Kin sa ɗana ya mutu da tunanin bana son shi, baki kalli lalurar da take tare da shi me yasa kika cusa wannan a kwakwalwarshi? Yanzu ta ina zan fada masa ina kaunarsa? Ta ina zan nuna masa kaunar da nake masa? Why Chidimma why? Shiyasa ya daina son na rabe shi na baya yarda da ni sai ke? Why Chidimma why?"
Kalaman Emily ba su daga mata hankali ba kamar kallon da Vito yake mata.
" Ki amsa me yasa kika yi?"
Ta girgiza kai jikinta na rawa numfashinta na gargada.
"Ba haka ba ne, wata kila be fahimta ba shiyasa yake rubuta wannan, amman ban fada masa cewar baki kaunarsa ba, ba gaskiya ba ne"
"Meyasa Matata tsone miki ido? Na sha fada miki ki daina fada min idan Emily ta yi wani abu, kamar jiya, ke kika fada min ta shirya ta shirya Fatima cikin abaya sun fita, kika sa na zo na mata duka da ya tsaya min a rai yanzu yana ci na, kuma na gargade ki ba tun yau ba akan ki cire idonki akan Emily, the more kika fada min laifinta the more zan tsane ki, me yasa kika shiga tsakaninta da London why? Answer me....!!!“
Da farko cikin natsuwa ya fara magana da mugun kallo, daga karshe kuma ya karasa da tsawar da ta saka Chidimma sakin fitsari...
Hmmmmmm, masu karatu wai ba ku ganin Aliyu yana wuce gona da iri ne?
Ina Team Vito? Ni fa iya wuya muna tare🥰🥺 wanda ya so ka taimaka a lokacin da baka da komai ai shi ne naka.
_______________________
Sannu ‘yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe ɗinki da kaya masu kyau, masu ƙima daga Khadeeja Candy Store
Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sauƙin sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing.
Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taɓawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet ɗinmu sun dace da ke
Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sauƙi ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko’ina!
Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1
da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0
Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame.
Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ƙayatarwa duk a farashi mai sauƙi.
Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu!
Baki da lokaci? Muna da sauƙin oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina!
To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08
Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store.
Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haɗuwa.
[6/22, 6:33 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08
*🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
FOLLOW ME ON 👇🏻
FACEBOOK
https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914
TIKTOK
https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1
INSTAGRAM
https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0
CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01
KHADEEJA CANDY STORE
https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08
Page 3️⃣8️⃣
Cikin karfi hali da kashe murya ta fara magana tana kuka.
"Shekara cikin ta shida nake a gidan nan, idan ina nufin cutar da Emily ko yaranta zan yi tun kamin a kawo yanzu, a janye maganar London tun da shi ba shi da lafiya, amman Fatima tana da wayo tana da fitina, da a ce ina musu wani abun cutarwa da yanzu ta fada, ko kuma ta ki ni, bata kila London be fahimce ni ba ne, shiyasa ya rubuta abun da ya rubuta, amman ni miye ribata idan na rabaki da dank? Idan baki gode min a tsawon shekarun nan ba, toh be kamata ki tuhume ni da wani abun ba"
Ta juya gurin Vito.
