Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
jirana. Ya sallami mai okadan ya goya ni ya tafi da ni wani kangon gidan ya aje ni a nan, be dawo ba sai dare ya dawo da kudi mai yawa ya fada min ya siyar da babur dinsa kudin ne zamu hada da wanda ke gareshi mu tafi garinsu. A gurin ya bar na kauna ni kadai shi kuma ya kwana a inda ya saba washe gari da asuba dai gashi tare da kayansa, ba bishi muka isa tasha ni da shi muka kama hanyar Kaduna. Shi a tsorace ni, a tsoroce hankali be kwanta ba sai da muka isa cikin garin kaduna. Garin da ban taba zuwa ba kuma ban taba saka ran zuwa ba ko a mafarki sai ranar. A cikin tashar ya saka ni saka hijabi, kusan ko'ina muka bi kallona ake saboda farin fatana ba fari ba ne na sauran mutane, fari ne mai haske sosai da ya fi kama da na turawa ga kuma idanuwa blue. Tashar muka bari muka isa wata dabam muka hau motar garinsu Khaleepa, garin da basa son tubaben, basa marasa ba ni, bana tausayin kaddara da kuma kuskure da na aikata, garin da suka koya min hankali da sabon karatu, suka maida ni wulakantacciya. _________________________ A jiya na yi mistake a page 17, na yi page din ne kamin na canja akalar labarin, bayan na canja kuma sai ya zama na manta ban yi editing ba, wadanda suka karanta wanda na yi ba edited one ba, za su ga Nace Emily baka ce, ku manta wannan kuskuren ku shafe shi a Kwakwalwarku, ni yar adamce ina kuskure dole na. Emily fara ce kamar yadda aka fada tun a farkon labarin. Shin zaku iya fada min abu daya zuwa biyu da kuka fahimta a page din yau kawai? Kuna son a karo? Zo na gani a kasa, ance da kare ana biki a gidanku yace mu gani a kasa๐Ÿ˜ Ma'ana ku suburbudo comments na suburbudo muku pages๐Ÿค™ Don't forget to follow my channel https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 *Karku manta ku yi Sharing* [5/1, 8:59โ€ฏPM] ๐—ž๐—ต๐—ฎ๐—ฑ๐—ฒ๐—ฒ๐—ท๐—ฎ ๐—–๐—ฎ๐—ป๐—ฑ๐˜†: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=KhadeejaCandy ๐Ÿ’ ABOKIN RAYUWA ๐Ÿ’* *ยฉ Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... โœ๏ธ Page 2๏ธโƒฃ0๏ธโƒฃ Mun sauka garin Rizaga (Sunan garin kirkiren ne) Da dare sosai kusan sawun mutane da yawa ya dauke. Daga tashar garin ya dora ni a babur shi ma ya hau daya muka kama hanyar gidansu, tafiya muka yi mai nisa sannan muka isa. Da duk inda muka bi muna ganin mazan garin kwance wasu a bakin kofafin gidajensu wasu kuma a fili. Bayan mun sauka ya biya mai achaban su biyu sannan ya nufi kofar gidan data kasance katuwa da aka yi da gambun kwano. "Su waye a nan?" Na ji an tambaya, sai Khaleefa ya nufi daya daga cikin maxan da suke kwance a wajen yace ni ne baba, mutumen ya dauko fitilarsa ya haska fuskar Khaleefa duk kuwa da kasancewar akwai hasken wutar nepa. "Lafiya? Hamza kai ne a dare haka?" "Lafiya kalau Kawu, bari na shiga ciki" Sauran mazan duk suka tashi zaune suna gaisawa da shi suna tambayar lafiya ya ce musu lafiya kalau. "Da muka a kuke tare?" Ya tamabaya bayan ya haska fuskarta. "Zuwa da safe za ku ji komai ba Kawu" Ya nufo ni muka doshi cikin gidan, Tun kamin mu shiga gidan na gama fahimtar gidansu family house ne, ashe kuwa na canka daidai da muka shiga ciki sai na bangare bangare na gidan, yana gaba ina biya har muka isa bangare da mahaifiyarsa take, tana cikin bachi ya tasheta ta zabura tana daura dankwali. "Hamza lafiya? Saukar dare? Kuma baka fada mana zaka zo ba?" "Lafiya kalau Inna, ga dai bakuwa na zo da ita a bata gurin ta kwanta, kuma idan akwai abinci a bata ta ci