Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gabatar mata da yaranta suka gaisa da Emily suka rumgumeta. Emily ta zauna tana hawaye. "A tsawon rayuwata, na yi ta ne ni kadai, idan na hango wani mai dangi ko iyaye sai abun ya burge ni, saboda na yi tunanin ni ba ni da kowa, ba uwa ba uba ba yan'uwa ban san yadda ake ji ba, amman hakika iyali suna da dadi" Dr A-B ya kai hannunsa ya rika nata. "Wani lokacin kaddarori sukan faru da mu, wadanda ba mu isa mu canja komai daga karesu ba, idan ka hango wani yana rayuwa mai kyau sai ka ji ina ma kai ne, idan kuma wani yana rayuwa marar dadi sai ka ji dadi da ya kasance ba kai ba ne, hakan yana nuna mana ba mu da ikon canja komai daga kaddarar mu, domin da za mu iya da mun zama irin wadancan da su ke burge mu, tun da ba za mu iya ba, ai sai mu yi hakuri mu da yadda muka samu kan mu, abun da duk ba zaka iya canja shi daga halitta ko kaddara halayya ba toh be kamata ya zama abun damuwa ba" Emily ta daga mai tare da kai dayan hannunta ta rike hannunsa daya da duka hannayenta, ita kadai ta san me take ji lokacin da bata da kowa, haka kuma a yanzu ita kadai ta san yadda take ji da ta samu yan'uwa. "Na san idan Daddy ya ganki zai yi farinciki domin ko yayansa da suke can ba su yi kama da shi sosai kamar yadda ke kike kama ba, kuma mutum ne mai son yara, na kan ziyarce once in a while" Ta yi murmushi ta sauke kai kasa tare da kai hannunta daya ta share hawayenta, jin an taba kofar falon ya saka ta dago ta kalli kofar sai suka yi ido hudu da Turhan, murmushin dake fuskarta ya gushe ta kalli Mama Baraka dake zaune, sai Mama Baraka ta girgiza mata kai ta juya ta kalli Turhan da ya tunkaro inda Emily take zaune, idonsa a kanta zuciyarsa na bugawa ganin hannun Emily cikin na Dr A-B. "Ban ce ya zo ba, ban san da zuwansa ba, yana zuwa nan mu yi magana amman yau ban fada masa zaki zo ba, kuma ba saboda shi na shirya wannan ba, na shirya miki wannan liyafar ne saboda ina sha'awar ki zo kusa da ni, kuma ina nufin baki mamaki da Dr A-B ne, ba Turhan ba" Mama Baraka ta fada cike da tsoron batawa Emily rai. "Ni na ce ya zo" Emily ta kalli Dr A-B. "Ya kamata mu zama masu yafiya Emily, dukanmu muna laifi wa junanmu, kuma akan daga mana kafa a yafe mana, na san abun da ya aikata be kyauta ba, kin ba mu labari, shi ma kuma ya maimaita min cikin nadama, kusan shi ne dalilin zuwa ba wai domin Madam Baraka kawai ba" Emily ya maida kanta kasa tana jin kamar suna son mata dole ne. Dr A-B ya matsa kusa da ita yana mata magana a hankali yadda zata fahimta. Turhan ya zauna a kujerar dake fuskantarsu yana maida numfashi da karfi, be tana sanin yana kishin Emily har haka ba sai a yau da wani wanda ba Aliyu ba ya zauna kusa da ita kuma ya rike hannunta, saukin abun ma tana da alaka ta jini da shi, da ba haka ba wata kila na zai iya zama ya kalli wani yana kallar masa mata har ya rika hannunta ba. "Ni ma na ba shi rashin gaskiya na abun da yayi, kuma ya karba ya nuna min ya fada min kuma na ga hakan cewar yayi nadama, ban fadawa Madam Baraka ba, amman ya fita matsawa na zo saboda yana ganin ina da alaka da ke kamar idan na saka baki zaki iya yafe masa" "Na yafe masa ai, na fadawa Ammy tun satin da ya wuce, komai ya wuce yanzu gaba nake hari" Dr A-B yayi murmushi. "Haka nake so, daman na san baki da wahalar sha'ani, na gode" Turhan yayi murmushi, Dr A-B ya daga ya kalleshi. "Ka yi farar dabara da ka biyo ta gurina gashi ya yafe maka" "Na jidadin