Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ka gwada Taliyar Hausa – Yar Murji yau! 📞 wa.me/+2347071821482 tuntube mu yanzu domin yin odar ku. 👉 Ka more ɗanɗanon gargajiya mai tsafta, mai daɗi, mai ɗorewa! "Okay bari idan na duba zan miki magana" Ya amsa sannan ya kashe wayar ya aje sannan ya dauki comb din yana gyara mata gashi, suna zaune a falo, shi kan kujera ita kuma tana kan kasa. "Daga gurin aiki ne" Ta dago ta kanta ta kalleshi. "Ban tambaya ba ai, Aliyu i trust you, kullum aka kira idan agabana sai ka ce min ga wanda ya kira, ina son ka san kai ka aje ni ba ni na aje ka, kuma kana aiki dole mu'amala zata hadaka da wasu wani lokacin, dole na yi hakuri, kuma kana da yancin haka, matukar be tsabawa addini ba kamar yadda kake yawan fada, kuma be tsabawa zamantakewarmu ba, ba zai kawo matsala ba, ni na yarda da kai, na san wa na aura" Ya ja hancinsa yana murmushi kadan. "Kin ance hadarin da ya baka kashi, gobe idan ka gan shi gudu kake, na dan shiga damuwa ne, saboda irin haka, kuma ya haifar da matsala kala kala a zamantakewata ta baya, na yi iya yadda zan iya wajen ganin ba a samu matsala ba amman hakan be samu ba, kuma ba a raba mata da kishi dole za ku yi kishi ai, kawai dai ba a son ya wuce gona da iri ne saboda yana haifar da matsala, ko ga matar ko ga miji ko kuma duka" "But don't get mad at me idan na yi kishi" Ta fada a shagwabe tana turo baki. Yayi murmushi ya saka hannayensa ya dagota "Come here" Ta daga ta koma saman jikinsa ya rumgumeta irin yadda ake ma yara har ya dan girgiza ta a hankali. "Thank you for trusting me, i love you Qalbin, ba zan ji haushi ba idan kin yi kishi, ke ma ina hango kishi a idonki, amman ki iya rike shi ki yi controlling dinsa kar ya cutar da ke" Ta lafe a jikinsa tana ta zuba shagwaba. Ya cigaba da shata mata kan a haka tana masa raki har da kuka wai da zafi. "Shiyasa ai nake miki a gida, ba zan yarda kina tafiya shagon gyaran gashi ana kalle min kaya kuma jansa da karfi ana wahalar min da mata ba" Ta kai hannunta tana taba chin dinsa zuwa wuya. "Babe..." "Mhn" "Ina son na yi ma Dr A-B maganar tafiya gurin baban shi ina son na gan shi na ji yayi shiru be sake min maganar ba" "Lallai kuma ya kamata ya hadaku ko a waya, kuma ina son idan kin samu time ki tafi ki gurin Ammy ki bincika Fatima ko lafiya" Ta kara daga kai ta kalleshi. "Ba matsala?" "Bana jin wata matsala to matsalar me? Ni da na rike na mallake ki na malleke zuciyarki, na san kin damu ki san halin da take ciki ai, kina da aurena yanzu idan ma Turhan yana gidan dole ya daga miki kafa, balle na san ba ya nan, kuma ba ni da hujjar hana ki ziyarta su tun da Fatima ta shiga tsakani, kawai dai abun da ba zan yarda ba shi ne ki shiga ki dade ko ki wuni, ni zan kaiki na jira ki gama abun da za ki yi na dawo da ke" "Na damu sosai na san halin da take ciki" "Na sani, ina karantar damuwarki ko ba ki fada min ba, ya kamata ace ko sau daya ne ta zo gidan nan ai" "Za mu iya tafiya gobe?" "Mu tafi anjima da dare" "Da gaske?" Ya kai mata rankwashi a kai. "Ina miki karya ne?" Ta dafe kan "Da zafi fa" Ya kara mata wani, da ta ga zai kara mata na uku sai ta sauka jikinsa da sauri ta dauki fillon kujera ta jefeshi da shi. "Zan kama ki ne ai" Ta masa gwalo ta gudu. Bayan Sallah isha'i ta shirya, Aliyu ya sakata mota suka dauki hanyar gidan Ammy. A waje ya faka ta bude zata fita sai ya sumbanci hannunta dake cikin nasa. "Ko da Ammy ta fada miki wata magana marar dadi karki ce za ki