Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
murya kamar mai shirin yin kuka. Tun da ya furta cewar Khaleefa ne Emily bata juyo ba ta cigaba da tafiya, a lokacin ne Ummi ta juyo bayan ta kare wayar da take sai ga Emily ta biyo bayanta Khaleepa kuma ya biyo ta yana mata magana. "Dan Allah ki taya dan girman Allah ki saurare ni" "Kin san shi ne?" Ummi ta tambaya. Sai Emily ta tsaya a gabanta "Tsohon mijina ne, shi ne ya fara cutar da ni, shi ya budewa kowa kofa, shi ne mutumen da ya fara raba ni da gata, shi ne ya fara karantar da ni rauta tata, shi ya janyo min duk masifar da nake ciki yanzu, shi ne uban da har ɗana ya mutu ba taba ganinsa ba, shi ne mutumen da ya koreni da tsohon cikin dansa, yan'uwansa suka juyo min baya, su suka fara kirana da tubabbiya" Ummi ta matsa daga gaban Emily fuska a hade ta kalli Khaleefa. "Karka sake ko da wasa ka sake mata magana, taya zan shigo da bakuwa ka tari gabanta ba tare da neman izini ba? Direba ne kai a nan karka manta da wannan" "Tohm Hajiya ayi hakuri" Ya fada yana tare hawayen da suka cika idonsa. Ummi ta kama hannun Emily suka shiga ciki kowa sai kallonta yake saboda dress din dake jikinta ga kuma sarkar cross, Ummi ta shiga da ita ciki ta kaita dakin da Aliyu dake gidan. "Nan dakin ɗana ne Aliyu, ki zauna a ciki ki yi duk yadda kika so, ki sake jikinki kamar kina cikin gidanki" Emily ta kalli dakin. "Idan kin bani dama zan je na dan ji da bakin da suka zo mana jaje" Emily ta saki hannun Ummi ta nufi gadon da Aliyu yake kwana a lokacin da yake gidan ta zauna. Ummi kuma ta juya ta fice, kwantawa Emily ta yi kan gadon ya lumshe ido zuciyarta na mata wani irin zafi. "Wayyo Zuciya" Komai ya taru a zuciyar ya tsaya mata... TURHAN POV. "Kamata yayi kawai na koma na daukota, to miyasa amfanin barinta a can ma? Macen da na shekara nawa ina nema yanzu na ganta na bari wani katon banza yana controlling dinta" "Idan ka je daukar ta zata yarda ta biyoka ne? Tun da fari da baka bata komai ba, ai duk haka ba zai faru ba, ni na ma manta ban tambaye ka ba, sakinta ka yi ko guduwa ta yi?" "Guduwa ta yi ni ban sake ta ba" "Amman ka munana mata a zamantakewarku?" "Ba cancan ba, sai dai wani abun ta dauke shi da zafi saboda bata son zama da ni yanzu, kuma dole za a samu abubuwa da ba za su mata dadi ba, Ammy saboda Al'adar ba daya ba, kuma kin ga ina da mata, ko ma dai minene Ammy abun da ya wuce ai ya wuce yanzu ake fuskanta, tun da gashi har da yarinya a tsakaninmu, kuma matar nan ita muke da ni ma saboda gyara kuskuren da na aikata, ke da kanki fa kin ce na gyara abun da na bata" Ammy ta sauke numfashi. "Tun da har an ganta, to komai ya zo da sauki, balle kuma har ga ya tsakani, ka rika bin abubuwa a hankali, yanzu idan ka ce zaka yi rigima ai zaka karawa kanka bakin jini ne kawai a gurin Emily" "Amman kuma sai na bar wani katon banza yana kallar min mata yana jin sautin muryarta yana karanta mata karya da gasjiya akaina" Ya mike tsaye. "Zan je na yi magana da ita zan bi duk wasu matakai da suka dace ta ruwan sanyi tsakanina da ita, kuma zan jawa Aliyu kunne, shi yana da tasa mata ni kuma yana son ya kashe min aure saboda ya bata tsakanina dake kuma da Fatima, ni na rasa me na tarewa Aliyu ne Wallahi, ashe haka hassada take" "Karka je" "Ammy me yasa kike hana ni abubuwa ne? Miyasa kika kin goya min baya a komai, yau na tabbatar da ace ni na na aikata abin da Aliyu ya aikata Wallahi ba zaki goya min baya ba, amman da idona na ga Ummi