hakan, kuma ina son na kora da bayanin yadda aka yi na san Dr AB dan'uwanki ne, na biyo ta bangaren Mama ne, na fada mata komai kuma na roki yafiyarta na roki ta nema min taki, sai ya zama ita ma tana jin tsoro, hakan ya saka na yi kamun kafa da Dr Adam bayan Mama ta fada min komai na rayuwarki, Congratulations Aisha yanzu komai ya samu, ina miki murna" Emily ta kalleshi kawai ta dauke kai. Emily bata sake sakewa ba a falon saboda Turhan yana ciki, not because of bata yafe masa ba, ta yafe masa har zuciyarta sai dai ta kasa jin walwala saboda yana kusa da ita, idonsa akan duk wani motsi nata. Da suka hadu dinning gurin cin abinci Turhan ya zauna saitin da Emily take, abincin kadan ya ci, Emily ma kadan ta ci tana murmushin dole. "A yanzu nan zaki zauna ne?" Dr A-B ya tambaya. "Aa ina zama gurin Ummi ne" Ya dan tabe baki. "Haka Madam Baraka ta fada min, gidansu wannan yaron ko?" Emily ta kalleshi tana murmushi "Aliyu ba yaro ba ne" "Yayi kamar ni?" "Aa amman dai ba yaro ba ne" "Okay, idan kina zon zama can ba laifi, amman dai ki kula da kanki" "I will" Ta aje spoon ta mike tsaye. "Zan shiga bandaki" "Muje na nuna miki" Daya daga cikin yaran Mama Baraka ta fada, ba musu Emily ta bita zuwa sama ta nuna mata bandakinsu sannan ta fito. Emily na shiga ta maida kofar dakin ta rufe ta jingina ta busar da numfashi. "It's okay Emily, that's how life is komai ya wuce, Turhan shi ne uban yarki, na zaki iya canja wannan ba, dole alaka zata shiga, akan yarsa kawai ba akanki ba, yanzu komai ya wuce" Ta fadawa kanka da nufin karfafawa kanta guiwa, sannan taja numfashi ta sauke har sau uku ta bude kofar ta fito. Ta sauko sai ta zauna a sitting room bata koma dinning din ba, ba su san ta sauko ba sai da suka gama cin abinci suka taso. Sai kuma ga Mahaifin Kameela ya shigo cikin sakin fuska ya mikawa Dr A-B hannu suka gaisa. "Ban san ka zo ba, sai da muka yi waya da Mai gida yake tambayar ya ka sauka kuma an mata tarba mai kyau" "Tafiya ce ta gaggauwa shiyasa ban fadawa kowa ba, shi ma ya sani ne saboda wasu dalilai, na zo ne saboda kanwata Emily fatan na same ku lafiya" "Alhamdulillah, muna maka maraba da zuwa, mu shiga ka gaisa da sauran yan gidan mana" Mahaifin Kameela ya rike hannun Dr A-B suka fita falon suna magana ya shiga da shi bangarensu Kameela ya gaisa da su da sauran yaransa, yayi hakan ne saboda Dr A-B da duk sauran business partners dinsa ba su san Hajiya ba, Mama Baraka aka sani da ita yake yawo, a yanzu kuma basa tare. Da suka fita sai ya zama falon daga Mama Baraka sai Misra second born dinta after Emily, and Turhan. Mama Baraka sai jan Emily take da hira sama sama a kasan zuciyarta kuma bata jidadin abun da mijinta yayi ba, domin da ya shigo be kalleta ba balle yayi ma Emily yayi magana, ko da yake a yanzu ba zata kira shi da mijinta ba sai dai uban yayanta. Turhan kan idonsa na kan Emily wani irin kallo yake mata da ya tafi da hankalinsa ya kusa hango masa yadda jini yake yawo a jikinta. Emily ta mike tsaye. "Bari na jira Dr a waje" Mama Baraka ta kalleta. "Ba a nan zaki kwana ba" "Aa maybe wata rana amman ba yau ba" Turhan ya bita da kallo har ta fice falon sannan ya kalli Misra dake kallonsa ya kalli Mama Baraka ya ciro wayarsa ya shiga tabawa. Da Emily ta gaji da tsayuwa sai ta fita gaban gate din bangaren Mama Baraka tana kallon katon gidan, hakan yayi daidai da fitowar Dr A-B bangarensu Kameela suna tafe Alhaji na masa hira, Kameela da yan'uwata