Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kallon fuskarta. Ita kan bata ga wani banbanci a tsakanin kyauta na jiya, shekaran jiya da kuma yau ba. Mai da wayar ta yi ta aje, tana nan tsare da danta har ya farka misalin bakwai da yan mintuna. “Good Morning Sunshine" Suna hada ido sai ya koma ya kwanta ta rufe ya bata fuska sosai kamar zai yi kuka. “Chichi chichi“ "Okay zata zo yanzu" Ta fada ba dan ranta ya so ba sai dan Chidinma ta fi soyuwa a zuciyar danta fiye da ita a yanzu. Ta dauki wayarta ta nufi kofar dakinta ta bude fice tana jin kamar ta fasa kuka. Ta fito asibitin sai ta tsaya a harabar tana kallon mutanen dake hada hada kamar wacce ta rasa abun yi, gaba daya ta rasa me ke mata dadi. Daga inda take tsaye ta dagawa wata matar dake tunkaro inda take hannu matar ma ya dago mata tana murmushi. Emily ta fara takawa ta karasa gurin matar dake tahowa. "Sannu kin gane ni?” Matar ta dan yi jimmm kamin ta amsa. “Eh kamar ke ce na kusan kade yarinyar ki ko?” “Haka ne, kina aiki a nan ne?“ “No na shigo kawo ma wata abincin ne, ke fa?“ “Yarona ne ba shi da lafiya” "Da sauki amman?” "Eh” “Allah ya ba shi lafiya” Tana fadar hakan ta wuce abun ta ta bar Emily tsaye a gurin da mamaki kuma da takaicin yi mata magana da yi. “Okay…“ Ta fada sannan ta juya tana kallonta kamin ta tsuke baki ta cigaba ta tafiyarta, tana fita wajen asibitin ta dauki drop zuwa unguwarsu. Har ta isa gida haushin kanta take ji meyasa ta yi ma Matar nan magana gashi ta wulakantata. “Chere m, a ga m ala n'ulo nweta ego gi ugbua" Ta fada masa da yaren Igbo cewar ya dan jira zata shiga gida ta dauko masa kudinsa. "Okay" Ya amsa mata ta nufi gate din ta buga, mai gadinta ya fara lekowa ya ga ganta madadin ya bude mata sai ya bude ya fito ya nufi motar da ta shigo ya leka mai motar, hakan kuma ba karamin mamaki ya bata ba domin be taba yi mata haka ba. “Me ya faru?” “Babu komai ranki ya dade” Ya amsa sannan ya bude mata ta shiga, kamar zata yi masa magana sai kuma wata zuciyar ta hanata, dan haka ta maida hankalinta gurin manyan bakaken karnukan da suka fara kuka saboda shigowarta, ba karamin tsorata ta yi ba ganin manyan karnukan har biyar daure da sarka a harabar gidanta. Tsayawa ta yi cak tana kallonsu daya bayan daya kamin ta kalli Vito da ya fito daga cikin gidan. “Baka na son kare ka sani” “Na sani ba saboda ke na kawo ba” “Saboda wa?” Ya saka hannu aljihunsa ya ciro kudin da shi kansa be san nawa ba ne ya mika mata. “Je ki sallami mai mota, me yasa kika dawo yanzu? Ina London?” Ta kalli kudin kawai ta dauke kai sannan ta kalli karnukan. “A daure suke ba za su taba ki ba” Tana matukar tsoron kare, amman a haka ta jure ta shiga cikin falonta, Fatima ta zo da gudu ta tarbeta tana sanye da uniform din makaranta. “Momy good morning“ Ta rage tsawo tana shafa kan London “Morning My love” Ta amsa da murmushi kadan a fuskarta sannan ta daga kai ta kalli Chidimma dake jera cups a dinning. “Me yake faruwa a gidan nan“ “Kamar na me ranki ya dade?” “Me yasa Vito ya kawo karnuka a gidan nan? Kuma mai gadina ya leki motar da ta sauke ni yanzu, be saba min haka ba, kuma a yanayin yadda na ga Vito da alama gidan nan ya kwana” “Haka ne, Sir Vito ya kwana a nan a falon nan ma, sauran amsoshinki kuma sai dai ki bincike shi, ban san amsar ko daya ba” Emily ta kalleta daga sama har kasa tana kallon yadda ta saka riga da wando da suka dame mata jiki sosai suka fitar mata da halittar