yi fada da ita a gaban Fatima" "Okay" Ya sake mata hannun ta fita ta rufe motar, sannan ta kwankwasa gate din gidan aka bude mata. "Ammy na ciki?" "Eh tana nan" Emily ta shiga tana sayen da hijabinta na islamiya da ya kai mata har kasa, cike da zumudin son ganin Fatima ta kwankwasa kofar falon, aka bude mata ta shiga. Da sallama yan matan da suke nan suka amsa mata bata zauna ba sai da ta tambaya ko Ammy na nan aka ce mata eh tana nan, sannan ta zauna zaman jiran fitowarta. Ammy ta dade sosai kamin ta fito falon ta zauna fuska ba yabo ba fallasa ta zauna tana kallon Emily dake gaisheta. "Lafiya kalau" Emily ta dan yi shiru na lokaci kamin ta ce "Daman kwana biyu ban ga Fatima ba, shi ne na zo na dubata" "Fatima kuma? Ba Turhan ya fada miki zai tafi da ita ba? Ai Fatima bata gidan nan tana gurin Babanta" "Gurin Babanta kuma? Ya fada min amman ban ce masa na amince ba, kuma ko bankwana bata zo yi min ba" "Bankwana me ko? Ba an kai miki ita kun yi biki ba?" Idon Emily ya cika da hawaye. "Amman sai a dauke ta a tafi da ita ba tare da an fada min ba, kamar na ni na haife ta? Wannan wane irin abu ne haka? Yarinya karama a dauke ta a kaita gurin larabawan da basa son kowa idan ba jinsu su ba? Kun zalince ta kun zalince ni" "Kin damu da ita kika bar ubanta kika auri makiyinsa? Ko kuma saboda ke sai ya fasa tafiya da yarsa gidansa? Ita ba jininsu bace? Yadda Turhan yake son Fatima ai ba zai bari a cutar da ita ba, ba fin shi sonta kika yi ba" Emily ta mike tsaye tana hawaye. "Ke ma fa uwa ce, zafin nakuda zafin haihuwa wahalar raino duk kin sani, da aka dauke Turhan daga gurinki ina ne baki shiga kin fita ba saboda ya dawo gareki? Miyasa ni zaku azabtar da ni da wannan?" Ammy ta mike tsaye. "Fita ki bar gidan nan, na girmi na tsaya sa'insa da ke, kuma karki kuskura dora misalinki da nawa, dan muna da banbanci, da kina son Fatima da labarin yanzu ai ba haka yake ba" Emily ta dubeta tana hawaye ta sake dubanta sannan ta fice tana hawaye har ta fita gidan. Ko da ta iso gurin motar Aliyu na tsaye jikin motar yaja jiranta, ya ga hawaye a fuskarta amman be ce mata komai ba ya bude mata motata shiga, ya zagaya ya shiga yaja motar, sannan ya kai hannunsa ya kwanto da kanta jikinsa ya rike hannunta yana tukin da hannu daya. Daman ya raya a ransa Fatima bata gida, ya san da tana gidan ta yanzu ta matsa an kawota gurin Emily ko dan ta ga sabon gidan da Emily take. Aliyu be tambaya me ya faru ba, hawayenta kadai sun sanar masa ba ayi da dadi a gidan ba da suka iso gida ya faka motar sai ya fito ya bude mata ya riko hannunta ta fito yana janye da ita har cikin falonsu. Saman kujera ta zauna shi kuma ya risina gabanta yana kallonta. Kamar jira take kawai ta fashe masa da kuka tana fada masa abun da ya faru. Yanayin fuskarsa ya sauya zuwa damuwa, sai dai be ce mata komai ba ya mike tsaye ya shiga dakinsu ya dauko wayarta data bari a gidan ya dawo falon, da kansa ya saka number Turhan dake wayarsa cikin wayarta yayi dialing sannan ya mika mata. Kallo daya ta yi ma wayar ta gane number Turhan ce saboda number bata Nigeria ba ce kuma akan rigimarsu ake ta san ba zai wuce ya kira mata Turhan din kai tsaye ba. "Are you okay with that?" Ta tambaya cikin kuka ya daga mata kai, sannan ta karba shi kuma ya zauna gefenta ya saka hannunsa daya cikin nata domin karfafa mata guiwa. "Hello..." Ta fada cikin sautin dake nuna ta yi kuka. Turhan yayi shiru be ce komai ba, ba dan kuma be fahimci mai magana sai