bude motar a hankali ta fita ta dauko kudinsa ta mika masa sannan ta nufi babbar kofar ma'aikatar da mutane suke hada hadar shiga da fita, sosai gabanta ya tsananta faduwa domin abu ne da bata taba yi ba zata fara a yanzu, wato aiki, a yanzu zata yi mu'alama da mutane bayan ta yankewa kanta mu'amala da kowa sai mutumen da shi ne silar dalilinsa take tsaye a yanzu wato Vito.
Bata bukatar wani yayi mata iso domin wannan ne karo na uku da ta zo ma'aikatar bayan zuwanta na farko da ta kawo CV ta, sai kuma zuwan da ta yi interview. Third floor ta nufa bayan ta shiga elevator and she pressed the buttom. Kanta ta daga sama tana kallon gurin tare da aje numfashi a hankali, feeling awkward and excited as the same time. Elevator ya rabe biyu ta fita tana kara gyara gashinta, kai tsaye ta nufi office din da aka musu interview ta yi knocking sannan ta tura ta shiga.
Wani saurayi ne a ciki da ba zai wuce sa'arta ba, ta dan yi mamaki domin wacan zuwan nata na farko ba shi ta tarar ba, ta gaisa da shi cikin mutunci ta gabatar masa da kanta.
“Nice to meet you Aisha, a nan an muku interview ne kawai, a hawa na hudu dama dake akwai wani office na farko shi zaki shiga, ki gabatar masa da kanki zai fada miki gurin da office dinki yake”
“Okay na gode”
Ta juya ta fita har lokacin bata jin sakewa domin yau ne ranarta ta farko kuma abu ne da bata saba ba. A tsanake ta nufi gurin da Elevator ke daf da rufewa mutumen dake ciki yana tsaye yana kallonta ita ma kallonsa take bata dauke ido ba har sai da elevator ta rufe. Tsaye ta yi a gurin tana kallon floor din da kowane office yake rufe. Babu tsammani elevator ta sake budewa mutumen da ta hango dazun a ciki shi ne har yanzu, matsawa ta yi gefe domin ba shi hanya a zatonta fita zai yi, sai ta ga tsabanin haka, be ce ta shigo ba kuma shi ma be fita ba, ganin kofar na kokarin rufewa a karo na biyu ya saka ta yi hanzarin shiga sai ta matsa daga gefe.
Kamata yayi ta gode masa? Saboda ita ya sake pressing floor din da take ko kuma dai wani abu zai yi, ya fasa. Ta dan dago ta kalleshi kadan sai ta ga idonsa yana kanta ta yi hanzari dauke kai.
“Okay Momy zan yi, i love you”
Ta ji ya fada sannan ya kai hannu ya taba black iPod din dake kunnensa. Da sauri ta dube shi jin ya ambaci uwa, a duk gurin da mutun yake tare da mahaifiyarsa ko ta ji ya ambace ta, ko kuma ta yi arba da alakar uwa da da, sai hankalinta ya tashi, sai ta ji wani abu ya tsaya a zuciyarta, domin ita bata san wannan gatan ba, bata san mutum daya a duniyar da zata nuna a matsayin dan'uwanta na jini ba balle kuma uwa. Ita din wane laifi ta yi ma iyayenta suka jefar da ita a gidan marayu? Su waye iyayenta? Wane addini suke yi? Wane yare suke ji? Ita ce tambayar da take yawan yi ma kanta.
“Excuse me, can i help you?”
Ashe kallonsa take da kyakkyawan blue eyes dinta masu matukar daukar hankalin mai kallonsu. Blue eyes din ne suka karafafa masa guiwar kallonsa har yake jin kamar ta taba wanzuwa a wani bangare na rayuwarta ta baya, wata kila kuma kyauta ne yake masa gizo har yake ganin haka, but this is the second time da yayi arba da mace mai blue eyes a Africa.
“No, I'm sorry”
Be sake ce mata komai ba, sai dai har lokacin kallonta yake ta gafen ido, ita din ai ta kai ayi mata kallo fiye da goma ma, ba daya ko biyu ba, but wait ina ilminsa da tarbiyarsa da koyarwar addininsa suka tafi? A take yayi hanzarin dauke idonsa gaba daya daga barin kallon abun da ba halalinsa ba.
