yi ai ba shi da amfani yanzu tun da ta riga ta san gidan Ammy, daman sau daya ta taba zuwa shi ma kuma Aliyu ne ya kaita.
"Dan ubanki gurin uwar ubankin zan kaiki, ayi ta ta kare, na huta da wannan bibiyar da uwarki take ma mijina, sai kace shi yake nemanta, ga mai nemanta ga wanda take likewa, ina na taba ganin haka dan kawai neman a dora min hawan jini"
Bata sha wahala gurin gane gidan ba kasancewar unguwar ba a boye take ba, kuma gidan babban gida ne a layin, tana isa bakin gate din gidan ta gane lallai gidan dai da suka taba zuwa da Aliyu sau daya. Ta yi horn mai gadin ya bude mata ya shiga ciki ta faka ta zagayo ta budewa Fatima ta riko hannunta ta fito da ita.
"Ina yake?"
"Yana ciki sai mun shiga"
Fatima ta bita babu wani rigima suka shiga cikin falon, tsabar neman fitina da tsoron abun da zata aikata da kuma bakin kishi da suka hade mata guri daya Kameela har numfashi take sama sama kamar wanda ta dauko katon dutse. Da sallama ta shiga falon Yan matan nan biyu da Ammy take riko suka amsa mata, Ammy na zaune kan kujera nurse na kusa da ita tana hauna bp dinta, daman ta fi yawan zaman falon gudun wahalar da mazu zuwa ganinta ba sun haura sama inda take ba.
"Ina yake?"
Fatima ta tambaya da karfi tana fisge hannunta daga rikon da Kameela ta yi mata. A take Kameela ta daka mata tsawa ta watsa mata harara.
"Ki zauna"
"Ba zan zauna ba, ina Uncle Aliyu? Kina kokarin sace ni ne? Su waye wadannan mutanen mama na tace kar na yi magana da wanda ban sani ba"
Ta saka ihu mai karfi babu saurara ahhhhhhhhhhhhhhhhhhhhh ta cika musu kunne. Ammy ta kalli Kameela tana tambayar tafiya, Kameela ta rasa ta ita zata fara bayani ga Fatima na mata ihu gashi bata san yadda zata fara warware zaren zancen ba.
Ihun Fatima ne ya saka Turhan dake dakinsa cikin damuwa ya saukowa kasa domin duba abun da ke faruwa. Saukowa da Turhan yake ne a hankali ya saka Ammy daga kai ta kalleshi daga kansa ta sauke idonta akan Fatima dake ta ihu, sai gata a tsaye kamar ba marar lafiya ba. Ta ko'ina Fatima kama take da Turhan kamar an tsaga kara kamar har ta bace har gashin kanta baki ne kamar na mahaifinta sai ka rantse tsumata aka yi a cikin jikin Turhan aka ciro bata rage komai nasa ba, banbancin kawai ita mace ce shi namiji kuma ita tana karama shi kuma babba.
"La'ilaha illallahu, La'ilaha illallahu, La'ilaha illallahu"
Kawai Ammy take maimaitawa jikinta na rawa hawaye na sauko mata.
"Yauwa kin gane kenan"
Kameela ta fada kamin ta juya ta kalli Turhan daya tsaya be karaso ba, bata san yana garin ba sai a lokacin.
"Alhamdulillah faduwa ta zo daidai da zama"
Ta fada tana kallon Turhan da gabansa ke dukan uku uku ba kuma tare da fahimtar komai ba, shi dai ya san ba lafiya ba, ganin yadda Ammy take ta ambaton Allah ta mike tsaye ga kuma yarinyar dake ihu ga kuma Matar Aliyu.
"Ka karaso mana Turhan wannan yarka ce"
Turhan ya kalleta ya kalli Ammy.
"Ban fahimta ba"
"Yarka ce sunanta Fatima, Emily ta haife ta muma jininka ce Aliyu ma da kansa ya fada, tana boye maka ita ne tana boye maka kanta, ni na gaji shiyasa nake son ayi ta ta kare shiyasa na kawo ta, na gaji dan Allah idan ka ga Emily ka rike ta na huta, na samu kwanciyar hankali da mijina, ta kyale min mijina dan Allah duk wani boye boye da ake ban gane kanshi ba, matar nan ta hana ni zaman gidana cikin kwanciyar hankali abun ya wuce PH ya biyo har nan Kaduna na gaji, Aliyu be san na kawo ta nan amman na san dole Emily zata zo"
A cikin kalamanta babu wanda Turhan ya ji kuma ya fahimta sai kalmar ƳARKA CE... kalma ta maimaita kanta a kunensa ya fi sau saba'in tun da ya dora idonsa akan Fatima be kyabta ba, sigar jikinsa kawai ke tashi zuciyarsa ta karaya bugun zuciyarsa ya karu fiye da kima, sai a yanzu ya fahimci Ammy na ambatar Allah ba tare da an bata mata ba, kamaninsa ne sak a fuskar Fatima.