jiki, bata sake furta komai ba ta mike tsaye ta nufi hanyar dakinta, babu jimawa ta sauko rike da kudi a hannunta ta fice daga falon. Har lokacin Vito na tsaye Balcony din yana kallon gate din gidan kamar mai jiran shigowar wani, shi ma kallonsa ta yi daga sama zuwa kasa ta dauke kai ta nufi gate din. Ta bude da kanta, ga mamaki sai ta samu direban ya tafi sai wata farar sabuwar mota ce fake a baya kadan da inda mai taxi din ya faka. Ganin yadda ta tsaya kallon motar ya saka Aliyu ya bude motar ya fito ba tare da ya rufe ba ya doso inda take tsaye tana kallon motarsa, da sauri ta sauke idonta kasa wani irin fargaba da faduwar gaba suka tunkarota da bata san na miye ba, a ka'idar rayuwarta, tana iya kallon kowane kalar namiji ido cikin ido ba tare da tsoro ko jin wani abu ba, sai dai a yau ta samu kanta da kasa motsa ta balle kuma har ta ido da mutumen da yake cikin jerin mutanen da ta tsana. "Ki yi hakuri na sallami mai taxi din da kika hau ba tare da izininki ba” "Me ka zo yi nan?” Ya daga kai yana kallon gidan. “Na zo na bada hakurin abubuwa da suka faru ne, kamar hotunan da Fatima ta tura min ba tare da saninki ba, kokarin shiga rayuwarki son sani wasu abubuwan, aje aikin da kika yi saboda abun da Amal ta yi miki...” “Ka daina kokarin shiga rayuwata, karka janyowa kanka matsalar da ba zaka iya hadewa ba, sanin abubuwan da suka faru ba za su kara maka komai ba face su jefaka a ramen da ba zaka iya cire kanka ba, biya kudin taxi da ka yi kuma ban yafe ba” Ta juya ta fara tafiya. “Ban yi da gode ba, ba jarumi ba ne ni, balle a ba ni kambu ko ayi min jinjina, na zo nan saboda wani dalili, idan ba haka ba ba zaki gan ni kofar gidanki ba” Ta juyo ta tana son ta kalleshi sai kwarjininsa a yau ba zai bar ta ta aikata hakan ba. “Taya aka yi ka san gidan nan” Yayi shiru kamar mai tunanin irin amsar da zai bata. “Baka yi kama da mai boye gaskiya ba, magana biyu bata dace da namiji irinka ba, kuma addininku ya hana karya ko ba haka ba?” "Kokarin sanin gaskiya ko gyara kuskura bai isa ya saka na dora tubalin ginin da karya ba, saboda na faranta miki ko na burge ki ba zai saka na sabawa Ubangiji na ba” Ta yi wani murmushin shedanci tana kallon wani gafe. “Ku dai musulman nan idan kuna magana kamar ace zuciyarku ma haka take, aikinku dabam addininku dabam” “Kar ki yi la'akari da aikinmu ko kalamai, ke dai ki maida hankalinki gurin addini kawai, Williams ne ya bani addreshinki” Ya amsa mata tambayarta bayan ya shimfida mata matashiya akan addininsa. Ta juyo da kyau ta fuskance shi, sai dai har lokacin ta kasa kallon wayar idonta, tana dan mamaki waye ma Williams. Aliyu ya saka hannunsa aljihu ya dauko wayarsa ta kamo hoton Williams ya nuna mata. “Idan ma ya taba fadin sunansa tohm na manta, amman dai shi Williams din be san gidana ba, be san komai a kaina ba” Wani tunanin ne ya zo mata. “Ka yi hanzarin barin gidan nan wata kila saboda kai Vito ya kawo dog's yau, kuma saboda kai ya kwana a nan” Rufe bakinta yayi daidai ta daga kan da Aliyun yayi ya kalli kofar gate din da aka bude gaba daya, Emily ta juya da sauri ta kalli gate din, a take hankalinta ya tashi ganin gogan ne a tsaye fuskarta kamar kullum babu annuri. “Ka yi hanzari bari gurin nan” Ta fada ba tare da ta juyo ba, kana ta saka kai ta nufi gate din da nufin shiga cikin gidan, tana isa a daidai gurin da Vito yake tsaye zata wuce shi, sai ya fisgota da karfi ya dawo da ita. Kamin ta yi wani