‘Astagafullah’
Ya furta a ransa a daidai lokacin da elevator ya bude a hawa na hudu, ta dan kalleshi tana jiran ya fara fita sai ta ga be fita ba sai danna Apple watch dinsa yake, hakan ya saka ta fita cikin rashin sakewa ta fara tafiya. Sai a lokacin ya dago mistakenly idanuwansa suka sauka bayanta, sai ya rufe ido da sauri ya taba numbers din da suke jikin Elevator a take ya rufe yayi sama da shi to 5 floor.
Office din farko ta fara murdawa kamar yadda aka fada mata ta tura ta shiga.
Ya san ko dai ta tsaya a 4 flour ko kuma kasa zata koma, domin ma'aikatan kamfaninsa basa wuce 4 Flour the 5th floor is his and his entire team, and be taba ganin fuskarta a kamfanin ba, maybe she's among the new employees ko kuma ta zo gurin wani ne, ko dai minene she should be tsakanin fourth to first floor.
Sai ta samu kanta a babban guri da wasu dakunan a rufe, da dan tsoro irin na rashin sabo ta tura kofar Office din da shi ne farko ta shiga ba tare da ta yi knocking ba.
Matar dake sanye da abaya da karamin hijab half sunna, tana amsa wayar telephone ta dago tana kallonta fuska babu annuri. Emily ta tsaya a gurin gabanta na faduwa zuciyarta na tsanar matar da ko sunanta bata sani ba a yanzu, ba dan komai ba sai dan shigar ta wato suturar jikinta ta isar da sakon addininta ga duk wanda yayi ko zai yi arba da ita.
Ta tsaya a gurin har sai da ta gama amsa wayar, sannan ta karasa kusa da ita.
“Am... Sunana Aisha Muhammad ina daya daga cikin sabin ma'aikatan da aka dauka, kuma yau ne zuwana na farko, a office din da aka mana interview yace na shigo nan”
Ta fada cikin sakin fuska da murmushi, sai matar ta kara hade rai ta jefa mata wani kallo.
“Amman dai baki manners, ta ya zaki shigo cikin office ba tare da knocking ba? Kuma a farkon Shigowarki ai ya kamata ki tsaya sai an miki izini tukuna”
Emily ta sassauta murmushinta tana dan ji babu dadi, matar dake gabanta ba san yadda Vito ya jikata da gata ba, wata kila da bata fada mata magana irin wannan ba.
“Ki yi hakuri, mantawa na yi”
“Koma ki yi knocking idan na miki izini sannan ki shigo”
Ta fada kai tsaye tana bude wasu files dake gabanta, Emily ta tsaya kallonta like are you serious right now? Ganin hakan ya saka matar ta sake duban Emily.
“Kurma ce ke?”
“Aa”
Ta amsa sannan ta juya jiki ba kwari ta fice daga office din. Taja tsaki after Emily ta fice.
“Mtswwww, na ga Aisha Muhammad na dauka ke kadai ce Musulma a cikin sabin da aka dauka, ina cewa zan samu yar'uwa ashe kafirar ce, irinsu ne ke batawa musulmi suna, suna aikata abu ace musulmai ne, sunan mahaifinta da nata na musulmai amman fuskar kafirai da sarkar Cross a wuya, na tsani kafiran nan Wallahi”
Sai fada take kamar zata yi duka, abu ne da ta boye a zuciyarta saboda mu'amalarta da mutanen da suke garin Port Harcourt da kuma kamfanin mafiyawancinsu kistoci ne, amman bata kaunarsu ko kadan.
“Na riga na zabe ki, na dauka Musulma ce Wallahi, amman zaki ci ubanki”
Ta fada tana dora hannunta a laptop din dake gabanta. Emily na fita kai tsaye ta nufi gurin Elevator yake a fusace domin ta manta when last a wulakanta, kusan wani be taba gwada yi ma makamancin wannan wulakancin ba a sabuwar rayuwarta ta yanzu. Kamin ta karasa wayarta ta yi kara sai ta saka hannu a jaka ta ciro wayar, ganin sunan dake jikin screen din ya saka ta tsaya ta daidai numfashinta, ta sani idan har ta amsa wayar a cikin yanayin da take a yanzu na bacin rai zai ji haka a muryarta zai iya tashin building din ba tare da tsayawa ya ji dalilin bacin ran ba.
