Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kuma rashin zama a guri daya, ya saka dukanmu muka maida hankalinmu gurin wasu abubuwan, amman ni har gobe idan ina cikin wata babbar matsala Aliyu kai ne mutum na farko da zan kira na shaidawa, domin bana kallonka a matsayin aboki kawai ko abokin karatu ko abokin gari daya, ina kallonka ne a matsayin dan'uwa na jini, domin sanadinka na zama abun da na zama Aliyu sanadinka na samu komai da na samu a yanzu, idan kana cikin wata damuwa dan Allah ka fada min" Aliyu ya sauki ajiyar zuciya. "Nura ka san Turhan ai?" "Eh na san Turhan" "Amman kamin nan daman Kameela tana da kishi kai ka sani kuma...." Ya fada masa abubuwan da suka faru tsakaninsa da Kameela da kuma Emily ciki har da alkawarin da yayi ma Kameela cewar ba zai mata kishiya ba. "Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, a lallai Kameela bata da hankali, taya zaki yi kokarin kashe mijin da be bijiro miki da maganar aure ba ma? Gaskiya rayuwarka tana cikin hadari, kana iya yanzu?" "Ina hotel na bar gidan" "Ka yi tunani mai kyau, amman ka yi kuskure Aliyu, tun farko be kamata ka mata alkawarin cewar ba zaka mata kishiya ba, be kamata ka haramtawa kanka abun da Allah ya hallata maka ba, ita mace mai kishi daga lokacin da aka fahimci tana da kishi taka mata burki ake, tun tana haukan tana kishin har ta gaji ta hakura idan ta fahimci ba zaka fasa son wata ko auren wata saboda kishinta ba, bayan kuma kishi ka yi hakuri da abun da zan fada da alama Kameela bata da zuciya mai kyau" "Na mata alkawarin ne saboda bana da ra'ayin kara auren, kuma da farko na yi tunanin aikata hakan zai saka hankalinta ya kwanta mu samu zaman lafiya ni da ita, shi aure Allah yace idan baka iyawa adalci karka yi, kuma ba lallai ne na iya adalci a tsakanin mata biyu ba, saboda rayuwa ni ba mutum ne mai son yin nan na yi can ba, ba kuma zan so na tashi gaban Allah da hakkin kowa ba" "Na fahimce ka duk namiji mai son zaman lafiya a gidan sa dole zai bi hanyoyin da yake ganin sun dace domin ya samu salama da matarsa, shawarar da zan baka a yanzu karka sake cin abincinta" "Daman na yanke wannan shawarar, kwana da ita a gida daya ma ba zan iya ba a yanzu sai ta samu lafiya" "Bayan samun lafiyarta ma, Aliyu babban abun da zaka yi shi ne kara aure, ta fahimci ba a ketare iyakokin Allah, kuma hakan zai rage mata kishi wata kila har ta zabi rabuwa da kai, dan na fahimci kana sonta sosai shiyasa ba zan iya baka shawarar cewar ka saketa ba, amman Wallahi zama da ita hadari ne sosai ga rayuwarka" "Zancen aure ko rabuwa da ita be taso ba yanzu Nura, shiyasa ban fadawa Ummi ba, dan na san ba zata bari na zauna da ita ba idan ta ji, kuma komai dan hankali ne, a sannu ake bi ayu bincike, shin yanzu zaka samo min likitan da zai dubata ko kuma na kashe wayata" "Zan samo maka mana dole na, akwai wane babban likitan kwakwalwa sunansa Dr Adam Bello, sai dai yana da wahalar gani gaskiya kamin ka sami ya duba ka ma sai kana da Connection, zan yi kokari na nema maka appointment da shi idan zaka ganshi sai ku zo Abuja" "Shi kenan na gode sai na jika" "Okay" Yana sauke wayar daga kunnensa kiran Emily ya shigo wayarsa, ya dade yana kallon kiran baya cikin yanayin da yake son magana da ita a yanzu, sai dai kuma ba zai iya ganin kiranta ya kasa dagawa ba, domin be san dalilin kiran ba, sai da ta kusa yankewa sannan ya daga ya kara a kunne, daga ita