da kuma Hajiya suna tsaye jikin gate din bangarensu. Alhaji be karaso ba ya tsaya nesa da bangaren Mama Baraka, Dr A-B ya karasa shi kadai ya kama hannun Emily da bata san Turhan na tsaye bayanta ba domin nata idanuwan suna gurin Kameela dake aiko mata da wani kallo mai cike da tsana da kiyayya. "Ka dawo" Mama Baraka da fitowarta kenan ta fada. "Eh zan wuce yanzu, mun gaisa da su, ashe kina da co-wife ban taba sani ba sai yau" Mama Baraka ta yi murmushi. "Ka ga zuwan ai yayi amfani, daman ba ni kadai ba ce mu biyu ne ita ce uwargida" "Maa Shaa Allah, Emily a nan zan barki ne ko kuma zaki raka ni Airport?" "Zan raka ka Airport" "Okay" Ya mikawa Mama Baraka hannu. "Thank you so much Madam Baraka i appreciate everything" Mama Baraka ta gaisa da shi, kusan abu nw da ya sana shaking hands da kowa. Sannan ya dafa kafadar Emily to him ita ce kadai yar'uwa ta jini da yake da a kusa a yanzu yana jin muhimamcinta fiye da baya. Tare suka nufi mota ya bude mata gidan baya ta shiga shi ma ya shiga yana dagawa Alhaji hannu. Mama Baraka ta shiga dayar motarta tare da Misra. Kameela ta bisu da kallo har motocin suka fice zuciyarta kamar zata fashe saboda bakinciki. "Hmmm, wai ni aka zo a nuna bakinciki, ga mijinta a gafe ta hada da nawa Aliyu ta zabi wanda take so ko? Ga wani yayanta wai shi mai kudi, ga ubanta bature, ga ta kyakkyawa arziki na daya ma ba da aure aka haife ta ba, da yanzu ina zan kai bakinciki nan? Ga Mama Baraka tana kishi da uwata, diyarta kuma ta karbe min miji, ta hada da nata, wannan bakinciki da me yayi kama? Shekarar nan idan ba so ake na haukace ba me ake so na yi?" Ta fada cikin kuka bayan mahaifinta ya bar gurin. "Ke yanzu miye hadinki da Aliyu? Idan ma dafa shi zata yi ta ci ai sai ta yi" Anty Shafa ta fada, Kameela ta kalleta a fusa. "Aliyu mijjna ne, kina tambayar alaka ta da shi? Duk ba ku kika kashe min auren ba? Kullum mijina yana cikin bakinku cin mutunci babu wanda baku masa, idan ku ba ku san shi ni ina son mijina, yanzu ai gashi nan ya sake ni" "Uban waye ya aikeki saka masa guba a abinci? Ke ba dan ya sake ki ya kyale ki ba ai da yanzu ma gidan yari za a kaiki, karyar banza karyar wofi har ke fada mana wani wai kina son shi, kina son shi kika tashi kasheshi? Ko kina son shi kike daukar sirrinki ki kaiwa Bakar Mama Baraka? Yanzu wa gari ya waya?" Anty Shafa ta maida mata da martani. "Idan ban tafi da damuwata gurin Mama Baraka ba ina zan je? Saurarata kuke yi? Burinku Aliyu ya sake ni kuma ya sake ni, ita kuma zata dauki bakar kafirar yarta ta aura masa ai" Hajiya ta daka musu tsawa. "Miye haka wai? Sai yayanta sun kwashe komai sun fada mata an dawo amana mana dariya? Ke kuma Aliyu autan maza ne da zaki zauna kina fadawa yar'uwa ki magana saboda ya sake ki? Ke daga kin auna arziki ma baki haihu da shi ba? Nan da kwana biyu zaki shige wani gidan, daman can Aliyu ba sa'ar auren ki ba ne, manyan mutane suke sonki kika nace sai shi waya sani ma ko ba banxa ya barki ba? Ɗan makiyinmu kika dage sai kin aura kuma kika aura uwarsa ta mana cin mutunci" Kameela ta fashe da kuka ta juya ta koma ciki a fusace. Turhan da ya shiga motar ya dauki hanyar gida, yana jin farinciki sosai domin Emily bata taba sake masa haka ba and he feel something special about her today. "Ina son Emily ba ki sani ba ne, na yi farin ciki kin samu family a yanzu, kuma na miki alkawari idan kika ba ni dama ta biyu ba zaki yi nadama ba, zan maida ke sarauniya zan baki