Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta kasheni, ban san hawa ba ban san sauka ba, Aliyu ba ni da kowa garin nan sai Allah, bana son wani tashin hankali duk abun da za ku yi ya tsaya tsakaninku da Emily da Kameela ka jawa Emily kunne dan Allah ta daina saka ki cikin rigimarku, babu ruwana sa soyayyar dake tsakaninku da ni dai ina zaune da kowa da zuciya daya" Bata jira abun da zai fada ba ta kashe wayar tana kuka. Ya mike tsaye yana tunanin damuwar Kameela shi ta saka masa guba ta duki Tasmia bayan ta gama haukata akan Emily. Number Emily ya kira domin ya ji dalilinta na turawa matarsa sakon da yayi sanadin da aka duki Tasmia kuma aka kara kunno masa wata sabuwar wutar. Emily ta amsa wayar ba yabo ba fallasa. "Hello" "Emily" "Na'am" "Kina ina? Me kike yi a yanzu" Ta kalli kitchen din da take zubawa Tasmia abun karyawar da Chidimma ta shirya domin ita ta kwana a asibiti ne sai washe gari ta dawo. "Ina gidana" "Wata magana ta shiga tsakaninki da Kameela?" "Aa" "Tasmia fa?" "Meyasa ka tambaya?" "Meyasa kika turawa Matata sako cewar ina zuwa nemanki a gurin Tasmia?" A take ran Emily ya bace "Matarka bata da hankali, wane irin magana ne wannan? Sai kace akanta aka fara aure? Kwanan baya ta yi min cin mutunci yanzu kuma taje ta daki Kameela hakan be mata ba sai ta hada karyar cewar na aika mata sako?" "Karki sake kiran matata mahaukaciya karki sake fadin wata magana marar dadi akan matata, ban kira ki dan ki zageta ta ba, sai dan tabbatar da abun da na ji ko na gani" "Kasan matarka ai zata iya shirya komai saboda da kanta" "Cikin abun da zata shirya har da tura ma kanta sako da Numberki? Emily karki maida ni dan iska mana, na san matata tana da kishi amman idan an ciza dole za a hura ai" Emily ta yanke wayar ba tare da ta sake cewa komai ba, hakan kuma ba karamin fusata Aliyu yayi ba. Keys dinsa ya dauka da wallet ya fito daga hotel din ya shiga motarsa a hanyarsa ta tafiya gida Nura ya kira shi ya sanar masa Dr A-B yana cikin PH. "Ka je ka ganshi misalin karfe tara, na yi magana da Dr Osman zai hada ku sai ku yi magana ya baka ranar da ya kamata ku hadu, idan a Abuja zaka same shi sai kaje idan kuma a zai iya dubata idan ya shigo PH duk daya domin yana yawan shigowa nan aka ce" "Okay na gode Nura zan shirya zuwa 9 na tafi gurin ka turo min address da number Dr Osman din" "Okay" Daga haka suka yi sallama, Aliyu ya koma gidan sai ya samu Kameela ta yi masa gyara, wato ta hargitsa gidan gaba daya ta fashe abubuwan da zata iya fasawa ta watse wasu. Zaunawa yayi kan stairs din ya dafe kansa yana ta ambaton Allah, daya daga cikin dalilin daya saka yayi ma kansa kuma yayi ma Kameela alkawarin ba zai kara aure ba har da gudun tashin hankali da kannan maganganun ashe dai ko a yanzu bw tsira ba. EMILY POV. Cikin bacin rai ta fito Kitchen din, Vito dake zaune a dinning yana karyawa ya bita da kallo. "Jiya baki kwana a gida ba" Emily ta kalli Chidimma, domin ta san Vito baya kwana a gidan balle ya san ta kwana ko akasin haka. "Ni ba karamar yarinya bace, ina da damar na kwana a duk inda nake so" "You're just 25yrs old kuma kina karkashin ikona dole ne na san a duk halin da kike ciki" Ta juyo a fusace "Wai duk wannan gatan da wannan kulawar da ka ba ni ka bani ne saboda ka yi iko da ni? Ka juya ni yadda kake so? Da zarar na yi abu sai kace ina karkashin ikonka bauwa ce ni? Nawa ka biya ka siye ni?" "Babu kudin da zai siye ki a