Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ Page 2️⃣1️⃣ Ban san a addinin musulunci idan namiji yayi aure yana sati a gurin amaryarsa ba idan budurwa ce, idan kuma bazawara ce kwana uku, dan haka da aka kwana biyu ban ga mijina ya shigo dakina ba sai na sami wata makociyarmu da nake siyen kayan girki gurinta wato Malika ita ma dai yarinya ce sai dai ba kamar ni ba domin tana da yara har uku. Na fada mata cewar ina son ta rakani gurin mai gari saboda ina son na kai karar Khaleefa, ita kam bata yarda taje ba wai gudun kar ace ita take zuga ni nake abun da nake, amman ta kwatanta min gidan kuma ta dorani akan tsarin yadda zan yi magana da shi idan na tafi. Ina fita gidanta ban zame ko'ina ba sai kofar gidan mai gari na aika a sallamo min shi sai iyalinsa suka ce na shigo ciki, na shiga na yi musu sallama suka amsa muka gaisa na gabatar musu da kaina sai dayar tace. "Oh ke ce wadda aka ce an musuluntar ko?" "Eh" Na amsa ina maida kaina kasa, babu jimawa Mai garin ya fito muka gaisa na gabatar masa da korafina cewar Khaleefa ya aje ni a daki daya ita kuma matarsa ya kaita gidansa kuma ya siya mata abinci mai kyau ni kuma ya daina ba ni, gashi kuma kusan kwana biyu be shigo dakina ba, ko da ya shigo gaishe da iyayensa babu ruwansa da dakina, ga kuma duka da yake yawan yi min. A take Mai garin ya aika aka kirashi tare da iyayensa na zayya abun da na fada da farko, sai ya tambayi ba'asi, Khaleefa yace karya nake yana bani abinci kuma baya shigo bangarena ne saboda ai kwana bakwai ake idan aka aure budurwa, ban san mace na zuwa da abinci ba idan aka aureta sai ranar. Yace da abincinta ta zo da komai nata, kuma wai bana masa biyayya abu kadan zan fara cewa ba shi da adalci ina masa ihu da Allah ya isa. Iyayensa ma suka goya masa baya mai garin ya rufe ni da fada. "Ke mu fa irin tarbiyar da kuke a can ta arna ba ita muke a nan ba, tun da har kin yi aure kuma kin musulunta ya kamata ki watsar da wannan dabi'ar" Mahaifiyarsa tace "Ai matsalar auren tun farko bata san musulunci ba ko kuma bata tashi a cikinsa kenan, su fa tarbiyar su da auratayyarsu dabam take, musulunci ma ai suna yi ne kawai a baki" Mai gari ya fadi nasa iyayensa da shi kansa su fadi na su, na rasa ya zan yi sai kuka nake ina bashi hakuri. Da muka dawo gida sai ya fara dukana irin dukam da be taba min ba, dukan da zaka rantse dansa na kashi ko na aikata wani criminal abu, ina bashi hakuri yana duka wai abun nawa ya wuce ina fada a makota cewar yana bari na yunwa da sirrin gidansa ya kai har na dauki kararsa na kai gurin mai gari a nemi tozartashi. Duka yayi min ba na wasa ba, yana dukan yana min gorin wai daga ya taimaka ya tsamoni daga wuta da yanzu idan na mutu wuta zan tafi. "Iyayenki ma suna can cikin azaba, saboda sun yi shirka da Allah, kuma Allah kadai ya san ta hanyar da aka same ki, shiyasa kike butulu, matar ma data rike ki yanzu ai gudowa kika yi kika barta, ni kuma na dauko ki na musuluntar da ke na aureki amman kina min butulci, idan ba ni ba wane namiji ne zai auri arniya ya kuma ba a kawo ta da komai ba, marar asali ma irinki" A lokacin ne kalamansa suka fi yi min zafi da daci fiye da dukan da yayi min, na ji kamar ace ina da ikon da zan zare numfashi daga jikina na manta da kowa da komai. A daren na sha kuka washe gari na