gatan da ba a taba baki ba, ke kika fara dandanin dadin zama uba, ke kika fara saka ni wannan farinciki, kuma kika yarda kika aure ni saboda Ammy, na yi kuskure na sani, amman yanzu na miki alkawari zan jiyar da ke dadi na wadata ki da komai zan ninka miki farinciki fiye da wanda kika sani, shiyasa na yi alkawarin zan yi hakuri zan jira har ki aminta da ni, kalli yadda kike da kyau da shiga rai, kika ba ni ƴa mai kamanina, to me kuma zan nema a gurinki? Sai dai ni na nemi saka miki, ina son komai naki Emily ina son duk wani abu daya shafe ki, zan kaiki inda ban taba kaiki ba, zan siya miki tufafi mai tsada, zan rumgume ki na nuna miki yadda nake kaunarki na baki kulawa" Yana tuki da hannu daya dayan hannunsa kuma yama shafa kansa yana magana da kansa sai murmushi yake kai kace Emily ce kadai matar da ta rage masa a duniya. Ya isa gidansu tun kamin ya faka motarsa harabar gidan Ammy ya fahimci akwai baki a gidan domin yayi arba da manyan motoci da be tantance na waye ba. Ya faka motar ya fito yana kallon motocin ya tun kari kofar falon, sai kamshin turaren masarautarsu ya tunkari hancinsa. Ya tura kofar da hanzari ya shiga, dogaran da ya fara arba da su suka saka shi fadada murmushinsa, ya kai tsakiyar falon yana jin wata madarar dadi sakamakon arba da yayi da mahaifinsa zaune a falon na Ammy. EMILY POV. "Na ga nadama sosai a gurin mutumen nan, kuma na jidadi da kika yafe masa, kuna da ƴa a tsakaninku ya kamata ace kun fahimci juna" Emily dai ta yi shiru bata ce komai ba sai kallon titi take. "Duk inda namiji ya kai, Mutumen nan ya kai, kuma na tabbatar yayi nadama tun da har yake bibiyarki, wata kila baki san komai akan sarauta ba, amman dai samun dan sarki babban mutum kamarsa yana zubar da kai kasa da neman yafiya abu ne da ba a saba gani ba, shiyasa na yarda da nadamarsa, kuma dukanmu muna kuskure, turawa suka ce the devil you know is better than the angel you don't know, ina son ki san babu mai cilasta ki yi komai, amman dai ki yi a hankali, kar wani ya sake breaking heart dinki" "Turhan ya fada maka wani abu akan abokinsa ne?" Dr A-B yayi murmushi "Ya fada min yadda abokinsa ya ci amanarsa kuma yayi rawa yayi tsaki wajen ganin baki saurare shi ba, bayan wannan be fada min komai ba, ina miki wani furuci ne saboda ina hararo wani abu na dabam, kuma na san yadda halinmu maza yake ai, ki yi taka tsantsan" "Aliyu ba kamar sauran mazan da na hadu da su ba ne, a rayuwa ban taba haduwa da wani mutum mai rikon addini da gujewa tsaba addininsa ba kamar Aliyu, yana da amana, adan karamin lokacin da muka san juna da shi sosai na fahimci mutum ne mai kyaun hali ya nuna min kula, ba tare da duban addinina ba, ko Vito da ya maida ni yadda nake ya maida ni ne saboda na yarda na bar addinin musulunci na dawo nasa, amman Aliyu be taba duba wannan ba, ko a lokacin da ya taimake ni be san wacece ni ba, ya bi ni har a gidanku saboda ya damu ya san halin da nake ciki a lokacin da ban yi tunanin akwai wanda zai da mu da ni ba" "You trust him ko ba haka ba?" Dr A-B ya tambaya da murmushi a fuskarsa. "1,000%" Ta fada ba tare da fargaba ba. "Kin yarda da shi saboda wasu abubuwa da kike jin kin gamsu da su, hakan yana da kyau, amman dai duk da haka ki yi hankali" "Dukanku ba ku fahimce ni ba ne, Aliyu ba so na yake ba, ni ma ba son shi nake ba, ni ban shirya soyayya ba, ba a yanzu ba ko a nan gaba" "Time will tell, amman dai idan lokacin yayi ina fatan wani ne wanda na sani" Ya