ta fito ta rungume Emily sun shiga tare, kin ga ta goyawa danta baya kenan da saninta ake komai waya sani ma ko Emily a gidanta take, shiyasa har Kameela ta san da komai" "Turhan..." Ammy ta kira sunansa, ya kalleta ba tare da amsa ba. "Zauna" Ya koma ya zauna. "Mahaifinka ya fada maka ni na dauki cikinka wata ta haife ka ne?" "Aa" "To taya kake tunanin zan fi son wasu da kai? Duk abubuwa na nake maka ko nake fushi da kai akansu saboda ina kaunarka ne, na aura maka yarinyar nan saboda na samu ka yi kusa da ni, kuma ita ma ina hango mata jindadi a zamantakewarku, saboda ta auri wani bata dace ba, ina ganin idan aka kyautata mata kamar an yi ma musulunci hidima ne, daga lokacin da ta gudu ta bar min bakar wasika na san zamanku be tafi a yadda na yi tsammani ba, shiyasa ban taba tambayar ya kuka yi zaman ba, amman a zuciyata na ji babu dadi kuma na ji idan har baka nemo yarinyar nan ba, ni da kai ba mu gyara abun da ka bata ba, ba zan samu salama ba, na yi fushi da kai ne saboda na auna hakikan abun da yake zuciyarka da gaske zaka iya min biyayya ko aa kuma zaka so abun da nake so ko aa, daga lokacin da ka dage kana neman yarinyar nan zuwa yau data bayyana a garemu, ya tabbatar min da biyayyarka da kuma son farinciki da gujewa bacin raina, gashi kuma ta zo mana da alheri haihuwar da kake ta nema sanadinta ka samu, ko bana raye na san zaka yi alfahari da hakan, kuma na san zaka rike yan'uwa ka rika ziyartarsu, aurenka da Emily zai kara kusancinka da ni, na san yanzu ba zata yarda ta bika ba, amman zata yarda ta zauna a nan, kuma na san a yanzu kam dole zaka bata hakkinta, inda kana son zama da ita kana son yarta dole zaka zo, toh kuma sai ka yi tunanin ba zan taya ka wannan yakin ba?" Kalman Ammy sun kwantar masa da hankali kuma sun saka ya ji sanyi kana sun karfafa nasa guiwa, sai dai hakan be kawar da abun da yake ji na kiyayyar ganin Emily ko magana da ita da Aliyu yake ba, domin baya kusa da ita yanzu. "Tashi ka tafi gurin yarka, ni zan shirya yanzu na tafi gurin Ummi zan yi magana da ita dole ai ayi ma tukar hanci" Turhan ya mike tsaye ya karasa inda Ammy take zaune ya kama hannayenta ya sumbanta sannan ya sumbanci goshinta. "Na gode Ammy" Ya nufi sama, sai ta bi bayansa da kallo tana murmushin jindadi, a yanzu ba ɗa kadai take da shi ba har da jika gashi kuma Emily ta dawo komai zai daidaita ya zama daidai a rayuwarsu. Tashi ta yi ta shiga ciki ta shirya shirin fita kamin ta fito Nurse dake duba jininta ta shigo ta hauro har sama ta auna jinin. "Maa Shaa Allah, Hajiya jiki ya sauka sosai daman Dr yace idan na auna jinin na ga be hau ba, to na fada miki karki sake shan maganinki sai ya shigo anjima zai canja miki da su kuma ya fada miki yadda ya kamata a sha" "Alhamdulillah, hankali na ne ya fara kwanciya yanzu, ciwon sugar ma ina tunanin zai sauka In Shaa Allahu" "Eh shi ma naga jiya ya sauka sosai, Allah ya kara lafiya" "Ameen" Ammy ta janyo jakarta ta ciro kudi mai kauri ta mikawa Nurse din. "Aa Hajiya" "Haba ki karba mana, alheri ne ai ba a maida hannun kyauta baya" Nurse din ta karba tana mata godiya sannan ta fice. Waya Ammy ta janyo ta nemo number Ummi ta kirata sai da wayar ta fara ringing sannan Ammy ta karaa kunne. Ummi ta amsa tare da amsa sallamar da Ammy ta yi, bayan sun gaisa Ammy ta ce. "Ya Aliyu da karfin jikin?" "Alhamdulillah" "Ina son na shigo ne, kina gida ko kina asibiti?" "Ina gida" "Toh gani nan zuwa" Ta aje wayar sannan ta dauki mayafinta ta