aka kawo ki asibitin nan kike fushi da ni, ko dan rantsuwa da alkawarin da na daukar miki ai ya kamata ace kin yarda da ni”
“Cikin alkawarin da rantsuwar ai na ga chat dinku”
“Ke yanzu ko a mafarki aka ce miki ina son Emily zaki yarda”
Ta dube shi kamar zata yi kuka.
“Har ka rike sunanta ma”
“Turhan fa ya auri yarinyar nan kuma har sun haihu da ita, Turhan kuma abokina ne mahaifiyarsa kamar uwa take a gareni, taya zan iya soyayya da ita ma balle har nace zan aureta? Kuma addininmu ba daya ba, ba abun da kike tunani ba ne”
“Yanzu dai gashi nan ai ka janyo min nakuda Edd na be cika ba amman gashi nan nakuda ta same ni, kuma gashi sun ce idan ban haihu da kaina ba za su min CS”
Ya rumgumeta.
“Zaki haihu da kanki lafiya In Shaa Allahu”
“Me yasa ba zaka fadawa Turhan gaskiya ba, bayan kasan nemanta yake idan har baka da wata manufa akanta? Ka san yadda Turhan yake son haihuwa amman baka fada masa yana da ya ba, idan baka da wata mummunar manufa akansa miyasa ka yi haka?”
Tana maganar tana cige baki tana numfashi da karfi.
“Idan Allah yasa kin haihu lafiya wan warware miki komai”
“Allah dai yasa na haihu lafiya, Allah yasa na tashi Wallahi babu wanda zata aurar min miji Wallahi Allah kuwa na rantse”
Shi dai kallonta kawai yake be yi zaton tsananin kishinta ya kai haka ba sai yau.
“Ummi bata iso ba har yanzu?”
“Ta iso kin san ai ta fi kusa, ta sauka gida ne sai ta yi wanka zata zo, su Hajiya ma suna hanya”
“Ka min addu'a Aliyu”
“Ina ta yi”
Ya shafa kanta yana ta karanta mata addu'o'i.
Misalin karfe goma sha daya na safe iyayen Kameela suka iso asibitin, a lokacin nakudar ta taso mata gadangadan ya fito waje sai addu'a yake yana kai da kawo. Da waya ya kwatanta musu gurin da yake har suka iso, kana kallon mahaifiyarta zaka fahimci tana cikin tashin hankali haka ma yayarta. Cikin ladani ya gaishe su kamar yadda ya saba mahaifiyar ta amsa rai a hade domin Kameela ta labarta mata komai ta waya.
“Hajiya ai da kun wuce can gidan kun dan huta tun da ni ina nan”
“Aa kara dai zamana kusa da yata, tsayuwarka a nan wani amfani yayi mata, ba kai ne sanadin duk wannan ba”
A take Anty Shafa wacce ta kasance yayar Kameela ta karbe zancen Hajiya ta dora da nata.
“Gaskiya Aliyu baka kyauta ba, kasan matarka tana da ciki be kamata kana yin wasu abubuwan ba”
Aliyu ya kalli Anty Shafa da duba na tsanaki.
“Me tace na yi.?”
Ta yi shiru bata ce komai ba, sai dauke kai da tayi. Ya ciro wayarsa yana amsa kiran mahaifiyarsa.
“Okay Ummi bari na zo na dauke ki”
Ya sauke wayar, ya kalli sarakuwarsa.
“Zan je na dauko Ummi daga gida yanzu”
“Toh”
Ta amsa masa a takaice cikin bacin rai. Aliyu ya saka kai ya fice cikin rashin jindadi, daman ya san za a rina domin Kameela bata da sirri ko kadan mu'amalar auratayya ma sai ta fadawa kawaye ta, be yi mamakin dan ta fadawa iyayenta sanadin nakudarta ba, wannan halin nata na rashin sirri yana bata masa rai sosai.
Ko da ya isa ya samu Ummi a harabar tana jiran isowarsa.
