Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fuskarta ya saka ta bude blue eyes dinta a hankali ta sauke su akan fuskar mutunen da murmushi ba shi da muhalli a gurin. Ta tashi zaune tana kallonsa sai na juya ta kalli gadon ta kalli agogo ta ga karfe biyar na yamma ta sake kallonsa. “Yaushe ka zo?” Ya ki ya amsa sai kallonta yake. “Kace min zaka tafi Lagos? I thought kana can” Nan ma be ce mata komai ba sai kallonta yake. “Why are you here?” Ya saka yatsansa ya shafe mata gefen bakinta. “Waya taba ki?” Kallon fuskarsa take zuwa kirjinsa da boturan rigar suke bude, sannan ta sake kallon fuskarsa sai ta fashe da wani sabon kuka. “Kowa baya so na, babu mai bukatata a kusa da shi, Fatima tana bata min rai yau sauran kadan mota ta bugeta saboda ta bata min rai, na tafi asibiti London yace baya so na ya tsane ni” Ya matsa kusa da ita ya rumgumeta tare da dora chin dinsa saman kanta. “Sai kuma wa?” So yake ta ambata masa sunan wani dabam ba yayanta ba tace su suka bata mata rai, domin ya san ba zai iya taba yayanta ba, amman zai iya taba kowa bayan jininta. Ita kuma bata yarda sunan kowa ya fito daga bakinta domin ta san waye Vito ta san abun da zai iya, kuma ta san yadda yake sonta. Ya dago ta daga jikinsa ya rike fuskarta da hannunsa biyu yana kallon kyakkyawan idanuwanta. “Akwai wanda ya taba ki bayan Fatima da London? Akwai wanda ya fada miki wata magana?” Ta girgiza kai alamar aa, ya mutsa bakinsa kamar zai yi magana sai kuma ya saketa ya mike tsaye, kasa ya sauka ya shiga kitchen ya dauko mata ruwa ya fito har ya nufi stairs ya fara takawa sai kuma ya juyo ya dawo gurin da fatima take zaune a dinning ya kalleta. “Idan kika sake batawa mahaifiyarki rai har ta yi kuka idonta ya kumbura kamar yau, sai na miki danyen hukunci” Ya fada fuskarsa babu alamar wasa sai ma kara hade mata rai da yayi. “I hate you, kuma Momy ba zata aureka ba” Ta fada masa cikin tsiwa tana murguda baki. Wani mugun kallo ya watsa mata sannan ya dauke kai ya haura sama. Tana ganin haka ta mike tsaye ta nufi wayar mahaifiyarta ta dauka ta haura sama da gudu ta shiga dakinta, jakar makarantarta ta bude ta dauko kati da Aliyu ya bata ta zauna bakin gado tana cire password din wayar. ALIYU POV. Misalin karfe 3pm ya faka motarsa harabar gidan ya bude ya fito yana kallon bakuwar motar dake fake kusa da balcony. Bayan ya rufe motarsa ya nufi entrance din ya fara takawa har ya isa bakin kofar falon ya tura ya shiga. Matarsa ya tarar a tsaye tare da wata bakuwar fuska dake rataye rike da karamin mayafi a hannu dayan hannunta kuma rike da jaka. Aisha na ganin shigowarsa sai hankalinta ya tashi, ta juya ta gefen da bakuwar take tana tarewa dan kar Aliyu ya kalleta da kyau, domin atamfar dake jikinta da matse ta sai dai ba sosai ba, amman ta karbe ta yi mata kyau. Ta inda ta yi sa'a mijinta baya daga cikin irin mazan nan da suke son kallon mata balle kuma ya san halin matarsa da kishi ko a tv ya kurawa mace ido sai ta yi masifa balle kuma a zahiri, tun kallon farko da yayi ma bakuwar a farkon shigowarsa be sake kallonta ba. “Sannu da zuwa” “Sannu Babyna ya gidan?” “Lafiya Kalau” Yayi kamar be san da bakuwar ba ya shafa fuskar matarsa zai wuce sai ta gabatar masa da kawarta tana dan kareta. “Tasmia ce ta zo mana” “Maa Shaa Allah, ina mata barka da zuwa” Ganin alamar be gane ta ba ya saka ta ce. “Tare muka yi Secondary School” “Nice” Ya fada ba tare da ya kalleta sannan ya wuce zuwa dakinsa, tun da ya bada baya Aisha take kallon Tasmia ta ga ko ta kalli mijinta and yes ta kalleshi