yafa a jiki ta dauki jakarta ta saka talkaminta ta fice, dakin da Fatima take ta fara turawa a hankali sai ta hangota zaune a kasa Turhan yana zaune gabanta. "Zan tafi" "Okay Allah ya kiyaye Ammy, Wallahi Aliyu yayi min Illa Ammy yarinyar yanzu sunansa kawai take kira sai na mahaifiyarta, tana da hujjar kiran sunan Aisha amman Aliyu fa? Miye hadinta dashi? Yanzu fa ko da na shigo ya kirata a waya magana suke yi" "Ka bi komai a sannu, ai mutum be taba cin amana ya ga nasara a rayuwa ba" "Ni mamana nake so, na tsane ku duka, sace ni kuka yi, Uncle Aliyu zai zo ya dauke ni" Fatima ta fada tana hararar Ammy daman karamin aikinta ne rashin kunya. Ammy ta saki kofar dakin ta shigo ciki ta karaso inda Fatima take zauna ta rikota sai Fatima ta fisge hannunta, Ammy ta sake rikota ta dagota ta nufi gaban madubi da ita ta dorata tsaye akan kujerar madubin, sai Turhan ya taso ya zo ya tsaya kusa da ita yana kallon madubin. Ta cikin madubin Ammy ta nuna mata Turhan tace "Kalli wannan mutunen" Fatima ta kalleshi tana kumbura baki. "Kalli wannan yarinyar" Fatima ta kalli kanta. "Fada min da wa take kama?" Fatima ta kara turo baki ta ki ta yi magana, ba dan kuma bata fahimci me Ammy take fada ba sai dan shakiyancin ba zai barta ta bada amsa ba. "Wannan yarinyar ta yi kama da wannan mutumen ko baki gani ba?" Fatima ta sake kallon Turhan ta cikin madubi ta kalli kanta. "Saboda wacan mutumen shi ne mahaifin wannan yarinyar" "Ba ni da mahaifina Momy ta fada min haka aka haifa ni ba ni da mahaifi, baki ji sunana ba Fatima Emily Aisha" "Aa kina da shi, kowa na duniyar nan yana da uba sai ke kadai ce za ace baki da uba? Kina uba Fatima ni kuma kakarki ce, ke yar dangi ce jinin sarauta daga da baya kuma yar larabawa, kina da uba Fatima kalli ki gani kin taba ganin wani wanda kuka yi kama kamar wannan" Fatima ta juya ta kalleshi. "Meyasa Momy tace bani da Baba? Kuma miyasa be taba zuwa ba?" "Yanzu su ya kamata ki tambaya, kowanensu sai ya baki amsa, amman tabbas wannan mahaifinki ne, daga sunanki ya tashi daga Fatima Emily Aisha, ya kuma Fatima Turhan Muhammed Abdo, idan ba mu da alaka da ke ai ba zai taba yayu mu rike ki mahaifiyarki ta kyale ba" Fatima ta kalleshi da cikin madubi ta ga kamaninsu sosai kuma tana ji ya kwanta mata a rai a matsayin uba tun a ranar daya rungume ta, sai dai kawai bata yarda da su ba ne, domin ba mahaifiyarta ce ta fada mata ba. Fatima ta fashe da kuka "Miyasa Momy tace ba ni da Baba? Idan shi Babana ne miyasa be zo ba shekara da yawa? Yan makarantarmu suna min dariyar sunana, suna cewa ba ni da Baba" "Tsawon lokacin nan, nemanki muke ke da Emily ba mu san inda za mu ganku ba, sai a yanzu da Aliyu ya zo da ke, wata kila shiyasa ya zo dake saboda ya nuna miki mahaifinki ne" "Ina son na yi magana da shi" Ta sauka daga kan kujerar ta nufi inda wayar Aliyu take ta dauka ta mikawa Turhan. "Kira shi" Turhan ya karɓi wayar ya rike, har sai da Ammy ta ce. "Kira mata Aliyun" Kamar zai musa sai kuma ya taba number Aliyu ya saka hands-free, yana jin zuciyarsa kamar zata fashe tsabar bakinciki "Hello My Beautiful Angel" "Uncle Aliyuuuuu wani ne a nan yana cewa shi ne Babana da wata tsohuwa, a nan gidan da wannan matar ta kawo ni gaskiya ne? Tun ranar yake cewa shi ne mahaifina, kuma yana kama da ni" Aliyu yayi shiru na dakiku. "Eh mahaifinki ne" "Miyasa Momy tayi min karya tace ba ni da Baba?" "Saboda.... Ta yi tunanin ya rasu ne... Bata son ta fada miki ki shiga damuwa