dora haka na kwashe kwana uku bana iya komai sai kuka. Abun da ban sani ba be sani ba shi ne, ashe lokacin da ya doke ni ina dauke da cikin dansa, shi be sani ba saboda ba nice a gabansa ba, ni kuma tunani da tashin hankali da nake ciki be bar ni na ankara ba, daukewar da al'ada ta yi min na tsawon wata hudu ban gane ba saboda hankalin ba nan yake ba, gashi kuma cikin fari ne ban san komai akan ciki ko haihuwa ba, domin a gidan marayun da muke zaune ban da karatu da sana'a ban maida hankali gurin koyon komai ba ko kuma sanin wani abu wai shi ciki da haihuwa. Sai da ciki ya kai wata biyar sannan na gane cewar ina da ciki shi ma Malika ce ta fada min. "Wata nawa ne Aisha" "Ni ban sani ba, ni na dauka ko yunwar da nake fama da shi ne ya janyo cikina yayi girma" Ta yi dariya. "Kai Aisha kina da wauta, ga abu har ya fito yaushe rabon da ganin al'adarki?" Na tsaya tunani ni kam bana ma iya tunawa. Ta bani shawarwarin yadda zan yi kuma ta fada min na tafi asibiti. Na dawo gida ina ta murna da dare da Khaleefa ya shigo na masa maganar sai yace min ai ya sani, shi mahaukaci ne da ba zai gane ba. Na yi mamaki ya gane amman be taba min maganar ba kuma be nuna min komai ba? Da na masa maganar zuwa asibiti sai yace shi ba shi da kudi yanzu na bari sai gaba idan ya samu kudi. Ma zan yi a lokacin idan ba hakuri ba, na san ba dan ba shi da kudin ba, domin yana cikin shirye shiryen bude shago a kusa da gida ne, idan kuwa ba shi da kudi ba zai bude ba, nice ba ya son kashewa kudin, sai na bawa zuciyata hakuri na saka masa ido, na jidadi samun ciki domin ya dauke min damuwa sosai ban sani ba ko dan saboda ina da son yara ne ko kuwa dai saboda ina kurciya ne, wata kila kuma saboda ina jin cewa zan samu iyali ne, ma'ana dai zan samu dan'uwa na jini daga gareni. Kusan sai ya dauke min rabin damuwa da tunanin da nake idan na ji motsinsa sai farinciki ya baibaiye ni. Ina cikin wata na shida ne da ciki, na ji yan'uwansa suna shelar Amaryarsa Hindu tana da ciki, shi kansa na lura da farincikin da yake da cikin, amman a nawa shi da yan'uwansa ba su nuna min jindadinsu ba kamar wanda zata haihuwa ba da igiyar aure ba, ashe wai kallon suke wata rana zan iya komawa kafira saboda iyayena da asalina ba na musulunci ba ne tun farko, kuma zan iya komawa da rayana, kusan a lokacin zamana a gidan da kuma aurena kamar ya zamewa Khaleefa dole ne. Wallahi akwai zafi akwai ciwo, ka ga mijinka yana zumudin zuwan wasu yara amman ban da naka, bayan wankin da nake na siyarwa da ya dauke me sakamakon abincin da Mahaifiyarsa ta dawo tana ba ni a kullum babu wani abu da Khaleefa yake min, ko dan siya min wani abun kwadayi babu ruwansa. Ashi ma kwadayi mace mai ciki guri yake samu, domin ba kasafai nake jinsa ba, idan ma naji sai dai na yi hakuri ko kuma na tafi makota gurin Malika na samu idan tana ta ba ni. Amaryarsa ita take girkinta a ranar girkinta ni kuma aka fashe da cewar ban iya girki ba sai idan mahaifiyarsa ta girka ta ba ni. Da cikina ya shiga wata na bakwai sai na fara rashin lafiya da amai domin ban yi laulayi a farkon cikin ba, da na masa maganar tafiya asibiti sai yace min na bari sai wani sati. Haka kuwa na hakura na zubawa sarautar Allah ido. Wata ranar jumma'ah gidan babu kowa sun tafi bikin yan'uwa mazan musu wasu sun fita wasu kuma