raine su ba tare da taimakon kowa ba, ni din na tashi a gidan marayun ne ban san uwa ko ubana ba, balle ayi zancen yan'uwa, bana da kawaye bana da kowa sai Vito da yarana, ni din wata ce da wani musulmi ya yaudara, mummunar kaddara ta yi min dabaibai hada ni da mutanen da bana kirki ba, a yanzu kuma ni christen ce mai alfahari da jindadin addininta, mai kokarin gina kanta da rayuwar yaranta, bayan wannan sai me kake son ka sani?”
“Ina son na san a lokacin da kika wanzu tsakanin rayuwa da mutuwa ne, ina son na san komai akanki, ta ina lamarin ya fara? Taya kika kawo har yanzu? Su waye suka munana rayuwarki, miye dalilin komawarki addinin Christianity? Su waye suka saka kika tsani musulmi da addinin musulunci? Miyasa baki son Fatima ta san tana da mahaifi? Wacece ke Emily? Na damu na na sani, kuma na damu da ke”
Taja numfashi tana karanta sakon hawaye na cika idonta, kai ta daga sama ta lumshe ido ta bude sannan ta maida idonta a kan wayar, tana kokarin rubuta masa amsa ta WhatsApp din Vito ya turo kofar dakin ya shigo, sai ta yi saurin saka wayar a lock ta dora ta a kan madubi.
“Miye hadinki da likitan da zo duba London da har zai baki card dinsa? Idan wani abun da ya shafi rashin lafiyarsa ne ai da ni zai yi magana”
Ta juyo idonta a kumbura ta kalleshi hawaye na sauko mata.
“Waya kalleki? Waya miki magana? Gurin wa kika je? Da wa kika waya? Me ye hadinki da wannan? Ina zaki je? Shi ne kawai abun da ka iya”
Ta matsa kusa da shi cikin ihu ta fara fashe mata kurcin dake mata ciwo a zuciya.
“Ni ba ni da ikon kaina, da wa zan yi mu'amala, su waye masu aikina da masu gadina, su waye makota na, a ina zan zauna, duk kai kake zaba min, ka hana in yi abota da kowa, ka hana na yi mu'alama da mutane kamar kowa, takamarka saboda ina zama a karkashinka ne, takamarka saboda ka tsamo ni daga rana zuwa inuwa ne, idan na yi magana sai kace kana so na ne? Taya ina aka soyayya da son kai? Miye banbancinka da sauran ne? Miye banbancinka da Khaleefa sa ya cusa yarda da soyayya a zuciyata ya aureni saboda kawai ya yaudare ni? Banbanta min banbancinka da Turhan mutumen da ya aureni saboda cika umarnin mahaifiyarsa ya maida ni kaskantacciya a cikin bayinsa, sai yaushe ni zan samu yancin kaina? Sai yaushe zan yi farinciki na har abada?”
Yin sa'insa da ita ba abu ne da ya saba yi ba, musamman idan ta ci galaba akansa da hawayenta, saboda haka ya zubar da makaman yakin da ya zo da su ya karasa gurin da take tsaye ya rumgume ta. Sai ta cigaba da zubar da hawayen da take.
“Ina tsananin sonki Emily, ban taba son wata mace ba sai ke, kina da kyaun da maza ba za su iya dauke miki ido ba, shiyasa zuciyata ta kasa natsuwa da wasu abubuwan, ina kokarin baki kariya ne, saboda ina jin cewar ke kadai ce mace a duniyar nan, bayan ke babu wata”
Ta daga kai tana kallonsa ta san yadda yake ji domin ta taba tsintar kanta a makamancin halin da yake ciki a yanzu, a lokacin da ta yi soyayya da Khaleefa bata ji bata ganin kowa sai shi. Ya sumbancin tsakanin girarta guda biyu sai ta lumshe ido tana tausayinsa da kuma kanta.
ALIYU POV.
Da abincin dake gabansa yayi feeding dinta daman ba wani son cin abincin yake ba a safiyar nan. Sai da suka gama sannan ya hada kayan ya dauka ya kai kitchen, kamar jira ake ya aje plates din sako ya shigo wayarsa kasancewar data sa kullum a bude take. Ciro wayar yai daga aljihunsa ya duba sakon da ya shigo yanzu. Sakon Emily ne da take gargadinsa tare da shimfida masa dokokinta. Bayan ya gama karantawa ya bata amsa, ta sake rubuto masa wani ya aika mata da tambayar abun da ya fi damunta, ta zayyana masa kadan daga sanin wacece ita, sai ya yi mata matashi da dalilinsa da kuma damuwarsa akanta.