duniyar nan Emily, ina kulawa da shiga da fitarki ne saboda ke Matata ce" "I'm not your wife, ni ba matarka bace ba matar kowa ba ce, and i need another maid bana son Chidimma" Chidimma ta kalli Vito tana girgiza masa kai idonta na cika da hawaye. "Dan Allah karku koreni aikin nan da shi kadai na dogara da shi nake komai na rayuwata" Emily ta dauke kai ta fice rike da abincin, motarta ta koma ta shiga ta dauki hanyar asibitin domin kaiwa Tasmia abun karyawa, bayan bacin ran Aliyu na zarfinta da abun da bata aikata ba, yanzu kuma Vito ya kara mata da shi. Ta faka motar a harabar da aka tanada domin aje ababen hawa sannan ta fito rike abincin ta nufi cikin asibitin, tana tafe ranta da fuskarta a bace kamar zata yi kuka. "Da alama kin fini tsada, shiyasa baki nemi ni ba" Ta karkato kadan ta kalli gefenta sai ta yi arba da fuskar likita daya taba bata katinsa saboda rashin lafiyar London, tare da wani likita a gefensa. "Hi" "Hi, ashe kin gane ni" Ta yi murmushi. "Wacan karon na manta ban tambaye ki ba, are you married? Kar mijinki ya fasa min kai" "No" "Cool, ya mai jikin?" "Ai ya rasu" Ta fada cikin wani yanayi marar dadi idonta na son tara hawaye. "Ayyah... I'm sorry" Ya fada cike da tausayawa. Ta sauke kanta kasa ta cigaba da tafiya har suka isa gurin da zai shiga. "This Way Ma'am" Ta kalli hanyar da zai bi. "No ni nan zan bi, akwai wata kawata da bata da lafiya ita na kawoma abinci" "Toh kuma ba zaki so mu gaisa ba" "Mun gaisa a nan ai?" "Asibitin tana da mutane da yawa, ba zai yayu na siyar da ke ba, ni ma akan hanya nake nan da minti arba'in zan bar garinku" Ya fada yana kallon agogo hannunsa. "Da alama baki san waye Dr A-B ba ki zo kawai ku gaisa" Likitan dake tare da shi ya fada, a yanzu kuma Emily bata da wani zabi daya wuce ta yi abun da ya kamata even though bata san makasudinsa na son hakan ba. Da suka jera suna tafiya yake fadar. "Daman alamu sun nuna min baki da aure, amman na yi tunanin mutumen da ya saka aka nemo ni na duba yaronki shi zaki aura" "Aa" "Kin yaudare shi kenan" "Aa ni bana soyayya da kowa, babu zancen aure a gabana ba zan sake yin aure ba balle na yaudari wani" Ya dan tabe baki kadan. "Ihhh da Alama yan'uwa rijalu sun dandana miki gubar soyayya, kin huta ai, ni ma dai ba a dandana min gubar ba amman soyayya bata burge ni, shiyasa mutane har mamaki suke wai ina da shekara 37 na doshi arba'in kuma ban yi aure ba" Ya bude mata kofar Office din da za su shiga sannan ya tsaya. "Ladies First" Sai da ta fara shiga sannan ya shigo, kana ganin Office din ka san ba na shi ba ne, amman a haka yayi mata gurin zama. [6/3, 8:23 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ FOLLOW ME ON 👇🏻 FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914 TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Page 3️⃣3️⃣ Ya duba agogon hannunsa. "Wani kake jira ne?" Ta tambaya tana jin sakewa da shi kamar yadda ta ji a farkon haduwarsa. Sai yayi murmushi "Abun dariya ne, ni bana jiran wani sai dai a jirani, amman ban sani ba ko abubuwa za su canja wata rana na zo ina jiranki" "Miyasa baka jira?" "Wani mataki ne Allah ya kaini, bana jira sai dai a jira ni saboda kullum na tashi aiko aiki har sai na ture idan ina son hutu, saboda haka ya zama mutane sai dai su jira idan na gama wani aikin sai na fara na su" "Toh amman me yasa kake duba agogo" Ya wara ido. "Hmmmmm ashe dai ke ma kin iya sa'ido" Ta rufe idon tana murmushi, likitan