da kyau har ya shige ciki, Aisha ta dan canja mata fuska tare da jefa mata zagi cikin wasa sai dai har a zuciyarta ta ji zafin kallon da ta yi ma Aliyu. “Yar iska me kike kallo? Da wani billenki a nan” Tasmia ta kalleta ta yi murmushi. “Masu ciki fa zuciyarsu a kusa take, daman gaki ba tsaye kin san ance short people suna da saurin fushi, wai su da fushi 5&6, ni kin ga tafiyata” Ta nufi kofa, Aisha ta tsaya a gurin bakinciki ya hanata raka kawar da suka shafe shekaru ba su ga juna ba, sai ma binta da ta yi da harara. Aliyu na shiga dakinsa wayarsa ya fara cirowa ya aikawa Turhan da sako bayan ya gama karanta wanda ya turo masa. “Yau gidan marayu hudu muka je ba mu dace ba, ko'ina cewa suke ba su santa ba” “Baka amsa ni ba, Turhan me ya rabaka da yarinyar nan? Me yasa ka sake ta?” Ya aika masa sannan ya aje wayar ya fara cire tufafinsa. [4/20, 9:59 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/FdvabUKwybz6ogMKtgx02w *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ Page 1️⃣0️⃣ EMILY POV. Tana shan ruwan tana shan ruwan tana ajiyar zuciya kai kace yar yarinya ce aka saka kuka, hannu ya kai yana shafa saman kanta har ta shanye ruwan, sai ya karbi kofin ya aje. “Ba Fatima ce kawai ta saka ki a cikin damuwa ba, waya taba ki?” “Ita ce kawai” Ya kalleta ba dan ya gamsu ba, ba zai cilasta mata ta fada masa abun da ya haifar mata da damuwa a yanzu ba, amman da sannu zai sani domin ya san yadda take sauyawa idan ta shiga damuwa. Mikewa yayi tsaye rike da cup sai ta rike hannunsa na hagu ta dago tana kallonsa da idanuwanta dake bayyana damuwa sosai. Komawa yayi ya zauna sai ta dora kanta a cinyarsa ta lumshe ido tana maida numfashi a hankali, ta sani bata da sauran kima a idon kowa sai Vito a yanzu, ita din ba abar tausayin kowa bace sai mutumen da ya ganta a rana ya saka a inuwa kuma ya lullube ta da kulawa da kauna, yake gudun bacin ranta yake kaunarta fiye da kansa, tana jin kamar shi kadai ya rage mata a yanzu. “Mommy ta fada min zata zo satin nan, idan ta sauka a nan na san zata rage miki kewa, ko ba komai zaki samu uwa zata kula dake kamin ta tafi, amman idan baki ra'ayi zata sauka gidana sai idan kin bukaci ganinta” Ya fada yana shafa fuskarta a hankali kaunarta na kara zafafa a zuciyarsa. Bude idon ta yi ta tashi zaune tana kallon wani gafen, ta yi marmarin kasantuwa kusa da wasu iyalin, sai dai kudurin da take da shi ba zai barta ta sake kusantar iyalin Vito ba a yanzu. Ta mike tsaye ta cire ribbons din dake kanta jan gashinta ya sauko har bayanta, sai ta tsaya gaban madubi tana cire dankunenta, shi ma tsayen yayi ya matsa kusa da ita yana kallon kyakkyawar fuskarta ta madubi, baya bukatar ta bashi amsar tambayarsa, ya zauna da ita na tsawon shekara bakwai ya san me take so da wanda bata so, yana iya karantar yanayinta tun kamin ya san dalilin farinciki ko bakincikinta. Ya dafa kafadarta har lokacin kallon fuskarta yake ta madubin dake tsaye gabansu, ta dago ta kalleshi da blue eyes dinta. “Zata zauna a gurina har sai kin bukaci ganinta” “Ba wai bana son zuwanta a nan ba ne kawai...” Bata karasa ba ya juyo da ita ta fuskance sai ya saka hannunsa biyu ya rike fuskarta yana kallon zanen halintarta hancinta. “Ina sonki Emily, ina sonki, so mai tsanani irin son da alkalin ba zai iya rubuta bawa, irin son da zan karar da kalamai gurin furtawa, ina sonki, irin son da zan iya kashe kowa a duniyar nan na rayu daga ni sai ke, zan iya rabuwa da kowa na rayu da ke, rashin zaman mahaifiyata a kusa da ke ba zai haifar da komai ba sai karin