“Ummi madadin ki zauna a ciki kika fito waje”
“Idan ka iso ai zaka iya dadewa shiyasa na tsaya jiranka a nan, mu tafi”
Kamin ta shiga motar ya fito da sauri ya zagayo ya rumgume ta.
“I miss you Ummiiiiii”
“Kai wai baka san ka girma ba, baka jin kunyata”
“You're my best friend my first love”
Ya je zai sumbance ya ta tureshi ta bude motar ta shiga, dariya yayi ya koma motar yaja suka fice daga gidan, suna tafi suna hira har suka isa asibitin ya zagaya ya bude mata ta fito ya suka jera zuwa gurin da ya bar su Hajiya dazun.
Ummi na hango Hajiya da Anty Shafa ta kalli Aliyu.
"Kasan ka fadawa iyayenta sun zo to ni miye na fada min na zo?”
“Ke ma ai mahaifiyarta ce”
“Idan ba mahaifiyarta a kusa ba”
Ummi ta dan sham kamshi domin ko kadan bata son raini. Anty Shafa ce ta fara gaishe da Ummi sannan Hajiya ma ta miko mata gaisuwa.
“Lafiya kalau”
Daga Hajiya har Ummi babu wanda yacewa wani an iso lafiya.
"Allah dai yasa ta haihu da kanta, idan ba ita ba haushe zaka dauki halin da namiji ka saka a zuciya”
Cewar Anty Shafa. Ummi ta yi kasa da ido tana saurarenta, kamin ta dago ta kalleta tana murmushi.
“Shafa ya yaran? Ya Step Mom dinku? Har yanzu dai shiru kin ki kawo mana kati?”
“Ina nan ina lalabe Ummi kin san mazan sai a hankali, yara suna lafiya”
Ta amsa cike da gatse.
“Haka ne Allah ya kawo na gari”
“Ameen”
Ta amsa. Aliyu ya ciro wayarsa dake ringing ya fice daga gurin, Ummi kuma ta nemi guri ta zauna Hajiya nata safa da marwa tana daga hannu tare da rokon Allah ya saukar da Kameela lafiya.
“Ameen ya rabbi, idan ba sakarci irin na Kameela ba, yaushe namiji zai maka alkawarin ba zai kara aure ba ka yarda, gashi nan ta jawa kanta nakudar dole”
Hajiya ta juyo ta kalleta.
“To miye laifinta? Allah dai ya bude mana idonta lafiya?”
“Ameen”
Ummi dai bata ce komai ba sai saurarensu take, ta san kuma saboda ita ake yi dan ta ji. After like one hour Kameela ta sauka lafiya sai dai abun da ta haifa be zo da rai ba. Hakan kuma be hana iyayenta mijinta da surukar murna ba domin ita dai ta haihu lafiya bayan ta sha wahalar nakuda.
Sai da Aliyu ya rada ma yaron suna sannan aka yi masa sallah aka binne shi a makabarta musulmi dake garin Part-harcour.
Ko kadan Aliyu be jidadin yadda yaron ya zo babu rai ba, sai dai babu yadda xa'ayi da hukuncin Allah sai hakuri, ganin yanayinsa ya saka Ummi ta hade maganganunbda take da su a zuciyarta ta daga masa kafa.
[4/22, 9:24 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL
🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
Page 1️⃣5️⃣
Ta hado tea ya kawo ma Ummi.
“Ni ba irinka bace, me zan yi da tea yanzu da yamma"
Murmushi yayi ya zauna yana updating status dinsa domin sanar da duniya matarsa ta haihu amman dan be zo da rai ba. Bayan ya gama ya aje wayar ya kai hannu zai dauki tea kiran Kameela ya shigo wayarsa, fasa shan tea yayi ya dauki wayar.
“Hello...”
"Kana ina“
“Ina gida“
“Tare da wa?"
