina zuwa coci a lokacin da kike can? Kar ya zama mun tauye ki a nan ki kasa mana magana" Emily ta kalli Ummi ta mamaki. "Aa bana zuwa coci ko a can" "Okay, tohm yayi kyau, idan kin gama kallon sai ki shiga Kitchen ki wanke kayan da muka ci abinci da su, zan shiga na kwanta" Ummi ta mike tsaye ta nufi hanyar Stairs, Emily ta bita da kallo tana murmushi, sosai take jindadin yadda Ummi take daukarka kamar wata wanda ta dade a gidan ba bakuwa ba, akwai mai aiki da Ummi zata iya sakawa ta yi wanke amman ta zabi ta sakata haka ya faranta mata rai, haka take mata idan za a jera abinci ko a kwashe kayan ita da Nafeesa suke kwashe, su kai Kitchen. Ummi na haurawa sama Emily ta tashi ta shiga kitchen ta fara hada kayan ta daurayewa kamin ta saka kumfa. Tana tsaka da wanke wanken ta ji muryar Aliyu ya shigo falon da sallama, duk yadda take zumudi da marmarin ganinsa bata aje ta fita falon ba, har sai da ya leko Kitchen din yana zaton Ummi ce a ciki, don ya san halin Ummi ba girkin kowa take ci ba, haka kuma bata yarda kowa yayi ma mijinta girki ba sai ita. Ta juyo ta kalleshi suka hada ido, sai suka sakarwar juna silent smile mai laushi. "Barka da zuwa" "Barka da aiki" "Kusan sati baka zo gidan nan ba" "Kirgawa kike yi?" "Har da mintunan da dakikun na sani" Ta amsa a nutse cikin sanyi hali mai shiga rai. Ya fadada Murmushinsa. "Na dan tsaya na huta ne, kusan tun da kika bata ban samu wadataccen huta da bachi ba, shiyasa yanzu nake ranko, kuma akwai guraren da ya kamata na leka sai a yanzu nake samun dama, and you need space too, bana son wani bacin rai ya samu zuciyarki a yanzu" "A space? Space din da zai karantar da ni yadda kewarka take? Ya zabtar da idona da kaikayin ganinka? Nisanta kamar hukunta ni ne Aliyu" "Kina ta siye ni da kalamai, ala dole so kike na ji cewar ban kyauta ba" Ta wanke cup ta dauraye. "Da kalamai suna siye mutum, da ka dade da karbar kudina, ina fada maka abun da yake zahiri ne kuma nake ji, ba wai ina kokarin wuce gona da iri ba ne, ina jinka kamar wani ษ—an'uwana na jini" Ya hade yawu yadda take maganar softly and calmly ya saka kara jin tausayinta, a kokarinsa na canja maganar ya dauko wata maganar. "Har yanzu lokaci be yi ba da ya kamata ki fara rufe gashinki Emily? Shi ma fa ba muharramina ba ne" "Gashin?" "Uhmm..." "Ina jin sakewa idan ban saka dankwali ba saboda na saba" "Ni kuma zan fi sakewa idan kika saka" Ya cire black facing cap din dake kansw ya jefa mata ta chabe, ta saka a saka a kanta da ta juyo ta kalleshi sai da gabansa ya fadi saboda yadda ta yi maya kyau ga wani lafiyayyen murmushi dake fuskarta. Fa sauri ya dauke idonsa ya juya zai fita. "Aliyu zan iya samu ayi min welcome back din layina?" Ya juyo. "Yeah amman yanzu? Ba sai gaba ba?" "Saboda Vito ne..." Aliyu ya jingina da kofar dakin ya rungume hannayensa. "Vito... Ba wanda ya san inda yake for now, ya boya inda babu wanda ya sani, saboda an tattara duk wani laifi da ya kamata a tattara a kama shi da shi, tun daga kan abun da muke zaton yayi min da kuma sana'arsa, yanzu haka neman sa ake ruwa a jallo, shi ne dalilin daya saka Ummi bata son na koma aiki har sai an kama shi, kuma Daddy ya fada min ana yin duk abin da ya kamata" Fuskar Emily ta sauya. "Idan aka kamashi kashe shi za'ayi?" "Ko dai ba a kashe shi ba, to za a daure shi a gidan yare ne, ba kuma saboda ni kadai ba har saboda ke" "Idan kuma yace ya tuba fa?" "Irinsu suna da wuyar tuba Emily, kuma suna da wuyar sha'ani mai shaye shaye tunaninsa ba daya yake da na sauran mutane ba, haka kuma zuciyarsa bushewa take shiyasa suke aikata abubuwan da ba'ayi tsammani ba, and ke kika ba ni labarin yadda ya dauki rai ba a bakin komai ba" "Ya taimake ni sosai, shi ne mutumen da ya fara yarda zan iya kamin kowa, mutumen nan ya tsaya a tare da ni lokacin da ba ni da gata, shi ya inganta rayuwata ya ba ni gata, ya kula da yarana, idan ya ji ni a cikin damuwa komai yake zai