kaunarki, kar hakan ya dame ki, zata a gidana har sai idan ke da kanki kin bukaci ganinta” Ya karasa yana kallon kanta, yana sonta wannan rubuce yake a cikin kaddararsa, shiyasa baya haufin nuna kaunarta a ko'ina haka kuma baya babu wanin abun da zata aikata a duniyar nan da zai saka ya nisance ta. Ya runtse ido yaja dogon numfashi ya sauke ya bude idon ya sauke su a kanta. “Har yanzu baki san miye so ba, har yanzu baki fahimce waye ni ba, har yanzu baki san irin son da nake miki ba, amman ina fatan wata rana zaki san haka” Hawaye ya sauko a idonta sai ya share mata da yatsanta. “Zan tafi gurin London komai zai wuce” Ya saketa ya matsa baya, kallonsa kawai take har ya fice sannan ta lumshe ido hawayen na cigaba da sauko mata, tana tsananin tausayin Vito fiye da yadda take tausayin kanta, ya mata fahimtar baibaine amman ta san son domin ta so mutumen da be dan darajar ta ba, son ne ya janta ga halaka har ta rasa makomarta ta butulcewar mutanen da suke rike a matsayin ďiya. Tana jin tsoron irin son da Vito yake mata, tana tsoron abun da zai haifar tana tsoron yadda makomarsa zata zama idan babu ita a kusa da shi. Tufafin jikinta ta cire ta daura tawul ta shiga bandaki ta kunna shower da nufin wanka sai kuma ta samu kanta da zama a cikin tube din tana nadamar shiga rayuwar Vito da ta yi... Ta dade a haka sannan ta yi wanka ta fito bata shafa komai ba ta saka short gown ta kwanta kwanta saman gadonta, korar da aka yi mata a yau ta dawo mata a rai, a take hawaye ya cika idonta, meyasa bata da sa'a a rayuwa? Meyasa farinciki yake mata nisa? A duk lokacin da ta daura damarar gina ramen farinciki sai bakinciki yayi mata kawanya, idan bata samu damar tsayawa da kafarta a yanzu ba sai yaushe zata yi? Ita kenan ba zata iya bawa kanta farinciki ba sai idan wani ne ya bata, wanin ma Vito mutunen da ya gama mata komai kuma bata da wata sakayya da zata masa, yanzu ko nan gaba. Motsin turo kofar dakin da Fatima ta yi da gudu ta shigo ya saka ta yanke tunanin da take ta tashi zaune, kamin ta yi wani yunkurin goge hawayen da suka bata mata fuska Fatima tace. “Momy ki duba wannan number ki goge ta, amman karki kar duba abun da na tura gashi nan yana kira na san zai ce na goge ne kuma ban iya ba ban gane gurin ba, yace koya min amman na manta ban san ya ake gogewa ba...” Kamar wanda aka ce amsa kiran mana, haka ta taba green botton din sai ga fuskar Aliyu ta bayyana. ALIYU POV. Ya fito wanka rike da karamin tawul yana goge jikinsa sai da ya gama sannan ya zauna gefen gado ya dauki wayarsa yana duba whatsapp dinsa, domin a yanzu ba shi da wani abu mai muhimmancin kamar jiran amsar Turhan, gashi kuma har yanzu Turhan be amsa masa ba bayan kuma ya karanta sakon nasa. Yaje wayar yayi ya mike tsaye ya fara shafa mai ya shirya tsab cikin shigar kanana kaya black T-shirt and White jean, yana tsaka da fesa turare Aisha ta shigo dakin, fuska ba yabo ba fallasa tana kallon bayansa har ta karasa kusa da shi. “Ga abincinka can a falo fa, kai nake jira ka sauko mu ci” “Na ci abincin a waje” Ya amsa mata ba tare da ya kalleta ba, sakin baki ta yi tana mamakin furuncin, tasan waye mijinta cin abinci a waje ba dabi'arsa ba ce. “Wai duk fushin ne haka? Fisabilillahi ganin chat kawai ya kai ace ka dauki fushi da ni har haka?” Ya juyo ya kalleta. “A gurinki abun da kika aikata ba laifi ba ne?” “Idan ma laifi ne ai ya kamata kayi min uzuri ko? Har sai idan na sake aikatawa” “Rashin daukarsa laifi shi yake kara bakanta min rai, taya zaki zauna da kawarki ki labarta mata yadda muke