sun tafi masallaci, ina zaune cikin dakina bayan sallah la'asar daya daga cikin matan gidan da bana magana da ita saboda yadda suka hade min kai. Sai gata a dakina da sallamarta na amsa ina kallonta sai ya duka ta ce. "Aisha, na zauna na yi nazari abun da ake miki a gidan nan an zalince ki, ki yi hakuri ki yafe min, ban gane ba sai da kika samu cikin nan, kalli yadda ake farinciki da cikin Hindu amman ke kamar kin kumsa cikin shege, kuma Hindu tana zuwa asibiti amman ke baki zuwa" Ta kowance gefen zagenta ya ciro kudi yan dari biyu da naira dari ta miko min. "Ungo wannan duku uku ne, ki shirya ki tafi asibiti a duba lafiyarki da abun da yake cikin ki" Na saka hannu biyu na karba na mata godiya sai ta gargade ni akan kar na fada ma kowa, ta miko min takardar da number waya a rubuce. "Kin ga number wayata, idan kina son magana da ni ki tafi wani guri ko makota sai ki kira ni ki tambaya, kin ga ba zai yiyu mu yi magana da juna idan Inna na nan ba, sai mijinki da ita kanta Inna da sauran jama'ar gida su ce na yi munafurci, amman idan kika fita makota kika ari waya sai ki kira mu yi magana ba san mun yi ba, amman ba karki bari a gane da ni kike waya" "Toh na gode" "ba komai Allah ya saukeki lafiya" "Ameen" Ta fita ni kuma na boye kudin, washe gari ban ma fada masa zan tafi asibiti ba saboda gudun kar ya hanani ko yace na bari sai lokaci kaza, domin ina jin rashin lafiya a lokacin, sai na shirya na fita ba tare da na fadawa kowa inda zan je ba, a tunaninsu na shiga makota ne. Kuma tabbas na shiga amman gidansu Malika na tambaye ta wace asibiti ce mai saukin kudi domin dubu uku ne da ni ina son na je, sai ta fada min na kama hanya na tari achaba na tafi, duk abubuwan da ake bukata na yi da na shiga ganin likita sai ta yi ta fada wai miyasa ban zo awo da wuri ba gani yarinya kuma haihuwar fari, ai yanzu an daina wannan dabi'ar ta kauye, sai na fada mata mijina ne be aminta ba yanzu ma ba da saninsa na zo ba. Ta auna ni bayan na fada mata abun da nake ji tace naje na yi hoto a yau din na kawo mata, na je na yi hoton wa inda aka fada min na biya 1200 a lokacin na dawo Allah yasa na same ta da ta duba sai ta fada min abun da ke ciki jirkice yake madadin kan yaro ya juyo ta gurin marata sai ya zama kafafuwansa ne a nan. "Hakan yana da wata matsala ne?" Na tambaya domin ban san kan abun ba. "Sosai kuwa mace zata iya mutuwa ko ta kasa haihuwa sai an fasa ta, ko kuma ta samu matsala ko danta ya samu, za a iya rasata ko a rasa dan, gashi kuma baki da jini sosai ba ki da ruwan jiki da yawa baki cin abinci mai kyau" A take hankalina ya tashi, zancen abinci mai kyau kam bata taso ba domin abinci ma bana iya ci na koshi balle wani mai kyau ko mai gina jiki. "Za mu dora ki akan magani, kuma kije ki shirya ki dawo gobe, akwai abun da zamu fara miki da juyo da kan yaronki kamin ki cika wata tara, dan yanzu cikinki yana da wata bakwai da kwana sha takwas" Na mata godiya na fito jikin a sanyaye domin na san babu wani kudi da zan samu a gurin Khaleefa, ashe ma abun da ban sani ba gidan yana nan ya kusa kamawa da wuta saboda na fita tun safe ban dawo ba har la'asar. Dan canjin da na rage min ne na hau achaba da shi na iso gida sai da na fara biyawa na fadawa Malika halin da nake ciki ina kuka sannan na shigo gidan. "Idan uban wa kika