"Ka gafarce ni, ina saka kaina aikin da ba nawa ba, amman ni ina tayaka yaki ne kawai, tun da ka kawo ni a gidan matsayin yar aiki, ma lura kuma duk wanda ya kalli yadda kake nunawa Emily gata ya san kana sonta, hakan yana min dadi, ina sha'awar mace ta samu kulawa a gurin wanda take so kamar uba ko miji ko dan'uwa, domin ni nawa uban be dauke ni a matsayin ya ba, na kan fada maka Emily ta kula wani ne saboda taya ka yakin da baka san ranar cin nasararsa ba, na kan zauna na yi tunani yadda ka yi ma Emily gata ita da yaranta ka nuna mata so da kauna fiye da kowa a duniyar nan, amman ko na rana daya bata taba duba wannan ba, har takan bawa wasu mazan damarda za su iya sonta, bayan kuma kai ka cancanci zama a zuciyarta, na kan fada maka ne saboda ayi ma tukkar hanci, amman son da kake yi ma Emily ya hanaka fahimtata, a yanzu kuma kuna zargina da abun da ban aikata ba, kar idonka ya rufe, ka tsaya ka yi tunani gudun yanke hukunci a ciki fushi domin komai daren dadewa sai ka fahimci dalili kuma ka yi nadamar abun da zaka yi min a yanzu, London ba shi da lafiya ba mamaki lokacin da ya rubuta hakan ba a cikin hayyacinsw yake ba"
Duk wani yanayi da muryar da Chidimma ta san zata iya amfani da ita ta siye zuciyar Vito daga yi mata hukunci a cikin fushi sai da ta yi, kuma ta yi nasara domin kuzarinsa na son yanke mata hukunci mai tsauri ya karaya, maganganunta suka shige shi. Emily ta turata ta karfi.
"Are you saying all this saboda kina son Vito? Ko kuma saboda ki kawar da laifin da kika aikata?"
"Ban aikata ba, idan ma na aikata har kake kokarin kawar da laifin shim bancanci ki taya ni ba? Tsawon shekara biyar da na yi ina kula da yaranki ban cancanci godiya ba? Ko kuma dai ke haka halinki yake? Butulu ce ke? Shiyasa shi kansa Oga Vito kika duba halaccinsa ki kaunace shi ko da na kwana daya ne? Ya so ki kamar zai mutu, ya so yayanki kamar nasa, ko matar governor ba zata nuna miki gata ba, amman duk baki gani ba, ni kuma na bauta miki babu dare ba rana, ni nake kula da yaranki, ni nake girka musu abinci na gyara gidan, na karanta musu storybook ko wane dare, idan ba su da Lafiya ni da ke muke jinyarsu, ki kaddara ma na aikata abun da London ya rubuta shin ban cancanci yafiya ba?"
Cikin daga muryar da ya fi kama da tsawa take maganar tana nuna kanta sai kuka take sosai. Emily ta kai hannu zata mareta Vito yayi karaf ya rike, Emily ta kalleshi da sauri tana mamaki.
"She's right, shekara biyar ba kwana biyar ba ne, ta bauta miki, ni kuma na so ki fiye da komai da kowa a duniyar nan, ita baki gode mata ba, ni kuma baki ba ni abun da nake so ba, akanki na kusa haukacewa, akanki bana ji bana gani na kyautata miki iyakar kyautatawa, na baki gatan da babu wanda ya taba baki, a tsawon lokacin nan bana son bacin ranki, ban taba cilasta miki kwanciya guri daya dake ba jira nake har sai kin amince da kanki, fada min bayan ni ba zai iya miki? Babu mahaifiyata bata fada min ba akanki amman ban saurareta ba, babu iya cin fuskar da yarki Lisa bata min amman na daure saboda ina sonki, na kashe kudi mai yawa akan maganin danki, Emily ni na inganta rayuwar ki kika zama abun da kika zama a yau, a haka duk ban cancanci tukuicin so ba? Amman a kwana daya ko biyu kin hadu da wani a gurin aikinki kin soma ba shi fuska da kofar da zai so ki"
"You take her site?"
"Yes saboda gaskiya ta fada, abu ne da ya kamata na gane tuntuni, shiyasa yanzu kika tsane ta ai, kike son a kareta what if you make all of this?"
Ya fisge takardar hannunta ya yaga.
"Enough is Enough Emily, I'm tired, kuma a yanzu na gane duk abun da ya faru da ke, kin cancanci haka, domin ke ma butulu ce, kin butulcewa addininki, kin butulcewa mutanen da suka dauki a matsayin ƴa suka yi nufin baki gata, shiyasa ke ma kika hadu da tasgon rayuwa, yanzu kuma kina son butulce min bayan duk abun da na yi miki"
Kallonsa kawai Emily take hawaye na sauko mata. Chidimma ta zube kasan guiwoyinta ta hadu hannayenta.