rayuwa a shimfidar da ko dan'uwanki ba a yarda ya sani ba, taya zaki ji idan kika kama ni ina fadawa abokina yadda nake da ke a gado?” “Dadi zan ji mana, ai kana fada masa yadda na iya gyara shimfida ne, Aliyu wannan abun fa is normal, yanzu rayuwa ta canja ba yadda muke a baya ba ne, wacan rayuwar da kake tunani ko iyayenmu ba su yi ta balle kuma mu, amman dai shikenan tun da baka so zan daina” “Ina fatan haka” Ya furta yana kokarin danne fushinsa domin kara bata masa rai take da kalamansa na yanzu. Murmushi ya sakar mata ya matsa kusa da ita. “Muje mu ci abincin” “Ba kace ka ci abinci a waje ba?” Ta fada tana masa kallon da yafi kama da harara, ya fadada murmushinsa tare da shafa cikinta. “Wasa nake kawai ina fushi ne amman yanzu na sauko” Ya rike hannunta suka fice daga dakin, falo suka sauka ya ci tuwon shimkafa da favorite miyarsa miyar kuka, sai da ya ci yayi nas sannan ya soma bata labari, da hira ta yi dadi sai ya dauko mata zancen sabuwar ma'aikaciyarsu da kuma fadan da ta yi da Amal a yau. Har a ranta ta ji dadin korar da aka yi mata domin bata son kowace mace a kusa da mijinta, Amal din ma dan ta zama dole ne. “Kasan wasu matan ba ba su da kai, musamman kabilun nan kara ana musu haka, ta nan za su fahimci matsayinsu, kuma wasu ma fa kawai neman maza ke kawo su” Tana maganar tana yatsina fuska. Kallonta yayi yana girgiza kai. “Madam ba fa ni kadai ba ne namiji a kamfanin nan, kawai ke da kin ji maganar mata sai kishi ya tashi” “Matan ne fa yanzu kamar za su auri namiji da karfi, idan mutum be yi taka tsantsan ba sai a aure masa miji” “Ke da kika san waye mijinki ai be kamata ki daga hankalinki akan ko'ina zan shiga ba, kuma karki manta ke kadai zaki rayu a gidan Aliyu daga ke sai yayanki, ko kin manta alkawarin da na yi miki? Ba ke ba kishiya” “Ban manta ba amman ku maza ai wani lokacin zaku iya ganin mace ku bi ku rude kanta duk wani alkawari da kuka yi ku watsar da shi, musamman idan ka ga wata fara kyakkyawa yar doguwa” Yayi murmushi. “Allah ya saukaka miki wannan kishin, ni bana da ra'ayin karin aure” Dadi ya lullubeta ta kwanta jikinta. “To yanzu zaka je ce ta dawo aikin ne ko kyaleta zata ka yi?” “Aa ai ta riga ta rasa kenan, ni ban san a ina take ba balle nace ta dawo, kuma an riga an yi replacing dinta da wata ai” Sanin halin matarsa ya saka shi bata wannan amsar. “Haka ma yafi, waya sani ma ko tana da kyau” Wannan karon dariya yayi, domin ta canja daidai Emily tana da kyau kuma ya san da ta san haka ba zai zauna lafiya ba. “Ai ni kowace mace na kalla ke nake gani a fuskarta” Ta buge masa hanci tana dariya, shi ma dariyar yayi ya dauko mata wata sabuwar hira, sai da aka kira sallah la'asar suka daga falon, a shi ya nufi masallacin dake unguwarsu ita kuma ta gabatar da sallah ta a gida kamar yadda Annabi ya umarta. Misalin karfe biyar da mintuna 58 wayarsa ta yi kara alamar kira, a ka'ida idan yana kusa da matarsa baya taba waya saboda ya bata lokacinsa, sai idan kiran ya tsananta ko kuma ya kasance na gaggawa ne, sai dai jiran amsar Turhan ya saka shi mikewa tsaye ta nufi wayar ta dauka sai ya kira ne ta whatsapp kuma video call da wata bakuwar number da be san waye ba. Rejecting yayi ya bude whatsapp din ya duba bakuwar number sai yayi arba da hotunan Emily sun fi guda hansi, Hello Hi kuma ya fi ashirin, kamin ya samu damar reply wani kiran ya sake shigowa. And this time around baya son rejecting domin ya fahimci mai kira, gashi kuma ba zai iya amsawa a gaban matarsa ba, dan haka ya fice daga falon ya haura sama sai da ya