Ya kalli Ummi sannan ya amsa mata
"Tare da Ummi"
"Na ji Hajiya tana maganar wai zata tafi da ni gida gobe idan an sallame ni”
“Kamar al'ada ce ko mace ta koma gida idan ta yi haihuwar fari”
"Bana son na barka, ni bana son tafiya, za a iya min komai a nan mana"
"Haka ne amman idan ta nuna tana son tafiya dake ba zamu iya hanawa ba”
“Ina son idan ta maka maganar tafiyata kace mata aa kana son na zauna a nan din"
Yayi shiru be ce mata komai ba jin hakan ya saka ta kashe wayarta, domin ita ma ta san mijinta ba kasafai take saka shi abun da be yi niya ba.
"Kameela ce?“
“Bata son tafiya gida, ni kuma ba zan iya jayayya da iyayenta ba, bana son abun da zai kawo mana rashin jituwa musamman da Hajiya“
"Rashin jituwa na nawa kuma? Bayan wanda aka sha kamin auren?”
“wacan ai ya wuce Ummi, kuma tun daga lokacin sun san ni ba kanwar lasa ba ne, Aliyu kike ji fa Ummi”
Ya fada yana murmushi, Ummi ta tabe baki.
“Aliyu soyayya? Romeo baban kauna, sharukan din masoya? Mai alkawarin da ba zai iya cikawa ba”
Ya kalleta da dan mamaki still yana murmushi.
“Ummi ina kika samo duk wannan kuma?”
“Baka yi alkawarin cewar ba zaka kara ma Kameela abokiyar zama ba?”
Ya rausayar da kai.
“Ta fada miki ne?"
“Aa ai kasan iyayenta ba yan dattako ba ne, sun fada dan na ji kuma na ji"
Ya shafa kansa.
"Idan baka yi hankali ba, kishin Kameela sai ya halakata ya jefaka a matsala, domin zafin kishin yayi yawa, madadin kai kuma ka nuna mata abun da take yi kuskure ne sai kawai ka shimfida mata tabarma ta hau, akan wane dalili zaka mata alkawarin ka haramtawa kanka abun da Allah da kansa ya hallata maka? Kai da malami ne Aliyu, ban yi tsammanin wannan daga gareka ba”
“Ummi baki fahimta ba ne”
Ummi ta hade rai.
“Toh fahimtar da ni“
Ya gyara zamansa ya aje wayarsa gafe.
“Ummi ke kika haife ni, kin san halina ciki da waje, tun kamin na yi aure ke kin sani, bana da ra'ayin auren mace sama da daya, Allah ya hallata mana auren mace mace sama da daya ne idan zamu iya adalci, shi kuma adalci wani abu ne mai nauyi sai dai mu kwatanta, ni kuma bana son na aikata wani abun da zan tashi a gaban Allah wani dan'adam ya tuhume ni da shi, kuma Ummi kin san iya gwagwar mayar da muka sha kamin iyayenta su yarda su ba ni aurenta”
“Saboda an yi fadi tashi sai ya saka ka zo ka yi mata alkawarin da ni na san wata rana sai ka karya shi, mata na mahaifinta yake aure bayan Hajiya? Ina ce matansa uku, ai ta tashi ta ga ubanta da mata biyu ko bayan mahaifiyarta, sai kai dan ta raina ka zata saka ka yi mata alkawarin ba zaka kara aure ba, yan'uwanta ma saboda basu da kunya za su nemi fada min magana”
"Wata kila yanayin abubuwan da suke faruwa gidan su na kishin ne ya saka take tsoron kishiya, amman me Hajiya ta fada miki? Sun miki wata maganar marar dadi ne?"
Ya tambaya yana jiran amsarta, karamin aikinsa ne ya daga waya ya kira Anty Shafa da take yayarta ya ci mata mutunci akan Ummi, bayan kuma abun be kai ya kawo ba.