yunkuri ya dauke fuskarta da mari mai zafi, har sai da dafe kunci hawaye ya cika idonta, sanin karamin aikinsa ne dukanta ya saka ta auna da gudu cikin gidan tana ihu, binta yayi a baya kamin ta haura entrance din ya janyota ta fadi kasa ya fara shurinta yana kai mata duka ta ko'ina. Kan kace me ta cika gidan da ihu tana kuka shi ko dukanta yake kamar an aiko shi. Chidimma da Fatima suka fito da gudu saboda ihun da take, sai dai babu wanda ya iya kawo mata agajiya har sai da ya duketa iya son ransa, sannan Fatima ta zo gurinta ta fada jikinta tana kuka, Chidimma kuma ta juya ta koma cikin gidan ba tare da rika Emily ko bata hakuri ba. Duk abun da ya faru Aliyu yana tsaye yana kallo hannayensa biyu rumgume a baya, sai a lokacin Fatima ta lura da shi, da sauri ta dawo daga jikin Emily tana kuka ta nufi gurin da Aliyun yake tsaye, sai dai kamin ta karasa mai gadin ya hada gate din ya rufe. Aliyu ya sauke numfashi a hankali ya juya ya shiga motarsa dake bude har lokacin, ya dan jima a motar zaune kamar mai tunanin abun yi, kamin ya ja motar ya juya ta hanyar da ya fito. Har ya isa gidansa ransa a jagule yake, damuwar da bata tasa ba na neman mamaye masa zuciya. Be san ya dade a cikin motar zaune ba har sai da Kameela (AISHA) ta fito daga falon ta kwankwasa motarsa sai ya sauke gilashin motar yana kallonta da murmushin da ya fi kama da damuwa a fuskarsa. “Mai ciki?” “Lafiya ka shigo cikin gidan ka zauna a mota, kuma ga damuwa a tare da kai” Ya san daman zata ga damuwar kam domin be iya sauya kansa a duk lokacin da wani abun na damuwa ya same shi, iyakar abun da yake shi ne boye sirrin damuwar tasa har sai ya samu mafita. Sanin halinta na zafin kishi da kuma saurin juyar da abu ya saka be fada mata daga inda yake ba, da kuma dalilin damuwar tasa, haka kuma ba zai iya mata karya ba, domin karya ba dabi'arsa ba ce. Kiran wayarsa ya yanke masa tunanin da yake na yadda zai kawar da maganar a gurin matarsa Kameela, kusan kamar an yi sara akan gaba ne, domin kiran da Turhan yayi masa yayi daidai a yanzu da yake neman amsoshin wadansu tambayoyi. Sanin ba zai iya amsa wayar a gaban matarsa ya saka shi daga gilashin motar ya rufe ruf sannan ya amsa wayar. “Assalamu Alaikum” “Wa'alaikumussalam, Aliyu ya gida” "Alhamdulillah, har yanzu babu wani labari ne?" Aliyu ya shiga shi tambayar ne a kokarinsa na gujewa tasa tambayar. "Babu, na yi yawo duk inda ake saka ran za a samu yarinyar nan ba a same ta, da har nace yau zan dawo gida, sai kuma mutumen da ka hada ni da shi yace na yi hakuri mu sake bincikawa daga yau zuwa gobe, idan ban same ta ba, sai na hakura” "Toh ya zaka yi da Ammy?” “Ba dan Ammy ba, taya zan bata lokacina ina nemanta, kawai dai ina hakuri ne saboda Ammy mahaifiyata ce ba yadda zan yi, amman su ma iyayen suna shiga hakki yaya wani lokacin Wallahi” “Wata kila Ammy ta ji ko ta gani ko tana tunanin ka munana mata a zamanku ne, shiyasa ta gagara shiryawa da kai” “Kaddara ma ace hakan ta faru, amman ai ni danta ne, be kamata ta juya min baya ba a kowane condition, taya zaka fifita wani fiye da naka? Kuma tun farko ita ta cilasta min auren yarinyar nan ni gaba daya bana sonta” “Amman ka cutar da ita?” "Sau nawa zan amsa maka tambayar nan ne Aliyu? Shi daman zaman aure sai an yi hakuri, saboda zo mu zauna zo mu tsaba ne, kuma al'adarmu da addininmu ba daya ba, kuma yarinyar nan bata da asali” “Ban fahimta ba” “Ba a san su waye iyayenta ba, kuma ko