Ikon da zai iya kula da yarsa, ya juya mata baya sai a yanzu da yarinya ta yi wayo zai dawo yace shi ne ubanta? Yarinyar da na gina rayuwarta da tsanarka? Yarinyar da bata taba yarda ta zo duniya da uba ba? Kai kan wane irin mahaukaci ne? Har kana da idon da zaka kalli Fatima ka fada mata kai ubanta ne? Allah ya waddaran namiji irinka, Allah ya kwashewa rayuwarka Albarka, ka yi hasara"
Kallonta yake kallon da ya hango tsanarsa a cikin idanuwanta ya karantar da shi kiyayyarsa a cikin kalamanta da muryarta, ta tuna masa da abubuwan da ya manta kuma yake ganin kamar ba komai ba ne, ta yi gaskiya shi din be cancani ya kalli Fatima ya fada mata shi din ubanta ne ba, amman hakan ba zai karya guiwarsa ba domin komai ya faru ne saboda rashin sanin inda take da kuma cikin da take dauke shi. Ya bi bayanta da kallo ganin rashin dacewar tufafin dake jikinta. A sanyaye ya juya ya nufi gurin da ya aje motarsa ya shiga ya zauna kalamanta na ta yi masa yawo a cikin kai.
Be kyauta ba ya sani, kuma ya zafafa da yawa a yanzu ya gane hakan, kuma ya fahimci kirjinta ya cika da tsanarsa da kiyayyarsa tana ina ma zai fara gyara abun da ya bata, tun da bata ba shi hadin kai, kamata yayi ace Aliyu yayi masa wannan yakin tun kamin ranar yau wata kila da abubuwa sun zo masa da sauki, tun da gashi ya san har da ya a tsakanin su amman be masa ba sai ma kokarin boye masa yake yana munafurtarsa, a yanzu ya kara gane Aliyu ba abokin kwarai ba ne, ta ina ma ya gane ta? Ina ya hadu da ita taya suka kulla alaka abu ne da yake bukatar ya sani..
Ya dauki wayarsa ya kira layi Ammy ta amsa kiran ya gaisheta ta amsa, kasancewarta uwa sai ta fahimcin canjin muryar danta ta yanayin yadda yake amsa mata magana alamar akwai abu a kasan halshensa.
"Ammy ina Fatima?"
"Tana can falo tana cin abinci, daker ma na samu take cin abincin, babu wanda take kira sai Aliyu da Aisha, gaba daya ta ki yarda da mu, na fada mata ni ina matsayin kakarta ne amman ta ki karbar hakan tace mahaifiyarta bata da kowa, ita kuma bata da uba, ban san yadda zan yi na fada mata kai ubanta ba ne, Turhan ka lalata abubuwa da yawa"
Ya sauke ajiyar zuciya yana taba hancinsa da har yanzu yake masa ciwo.
"Na sani Ammy zan yi kokarin gyarawa kamar yadda kika ce, ba za su karbe ni da sauki ba amman zan... Zan jure wajen ganin komai ya tafi daidai, wata kila shiyasa Allah ya kawo ciwon nan naki yasa na zo abubuwan nan suke ta faruwa"
"Kana ina? Ina Aisha take?"
"Ina asibiti, na kwana a gidan Aliyu jiya saboda ina tsoron kar na tafi tayi tafiyarta ban san inda zan same ta ba, kuma yanzu ta zo asibiti ban san wa take nema ba, amman dai kuka kawai take"
"Ka tambaye ta mana"
"Ba zata min magana ba, na gwada yin hakan ban dace ba, amman dai ko minene yana da muhimmancin sosai a gurinta domin kuka take sosai kuma hankali a tashe ta zo nan"
"Duk yadda zaka iya idan ka gano matsalar ka taimaka mata, kuma ka fada min ta hakan za mu yi ta yakin har mu yi nasara In Shaa Allahu"
"Okay"
Ya sauke wayar, ya sake fita motar jiki a sanyaye ya fara zagayawa ta asibitin har ya samu inda take zaune ya zauna nesa da inda ba zata ganshi ba yana ta kallonta, ta ya ta canja haka? Ina wacan yaron? Yaushe da bar addinin Musulunci ya yi ma kansa tambayoyin a take, tun yana tsayuwa da dadi har kafafuwansa suka yi tsayi domin yayi awa daya da rabi tsaye a gurin yana ganin Emily, a tsawon awa daya da rabin babu abin da Emily take sai kuka domin jikinta na raya mata ko dai Aliyu ya mutu ko kuma yana cikin mummunan hali bata san me zata yi a yanzu ba.