fito?" Ita ce madadin amsa sallamata da yayi kasancewar yana cikin dakin na yi sallama. "Asibiti" Na amsa jiki ba kwari murya na fita daker. "Ina kika samu kudin zuwa asibiti? Da izinin wa kika fita" "Idan na tambaya ba zaka bar ni ba, kudin kuma daman ina da shi" "Karya kike sai dai idan satar min kika yi ko kuma kin fara bakin halinku na kafirai, wato yanzu ya kai ki fara fita baki fada min ba" Na kalleshi cike da takaici da nadama da bakinciki na ce. "Wai kai Hamza wane irin zuciya ce a kirjinka? A matsayinka na musulmi mai addini be kamata na same ka haka ba, dabi'unka da ka nuna min ba su na tarar ba, ka zalince ni kai da iyayenka kunci amanata" Ban gama rufe baki ba ya rufe ni da duka. "Me kika sani akan addini da zaki tsoma baki a ciki? Kafira diyar kafirai? Bubabbiya marar alkibila, rashin kunyarki ya kai ki kira da Hamza gatsatsa ko? Irinki ma son haihuwa ake da ke? Mugun iri irin kafirci wadanda basa tuban Allah da ma'aiki, na haihu da ke kije gaba ki maida yarana kafirai" Ban taba sanin rashin imanin Khaleefa ya kai haka ba sai ranar, baya ji baya gani duka yake ina tare cikina yana kai masa halbi da kafarsa, Matar nan da ta taimaka min da kudin tafiya asibiti Maman Luratu ita ce ta shigo tana ba shi hakuri tana jansa sannan fa sauran suka shigo suna jansa suna fadin ban kyauta ba amman dai yayi hakuri ko dan cikin dake jikina. "Na gaji da ke na gaji da halinki kowa ya san ba haka na tsara rayuwar aureba amman ji yadda kika maida gidana, Aisha na sake" Maman Luratu ta yi hanzarin rike shi. "Abun he kai can ba Hamza ka yi hakuri ga ciki kuma ta tafi ina?" "Ta tafi duk inda zata tafi, ba gaji da halinta bata da tarbiya" Nasan ma'anar saki a musulunci kamar yadda na san ma'anar aure, wato ya barranta kansa daga gareni, ni din nan na haramta a garesa, sanin ba ni da gurin zuwa ba ni da kowa ya saka ni ba shi hakuri ina rokon mutanen gidan su ba shi hakuri na zauna. Sai suka ce na bari sai ya huce na zauna a gidan idan ya huce zai maida ni. Na san yadda suke kina sai zuciyata ta raya min kamar abu ne mai wahala su saka ya maida aurena. Dan haka na tashi cikin daren nan na tafi gidan mai gari na fada masa halin da ake ciki, ashe fita ma matsala domin har an kira an fada masa, mai garin ya aiko kiransa ya zo take a gurin kamin a mana umarni da komai ya ce. "Da zu na sake ki ne da nufin saki daya, toh yanzu na kara miki na sake ki saki uku babu aure tsakanina da ke har abada" Na rude na kama kafafuwansa na rike ina kuka ina rokon gafara, ban wayi addinin sosai ba saboda haka ban san idan an yi saki uku aure ya kare ba kenan. "Khaleefa ka san ba ni da kowa ba ni da komai dan Allah karka min haka, Alkawari be ce haka ba, ka yafe min Wallahi ba zan sake ba" Ni kam rokonsa kawai nake ina son ya maida sai da matar mai garin tace min ai auren ya kare kanan babu zancen gyara. Na yi tunanin ko mai garin zai ce na zauna a gidansa har sai na haihu, daman iyayensa kam ban saka ran za su ba ni gurin zama ba. Ina dawowa gidan na ji na zaba bukatar kowa a tare da ni sai na shiga dakin na dauki can chanjina da fitila da number da Maman Luratu ta ba ni na fice ba tare na dauki komai daga suturar da na samu a gidan ba. Na karasa inda yake zaune a kofar dakin mahaifiyarsa sai duk idon yan gidan ya koma kaina wata kila