zuwa sa safe za mu yi magana" Ta kalleta daga sama har kasa a lokacin ina sanye da jean sai hijab din da Khaleepa ya siya min "Sannu da zuwa zo nan ki zauna" Na gaisheta ta amsa min, na karasa na zauna a inda ta nuna min zuciyata cike da tsoron abun da na aikata da kuma wanda zan tarar. Tuwon gero aka kawo min da miyar kuka, luma daya na yi na gagara ci domin ban san miye tuwon gero ba a lokacin, miyar kukar ma ban taba jin sunanta ba sai a ranar. Haka na kwana da yunwa, washe gari tun da asuba na ji garin ya karade da kiran sallah, Wallahi idan na ce ban jidadin sautin da na ji ba na yi karya, natsuwa ta sauko min, sai na ji kamar ina cikin wata duniyar ta dabam... A daki aka maida min shimfidar su kuma suka yi sallah a ciki, tun da na shiga bachi mai nauyi yayi gaba da ni, ban farka ba sai karfe tara na safe, ban sani ba ashe Khaleefa yana nan yana rigima da iyayensa akan cewar ba zai maida ni domin shi a yanzu tsoron komawa garin Lagos yake, kuma ni na yarda na biyo shi ba cilasta ni yayi ba. Suka kira ni aka tsare ni a gaban manyansa suka tambaye ni, da amincewata ya taho da ni na fada musu cewar eh ni na mince masa na ce masa mu gudu domin iyayen dake rikona ba za su bar ni na aure shi ba, kasancewar shi musulmi ne, suka sake tambayata shin zaki musulunta ki auri danmu? Na amsa musu a take cewar eh zan musulunta. Sai suka yi farinciki suka nuna jindadinsu musamman mazan, amman mahaifiyarsa kamar bata yaba da hakan ba. Da yamma aka aiko mai gari yana neman yarinyar da aka zo da ita da kuma Khaleefa. Muka tafi har da iyayensa irin bayani na yi a nan shi na yi a can shi kuma haka, mai garin ya gamsu yace gobe idan Allah ya kaimu za a kai ni gurin limamin garin na musulunta kuma a daura mana aure, suna tambaye ni wane suna kike so nace musu Aisha Muhammad, haka nake son sunana ya zama. A lokacin farinciki ne kamar ragagge ne, sai ya zama ban ji wani dauki na auren ba sosai ba, wata kila kuma ishara ake min cewar babu alheri a ciki. Yadda mai garin ya fada haka aka aiwatar washe gari aka kai ni gurin wani limani na musulunta kuma suka daura mana aure, kusan kowa zuwa yake kallona har sai an boye ni, abubuwa biyu ke kawo su, jin cewar ni ba musulma bace da kuma yanayin hallitata. A dakin mahaifiyarsa na fara zama kamin ya gina mana karamin dakin da zamu zauna a tare a bangaren mahaifiyarsa, ya siya mana katifa da zanen gado da dan abubuwan bukata na aikin gida domin ni ba ni da kowa kuma bani da kudin siya. Sannnu sannu ya fara koya min sallah karatun sallah da wasu gajerun addu'o'i kasancewata mai saurin gane abu sai na fara fahimtar yadda zan yi ibada ta. Kusan a lokacin bani da wata matsala kamar yadda idan na gaishe da mahaifiyarsa take amsa min kamar dole, ga kuma rashin iya girki, ya siya min gawayi da murhun gawayi ina girki da shi, akan girka shimkafa ko taliya, ko indomie na girka chabewa take saboda ban taba girki ba, shi kuma yana da saurin fushi, ko kirana yayi na dade ban amsa ba ko ban zo ba sai ya fusata, ya fara fushi da ni, ko gaba, idan ya fara gaba da ni sai ga na zama kamar marainiya yake kula ni, domin ba ni da kowa a garin, gashi mutanen gidan sun ki su saba da ni, ni ma naki sakewa da su, kullum ina ciki daki. Abun da na fahimta bayan aurenmu shi ne Khaleefa yana da farin jinin yan matan garin, shi ka kansa ya fada min kuma kanwarsa da ke dan leko ni muna taba hira wani sa'in ta fada min. Ban kuma yi mamaki ba domin yana da kyau ni kaina kyaun ne ya dauki