shiga dakinsa sannan ya amsa kiran dake shigowa da zarar wani ya yanke. “Hello...” Fatima ta fada da karfi tana masa waving. “Hi ya kike?” A take murmushin fuskarta ya gushe ta bata fuska ta fara kukan da babu hawaye. “Ba Lafiya ba, Vito yayi min fada sosai har yana cewa sai ya yanka ni, kuma Momy ma fushi take da ni bata so na, saboda na yi mata tsawa lokacin da muke tafiya a hanya dazun kuma, na je gurin titi har mota ta kusan bugeni, muka hadu da wata mata ita ma ta dinga min fada ta kai mu gida, amman ai ina fushi ne na yi, shi ne Vito ya dawo Momy ta fada masa sai yayi min fada, ni kuma na shigo daki na turo maka hotunan Momy ka duba ka gani ko kana sonta” Daga idonsa har girarsa da bakinsa a bude suke, ya rasa ta ina zai kama zaren zancen ma, yadda ta aika masa rahonta ya saka ya manta labarin farko da na tsakiya, na karshen kawai ya rike wanda shi ya fi bashi dariya. Wato ya duba ya gani ko yana sonta, ita a tunaninta son mahaifiyarta yake. “Me ya faru ma?” Ya tambaya domin ya manta labarin nata, yadda ta zayyana masa dazun haka ta sake zayyana masa yanzu. “Okay wait now, yanzu dai me kika yi ma Momy” “Tsawa” “Fada” “Meyasa kika mata tsawa to? Baki san ba ayi ma iyaye tsawa ba? Babu kyau, ko a gurin wanda ba musulmai ba, balle kuma ke da kika fada min ke musulma ce, yana da ace kin fi kowa tarbiya” “Ai musulmai ba su da kirki haka Momy tace” “No ta yi ma musulmai mummunar fahimta ne kawai, amman musulmai sun fi kowa kyan hali da tarbiya” “To miyasa wannan matar girlfriend dinka ta kore Momy? Why?” “She's not my girlfriend, kawai abokiyar aikina ce, abun da ta aikata ba abu ne mai kyau ba, amman musulmai ba haka suke ba, idan kina son na yi shiri dake to karki sake yi ma mahaifiyarki tsawa” “Amman ai bata sona” “Inji wa tana sonki mana, idan kika bata mata rai ni ma raina zai bace, kina son raina ya bace?” “Aa” “Momynki ma ba zata jidadi ba idan kika bata min rai, dan haka ki daina bata mata rai kin ji” “Zan yi tunani akai” Yayi murmushi. “Okay, zan duba hotunan sai mu yi magana” “Okay, zan turo maka wasu ma idan ka gani sai ka goge komai kar Momy ta gani zan aje mata wayarta” “Ba zan iya gogewa ba, ai na nuna miki yadda zaki goge” “Na manta kawai na iya saka number ne, amman zan bawa Momy ta goge min” Tana fadar hakan ta yanke kiran. “Nooo nooo nooo nooo” Ya fada yana girgiza kai, ya sake kiranta videos calls din amman bata daga ba, ya rasa ya zai yi sai ya zauna gefen gadonsa yana dafe goshi. “Oh Allah matsalar yara kenan” Ya hade yawu da karfi yana tunanin abun da zai sake yi ba, can wata zuciyar ta bashi shawarar sake kiranta sai ya sake kiran Number ta whatsapp as videos call kamar yadda suka yi da farko. Boom Emily ta amsa kiran ta bayyana gaban screen din wayarsa tana kallonsa da mamaki fuskarta kuma dauke ta hawaye. Shi ma kallonta yake zuciya na bugawa ciki na kukan rashin gaskiya. TURHAN POV. “Fara ce sosai, tana da jan gashi da blue eyes amman tana da kima” “Gaskiya ba mu santa ba, babu mu da marayu masu wannan bayanin da ka bayyana” “Ba a yanzu ba ne, ta kwana biyu fa, ita kanta yarinyar ta zama babbar mace har da yara” “Gaskiya ba mu santa ba, amman zan bincika maka, idan na ga wani abu makamancin wanda ka fada zan nemeka sai ka bar mana information din” Ya busar da iskar bakinsa ya kai hannunsa a kai, gaba daya ya gama zagaye gidajen marayu dake nan kusa be samu Aisha ba kuma ko'ina yaje cewa ake basu san wata mace mai wannan siffar ba. Kamar yadda suka bukata information din ya bar musu ta yadda idan an samu wani abu