dan kiran ya zo masa ba a lokacin da yake tsammani ba. "Turhan Aisha ce Emily" "Me ya faru? Me yasa kike kuka?" Ya tambaya daga dayan bangaren. "Na tafi ganin Fatima Ammy tace ka tafi da ni? Meyasa?" Ya lumshe ido ya shafa goshinsa a tunaninsa zata fada masa Aliyu ya mata butulci ne. "Bata min bankwana ba, tun da na yi aure bata zo gidan nan ba, a can bata san kowa sai kai, ta yi kankanta ta fuskanci kalubalen masarautarku a yanzu, kuma ni ina son ƴata, karka raba wannan soyayyar dan Allah, idan ma ba zaka yarda ta zauna a gurina ba, ka barta ta zauna a gurin Ammy mana, idan na so ganinta sai na tafi can na ganta, ka ce ba zaka sake cutar da ni ba miyasa ka yi haka?" Tun da ta fara maganar be ce komai ba sai da ta gama. "Kamin na dauke ta na yi magana ke, kuma alamunki be nuna min kin yarda ba, sannan na fada miki ba zan taba bari a taba ta ba, na zo da ita saboda ina sonta akusa da ni, kuma nan din ma gida ne, ya kamata ta san kowa kowa ya santa, idan tana bukatar zama a can ko nan zata zauna, amman gurin Ammy ba gurinki, Ammy ma da kanta ba zata bar ni na zauna da ita a nan ba, kuma ba zan so karatunta ya kasu guda biyu ba" "Zaka dawo da ita kenan?" "Zan dawo da ita, na yi nufin ta zauna na dan lokaci, amman yanzu tun da hankalinki ya tashi zan dawo da ita satin nan" "Na gode, tana kusa da kai" Yayi shiru na tsawon lokaci kamin ta ji muryar Fatima cikin haki tana fadin "Momy?" Emily ta kara matse wayar a kunnenta. "Fatima, kina lafiya" "Lafiya kalau, Momy i miss you" "I miss you too baby, kina lafiya babu wani damuwa?" "Babu, ina yin wasan doki yanzu, Momy na iya hawan doki, Momy Zaki zo?" "Aa" "I miss you" "I know, babanki ya ce zai dawo da ke gurin Ammy za mu ga juna a can" "Okay Momy i love you, ki rika kirana kinji Momy?" "Tohm, idan wani yayi miki wani abun da baki ji dadi ba ki fadawa Babanki kinji" "Tohm momy gidanki yana da kyau" "Eh" "Mu ma nan yana da kyau" "I know, zan aje waya sai an jima" "Okay bye i love you" "I love you too" Ta kashe kiran sannan ta kalli Aliyu. "Na gode" "Anything for you" Ta kashe wayar. A ranar ta kwana da salama babu tunanin Fatima ko son sanin halin da take ciki. A kokarinsa na faranta mata kuma washe gari ya saka ta shirya da wuri ya sauke ta gidan Mama Baraka shi kuma ya wuce aiki bayan ya gaisa da ita cikin mutunci da girmamawa. After ya fice falon ne Mama Baraka ta kalli Emily tana murmushi ta ce. "Kin yi dace mijin, Aliyu ya dade yana burge ni, wani lokacin har cewa nake be dace da Kameela ba, ashe an kaddara zai rabu da ita ya aure yata ne, ya zama sirikina, ina jindadin yadda yake nuna kulawa da damuwa akanki" Emily ta yi murmushi. "Yana da kirki, ga addini" "Kusan fa duk wasu dabi'u da hallaya da ake so a gurin namiji Aliyu ya hada su, Allah yasa mutuwa ce zata taba, ga Ummi ma tana kaunarki baki da matsala ta ko'ina" "Alhamdulillah" "Allah ya datar da yan'uwanki su ma, su samu mazajen na kaurai" "Ameen, har da ke ai Mama, ko Babansu Kameela zaki komawa?" "Kai anya, ai aurena tsakanina da shi ya kare, kuma ni yanzu ba wani auren zan sake ba, kula da ku ya wadatar, sai idan na ga na aurar da duka yayana" "Allah ya nuna mana" "Ameen Ya Rabbi, kina da labarin Fatima?" "Eh..." Emily ta bata labarin abun da ya faru jiya.. "Daman Aliyu ya fada min yana ganin kamar bata nan" "Ya zo nan ne?" "Eh ya kan biyo, har alheri yake kawo min, da nake tambayarsa ya kike kuna da labarin Fatima yake fada min yana ganin kamar Turhan ya tafi da Fatima" "Be taba min zancen ba" "Ni da har na yi zaton wata kila yana jin tsoron ko kar Rito yake ki bitto? Ya cutar da ita ne da shi shiyasa Turhan din ya dauke ta suka koma can, sai yace aa ba wannan matsalar ba ce, ai Vito ya dade da mutuwa" Wani rudududun Emily ta ji kamar saukar cida, ko a mafarki bata taba mafarkin Vito ya mutu ba, bata ma taba mafarkinsa tun da ta bar gidan? "Ya mutu yaushe? Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un" Ta kai tsaye numfashinta na rawa, jikinta ma haka nan da nan hawaye suka taru a idonta sai kuka. "Miye abun innalillahi a mutuwar kafiri kuma mutumen da ya addabeki? Yake neman rayuwarki data yarki da ta mijinki? Daman baki san ya mutu ba?" "Wallahi ban sani ba, Aliyu be fada min ba, babu wanda ya fada min, yaushe ne?" "Zuwansa na karshe da yayi muke wannan maganar da shi" "Miyasa suka kashe shi? Why not su kama shi su hukunta shi, be cancanci kisa ba" "Mutumen dake kashe mutane? Kuma idan yana raye ke kanki ai rayuwarki na cikin hatsari" "Kawai ya fada ne, amman ba zai iya komai ba, ba mamaki lokacin da ya turo min sakon baya cikin hayyacinsa ma, Vito ne mutumen da ya fara taimakon rayuwata, ya maida ni mutum na zama yadda nake a yau, miyasa za su saka masa ta wannan hayyar? Ban kyauta masa ba, ni ce sanadi be kamata ba" Kuka take sosai kai kace Aliyun ne ya mutu ma, daker ta iya janyo wayarta ta kira Aliyu. Jin muryarta da kuka yayi mugun daga masa hankali. "Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un, me ya faru Qalbina?" "Me... Me... Me... Yasa kuka kashe Vi.. Vito?" "Kun yi magana da Mama ne?" "Mutumen da ya taimaki rayuwata ya so ni shi zaku kashe, ya zama kamar na ci amanar sa kuma sanadina ya rasa ransa, bayan ka yi min alkawarin ba zaka kashe shi ba" Tana kuka tana maganar. Kashe wayar yayi sai ta kara fashewa da kuka sosai tana jin silarta komai ya faru, bata kyautawa Vito ba, be cancanci irin wannan sakamakon daga bangarenta ba. Babu jimawa Aliyu ya faka harabar gidan domin yana jin kamar ba zai iya jure rarrashinta ta waya ba, ba lallai ta fahimce shi ba. Ya shigo falon babu ko sallama a lokacin Emily ta ci kuka sosai har idonta ya kumbura, Aliyu ya zauna kan kujera ita kuma tana zaune kasa rike da dankwali a hannu sai sharbar kuka take. "Na yi rarrashinta har na gaji ta ki ta yi shiru" Mama Baraka ta fada cikin yanayin damuwa. Aliyu ya kai hannu ya karbi dankwali ya rike kanta ya shafe mata hawayen. "Wallahi Wallahi ba mu muka kashe shi ba, ba ta sanadinmu aka kashe shi ba, ko da aka aje an samu police har sun dauke garwarsa da ta matar da yake tare da ita, Chidimma sun kaita gurin aje gawa, lokacin da na nunawa Daddy sakon da ya turo miki, sai Daddy yace na sanar da Turhan saboda kar wani abu ya faru tun da har ya dauka Turhan kika aura ba ni ba, kuma Fatima tana gurinsu saboda kar ayi sake ya cutar da ita, na san Turhan ba zai saurare ni ba, ko ya dauki abun da muhimmanci shiyasa na aikawa Ammy da sakon, kuma na tabbatar mata ana kan nemansa, da sakon da ya turo miki aka yi amfani da Location din sim din aka gano inda yake a Lagos, amman ko da aka tafi sai aka samu gidan a rufe da shairdar police saboda an yi musayar wuta a gidan makota suka kira police amman ko da suka zo aikin gama ya gama sai gawa suka dauka, sun turo mana komai sun mana bayani, kuma da suka zurfafa binciken sai aka gano abokan sana'arsa ne suka masa wannan aikin, ba daga mu ba ne, Ki yarda da ni Aisha Wallahi tallahi a haka muka