"Ranar yau ta kasance bakar rana a gurina, domin wannan ce rana ta farko da na ga tsakani tsakaninka da Emily, dan Allah ka gafarce ni bana nufin shiga tsakaninku, ni na aje aiki na bar aikin daga yau"
Vito ya saka hannayensa ya dago ta tsaye.
"Baki yi laifin komai ba, kuma ba zaki bar aiki ba, amman zan kaiki gidanku ki huta har sai ta gane muhimmamcinki"
Yana fadar hakan ya kama hannun Chidimma ya nufi kofar fita falo, Emily na tsaye tana kallonsu har suka fice, sai ta lumshe ido tana jin wani abu mai nauyi yana mata yawo a cikin zuciya, duk abun da Vito yayi mata a yanzu, ko wanda zai mata a gaba ta cancanci haka ko fiye da hakan ma, domin ya sama mata komai ya mata gata amnan zuciyarta ta kasa bata hadin kai gurin mallaka masa abun da yake muradi, ta mari kanta ta sake marin kanta ta sake marin kanta har sau uku sannan ta bude ido hawaye na mata zuba ta hada takardar da VITO ya yaga ta kwashe ta juya ta fara haurawa stairs din idonta na rufewa saboda hawayen da take. Dakinta ta shiga ta kwanta kan gadon ta lumshe ido tana miada numfashi.
Bata dago ba sai da wayarta ta yi kara alamar shigowar sako, sannan ta bude ido ta daga kan ta kai hannu ta dauko wayarta ta duba sakon da Aliyu ya turo mata.
"Barka da safiya, fatar kina lafiya"
Ta girgiza kai alamar no bata lafiya, amman bata iya amsa masa kuma ba zata iya fada ba. Ta koma ta kwanta tana aika masa da sako bayan ta yanke shawarar abun da take ganin kamar shi ya fi a gurinta, domin ganin take rayuwata bata da wani sauran amfani a yanzu, ita kanta ta gaji da shiga gararin rayuwa daga wannan sai wacan, idan Vito ya watsar da ita a gurin wa zata koma yanzu kuma? Bayan shi me sake faruwa da ita..
"Na san na hadu da kai akan kaddara like accident, amman zuciyata ta aminta da kai, idan har bayan rayuwa ta ji cewar Turhan zai iya kula da Fatima, kuma zaka rika dubata toh ka ba shi ita"
Sakon na shiga wayarsa ya kirata sai ta ki ta daga, hakan ya saka shi aiko mata da sakon karta ya umarce ce data bude whatsapp dinta. Ta bude WhatsApp din ta shiga chat dinta da Aliyu hotunan Fatima ta fara cin karo da su, sai kuma short Video da yayi mata, gaba daya tana cikin farinciki ne da nishadi.
"Emily kin yanke shawarar kashe kanki ne? Kin manta da farinciki Fatima? Wannan farinciki kike son ta rasa? Bayan kin san yadda rayuwa take da wahala ga mutunen da ba shi da uwa a kusa? Ashe ke na jaruma ba ce? Kin ce zaki canja ina canjin yake? Ashe ba zaki iya ba? Akwai abun da yake faruwa ne? Ki fada za mu iya maganin abun a tare, Amman dai ki sani Fatima ta yi kankanta da rasa mahaifiya, ya kamata ki girmama farincikinta fiye da naki"
Shi ne rubutun da ya biyo bayan sakon. Sai kuma ga Voice din Fatima cikin murna.
"Momy ina jindadin zama a nan, Momy ki bar ni na kara kwana, ke ma ki zo kin ji Momy hahaha"
Ta shafa screen din wayar tana kallon Fatima da murmushin da ya fi kuka ciwo. Sannan ta rubuta masa amsa.