“Wannan maganar suka fada mana, ni ba zance ka kara aure ba, domin Kameela bata min komai ba ta rike ni kamar uwa, family ta ne dai ba su da mutunci shiyasa ake son idan za'ayi aure a nemo yar gidan mutunci, ka karanta ka gani amman duk ka tsallake wannan ka aurota”
“Kameela tana da tarbiya Ummi, tana da biyayya daliba tace fa, tana da ilmi daidai gwargwado, ita dai bar ta ga rashin sirrin sai kuma zafin kishi, kuma duk mace ba zata rasa wannan ba, kuma ni ba cilasta ni na yi mata alkawari ba, na mata alkawarin ne da yakinin zan cika kuma zan iya, saboda ina son kwanciyar hankalinta da farincikinta, kamar yadda Daddy na yake son matarsa”
Ummi ta watsa masa harara.
“Dan iskan yaro, ai ni ban hana Daddynku aure ba, kuma ban ce yayi min alkawarin ba zai kara aure ba, kawai be yi niya ba ne, waya isa ya hana Daddynku abun da yayi niya?”
“Tohm Daddyna zan gado“
“gamu gani ai, farin tuwon nan dai cikin bakar tukuyar can ya fito, muna nan da kai wata rana sai ka zo min jikinka na rawa kace zaka kara aure, saboda iyayenta ba yan mutunci ba ne, kuma ba su so aurenka da ita tun farko ba, na lura matukar ba kashe auren nan suka yi ba hankalinsu ba zai kwanta ba”
“Haba Ummi ke ma kin san idan na auri mace ta auru Wallahi, aje dai sama a dawo a shiga wuta da ruwa a mutu ayi rai amman ba zan sake mace ba, noooo saki be ma cikin abun da nake magana, ni dai ina son matata, matata kuma tana so na to duk abin da zai biyo baya daman dole mu yi hakuri da shi”
Ummi ta tabe baki.
"Allah ya baku zaman lafiya"
"Ameen, Ummi ke ma yanzu dai kamar Kameela ta fita ranki"
"Aa ina sonta, ai tana mutunta yan'uwanka kuma tana sonka tana girmamani, ni kawai familynta ne bana so, abubuwan da suka yi ta yi kamin aurenku har yanzu ban manta ba“
Yayi murmushi kawai be sake cewa komai ba, Ummi ta dauki wayarta tana amsa kira, shi kuma ya shiga amsa sakwannin dake shigo masa. Sai dare Ummi ta koma asibitin tare da Aliyu, Kameela ta tarbe ta da hannu biyu Ummi ta zauna kusa da ita tana mata sannu. Sai kusan goma Ummi ta yi mata sallama ta fita Aliyu ya mike tsaye.
"Zan je na kaita gida na dawo, gobe zata wuce jirgin Safe zata bi"
"Okay sai ka dawo"
Ya matsa kusa da ita ya sumbance.
"Sai wani shinning kike kamar ba haihuwa kika yi ba, kumburin nan ma ya miki kyau"
Ta yi murmushi.
"Ba zaka yi ma Hajiya magana ba? Ina jin tana maganar tafiyar fa, gashi sunce gobe za su sallame ni“
"Idan an tafi dake zan zo na same ki"
Murda kofar dakin da aka yi ne ya saka shi aurin janye hannunsa a jikinta ya matsa baya. Anty Shafa ce ta shigo tana hamma.
“Yauwa Aliyu Hajiya tace ka hadowa Kameela kayanta a zo da su nan gobe za su wuce idan Allah ya kaimu"
Ya kalli Anty Shafa fuska ba yabo ba fallasa, kamin ya juya ya kalli matarsa.
"Me da me zan dauko miki my love"
Ta dan bata fuska kamar zata yi kuka, ita ganin take idan bata kusa da shi zai kalli wasu matan ne, kuma kamar ta bashi damar magana da Emily ne.
"Ba sai ka dauko komai ba, zan siya a can”
Yayi murmushi kawai ya fice. Sai da ya fita sannan Anty Shafa ta zauna tana fadin.