har shi shiru suka yi babu wanda yace uffan. "Ba zaka yi magana ba?" "Ba ke kika kira ni ba" "Da ka dauka amman kai ya kamata ka fara cewa Hello" Yayi shiru be sake magana ba. A shagwabe Emily ta fara magana. "Daman dai kawai na ji babu dadi abun da na yi maka dazun ne" "Kin san baki kyauta ba miyasa kika kira ni yanzu?" Tana jin hakan ta san ransa a bace yake wata kila har yanzu be sauka daga fushin fadan da ta yi masa ba. Sai kawai ta kashe wayar, tana jin haushi meyasa ma to ta kirashi yanzu. After ta yanke kiran sai kuma ya ji babu dadi na furucin da yayi mata, ko ba komai ta fahimci beta kyauta masa ba ta kira be kamata yayi mata haka ba, a yanzu zata kara jin babu dadin ne. Without second thought ya kira layinta ringing daya ta daga. Ita dai data daga sai ta ari irin halinsa ta yi shiru ba tare da tace komai ba. "Dazun da kika kira cewa kika yi ni ya kamata na farawa cewa Hello" "Na san yanzu ka kira ka yi min bakar magana ne ko fada" "Me kika sani a halina da zaki yanke hukunci?" Ta yi shiru, jin shirun ya saka shi katse kiran, a take ta biyo shi da wani kiran domin bata san dalilinsa na kiranta ba gashi ta yanke masa hukunci kuma ta kara bata masa rai. Da ya amsa kiran ita da shi sai suka yi shiru babu wanda yace uffan har na tsawon lokaci. "Hello..." Suka furta a tare, ita a kokarinta na yanke shirun shi ma kuma a kokarinsa na yin magana kar tace ta kira ya amsa be ce komai ba. Sai kuma shirun ya sake biyo baya. "Zaki ce wani abu ne? Ko wani abu kike bukata?" "Idan baka da abun da zaka ce, ba sai ka sake kirana ba, mu ba yara ba ne be kamata muna haka ba" "Remember I'm your boss, ni da ke waya kira wani yanzu?" Ashe fa ita ta kira shi, bata san lokacin da dariya ta kwace mata ba, shiru yayi yana sauraren dariyarta a kunnesa tun da yake da ita be taba jin dariyarta ba sai yau, and ya san dariyar zata mata kyau domin farinciki ya dace da ita a yanzu dan haka ya fara imaging yadda take dariyar, kamin ita da shi su sake hada baki gurin cewa. "Okay Bye" Ya mata sallamar ne saboda ya fahimci bayan dariyar bata da wani abun fada, ita kuma ta masa sallamar ne gudun kar ta bata masa rai tun da ba wani abun zai fada ba. Bayan ta katse kira ya bi number ta da kallo sai kuma yayi murmushi. Be dauke idonsa ba wani kiran ya sake shigowa wayarsa da bakuwar number. Wannan karon ya amsa da sallama domin be san waye ba. "Sallamu Alaikum" "Wa'alaikumussalam barka da dare" An fada cikin wata murya mai sanyi da be fahimci waye ba. "Barka dai" "Na san baka gane ni ba, Tasmia ce kawar Kameela, daman na zo gidan ne ban tarar da ita ba shi ne nace bari na kiraka ko kuna tare dan na kira wayarta ban samu ba" "No ban koma gida ba tukunan" Yana bata amsar ya katse kiran yana mamakin da ya kamata ace tambaya yayi mata cewar ina ta samu numbersa. [6/1, 9:15 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/HQSJMqxBuI985hZVzy0S03 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ Page 3️⃣2️⃣ Ta sauke wayar tana murmushi wani irin jindadi da farinciki suka lullube ta na jin muryar Aliyu, daman tana ta tunanin ta ina zata bullo ta fara gaisawa da shi babu dama, domin a yanayin yadda ta fahimce shi ba irin mazan da mata suke saurin burgewa ba ne, kuma ba irin mazan da ake zuwa ma da bukata kai tsaye ne ba, kusan zuwan Kameela gurinta ya taimaka mata sosai gurin samun damar magana da Aliyu tun a bayan da ta sace Numbersa a wayar