shiyasa take fada miki haka, amman yanzu mun gane yana da rai shiyasa aka kawo ki nan dan ki san shi kuma ki saba da shi, dan haka ki zama yarinyar kirki yi rika jin magana karki ce zaki yi tsiwa kinji ko?" "Ba zaka zo ka dauke ni ba?" "Zan zo amman sai kin kwana biyu kin saba da shi tukuna, sai na zo na dauke ki, ba na san kina son uba ba? Kina son canja sunanki ki hada da na mahaifi to daga yanzu zai canja" "Ba sunanka kace zaka saka min ba? Ni bana son sunan wannan ni bana son shi ni kai nake so, i don't want this old woman and her Son kai nake so da Momy" Ita kawai bata saba da su ba ne, tana son uba amman ta fi sha'awar ace akwai wani wanda ta wani a kusa. "Okay za mu zo ai, amman sai idan kin yi biyayya kin zama yarinyar kirki, bana son rashin magana da tsiwa, idan kina musu fushi ba zan zo ba, amman idan kika zama yarinyar kirki zan zo" "Okay i will be a good girl" "Yauwa, i love you can you say you love me back?" "I love you ka zo da sauri" "Okay bye" Turhan ya karɓe wayar ya datse kiran ko da be iya mayarda duka yaren turanci ba ai yana jin abun da yake fada kuma ya fahimci komai, kamar zai buga wayar a kasa sai kuma ya daure ya saki murmushi ya mika mata wayar, sai ta kura masa ido tana ta kallonsa ya rage tsawonsq ya duka daidai ita sai ta matsa jikinsa ta kwanta ya rungume suka zauna a gurin Each and every second sai ta daga kai ta kalleshi ya kalleta tana kuka mai karfi ta ce "Zan fadawa yan makarantarmu ina da Baba, zan tafi kai zan nuna musu, i hate Momy i hate her" Hawaye ya cika idon Turhan Ammy daman tuni ta fara zubar da nata. "Ni ma zan fadawa family ina da ya, ina da kaso a jinjina, zan baki duk wani gata da kika rasa Fatima, ki yi hakuri na zo a makare" Ammy ta share hawayenta tana murmushin farinciki. "A yau zaka kara sanin muhimmanci na Turhan, zaka san abun da ake kira da iyaye, zaka san sha'anin yaya" Ta dauki jakarta ta fice daga dakin tana kara shaye hawayenta, sai da ta fito sannan ta sanar da direban ya fito ya same ta ya bude mata mota ta shiga, ta zauna kenan wayarta ta yi ringing sai ta ciro wayar daga jakarta ta duba sai ta ga bakuwar number. "Sallamu Alaikum" Mai kiran ta amsa mata ta dayan bangaren sannan ta gabatar mata da kanta. "Sunana Hajiya Barakat, amman yara suna kirana da Mama Baraka" "Maa Shaa Allahu, sai dai ban gane ki ba" "Eh to ba mu taba magana ba, ba lallai ki yi saurin gane ni ba, ni step mother din Kameela ce matar Aliyu abokin danki" "Okay Tohm Lafiya?" "Ba lafiya ba, ina son mu yi magana da ke ne akan Emily da kuma yarta Fatima da take gurinku" "Ina saurarenki" "Ba maganar waya ba ce ina son ganinki ne" "Zaki iya zuwa gidana zuwa anjima yanzu dai ina hanyar tafiya wani gurin ne, idan zaki taso sai ki sanar da ni na kwatanta miki" "Tohm shi kenan" Ammy ta sauke wayar tana mamakin kiran, zuciyarta na raya mata wata kila Kameela tana son ta karbe Fatima ne ta maidata gurin Emily saboda Aliyu, ko kuma dai wani abun ne tun da Allah kadai ya san me ya faru na kawo yarinyar da Kameela ta yi ba tare da izinin Aliyu ba. Haka dai Ammy ta yi ta sake sake har suka isa gidan Ummi. [7/11, 10:21 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=KhadeejaCandy *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 5️⃣0️⃣ Ummi na falo tana ta gaisawa da mutane yan'uwa da abokan arziki da suka zo mata jaje sai ga Mama Barakat ta shigo falon da sallamata tare da rakiyar yarinyarta ta biyu. Ummi na ganinta ta dan daure fuska kadan domin