Sau goma sha daya yana yunkurin tafiya ya sameta ya sake tambayarta damuwarta sai kalamanta na dazun su rike masa kafa, sai dai kuka yana jin wani iri kamar dai babu dadi tana kukan ko ba komai kukanta na yanzu yana tuna masa da kukanta da ta yi a wacan lokacin har take rokon ya dawo da ita gida ya ki.
Ya shafa kansa yana jin babu dadi, lokuta da dama mutum ya kanki abu kuma ya zama shi ne alheri a gurinsa, ko kuma ya so abu ya zama abun sheri ne a gurinsa, a yanzu ya fahimci hakan domin gashi tsananin rabo ya saka ya samu haihuwa da matar da ya tsana yake ganin kamar bata dace da shi ba, ashe uwarsa ta iya zabe kuma ta hango masa abin da shi be hango ba be fahimta ba, kibar ma ashe da ta samu kulawa mai kyau jikinta zai canja ne yayi kyau ita ma ta yi kyau kamar yadda take yanzu, wato sai a yanzu ya fahimci ba karamin aika aika yayi ba, gaba daya ya rasa ta ina zai kama zaren lamarin ma balle ya dinke.
Hango waya a kunnenta ya saka shi maida hankali sosai gurin kallonta na son fahimtar abun da yake faruwa, bata ji ma da sauke wayar ba ya hango Ummi ta iso gurin da take zaune sai Emily ta mike tsaye Ummi ta yi mata magana sannan ta rumgumeta, can kuma ta kama hannunta suka shiga cikin asibitin. A nan ne kansa ya kara daurewa zuciyarsa ta hararo masa ko danta din nan ne ba shi da lafiya Aliyu ya turo Ummi ta taimaka mata? Waya sani ko Aliyun ma yana ciki? Amman kuma Ummi ai ba anan take ba Abuja take zama. Motarsa ya koma yana ta tunanin me ya faru me zai faru, be san a inda zai samu labarin komai ba sai da Kameela ta fado masa a rai sai dai kuma ba shi da Number ta.
Ya kira Ammy ya bukaci ta kira layin Kameela ta bincika masa abun da yake faruwa, sai Ammy ta fada mata da number Kameela kuma ta labarta masa Aliyu yana asibiti, ta gane hakan ne a lokacin data kunna wayarsa dake hannun Fatima saboda Fatima nata yi mata kuka sai aka yi ta kira ana tambayar abun da sauki.
"Ina tunanin ko dai ya samu hatsari ko kuma wani abun ne ya faru da shi"
Turhan ya sauke wayar a kunnensa yana wani kashe ido.
"Kam uban nan, wato Aliyu take yi ma kukan nan? Lallai ko a cikin munafukai wutarka ta dabam ce Aliyu, har ya aka yi irin wannan shakuwar da ita? "
Ta ji kamar ya tafi ya bi bayanta sai kuma wata zuciyar ta hana shi, ya yi ma motarsa key ya dauki hanyar gidan Ammynsa, sai da ya kusa isa ya ji kamar ba zai iya barin abun ya wuce ba yayi reverse ya juya sai kuma wata zuciyar ta tuna masa shi da yake neman mafita a yanzu ai be kamata yayi rigima ma be kamata yayi abun da zai saka Emily ta tsane shi ba, ya sake reverse ya juyo sai kuma zafin abun ya doki zuciyarsa taya wai zata zauna tana kuka hehehe akan wani katon banza munafiki? Alhalin tana matarsa? Da ama ace Aliyun yayi masa abun arziki da sauki ko shi ya bata aurensa ai kukan da take yayi yawa balle kuma yanzu a duk duniya ba shi da makiya kamar Aliyu.
Ya juya ya sake daukar hanyar asibitin sai kuma ya sake juyowa haka zuciya ta yi ta juya shi kamin yayi nasara cin galaba akanta ya kawo kansa gida gurin Ammy, ya shigo cikin falon ya zauna takaici ya hana shi magana. Ammy ta dube shi daman ta fahimci damuwa tun a dazun da suka yi waya.
"Me ya faru? Ko yunwa kake ji ne? Ko dai minene ka saita kanka be kamata Fatima ta kanka a cikin wannan yanayin ba"
Ya kalli Ammy sai a lokacin ya tuna da wani zancen abinci daman rabonsa da abinci tun wanda ya ci a jirgi.