Emily. Ta dade tana murmushi kamin murmushin dake fuskarta ya gushe kamar mai tunanin wani abu, ta goge number a gurin kira sannan ta fito bandaki da aje wayar a karamin gadonta ta fito falo ta samu Kameela da ta ci kuka har idonta ya canja kala. "Toh ke yanzu miye amfanin kukan da kike yi?" "Ba zaki gane ba, baki san minene soba Tasmia ba" Tasmia ta zauna kusa da ita ta dafa ta With Straight face. "Na san miye so, so yana iya haukata mutum domin yana saka ka ka aikata abun da ba halinka ko kuma baka yi niya ba, so yana maida kai kamar wani wawa ko kuma kakkarfa, shi so wani abu ne da ba a iya cusa shi sau daya yake shiga zuciyar mutum, kuma ya hanaka zaman lafiya har sai ka biya bukatarsa" Ta lumshe ido ta bude. "Amman ke irin son da kike yi ma Aliyu yayi tawa Kameela shi ya kamata ace yana miki irin wannan son, ke fa mace ce, gashi yanzu har yana kokarin wulakantaki akan wata banza da addininmu ma ba daya ba, ba tare da kin masa komai ba" "Ban masa komai ba sai kawai dan na zagi Emily, yanzu haka baya gidan yayi tafiyarsa, kuma yace na bar masa gidansa na koma gida wai zai samu likitan da zai duba ni, mahaukaciya ma ya dauke ni kenan, shiyasa na rasa me ke min dadi naji bana son zaman gidan gashi ba ni da kowa a garin nan" Tasmia ta bude baki. "Ahhh lallai kuwa mahaukaciya ya dauke ki, amman kin yi hakuri nuna masa kishi da kike ai soyayya ce, shi duk be gani ba sai kora da hali? Da ni ce ke ba zan sake kwana a gidansa ba sai na koya masa darasi" Kameela ta kalleta. "Ni ba inda zan je ina son mijina Wallahi, idan na tafi ai na bawa Emily din damar ta rika magana da shi tana samun yadda take so gashi ma gurin aikinsu daya" Tasmia ta girma mata kai. "Kameela ke fa yar manyan mutane ce, kina da gata ina da yan'uwa da kudi, be kamata Aliyu ya wulakanta kuma ki zauna ba, ai tun da har ta kai ya furta ki koma gida idan baki koma ba ai zai cigaba da wulakanta ki ne, ai kawai ki yanki ticket gobe ki kama hanyar gidanku sai ya nemi ki, ai ba ayi ma namiji haka, tun da har ya iya nuna wata ta fiki kara ya san darajarki" "Akwai abun da baki sani ba Tasmia, iyayenmu ba san auren za su iya raba auren idan suka ji cewar Aliyu ya kore ni saboda na kira wata a gurin aikinsu na zageta saboda tana budurwarsa" Tasmia ta daka mata tsawa. "Ke dalla can Aliyu autan maza ne da kike ta wannan rawan jiki da tsoron rasa shi? Haba Kameela sai kace maza sun kare aduniyar nan ne" "Tasmia Aliyu na dabam ne fa, cikin maza dari irinsa daya ake samu, ni na san yana hakuri da ni, yana min komai kuma be taba wulakanta ni irin haka ba sai da bakar Emilyn nan ta zo" Tasmia ta shiru tana kara jin kalamanta cewar Aliyu na dabam. "Toh yanzu ko number shi zaki ba ni na kira na ba shi hakuri? Domin na lura baki shirya tafiya gida ba, kin shirya karbar wulakancinsa ne, daman maza ai idan suna son ka babu abun da ba za su maka ba, idan kuma suka ki ka zaka fara ganin wulakanci kala kala" "Tasmia ko hauka nake dai ai ba zan dauki number wayar mijina da kaina na ba ki ba, tafiya gida dai zan tafi ko dan ya gane ni ba kanwar lasa ba ce" Tasmia ta watsa mata harara. "Kin dauka kowa irin Emily ne? Ko mazan duniya sun kare an fada miki ni zan iya auren mijin da zai nuna ya fi son matar waje da matarsa?" Kameela ta watsa mata wani kallo tana jin zafin kalaminta. "Mijina ba manemin mata ba ne, balle ki ce ya fi son matar waje akan ta gida" "Idan ba haka ba