game da ita za a iya tuntubarsa. Sannan ya fito jiki a sanyaye ya shiga motar da suka shigo. Ya sauke ajiyar zuciya ya kai sau hudu sannan ya dago hannunsa ya duba wayarsa, babu wani sabon sako bayan wanda matarsa ta aiko masa sai kuma na Aliyu, ya kasa amsa ko daya daga na matar har na Aliyun saboda baya cikin yanayi mai dadi. Faruk ya tashi motar suka fara tafiya, sai a lokacin ya samu sukunin amsawa Aliyu tambayarsa, tare da dora masa da wani bayanin. “Abun da Mommy take kokarin yi a yanzu zai iya haifar da matsalar da tafi ta baya, domin har yanzu bana son yarinyar nan, kawai ina nemanta ne saboda Ammy, wahalar neman nan nata da nake sha ya saka na kara tsanarta Ammy ta kasa gane banbanci...” Be gama amsawa ba ya dago ya kalli Faruk dake kokarin fakawa gefen titi. “Lafiya” “Toh gamu gani, tsohon nan ne yake ta min hannu” “Wane tsoho?” Turhan ya kalli gefensa, mutumen da ya tarbe su ne a gidan marayun har yayi musu iso a gurin shugaban gidan. Faruk ya sauke gilashinsa. “Lafiya?” “Lafiya dai ranka ya dade, kawai dai ina da bayani ne da zai taimaka maka akan neman yarinyar nan” Turhan ya gyara zamansa da sauri yana leken tsohon da yayi jika da shi. “Okay Sir muna jinka” Tsohon ya kalli hanya gefe da gefe sannan ya sauka daga kan okada da yake ya sallami mai okadan sannan ya matsa kusa da su sosai yace. “Ba zai yi na baku bayani akan hanya ba, saboda za a iya ganina a nan, hakan kuma zai iya haifar min da matsala” Turhan ya bude motar ya fita ya bude masa gidan baya ya shiga ya zauna, sannan ya koma ya zauna ya juya yana fuskantarsa. Da yaren turanci tsohon ya fara magana yana hadawa da yarbancin kamar yadda yake da farko, daman kana kallonsa kaga bayarabe tsagen fuskarsa ma ya bayyana haka. “Na ji lokacin da kake bayani akan matar da kake nema, ai ba a neman mutum haka a babban guri irin wannan, saboda ba mu da tabbacin abun da ka fada akanta haka din ko akasin haka” “Haka ne” Turhan ya fada da sauri. “Ba ni da tabbacin neman da kake mata, amman ina fatan ba zaka cutar da ita ba” “Babu cutarwa a ciki dan Allah idan kasan inda take ka fada mana” “Ban san inda take ba a yanzu, amman na san matar da ta dauke ta, akwai information din komai a file din gidan da nake, na san Emily farin sani domin na yi shekaru ina aiki a nan, na gane ta ne ta hanyar kamaninta daka fada amman sunanta Emily ne ba wacan sunan daka fada ba Acha” “Mun gode sosai, yanzu zaka iya kai mu gurin matar da ta dauketa din?” “Aa zan dai iya neman file din da addreshin matar yake sai na nuna muku ku tafi nemanta, amman a bisa sharadin guda uku” Faruk ya kalli Turhan Turhan ma ya kalleshi suka hada ido sannan suka kalli tsohon. “Miye sharadin” “Sai kun yi rantsuwa ba za ku cutar da ita ba, kuma ba za ku bayyana komai akaina ba cewar ni na baku wannan bayanin na yadda za a same ta, na ukun kuma za su biya kudin bayanin da na muku a yanzu, za ku biya kudi idan na kawo file haka ma idan kun tafi gidan matar za ku biya kudi ko da ba ku same ta ba, sannan kuma idan kun ga Emily komai tsawon lokaci za ku biya kudi” Turhan yayi murmushi, kudi daman ba matsalarsa bace, ganin Aisha ne abun da yake buri a yanzu, wai hausawa suka ce bukatar maji hajji Sallah. ___________ Kuna ganin Aliyu zai fadawa Turhan ya san inda matarsa take? Anya da gaske tsohon nan yake ko kuma dai ya shiry cin kudinsu ne.? Ya kuke gane za a kare tsakanin Aliyu da Emily? Ga barawo ga mai kaya...! Kallon kallo akuya kallon kura... 😅 [4/20, 9:59 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆:

Chapter 8 of 63