"Ke dalla dufewa mutane baki kin ga ubanki can"
Kameela ta fada ma Fatima da turanci tana nuna mata Turhan. Sai Fatima ta lake kafada ta fara magana cike da tsiwa da iyayi.
"Noooo Momy ta fada min ni bani da Baba ni kadai aka haifa haka, kowa yana da Baba amman Momy tace ni ba ni da Baba baki kiji sunana ba Fatima Emily Aisha"
Turhan ya zube kasan guiwowinsa ya daga kansa sama ya bude baki yana numfashi da karfi kamar wanda zai mutu. Fatima ta fashe da wani irin kuka mai karfi na gaske domin bata fahimci me suke ba, gashi bata san kowa ba a cikinsu yanzu kam ta fara tsorata.
"Take me back to uncle Aliyu or Momy"
Kameela ta buge hannu. Ammy ta karasa ta dafa Fatima tana kuka ta kama fuska tana kallo, ta zube a gurin tana ta taba taba jikin Fatima
"Allah na gode maka, Allah Aisha kawai nake nema amman ka hado min har da yarta, jikata Allah na gode, Allah ya miki albarka Kameela"
Kameela dai bata ce komai ba ta juya ta fice da sauri.
"I want my momy"
Ammy ta dorata a cinyarta tana kuka ta rumgumeta. Turhan ya ka dagowa daga inda ya fadi durkushe ya kara karasa gurin da Fatima take jikinsa da zuciyarsa sai rawa suke abun ya zo masa kamar mafarki, ya rasa ta yi zai yi ya yarda wannan abun ba mafarki ba ne, shi dai Emily kawai yake nema shi ma kuma saboda Ammy. Da rarrafe ya karasa gurin tana kallon Fatima ya kai hannunsa zai taba ta sai ya kasa ya maida hannu, ya shafe hannunsa jikin rigarsa gaba da baya kamar mai kokarin cire kazanta ya sake mika hannunsa zai taba ba a nan ma ya kasa jikinsa sai rawa yake.
"Yarka ce Turhan, jinin ya fi ruwa kauri, jini be karya, yarka ce"
Ammy ta kama hannun Turhan ta kai a jikin Fatima, sai ya ji wani abu kamar shokin Fatima kuma ta zabura da karfi, a take ya tuna da abun da ya faru a airport lokacin da suka hadu da Aliyu ya taba babyn da yake dauke da ita tana bachi amman sai da ta zabura. Turhan ya fisge Fatima a jikin Ammy ya rumgumeta da karfi jikinsa ya mike tsaye yana kuka kamar wani karamin yaro, a take kukan Fatima ya yanke ta yi shiru kamar ba ita ba, ita m ta ji wani abu na dabam gashi ta ji yana kuka bata san dalilin ba, daga tsayen kukan ya kasa rike shi ya zube kasa yana rumgume da ita, kusan kowa a falon kuka yake har Nurse din da bata san hawa da sauka ba. Ammy ta daga hannunta tana magana.
"Haka na yi nufi, ku zauna tare ku yi zuri'a ta dalilina, Alhamdulillah ko a yau na mutu burina ya cika, na ga jininka Turhan, ashe ba a banza na ke jin bukatar ganin yarinyar nan ba, ashe akwai abun da Allah ya shirya min da ban sani ba Allah na gode"
Ta shafa kan Fatima ta shafa kan Turhan hawaye da murmushi, Turhan ya kwanta jikinta yana rumgume da yarsa Fatima. Wayar dake Hannun Fatima ta yi ringing Turhan ya dago da sauri ya karɓi wayar, Emily ya gani rubuce a wayar ya amsa kiran amman ya kasa cewa komai.
"Hello Fatima My Baby Girl where are you?"
Muryar da ya dade yana nema ta daki kunensa, amman ya kasa amsawa.
"Hello baby girl talk to me, ina kike?"
