Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da gida kusan nauyin mu da na mahaifina a wuyanta yake, mahaifina ba shi da wani karfi kuma be damu da nema ba, ta kan ce min: “Baraka, mace na da ƙafa biyu ɗaya tana goyon gida, ɗaya tana neman arziki.” Na shiga cikin harkar girki wato siyar da abinci, tun ina 15yrs mahaifiyata kuma tana fita shago siyar da kayan masarufi, a lokacin ban fara karatu a kolege ba, na iya hada tuwo da hannu, da kwasar romon miyar ogbono cikin harba guda. Na kammala karatu a wata college Ibadan, amma bayan na gama sai na gane cewa takarda ba ta nufin abinci a kwano. Domin bayan gamawa, ba aikin da ya biyo ba. Na zama kamar mutumin da ya haɗiye ƙashi, ba zai hade wuce ba, kuma ba zai iya fitarwa ba. Na tattara kayan da ba su wuce buhu biyu ba, na tafi Lagos, wurin kanwar mamata, saboda gurin da nake siyar da abinci a da gonati ta kwace, mahaifiyata ta kuma shagonta yayi kasa, ga shi mu bakwai mahaifinmu ya haifa ba daya ko biyu ba, ni ce ta biyu idan ban tallafi mahaifiyar da ta tsaya akan ilimi da abincin na ba me zan yi? Na fara komai daga tushe. Na rika siyar da abinci a Mile 12, da jarin da mahaifiyata ta hada min, wata rana a siyar wata rana ba za a siyar ba, wani sa'in sai na roki kanwar Mamana ta ara min kudi nake samu na kulla wani jarin, gashi mijin aure ya gagareni a lokacin ko da yake ni kaina ban shirya auren ba domin ban tanadi komai na aure ba, haka mahaifiyata ma bata da wani abun aurar da ni a lokacin. Na ci gaba da girki har wani lokaci sai wani NGO ya fitar da talla, na neman ma'aikata, cika da takarduna na karatuna, ban sani ba ashe aikin ne silar wargewar rayuwarki, bayan wani lokaci. suka sanar min sunana ya fito. Na tafi gurin horarwa suka min interview bayan na yi nasara suka sake sanar min an dauke ni, farincikin be bar ni na kwana ba a ranar. Kusan zan iya cewa addu'ace ta ba ni nasara domin babban guri ne da shugaban gurin ya kasance bature jar fata mai tsakanin fari da jan gashi ga kuma blue eyes, kyakkyawa ne mai far'a da son bakar mace kamar ba jan kunne ba, na fara aikin a gurin a matsayin sakatariya ina kula da komai zuwa kan lokaci girmama kowa bawa komai hakkinsa. Sannu a hankali aka na saba da kowa a gurin ba iya ma'aikan gurin ba har da masu zuwa su fita. Daga gaisuwa da mutunci muka fara sabo da Rowan Alaric MacLeod wato shugaban gurin, a lokacin akan masa lakani da bello, domin farar fata idan suka tsallako kasashenmu sukan nemi suna su sakawa kansu saboda ku saje da mu kuma mu saki jiki da su. Bature ne da ya zo daga Scottish, zan sake maimaita miki wannan, Me kyau ne sosai kamar ke kyaunsa ne abun da ya rude ne, na kasa dauke ido daga gareshi shi kuma ya saka min fuska ya rika ba ni damar matsawa kusa da shi, ba kuma zan miki karya ba ta dayan gefen ina hange kudi da yake da su, kamar idan na same shi a matsayin saurayi na huta, domin ba addininmu daya ba, na san abu ne mai wahala mahaifina ya amince na aureshi, ban sani ba ashe yana da mata, nina fara nuna matsa kauna sai ya sanar min yana da mata yar da yara biyu a tsakaninsu, hakan sai ya saka na yi baya, shi kuma a lokacin ne ya kamu da kauna ta sosai, sai kusancinmu ya fara yawa, har ta kai ya kan bukaci na kawo masa abu a gidansa ko kuma ya saka matarsa da kanta ta kira ni ta sanar min idan wani abun ya taso na aikin ko kuma familynsu kamar taron