hankalina a lokacin, gashi ya iya wanka idan ya shirya ba zaka taba yarda a kauye yake zaune ba, su kan shigo gani na wasu wasu kuma idan na fita tsakar gidan nake ganinsu ko su gan ni. Akwana a tashi dan abun da Khaleepa yake da shi ya kare domin ciki muke ci, ga mahaifiyarsa ko gishiri ya siyo min sai ta karba ta raba biyu ta bani rabi, taliya ma idan daya ce to rabi zamu aje mu bata rabi. Da kudinsa suka kare sai ya rika karbo mana abincin da suke, da safe kunu ko dumame, da rana kuma sai dai ayi kwado ko kuma asiyo abunci na siyarwa a ciki da dare kuma tuwon gero. Bana iya cin tuwon kunun ma kadan nake sha domin babu suga, da rana kuma sai na wuni da yunwa, na ga alamar yunwa zata halaka ni idan aka ba ni tuwon geron sai na dukula na hada da ruwa na rika hadewa ba sai na saka miya ba. Washe garin ranar Inna da kanta ta sallama min na fito ta ba ni tabarya wai ai da ni ake cin abinci yanzu, ta saka ni turfe ban iya ba amman haka na rika yi ba, daker na samu yayi na kwashe mata, na dawo daki ina duba hannayena da suka yi kwancin jini suna ciwo. Sai yace "Da sannu zaki saba, mu a nan garin yawanci duk gidan da ake cin tuwon gari a gidan ake surfe, Inna ma bata yi, amman da kin lura dayan bangaren ai har na siyarwa suna yi" Ban ce masa komai ba, gudun kar na yi wata maganar ya fusata. Wasa wasa matar nan ta fara sani surfen siyarwa idan aka kawo kudin kuma sai ta karba tace za a hada a kudin cefane. Gashi haka nan nake wuni da rana babu komai a ciki, domin Khaleefa be da kudin siya min abinci yanzu, sai can wata rana idan an yi kwado ta aiko min idan na ci cikina yayi ta ciwo, da dare kuma abinci kadan nake ci haka da safe. Kan kace me na rame na lalace ba kadan ba, idanuwana suka cicciko suka fito fuskar ta koma karama, kassana suka bayyana. A lokacin ne Khaleefa ya dauki katifar dakin ya siyar mahaifiyarsa ta hada masa da wasu kudi yayi kudin mota ya tafi Nijar gurin nema, ya bar ni babu komai sai damuwa, kullum da fargabar daka nake kwana nake tashi, ga abinci bana iya cin na kirki. Sai aka fara rade raden wai ina da kanjamau shiyasa na yarda na biyo shi. Wata rana ina cikin surfe matar da muke zaune da ita gida daya wadda take kamar matar kawunsa ce ta dube ni tace. "Aisha amman kamin Khaleefa kina da wasu samari ko?" Na yi murmushi ina gyara rigar atamfar da ta yi min yawa, daman tufafina gaba daya kala shida ne a gidan. "AA ban taba yin saurayi ba sai Khaleefa" "Ban yarda ba gaskiya yadda kike da kyaun nan haka ai sai maza sun yi ta kawo miki hari, ko da yake ance ku baku dauki wannan komai ba, ance dan miji ya yayi mu'alama da ku ba komai ba ni shiyasa sai an gwada mace ake aurenta" "Ba kowa ba, wasu dai suke yin haka" "Toh Allah yasa wannan rama taki dai ta yi yawa" Ban fahimci inda ta dosa ba dan haka ban maida hankali akan zancenta ba, na gama surfen na dauka na wanke na kawo na aje na nufi dakina. Na shimda tabarma na dora zane na kwanta, nan da nan sai bachi yayi gaba da ni, can cikin bachin na ji ana tashina kanwarsa ce wai na tashi na yi sallah, na tashi ina jin kamar na yi kuka, domin sallah na daga cikin abubuwan da suke wahalar da ni a lokacin saboda rashin sabo haka dai nake daurewa na yi. Bayan ta fice na dauki buta na zagaya bandakin, kamar ance saurara ki ji sai na ji muryar mahaifiyarsa kasancewar bandakin yana like da dakinta ne ta gafe. "Badan halin Hamza na son karya, shi gaba daya rayuwarsa ta karya ce ta son burge mutanen, ka tsallake garinku