nuna agogon hannunsa sannan ya bude motar ya fita, ita ma ta fita, ta raka shi har ciki sai da zai shiga jirgin sannan yayi mata side hug. "Ki kula da kanki, a yanzu ina tunanin babu wata damuwa a tare da ke, idan ma akwai wani abun da kike so ko kike neman taimako ki sanar da ni" "Na gode sosai na jidadin da kake nuna min kulawa" "Always, idan komai ya laba abubuwa suka tafi daidai zan gabatar da ke a gurin Daddy, babanki mai kudi ne yarinya zaki shakata... Na gode da kika karbe ni a matsayin dan'uwanki na yi farin ciki da hakan" Ta yi murmushi tana kallonsa "Bye Sis" "Bye Bro" Ya juya zat tafi sai ta rumgume shi tana kuka, ya juyo ya rumgumeta yana murmushi, ta sake shi ya share mata hawayenta, sannan ya daga ma Mama Baraka hannu ya wuce. Emily ta juya ta nufi gurin da su Mama Baraka suke tsaye ta tsaya gaban mahaifiyarta tana kallonta Mama Baraka ta kasa tsayar da idonta guri daya saboda kunyar Emily take ji. Emily ta rumgumeta ta ji sanyi a ranta a yanzu tana da mutanen da zata kira da sunan yan'uwanta na jini. Mama Baraka sai hawaye ya sauko mata ya rumgume Emily kamkam ta lumshe ido. Misra ta kai hannu tana shafa bayan Emily tana murmushi. Motar Mama Baraka Emily ta biyo, Mama Baraka ta tuka ta har gidansu Ummi tana jin kamar ace za ta iya ta roke ta ta kwana a gidanta, amman ta kasa, daman kuma Emily ta fada cewar tafi son zama a gidan Ummi. [8/16, 8:57 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 6️⃣7️⃣ Turhan ya kalli Ammy dake sanya da Hijab tana zaune can gefe, ya dube manyan Bakin da mahaifinsa ya zo da su. Sai ya zube gaban mahaifinsa yana jin farincikinsa ya ninku marar misaltuwa. Ya kwashi gaisuwa ya sake kwasa sannan ya hannun mahaifinsa ya sumbanta ya shafa goshinsa a kai. "Ihlan beek ya farḥat ʿomri, sharraftna ya baba w nazalt fi bēt al-mara illi hia ḥayāti.” _Maraba da zuwan mutumen da shi ne farinciki, na jidadi ganinka mahaifina na jidadin da ka sauka a gidan macen da ita ce Rayuwata._ Mahaifinsa ya yi murmushi kadan babban abokinsa da yake tare da shi ya ce. "Mun biyo sawunka na, domin mun lura idan ba mu yi haka ba na zaka gane cewar kana da muhimmanci a gurinmu ba" Ya kalli Mahaifinsa yana murmushi "Na san inda da muhimmanci tun a ranar da ka saka siya ticket aka yi min fatan sauka lafiya, soyayya ce ban tabbatar da ita ba sai a yau, ko a mafarki ban taba saka ran kafarka sata iya taka gidan nan ba, ta ina kuka samu adireshin?" "Ta hanyar Mai Martaba" Ya nuna Ammy da bata ko kallon inda suke zaune. "Gurinsa muka fara sauka, shi ya saka yi mana jagora har zuwa nan" Abokinsa mahaifinsa ne yake amsa masa mahaifinsa be ce komai ba sai hannu da ya kai ya shafa kan Turhan. "Ya labarin mata ta samu?" Sai a lokacin ya tambaya, Turhan ya rage murmushin da yake. "Har yanzu bata saurare ni ba, bata aminta zan iya kula da ita ba, bata yarda zan bata kulawa ba" "Baka fada mata ƴaƴan sarakuna basa karya ba?" "Bata duba komai daga sarautarmu ba, zuciyarta ta bushe da kiyayyata, ko wace gangar na buga bata ƙara" "Ƴar wane Sarkin ce?" "Ita din ba jinin sarauta ba ce" "Tana da tsada ne har haka? A nawa za mu siye ta?" "Kudi ba matsalarta ba ne, ko nawa za a zuba ba zai siyeta ba, amman zan jira zan biyaya har na yi nasara domin na fara ganin alamar hakan a yau" "Kar jiran wasu Iyalin ya saka ka, ɓata wasu Iyalin ko na manta kana da mata a gida?" "Ban manta ba, ba zan yi kuskuren aikata wani kuskuren ba, nakan kirata bata amsawa na aika mata