biki ko birthday ko kuma danta idan ba shi da lafiya ko yarta, ban sani ba ashe ya fada mata cewar nice kadai babu ruwana a cikin matan da yake aiki da su, ni ce kadai ya yarda da ni saboda sauran wasu ba su da amana wasu kuma suna nemansa. Ashe yayi hakan ne saboda matarsa ta aminta da ni da shi, ko da an kawo mata wani zance ko ganin mu wani guri ba za a zargi komai ba, da haka muka fara mu'amala yana sakar min kudi yana nuna min kauna, na sake jiki da shi kuma na zama mai fuska biyu domin matarsa da wacce ta fini komai na mata kuma ta kasance yar kabilar igbo ta aminta da ni, amince da har yau bata daina ba. Ban ankaro ba na samu ciki na tafi asibiti da taimakon likita aka zubar da cikin dan wata biyu, muka sake komawa ruwa. Ina samu kudi na aikawa gidanmu a inda nake kuma ina watayawa yadda nake so, rayuwa ta ci gaba a haka wata rana bayan gama al'ada na tafi aka ba ni maganin hana daukar ciki, aka fada min dokokin yadda zan sha kuma na bi ka'ida da haka ba ni da haufi muka cigaba da shedanci, ban sani ba ashe tun kamin na sha maganin na dauki cikin ki amman babu wata alama a tare da ni dake muna akwai ciki, idan lokacin al'adata yayi zan yi idan na gama na yi tsarki. Wata rana, na tashi daga aiki, ina isa gida ciwon mara mai tsanani ya rufe ni, na sha magani be daina ba kuma be saba min haka ba, kusan ma zan iya cewa ba watan al'adata ba ne, da abun yayi min tsanani kamar ana murza mini ciki da mashin din wuta, sai na yi mamaki "yau kuma al'adar ta zo min a tsakiyar wata da fushi ne? Amma me ya sa take murda ni kamar na yi hauka?” Na sha paracetamol. Na dinga juyawa a gado. Amma ciwon ya ƙi sakina. Na daina numfashi da kwanciyar hankali. Cikin rudani aka kaini asibiti, bayan an ba ni gado na samu kulawar likita sai, Likitan ya dube ni, ya ce cikin natsuwa: “Matar nan, ko kin san kina da ciki ne?” Na ce da shi cikin zafin rai “Dokta kar ka yi wasa da ciwo, al’ada ce kake gani, ba ciki ba ne.” Sai ya ce da ni: “Toh ina jin heartbeat ɗin yaro ma'ana bugun zuciyar jariri yana da rai a cikinki.” Na ce “Jariri kuma? Ciki?? Ai ni bana da ciki! Ba ni da wata alama ta masu ciki ma, Ina nono ya kumbura? Ina tashin zuciya? Al’ada ma tana zuwa kamar yadda ta saba!” Cikin natsuwa ya ce “Wannan ba ciki irin na mutane bane. Wannan cryptic pregnancy ne, ciki mai ɓoye kai. Na ga mata irin ki da yawa da ba su san suna da shi ba sai sun zo asibiti. Cikin na girma ne a ciki, yana ɓoyewa a waje. Kuma Jikinki da kwakwalwarki sun hana ki gane cewa kina ɗauke da rai.” Ya ɗan tsaya, ya ce: “Wasu mata sukan ci gaba da yin jinin da suke ɗauka a matsayin al’ada. Wasu ba sa jin canjin jiki saboda hormones ɗinsu ba su nunawa. Sai dai kawai wata rana a ga ciki ba tare da an shirya ba.” Be gama bayani ba ruwa ya fashe min, a nan na saki hawaye. Ina kallon likitan kamar ace zai iya yin wani abu. Ina tambayar kaina da gaske haihuwa zan yi? Bayan sa’a biyu kacal, na haifi wata yarinya da ta fi hasken idanuwa kyau, fara kyakkyawa mai matukar daukar hankali, ga jan gashi da blue eyes, kikashigo duniya cikin sirri, amma da annuri da kuka kamar kowane jinjiri. Baki rage komai daga kamanin mahaifinkin ba, kuma baki dauko komai daga gareni ba, sam ba za a taba yarda ni na haife ki, saboda gene din farar fata yana da karfi, a duk yadda aka haihuwa ko da yara ba su dauko gaba daya ba, su daukon wani kaso, masu