Muryar matar daya wulakanta ya nuna mata rashin gata da kiyayya ce take sake magana, ya rasa ta ina sauti zai fito daga bakinsa.
"If you hurt my baby Kameela, sai na kashe ki Wallahi sai na halaka ki"
Daker ya iya hada kalmomin bakinsa cikin wata iri siga ta kwantar da hankali da rarrashi da be taba sanin yana da ita ba ya furta.
"Your Baby is in safe hands....Aisha.... Emily...."
Daga nan be sake jin komai ba, aje wayar yayi ya kara rumgume Fatima a kirjinsa yana motsawa a hankali kamar wanda ke rike da sabon kwai.
"Momy ta fada min ba ni da mahaifi waye kai?"
Fatima ta tambaya tana ta sauke ajiyar zuciya na kukan da ta yi da karfi, Turhan ya girgiza kai ya rufe ido ya kasa cewa komai.
KAMEELA POV.
Ta kama hanyar komawa gida wata zuciyar na raya mata ta koma ta dauko yar mutane abun da ta aikata zai batawa Aliyu rai, wata zuciyar kuma na raya mata abun da ta aikata daidai ne domin idan ba haka ba Aliyu ba zai fita sabgar Emily ba, gashi abun har ya fara wuce gona da iri, ta san yadda Emily take da kyaun nan komai zai iya faruwa, idan ba haka ba bata ga dalilin Aliyu na boyewa Turhan lamarin ba. Ta isa ta faka motar waje ta fita ta shiga dakinta amman ta kasa natsuwa gabanta sai faduwa yake tana ta jin tsoro da tunanin abun da Aliyu zai fada mata, iyakar abun dai yayi fada yayi fushi, ko kuma yace ba zata koma yanzu ba, idan kuma ya wake ni fa? Ta raya ma kanta. No ba zai ma taba farawa ba da na saka masa guba ma be sani ba balle dan wannan.
Kiran wayar Aliyu na shigowa wayarta sai da ta zabura tana kallon wayar har ta gama ringing bata daga ba, ya sake kira baya daga ba har yayi mata kira uku, tasowa ta yi ta fito daga dakinta ta zauna falo tana ta sake sake ta san ko ta koma Turhan ba zai bata yarinyar nan ba, ko da ya bata ai aikin gama ya gama ta fada musu komai, ta saka wannan ta kwance ita kadai ita dai babban hujjarta ita ce Emily tana kokarin anshe mata miji alhalin ga mai nemanta har da ya a tsakaninsu. Tana jin tsayawar mota ta leka Window ta hango motar Aliyu sai ta nufi kofar falon da sauri ta bude kamin ta saka kafarta waje har ya iso bakin kofar falon cikin wani irin yanayi da bata taba ganinsa a ciki ba, kuma bata taba tsorota da bacin ransa kamar na yau ba.
Baya baya ta yi hakan ya ba shi damar shigowa falon fuska kamar bakin hadari.
"Ina yarinyar da kika dauka take?"
"Tana gurin da ya kamata ta kasance, gurin mahaifinta"
Aliyu ya dauke ta mari da bayan hannunsa, sautin mari yayi mata chauuuuuuu har cikin kunen, ta dafe kuncinta ta zaro ido kamar za su fado.
"Saboda wata banza zaka mare ni a cikin gidan Ubana Aliyu?"
Ta daga hannu zata rama ya rike hannu ya jefar ya sake sauketa da mari sai da ta fadi. Mai aikinsu ta fito da sauri, kanwarta Farida ma ta fara saukowa da gudu. Aliyu ya nunata cikin tsananin fushi.
"Abun da kika aikata ba kishi ba ne, hauka ne da rashin tunani, kin dauki yarinya kin dankata a gurin mutumen da bata taba sanin waye shi a duniya ba, kin rusa abota da aminci da ke tsakanina da Turhan na shekaru da yawa, kin yi sanadin karya alkawarin da na daukarwa Emily, kin zubar da kimar da Ammy take kallona da ita, wace irin mace ce ke? Alkawarin da na miki be wadatar ba? Bibiyar wayata be gamsar da ke ba? Kokarin kashe ni be saka kin natsu ba? Toh babu abun da zai sauya halinki Kameela, na gaji ko diamond ce ke haihuwar gold na hakura dake Kameela, na dauki abun da zan iya dauka yanzu kam anyi na karshe... NA SAKE KI... Enough is enough"
Ya fada kai tsaye sannan ya juya ya fice daga falon ya koma motarsa, yaja ya fice daga gidan rai a bace, gidansa ya sake komawa domin a can ya baro Emily. Ya shiga cikin gidan ya faka ya fita motar ya shiga falon gidan, tsakiyar falon ya samu Emily duke dafe da kanta wayarta kuma a kasa.