da na zauna da ita zuwa can gaba idan an yi zuri'a baka tunanin zata iya juyar da hankalin yaran zuwa addininta?” "Ita miye laifinta dan an haife ta a inda be dace ba, ba a shawara da mu kamin a zaba mana iyaye ko irin rayuwar da za mu yi kai kasan haka” “A haka din kuma addinin musulunci ya hore mu da auren mai asali, abubuwan da suka faru dai sun faru shikenan, sun wuce yanzu kuma nemanta nake na shirya tsakanina da mahaifiyata” “Allah yasa a dace” Ya fada sannan ya aje wayar ya kalli Kameela dake ta leken motar tana dora kunnenta a jikin gilashin ita ala dole sai ta ji da wa mijinta yake magana. Murmushi yayi ya bude motar ya fito. “Wannan ba halinki ba ne” "Kai ma ai ba halinka ba ne idan kana waya ka boye min, me yasa baka son na ji” “Dole ai kin san akwai sirrin da zan yi da yan'uwa ko abokai ba zai yayu kiji ba ko? Kamar yadda ke ma na san akwai abun da ba zaki fada min ba” “Ni ai bana boye maka komai?” “Uhmmm” Ya sumbance ta sannan ya kama hannunta suka shiga cikin gidan. “Baka yi breakfast ba ka fita, kuma gashi ka dawo da damuwa, yanzu kuma ka yi waya ban san da waye ba ka rufe ban ji komai ba” “Be shafe ki ba ne ai” "Abun da ya shafe ka ai ya shafe ni, ka fada min minene dan Allah dan Allah" Allah da ta hada shi da shi sai ya ji ba zai iya boye mata ba, kamar yadda ba zai iya fito mata da komai a zahiri ba. Yaja mata kujera ta zauna ya fara zuba musu abun karyawa sannan shi ma ya zauna. Cin abinci kawai yake baya jindadinsa ba dan matarsa bata iya girkin ba sai dan bacin rai da ya fi kama da damuwa dake tare da shi. “Dan Allah ka fada min” Ya kalleta yana murmushi. "Kina da son gulma, toh akan Yarinyar da Turhan yake nema ne” “An same ta ne?” “Be same ta ba har yanzu, yana cikin damuwar rashin samun nata, hakan kuma ya shafe ni” “Toh ai be kamata hakan ya shafe ka ba, damuwar wani be kamata ace ta zama damuwarka ba” Ya aje fork din hannunsa ya kama hannunta “Ki daina wannan tunanin, indan akwai tausayi a tare da mutum dole ko da ba musulmi ba ne ya shiga wani hali marar dadi zaka ji babu dadi balle kuma musulmi dan'uwanka” “To wai shi ba zai je ya nemi yarinyar da kansa ba sai ya rika dora maka lalura waya sani ma ko yarinyar kyakyawa ce?” Ta fada tana turo baki, hakan ya saka shi yin murmushi. “Idan kyakyawa ce fa?” "Idan kyakyawa ce ko ka ganta ai ba zaka fada masa ba" “Baki yarda da mijinki ba?” "Tohm zuciya ita kuma ai bata da kashi" “Wai ke da na yi ma alkawari na yi ma rantsuwa aka yi abun har a rubuce cewar ba zan kara aure ba, ina ruwanki da duk inda zan shiga" "Shedan fa yana nan kusa zai iya sakawa ka karya alkawarin nan, kuma yadda kake da kyaun nan kake wanka idan zaka fita, ai dole hankalina ya tashi” "Wallahi Kameela ba zan miki kishiya ba, ba zaki taba sharing dina da wata da sunan kara aure ko akasin haka ba, shikenan?“ Ya sumbance ta sai ta yi murmushi ta kwanto jikinsa. [4/20, 10:01 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ Page 1️⃣3️⃣ Masu tambaya daga farko zaku iya duba channel dina https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 Ko kuma wattpad @KhadeejaCandy Masu tambayar free ne ko na kudi, toh Free ne, yan bati sun hada kai da Iya sun min kiranye ya kamani tare da hadin kan Ummu Faisak yayar Wasim 😜 Asha karatu Lafiya 🥰 ***. ***. *** VITO POV. Falon ya shiga ya zauna, can kasan zuciyarsa ya ji babu dadi na dukan da yayi ma Emily, ya saba samun kansa a irin wannan yanayin a duk