“Abun dai be yi ba, kin haihu ace uwarsa wai zata koma gobe gobe kuma jirgin safe zata bi, kamar dai bata sonki, shi kansa ban ga yana wani daukinki ba”
Kameela ta hade rai tana magana a shagwabe.
“Kin ga Anty Shafa ki daina zarga min uwar miji, kuma ni mijina yana so na na sani”
“Gaki ga shi ai indai namiji ne, har zai miki alkawari ki yarda, ba gashi kin janyowa kanki ba har kin rasa danki? Farawa da iyawa kenan daga chat da mata sai zancen kara aure, muna nan dake sai Aliyu ya saka ki kuka da bakinciki, ba namiji ba, can talkaminmu suka tsinke"
Kameela dai ta yi shiru bata ce komai ba, sai dai ranta babu dadin tafiyar da zata yi da kuma kalaman da Anty Shafa take fada akan mijinta. Aliyu be dawo dakin hannu sake ba sai da kayan kwalama da kuma akwati daya babba ya saka mata abubuwan da ya san za su mata amfani, ko ba su fada masa ba ya fahimci ba su son tafiya gidansa ne shiyasa suka ce ya hado mata kayan, madadin ita yayarta ta tafi ta hado mata kayan, shiyasa Hajiya take son da am sallameta ta wuce da ita daga nan ba tare da sun tafi gidan ba.
Shi kuma be shirya wulakanta kansa ba, ko neman rigima da su ba shiyasa, be musa musu ba ko ya nuna musu damuwarsa akan yunkurinsu. Da kansa ya hada nata wani tea mai kauri ya bude naman da ya zo mata da shi har tiriri yake yana saka mata a baki.
“Yanzu ya aka yi da Emily din? Kuma taya aka yi ma ka gane ta?”
Anya zai iya fada mata a gurin da yake aiki take aiki? No.. Ya tambayi kansa sai kuma ya bawa kansa amsa.
“Hotonta ai ya bada yanayi da kamaninta, kuma kana ganin yarta zaka san yar Turhan ce domin fuskarsa ce”
“Meyasa ba zaka fada masa ba, bayan kasan yadda yake ta nemanta”
Ya kai mata tea a baki.
"Ita ta bukaci kar na yi haka“
“Saboda me?”
“Wata kila tana da dalinlinta“
“Dan Allah ka fita sabgarta ka cire kanka a tsakaninsu, ba a shiga tsakanin mata da miji ni dama ace be saketa ba abun zai fi min sauki"
"Saboda ke zaki hada aurensu? Dan Allah masoyiyata ki bari mu rabu tafiya, karki saka kanki a wata damuwa dan Allah, ke kin san wanene, kuma yaushe na ce miki ya sake ta."
"Au be sake ta ba? Au to da sauki ai"
Yayi murmushi yana kara jinjina lamarin Kameela, shi dai ya fadi haka ne saboda hankalinta ya kwanta. A asibitin ya kwana tare da matarsa ya kwantar mata da hankali kuma ya lalabata akam tafiyar da Hajiya za ta yi da ita.
EMILY POV.
Driving kawai yake tana kalle kalle bata shirya komawa gida, kuma bata san gurin da zata je ba, haka ta yi ta yawo kamar zata zagaye garin kamin ta faka motarta kusa da wasu dakuna da suke kamar quarters. Bude gambun motar tayi ta fito daga cikin motar ta nufi wani katon dutse da yake gurin ta zauna. Kallo daya zaka yi mata ka fahimci bata cikin farinciki, domin fuskarta a fili take nuna damuwar dake zuciyarta.
Rabo ido take amman zuciyarta da hankalinta suna wani gurin na dabam.
“Me kike a nan?”
Maganar ta ji ne daga gefenta ya saka ta juyo gaba daya sai ta yi arba da matar da ya kusan kade Fatima, kuma ita dai matar da ta gani asibiti ta yi mata magana.