“Hello”
“Emily miyasa baki fita da motarki ba?”
“V, idan na dawo za mu yi magana”
Ta fada a daidai lokacin da ta dora hannunta Elevator zata danna.
“Answer me...!!!”
Ya daka mata tsawa har sai da zuciyarta ta yi rawa, and yes this is not the first time da yake tsawa, ya saba dukanta ko ya takata ko ya yi mata fada ko raunatata but shi kadai zai iya mata haka, idan wanin da ba shi ba yayi mata kallon banza sai ya saka an cire masa ido. Ta kashe wayar da sauri tana maida numfashi da karfi, rauni da damuwa irin na wanda ya rasa madafa suka bayyana a fuskarta. Dauke hannunta ta yi ba tare da ta taba ba, ta juyo ta nufi office din da ta fito. Vito na daga cikin dalilinta na son ta inganta rayuwarta ita kadai a yanzu ba tare da taimakonsa ba, duk kuwa da kasancewar shi ne silar komai nata a yanzu.
But tana son ta samu freedom so take ta samu yancin rayuwa ita da yayanta kamar sauran mata, ta jika a kangin bauta har yanzu so take ta yi rayuwa ita kadai ta tsayu da kafafuwanta, ta zama Independent woman.
Sai da ta daidai tsayuwarta ta nemi kwarin guiwa da confidence ta lullube zuciyarta da shi sannan ta kai hannu ta yi knocking Office din. Shiru ba ta ji ance ta shigo ba, hakan ya saka ta sake kwankwasawa a karo na biyu, ta sani a yanzu kam ba zai yi ace bata ji ba, sai dai dan wulakanci zata aje ta a gurin, kuma ba ta yi mamakin wulakancinta ba, saboda ga dukan alamu macen musulma ce, a iya kar ilimin Emily kuma musulmai ba su da kirki. Ta kusa minti biyar a tsaye sannan ta yi mata izinin shiga. Emily ta tura office din ta shiga sai dai wannan karon babu irin murmushi dake fuskarta a wacan karon.
A nan din ma sai da ta sake gabatar mata da kanta, matar ta dan kalleta ta dauke kai, after like 10 seconds, ta dubi Emily tace.
“Aisha sunanki ko what so ever, za ki yi aiki da ni a matsayin Assistant dita, aikinki shi ne kullum zaki shigo 6:30am 7am ta yi miki a nan, zaki yi mopping office din nan ki gyara komai, kamin na shigo, zaki hada min abun karyawa kamar tea ko coffee duk abun da yake available dai ko kuma nake ra'ayi, and duk abun da nake bukata na aika ko yi ke zaki min, and lastly Office dinki yana next to mine”
Ta mike tsaye cikin izza ta isa gurin wata karamar durowa ta bude ta dauko file da keys ta dawo ta mika mata.
“Akwai ID na aikinki a kamfanin mai dauke da sunanki da hotonki, zaki saka a wuya ne kullum idan zaki shigo kamfanin nan, a cikin file din akwai rules and regulations na kamfani ki yi saka hannu ki dawo da shi gobe”
Ta dora mata keys din a saman file.
“Wannan key din office dinki ne, hadi da nawa saboda ki samu damar gyara min nawa ko daukar wani abun idan bana kusa”
“Okay, Ma'am Thank you”
Emily ta furta sannan ta juya.
“And... Sunana Amal not Ma'am, ba dole sai kin yi aiki ba, idan kin duba office din ki yi tafiyarki, gobe ki shigo da wuri”
“Okay”
Ta amsa ba tare da ta juyo ba, Amal ta bita da kallo tana yatsina fuska har ta fice sannan ta nufi kujerar.
“Da wasu idanuwa blue kamar na aljannu, ko mage, waya sani ma ko mayyace, ko wace yare ne ma oho”
Sai kuma ta bawa kanta amsa.
“Zata wuce Igbo dama sune kafirai ai”
emily na fita office din ta nufi office din dake kusa dana Amal, sai da ta karewa kofar kallo sannan ta saka key din ta bude ta shiga. Komai fes ga computer da karamin tebur daidai ita, ita ma tana da karamin dorowa kamar Amal. Window ta kuma yana facing din gari da makwantan gine gine da suke wajen kamfanin sai titi da zata iya hango hada hadar mutane, ta dan samu sakewar zuciya wanda har ta kaita ga murmushin jindadi.