gene mai karfi kuma basa raga komai haka kika zo min, kamar dai na rike ki, amman ina tsoron kallon da duniya zata min da kuma abun da iyayena za su ce, kanwar mamana ta siyo kayan jaririya na saka miki na lullube ki cikin zane, tun a asibitin tayi min fada bayan ni ma na yi ma kaina, ni da ita muka shirya ba za mu bar asibitin ba sai dare saboda mun shirya jefar da ke a inda muke ganin zaki samu masu rika ki. Sai karfe 8pm muka fita asibitin muka tari abun hawa zuwa inda ta bincika tun da rana ta samu, nesa da gurin muka mukaci mai taxi ya aje mu, da kafa muka taka muka isa gurin babban gida ne zagaye kuma inguwa ce da babu mutane sosai, na bude jakar da na zo da ita asibiti kuma wanda nake zuwa da ita aiki na dauko pen da farar takardar na rubuta sunanki "Aisha" domin shi ne sunan da na fi so, na saka a saman jikin ki sannan muka zagaya ta bayan gidan muka aje ki. Ni da ita muka yi ta gudu muka barki kina kuka, ni ma ina kuka. Tun daga ranar mafarkinki be bar ni ba, ban kuma sake zuwa aikin ba, an aiko har inda nake nemana na sanar musu ba ni da lafiya, da kansa ya zo dubani amman ban fada masa ba, matarsa ma ta zo duba ni ita ma bata sani ba. Tsoron yadda duniya zata kalle ya saka ban waiwayeki ba, wata kila sun ga kin yi kama da turawa ne suka saka miki Emily, ko kuma basa bukatar musulmai ne, domin bayan na aje ki na sake bi da gurin sai na ga gidan marayun na Christian ne karkashin kulawar wata coci. Daga lokacin kuma zaman garin be sake min dadi ba, sai na tattara na koma garinmu da zama, dan abun da na tara na cigaba da kasuwancina da shi, ban yi wata uku na miji aure ya fito min daga dangin mahaifiyata na aure shi, ba mu dade ba ya rasu kuma ban haihuwa da shi ba, bayan rasuwarsa rayuwa ta cigaba na kama sana'a duk inda na ji ana neman aiki na kan kusa na nema ni ma, amman ban yi nasara ba sai a wani banki da ke kusa da mu. Sanadin wannan aikin na hadu da mijin da nake aure yanzu, kasancewar dan kasuwa a wacan lokaci ya kan siya abubuwa daga arewa ya shigo da su gurinmu, na gurinmu kuma ya dauka ya shiga da su, wata rana ya samu matsala ya zo bank a nan muka hadu. Har ta kai ya san gidanmu ya fada min labarinsa kuma ya nuna yana son ya aureni, da farko iyayena ba su amince ba, saboda suna ganin bahaushen mutum baya rike aure tun a wacan lokaci sai dai kudin da yake da su sun taka rawa gurin amincewar iyayena, ni kuma ina hangen yadda bahaushe yake wadata matarsa da komai ba sai taje nema ba, a wacan zamanin mazan hausawa suna daukar nauyin dawainiyar iyalansu ne. Da haka aka amince muka yi aure ya dawo da ni gidansa a garinsu, a nan kuma wani tashin hankali ya same ni, domin matarsa fitinanniya ce yayansa kuma fitsararru ne, sai dai yarda da yake da ni da kuma yadda yake kaunata ya taimaka min wajen jure zama da su, sannu a hankali likkafa ta yi gaba arziki ya kara bunkasa har siyasa ta shigo ciki, zuri'a kuma ta samu, ta karkashin kasuwancin ya zama bashi da uban gida sai Alhaji Bello Bulama wani mutumen Maiduguri ne wanda ya shahara ciki da wajen kasar nan ta bangaren kasuwanci. Ba zan yi karya ba, mijin da nake aure a yanzu yana sona sosai domin ba ni da hayani duk kuwa da kasancewa ta bayarabiya wasu sukan ce yarbawa suna da fada, amman ni na sha banban, kuma na rike matarsa da yayansa da amana, sannan ni ce yar boko kusan duk inda zai shiga da ni yake