suna tunanin ko zan rokeshi gafara ne ko kuma ya bar ni na zauna a gidan ne, na tsaya a tsaya ina kallonsa ido cikin ido na ce. "Ka ci amanata Khaleefa, ka yaudare ni, ba ni da kowa ba ni da komai wannan tabbas haka ne, saboda kai na zo gidan nan kuma yanzu aure ya kare zan tafi, ka sani na rayu kamin na hadu da ni, na rayu babu uwa babu uba, babu daya daga cikin danging uwa ko uba, yanzu ma zan rayu domin mai rayawa ya kashe be manta da ni ba, Hamza na barka da Ubangijin da ya aiko Annabinsa da Addinin Musulunci, na barka da Ubangijin da be kwana be haifa ba ba a haife shi ba, Hamza na barka da ALLAH... " Mikewa yayi tsaye yana kallona baki a sake, matan gidan kuma kowa yayi tsit kamar babu abu mai rai a gidan. Bayan wannan wata kalar bata sake fitowa daga baki ba har na doshi kofar fita gidan na fice, ban yi nisa ba na ji ana kirana Maman Luratu ce ya biyo ni tana kuka. "Aisha ina zaki" "Koma ina ne zan tafi Wallahi yau ba zan kwana a gidan nan ba" "Toh Allah ya miki mafita, dan Allah idan kin samu waya ki kira ni, Allah ya sauke ki lafiya, ungo ga dubu biyar ki rike" Ina karba kudin na fashe da kuka sai ta rumgume ni tana kuka, na dago godiya ma kasa yi mata na yi na kama hanya, achaba na fara hawa ya kai ni tashar garin, ina zuwa kuwa na samu mota sanin kudin ba zai ishe ni na je Lagos ba na hau motar Kaduna, idan ma naje Lagos din gurin waje zan je? Matar da na yi butulci? Ko gidan marayun da ba lallai su karbe ni ba zan koma? Lokacin da na hau motar ba zai wuce karfe goma ba kasancewar garin da kowane lokaci ka je ana samu direba saboda akwai masu cin kasuwa, kuma ranar da abun ya faru ranar kasuwa ce. A ranar ban kwana a garin ba da cikina da ciwon da nake ji da kuma bakincikin dake kumshe a zuciyata na kwana a tashar Kaduna... Follow my channel domin samun update https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 And don't forget to SHARE [5/6, 8:51 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ Page 2️⃣2️⃣ Da gari ya waye sai na yi ta raba ido a cikin tashar ina kallon mutane, daman na kwana a kusa da massalaci ne a wani guri da ake aje sako tare da wasu matafiya da dare yayi musu. Na zauna a gurin har zuwa karfe daya na rana saboda ban san a inda zan je ba, ba zan iya komawa lagos ba idan ma nace zan koma ba ni da kudin motar idan kuma na koma ba ni da tabbacin a karbe ni. Jama'ar gurin da suka lura ina zaune a gurin har ana daf da ayin la'asar sai suka same ni suna tambayar na san a inda nake kuma wana sani a garin Kaduna? Nace musu na sani kuma bani da kowa a garin kaduna. Sai suka tambaye ni ni matar aurece? Nace musu aa domin a halin da nake ciki babu aure a tare da ni, idan ma akwai vana bukata domin na gama kakkabe Khaleefa a rayuwata yanzu, sai kuma suka sake min wata tambayar da na rasa amsar da zan ba su. "Toh cikin dake jikinki fa?" Na shafa cikin ina hade wani abu mai daci, dole kowa zai yi zaton cikin shege ne, wata kila su yi tunanin ko na gudo daga gidanmu ne. "Dan Allah inda ake bada taimaka idan mutum yana cikin matsala?" "Kamar wani irin taimako?" Dayan ya tambaya. "Kamar wata kungiya ta musulmai da take bada taimako haka ko masallaci" "Toh sai zakka da wakafi" Dayan kuma yace na tafi massallaci, wani kuma ya tambaya wani irin taimako nake nema, na ce na wanda