ta san zuwanta ba zai wuce saboda Kameela ba, sama sama suka gaisa da Ummi sai Ummi ta maida hankalinta gurin sauran baki bata sake bi ta kan Mama Barakat ba har sai da Mama Barakat ta gaji da zama ta ce. "Hajiya gurinki na zo" Ummi ta maido da hankalinta gurinta sannan ta mike tsaye ta nufi wani dakin baki dake falon ta shiga tana fadin. "Bismillah Hajiya Baraka" Ummi ta fara shiga ta zauna sai ga Mama Baraka ta shigo ta zauna kan kujerar dake dakin. "Na katse ki kina da baki, na tafi asibiti ai aka ce kin zo gida kuma ba su yarda na shiga na duba Aliyun ba" "Eh ana son ya huta ne, kuma saboda abun da ya faru da shi ya saka ake ba shi tsoro dole a san suwa suke shiga da fita" "Allah sarki, Allah ya ba shi lafiya kuma ya tsare gaba, mu ma a gari muka ji abun da yake faruwa" "Ameen Ya Rabbi" Daga haka sai shiru ya biyo baya, Mama Barakat bata sake cewa komai ba hakan ya saka domin ta yi tunanin wata kila ta zo nan ne amadadin mahaifiyar Kameela, dan haka Ummi ta tari hanzarinta tun kamin ta fara magana. "Hajiya Baraka Allah dai ya sa ba kin zo maganar Kameela ba ne, domin dai yanzu Aliyu yana bukatar hutu da kwanciyar hankali, kuma iya hakuri ni dai na yi a matsayi na uwarsa na dauke ido iya yadda zan iya, yanzu kan abun ya wuce duk inda ake tunani ba kuma zan yarda ta kashe min ɗana ba saboda kishinta na banza. Abun ya kai har ta saka masa guba kin ga ai ba so ba ne ba kuma kishi ba hauka ne" "Subhanallahi, guba fa kika ce Hajiya" "Da bakinsa ya fada min, shi ne dalilin turo ta gida da yayi ai, amman be fadawa kowa ba sai a yanzu da ta kai shi makura, kin ga yanzu ko za su zauna da junansu ni ba yarda zan yi ba, ba zai yiyu su da aure ni da zaman zullumi da fargabar me zai faru ba" "Ban taba ji wannan, amman Kameela bata yi ma kanta adalci ba, Subhanallahi, ni ba ma zancen ta ya kawo ni ba, Wallahi ba dan kowa na zo ba sai dan yarinyar da aka ce saboda ita Aliyu ya saki Kameela, shiyasa na tafi asibiti aka ce baki can na tambaya dan Allah ita Emily tana tare da shi ne na kwatanta musu ita suka ce min kun taho tare" "Emily? Toh Allah yasa ba daga mata hankali za'ayi ba, domin yarinyar nan tana cikin damuwa, kuma kamar amana take a gurina" "Haba Hajiya ni ma fa Uwa ce, ta ina zan nemi daga hankalin wata ya? Magana kawai nake son yi da ita, saboda ina tunanin kamar ita ce yarinyar da aka taba hada mu da ita a lokacin da muka je Abuja, na zo da ita har Kaduna sai ta gudu bata tsaya ma na taimaka mata ba" "Allah sarki Ashe kin santa" Nan Hajiya Barakat ta labarta ma Ummi farkon haduwarsu da kuma dalilin haduwa. "Toh ki haura sama, tana nan daki na farko hannun hagu" "Toh na gode Hajiya" Mama Barakat ta tashi tare da Ummi suka fito Ummi ta koma gurin Mutanenta Mama Barakat kuma ta nufi upstairs ta haura sama ta bi hagu da ita kamar yadda Ummi ta fada mata, dakin farko ta fara turawa a hankali ta leka sai ta hango Emily zaune kan gadon Aliyu tana rutsar kuka a hankali marar sauti. A take zuciyar Mama Barakat ta kara karyewa daman ta shigo gidan zuciyarta cike da rauni, ta shiga ciki gaba daya ta maida kofar ta rufe karar rufe kofar ya saka Emily ta kalli kofar sai ta yi hanzarin takaita kukanta ta sauke kanta kasa. Mama Barakat ta karasa cikin dakin ta zauna bakin gadon tana kallon Emily babu shiri hawaye suka zubo mata, yadda Emily ta takure guri daya ya bata tausayi sosai. "Ba lallai ki gane ni ba, sunana Mama Barakat, mun tana haduwa da ke a lokacin da kika bar Sudan