"Emily..."
Be fadi abun da yayi nufi ba ta katse shi.
"I want my baby"
"Ta... Ta... Tana.... Gurin... Turhan..."
"I know ka kawo min yata, ba zan je can ba saboda bana son ganinsa bana son jinsa"
"Okay but i want you to know ba ni na shirya wannan ba?"
Ta mike tsaye ta daka masa tsawa.
"To waya shirya?"
"Calm down Emily ki kwantar da hankalinki"
Ta zaburo masa ta yi cikinsa da masifa idonta na cika da hawaye.
"How dare you told me that? Kana son kwanciyar hankalina ka taho min da ƴa? If you didn't plan all this taya ka san Turhan ya zo? Meya ka zo garin nan just for two days? Ka taho da Fatima ba tare da na sani ba ba, that's means ka san da wani abu Aliyu! Zuwa ba tare da ka sani ba ya rusa yadda ka tsara abubuwa shiyasa ka saka matarka ta dauke ta kamin mu zo ta kaita gurin Turhan right? Saboda ka san ina son yata dole na kai kaina a gurinsa ko? Ka min alkawari Turhan ba zai taba sanina ta hanyar ka sai idan ni na bukata, ina alkawarin yake? Ka ci amanata ba zan sake yarda da kai ba Aliyu, kallon da nake ashe ba haka kake ba, ka dawo min da yata Aliyu"
Wani irin ihu take kamar zata tashi gidan sai da Aliyu ya ji wani tsammmmm yayi baya ya runtse ido ya bude saboda tsawar dake saka masa, ya juya da sauri ya fita a rikice. Motarsa ya koma ya koma ya shiga ya dauki hanyar gidansu Ammy.
Zuciya a karye jiki a sanyaye kunyar yadda zai yi ido hudu da abokinsa ya rufe shi amman a haka ya daure ya shiga gidan saboda Emily ya san idan be dawo mata da Fatima ba ba zata taba yarda da shi ba, kuma ya san gaskiya idan ba shi ya dawo da Fatima ba Turhan ba zai bata yarinyar nan ba.
Be raina kansa ya kara girmama laifin da Kameela ta yi ba sai da ya isa bakin kofar falon Ammy for the first time ya ji kunya da nauyi tura kofar dakin ya shiga, yayi unkurin fasawa ya fi a kirga kamin ya samu kuzarin tura kofar ya shiga da sallama.
A tsaye ya riski Turhan yana maida hannayensa duka biyu a baya ya daure fuska yana kallon kofar falon da alama yana jiran shigowar Aliyu ne. Aliyu be taba gani abokinsa a cikin irin wannan yanayin ba sai yau. Aliyu ya gagara furta komai sai kallon Turhan yake babu kowa a falon sai shi kadai.
"Fatima ka zo nema ko ka zo ka shirya wata karya ne? Ka ba ni mamaki Aliyu, daman ance acikin abokai da yan'uwa akwai makiyan mutum a yau na yarda, me na maka? Miye manufarka na boye Emily? Matar da ka san nemanta nake ido rufa? Matar da saboda ita mahaifiya ta gagara fahimtata har take ciwo? Abun bakin ciki kuma da kai nake shawarar nemanta? Har a airport na hadu da kai amman ka gagara cewa yata ce? A tsawon lokacin nan a tsawon wahalar nan ka san inda Emily take ka boye min? Da kai muka zo nan kana jin kalaman Ammy akaina amman ka gagara furta cewar ka san inda Emily take? Miye manufar ka? Wallahi kallon mutunen kirki nake maka aboki da ya juye ya zama kamar dan'uwa amman a yau wannan duk ya kau... Ka zama koren maciji a cikin korayen ciyayi, mutum mai fuska biyu! But thanks to your wife daman haka abun yake ka ci amanar wani kai ma aci taka, ta bayyana komai a lokacin da ya dace"
Har lokacin Aliyu ya rasa abun cewa tambayar ina Fatima take ma ya gagara yi, Ammy ce ta fito dakin dake kasa a falon, Aliyu ya kalleta cike da kunya da nauyi, ya ambaci sunanta wai ko ita zata fahimce shi.
" Ammy..."