jiharku ka tsallaka har kudu kudun ma Lagos ka dauko mata, Allah kadai ya san dalilinta na biyosa, wannan ramar da take yanzu na fara tsorata da ita" Na kai hannu ma dafe zuciyata idona ya cika da hawaye, can na ji wata kanwarsa mai da da zo ta karba mata. "Yawanci fa yan kudun nan ance idan suna da hiv suke bin yan arewa saboda su lika musu, gashi nan a gari sai rade rade ake wai Ya Khaleefa ya dauko mai ciwo, wasu har da cewa wai ciki yayi mata aka korosu" "Ai yaje dai ya dawo, aure zan saka ya kara yaushe zai zauna da zabiya kalli idonta ma kamar matsafiya, ance a can fa kowa da kalar tsafinsu na gado, kuma nan gaba idan suka haihu ai zata iya kwashe yaranta ta koma can" Kasa fitsarin na yi na fito na dawo dakina na zauna na ci kuka na har na koshi. Sannan na fito na yi sallah, kalaman da na ji ya saka na ja jikina daga mutanen gidan domin idan wani abu ya faru za su iya cewa ni ce. A lokacin damuwa ta kara yi min yawa gashi tun da ya tafi be taba kiran waya yace a ba ni mu gaisa ba sai dai ya yi waya da mahaifiyarsa. A haka ya shafe shekara daya be waiwaye mu ba, sai dai yayi mana aike idan kuma ya aiko komai yana hannun mahaifiyarsa babu wani canji. Yanayin yadda ya turo kudi aka siya masa fili a kusa da gidan aka fara masa gina na fahimci ko wane kalar kasuwanci ko aiki yake can toh ya karbe shi, ina ta jindadin ina murna mijina zai gina gida mu koma a can mu tare, ashe ba ni yake yi ma ginin ba. Ranar da na yi ma mahaifiyarsa maganar ina son ta rika ba ni kudin surfen da nake na rika siyen abinci ranar ta yi min tatas wai duk abun da take min bana gani, ba zata sake min komai ba daman hakkin ciyarwarta ba a hannunta yake ba, har tana fadar musuluntar kawai na yi amman zuciyar kafirarce a kirjina. Da mutanen gidan suka taso madadin su shiga tsakani su bawa mai gaskiya gaskiyarsa sai duk suka goya mata baya, wasu suka dauki gaba da ni ciki har da kanwarsa da nake shiri da ita. Tun daga ranar ba a sake bani abinci ba, sai dai idan na yi surfe dan abun da na samu sai na siya abinci da shi, bayan surfe sai na rika hadawa da wanki domin na samu kudin su min auki, wahala sai ta taru ta yi min yawa har wasu kujera suka fito min kamar na sauyin ruwa kamar na wahala. Idan na samu matsala kadan da mutanen garin sai min gori akan kudin surfe na ko wanki, ko aika ko kuma wani abun dabam, sai min gori, wasu su zage ni ni da iyayen da ban san a ina suke ba, wasu suce min zuciyar kafirar ce tana cikin kirjina, wasu suce min tsintacciyar mage. Gashi idan ina son abu sai dai na fita na yi da kaina, babu mai bari na aiki danta, idan na fita mutanen su yi ta kallona. Ana sauran wata uku ya dawo wata rana ya kira waya sai aka kawo min na karba da murna ina kai masa gaisuwa sai ya rufe ni da fada. Wai an fada masa na yi fada da mahaifiyarsa na ci mata mutunci, kuma ina fita yawon gantali a cikin unguwa, shi ba zai dauki wannan ba. "Ba zan iya daukar wannan rashin kunyar da rashin tarbiyar kafiran lagos ba, yadda kike tubababiya dole ki dauki halinmu da al'adarmu wannan kiristancin da bakin hali ki aje shi a gafe, ba ni da kamar mahaifiyarsa" "Baka saurara ka ji bangarena ba, yadda kake da addini Khaleefa be kamata ka yanke hukunci ba tare da jin dayan bangaren ba" "Bana son jin bangarenki marar kunya, rashin tarbiyace zaki nuna min ko? Da an yi magana kice baki da kowa sai ni baki da kowa amman baki kokarin rike mahaifiyata? An fada min kuma gaba kika da kowa a gidan, ki gyara halinki Wallahi