Ya dauki dakiku yana jiran amsarta amman be samu hakan ba, maybe mata shiryawa hakan ba, ya raya a zuciyarsa, kamin ya ji takun tafiyar Kameela a bayansa, da sauri ya juyo sai yayi hanzarin saka wayar aljihunsa yana mata murmushi.
“Me kike bukata”
“Na ga ka dade a kitchen din ne, na dauka ko wanke wanke kake ma”
Ta fada da dan mamakinta na rashin yarda, mo matter how Aliyu zai mata rantsuwa, zuciyarta bata natsuwa saboda tsananin kishinta. Ya juya ya kalli kayan da ya aje sannan ya juyo ya kalleta.
“No, bari na je na yi wanka yau da wuri nake son tafiya aiki”
Kamin tace komai ya fice daga kitchen, ba dan komai ba sai dan gudun ta zargi wani abu, duk da haka kuma be tsira ba, domin hankalin matarsa be kwanta da yadda yayi sammakon fita dazun ba, da kuma yadda yake chat a kitchen dinta ba, ita dai ganin take sheidan zai iya zuga shi ya karya alkawarin da ya daukar mata. A take ta ji ta kwadaitu da son ganin chat dinsa, ta san mijinta ba zai mata karya ba, amman dai yadda mata suke ta zillo akan maza kamar za su aurar da kansu, ai wata zata iya tankwasashi ya fara halayen da ba nasa ba. Ita kam dai ba zata yarda mijinta ya lalace da kara aure ba, kara ta duba chat din ta ga koma miye ko hankalinta zai kwanta.
Falo ta dawo ta zauna tana ta sake sake kamin zuciyarta ta fi karfinta har ta tashi ta nufi dakinsa ta tura kofar dakin ta shiga, ko da ta shiga ta samu yana bandaki yana wanka, farkon abun da ta fara neman shi ne wayarsa ta wurga idonta a ko'ina na dakin bata ga wayar ba har sai da ta daga fillon da suke kwanciya. Sai ta samu wayarsa a kasan fillon ya kifeta hakan kuma ba karamin mamaki ya bata ba domin ba halinsa ba ne boye waya, wannan ya saka ta san password dinsa kuma take shiga ko'ina a cikin wayarsa tana masa bincika son ranta.
Zaunawa ta yi gefen gadon rike da wayar da bude password dinta ba zai mata wahala ba domin ta saba budewa, kai tsaye ta tafi messenges dinsa wato sakon kar ta kwana ta duba bata ga wani abun ba, ta fito ta shiga WhatsApp dinsa, bayan chat biyu da aka masa dayan na group dinsu na makaranta dayan kuma na abokinsa na ukun ne na Emily mai dauke da kyakkyawan hotonta. Kai tsaye ta tafi kan dp Emily tana kallon yadda Allah ya tsara kyakkyawar halittar kyaun a fuskarta, a take hankalinta ya tashi.
Sabon chat ne da aka yi shi da number ta da be yi saving ba, sai da ta karanta sakon da ta turo masa ta karanta wanda ya aika mata sannan ta sauko daga kan gadon ta zauna a kasa hannunta daya a kanta. Miyesa mijinta zai shimfidawa wata mace kalaman ya damu da ita yana son sanin rayuwarta har haka? Watan ma kuma kyakkyawar kamar Emily. Bata san lokacin da ta jefar da wayar ba ta kwala wani uban ihu zuciyarta da mararta suka hau murdawa lokaci daya.
”Wayyo Wayyo...wayyo... Zuciyata... Marata... Bayana... Na shiga uku zan mutu”
Aliyu be gama daure bathrobe din jikinsa ya fito da sauri daga bandakin cikin tashin hankali ya rikata.
“Meya faru?”
Ta rike mararta tana kallonsa son take ta yi kuka ko ta yi masa magana amman azabar ciwon marar da take ji ta hanata aikata hakan. Jini ya fara yi mata zuba da sauri Aliyu ya saketa ya saka tufafi ya saka mata hijab ya dauketa ya fice da ita daga dakin.
TURHAN POV.
Ya dora hannunsa yana karon addireshi da kuma sunan mutanen da suka karbi Emily a wacan lokacin.
“Amman kana da tabbacin idan muka je zamu same su a gurin”
Turhan ya tambaya da hausa sai Faruk ya fadawa mutanen da yaren Yarba.