zuwa, idan wani abu ya taso ma kasuwanci na kan ba shi shawara kuma idan ya bi sai ayi nasara, wannan ya saka har maigidansa ya san da ni, da muka tafi gidan muka samu tarba daga matarsa wacce ta kasance mai son mutane kuma ita ma yar kasuwa, muna gaisawa ni da ita muka gane juna, ita ce matar da na yi aiki da mijinta kuma mijinta ya amintar da ita da ni. A nan ta fada min sun rabu da mijinta saboda baya son haihuwa kuma yana da wata mata a can bata sani ba sai da lokacin da zai koma garinsu yayi ya koma da ita, daga baya ta gano yana da wasu iyalan kuma ita baya son ta haihu da shi, ashe a can idan ka saki mace sai ka bata rabin dukiyarka musamman idan akwai yara, ta shigar da kara kotu ta rabu da shi aka danka mata dukiya mai yawa sai ta siyar da komai ta bar kasa ta dawo garinta na Lagos ta fara kasuwanci ta fada min bayan dawowarta yarta ta rasu ya rage yaro ne kadai take da shi. Ta sake wani aure sai ta auri musulmi wanda ya kasance Alhaji Bello Bulama, mai gidan maigidana a bangaren kasuwanci, da haka ni ma na shiga cikin mukarrabanta, ta ja ni a kusa tana saka ni cikin huldodinta. Idan mijinta yayi tafiya ya dawo ko'ina mai gidana yake zai aje abun da yake yaje ya yarboshi, ba shi kadai ba kusan duk yaran da suke karkashinsa haka suke, idan zai tafi daga Kaduna tare muke zuwa saboda yana ganin mun san juna ni da ita kuma muna da kyakkyawar fahimta. A lokacin da suka dawo daga Sudan muka tarbe su har ta hado ni da ke, ina ganinki jikina ya ba ni, ba na gane ki ba, na sanin ni ma ina da ƴa mai kama da turawa a wani gurin da ban sani ba ko tana raye ko a mace, amman daga lokacin da muka shigo jirgi kika ba ni labarinki sai na kasa rike kaina a kamaninki suka bayyanar min fuskar mutumen da na bi son zuciya na biye masa na lalata rayuwata. Na tsorata kuma na yi bakinciki da halin da na ganki kuma kika fada min domin ni ce silar komai na san dole ina da kaso mai tsoka na zunubin abun da na aikata da kuma yadda kika tsinci kanki a matsayin kirista, mun shigo gidana kamin na haura sama na sauko kin gudu, a lokacin na ji babu dadi, amman ban neme ki ba saboda ban san yadda zan fuskance ki ba, kuma ban san kalar amsar tambayoyin da zaki min ba, kuma ban san da wane ido zan kalli yayana da mijina ba, ga ni da kishiya mai zafin kishi da yayanta marasa tarbiya. Amman a yanzu na gane kuskurena na fadawa mijina komai kowa ya san ke yata ce, a daren da na mari Kameela mahaifinta ya same ni da zance tare da neman dalili na fada masa komai ban boye ba, sai ya zabi ya sake ni amman baya son na bar gidan saboda yaransa da kuma gudun makiya kar su masa dariya, yace na yi zaman yayana. Ni kuma na amince na zauna ne kawai saboda baki zo ba, na fadawa yayana daga lokacin da muka gano inda kike kika dawo gareni, zan koma gidana da na siya ne mu zauna ba a gidan da zaki ji wata magana marar dadi ko ayi miki kallon banza ba, idan sun yarda sun ni falillahil Hamdu, idan kuma suka zabi zama gidan ubansu, ni dai ke ce damuwa Aisha... Tun da Mama Baraka take bata labarin Emily ta rufe fuska tana ta sharbar kuka. Mama Baraka ta sauka kwanta a kasa irin na mai neman gafara ta hade hannayenta ta kama kafar Emily tana kuka sosai mai cike da nadama. "Ki yafe min, ki yi hakuri ban kyauta ba na sani, ban sauke nauyin da Allah ya dora min ba na ki, kuma na zalince ki, hakkina yana nan akaina, ku ma yaya