TURHAN POV.
Bude motar yayi ya fito yana shafa fuskarsa ya kalli kofar falon bayan ya rufe motar, sai da sauke ajiyar zuciya irin ta manyan mazaje yayan sarauta sannan ya sake komawa falon mahaifiyarsa.
Yana turo kofar falon Ammy ta juyo ta kalli kofar, ba yi mamakin sake ganinsa ba, domin haka yake mata naci a duk lokacin da ya zo gidan.
“Jajirtacen namiji, gwani na gwanaye, mai isa da tinkaho da burinkasa da sarautar gidansu, mai son farinciki ubansa fiye da na uwarsa, mai martaba auren ubansa ya watsar da na uwarsa”
Ya zube kasa yana taba kafarta damuwar dake fuskarsa kadan ya rage ta saka shi birgima, domin ya san ma'anar kirarin da Ammy take masa. Ammy ta matsar da kafarta daga hannayensa.
“Da haka kake da na ci da jajircewa a baya, da yanzu Aisha tana nan tare da mu, bata gudu ba”
Kansa a kasa ya soma magana cikin magiya tare da fatan zata amsa rokonsa.
“Ammy na dawo nan ne saboda na tambaya, a dan zaman da Aisha ta yi a gidan nan ta taba fada miki suna da kuma unguwar da gidan marayun da ta zauna a Lagos yake? Zan tafi Lagos din na bincika ko Allah zai saka a dace”
Har Ammy ta yi shiru sai kuma ta kalleshi.
“Eh ina zuwa”
Ta mike tsaye ta nufi hanyar da zata sadata da dakinta, wani sanyi ya ji ya sauka a zuciya jin cewar kamar ya kusan samun hanyar da zata sadashi da Aisha. Babu jimawa Ammy ta sauko tana kallonsa idauwanta a kankance irin bacin rai, sai da ta zauna sannan ta mika masa takardar dake hannunta.
“A lokacin da ta shigo ta dauki danta ba tare da na sani ba, ta bar min wannan akwai address dinta a ciki”
Turhan ya karba da sauri ya warware takardar da kana ganinta kasan ta jima a ajeye.
_Kin ce danki ya sha babban da sauran, wata kila dai baki fahimci danki ba ne, wata kila kin hada aurena da shi ne saboda kina neman mafitar yadda zai dawo gareki, amman duk halinsu daya, shi ma be san daraja ta ba, na fada miki musulmai ba su da kirki kika karyata ni, akan abun da yake zahirinsa, musulmai basa kaunar tubabben basa son kowa sai wanda ya tashi dan asalin dan musulmi, ba su da mu'alama mai kyau, basu san darajar kowa ba sai junansu, abun da kuke aikatawa dabam karantarwarku dabam, shi ma ďan da kike cika baki da shi ya wulakanta ni kamar wancan, duk akan me? Addininku? To na bar muku, zan koma a gurin da nake da daraja”
Tun gabani ya gama karanta wasikar zuciyarsa ta tsinke hawaye suka taru a idanuwansa har suka sauko a fuskarsa.
“Saboda kai Aisha ta ji cewar bata da gata a gurin Musulmi, ka karyata duk wani abu da na yi amfani da shi na karfafa guiwar yarinyar nan, kuma ka saka ta ji cewar na yaudareta, ba ni da wani addireshinta bayan wannan”
Turhan ya daga kansa ya kalli Ammy, ganin hawaye a fuskarta, ya saka shi cikin tashi.
“Zan nemo ta Ammy, zan nemo ta ko da hakan yana nufin na yawace duniyar nan, zan samo ta ko da hakan yana nufin rasa rayuwata ne, zan kawo miki Ammy wannan alkawarina ne”
Ya mike tsaye ya share nasa hawayen ya fice daga dakin rike da takardar.
_________________________
Wai me Turhan ya aikatawa Aisha ne? Me yasa Ammy ta gagara shiryawa da shi?
Anya kuna ganin Emily zata jure aiki a karkashin Amal kuwa? Bayan kuma Amal bata son kafirai, Emily kuma bata kaunar musulmai?