"Bana nufin kashe kaina"
"Akwai abun da ya faru ne? Ina son na ganki mu yi magana"
Sanin kanta ne idan ya ga duka a jiki zai iya cewa zai shiga fada da Vito, a yadda Vito yake fusace a yanzu komai zai iya faruwa, dan haka ta haramtawa kanta ganinsa har ma ta bukaci kar ya kawo mata Fatima a yanzu sai nan da kwana biyu.
"Aa ba yanzu ba, idan babu damuwa babu takura Fatima zata iya kara biyu a gurinka? Ka yi hakuri na saka ka ba tare da neman izini ba, ban san ko zai kawo rashin fahimta a tsakaninka da Matarka ba"
"Aa, zata iya zama har na zuwa lokacin da kike so, amman ina jin kamar akwai abun da kike boye min shiyasa baki son na ganki ko?"
"Babu, kawai ina son ta yi enjoying zama da kai, wannan farinciki data rasa na uba ta ji shi a tare da kai ko na kwana biyu ne"
"Toh zan iya kiranki Video Call?"
"Aa Vito yana yawan zama gidana a kwana biyun nan bana son na samu matsala da shi ko da kai, zan jidadi idan baka takura dole sai ka gan ni ba"
"Okay na fahimta, zan jira har sai kin samu natsuwa sai na kawo miki Fatima, daga nan ki karasa min labarina"
"Zan karasa maka labarinka ta nan, zan bar maka sako a duk lokacin da ka samu dama sai ka saurara"
"Idan haka kika zaba ba ni da matsala"
ALIYU POV.
Ya bata amsa yana mai gamsuwa da cewar data yi Vito yana zama a gidanta, da farko kam yayi tunanin ko Vito ya mata wani abun ne shiyasa take ta boyo bata son ya ganta.
Yana dagowa ya kalli Fatima sai ta bata fuska.
"Ni ba yanzu zan koma gida ba"
Yayi murmushi shi kan shi yana jindadin zama da ita.
"Momy tace abarki ki kara kwana biyu"
"Yeehhhhhhhh"
Ta rumgume shi sai yayi dariya.
"Zamu je da ke yau, na siya miki new clothes kina so ko?"
"Eh"
"Okay, gobe zan yi tafiya zan tafi Kaduna kuma zan tafi da ke, amman ba zamu fadawa Momy ba sai mun dawo, wannan sirrinmu ne kin yarda?"
"Yes yes yes yes....."
Ta shiga tsalle da murnar zai tafi da ita. Ya yanke shawarar tafiya da ita ne ganin zata yi kwana biyu a gurinsa albashi idan ya dawo sai ya fadawa Emily cewar ya tafi da ita, tafiyar ta kwana biyu ce idan ya isa Assabar da wuri zai tafi gidansu Kameela, idan kuma hakan be samu ba zai bari sai washe gari, on Monday sai ya dawo PH. Yadda ya fada haka ya aiwatar daga Office dinsa ya wuce da Fatima shipping ya siya mata tufafi da wasu abubuwan da ya san zata bukata, kamar Turaren yara shoe's da kuma ribbons. Fatima ta saka jin sha'awar kasancewa uba saboda yadda yake kula da ita a dan zaman da ta yi na kwana biyu shi yake gyara mata gashi da taimaka mata gurin wanke baki.
Ta dayan bangaren kuma yana tausayin rayuwarta domin ya fahimci yadda take tsananin bukatar uba a kusa da ita, sannan ya fahimci sakacin mahaifiyarta na bar masa ita a hannunsa ba tare da damuwa da wani abun zai same ta ba, ko da yake Emily ta aminta da shi ne ya saka ta bar masa Fatima hannunsa, sai dai abun da yake ganin ya kamata ta damu da shi, shi ne Fatima mace ce kuma yarinya karama kyakkyawa sosai, zata iya haduwa da wanda zai iya lalata mata rayuwa, shi kanshi Vito ba dan hankalinsa be gurin ba, da tuni yayi mata aika aika sai dai ta koma kuka da bakinciki, ta dayan bangaren kuma yana ganin kamar saboda Fatima bata da uba ne, dawainiyar ta yi ma Emily yawa ita kadai, sai dai duk da haka wannan yana daga cikin abun da yake son tattaunawa da ita akansa idan ya dawo sun hadu.