"Ban sani ba, amman tun da har sun taba zama a gurin ko da baka same su ba zaka samu wani bayani a kan inda suka koma da zama ai, ni na gama aikina sai ka salleme ni yanzu”
"Emi ko mọ, ṣugbọn niwon igba ti wọn ti gbe ni aaye tẹlẹ, paapaa ti o ko ba ri wọn, iwọ kii yoo ni alaye eyikeyi lori ibi ti wọn gbe lọ ati gbe. Mo ti pari iṣẹ mi, nitorina o le fi mi silẹ ni bayi."
Yadda ya bukata haka aka yi, Turhan ya biya shi 20k yayi copy din files din ya maida masa da original. Turhan be yarda sun kara minti talatin a gidan ba ganin sun samu abun da suke nema suka kama hanyar address din da ya ba su, sai kuma suka yi rashin sa'a mutanen sun tashi daga gidan sai yan'uwansu suka tarar, a nan ma addireshin sabon gidan da masu gidan suka koma Turhan ya karba, sannan suka kama hanyar Ikorodu daya daga cikin unguwanin da suke da nisa sosai a birnin Lagos.
Sun isa da yamma sosai, suka buga kofar gidan mai gadin ya leko ya tambaya su waye su.
"A wa lati okere lati ri oluwa ile."
Faruk ya fada musu da Yoruba cewar mun zo ne daga nesa muna son gani mai gidan.
"Ya sunan mai gidan?”
Mai gadin ya tambaya, Faruk ya duba takardar copy dake hannunsu.
“Mr Chibuike Adanna”
“okay ku jira ina zuwa”
Ya shiga cikin gidan babu jimawa ya fito yana tambayar daga ina suke.
“Arewa“
Faruk ya amsa masa, babu jimawa aka musu izinin shiga cikin gidan aka kaisu falon matar gidan kasancewar mai gidan baya kusa a lokacin.
________________
Maganar gaskiya Kameela fa tana da gaskiya akan mijinta 🤭
Me kuke hangowa idan Turnan ya samu haduwa da Emily?
[4/20, 10:01 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL
🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
Page 1️⃣4️⃣
Dogon numfashi taja ta sauke ta matsa baya ta nufi kujerar dake dakin ta zauna. Ya bita da kallo for few seconds.
“Kina bukatar wani abu a yanzu?”
Ta girgiza kai alamar aa. Ya gyara tsayuwarsa.
“Baki bukatar yin aiki saboda ki gina kanki, baki bukatar tara kudi saboda ki gudu ki rayuwa a wani gurin dabam, daga lokacin da na baki gata ba zaki guje min ba, duk inda zaki je, duk iya gudun da zaki yi kina a cikin duniyata ne, ya kamata ki natsu karki jawa mutanen da suke kusantar kusa da ke mutuwa, bana sharing what ever is mine nawa ne har abada so you're mine”
Yana maganar zuciyarta na bugawa da karfi, hausawa suka ce idan babu rame me ya kawo maganar rame, ta san Vito yana kishinta, amman zancen ta daina kokarin gina kanta a ina ya ji wannan? Har ya juyo sai kuma ya juyo ya kalleta.
“Wannan mutumen da ya zo yau kin san cewa musulmi ne?”
“Na sani”
Ta amsa tana hade yawu.
“Ba mu da alaka ta kusa ko ta nesa da musulmi, kuma baki da alaka da kowa”
Ya juya ya fice ba tare da ya jiran amsarta ba, is like umarni yake bata, ya saba hanata hukda da kowa ciki har da kawaye be yarda da kusanci kowa haka ma baya yarda wasu su kusance ta. Ya mike tsaye ta nufi windows din dakinta tana kallon waje ta saka hannunta a baki tana cizon akaifarta, ita kam haka zata yi ta zama karkashin kulawar mazan dake da son zuciya? Kowane burinsa ta rayu a yadda shi yake so ba yadda ita take so, sai yaushe zata samu yancin kanta.
Ficewa ta yi daga dakin ta sauko falo sai ta samu Fatima zaune tana zane.
“Kin yi magana da Uncle Vito”
“Ba Uncle dina ba ne, bana son shi”
"Kin yi magana da shi?”
" Eh na fada masa, zaki yi aiki ki samu kudi zaki gina mana gida zamu koma can mu bar masa komai nasa”
Emily ta rufa ta fada.
“Wannan ai sirrinmu ne miyasa zaki fada masa?”