dake tare da shi yayi murmushi ya mike tsaye ya fice daga office din. "Ya kamata ki saka min number wayarki, saboda mu rika gaisawa ko? Domin na lura kin fini tsada shiyasa da na baki number wayana baki kira ni ba" Yana maganar yana kallonta har ta bude ido. "Gashi ko sunanki ban sani ba" "Emily, sometimes akan ce min Aisha" "Ehhhh nice name, Allah yasa baki kyamar musulmi" "Kai baka kyamar Cristian?" Ya girgiza kai. "No... Ko kadan Mahaifiyata ahlul-kitab ce ita christen ce kin ga ba ni da hujjar kyamar ki" Ta nuna shi "amman kai..." "Aa ni Musulmi ne mahaifina Musulmi ne, aljanar data aure ni ma ta hana ni aure musulma ce" Emily ta kyalkyale da dariya... "Interesting" Ya fada yana kallonta da murmushinsa mai kyau. "Wa yace aljana ta aureka?" "Haka suke cewa wai saboda kullum cewa nake na ban ga wanda ta yi min ba, amman ina tunanin ta fara gajiya da ni ta kusa sakina" Ta sake kyalkyalewa da dariya. "you're so funny" "Yeah my second job is to make you laugh" Tana kokarin saka hannunta ta rufe bakin daga dariyar da take, Dr da ya fita dazun ya kwankwaso ya turo kofar ya shigo Aliyu na bayansa. A lokacin ne Dr A-B ya mike tsaye "Bakonka ya zo a late jirgina ya kusa tashi" "Hakuri zaka yi Dr ka saurare shi kuma ka ba mu lokaci ba sai mun yi ta daku ba" Cewar Likitan dake tare da Aliyu, Dr A-B ya girgiza kai zai yi magana Emily ta kalli Aliyu da tun da ya shigo ita yake kallo tace. "Da dai ka saurare shi, ba zan jidadi ba idan ka tafi baka ji uzurinsa ba" "Emily ai ba zan ce miki aa ba" Ya koma ya zauna sannan ya nunawa Aliyu kujera. "Malam Bismillahi" Aliyu be zauna ba domin baya son yayi maganar cewar yana son a duba matarsa ne a gaban Emily and the way da ya samu Dr A-B jikinsa ya ba shi kamar ba za su jitu ba saboda alama sun nuna masa Dr A-B is arrogant. "No ka ba mu katinka kawai i will contact you though it" Dr A-B ya dan tabe baki kadan. "Okay Dr Osman zai baka Katina" Ya mike tsaye yana kallon Emily da murmushi a fuskarsa, ita ma ta mike tsaye. "Toh yanzu kuma sai yaushe?" "Sai randa kaddara ta yi nufin sake hada mu sai mu hadu mu gaisa" "Ehmmm hmmm idan kaddara ta sake hada mu, toh na san manufar hakan kuma zan baki mamaki, fatan alheri" Ya risina mata kadan sannan ya wuce ya bude kofar ta bishi da kallo tana murmushi har ya fice Dr Osman yayi masa rakiya. Sai da suka fice sannan ya maida idonta kan Aliyu sai ya gwatsaleta. "Ashe haka kike da arha?" Ya fada fuska ba yabo ba fallasa. A take ta hade rai ta turo baki. "To miye na min magana ba mun yi fada ba" "Na miki magana zo ki saka wuka ki yanka ni" Ta sauke idonta kasa. "Breakfast kika kawo masa ne?" "Na Tasmia ne" Ta amsa da dan fushi. "Toh ki dauki abincin ki fice ko gadin office din ya barki ki yi?" "Toh ka daina min fada kamar wani ni yarka ce" "I'm your boss tarbiyarki a yanzu karkashina take dole na gyara miki zama" Ta duka ta dauki abincin ta nufi kofa ta bude ta fita sai gashi ya fito. "Tasmia da kika yi sanadin aka yi mata duka yanzu zaki dauki abinci ki kai mata babu ko kunya?" A nan ta zaburo masa ta juyo a tsawace tace. "Ni ban aikawa Matarka sakon komai ba, babu dalilin da zai saka na yi maka karya, babu dalilin da zai saka na turawa matarka wannan sakon, kai ma idan kana neman janye kanka daga jikina ba sai ka yi min shari ba, you can walkway ba tare da ka dasa min bakin ciki ba, ba sai ka zarge ni da abun da ban aikata ba" Ta karasa maganar idonta na