"Aa Aliyu ban da yau, da ka dauke ni uwa da baka aikata haka ba, na tabbatar da Ummi ce ba zaka aikata mata abun da ka aikata ba, ka ba ni mamaki shiyasa hausawa suka ce halin mutum dabam kalamansa dabam, bana son wani abun bacin rai dan Allah ka tafi"
Ya juya ya fice daga falon tsabar kunya da bakinciki yana jin kamar kasa ta bude ya shige ciki ta rufe da shi, yana tafiya yana jin kamar ba kafafuwansa ba, haka dai ya shiga mota ya sak juyawa ya fice gidan sai kuma ya rasa ina zai tafi, ya san be isa ya koma gidansa ba tare da Fatima ba to yace ma Emily me? Haka kuma be isa ya dawo ya ce Turhan ya ba shi Fatima, gaba daya sai ya rasa ina zai saka kansa, gefe hanya ya faka ya bude motarsa ya fito yana sauraren kiran sallah da ake ko zai samu sallama. Shi ma dai yau ya zama marar mafaka be da wani gurin fakewa sai gurin mahaifiyarsa, wayarsa ya ciro ya kira Ummi tana dagawa ya ce.
"Ummi ki min addu'a dan Allah"
"Lafiya Aliyu"
"Ba lafiya ba, kawai ki min addu'a ko zan samu mafita"
"Ka daga min hankali wace irin addu'a zan maka? Me yake faruwa?"
A takaice ya labarta mata abun da zai iya na haduwarsu da Emily zuwa abun da ya faru yau.
"Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un, abu be yi dadi ba Aliyu ka yi sakaci na shiga tsakanin mutane biyu, gashi Allah ya baka mata da bata dace da kai ba ta jefaka a kunya, sannu a hankali idan baka rabu da yarinyar nan ba, nan gaba kadan ma sai ta yi kokarin kashe ka"
"Already ta gwada Ummi ta saka min guba a abinci saboda Emily, amman ban ci ba sanadin haka na maida ita gida Mama Barakat ta ba ni shawarar maida ta na dawo ne wannan abun duk ya faru, but i divorced her today"
"Guba kuma..... Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un..."
Ummi na rufe baki ta ji Aliyu ya amsa yana fadin Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un da karfi sai maimaitawa yake wayar ta fadi yana nishi da karfi sai karar abu take ji kamar ana dukansa.
"Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un.... Aliyu.... Aliyu.... Lafiya? Kana ina?"
Baya ina magana sai karar take ji kamin ta soma jiyo hayaniyar mutane sai kuma kiran ya yanke.
"Sun kashe min ɗa sun kashe min ɗa, ko dai Turhan ko ita yarinyar ko Kameela sun kashe min ɗa, Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un..."
Ta fada da karfi tana fitowa dakinta da gudu har tana zubewa kasa ta tashi tana kuka.
TURHAN POV.
Bayan Aliyu ya wuce ya ji ba zai iya natsuwa ba ya haura sama ya dauko keys din mota ya sauko keys din a hannunsa.
"Ina zaka je?"
"Gidan shi zan tafi ba mamaki Aisha tana can, ina bukatar ganinta kuma ba zan sake bari ya keba da ita ba"
Ya fice da sauri ya shiga motar da ya dauko key dinta mai gadin gidan ya bude masa ya fice, Ammy fitarsa da mintuna kadan Ammy ta kasa natsuwa da hakan ta dauki wayarta ta kira direban ta ya shirya mota ta saka hijabinta ta bi bayansa.
@360 Turhan ya isa kofar gidan Aliyu, yayi horn da karfi babu daga kafa mai gadin ya fito a tsorace ya leka motar.
"Me gidan baya nan"
"Bude min Malam"
Turhan ya fada da karfi mai gadin ya kuma ciki yana fadin
"Allah yasa lafiya wannan lamari dake faruwa"
Ya bude masa gate din Turhan ya shiga habarta gidan ko fakin din kirki be yi ba ya fita motar ya doshi kofar falon Aliyu ya tura kofar ya shiga Emily na zaune kan kujera ya duba ko'ina a gaggauce ya nufi sama ba dan be ganta ba sai dan tunaninsa da idonsa ba su zayyana masa matar da ya gani zaune a falon a matsayi Emily ba, sai da yayi rabin stairs din idanuwansa suka dawo masa da kamanin jan gashin da ya gani a gurin mace da ya tarar a falon sai ya tsaya cak ba tare da ya juyo ba, yana kokarin kamanta Emily da wannan matar da ya gani a yanzu. Ya juyo ya kalli Emily da ko kadan bata kalli inda yake ba, sun yi kama ta gashi da hasken fata har ma a fuska amman wannan ta fi Aisha da yake nema kyau da tsari sau miliyan ma, to amman idan ba Aisha bace to wacece? Ya sauko yana kallonta har ya karasa inda take zaune ya tsaya gabanta zuciyarsa kamar zata fado, tsabar kwarjinin da ta cika shi da shi.