“Saboda na tsane shi”
“Toh miye amfanin abun da kika yi yanzu? Ya ssn manufata kina tunanin zai zuba min ido ne? Fatima me yasa kike da surutu ne? Kin lalata komai”
Emily ta zauna dafe da kai tana nadamar fadawa Fatima da ta yi tun farko.
“I hateeeeeee youuuuu”
Fatima ta fada cikin tsiwa da fusata. Emily ta dago ta kalleta cike da takaici.
“Idan baki tsane ni ba ai baki cika jinin Turhan ba”
Ta mike tsaye a fusace ta fice daga falon, dakinta ta sake komawa ta shiga bandaki da nufin wanka amman ta kasa aiwatar da komai sai kuka. Kuka ta yi sosai mai isarta sannan ta fito ta shirya cikin wasu riga da wando ta dauki wayarta da keys ta fice daga dakin.
Ta kai hannu zata bude kofar falon Fatima ta yi mata tambayar da bata yi zaton ta tsinci wani abu a maganar dazun ba.
“Waye Turhan Momy?”
“Abokina ne“
Ta amsa mata kai sannan ta bude kofar ta fice daga falon. A mota ma sai da ta yi da gaske sannan ta iya hana kanta kuka, bata tafi asibitin kai tsaye ba sai da ta fara shiga super market ta yi ma London siyayya abubuwan kwadayi da na wasa ta musu transfer sannan ta nufi asibitin. Sanin waye danta da kuma halinsa ya saka ta guzarin da ya rage mata ya tafi. Ta samu minti talatin zaune a motar sannan ta bude ta fito ta dauki kayan da ta siyo masa ta rufe motar ta nufi cikin asibitin.
Kamin ta karasa ta inda zata karya kwanar da ward din London yake ta hango Aliyu tsaye yana waya, tun da ta sauke idonta kasa bata sake kallonsa ba har ta isa gurin da yake tsaye, ya sauke wayar dake kunnensa ya kalleta kadan ya dauke ido domin tsare mace da ido wanda ba muharamararsa ba halinsa ba ne.
“Me kake so? Miyasa kake bibiyata? Baka lura da irin mutumen da nake tare da shi ba?”
“Be tsorata ni ba, be kuma burge ni ba”
“Yana isa sanin komai nake aikawata, kuma ko'ina akwai mutanensa, shin baka yi mamakin yadda Williams ya baka address dina ba? Bayan kuma be taba zuwa gidan ba? Ki ba musulma bace bani da wata alaka da kai”
Be sake magana ba yayi gaba ya barta a gurin tsaye juyawa ta yi ta bi bayansa da kallo har ta daina hango shi, sai kuma ta ji babu dadi, a zatonta ta tsorata shi ne. Dip sakon kar ta kwana ya shigo wayarta.
“Ba halina bane tsayuwa da mata, balle kuma wanda addininmu ba daya ba, a duk lokacin da kika shirya zaki iya dawowa aiki zamu yi magana a can”
Ta maida wayar aljihu sannan ta shiga ward din, tsayawa ta yi jikin kofar ta daidaita fuskarta ta cusawa kanta murmushi da farincikin dole sannan ta tura kofar da shiga.
“Hello Big Guy”
"Dariya yake amman yana ganinta sai ya hade rai ya juya baya daga kan gadon da yake zaune”
“Har yanzu fushi kake da ni London?”
“Sannu da zuwa”
Chidimma ta fada, ta mike tsaye London ya rike hannunta alamar baya son ta tashi. A haka dai Emily ta danne zuciyarta ta karasa kusa da shi ta gefen da fuskarta take ta leke shi da murmushi a fuskarta.
“My Handsome Guy...”
Aiko yace me zai mata ba ihu ba, yana ihu yana matsawa nesa da ita kai kace be santa ba ne, ko ayi zaton sace shi zata yi. A gurin ta watsar da kayan dake hannunta cikin tsawa da fara magana.
“Kullum damuwata akan yarana ne, tun ina karami ban san wani wanda ya damu da matsalata ba, ban san wani wanda ya damu da farincikina ba, kowa da na gama masa amfabi jefar da ni yake, guduna yake yanzu kuma ta kai har ga Yayana? To ka zauna da wanda kake so”
Ta fice daga dakin a fusace. Chidimma taja shi jikinta ta rumgume jikinsa sai rawa yake domin ba kasafai take masa fada ko tsawa ba.
“Momy bata son London, Momy ta yi fushi ta tafi ta gurin Fatima, Fatima kawai Momy take so, bata son London, ta gaji da London ta tsane shi”
Tana masa maganar tana shafa bayansa.