Abu ne da ya sani hatsari ne Sosai tafiya da Fatima ba tare da sanin mahaifiyarta ba, alkawari daya ya daukarwa kansa duk tsanani duk rintsi ba zai taba barin Turhan ya ga Fatima ba, kuma ba zai bari Fatima ta ganshi ba, dan haka zai yi iya kar kokarinsa duk yadda zai iya wajen kare afkuwar hakan. Business class ticket ya siya saboda ya samu yin walwala shi da Fatima, yana gama sallah ya shiga Kitchen ya hada musu light breakfast sannan ya tashi Fatima ta yi sallah ta yi wanka ya ci abinci ya dawo mata rigar da zata saka ya tsaya bayanta ya gyara mata kanta sannan ya fita dakin ya shiga dayan dakin ya shirya ya, ko da ya dawo ya samu ta saka rigar ya saka turare tana gyara masa kayan kwalliyar dake gaban Madubin.
"Good Girl"
Ya bata hannu suka taba tana dariya sannan ya fito da suitcase karami da babba ya aje direbansa ya dauka ya saka mota. Sai da Aliyu yayi addu'ar fita ya karantawa Fatima ya biya sannan suka fito, a lokacin da suka doshi motar da za su hau yana rike da hannu Fatima sai wata zuciyar ta raya masa ya kira Emily ya fada mata zai yi tafiya na kwana biyu kuma zai tafi da Fatima mana, zai fi zame masa kwanciyar hankali, sai kuma dayar ta hana shi ta hanyar nuna masa Emily ba zata yarda da shi ba, zata yi tunanin ko yana son kai Fatima ne gurin Turhan, shi kuma baya son maida Fatima a yanzu domin yana jindadin zama da ita, ita kanta tana son haka, bayan duk wannan ma ai Emily ce da kanta ta bukaci ya bar Fatima a gurinsa na kwana biyu.
Haka dai ya shiga motar yana ta sake sake, can kuma sai ya ji gabansa ya fadi, ba tare da sake wani tunani ba ya ciro wayarsa ya kira Emily 3 missed calls bata daga ba, ya yanke shawarar fada mata idan ma tace bata aminta ba sai ya maida Fatima a gurinta ai ba laifi ba ne. Ta dayan bangaren ma yana jin kamar ba daidai ba ne ace ya tafi da Fatima a garin da Mahaifinta da kakarta suke ba tare da ya barta ta gansu ba. Da be samu magana da ita ta waya ba ya duba agogon hannunsa ya kalli time sai ya juya ya kalli Fatima.
"Sweetheart zamu je mu fadawa Momy zan yi tafiya dake, idan ta aminta sai mu tafi, idan kuma tace aa sai na tafi ki ki zauna"
A take Fatima ta lake kafada ta fashe da kuka.
"Aa ina son na tafi, Momy ba zata bari ba, zan tafi nidai ina son tafiya please"
Ta shiga yi masa magiya tana kuka.
"Okay zamu tafi ba sai ta sani ba"
Ya amsa mata ne kawai saboda ya samu ta yi shuru domin ta fara hargitsa motar da ihunta tana shure shure da kafafuwanta. WhatsApp dinsa ya shiga sai ya tarar Emily ta aje masa voice ne mai yawa and part part, ko be tambaya baya san ba zai wuce labarin da tace zata karasa masa ta nan ba. Sai da ya aje mata nasa sakon ta whatsapp ganin bata online ya saka shi aika mata the same sako ta layin karta kwana sannan ya sake kiranta still bata daga ba kuma bata maido masa da amsa ba.
Dan lokacin da ya rage masa a airport din ya karasa shi har zuwa lokacin da suka fara shiga jirgi bata maido masa da amsa ba, suna shiga jirgin ya saka wayarsa Airplane mode.