akan me zai fifita Emily take da suna ko Imily akan ki? Ke mai dai ki yi tunani mana" Kameela ta nuna ta da yatsa. "Ke ki iya bakinki, ban zan dan bana son mijina ba, sai dan na rasa gurin da zanje a cikin daren nan, tun da na zo na fada miki damuwata sai wani zuga ni kike kina zagin mijina, an fada miki rabuwa muka yi ne? Ni fa na zo nan ne saboda na samu mafitar yadda zan shirya da mijina, amman sai wani zakewa kike kina ta zaginsa" Tasmia ta yi murmushi. "Matsala ta dake ke zahila ce, idan yabon Aliyu kike son ayi ai nan zaki zo ba, dan ni na san darajar kaina ba zan baki shawarar zama da mutum da har yanzu baki gama sanin ba, Aliyu yana neman hanyar rabuwa da ke ne kawai shiyasa yake wulakantaki domin ba Emily ce kadai budurwarsa ba" Tasmia ta karasa fuskarta babu alamar wasa. "Me kike nufi?" Har Tasmia ta daga wayar sai kuma ta fasa abun da ta yi niya ta dauke kai. "Ki daina yarda da namiji dai kawai" "Ai ke baki yi auren ba balle ki fada min kabli da bad'adin namiji" Fadar bata yi aure Tasmia ta ji abun kamar gorin auren take mata a take zuciyarta ta haye sama san lokacin da ta mayar mata da zazzafar amsa ba. "Kara ni ban yi auren ba, ke da kika yi auren ai ta wuje ta fiki daraja a gurin mijinki, mijin ma da Emily kadai yake nema ba ni kaina da kansa ya saka min Number wayarsa, kuma idan kin koma ki tambaye shi sau nawa ya zo gidan nan gurina" "Karya kike yi Wallahi ai ko Aliyu zai kula mata ba irinki zai kula ba, domin ba ki fini da komai ba, sai idan ke kika nemi shiga gurinsa saboda an yi kwantai babu miji kuma ga bakin jini, ga kuma rashin tarbiya, idan ba rashin tarbiya ba yaushe mace cikakkiya rikakkiya kamar ke zata zo ta kama gidan kanta set-contain da sunan bautar kasa? Duk garin Kaduna be ishe ki zama ba sai kin tsallako kin zo garin da mijina yake saboda shi ne abun farautarki ko?" Ta dago wayar ta kama Number Aliyu ta kira shi na farko be daga ba sai a na biyu. "Assalamu Alaikum" Ya fada Tasmia bata ce komai ba ta katse kiran daman burinta Kameela ta ji muryarsa domin ta gasgata karyarta. "Komai zaki fada ki fada ni dai na riga na gama da ke Wallahi" Kameela ta rufe ta duka Tasmia ta maida himma suka fara dukan dukan gashi babu mai raba su, ta ko'ina Kameela dukan Tasmia take ba kuma dan ta fi Tasmia karfi ko jiki ba halima Tasmia ta fita cika amman ta yi mata kwance galala tana dukanta, da ta gama da ita ta koma gurin kayan falon ta fara watse su. "Wallahi Wallahi akan Mijina sai na kashe ki Tasmia, daga ke har Emily sai na yi maganinku" Ta Dauki Jakarta ta fice daga gidan tana huci. Sai da ta yi tafiya mai nisa sannan ta samu abun hawa ta hau ta koma gida, tana shiga ta fadi kan kujerarta ta fashe da kuka bakinciki ya mata yawa, yanzu mayakan sun zame mata biyu kuma ba kowa ya janyo ba sai Aliyu, ta san wani abun da Tasmia ta fada gaskiya ne cewar yana neman rabuwa da ita ne shiyasa yanzu yake wulakanta ta, a yanzu ta gano dalilinsa na yi mata alkawarin ba zai kara aure ba ashe saboda yana son ya tara mata awaje ne, gashi daga tafiyarta haihuwa komai ya canja kamar daman dagawarta kawai yake jira, a daren ta siye flight ticket daga PH to Lagos daga Lagos ta hau jirgin Kaduna kwana ta yi tana kuka tana bakincikin da nadamar dama ace ta bar shi ya ci abincin dazun da yanzu duk bata ji wannan ba. EMILY POV. Kanta a sama tana kallon taurarin da suka yi ma samaniya ido, har lokacin hakoranta ba