“idan kina son na tashi na baki guri, zaki iya cewa na tashi na bar unguwar ko gurin, ba sai kin tambayi mai nake ba, ai zaune kike same ni, zama nake yi”
Ta dan yi murmushi ta zauna kusa da Emily.
“Baki yi kama da masu zafin rai ba, daga ganin yanayinki na san ranki ne a bace, na hango ki tun daga dakina, karki manta jiya ne ko shekaran jiya ke kika min magana kamin na miki”
“Da na yi miki magana yi kika yi kamar baki san ni ba”
“Ni ma ranar raina yana bace ne ki yi hakuri, Sunana Tasmia"
Ta mika mata hannu, Emily ta kalleta kamin ta mika mata nata hannun.
“Aysha Emily”
"Nice to meet you Aysha, me kika zo yi unguwar mu?"
“A nan kika"
"huh"
Emily ta daga kafadunta.
“Kawai dai ina yawo ne ban san inda zan je ba"
"Zaki iya shigowa ciki ki sha ruwa?"
Emily ta kalleta for few seconds...
"Be kamata na yarda da kowa ba"
"Haka aka fada miki?"
Cewar Tasmia tana murmushi.
"Haka duniya ta koya min"
"Da alama duniya ta rike ki a makarantarta ta yi ta zuba miki darussa a ajinta"
"Haka ne, na zuba min ilmi kuma na karantu, yanzu yayewarta kawai nake jira“
Emily ta karasa zance idonta na cika da hawaye.
“Matsalar miji ce? Ko ta yaya? Ko ta family?”
“Ya kamata na yi wata maganar dake?”
Emily ta yi maganar a siga tambayar.
“Zaki iya yarda da ni, baki ga yadda kaddara take ta hada mu ba? Wata kila tana nufin mu zama kawaye, ko kuma abokan shawara ta wani bangaren, karki damu da banbanci addininmu ba, ko launin fatarmu dukanmu mata ne, da suke dauke da matsala in one way or the other”
"Zan fada miki damuwata ne kawai saboda ina bukatar fashe kurjin dake min ciwo, kamar yadda na so na yi a wacan ranar da na yi miki magana, saboda bani da kawar da zan tattauna damuwata da ita, ba ni da uwar da zata ba ni shawara, bani da dan'uwa da zai share hawaye, ba ni da kowa sai ni kadai”
Tasmia ta zauna a kusa da ita tana kallonta cike da tausayin ganin yadda hawaye suke kwaranya a idonta.
“Kin rasa iyayenki ne?“
"Kin rasa iyayenki ne?“
“Ni ma dai ban sani ba, mutuwa suka yi aka rasa inda za a aje ni sai gidan marayu? Ko kuma dai haihuwata aka yi ta gurbatacciyar hanya aka jefar da ni, su waye iyayena miyasa suka bar ni? Shi ya fi tsaya min a rai, ki kalli fatar jikina haskena yayi yawa, ina da blue eyes, gashin kaina ja, waya biyo mahaifina ko mahaifiyata, ban sani ba”
“A ina kika samu kanki bayan kin girma? Su wa suka rike ki?"
"Mutanen da ban sani ba, labari ne mai tsawo“
"Toh yanzu wa kike aure? Baki jin dadin zaman gidan mijin ne ko me da har kika tunawa da baya tunatar da ba zata miki amfani ba”
Ta share hawayen da suka ki tsaya mata.
“Wasu sun yi dacen rayuwa Tasmia, sun san su waye iyayensu, wasu sun yi rayuwa da su, wasu sun san a ina familynsu suke, wasu suna da kawaye, suna da masu kula da su, ni ba ni da kowa yarana ma basa bukata ta a yanzu"
Jimmm Tasmia ta yi kamin ta ce.
“Yaranki suna bukatar tsawatarwa, gaskiya na lura da tarbiyar yarki sai a hankali, me zai saka ba za ku tattauna da mahaifinta...”
Bata karasa ba Emily ta tari numfashinta.