cika da hawaye, kallonta kawai yake har hawayen suka zubo mata ta saka hannu ta share. Ya ciro wayarsa daga aljihunsa ya kama chat din da Kameela ta aika masa daidai gurin da number wayar Emily ta fito ya nuna mata. "To wa aika? Vito?" Emily ta karbi wayar ta duba ganin Number wayarta ya matukar bata mamaki. "Wallahi ban aika ba, ban tura mata wannan sakon ba, kuma Vito baya daukar wayata..." "Toh waya aika?" Ya tambaye sannan ya karbe wayarsa. Ta yi shiru tana nazari babu wanda ta fado mata a rai sai Chidimma da Tasmia domin Chidimma ta taba daukar wayarta, Tasmia kuma ta karbi wayarta a jiya tace zata kira ta sanar da iyayenta, sai dai bata saka ran Tasmia zata shirya mata wannan Chidimma kuma bata iya hausa kamar haka ba, a ina ma number Kameela ta fito bayan ta yi blocking dinta. "Waya karbi wayarki jiya?" "Tasmia tace zata kira iyayenta bayan Kameela ta mata duka, amman Tasmia ba zata yi hakan ba" "Karfe nawa kika je gida?" Ta yi shiru tana nazari "Karfe tara tayi bayan mun gama waya da kai ne" Ya duba time din sakon sai ya ga da safen nan aka turo masa shi, ya duba kiran da Tasmia ta masa jiya sai ya kalli Emily. "Karki yarda na riga ki isa Office" "Kamar ya kuma? Yaushe na kai mata abun karyawa har na koma gida na shirya na tafi office" "Wannan matsalarki ce kamin ki zo nan ya kamata ki yi wannan tunanin ba yanzu ba" Ta kalleshi tana mamakin yadda yake kokarin tsanarta. "Why do you hate me now?" "I didn't hate you" "Zan aje mata abincin sai na tafi" Ya daga mata kafadunsa alamar he don't care. Da sauri ta yi gaba da abinci ya bi bayanta har ta shiga dakin da Tasmia take, tana zaune kan gadon tana waya Emily ta shigo, shigowar Aliyu ya saka ta yanke wayar tana yana jin wani yanayi da dabam tare da mamakin ganinsa a lokaci daya. Emily ba zata iya fadar zata je gurin aiki ba saboda kar Tasmia ta ji kamar ta fifita aikinta akan lafiyarta dan haka tace. "Ga abinci nan ki karya, zan tafi yanzu ina da uzuri" Ta kalli Aliyu sannna ta fice Tasmia na mata godiya murya kasa kasa. "Ina kwana" Tasmia ta fada bayan Emily ta fice ta bar Aliyu. Madadin ya amsa mata sai yace. "Do you plan all this?" Ta sake dubansa kamar da can ba kallonsa take ba. "Ban fahimta ba" "Kin fahimta Tasmia, don't deny it, Emily tace ba ita ta aika sakon nan ba" "Kuma ka yarda da ita?" "💯 percent" Ta nuna kanta gabanta na faduwa sosai. "To miyasa ni ka zarge ni? Me zai saka na aikata hakan? Yaushe ma na dauki wayar Emily?" Ya saka hannayensa duka biyu aljihunsa. "Ban sani ba tukuna, abun da na sani a yanzu shi ne Emily ta yarda dake, ban sani ba ko ta fada miki labarinta, ta sha wahala sosai kamin ta hadu da mu, ta hadu sa musulmai masu gurbatattaccen tunani da son zuciya sun bar mata tabon da take kallon kowane musulmi ma haka yake, sai dai haduwata da ita da kuma ke ya fara sauya tunaninta, toh be kamata ta same mu da wani nakasu ba, ko da musulma ce be kamata mu ci amanar junanmu ba, kuma mu watsar da yardar mutanen da suka minta da mu" Yana kaiwa nan be tsaya jiran abun da zata fada ba ya fice ba tare da ya bata hakurin zubar hawayen da take ba. Sai da ya fice sannan ta share hawayenta. "Shi namiji na gari nemansa ake ba sai ya kawo kansa ba, yadda Kameela tana walawa a gidanka tana watayawa abun so ne a gurin kowace mace, ko da ace baka da kyakkyawar sura kulawarce kawai, dole zata burge duk wata mace mai son auren namiji irinka, ballantaba kuma ka hada duka