Mrs Deborah ta zo da ke, sai tace na zo da ke Kaduna saboda kin fada mata a nan kike, kamin ayi bincike ba ki ma zauna a gidana sai kika gudu ko kin gane ni?" Emily ta kalleta da kyau ta daga mata kai, daman tun farkon shigowarta ta ga alamar kamar ta taba ganinta. Cikin kuka Mama Barakat ta ce. "Meyasa kika gudu? Me yasa baki tsaya ba? Wata kila da yanzu baki shiga cikin wata damuwa ba, baki yarda da ni ba ne a lokacin? Na yi tunanin ke musulma ce a lokacin?" Emily ta kalleta hawaye na sauko mata. "Gaba daya ni a yanzu ban fahimci rayuwa ba, ban gane me take nufi da ni ba, daga wannan sai na fadawa wannan, idan har iyayena ko yan'uwana ba za su iya rike ni tun a lokacin da ban san komai ba, bana tunanin akwai wanda sai rike ni na samu mafita, bayan barin gidanki abubuwa da yawa sun faru, a lokacin na samu gata kuma ina da yarana har biyu, sai ga shi kuma rayuwa ta sake juye min ta kawo ni nan, babu gatan babu uwa ba uba ba babu yaran, dayan ya mutu dayan an karbe, ni yanzu na kasa fahimtar komai" Ta fashe da kuka, Mama Barakat ta matsa kusa da Emily ta rungumota ta kwanto da ita jikinta ita ma ya fashe da kuka mai karfi wanda ya fi na Emily shiga zuciya da sosai rai, ta rumgume Emily sosai tana shafa kanta. Emily ta lafe a jikin Mama Barakat daman tana neman wanda zai rumgume ta kamar haka a yanzu, sai duk ta ji kewa da son kasancewa da tata uwar duk da yake bata taba sanin ya dadinta yake ba, amman ta sani idan har akwai iyaye a tare da ita ko yan'uwa na jini wasu abubuwan za su zo mata da sauki. "I Need my own parents, ni mace ce kawai mai son iyayenta da yan'uwanta a kusa da ita, why all this? Me na yi musu? Me na yi ma rayuwar? Me yasa kaddara take ta juya ni haka? Na gaji na gaji na gaji" Tana maganar tana kuka mai ban tausayi ta takure sosai a jikin Mama Barakat kamar zata shige jikinta, bankarewa Mama Barakat ta yi ta daga kai sama tana ta yaki da numfashi da kuma kukan dake son sakata ihu, hawaye suka rika sauko mata ta gefen ido wasu na bin wasu. Sai da ta kai ruwa rana tsakanin kukanta da numfashinta sannan natsuwarta ta samu daidaituwa, ta maido idonta akan Emily ta shafa kanta. "Na samu labarin abun da ya same ki a yanzu nw ta gurin Kameela saboda sakin da Aliyu yayi mata na abu...." Mama Barakat bata kai aya ba Emily ta daga daga jikinta da sauri ta matsa baya. "Fita dakin nan" Mama Barakat ta girgiza kai da sauri. "Ba ki gane ba ne, bana goyon bayan Kameela ina tare da ke ne..." "Ki fitar min daga nan, bana son Kameela bana son duk wani abin da ya shafe ta, fita yanzu nan" Mama Baraka ta mike tsaye ta dauki jakarta kamar mai tsoro jikinta har rawa yake. "Tohm, zan fita amman idan kina bukatar wani abu ko taimako zaki iya tuntuba ta, kuma zan kasance kusa da ke daga yanzu In Shaa Allahu, idan kina bukatar wani abu ki fadawa Aliyu zai fada min yana da number wayana" Ta nufi kofa tana yi tana juyo ta kalli Emily har ta fice, sai da ta tsaya ta share hawayen ta sannan ta sauko jiki babu karfi murya kuma ta sauya ga ido ma be isa ya karyata cewar ya zubar da hawaye ba. Ta sauko tana ta masa kasa da ido bata son hada ido ta mutane saboda bata son kowa ya gane ta yi kuka, amman hakan be hana Ummi tambayar lafiya ba bayan ta tambaye ta sun gana. "Eh mun yi magana da ita" "Allah yasa dai lafiya, yanayinki kamar ya canja Hajiya Barakat" "Lafiya kalau, dan Allah zan iya samun number mahaifiyar abokin Aliyu nan a gurinki? Domin na kira Aliyu be daga

Chapter 40 of 63