bari ya zo gurina, ba zan so wani abu ya same shi sanadina ba, a yanzu ne da na samu mahaifiyata nake fahimtar kyautatawar da mutane suke min tana da girma" "Rayuwarsa a fili barazana ce ga rayuwata da kuma ta ki, ban sani ba amman na san ba lallai ya fahimci kyautata muke miki ba, zai iya cewa zai dauki mataki da zai iya illataki, don a yanzu zuciyarsa a rufe take kuma daman ya saba dukanki, sannan shi baya son ki zauna da kowa fa karki manta da wannan, kuma idan ya dawo kusa da ke kin san kudinsa, yana son ya aure ki, ke zaki iya aurensa? Bayan kuma ba son shi kike ba?" Ta girgiza kai. "Bana fatan sake komawa dakin soyayya na rufe wannan kofar, bana marmarin zaman aure da kowa, yadda na sami rayuwa a haka ta wadatar" Aliyu yayi shiru be ce komai komai ba, ita ma ta yi shiru ta cigaba da wanke wanke da take cikin rashin dadin rai har da hawaye. Ya juya ya fita ta nufi inda mahaifiyarsa take, ya kwankwasa kofar dakinta kusan sau uku sannan ya tura ya shiga, kwance ya same ta waya a kunnenta tana ta magana da waya Inlaw dinta gwaggon Aliyu. Sai da ta gama wayar sannan ta kalleshi. "Ai na dauka ka yafe mu" "Na isa ne? Na dan huta ne kuma kuma na ba ku dama ku huta, yanzu ma ba zuwan kaina ne ba, Mama Baraka ce ta ce tana son na taho mata da Emily" Ummi ta tashi zaune. "Nice ko jiya ta zo gidan nan kuma sun yi magana" "Toh wata kila tana son ita Emily din ta tafi gidanta ne" "A yadda na karanci yanayin Emilyn kamar bata marmarin zuwa gidan ne shiyasa ban matsa ba, kuma ni kaina ba son zuwanta nake gidan ba saboda Kameela, kasan yarinyar zafin kishinta ya wuce misali za su iya sanadin da za a karawa uwar sauran igiyar ma, da dai ace bata gidan ne zai fi kyau Emily ta tafi, kuma ko zata tafi ba kai zaka kaita ba, ita zata aiko a dauke ta ko kuma a saka direba ya kaita gidan daga nan" "Ta fada min ta shirya mata wani abun mamaki ne, kuma bata son abun ya wuce yau, ban san miye ba amman ya kamata ta tafi" "Sauka ka fada mata idan ta yarda direba zai kaita, kai kam baka da alaka da gidansu Kameela a yanzu dan haka bana son ganinka a gidan, ka bari sai idan Allah ya kaddara Hajiya Bakara ta zama Inlaw dinka wannan dole ka shiga gidan, amman ba yanzu ba" Aliyu yayi mata kallon rashin fahimta. "Ta ina zata zama Inlaw dita?" "Ta abin da kake karyatawa mana" "Babu abun da make karyatawa, Ummi ba abun da kike tunani ba ne, bayan haka kuma Emily fa tsohuwar matar Turhan ce? Ko mutuwa yayi ai idan nw auri matarsa ban kyauta ba, sai yace daman kudirina kenan shiyasa na aikata abun da yake zargina, alhalin har ga Allah ba dan na aikata hakan ba ne" "Saboda me? Haramun ne? Da ka yarda da abun da yake ranka da karka yarda alaka dai tsakaninka da Turhan da Ammy ta riga ta lalace, kuma ba zata taba gyaruwa ba har abada, ni kawai ina fada maka abun da yake gaskiya ne, ba saka ka zan yi na ba hana ka zan yi ba, ai lokaci alhali ne, kuma komai rufin da aka yi idan ta yi tsami dole sai ya fito, na mu ji ne kawai" Ya mike tsaye ya fice daga dakin yana murmushi don ya san duk yadda zai buga misali ko ya ayyana Ummi ba fahimtarshi zata yi ba, nata tunanin take dabam. Falon ya sake dawowa ya nufi Kitchen kamin ya shiga Emily ta fito tana rike da hullar da ya bata, kamar mai tsoro haka ya waiga ya kalli upstairs sannan ya mika mata hannu. "Zan iya samun hulata yanzu?" Ta karasa ta mika masa sai ya karba ya saka a kansa tana kamshin gashin Emily da ya sha gyara da mayuka da turare. "Mama Baraka ce ta kira waya wai tana son ki zo yau gidanta, kuma yanzu nan ma" Emily ta dan wara ido. "Jiya ai ta zo nan, shekaranjiya ma ta zo kamin shekaranjiya ma ta zo kullum tana zuwa" "Toh yau so take ki tafi, kin san daman na mata alkawarin zan kawo ki, amman dai na zan samu zuwa ba direba zai kaiki, ki shiga ki shirya yanzu?" "Ni bana marmarin tafiya gidan" "Haka zaki daure, umarni ne ai nake baki ba neman ra'ayinki ba I'm your boss" Ta bude ido sosai