kamin na dawo Aisha" Ban iya cewa komai ba na fashe da kuka domin shi dai ba zai saurareni ba yan'uwansa kuma ba za su fada masa gaskiya ba. Madadin ya rarrashe ni sai ya kashe wayarsa na mikawa kanwarsa wayar ina kuka. "Baki san dadin yan'uwan ba, saboda baki tashi da kowa ba, kuma baki samu zuciyar kwarai ba shiyasa kike son idan ya dawo ya bata da kowa saboda gaki yar gwal ko?" Ban rama kalma daya daga maganarta ba domin a lokacin ban iya maida marta ni ba, kallonta kawai har ta fita. Haka na cigaba da rayuwa ta bakin ciki a gidan suka gade min kai bana jindadin zama da kowa, idan suna surfe su ta yi min haibaici tun bana fahimtar habaicin na su har abun ya fara damuna. Ina kofar dakina ina wanki mahaifiyarsa na madafa tana girka shimkafa da miya, sai gashi ya shigo dauke da kaya yayi burun burun gashi duk ya tarar masa kai yayi jiki sosai sai dai kuma yayi duhu a lokacin. Da gudu na je na rumgume shi ina murna, a take mahaifiyarsa ta daka min tsawa. "Ke ba mu san wannan rashin kunyar da rashin tarbiyar ta mutanen Lagos ba karki bata mana tarbiyar gida" Na sake shi ina murmushin karfin hali, domin idan na ce ban ji zafin maganarta ba na yi karya, ta taso ta sauri ta karbe kayan da ya zo da su ta kai dakinta kanwarsa ta kai masa ruwa yayi wanka, ya shiga dakin mahaifiyarsa ya canja kaya ya gaisa da mahaifinsa da yake kamar fanko a gidan, sannan ya shigo dakina ina ganin haka na tattara wankin na aje na bi bayansa wai ni mai miji. Abun da ban sani ba ashe shigarsa dakin ta shirya masa karya da gaskiyar abun da ban yi ba, sai ganin na yi yana ta hade min fuska. "Sannu da zuwa tun da ka tafi ko waya babu Khaleefa" "Tafiyata ai ta miki rana domin gashi nan kin samu sana'a kina yi, kin fallasani a gari kowa ya san bana iyar da ke" "Ko kawa ba ni da a garin nan balle na fada sirrina, ban taba fadawa kowa baka ciyar da ni ba, ban taba ba khaleefa" "wannan wanki da kike ai da shi da fadar duk daya ne" "ina yi saboda na samu abun da zan ci" "Matsalar auren yare kenan baku da tarbiya baku da rufin asiri ga rashin yarda da kaddara" Na nuna kaina ina kallonsa zuciyata na raya min kamar na Khaleefa da na sani ba ne. "Khaleefa ni kake fadawa wadannan maganganun? Ka chanja min ba, yanzu duk ka manta irin sadaukarwa da na yi? Ka yi tafiya shekara daya da wata uku amman daga dawowarka sai ka rufe ni da fada kana ta bani rashin gaskiya?" "Okay mahaifiyata zan bawa rashin gaskiya ke kuma na baki gaskiya kenan? Da kika zancen sadaukarwa sadaukarwar me kika yi? Ai ni na sadaukarwa ni da na dauko ki na kawo ki cikin yan'uwana, na musulumtar da ke, ba dan haka ba ai da yanxu ko mutuwa kika yi wuta zaki tafi" Kalleshi kawai na sauke kaina kasa kuka, daman idan ba kukan ba to me zan yi. "Tun da kin zabi haka, ki ta zaman wankewa jama'ar ga tufafi, sai ki ciyar da kanki" Ya fada, ashe kuma zai iya, sai gashi babu abun da ya sauya bayan dawowarsa, sai ya zama kamar yana kyamata saboda kurajen dake jikina na sauyin ruwa da kuma wahala, mu'amalar aure ma dan kawai ta zame masa kamar dole ne da ko kallona ba zai yi ba. Idan yana son abinci mai kyau zai fita waje ya siya ya ci ko ya siyo mahaifiyarsa ta girka masa... Wata rana na kebe kaina a daki ni kadai ina ta kuka, da nadamar da somin tabi ne a lokacin." ***. ***. *** Emily ta mike tsaye hawaye shar a fuskarta ta nufi dayar kujerar dake office din ta zauna jiki ba kwari ta kalli Aliyu dake kallonta cike da tausayi marar misaltuwa ta ce. "Akwai