kuna da na ku hakki akan iyaye, ki yafe min Emily ki karbe ni, "Ẹ jọ̀wọ́, ẹ dárí jì fún mi. Mo ti dá aiyé mi ru, Ẹ jọ̀wọ́, ẹ dárí jì. Mo ti ṣàìṣe, mo ti wàhálà gan-an" Emily ta kama hannyen mahaifiyata ta rike ta mikar da ita zaune tana kuka. "Idan ban yafe miki ba me zan yi? Zan hukunta ki ne? Zan doke ki ne? Mai faruwa ta faru, komai ya afku rashin yafiyar ba zai dawo da rayuwar baya ba, ba kuma zai cire ni daga kangin da na shiga a baya ba, amman na dauki darasi mai girma kuma na jidadi da ban tafi na bar nawa yaran ba, ina alfahari da haka" Ta sake hannayenta ta mike tsaye ta fice daga dakin ta nufo downstairs. Aliyu Ummi da Fatima Nafeesa suna dinning suna karyawa Emily ta sauko da kuka ta nufi gurin da Fatima take ta dauketa, ta rumgume. "Momy are you okay?" Fatima ta tambaya ganin tana kuka kuma ya rumgume ta sosai. "Karki sake zabar kowa ki bar ni, na wahala na rana da dare na ratsa wuta, amman ban taba sha'awar tafiya na barku ba" Aliyu da tun da Emily ta sauko ya mike tsaye ya kalli Mama Baraka data sauko ita ma tana kuka ta yi zaton ko Emily zata gudu ne, Fatima ta labe jikin uwarta kamar ba ita ba, Emily ta juya ta haura sama tana dauke da yarta sai hawaye take. "Mama lafiya?" Aliyu ya tambaya. "Lafiya kalau ka fada mata komai da take son sani ne" "Okay, amman ki dan bata lokaci yanzu, ki tafi gida na miki alkawari da kaina zan kawo miki Emily idan ta huce" Mama Baraka ta amsa masa da kai sannan ta hade hannayenta zata musu godiya tana bude baki sai ta fashe da kuka ta zube a gurin. Ummi ta taso ta zo tana bata hakuri. TURHAN POV. Da gadon yaki masa dadi gashi bachi yaki ya dauke shi sai fito dakin ya sauko kasa ya zauna falo a nan ma ya ji ba shi da natsuwa saboda Fatima bata gidan yau, haka kuma be samu saka Emily a ido ba, ga bakinciki kallon matarsa da zama gida daya da ita da abokinsa yake babban makiyinsa a yanzu, ba zuciyarsa ba jikinsa ma ya gagara yin dadi komai ya yamutse masa. Ya bude kofar falon ya fita ya zauna a balcony abun da be taba ba, sam be san damuwa na hana bachi ba sai a yanzu da yake kokarin ganin ya gyara tsakaninsa da Emily. Ta ina zai fara.? Gaba daya Aliyu ya bi ya tare masa kofa babu ta inda zai leka balle ta hangeshi, duk wani yunkuri da zai yi da zarar ya tuna cewar Emily tana gidansu Aliyu karkashin kulawarsu sai yaji ya karaya, abu da ya sani idan yayi sanyi Aliyu zai kwace masa mata ne shi kuma ba zai jure hakan ba. Ya mike tsaye ya sauka balcony yana safa da marwa a gidan kar kace ba karfe 3 dare ba ne, ya dade a haka yana ta sake sake sannan ya juya ya koma ciki ya rufe kofar, dakinsa ya shiga yayi alwala ya fito daga bandakin ya nufi corner da yake ibada a dakin ya fara sallah. Daman Larabawa sukan ware wani bangare a dakinsu da suke shimfida Carpet su aje qur'ane ana saka turare domin ibada. Be daga daga carpet din ba har aka yi sallah asuba. Bayan ya gama sallah bachi mai nauyi ya dauke shi, be farka ba sai da ya ji yatsun Ammy cikin kansa, ya bude ido ya kalleta sai ta yi murmushi tana cigaba da shafa kansa. "Ṣabāḥ al-khayr yā Ammy" Ya furta da murmushin karfin hali, ta amsa masa cike da kauna irin ta uwa da ɗa. "ʿĀmil shinu yā waladī? Allāh yiḥfaẓak lī. yā ḥabībī yā waladī? Keif ḥālak?" Ya daga kadan ya kwantar da kansa kan ciyarta. "Babu dadi Ammy" "Ka raya dare da damuwa ko? Ni ma jiya na ji babu dadi saboda Fatima