su rufu daga dariyar da take na wayar da ta yi da Aliyu ba, bata sauke kanta kasa ba sai da mai gadin gidanta ya bude gate motar Vito ta kunno kai a harabar gidan, tana kallonsa har yayi farkin sannan ta sauka ta karasa inda motarsa take, ya bude motar ya fito yana mata wani irin kauna da ke kara tabbatarwar kaunarta a zuciyarsa musamman data nuna masa kulawa da tsoronta na gudun kar wani abu ya same shi. "How are you?" "I'm good, ba su maka komai ba" "Ba su yi ba, kuma ba su samu komai ba" "Taya hakan ta faru" "Saboda cikin kasa nake aje abun da yake dole a gidan, kuma ina da yaran da suke hango abun da zai faru idan suka ga bakuwar fuska sai su shirya komai" Ta yi murmushi. "Na jidadi da wani abu be sameka ba" "Daman babu abun da zai same ni ai, sai dai ya samu wanda ya shirya hakan" Ya wuce ya nufi Gardenta gurin da ya binne bindigarsa sai ta bi bayansa da tambaya. "Ka gano ko waye ne" "Ban gano ba amman zan gano, kuma idan na gane kowaye sai ya dandani kudarsa, sai ya raina kansa" Har yayi ginar ya ciro bindigarsa bata sake cewa komai ba, mikewa yayi tsaye ya matsa kusa da ita. "Kin damu da ni Emily ko ba haka ba?" Ta yi shiru bata amsa masa ba. "Miya haka ki aurena? Mi ya rike ki daga nuna min soyayya Emily? Ba ki jin cewar lokaci yayi da ya kamata ace mun kasance karkashin inuwa daya?" Ta sauke idonta kasa tana shafa wuyanta. "Kina da wani buri ne da kike son cin ma kamin ki amince min ne?" "Vito bana son sana'arka" "Bayan shi fa" "Fatima-... La lall" Bata karasa ba ya katsi hanzarinta yayi gaba. "Oh Okay" Ta bi bayansa suka fito daga gurin ya nufi motarsa ya bude ya shiga har yayi mata key sai kuma ya fito ya dawo daidai inda take tsaye ya shafa fuskarta sannan ya koma motar, tana tsaye tana kallonsa har ya fice, abun da ba su sani ba duk abun da suke Chidimma na lekansu. Emily ta shigo falonta kenan wayar hannunta ta yi ringing data duba wayar sai ta ci karo da sunan Tasmia, babu bata lokaci ta amsa. "Hello" Tasmia ta fashe mata da kuka. "Emily dan Allah ki zo ina cikin damuwa ina cikin bakinciki, ki zo yanzu dan Allah ina da bukatar taimakonki" "Okay gani nan zuwa" Ta nufi staircase da sauri ta dauko key din motarta ta fito ta sauri ta nufi gurin da motar take, daga unguwar da take zuwa unguwar da Tasmia take tafiya ce ta mintuna Arbanin amman cikin minti ashirin da biyar ta isa gidan Tasmia hankali a tashe saboda ta ji muryarta tana kuka kuma gashi ta fada mata da bakinta cewar tana cikin tashin hankali. Tana faka motar ta bude ta fita ya fara kwankwasa kofar Tasmia kamin ta tura ta shiga, yanayin yadda ta ga falon a hargice ta san ba lafiya ba, ta zauna kusa da Tasmia dake rusar kuka tana tambayarta abun da ya faru. "Ni ma ban san miya faru ba, matar nan tana shigowa ta rufe ni da duka wai mijinta yana zuwa gidan nan nemanki, gaba daya Kameela bata da hankali, akan Aliyu zata iya komai Wallahi kara ma ki rabu da mijinta, ni din ta yi min haka ina ga ke kuma" "Ba soyayya nake da mijinta ba, kuma waya fada mata yana zuwa nan nemana? Yaushe rabon da na zo gidan nan ma" "Waya sani wata kila bincike tayi har ta gane ko kuma shi ya fada mata ai maza ba su da tabbas, zuwan ba na yanzu take magana ba tun a wacan karon ne, shi ma kuma karya aka shirya mata domin bayan tafiyarki Aliyu be taba zuwa gidan nan nemanki ba" "Toh yanzu me zaki yi? Reporting dinta za ki yi ma police ko kuma yaya? Ko a fadawa Aliyu" "Aa