samu shi, sun turo mana hotuna, ban fada miki ba ne saboda ina jin tsoron kar hankalinki ya tashi" Yana maganar yana share mata hawayenta da dankwalin. Mama Baraka ta ce. "Daman su irin wadannan mutane ai basa tsawon rai, saboda sana'arsu ta shadari ce suna neman rayuwar wasu ana neman ta su" "Haka ne, amman Wallahi ba daga mu ba ne" Ta kwantar da kanta jikin Aliyun da ya sauko kasa yana kokarin fahimtar da ita. Mutuwar Vito wani abu da ya tsaya a zuciyar Emily kuma ya zauna zaman da ba zai taba yiyuwa ta manta ba, daga lokacin da ta ji labarin mutuwarsa sai ya zama bata da walwala saboda tana ganin shi ma ya cancanci farinciki, ta bangaren da take jin sanyi da ya kasance ba Aliyu ne ko ita ba ce siyar mutuwarsa, da ba zata iya yafewa kanta ba. Haka Aliyu yayi ta fama da ita yana nuna mata amfanin mutuwarsa, da kuma tausaya mata har ta fara kwantar da hankalinta. Ba ma kamar ranar da Mama Baraka ta kirata ta sanar mata Ammy ta aiko da Fatima gidan Mama Baraka saboda bata san gidan Emily ba. Ammy ta yi hakan ne saboda bata son aika direbanta kai tsaye gidan Emily din ne, kuma daman bata san gidan ba saboda sanin gidan da Emily take rayuwa da Aliyu baya cikin lissafinta a yanzu. Mama Baraka ta aiko Misira ta kawo mata Fatima a ranar farinciki da far'a kamar su kashe Emily da Fatima. Sosai Emily ta jidadi da yarta bata rame ba, kuma bata labarta mata wani abu marar dadi da aka mata ba, sai ma jindadi da take fada mata da wasu abubuwa da ta iya a zuwanta garin, tana ta bata labarin yadda masarautar take da mutanen cikinta. [9/5, 12:32 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08?mode=ac_t *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 7️⃣5️⃣ Kin dade kina sha’awar sayen kaya a wajen Khadeeja Candy amma ba ki samu dama ba? Kin shirya fara tanadin kayan Sallah ko na azumi tun yanzu? Ko kuma tanadin kayan auranki ko na ’yarki? To, ga sauƙi ya iso! ADASHE NE NA GATA! Ki zuba kuɗi, ki ɗauki abin da kike so daga: Sutura da zannuwan gado Kayan kitchen Kayan electronics (fridge, freezer, washing machine, gas cooker, da sauransu) Talkami da jaka Zanen gado Frames (flowers decoration ko standing ones) Console mirror Boxes na Lefe ko na traveling. Warmers iri-iri Food flask iri daban-daban Jugs da flask. Kai abin fa sai wanda rai ya so! Sauƙi ya zo, za ki mallaki duk abin da kike so a wajen Khadeeja Candy cikin aminci da kwanciyar hankali, babu cuta babu cutarwa. 📌 Tsarin: Zubi ne wata-wata da kuma sati-sati. 📌 Akwai sharudda da ka’idoji. Domin ƙarin bayani, ki/ka tuntube ni ta wannan lamba: 08036126660 Ko ta hanyar WhatsApp 👉 Danna nan https://wa.me/message/2Y7RIJEODZO2K1 Ko kuma ku yi join WhatsApp Group https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08?mode=ac_t Thank you 😍 🙏 Yana warware hannunsa da yayi alwala ya ce. "Ki shirya ina dawowa daga Sallah za mu tafi mu kaita" "Da gaske wai ba zata kwana nan ba? Ni ma fa ina da hakki da ita" Ta fada a shagwabe. "Toh haka Mama Ta fada min, za su aiko a dauke ta da karfe 9pm" "Kai ba zaka saka baki ba? Yaushe rabon da na ga yarinyar nan ta zo kuma sai ace ko kwana ba zata yi ba?" "Yanzu indai ba son kike Turhan ya zo gidan nan da wukarsa ya kwantar da kaina ya yanka ni ba, ina ni ina saka baki a lamarin yarsa? Hakuri za ki yi idan suka ga kamar ba ki damu ba za su daina, damuwar suke so daman ai, ni na tafi masallaci" "Allah ya dawo min da kai lafiya" "Ameen I love you" "I love you" Fadawa junansu kalmar suna son