bata gidan, amman dai yau za mu tafi gidan" Ta sauke kansa. "Kwanta ka samu bachi, kana da bukatar kuzari ɗana, Allah ya maka albarka" Ya lumshe ido bayan ya amsa da Ameen, Ammy ta tashi cike da tausayin danta da kuma bacin ran halin da yake ciki ta fice dakin. [8/6, 11:10 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 6️⃣3️⃣ "Ya kamata na koma haka, ance sun dora wani ma" "Ba fa inda zaka je sai an kama yaron nan, mutumen dake neman ranka zaka koma garinsa ka zauna da sunan aiki, daman can ni bana son aikin da kake a kuda mutanen nan ba su da kyau" "Abun da Allah ya rubutawa bawa baya wuce Ummi, kuma ai yanzu guduwa yake ba zai iya komai ba" "A nan din ma kasan ko yana nan yana haka maka rame? Ba zan barka ka koma ba, idan ma suna son aiki da kai su dawo da kai Abuja ko nan Kaduna" "Idan kuma suka ki fa" "Sai ka bar aikin dole? Ina za a kusa kai da kai a kasar nan baka samu aiki ba? Ga ka da cancanta kuma ga alfarma ta ko'ina, kasan ko bangaren President muna yan gaba gaba" Aliyu yayi murmushi mai sauti. "Ummi wato dai abun da ake fada na yan siyasa da gaske ne, daga kansu sai iyalansu?" Ummi ta yi dariya. "Gurin Surukinka muka koya, kasan ya fi kowa son kai" Aliyu yayi murmushi, shi da Ummi suka juya suka kalli kofar falon da aka turo. Ammy ce ta shigo da sallama fuska ba yabo ba fallasa, Ummi ta amsa mata ita ma tana dan sham kamshi domin abu daya ne Ummi bata yarda da shi ba, shi ne raini wayo ko wulakanci, bata daukar rashin girmamawa daga gurin kowa wannan dalilin ne ya saka suke kara samun rashin jituwa da mahaifiyar Kameela. "Ammy ce a gidan ba mu?" "Ai dole za ku gan ni tun da surukata tana nan, ya muka iya da abun da ya fi karfin wuta, fatan na same ku lafiya" "Lafiya Ƙalau sai Alheri da ke ta shigo mana" Ammy ta yi tsaye bayan Ummi ta amsa mata. "Bismillah Ammy ki zauna" "Aa ba zama ya kawo ni ba, Aisha tana ciki?" Ummi ta yi murmushi. "Tana nan waje, idan kika fita ki zagaya dama kadan gurin Garden tana can ita da jikarki" "Ammy ina wuni" Aliyu ya gaisheta yana sirina. "Lafiya" Ta amsa tare da juya bata ko kalleshi ba. Sai da Ammy ta fice sannan Aliyu ya sauke ajiyar zuciya. "Ammy fushi take da ni, ban jidadin yadda abubuwa suka zo ba, ko kadan Kameela bata kyauta min ba, na so na tsara abun nan cikin hikima ba tare da kowa ya ga laifin kowa ba, Allah ya sani da zuciya daya na yi wannan abun ban yi nufin cutar da Turhan ba, na shiga tsakiya ne kamin na hankara tausayin Emily ya rinjaye ni, sai na fi fifita matsalarta saboda ina ganin ita ce tafi shiga matsala, har gobe idan na tuna abun nan sai na ji zafin abun da Kameela ta aikata" "Ai ni ba karamin taimaka min ta yi ba da ta yi haka, da yanzu ban san miye yake faruwa ba sai idan ka mutu ace ai ka ci guba, ko kuma ka ta daba maka wuka, ka ga masu shegen kishin nan tun wuri ana ganin abun da suke iya aikawa daga musu kafa ake ana ganin kamar ba komai ba ne, da yanzu bata yi wannan shirmen ba ba zaka fada min ta zuba maka guba ba, kuma ai ka kasa sakinta" "A lokacin ina kokarin bata hakkinta ne, hankalin namiji baya taba zama iri daya na mace, ina daga mata kafa da uzurine amman ko a lokacin na yi alkawarin ba zan sake cin abincinta ko kwanciya daki daya da ita ba, and zuwa nan da na yi saboda ita ne Mama Baraka ta kira ni, da na zo kuma mahaifinyarta ta wulakanta, sai kuma ta aikata min

Chapter 50 of 63