“Bana tare da mahaifinta, a yanzu ina zama a karkashin kulawa da ikon wani ne, da baya bari ma rabi kowa, baya barin na yi kawa, banbancin rayuwar baya da ta yanzu kadan ne, har yanzu a cikin kangi nake"
Tasmia ta dafa ta.
"Miyasa ba zaki yi nesa da shi ba?”
"Ba zai bari ba, saboda shi yake ciyar da mu shi yake mana komai ko da kuma na yi kokarin gina kaina ba zai bari ba"
Tasmia ta juyo da ita suka fuskanci juna.
"Ban san iya hidimar da yake miki ba, amman da alama akwai tsoro da fargaba a zuciyarki, irin tsoron da fargabar da yake samu kowane dan'adan mai rauni har yayi nasarar sauya tunaninsa ya saka shi a cikin wani kogo ya hana shi walwala, daga lokacin da tunaninki yake hango miki rauni a tafiyarki, zuciyarki take raya miki ba zaki iya ba, to ba zaki iya ba ne har abada, a yadda na fahimce ki kin sha wahalar rayuwa kamin yau, idan kuwa haka ne be kamata ace wani ne yake fada miki yadda zaki tafiyar da ita ba, ai babu wanda ya san kalar talkamin da suka dace da kafarki, ina nufin babu wanda yayi tafiyar da kika yi a hanyar rayuwar ki saboda kaddarar kowa dabam, idan babu mai sonki shin ke ba zaki so kanki ba? Kar tsoron sherin wani ya hana ki gina rayuwarki, ki tsaya da kafarki irin tsayin da ba za a iya kallon idonki a fada miki wata maganar ba, ki sakawa ranki zaki iya, ki yarda da kanki Emily, idan baki da kowa to ke ki zamewa kanki kowa mana, ki gina labarinki, ki yi taki duniyar ki cikata da zuri'arki"
Tasmia ta karfafa mata guiwa ta zuba mata kalaman da wani be taba tsaya ya tsara mata su a cikin kanta ba, hakan ya tsayar da zubar hawayenta a yanzu tunaninta ya karkata ta inda bata yi zato ba. Karar shigowar sako ne ya sauka a wayarta sai ta sauke kanta kasa tana duba wayar.
“Kina ina?”
Ta karanta sakon na Vito. Kamin ta dago ta kalli Tasmia dake zuba mata kalamai.
“Ki fara mafarkinki daga yanzu, kar kowa ya sake baki tsoro, karki yarda zuciyarki ta fada miki ba zaki iya ba, tsoron cutarwa wasu ta hana ki cika burinki, ita rayuwar duniya ciki take da kalubale babu mai kaiwa karshenta sai wanda ya barta, ke kadai kika girma babu kowa a kusa da ke! To taya zaki bari wani ya milke ke a yanzu? Wani be kamata ya rubuta labarinki ba, ke ya kamata ki aje alkamin da kanki... Ki rufe tawadar sai ki bada damar a karanta...”
Ta karasa tana share mata hawayenta tare da yi mata murmushin karfafa guiwa. Emily ta yi murmushi still hawaye a idonta.
“Ke ce mutum ta biyu da na gani musulma mai zuciya mai kyau, daga wacan mutumen da ya taimaka min lokacin da zan haifi Fatima sai kuma ke, amman duk sauran daga masu gorin addini sai masu cin amana“
“Haka muke mu musulmai cikin akwai na gari akwai bata gari, kamar dai kowane addini, idan kina son zaman lafiya da kowa da kuma fahimtar rayuwa, ki kalli addinin da mutane suke yi, da kuma abun da ya koyar, ba wai rayuwarsu ba"
"Haka ne"
Ta amsa tana share hawayenta.
"Toh yanzu zaki iya shigowa ki sha ruwa?"
Emily ta yi murmushi.
“Wata kila wani lokacin"
"Shikenan tun da haka kika zaba, amman yanzu zaki saka min number ki zan saka
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 63