"Wato Aliyu munafiki ne Ammy, Wallahi ban tana tsammanin haka daga gareshi ba, wai kin ga yadda yarinyar nan take kuka? Ashe duk shi take yi ma kuka kamar wani ubanta? Shiyasa aka ce makiyinka yana tare da kai Allah kadai ya san abun da ya shuka mata? Shi ko kunya baya ji ma? Ai na yi zaton ko mutuwa na yi Aliyu ba zai min haka ba, har da Ummi ta zo ta rumgume ta yadda kika san wani shirin film wata kila gidansa ko gidan Ummi take zaune, haka yake ta kallonta yana rayuwa da ita kuma ya san ina nemanta, ya boye min komai, ba wai ina kishi ba ne, sam amman dai ni ko dolo ne ai dole na nuna takaici ko?"
Yana maganar yana jin abun da be saba ba, daman babu wanda ya kai balarabe mugun kishi na bala'i, Balaraben mutum da muryar matarsa be son aji, ko da yake shi a yanzu ba kishi ba ne haushin Aliyun ne yake ji na abun da yayi masa.
"Zaka iya kwantar da hankalinka ka yi min bayani? Ni duk ban gane wannan kewaye kewayen ba"
Ammy ta tambaya yana kallonsa domin bata fahimci inda ya dosa ba, sai ya mike tsaye yana huci.
"Idan ma na yi kishi ai ina da hujja ko dan Fatima? Emily ko mutuwa ta yi dole na kare martabarta saboda wannan yarinyar, ai ba zan jidadi ace uwar yata ce take wannan shigar ba? Har tana hulda da abokina, lallai Aliyu ya hadiye kashin da zai zame masa masifa a wuya, ba fita ba wucewa, kuma har abada ni da shi Wallahi Tallahi babu wani uzuri, abun da yayi min ya fi ka dauki wuka ka chakawa mutum"
Ya koma ya zauna yana cizon hakora.
ALIYU POV.
Ya bude ido yana jin jikinsa yayi masa nauyi sosai kamar ba na shi ba, kuma yayi matsa tsami, amman karfin hali irin na namiji da juriya yana hada ido da mahaifiyarsa sai ya saka matar murmushi. Yayi yunkurin bude baki yayi mata magana sai ya ji bakin yayi masa nauyi kansa kuma ya fara ciwo daman shi ma kan na shi yayi masa nauyi. Ummi ta yi ma wata yar'uwarta magana ta fita ta kira likita ya shigo da sauri ya duba shi ya cire masa ruwan dake jikinsa ya taimaka masa ya tashi zaune aka kawo roba ya wanka bakinsa Ummi ta hada masa tea ya sha aka ba shi magani ya sha.
Ummi na kusa da shi zaune sai matsar kwalla take tana kallonsa.
"Ummi da sauki fa kina gani to kuka na me kuma?"
Cikin kuka Ummi ta ce.
"Allah kadai ya san zafin da kake ji amman ba zaka nuna ba dan kar na damu, kalli yadda suka maka rauni a kafa, jiki ko'ina duka"
"Saukin abun ma babu karaya, amman ko suwa gaskiya kashe ka suka so yi"
"Ni ban san ko suwaye ba, ni dai ina tsaye ina waya da Ummi kawai na ji duka ta ko'ina da itace da hannu, Allah yasa inda na tsaya kusa da mutane ne kuma ana hada hadar shiga Sallah Magariba domin an yi kira ne lokacin sai mutane suka hankalta da wuri suka kawo dauki, mutanen suka gudu, na ji dai ana ta Innalillahi ni ma kuma ina ta tun da suka hau ni da dukan, a nan jama'a suka taimaka aka dauke ni aka dora ni a babur din wani aka yo asibiti da ni, suka ce ba za su karba ba, saboda kaina da kafata suna zubar da jini lokacin ga hannayenta sun duka bana ma iya daga su, to daga nan dai hankalina ya bace ban san ya aka yi ba sai yanzu da na farko nan"
Ummi ta ce.
"Muna wayar nan da kai na ji kana ambaton innalillahi sai ina jin karar duka na san ba lafiya ba, ko dai ita yarinyar ko kuma Kameela tun da su ma ba hankali da su ba ko kuma shi Turhan din cikinsu akwai wanda ya saka aka yi maka haka, kiran yankewa yayi na fito na shiga bangaren Daddynka na fada mishi da ya gwada kira sai ta shiga, Allah yasa yana gida a lokacin shi yayi magana da su ya fadi asibitin da za a kaika kuma ya kira CP ya sanar masa maka, yanzu haka kofar nan police ne awaje ba abarin kowa ya shigo, sun ce sai ka farka za su shigo su dauki bayanai"
"Ummi ya aka yi kika zo?"