junansu wata sara ce da Aliyu ya koya mata, ba ya fita be ji kamar daga bakin matarsa ba, ita ma bata yarda ya fice be fada mata ba, furta kalmar i love you yana kara danko kauna da soyayya a tsakanin masoya ko da yaushe musamman wadanda suke son junansu. Kamin da dawo ta zubawa Fatima abinci ta kara ci ta shirya ita ma ta shirya. Key ya dauka da wallet ya rike mata kofar falon ta fita sannan ya fita ya rufe, mota ma shi ya bude mata ta shiga ta rumgume Fatima a jikinta. "Ba zaki barta ta zauna baya?" "Aa na fi son ta zauna a jikina" Ya kalli yadda ta lankwashe kai tana ta zuba masa shagwaba. Ba zai iya hanata ba, duk yana ganin kamar zaman zai taba ta, sai kawai ya kai hannunsa ya gyara zaman Fatima daga jikin Emily zuwa kafafuwanta. Sannan ya zagaye ya shiga dayan bangaren ya tashi motar yana tukin yana kai hannunsa ya daga Fatima idan ya ga ta kwanta jikin matarsa. Gaban wani katon shagon kayan alatu ya faka ya shiga yayi manyan ledodi uku ya dawo da su bayan mota ya zuba sannan yaja suka cigaba da tafiya. Harabar gidan Mama Baraka suka faka Aliyu ya fara fita ya zagaya ya bude mata ya riko Fatima ta fito sannan ya riko hannun Emily ta fito ya bude back seat din ya dauko ledodin biyu ya rike. "Ba uku na gani ba?" Ya ja hancinta sannan ya rufe motar. "Daya ta ki ce" Ya dafa kafadarta kamar wata kawarsa. "Uhm Qalbina, dazun Mama ta kira ta ce muna da bako tace na kawo ki bayan na dauki Fatima, sai na ce mata ta mana hakuri har sai idan zan kawo Fatima" "Waye?" "Sai kin shiga zaki gani" "Turha?" "Maybe..." "Ba zan shiga ba, idan ya fada maka wata magana marar dadi fa? Kasan ba zan kyale ba" "Ke yanzu kin shirya fada da kowa akaina kenan?" "Har da kai kanka ba zan bari ba" Ya bude ido. "Eyyyy" "Uhm" "Ba za ayi komai ba, muje ciki dai" Ya sauke hannunsa daga kan kafadarta suka jera suna tafiya, zuciyarta bata hararo mata kowa ba sai Turhan, wata kila zai fada mata wasu dokoki ne ko kuma yace zai sake dauke Fatima gaba daya. Shi ya fara rike mata kofar ta shiga sannan ya shiga, daman Fatima ta dade da shiga ta bar su a waje. Ta shiga da sallama tana ta rabon ido bata ga kowa a falon ba sai Mama Baraka da Fatima ke jingine da ita suna gaisawa. Emily ta kalli Aliyu yayi mata murmushi ta yi zaton karya yake dan kawai ya daga mata hankali ya fada mata haka, saboda haka ta taka masa kafa da kafarta sannan ta wuce kusa da Mama Baraka ta zauna suna gaisawa. "Ya ce mim wai ina da baki, ashe ba gaske ba ne" Mama Baraka ta kalli Aliyu. "Gaskiya ne, Aliyu je ka shigo da su, suna nan BQ da ka zagaya baya ta nan kadan zaka gansu" Sai da ya mike tsaye ya fice sannan Emily ta kalli Mama Baraka ta ce. "Su waye Mama?" "Wai tsohon mijinki ne... Ko Hamza ko Khaleefa, Ummi ta turo su gurina, saboda sun tafi can ita kuma bata nan sai ta kirani tace wai sun zo gidanta ne suna son magana da ke, ita kuma bata ma garin yanzu kuma tana ganin duk wani abun da ya shafe ki mijinki ya kamata a tuntuba ko ni" Fuskar Emily ta sauya sosai zuwa wani yanayi mai kama da fushi da damuwa. Sai dai bata ce komai na har aka turo kofar falon Aliyu ya fara shigo sannan mahaifiyar Khaleefa ta shigo tare da shi da wani kawonsa, duk a kasa suka zauna sai Aliyu ne ya zauna a kujera, Emily ta kalli Khaleefa da rabin fuskarsa take a kone idonta na cika da hawaye rayuwar data manta take tunawa a yanzu. "Toh ga su nan, sun min bayanin komai kuma sun roki alfarmar a kira ki su roki yafiyarki, na yi magana da

Chapter 60 of 63