Sai da suka taba hira da Fatima dake dan jin tsoro a lokacin da jirgin ya tashi, ya bata wayarsa tana game sannan ya saka airpods ya yi connecting da wayarsa, ya shiga WhatsApp dinsa ya bude chat din Emily ya fara sauraren Voices din data turo masa.....
_______________________
Sannu ‘yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe ɗinki da kaya masu kyau, masu ƙima daga Khadeeja Candy Store
Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sauƙin sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing.
Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taɓawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet ɗinmu sun dace da ke
Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sauƙi ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko’ina!
Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1
da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0
Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame.
Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ƙayatarwa duk a farashi mai sauƙi.
Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu!
Baki da lokaci? Muna da sauƙin oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina!
To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08
Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store.
Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haɗuwa.
[6/23, 9:05 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08
*🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
FOLLOW ME ON 👇🏻
FACEBOOK
https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914
TIKTOK
https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1
INSTAGRAM
https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0
CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01
KHADEEJA CANDY STORE
https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08
Page 3️⃣9️⃣
ALIYU POV.
Ya gyara zamansa da kyau sannan ya kunna Voice din ya fara saurare.
*** *** ***
Tun ana sauran sati daya Turhan ya zo garin Kaduna, mahaifiyarsa ta fara shirye shiryen tarbarsa, duk wani abun da ta san zata girka masa ta tanade shi da wuri, a tsawon satin daya kullum ni take sakawa na gyara masa dakinsa na saka turare. Ana gobe zai iso Ammy tasa na fara shirya masa abincin da ta san ko ya kwana ba zai lalace ba kamar snacks da nama, ranar da zai iso tasa na shirya masa full Medames miyar waken fava daya daga cikin abincin da mutanen sudan suke so sosai, ita ta koya min yadda zan hada har aka yi nasara na gama komai cikin sa'a, ragowar abinci kuma sai ta bukaci na girka miyar waina (masa) bayan na hada na bar miyar a wuta sai kuma ta bukaci na zo na toya Masar, haka dai na daure na karasa aikin, bayan na gama tasa na yanke masa fruit, na hada fruitsalad, kusan komai da Turhan zai ci ko ya sha ko ya taba Ammy ni ta saka na shirya, sannan ta bukaci na shiga ciki na yi wanka na shirya, tufafin da zan saka ma ita ta zaba min. Bayan na yi wanka ina tsaye gaban madubi ina daura lafayar da ya ki dauruwa a jiki Ammy ta shigo fuskarta dauke da murmushi tana kallo.
"Maa Shaa Allah kin yi kyau sosai yata, shiyasana zaba miki wannan lafayar ai, nasan bakin abu zai miki kyau sosai, ki yi hakuri yau na saka ki aiki da yau, so nake Turhan ya ci abincin kuma ke ma ki saba da fara yi masa hidima tun yanzu"
Ban ce komai ba, kuma ban ji farinciki ko kishiyarsa ba, ita da kanta ta taimaka min na daura lafayar sannan ta fice. Be shigo gidan ba sai da La'asar. Ina daki Ammy ta aiko a kira ni muka dugunzuma gaba dayan gidan har masu aiki zuwa tarbon da ɗaya a gurin Ammy. Sarauta da kudi wani abu ne mai matukar burgewa da daukar hankali, wa can lokacin kamin ranar ban taba ganin irin motar da aka kawo Turhan da ita ba, sai dai na ga tsabanin yadda Ammy ta fada min cewar mutanen kasar Sudan musamman a gidansu Jallabiya suke sakawa, dan haka na tsammaci ganin jallabiyar a jikinsa, sai dai ya zo akasin tunanina domin kananan kaya ne a jikin wando da riga, wani irin kamshi yake mai dadi. Kuma tabbas kyakkyawa ne a zahiri fiye da hoto ma, fari fes kamar dai kai yana da tsaye duk wata siffa da namiji zai cika aso shi ko ya burge Turhan ya cika wannan, Wallahi da na yi arba
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 31 Chapter of 63