"A dare nan ban iya kwana a Abuja ba ai, mota muka biyo da rakiyar jami'an soji sha biyu na dare na sauka garin nan, kowaye ya maka wannan abun ba zai tsira ba In Shaa Allahu"
"Allah y sauwake, idan kun dan gana sai a bar shi ya samu hutawa saboda ya ji ciwo a kai yawan magana zai iya haifar masa da matsala"
Likitan ya fada sannan ya fice.
"Emilyn ma tun dazun take kira ta zo nan ba su barta ta shigo ba"
Aliyu ya kalli Ummi.
"Taya aka yi ta sani?"
"Ban sani ba, amman dazun wayar tana hannun mubarak ya fada min ta kira ya fada mata kana asibiti"
Ummi na rufe baki sai ga kiran Emily ya shigowa a wayar Aliyu dake hannun Ummi.
"Gata nan ta sake kira"
"Ummi abarta ta shigo mana"
"Kana ta ciwo wa yake ta wani Emily? Waya sani ko ita ta saka aka yi maka haka saboda yarinyarta"
"Ba zata yi haka ba Wallahi na san ranta ya bace amman ba zata saka yi min haka ba, ita ma fa tana cikin matsala, dan Allah Ummi ki barta ta shigo kuma dan Allah Ummi karki nuna mata wani abu ko da ta zo dan ta yi fada da ni ne, Wallahi ta fi ni gaskiya kuma ni ne ban kyauta mata ba, sannan kuma yarinyar ancutar da ita an kuntata mata har tana kallon musulmai a matsayin azzalumai, tana son musulunci na fada miki kafira ce ta musulunta wahala ya saka ta koma ruwa, wannan abun nake son na kankare a ranta kuma na dawo da ita tafarki na kwarai, labarin da na baki jiya ko rabi ban fada miki ba na wahalar da sha a rayuwa, ni kadai ne mutumen da ta yarda da shi, dan Allah karki nuna mata wani abu, idan muka kyautata hali da kuma zamantakewa da ita har ta fahimci musulmai mutanen kirki ne kuma ta dawo addinin ai mun yi jihadi babba ba karami ba"
"Ya isa haka, likita yace karka rika yawan magana"
Yayi murmushi.
"Ummi tana tsoron rasa dan autanta"
"Autan da baya jin magana ma? Ashe har guba yarinyar nan ta saka maka amma... Dai bari ka ji sauki tukuna, sai na ci mutuncinka Wallahi Aliyu"
Yayi murmushi, ita kuma ta mike tsaye ta mika masa wayar.
"Cire min password din"
Sai ya fada mata password dinsa sunanta ne tare da numbers, ta yi murmushinn jindadi ta fice daga dakin, sai da ta fita waje sannan ya kira Emily da wayar Aliyu.
"Hello... Aliyu"
Emily ta amsa da muryar kuka.
"Ba shi ba ne mahaifiyarsa ce, kina ina"
"Ina wajen asibitin na zo an hana ni shiga, Aliyun yana lafiya"
"Daidai ta ina?"
Ummi ta tambaye ta tana ina Emily ta fada, sai ta fita da kanta ta isa har gurin da Emily ta fada mata, Emily na hango Ummi ta mike tsaye gabanta na faduwa ta yi tunanin idan Ummi ta karaso gurin zata mata fada ne ko ta tuhumeta, sai da Ummi ta kawo sai ta ce.
"Ke ce Emily?"
Emily ta amsa ta hanyar daga mata kai a hankali cike da tsoro abubuwa biyu ta ci mutunci ko kuma ta fada mata wani abun ya sami Aliyu wanda ba shi take fata ba. Sai kawai ta ga Ummi ta rumgumeta.
"Ki yi hakuri, ba a kyauta miki ba kuma hakika an zalince ke"
Emily ta fashe da kuka Ummi ta dagota ta kama hannunta.
"Zo muje ki ga Aliyun"
Taja hannunta suka koma cikin asibitin Ummi ta shiga da ita har dakin da Aliyu yake.