lokacin da ya duke ta, sai dai kuma dukanta a gaban ko ma waye abu ne da ba zai iya hana kansa ba, ba zai iya rike hannunsa daga taba jikinta da sunan duka a duk lokacin da laifi ya fito ta tsagenta ba. Kamar yadda ba zai iya fin karfin zuciyarsa a duk lokacin da wani yayi mata kallon banza ko na soyayya ba, yana sonta ya sani, yana tsananin kishinta irin kishin da shi kansa yana tsoron kar yayi masa illa wata rana. “Ban san ko kana bukatar ruwa ba” Chidimma ta miko masa cup da gorar ruwa a tray cike da ladabi da kuma gudun bata masa rai. Ya kalleta kawai ya kalli gurin da zata aje ruwan, sai ta risina ta aje a kasa ta daga gorar ruwan ta bude ta zuba masa a cups sannan ta dora ruwan a kan side table. Ruwan ya fi da kallo yana mamakin yadda ya kasa yi ma Aliyu komai a dazun har ya tafi, me yasa ma ya daki Emily bayan kuma Aliyun ya kamata ace ta hukunta domin shi ya nemi addireshinta ya biyo sawunta har gida? Ya kawo karnukansa da nufin idan Aliyu ya shigo gidan ya rufe gate din ya sakar masa su, amman duk be samu nasarar yin hakan ba. A zahirin gaskiya Vito wani kalar mutum ne sa kallonsa kawai zaka yi ka firgita, saboda rashin annurin dake fuskarsa da kuma shigar da yake ta tufafi, amman sam be ga alamar hakan a tattare da Aliyu ba, toh miyasa ma ya biyo ta har gida? Me yake nema a gurinta? Ya kai hannu ya dauki ruwan da Chidimma ta zuba masa ya kai baki yana sha sai wani sanyi ya sauka a zuciyarsa wanda ya kara taimaka masa gurin hararo dalilin Aliyu na bibiyar macen da ba ma addininsu daya ba. 'Tana da kyaun da kowane kalar namiji zai iya cewa yana sonta ko son mu' alama da ita` Zuciyarsa ta bashi amsar da yake bukata, mikewa yayi tsaye ya nufi kitchen din da Chidimma take, tana ganinsa ta juyo da sauri. “Kana bukatar wani abu ne ranka ya dade?” “Me kika shiryawa London na karyawa?” “Gashi nan” Ta dauko big basket ta risina kasa ta aje masa, zai kai hannu ya dauka sai ta riga shi. “Bari na kai maka mota ranka ya dade” Be ce mata komai ba, ya juya ta bi bayansa har gurin motarsa sai da ta saka masa mota sannan ya yi mata key ya fice daga gidan. Sai a lokacin Chidimma ta nufo Emily dake kwance a gurin rumgume da Fatima ta tsaya kanta. “Bana son na batawa daya daga cikinku rai ne, bana son daukar bangaren Sir Vito na bar naki, abu kadan zai iya sakawa ya koreni ko ya hukanta ni, shiyasa bana iya tarewa idan yana dukanki, ki yi hakuri” Uffan Emily bata ce mata ba, ita ma kuma bata jira cewarta ba ta juya ta koma ciki ta cigaba da aikin da take. Yana faka motarsa harabar asibitin wayarsa ta yi ringing, ya amsa kiran har lokacin ransa babu dadi saboda dukan da yayi ma Emily, mahaifiyarsa ce take sanar masa jirginsu zai taso yanzu daga Murtala Muhammed International Airport (MMIA) dake Lagos zuwa Port Harcourt International Airport. Daman ta sanar masa da zuwanta tun kwanan baya. “Safe journey" Ya fada as Answer sannan ya cire wayar daga kunnensa ya bude dayan side din ya dauko basket din da Chidimma ta saka masa ya nufi cikin Asibitin. Ko da ya shiga ya samu Nurse nata lallaba London ya fito daga kasan gadon majiyanta da ya boya amman yaki sai ihu yake mata. “Heyyy my boy” Vito ya fada cikin muryarsa ta manyan mazaje, London na jin muryarsa sai ya leko suna yi arba ya fito da sauri yaje gurinsa ya rumgume shi. Murmushi ko nuna farinciki ba al'adarsa bace balle kuma a yau da yake cikin damuwa, kan London kawai ya iya shafawa ya daga shi zuwa