“Bata son yayi wasa da kowa, amman Chidimma tana son London tana barinsa yayi wasa da ruwa tana fita da shi yawa”
London ya bata rai sosai ya labe a jikinta kamar zai yi kuka, sauka ta yi daga kan gadon ta duka kasa.
“Hau bayana zamu yi doki”
Da sauri ya hau yana dariya domin yana son kalar wasar da take masa.
TURHAN POV.
Sai da Faruk ya gama yi mata bayanin dalilinsu na zuwa gidan da turanci, domin Turhan baya jin turanci sai larabcin Sudan sai kuma hausar da ta kasance yaren mahaifiyarsa.
Matar ta yi murmushi ya gyara zaman kujerar da ta yi mata kadan kasancewar kujerar one seater, ita kuma mace ce mai jiki sosai ba kadan ba.
“Bani da wata alaka da Emily a yanzu, tana raye ko a mace ba matsala ta bace, ban kuma damu na san kowane irin hali take ciki ba, mu dai mun daukota daga gidan marayu ne da nufin bata kyakkyawar rayuwa da gata, sai gashi ta watsa mana kasa a ido ta gudu ta bi saurayinta, idan ma wani laifin ta yi muku ko to ku tafi can wani gurin ku nemata, bana da alaka da ita a yanzu”
“Amman baki san wata hanyar da zamu iya ganinta ba? Ko jin labarinta? A lokacin da ta bar nan kina da labarin inda ta koma da zama”
“Ban sani ba”
Ta mike tsaye ta fice ta bar musu falon, Faruk ya fadawa Turhan abun da ta fada, sai ya tabe baki yana magana da kakkausar murya.
“Butulu ce ma shiyasa ba zata ga daidai ba a rayuwarta, gashi nan ta zo ta shiga tsakanina da mahaifiyata, an kai karshen ba zan sake nemanta a ko'ina ba yanzu”
A tare suka fito da Faruk suka shiga mota, kamin su isa masaukinsu Turhan ya kira mahaifiyarsa a waya, sai da yayi mata kira biyu sannan ta daga wayar.
“Hello Ammy”
“Kuna lafiya?”
“Lafiya kalau, Ammy na yi iya yadda zan iya, na yi neman yarinyar nan har na gaji ban samu inda take ba, macen da ta rike ta ma tace bata da labarin inda take a yanzu, ban san ya zan yi ba Ammy”
“Ban cilasta maka nemanta ba Turhan kai ka cilastawa kanka”
“Amman Ammy fushi kike yi da ni fa, idan ban samu yarinyar nan ba ba zan samu yadda nake so a gurinki ba”
“Na dade da yafe maka, kuma bana fushi da kai, iyakar abun da na sani shi ne, Aisha ta tafi da farinciki, ta tafi ta bar min wani tabo da na kasa kankare shi a zuciyata, a duk lokacin da na kalleka sai na ga wannan abun a tare da kai, a dawo lafiya Allah ya tsare hanya”
Ta aje wayar. Turhan ya ji kamar ya buga kansa da motar.
“Allah ya kara tsine miki albarka Emily mushirikar banza, yadda kika jefa rayuwata a matsala kika raba ni da mahaifiyata Allah ya hana farinciki kusantarki”
Ya dafe kansa ya rufe ido, a yanzu kam ba shi wata babbar makiyiya irin Emily. Macijiyace yarinyar nan kawai rabar mutane take tana cutarsu haka zuciyarsa take raya masa. The fallowing day yayi sallama da Faruk yayi masa alheri sannan ya kamo hanyar dawowa Kaduna.
Yana sauka Airport ya sanarwa mahaifiyarsa babu bata lokaci da aika masa da direba ya dauko shi zuwa gida.
Ko da ya iso ya samu an shirya masa abinci mai kyau a dinning, amman be kula komai ba saboda hankalinsa yana gurin mahaifiyarsa, dakinta ya shiga sai ya zame ta zaune tare da Jawahir suna dariya da alama hira suke, sai dai shigowarsa ya saka Ammy sauya dariyarta zuwa murmushin da ba kasafai take masa ba.
“Sannu da zuwa”
Jawahir ta fada sannan ta tashi ta fice daga dakin. Cikin wata irin tafiya ta kaisaita daya saba yi ya karasa gaban mahaifiyarsa ya zube kasa ya zauna.
“Barka da yamma Ammy”
“Barka Labarabe”
Ya dan dago Kadan ya kalleta ya maida kansa kasa.