"Gata nan ka yi a hankali ka san dai yanayin da kake ciki da kuma abun da likita ya fada"
Cewar Ummi sai kuma ta kalli Emily take share hawaye ta sake kallon Aliyu ta ce.
"Kuma ka bi a hankali karka kuskura ka ce zaka fada mata wata magana marar dadi, ka san dai ta fika tarin damuwa, ba zan lamunci hakan ba"
Aliyu ya kalli Ummi cikin wani irin jindadi da alfahari na furuncin da ta yi a yanzu, Emily ma ta kalleta tana mamaki da tunani. Ummi ta juya ta fita daga dakin ta rufe musu kofa. Sai shiru ya biyo baya Aliyu ya kasa kallonta ita ma ta kasa kallonsa sai jan majina take tana yawo da ido.
A lokacin da ta yi jihadin dagowa ta kalleshi a lokacin ne shi ma sarkin ya fada masa ya kamata yayi nasa jihadin.
"How are you Aliyu"
"How are you Emily"
Suka hada ido da baki gurin tambayar junansu ya kowanensu yake, shi ya damu ya san halin da take ciki a yanzu bayan rabuwa da yarta da kuma abubuwan da suka faru, ita ma kuma ta damu ta san ya yake ji a jikinsa na abun da ya same shi domin ta ga bandage a kansa da kafarsa da jikin ya nuna alamar duka ta ko'ina. Shi ya fara sauke idonsa daga barin kallonta yana jefar da tambayar da amsar ta yi masa nauyi gurin dauka.
"Har yanzu akwai igiyar auren Turhan akanki? Da igiyar aurensa kika gudu?"
"Ba shi da amfani, na rika na sake shi, ba ni da wata alaka da shi yanzu"
Yayi murmushi ya koma ya jingina da ginin dake jikin gadonsa ya rufe ido. Ba shi da dalilin rashin jindadi amsarta, dan haka ba zai ayyana abun da ya ji a yanzu a matsayin rashin jindadi ba, sai dan tausayin rayuwarta da kuma na yarta, ko da yake yadda Turhan yake neman haihuwa yasan ba zai cutar da Fatima ba, ita ma kuma yadda Ammy ta juya masa baya ba zai yarda ya aikata abun da zai saka ya sake rasa Emily ba.
"Kin manta baki fada min wannan ba a cikin labarinki"
Ya fada bayan ya bude idonsa.
"Ba shi da amfani, na riga na sake shi"
Yayi murmushi mai nauyi.
"A musulunci mace bata sakin kanta, ke matarsa ce har yanzu"
"Ni ba musulma bace a yanzu, kuma a addininmu mace sakin namiji idan bata ra'ayi"
"Ai amman idan ta yi signing papers ko? Ke baki yi ko daya ba"
"Saboda ba a coci aka daura mana aure ba ko kotu"
"Shiyasa kike matarsa har yanzu"
"Duk tsawon lokacin nan? Duk bayan abun da yayi min?"
"It does not matter ke kika gudu ba shi ya barki ba, Emily you're still his wife"
Ta matsa kusa da shi ciki bacin rai.
"I hate you for telling me that"
"I know"
Ya amsa mata, ta nuna idanuwanta.
"Na yi bakinciki wannan hawayen da na zubar saboda kai, hankali ya tashi saboda abun da ya same ka yanzu ka farka kana fada min I'm still Turhan wife, i hate you Aliyu... I hate you... I hate you... I hate you... So much"
Ta furta da karfi ba tare data daga murya ba, sai yayi murmushi mai sauti.
"i hate myself more, what else?"
"Na tsane ka da ka kasance abokin Turhan"
Ta juya zata fice sai ya ce.
"Idan kika fita baza su bari ki sake shigowa ba, and we need to talk akan gurin da zaki zauna da kuma Fatima"
Sai ta juyo kawai ta fashe masa da kuka ta zube a gurin zaune, komawa yayi ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya.
[7/10, 1:55 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=KhadeejaCandy
*🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
Page 4️⃣9️⃣
"Kina son zama da ummi na ko hotel za a kama miki? Ko da yake Hotel ba tsoro, ke ma kuma baki jin magana, dan haka zaki zauna da Ummi"
Bata kula shi ba sai kuka take rarewa.
"Emily kina son karasa ni ne, hawayen ki nan na san akwai kaso na a cikin zubarsu, ba ni da lafiya ki gani, zubar hawayen nan na ki kuma ya saka zuciyata nauyi, so kike na mutu ne?"