[4/20, 9:57 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
3️⃣
Teburin dake office din ta nufa ta dora file din da Amal ta bata, tana karewa karamin office din da be karasa girman na amal ba kallo. Sannan ta nufi windows ta bude tana kallon kasa, iska mai dadi na shigowa office din. Ta dade tsaye a haka sannan ta matsa baya ta rufe, ta nufi gurin da durowar office din take ta fara budewa tana dubawa, kusurwar farko an rabata biyu ne da wani katako tsakiya, daga sama an dor Kur'ane daga kasan kuma Bible, doka ce ta sabon CEO na yanzu, aje Qur'ane mai fassarar turancin, da Bible a kowane office a kokarinsa na son tallata addininsa, ta dayan bangaren kuma gudun complain ya saka yake aje Bible din domin baya kowa hakkinsa, sai idan baka bujata sai ka yi magana a dauke.
Risinawa ta yi ta rage tsawonta ta taba Bible din da hannunta na dama. Wani bangare na maganar da Momy ta yi mata ya dawo mata sabo a yanzu.
_Emily karki bari yaron nan ya yaudareki, kar kyaunsa ya ja ki ga halaka, domin bayan kyaun ban ga wani abu da yake da shi ba, mun fi shi arziki a gidan nan, zaki samu miji mai kudi mai komai ba, zan inganta rayuwarki ni da mijina, please karki kunyata mu, abun kunya ne ace kina gidan Pastor kin bar mu kin bi musulmi, karki lalata rayuwarki da kananan shekarunki please Emily, ki rike wannan Bible din ki yi karatu bana son na sake jin maganar yaron nan, kin ji my beautiful Diamond Girl_
Ta dauke hannunta da sauri tana hawaye, ta rufe durowar ta juya ta zauna a gurin ta jingina da ita sai kuma ta fashe da kuka, jikinta na karma kamar wanda ta firgita.
“Hamza ka cuce ni... Ka cuce ni... Ka raba ni da matar da ta rike a matsayin ƴa, kasa na butulcewa macen da suka rike ni da amana”
Ta girgiza kai.. Ta dayan bangaren ba laifinsa take gani ba, laifin zuciyarta ne data barta ta fada soyayya da mutumen da be san darajar addininsa ba balle ita. Wani irin duka ta kai kirjinta tana jin kamar ace zata iya ganin zuciyarta a fili ta yi mata duka. Tuna cewar ba a gida take ba ya saka ta natsu ta sassauta kukan da be gama fita ba, ta hade kanta da guiwa.
Ta dauki lokaci tana rarrashin kanta sannan ta mike tsaye ta dauki file din ba tare da sake taba komai ba ta fice daga office din ta rufe kofar da key ta nufi hanyar da zata sadata da elevator.
Babu abun da take a cikin elevator sai tunanin yadda rayuwa tayi da ita. Har ta isa first floor bata hankara ba sai da kofar ta rabe biyu, ta fita ba tare da ta lura da mutanen da suke tsaye suna kokarin shiga elevator ba. Daya daga cikinsu ya biyo bayanta a sirance har sai da ta yi rabin gate din dake da tsayi sosai.
“Excuse me Miss”
Ta juyo ta yi sai ta yi arba sa wani bakin mutum bayanta yana sanye da yellow t-shirt da black jean.
“Can i help you?”
“Yes”
Ya matsa kusa da ita.
“Kin shigo neman wani abu ne? Ko kina daya daga cikin team din Resrezor?”
“No na fara aiki a nan ne”
“Yaushe?”
“Yau”
“A ina? Wane guri office dinki yake?”
“Four floor hannun hagu office na biyu”
“Nice to meet you, I'm William, ina 5 floor office na hudu”
Ta mika masa hannunta kamar yadda ya mika mata nasa.
“Emily”
“Nice to meet you Emily, kin samu aboki yanzu”
Ta yi murmushi tana kallon sarkar Cross din dake wuyansa hakan sai ya saka ta ji dadi ganin kirista ne dan'uwanta.
“Har kin tashi ne?”
“Eh”
“Okay Bye”
Ta yi murmushi ta juya ta cigaba da tafiyarta. Shi kuma ya tsaya a gurin yana kallon yadda wandon jikinta ya dame jikinta yayi mata kyau.
“Wow...”