matukar zafi, da bacin rai a auren mutumen da baka so, akwai da ci a auren mutumen da aka cilasta masa aurenka, akwai tsananin bakinciki da nadama a auren mutumen da baya sonka, ba ka son shi...! Yawancin irin waษ—annan aurarraki sakamakonsu nadama ne, da dana sani, wanda kan iya haddasa ciwon zuciya da kan iya silar ajali mai shi. Amman ina makomar auren da aka gina akan soyayya? Miye tukuicin kyakkyawar alaka da kaunar da aka gina aure da ita? Shin minene ribarta?' Soyayyah ruwan zuma! Haka na ke jin sunanta a bakinsu, haka na ke kallonta. Hakan yasa ni shiga dakinta. Da fari tai min marhabun tare da yi min shimfida mai laushi, sai da na mika duka karfina na kwanta a ciki sai ta shammace ni, ban sani ba ashe a saman k'aya da k'usoshi tawa soyayyar tai min shimfidar, tai min matashin kai a saman narkaken garwashin wuta, daga lokacin sai na soma kiranta da dayan sunanta, wato soyayya ruwan guba! Ruwan daya fi ko wane ruwa haษ—ari a duniya, ruwan da kan aika mai yinta a lahira nan take ta, ruwan da wanda ya dandana ta zai gwammace mutuwa da rayuwa...' Na yi zaton idan na samu matsala da Khaleefa mutanen garin ko na gidan za su rike ni kamar dai yarsu ko yar uwa domin sun san ba ni da kowa, ban sani ba ashe ni shashasha ce, idan na samu matsala da Khaleefa har ta kai ga duka Wallahi babu mai raba mu sai mazan garin idan suna cikin gida, ta zama na yayi masa dadi sai ta kai ko numfashi na yi da karfi sai ya rufe ni da duka, idan na yi magana yace na kai karar duk inda zan iya, ko yace na fadawa duk wanda nake ganin zai zame min gata, wai takamarsa kawai a lokacin ba ni da kowa kuma ba ni da gurin zuwa. Tun kamin ya dawo ake gina, zuwansa karasa kawai yayi, aka yi fanti aka saka wuta, sati daya da gyaran na ga ana ta hada hadar biki a gidan, ashe aure Khaleefa zai kara aure be fada min ba sai ranar da aka daura masa aure, ina zaune a dakina na ga an shigo da katifa sabuwa ya siyo min, na karba na yi godiya na shimfida zanen gado sai ya jefo min turmin atamfa guda daya, a nan na san hausawa suna da wata al'ada wai idan namiji zai kara aure yana yi ma matarsa ta gida kayan fadar kishiya. Na karbi atamfar na masa godiya sai yace. "An daura aurena yau, wannan atamfar fadar kishiya ce, a kuma ga katifa nan na siyo miki a al'adar garin nan ko kuma mu arewa idan aka yi aure ana kawo yarinya da komai, ke kuma na ga ba wasu kayan kike da su ba, dan haka ki zauna a nan tare da su Inna, anjima za a kawo amarya a sabon gidan da na gina, bana son tashin hankali kun zauna lafiya, ki bita sau da kafa kin ga dai baki da kowa a garin nan ita kuma yar gari ce" Ina daga zaune na daga kai na kalleshi. "Ba zaki ce komai ba" Bance masa komai ba bayan kallonsa da nake har ya gaji ya kada kai ya fice. A lokacin na sauko daga kan katifar na ji ba zan iya kwanciya akanta ba, na fara yi ma kaina wadansu tambayiyin da ba ni da amsarsu. "To wai ni mi na yi ma iyayena suka jefar da ni? Miyasa na gujewa matar data rike ni kamar yarta? A wane dalili na tsallake shawararta da dokokinta? Na yi sadaukarwa ga wanda be san darajata ba, na bar ki na zabi iyalin da ba su san kimata ba" Na kwanta a gurin ina wani irin kuka mai karfi ina jin kamar zuciyata zata fashe... Don't forget to follow my channel https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 Kuma karku manta ku yi sharing [5/4, 6:26โ€ฏPM] ๐—ž๐—ต๐—ฎ๐—ฑ๐—ฒ๐—ฒ๐—ท๐—ฎ ๐—–๐—ฎ๐—ป๐—ฑ๐˜†: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 ๐Ÿ’

Chapter 16 of 63