"Babu wanda zai fahimce ni, ni kadai na san wahalar da na sha, ni kadai na san damuwar da take cikin kaina, ba ni da kowa wannan ma kawai ya ishe ni bakinciki, yanzu kuma ya karbe min yarinya, be kamata ka kalleni ka fada min wannan maganar ba, Khalifa da Turhan ba ni da makiya irinsu a duniyar nan"
"Na fada miki ne, saboda shatawa kaina da ke da duk wanda zai rabe ki layi, abu ne da yake a hukunce ba ni na dora miki ba"
Ta kara fashewa da kuka har da buga kafa a kasa kamar yar yarinya, Aliyu ya tashi zaune kenan Ummi ta turo kofar dakin ta shigo, ganin Emily na kuka ya saka ta kalli Aliyu.
"Me ka mata?"
"Me zan mata Ummi ni da nake haka?"
"Toh dadi ya sakata kuka kenan?"
"Aa saboda na fada mata har yanzu akwai aure tsakanin ta Turhan ne"
Ummi ta dafata ta mikar da ita tsaye.
"Taso yata share hawayenki, ki daina bari ana ganin rauninki"
"Ummi zaku je da ita gida zata zauna saboda nan bata da kowa sai mu"
"Ita kuwa take da kowa tun da take da mu, je waje ki jirani kinji"
Emily ta share hawayenta ta fita dakin.
"Ka kwanta ka huta, zamu je da ita gida"
"Ummi karki bari ta gudu, kuma dan Allah ki kula da ita ki kwantar mata da hankali, Wallahi bana son damuwar Emily ko kadan, kuma ki fada mata da zarar na ji sauki zan dawo mata da yarta, sannu a hankali komai zai zama daidai"
"Zan kwantar mata da hankali, amman dai karka manta kai ma fa ka fada akwai igiyar auren Turhan akanta, karka manta da wannan"
Aliyu ya kalleta.
"Eh kuma hakan ba zai hana na taimaka mata ba, ko kwantar mata da hankali"
"Amman dai kar a wuce gona da iri, kar a tsallake iyakokin ubangiji"
"Subhanallahi, Wallahi ba abun da kika tunani ba ne Ummi sam sam sam babu wannan ko kadan, kawai dai ina tausayinta ne kuma ina son ta samu farinciki, ta dawo tafarkin musulunci"
"Ka san ni uwa ce, na kan iya hango abun da zai taho tun kamin ya taso"
"Toh gaskiya a nan baki hango daidai ba"
"Toh ga mu zuwa, Allah ya baka lafiya"
"Ameen, zan baki mamaki Ummi"
"Daman Mamakin nake son ka ba ni ai"
Ta shafa kansa ta yi murmushi.
"Zan je na girka maka abinci mai kyau, kamin na dawo na san ka samu yin bachi"
"Okay, can i have my phone please?"
Ya amsa yana sauke ajiyar zuciya, Ummi ta mika masa wayarsa sannan ta fice dakin taja masa kofa a hankali, a tsaye ta samu Emily ta rika hannunta suka fara tafiya Ummi na kwantar mata da hankali har suka isa gurin motar da aka kawo Ummi ita da Ummi suka shiga baya, daman front seat din akwai dan sanda daya a ciki, direba yaja motar yana tukawa a hankali har suka isa Family house dinsu Aliyu wato gidan da Ummi take zaune a Kaduna tare da Daddy, direban na faka motar harabar katon gidan dake cike da yan'uwa da abokan arziki da suka ji abun da ya faru da Aliyu kuma sun tafi Asibiti ba a barsu sun shiga ba.
Ummi ta bude motar ta fita tana amsa wayar Daddy dake sanar mata yanzu jirginsa zai taso daga Abuja zuwa Kaduna, ta doshi Entrance din gidan, Emily ma ta bude ta fito ta bi bayanta sai ta ji an kira sunanta da muryar da bata wayanci ko ta waye ba.
"Emily..."
Ta juyo domin jin dalilin kiran arba ta yi da direban da ya kawo su a yanzu, sai dai har ga Allah bata wayance shi ba domin rabin fuskarsa a kone take, ta sake juya domin be ce mata komai ba ita ma kuma ba ce masa zata yi ba saboda bata san waye ba.
"Emily... Ni ne Khaleefa ne.. Baki gane ni ba? Ni kam ba zan iya mantawa dake ba duk yadda kika chanja, tun da kika shigo motar nan na gane ke ce"
Yana magana cikin rawar jiki da rawar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 39 Chapter of 63