biyun ko uku ma, ga kyau ga kudi ga bada rayuwa irin wanda mace take so, ku kanku maza wata rana ba kusan wanda ya dace da ku ba, Aliyu kana bukatar mace mai hankali mai wayo ba irin Kameela ba" Ta sauka daga kan gadon "Kowa da kalar kaddararsa wata kila ni tawa a haka ta zo, son mijin kawata ko ba komai matarka ta kira ni da marar tarbiya kuma ta yi min gorin aure, toh sai na nuna mata rashin tarbiyan, kuma sai na koya mata darasin da ace kewa mace bata yi ma yar'uwarta mace gori" Ta zauna a kujera ta bude abinci. "Sai kace ni na fi kowa bakin jini daga fara plan har ya gano ni, wai ni haka rayuwata zata kare ne? Kalar mazan da nake son aure basa zuwa su ce suna so na sai yan wadanda basa cikin tsarina kamar ni na fi kowa bakin jini, gaskiya ba zan bari Aliyu ya subuce min ba, daman tun ganin da na yi masa da farko ya burge ni" Tana cin abincin tana magana da kanta kamar wata tabbabiya. KAMEELA POV. "Ai dama ya samu shiyasa kuma kin ji hausawa sun ce kowa ya ga rana yayi shanya, da bata karya farashinta ba tun farko ta zubar da kimarta Wallahi Aliyu ko marin uwarsa kike yi be isa yace ki dawo gida sai ya neme ki ba? Me yake takama da shi?" Cewar Hajiya Asma'u Anty taba ya tsina fuska. " Wallahi kuwa nan kika watsa mana kasa a ido kika tsaya kai da fata babu mai son auren nan kika ce sai Aliyu, gashi nan tun ba aje da nisa ba ya koraki ya nuna wata banza ta fiki muhimmanci ina alkawarin da yayi miki toh?" "Alkawarin banza, dadin baki ne irin na maza kuma ni daman na san ba da zuciya daya ya aureta ba, ya aureta ne kawai saboda ubanaa ya karbi mukamin ubanki a yanzu, ke kuma ya aure ki ya wulakanta mu, kuma yayi nasara tun da kin ba shi hadin kai" Hajiya ta fada, sai Anty Shafa ta sake karba mata "Ai kara ma auren ya kare kowa ya huta, idan abun be tsaya iya nan ba gaba ba a san ya zai kasance ba, kuma dan Allah Hajiya ki hana D Alhaji kiransa dan jin ba'asi ko kiran iyayensa" Hajiya ta daga hannu. "Ai Alhaji ma ya fini daukar zafi shi da kansa yace tun da ya turo masa ya gida sai ya san yarsa tana da gata" Ganin ba za su barta da damuwar abun da ya isheta ba ya saka ta tashi ta bar musu bangaren gaba daya ta koma part din Mama Barakat ba dan ranta ya so ba, kan kujera ta zauna tana rushe da sabon kuka bayan wanda ta sha har ya kumbura mata ido ya hana ta cin abinci tun da ta dawo gida. Mama Barakat ta aje abincin dake hannunta ta taso da sauri ta dawo kusa da Kameela dake zaune kasa ta zauna kan kujera. "Subhanallahi Kameela lafiya? Yaushe kika zo?" "Aliyu ne yace na tafi gida sai ya neme ni" "Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un Me kika masa?" "Ban masa komai ba, saboda wannan bakar kafirar ne, ba ma ita kadai ba har kawata yake bibiya" "Abun be yi dadi ba, amman kin yi bincike? Kar ya zama kin masa mumminar fahimta ne, ko kuma kim yanke hukunci cikin fushi" "Mama Baraka har test fa Emily ta turo min tana fada min magana son ranta" Mama Baraka ta yi shiru na mintuna tana shafa Kameela alamar rarrashi sannan tace. "Kina da hoton Emilyn ne Kameela?" "Ba ni da hotonta" Mama Baraka ta sauke ajiyar zuciya domin tun a fadansu na farko take son ganin hoton Emily saboda yadda Kameela ta siffanta ta. "Ki yi hakuri idan mahaifinki ya dawo zamu yi magana da shi" "Aa ni na hakura ba zan koma ba, kar ma ki masa magana ko Aliyu ne autan maza ni ba zan koma gidansa ba" "Ba'ayi ma aure haka, tun har kuna son junanku baki san abun da Allah ya tsaro a tsakaninku ba, hakuri zaki yi" Kameela ta kara fashewa da kuka tana fadar ita ba zata koma ba ta hakura da Aliyu. _______________________ Sannu ‘yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe ɗinki da kaya masu kyau, masu ƙima daga Khadeeja Candy Store Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sauƙin sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing. Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taɓawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet ɗinmu sun dace da ke Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sauƙi ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko’ina! Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame. Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ƙayatarwa duk a farashi mai sauƙi. Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu! Baki da lokaci? Muna da sauƙin oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina! To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store. Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haɗuwa. [6/11, 11:51 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_writing 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ Page 3️⃣4️⃣ Barka da Sallah, Allah ya maimaita mana. EMILY POV. Daga Asibiti kai tsaye gurin aikin ta wuce saboda gargadin da Aliyu yayi mata, duk wanda ya ganta ya san zuwan kawai ta yi ba dan ta shirya ba, domin gashin kanta a yamutse yake tufafin jikinta ma regular one ne irin da wanda ta saba sakawa a gida kafafuwanta sanye da talkamin da ta saba sakawa a gida. A yau din ma data shigo office sai ta rasa me zata yi saboda bata shiryama zuwan ba, dan haka ta zauna a kujerarta taba ta kallo kofa kamar ta san Aliyu zai shigo, after like 30 min ya turo kofar ya shigo fuska ya yabo ba fallasa. "Ai na dauka ba za ki ji magana ta ba" Yana maganar wayar dake hannunsa ta yi ringing da ya duba sai ya ga sunan Abokinsa Turhan kuma direct kira irin wanda ba kadafai yake masa ba, ba ma ta whatsapp ba, Aliyu ya kalli Emily dake cizon akaifa ya kalli kiran what a coincidence. "Sallamu Alaikum" Ya amsar wayar idonsa na kan Emily. "Hello Aliyu, ya kake?" "Ina lafiya ya kwana biyu" "Alhamdulillah" Daga haka Turhan be sake cewa komai ba yayi shiru kamar yana jiran Aliyu ya fara magana, Aliyu ma ya kasa cewa komai feeling so guilty. "Ya Ammy" "Bata jindadi, ina shirye shiryen shigowa na ganta, Aliyu har yanzu babu wani labari ta bangarenka?" Aliyu ya dauke idonsa daga kallon Emily ya juya baya yana shafa kansa. "Ciwon Ammy yana da alaka da hakan ne?" Turhan ya sauke ajiyar zuciya. "No Aliyu i want to make things right, mahaifiyata ta yi going through abubuwa marasa dadi a zamanta da mahaifina, and ni kadai ta haifa ni ne kawai last hope dinta and i failed her, idan na zauna na yi tunanin wasu abubuwan ina jin babu dadi kuma ina son na kyautata mata, ina bukatar Emily a yanzu saboda mahaifiyata if i can turn back the clock, zan gyara abubuwa saboda mahaifiyata, I'm losing my sleep bana cikin kwanciyar hankali a yanzu, Aliyu na shiga na fita na yi iya yadda zan iya just to fix what i broken, amman na gagara samun yarinyar nan, kuma mahaifiyata ta ki ta fahimce ni, rayuwa tana ta tafiya ina tsoron kar ni na mutu ko na rasa mahaifiyata ta tafi da wannan kuncin a ranta" "Hakan yana nufin ka bata abubuwa da yawa Turhan? Akwai abun da baka fada ba?" Emily na

Chapter 27 of 63