kan gadon Asibitin suka zauna. “Tun dazun yake labe a gurin baya yarda da kowa, idan ka matsa kusa da shi sai yayi maka ihu” Ta fada tana kallon London din da murmushi a fuskarta, Vito be ce mata komai ba, ya kai hannu ya dauko abinci ya bude ya fara ba shi da kansa, tana ganin haka sai ta fita ta bar musu dakin. Sai da London ya ci abinci ya koshi sannan Vito ya fara masa maganar Emily. “Meyasa ka yi ma Momy Ihu jiya?” “Ina fushi da ita” “Na fada maka Momy tana sonka ba zata aikata abun da zai bata maka rai ba, duk laifinta akan kuskure ne, ka yafe mata ka ji?” Ya daga kai, sai ya shafa kan yaron... “Ina son mahaifiyarka, duk kuwa da kasancewar ta haife ku, na kula da ku na nuna mata soyayya da gata, amman ta kasa ganin hakan” Yayi shiru yana kallon London. “Wata kila kuma ta gani, kawai dai bata shirya karbata ba ne” Ya ja numfashin da ya gagara saukewa. “Uhmmm zan mata uzuri har zuwa lokacin da ta dibarwa kanta, sai dai ina da tabbacin abu daya, idan ban samu mahaifiyarku ba, wani ba zai same ta ba, idan ban mallake ta wani ba zai ci galaba a kaina ba” London yayi murmushi domin be fahimci yaren ba. A hankali idonsa ya kai a kan card da Emily ta jefar a dakin. Mikewa yayi tsaye ya nufi card din ya dauka Dr A-B ne rubuce a jikin katin da kuma address din gurin aikinsa sai Email da number wayarsa. A take ya fara jin zuciyarsa ya tafasa, jimke katin yayi ya juyo ya kalli London. “Chi chi zata zo ta kula da Kai bari na je na dawo ka ji?” London ya daga masa kai alamar amsuwa, be bar dakin ba sai da ya kira Chidimma a waya ya fada mata ta bar duk abun da take ta zo yanzu asibitin gurin London, bayan ya shafa kansa ya sumbance ya fice. Kamin ya isa gida ya kira daya daga cikin yaransa ya fada masa ya tafi gidan ya dauke dog's da aka kai, yanayin yadda ya faka motar a harabar ya fito kadai ya isa ya sanar da bacin ransa balle kuma yadda ya turo kofar falon ya shigo, sai da Fatima dake zaune tana zane ta firgita. Yana kallonta ya dauke kai ya nufi upstairs. “Dukanta zaka sake yi?” Ya juyo ya kalli makiyiyarsa Fatima, domin ya fi tsanar ta fiye da kowa a gidan, sai dai duk da haka be taba unkurin kai hannu ya doketa ba, no matter what ta yi masa sai dai ya mata fada ko ya wani hukuncin na dabam amman ban da duka. “Momi zata yi kudi, tana aiki zata samu kudi mai yawa zata gina gida zata maida mu can mu rayu a can ba tare da kai ba, ba zaka sake ganinmu ba balle ka dake ta, i hate you” Ta fada cike da fitsara da tsageranci irin yadda ta saba yi masa, jimmm yayi yana kallonta kamar mai nazari ba tare da ya ce mata komai ba, kamin ya juya ya haura saura zuwa dakin da Emily take... EMILY POV. “Meyasa kake son saka kanka a hatsari? Baka san wacece ni ba, kuma baka san da wa nake tare ba, kuma ya kamata kasan ni ba musulma bace, babu abun da Zai hada ni da kai, domin mutanen da na tsana irin musulmai, karka sake bibiyata karka sake shiga rayuwata, idan ba haka ba zaka jefa kanka a bala'i” Ya mayar mata da amsa a take. “I'm sorry for what happened earlier, bana nufin jefa ki a matsala, akwai wani tsauni ne da na hau ba kuma zan iya sauka ba har sai da gamsantsun amsasoshinki, shin zan iya sanin wani abu akanki? Wata kila hakan zai taimaka ya gina wata katangar da zata katange ni daga fadawa mai nemanki gaskiyar a inda kike” “Ni uwa ce da bata da aure mai zama a karkashin inuwar wani mai karfin kudi da iko, uwa ce da ta haifi yaranta ta

Chapter 10 of 63