“Ammy ki yi hakuri da abubuwa da suka faru, na yi ina yina a yanzu amman ban samu ganin Aysha ba”
“Allah yasa hakan shi ya fi alheri”
“Ameen”
Ammy ta mike tsaye da nufin bar masa dakin sai ya sha gabanta da fadin.
“Na yi zaton komai zai wuce idan na dawo, Allah dai ya gani na iya yadda zan iya akan yarinyar nan abu ya gagara, Ammy ki daina bari ana zuga ki kina juya min baya”
Jin haka ya saka Ammy ta dawo ta zauna.
“Su waye suke zuga ni?”
“Jawahir mana Ammy, ita take tare da ke kullum wasu abubuwan ita zata saka ki yi min, saboda bata san zafinki ba, ba ke kika haifeta ba”
“Kai da kasan zafina ai gashi nan na aura maka yar mutane ka watsa min kasa a ido”
“Dan kuskure kadan ne na aikata Ammy, dan haka”
Ya nuna kan akaifarsa.
“Amman gaba daya kin canja min, kuma iyakar biyayya ni na san na miki, bana son yarinyar nan kika ce na aureta na daure a haka na aureta, addininmu ba daya ba, na san a lokacin da na aureta ta musulunta amman yawanci ai musuluntar karya suke yi saboda su yi makirci, kaskanci ne a gurin namiji irina, jinin sarauta kuma jinin larabawa ya auri mace irin Emily, sam bata cikin irin matan da nake so, ya kamata ki duba min Ammy”
Fuskar tausayi ta bayyana a fuskar Ammy.
“Baka fada min baka sonta ba a lokacin da na hada aurenku ba ba zan cilasta maka ba, Allah kadai ya san kalar azabar data sha a hannunka da masarautarku, baiwar Allah”
Ya dago yana kallon Ammy cike da mamaki, shi a tunaninsa idan na fada mata duk wannan zata tausaya masa ne, madadin haka sai ta kara jin tausayin Emily din ma.
“Haka ne, kaskanci ne auren wanda ba bata tashi a addinin musulunci ba, kuma wanda ba yarenka ba, ba yar sarauta ba ina mai baka hakuri akan hakan Dan sarauta”
Ta mike tsaye ta fice daga dakin.
“Da ace zan samu damar yin ido biyu da Emily a yanzu, tabbas zan bata hakurin saboda Ammy, amman bayan kwana biyu sai na hada ita da bokanta na kashesu, yarinya kamar mayya gaba daya ta tafi da zuciyar Ammy, ita wacan katuwar kafirar maganin be kamata ba sai Ammy, ni kadai ta haifa a duniya amman yanzu ta tsane ni saboda wata shegiyar yarinya.. عار عليك يا إميلي,
”عار عليك
Yama fadar yana wargar da hannu, be san kaskanci da wulakanci ba sai da Emily ta duro gidansu, tashi yayi ya fice daga dakin ya shiga dayan dakin yayi waya da matarsa da mahaifinsa sannan yayi wanka ya fito falon.
“Tun kamin na yi aure, ina addu'ar idan na yi aure Allah ya bani ya mace, sai gashi kuma da na yi auren na haifi namiji, sai ya zama ba zan sake haihuwa ba, a lokacin da Aysha ta zo gidan nan sai na ji kamar addu'ar da nake yi ce a can baya Allah ya karba min ya ba ni ya mace ta wani bangaren da ban yi zato ba, yarinyar nan ta tsaya min a rai”
Labarin da ya sauko ya samu Ammy na bawa Jawahir kenan, Jawahir din kawai ya kalla yana ayyana munafurcinta a zuciyarsa ya fice ba tare da ya taba abincin da aka jera masa a dinning ba. Bayan fitarsa Jawahir ta kalle Ammy.
“Dan Allah Ammy ki yi hakuri ki cire Aysha a zuciyarki, ki kaddara ta mutu, ki shirya da Ya Turhan ku dawo kamar yadda kuka a da, Wallahi tausayi yake ba ni”
Ammy ta kalleta tana murmushi.
“Baki san waye mahaifin Turhan ba shiyasa yake baki tausayi, larabawa suna da zuciya mai tauri, shi kuma ai jinin mahaifinsa, nonon ma na larabawa ya sha ba nawa ba, kar yi mamaki idan aka ce miki ya sake aikata kuskure bayan wannan”
Jawahir ta sauke ajiyar zuciya tana girgiza kai cike da tausayi.
ALIYU POV.
“Tun jiya da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 63