sako babu amsa, ni kuma sai na zabi daga mata kafa har ta huce, na maida hankalina gurin gyara abun da na bata, kuma an samu lokaci da ƴata" "Ina sanyin idanuwan take?" Sarkin ya tambaya da nufin Fatima. "Tana tare da mahaifiyarta, ta kan zo ta kwana biyu ta koma" Ya kama hoton Fatima ya nuna Mai Martaba a wayarsa. "Wata kila har yau baka bata damar sanin ainahin waye kai ba, baka tunanin idan muka saka baki zata amince?" Turhan yayi shiru yana nazari... "Da ace babu wanda yake zugata, babu mai saka baki, na san zata saurare ni, wani abun ba halin ta ba ne, a gidan da take zaune ne suka tsara mana komai, saboda abokina ne yana neman ya bata ni a gurinta shi kuma ya gyara kansa, wannan dalilin ya saka suka kiraka suka sanar maka saboda su bata ni a gurinka..." Ya labarta masa kadan daga abun da Aliyu yayi masa. "A ina iyayenta suke?" Turhan sai ya ki yarda da fadawa mahaifinsa asalin wacece Emily, saboda kar ya rage mata ƙima a idon mahaifinsa. "Mahaifinta Bature ne, nan yake zaune ba, mahaifiyarta kuma kawar Ummi ce wannan dalilin ya saka Aisha take zaune a gidansu Aliyu karkashin kulawar iyayensa" Shiru ya ratsa falon Mai Martaba be sake cewa komai ba, Turhan ma haka, ganin hakan ya saka Ammy ta mike tsaye, suka bita da kallo har ta haura sama. Mai Martaba ya kai hannunsa da kansa ya dafa kafadar Turhan. "Akwai kyakkyawan mata da yawa a jinsin larabawa, idan har matarka bata maka, akwai daga dangi na nesa da kusa, kai din mutum ne mai kima, ka yi iya yadda zaka iya ta fahimci, idan ta zabi ba zata zauna da kai ba, wannan ma shi ya fi alheri" "Matsalar ba ta neman yafiyarta ba ne kawai, ta neman soyayyarta ne" "Muna bautawa mata muna nuna musu soyayya da girmamamwa, amman balaraben mutum be yarda a wulakanta shi, be yarda mace ta taka shi, suna girmamamu muna ba su hakkinsu, karka manta kai namiji ne, kuma ɗan sarauta, karka bari ta gano rauninta, kuma karka bari makiyinka ya gano inda zame yake a jikinka, tun da har abokinka ya shiga gabanka to ka yi kokarin ganin be illataka" Mai martaba ya mike tsaye baya ya zuba masa wannan karatun a cikin kai. "Za mu tafi, wata kika za mu dawo kamin tafiya, wata kila kuma zan tafe tare da kai ne, ta kan iya yiyuwa na tafe na jira zuwanka, ka mika gaisuwa ga mahaifiyarka" Ya fara takawa cike da kasa mutanen da suke tare da shi suka rufa masa baya, sai da suka fice sannan Turhan ya fita ya tsaya kofar falon yana kallon manyan motocin har aka wuce da su, sannan ya juya ya koma ciki jiki a sanyaye ya shiga gurin Ammy ya sameta tana waya da wata kanwarta, ya zauna har sai da ta gama. "Ban yi saton ganin Sarki a gidan nan ba" "Yana sonka mana, ba abun mamaki ba ne" Ammy ta fada. "Yayi miki wata magana kamin na zo? Ya fada ai zuwan ba nawa ba ne kadai har da duba lafiyarki" Ammy ta dan yi shiru, da halshe larabci ta maimaita masa abun da ya fada mata. "Yace sun kawo jira, kuma sun zo neman afuwa da rokon na bari dansa ya zauna tare da shi wai yana fatan ban rike shi a rai ba" Turhan yayi murmushi. "Wata kila da Mai Martaba ya shige min gaba, da Aisha ta fahimce ni, ko da yake zugata suke ba lallai ta fahimta ba" "Kai kana ganin idan Mahaifinka da kansa ya nema maka aurenta zata ce aa? Ai iyakar kyautatawa fa mun mata, ba zama lallai ta duba wannan ba, amman a matsayinta da kuma indai mutum kamar mahaifinka zai nemi aurenta zata amince mana, be kamata ace ta bar zuciyarta ta kone akan kuskure da kowa yana

Chapter 53 of 63