Ya shafa kansa sannan ya juya ya cigaba da tafiyarsa. Ta isa gida da wuri saboda ta samu abun hawa da wuri, sai da ta sallame shi sannan ta kwankwasa kofar gate din. Mai gadin ya bude mata ta shiga tana amsa gaisuwarsa. Tura kofar falon ta yi ta shiga sannan ta rufe ta cire talkamin kafarta ta saka na falon sannan ta karasa ciki. Ganin kwalbar giya aje a tsakiyar center Table din dake falon ya karantar da ita V ya bar gidan cikin bacin rai, domin abu ne da ta sani, idan ransa ya bace giya yake sha ko marijuana.
Da sauri ta jefar da Jakarta da file din hannunta ta nufi dakin da London yake ta bude gabanta na faduwa, ta duba dakin har bandakin baya ciki, hakan ya saka hankalinta ya kwanta domin shan abun maye ko drugs abu ne da bata son yana yi a gaban yaranta, wannan yana daya daga cikin dalilin da ya saka ta zabi raba gida da shi, ta zabi rayuwa ita kadai sai yaranta.
Fitowa ta yi ta dawo falon ta dauke kwalbar ta shiga Kitchen ta tsiyaye ragowar barasar dake ciki ta fasa kwalba ta zuba a dustbin sannan ta wanke hannunta ta fito.
A gurin da ta jefar da jakarta ta zauna tana sauke ajiyar zuciya, tare da daga kanta tana kallon rufin falon zuwa gurin da katon plasma ta yake. Ta sani ahalin yanzu bata rasa komai ba sai kwanciyar hankali, Vito ya jika da kudin da bata jin akwai wata mace mai tarin dukiya irinta, ita kanta bata san adadin abun da ke account dinta ba, domin kowane sati sai ya saka mata kudi ita da yaranta London da Fadima duk kuwa da kasancewar karamar yarsa Fadima bata son shi, amman be taba kula haka ba saboda yana matukar kaunar mahaufiyarta.
A cikin gidan da take rayuwa gidane da ko wucewa kawai ka yi a gaban gate din sai hankalinka ya tashi saboda kyaunsa, shi kansa nasa gidan be kai nata kyau ba, ya zuba mata kayan more rayuwa daga sutura har abubuwan ado na kawata falo ko daki, ga mayan motoci da ya zuba mata a cikin gidan, ga Nannyn da ya dauka mata mai kula da yaronta, ya saka yarta a makarantar kudi ta yayan manya, London kuma da ya kasance Autism ya biya ake karantar da shi a gida. Bayan kudin da ya biya aka yi mata aiki, ya kaita waje ta yi karatu.
Amman duk da haka tana jin ta rasa wani abu a tare da ita, she felt something is missing inside her.
Ji take bata cika ba har yanzu, tana jin akwai abun da ta rasa kuma bata san miye wannan ba, sai dai ta san dalili daya da ya saka take son tsayawa sa kafafuwanta, wannan sirri ne da ba zata iya budewa kowa shi ba.
“Good Afternoon Ma”
Cewar Chidimma bayan ta shigo falon. Emily ta kalleta da irin fuskar nan na wanda tunani be gama sakin kansa ba.
“Chidimma, a gaban London V ya sha alcohol dazun?”
“Aa bayan na shiga dakin Landon ne na canja masa tufafi saboda za su fita tare”
Ta sauke numfashi a hankali.
“Okay please duk yadda za'ayi karki bari yarana su ga lokacin da Vito yake shan giya, balle har hannunta ya kai gurin”
“Okay Ma zan kiyaye”
“Ki shirya musu wani abu ni zan yi bachi”
Tana fadar hakan ta mike tsaye ta dauki jakarta da file din ta haura sama ta shiga dakinta ta aje jakar da file din a kusa da gadonta ta kwanta, tunani ya fara kawo mata ziyara kamin bachi yayi gaba da ita.
ALIYU POV.
Dagowa yayi a hankali ya kalli kofar office din da aka turo. Mutumen ya karaso gaban teburin cike da girmamawa ya bude masa daya daga cikin files din da suke hannunsa.
“Nan zaka saka hannu”
Sai da Aliyu ya gama abun da yake a computersa sannan ya kalli file din ya saka hannu.
“Ranka ya dade cikin sabin ma'aikatan da aka dauka har da turawa?”
Cewar mutumen dake tsaye gabansa, shi dai be ce komai ba, har sai da ya gama saka hannu a duka files din.
“Na ganta zata fita dazun”
Aliyu ya sake dubansa ba dan ya fahimci inda
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 63