da mamakinta. "Ai ba a gurin aiki muke ba, a nan gida ne, baka isa kamin dole ba" Ya saka hannayensa alhaji duka biyu. "Really?" "Yeah..... Kuma gwada ka gani" Yayi murmushi kawai. "Kin san daman mun saba fada ko? So kike mu tuna baya kenan? Direba yana jiranki?" Ya fada yana nuna mata kofa da ido, sai ta nufi upstairs ta canja riga da skirt din dake jikinta zuwa gown din atamfa har lokacin kanta babu dankwali bata samu Aliyu a falon ba, kai tsaye ta nufi kofar fita ta bude ta fita sai ta hango shi tsaye jikin wata mota dake kunne, na yi kyau? Ta tambaya da motsin baki ba tare da ta fitar da sautin ba, sai ya girgiza mata kai alamar aa ya dauke idonsa tare da hade rai yadda ake yi ma yara, ta san ba zai wuce saboda bata saka dankwali ba sai ta yi murmushi ta karasa gurin motar daya bude mata ta shiga ta zauna tana ta kallon fuskarsa domin kallonsa na daga cikin abubuwan da take so, shi kuma be yarda ya sake hada ido da ita ba ya rufe motar ya juya ya nufi hanyar shiga Falon. Direban yaja motar suka fice daga gidan, tana zaune cikin motar shiru shiru sai kallon titi take, can kuma sai ta yi murmushi. "Aliyu" ta furta sunansa a hankalita kwanta jikin motar tana juya ido zuciyarta cike da nishadi, sai da direban ya shiga gidan sannan ta saita kanta tana kallon rayuwar baya da ta taba shigowa gidan, ta kai hannu zata bude Direban ya ce. "Hajiya dan jira, Alhaji Aliyu yace kar na bari ki fita motar sai matar ta fito, tun da ban san wane bangare take ba" Ya daga wayarsa ya kira Aliyu ya sanar masa suna cikin gidan. Babu jimawa Mama Baraka ta fito ta dayan bangaren da farinciki ta nufo motar da suke ta budewa Emily. Emily ta fito bata wani dauki sosai Mama Baraka ta rumgume ta tana jindadin zuwanta, sannan ta kama hannunta suka nufi bangaren da ta fito, da suka shiga gate din ta ratsa da ita suka shiga falonta, suna shiga falon Emily ta yi arba da Dr AB zaune sai ta saki hannun Mama Baraka ta nufi shi, shi mike tsaye da sauri yana murmushi suka rumgume juna. "Kina lafiya?" Ya tambaya bayan ya dago ta daga jikinsa, sai ta daga mishi kai. "Ina lafiya, yaushe ka zo ya aka yi ka zo nan?" "Saboda ke" Ya kama fuskarta ya rike. "Madam Baraka ta fada min komai, a washe garin da kuka bar gidan, kuma na jidadi da ya zama ina da alaka da ke" Hawaye ya sauko mata ta runtse ido tana jin wani sanyi na sanin cewar shi dan"uwanta ne kuma ya karbeta. "A yanzu na gane dalilin da yasa nake ta son kasancewa da ke Emily, kowace haduwa kaddara ce take shirya mana ita, amman na kasa cireki a raina na kasa manta duk wani abu daya shafe ki, ada ina tunanin kamar na samu mata ne, ban sani ba ashe ke jinina ce, tun dawowarki gidanku zuciyata ta fara raya min kamar kina da alaka da mahaifina saboda kamar da kike da shi ta yi yawa, amman sai na rika tambayar kaina ta ina? Taya yaya? Da kika ba mu labarin rayuwarki, sai na fara tunanin ko sace ki aka yi aka jefar a can? Ko kuma dai bayan Momy mahaifina ya zauna da wata matar? Ita kanta Momy ta fada min kina kama da Mahaifina" "Ina Momy take?" "Tana gida, ni na saboda ke na zo, kuma yau zan koma" "Ta samu labarin abun da ya faru?" "Eh sai dai bata yi maraba ba, bata shirya karbarki yanzun ba" Emily ta kalli Mama Baraka sannan ta kalli Dr AB "Tana da gaskiya, kuma be zama dole ta karbe ni ba, shi kanshi be zama lallai ya karbe ni ba idan ma yana raya" "Yana raye, na kan je na ganshi a duk lokacinda bukatar hakan ta taso, kuma shi mutum ne mai son yara zai yi farinciki dake na tabbata" Emily ta zauna. "Ina son na ganshi, kamanin da ake cewa ina yi da shi ina son na ga ya fuskata take a jikin wani" Dr A-B ya zauna kusa da ita ya ciro wayarsa ya kama hotonshi ya mika mata wayar. Yaran Mama Baraka duk suka fito suka zauna suna kallon Emily. [8/13, 10:39โ€ฏPM] ๐—ž๐—ต๐—ฎ๐—ฑ๐—ฒ๐—ฒ๐—ท๐—ฎ ๐—–๐—ฎ๐—ป๐—ฑ๐˜†: *๐Ÿ’ ABOKIN RAYUWA ๐Ÿ’* *ยฉ Khadeeja Candy* Page 6๏ธโƒฃ6๏ธโƒฃ Mama Baraka ta

Chapter 52 of 63