bana son kowa ya sani, so nake ki raka ni asibiti" "Okay tashi mu tafi" Emily ta fada tana kallon fuskarta data dan kumbura kadan. Tasmia ta mike tsaye "Ban san inda wayata take ba, ara min wayarki na kira na sanar da iyayena halin da nake ciki" Ba tare da tunanin komai ba Emily ta mika mata wayar sai ta tashi ta shiga daki da sunan kiran sai dai a badini ba kiran zata yi ba, amfani ta yi da wayarta dake aje a dakin ta saka number Kameela ta aika mata sako sannan ta goge ta duba inbox din Emily ko zata ga sakon Aliyu bata gani ba, ta shiga longcalls a nan ta ci karo da kiransa da kuma wanda Emily ta yi masa ta dago ta kalle kofar cikin wani yanayi sannan ta sake maida idonta gurin wayar ta saka wata fake number ta kira ta yi canceling. "Kin ga na kira wayar Yayana saboda na sanar masa saboda shi namiji ne, kar na fada musu hankalinsu ya tashi su yi zaton ko wani babban abu ne, bari zuwa gobe zan sake kiransa" Ta fada bayan ta mikawa Emily wayarta. "Okay mu tafi asibitin" "Wace asibiti zamu je ni kin san ba wanin garin nan na yi ba" "Muje ni na san asibitin, sun gwarai sosai a can ake duba London ni kaina can nake zuwa idan ba ni da lafiya" "Okay" Ta shiga ta dauko jakarta da wayarta dake boye a jakar ta fito suka shiga motar Emily, da suka isa likitan dake duty dare ya dubata sai ya rubuta mata maganin ganin kamar ciwon be kai a bata gado ba, amman ta ki yarda wai ita ko'ina ciwo take ji ita dai tafi son a bata gadon, ganin tana bukata ya saka likitan bata gado, a dole Emily ta tsaya tare da ita asibitin ganin bata da kowa kuma be kamata ta tafi ta barta ba, domin ita ma ta tsaya mata lokacin da take cikin damuwar rasa danta. ALIYU POV. "Daman abun da kake takama da shi kenan? Shiyasa kace ba zaka min kishiya ba? Sai ta waje? Abun be tsaya iya kan Emily ba? Har da Tasmia kawata Aliyu? Emily ta turo sako ta fada min komai ta fada min ka fi sonta akaina, shiyasa ka zabi korata, ta fada yadda kake ziryar gidan Tasmia gurin nemanta, ka nuna kafira ta yi matarka muhimmanci Aliyu, toh na bar maka gidan sai ka dauko ta ka kawo daman ai ta fada min lokacin da bana cikin gidan har cikin gidan ta kwana ka yi ma danta jana'aiza ka kyauta" Shi ne sakon da ya fara cin karo da shi kenan a wayewar safiyar yau, ya dafe goshinsa yana kallon Number Emily da Kameela ta yi screenshot ta turo masa ta whatsapp tare da sakon data aiko mata, da yayi coping number ya duba sai ya ga number Emily din ce. Amman me zai saka Emily ta yi haka? Be samu amsar tambayarsa sai ga kiran Tasmia ya shigo wayarsa wannan karon be amsa ba, har wayar ta gaji da ringing be kula kiran ba. Sako ne ya biyo bayaj kiran Tasmia tana sanar da shi Kameela ta yi mata duka jiya da dare a asibiti ta kwana. "Ahhh Ahhh" Aliyu ya fada yana zaunawa bakin gadon dake dakin na Hotel. Da kansa ya kirata sai ta daga tana kuka. "Me ya faru?" "Baka ga sakona ba" "Na gani, garin ya ta miki duka?" "Ban san waya fada mata kana zuwa neman Emily a gidana ba, ban san hawa ba ban san sauka ba, sai ganinta na yi a falona babu bayanin komai ta hauni da duka" "Amman jiya ke kika kira ni kika ce kin je gidan nemanta bata nan, ina kika samu number na" "Mai gadinka ne ya bani da na kira ban same ta ba, sai yace ba ri ya ba ni number ka na kira kace baka dawo gida ba, sai na dawo gidana ina zuwa babu jimawa sai gata ta shigo kawai ta hauni da duka har tana fadar sai

Chapter 26 of 63