zai rike ni har na haihu. "Wannan cikin ba shi da uba ne?" "Yana da uba, ni ba ni kowa marainiyace ni, kuma mijina ya sake ni, kuma musulunta na yi ban san kowa a nan ba" Ina rufe baki daya daga cikin dattijan dake tsaye a gurin ya rufe da fada kamar zai dake ni. Wai na tashi na bar gurin haka muke muna zuwa muna cikin shege mu zo tasha mu tare muna haifa musu yara yan iska muna bata musu tasha. "Idan baki da kowa ki koma garinku mana, karya ce suke saboda kawai a tausaya musu, cikin shege suke yi" Ban san lokacin da na fashe da kuka ba, daman wai waye zai yarda da ni, suna da gaskiya suna bukatar tabtace tashar su. Haka na tattara na bar tashar na fito na kama hanya ina tafiya ban san inda zan je ba, can na samu guri kusa da wata mai wara na zauna na siya wara na ci saboda ban saka komai a cikina ba tun safe. "Dan Allah ina ne? Zakka da wakafi?" Ba tambaye ta, sai ta kwatantamin na bata kudin wararta na siye ruwan leda na sha, na tari mai achaba na hau na fada masa inda zai kaini ban tambaya nawa ba sai da muka isa yace min 500 zan bashi a lokacin 2300 ne suka rage min, na ba shi 500 na doshi gurin gabana na faduwa, domin maraicina be taba saka ni rokon kowa ba. Mai gadin gurin ya fara tambayar ina zanje na fada masa taimako nake nema a take na bayyana masa abun da ke tafe da ni da kuma taimako da nake bukata. "Kin tabbatar cikin nan baki ba na shege ba ne? Domin suna yin bincike idan za a bada taimako" "Wallahi gaskiya ne, ba karya nake ba" Sai yace na jira a nan ya shiga ciki ya fito da wani mutum mutumen yayi min tambayoyi ya yi rubutu akai sannan yace min yanzu kowa ya tashi aiki saboda yamma ta yi, amman na tafi zai saka sunana a cikin mabukata na dawo wani sati, sannan ya tabbatar min kamin su bada taimako suna yin bincike saboda akwai bata gari da suke zuwa suna karya nace masa na yarda su yi duk abun da ya kamata. "Amman yanzu idan na tafi ba ni da gurin zama ban san a inda zan zauna ba" "Ki yi hakuri dai wani satin ki dawo da wuri kamin rana ta yi" "tohm" Na amsa ina kuka, sai ya saka hannunsa aljihu ya ciro kudi naira budu daya ya ba ni wai na hau abun hawa. Na karba na juya na kama hanya daman kam wa zai karbe ni a haka dole kowa zai yi zaton karya nake saboda cikin dake tare da ni ga shi kuma ina fadar ba ni da kowa kuma nace ban san kowa a garin Kaduna ba, ga ina cewa musulunta na yi wasu ma sai su dauka karyar ma ta yi yawa. Daga gurin na kama hanya ina ta tafiya a kafa ba dan na san inda zanje ba, har dare ya fara yi na siye ruwan leda na yi alwala na raba gefen wani icce dake kan hanya na yi sallah, ina addu'a ina kuka ina rokon Allah ya kawo min mafita. A gurin na yi ta zama har aka yi isha'i a nan ma na yi sallah. Da yake akwai mai shayi nesa da inda nake zaune kadan da na yi yunwa ta matsa min sai na tafi na siya birede da ruwan lipton na koma gefe daya na sha, sai wani azababben ciwo ya taso min, da na kawo masa kofin kowa kallon wulakantacciya yake min domin mace mai daraja ba zata saya tea ta raba gefe ta sha ba, gashi na zama kamar mahaukaciya duk na firgice ga rama cikin ma yayi min nauyi haka dai nake ta fama. Da na bashi kayan sai na raba ta wata hanya dake kusa da shagon na bi na lulla da wasu kananan gidaje, a gurin na samu inda na raba. Na wahala a gurin domin

Chapter 17 of 63