Sai a lokacin Emily ta mike tsaye ta kalleshi. Cikin tsakanin mamaki da kokarin tantance Emilyn din ce ko mai kama da ita ya furta sunanta a zuciyarsa.
"Aisha.... Emily..."
Be sani ba ashe tsabar mamakin be iya rike kanshi ba, daga kasa ya kafara kallonta turawa suka ce from toe to head yana kaiwa saitin fuskarta ya ji sauka abu mai sanyi a tsadaddiyar fuskarsa.
Touf... Ta watsa masa yawu a fuska. Ya runtse ido da karfi ya jimke hannunsa da mugun karfin numfashinsa na fita da karfi, babban wulakanci a gurin balarabe shi ne ka jefe shi da talkami ko ka tofar masa da yawu. Sai dai a yanzu be isa ya nuna komai ba a hankali ya bude idon, ya sake kallon idanuwanta da be taba ganin tsarinsu da kyau ba sai a yau, tassaa ta wanke masa fuska da mari sannan ta kauce gaba gabansa ta nufi kofar fita falon kamin ta karasa Ammy ta shigo falon da saurinta jikin na rawa na son arba da Emilyn da take ta nema tsawon lokaci.
__________________
ABOKIN RAYUWA.... ✍️
[7/6, 9:18 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=KhadeejaCandy
🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
Page 4️⃣7️⃣
Ammy ta nufo ta cike da rawa jiki Emily kuma bata fasa dosar kofar ba har sai da ta ita da Ammy suka yi kicibus a falon, Ammy ta kai hannu zata taba Emily sai Emily ta matsa baya.
"Yata Aisha muna ta nemanki ina kika shiga? Ke ce haka? Ina Ibraheem?"
"Aisha ta dade da mutuwa..."
Emily ta fada, Turhan ya juyo da sauri daman zuciyarsa bata gama gamsuwa cewar wannan din Aishar da yake nema ba ce domin ta canja gaba daya.
"Aisha ta mutu tun a ranar da kika yi son zuciya kika aurawa mugun danki ita, wannan Emily ce ina yata?"
Ammy ta kalli Turhan idonta na cika da hawaye sannan ta kalli Emily tace.
"Aisha ki yi hakuri.. Wallahi..."
"Ba maganarku na zo ji a nan ba, ina yata take?"
"Tana nan lafiya, Aisha dan Allah ki saurare ni mu yi magana, na san kina cikin bakinciki amman yadda zuciyarki take raya ba haka ba ne"
"Where is my baby? Bani da wata alaka da ku, and bana cikin bakinciki ni baki gan ni ba? Na wuce yadda kuke tunani, ina yata take?"
"Tana gidana dan Allah Aisha ki saurare ni mu yi magana, tsawon shekara shida kenan muma nemanki, ba ni da lafiya amman da na ga sanadin ganinki sai na ji na warke, daman ciwon har da ke ne"
Emily ta tabe baki.
"A tsawon shekarun nan Ammy kike tunanin zan sake yarda da shirinki ne? Kin yi amfani da kyautatawarki kika cutar da ni yanzu kuma kina tunanin amfani da ciwonki zai saka na yarda ke sake cutar da ni ne?"
"Wallahi ban yi dan na cutar da ke ba! Duk wani abu da Turhan yayi miki ban san zai miki ba, ban san haka zai faru ba, ki fahimce ni mana wannan duk ba halinki ba ne waye hore miki kunne haka?"
Ammy na maganar cikin kuka domin gaba daya Aisha ta canja mata tun daga shigarta har kalamanta da kamaninta sun sauya.
"Ni da na zauna da kazakin mutum kamar wacan har jira nake wani ya hore min kunne"
"Kina cikin fushi ne kawai har yanzu, da zaki yi hakuri ki bi ni gida zamu karshe duk wannan"
"Har abada ni da gidanki, ba ni ba wata alaka da ke"
Turhan ya karaso gurin yana
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 37 Chapter of 63