Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ba, na manta sunan abokin nasa dai amman wanda aka kaiwa yarinyar ta Emily" "Oh Turhan? Eh ina da number mahaifiyarsa" Ummi ta kai hannu ta dauko wayarta ta kamo number ta karanta mata, Mama Barakat ta saka sannan ta yi mata godiya ta yi mata sallama ta fice tare da yarta wacce ta rakota. Fitar Mama Barakat mutane suka ragu har Ummi ta samu damar amsa waya daya daga cikin mutanen da suke kiranta, sannan ta haura sama ta yi wanka ta sauko domin shiryawa Daddy wani abu kamin ya iso, daman bata yarda mijinta ya ci abincin kowa sai ita, sai idan bata gida ko kuma wani babba uzuri ya sha gabanta. Tana Kitchen tana tsaka da girkin ne ta ji sallamar Ammy, sai ta rage wutar gas din ta yi kasa sannan ta fito. "Maraba da Hajiya Maijidda, yau Ammy ce a gidan na mu" "Ni ce Ummi, fatan mun same ku lafiya" "Toh Alhamdulillah, ya gidan ya kwana biyu" "Sai godiya, ya Aliyu da jiki? Ashe haka abu ya faru? Tohm Allah ya saukewa ya tsare gaba" "Ameen Ameen, ashe kun ji" "Eh ai kin san abu irin wannan yana saurin yado, balle kuma wayarsa tana gidanmu gurin Fatima, to yawan kiran da ake ne nake amsawa ta nan na ji" "Oh ashe wayar tana tare da ku, ikon Allah to yarinyar take?" "Tana nan lafiya kalau" "Maa Shaa Allah, tohm bari na duba girkina" "Tsaya dai tukuna Ummi na zo nan saboda mu tattauna abubuwan da suka faru" Ummi ta koma ta zauna. "Toh kamar me kenan?" "Haba ki daina yin kamar baki san komai ba mana, Aliyu be fada miki abun da ya aikata mana ba? Kuma na san Emily ai tana nan ko?" "Eh haka ne, Emily tana nan tare da mu, Aliyu kuma be fada min ya aikata muku wani abu ba" Ammy ta sauke ajiyar zuciya. "Na san kin san yadda muke ta faman neman Emily, shi kansa Aliyun ya fi kowa sani domin Turhan be boye masa komai ba, amman ace Aliyu ya san inda Emily take wai har da ya a tsakaninsu amman ko da wasa be kyankyawasa Turhan ba?" Ummi ta hade yawu. "Ammy a yanzu ba zan iya bawa Aliyu kariya ko wanka ko dora masa laifi ba, Aliyu dai danki ne kamata yayi ace ki same shi ku tattauna" Ammy ta yi murmushi mai sauti. "Emily tana gurinki ne duk tsawon lokaci nan ko kuma dai a yanzu ne ta zo nan" "Aa ni ma a yanzu na san da ita, shi ma saboda abubuwan da suka faru ne na daukar yarta da Kameela ta yi ta kai muku ba tare da izininta ba" "Ai Kameela ta kyauta mana Wallahi, ba dan ita ba wata kila da har yanzu ba mu san komai ba, kuma Aliyu ya san yadda Turhan yake ta neman yaya" "Ta kyauta tun da ta raba uwa da ƴa, kuma ta raba igiyar aurenta kin ga ai ta ci riba, ni kuma sai na yi mamakin da aka ce Fatima tana hannunku kun riketa uwarta tana nan tana fama da kewar da damuwa, kun san yarinyar bata da gata sai Allah, gashi yanzu har ta bar musulunci" "Ummi ya kike magana kamar kina goyon bayan Aliyu? Kina ganin hakan daidai ne kenan?" "Bana goyon bayan Aliyu, amman ni dai na san ban manta lokacin da kike zuwa kamun kafa a gurin Daddyn Aliyu ba saboda kina neman a baki dama ki samu ganin Turhan, daga baya kuma kika koma rokon a bar shi ya rika zuwa inda kike, ke dai uwa ce na san kin san zafin rabuwar da da uwa, ya kike tunanin Emily tana ji a yanzu? Yarinya ta raini yarta shekara da shakaru rana tsaka ku dira a rayuwarta ku karbe mata ya? Anya kun yi adalci kuwa? Abun ma ai da kunya" "Ba karbe muka yi ba, mun rike ta ne ta yadda zata saba da mu, ke kin sani Turhan kadaina haifa, ko kare aka ce nasa ne ya kike tunanin zan so shi balle jika? Ni dai ban aurawa Emily Turhan da nufin cutar da ita ba, idan ma ba su fahimci juna ita da Turhan ba, ni be kamata ta saka ni ciki ba, kuma ko yaya dai za a juya a juyo Emily tana da igiyar auren Turhan a kanta karki manta da wannan" "Ammy idan kin zo saboda Emily ne, tana sama daki na farko hannun hagu, ni dai ba zan fada miki fari da baki akan jikarki da yarki ba, kabli da ba'adin rayuwa kin sani, idan kin yi daidai ko akasin haka a bayyane yake, ni zan shiga na karasa girkina" Ummi ta mike tsaye ta nufi kitchen, Ammy ta bita da kallo mai wuyar fassara sannan ta tashi ta haura sama ta shiga dakin da Ummi ta fada mata Emily tana ciki. Emily ta sauko da kafafuwanta kasa ta kalli kofar tana jin tsanar sunan Kameela ma balle kuma abun da ya alakance ta. Mikewa ta yi tsaye ta nufi inda take kyautata zaton bandaki ta tura ta shiga. Kallon ko'ina ta yi komai yana nan na gyara jiki ko gashi na maza kai kace Aliyu yana rayuwa a gidan har lokacin. Shaving cream ta fara dauka ta duba sannan ta duba shower gel, ta nufo shower ta kunna ta daga kai tana kallo ta tara hannunta ruwan ya zuba a hannunta sai kuma ta juyo gurin madubi ta kalli kanta kamin ta kunna tab ta fara wanke fuskarta, bayan ta gama ta dauki karamin tawul data gani aje a gurin ta dauka ta goge fuskarta ta aje sannan ta fito, tana karewa dakin kallo gaban madubin gadon ta fara nufa tana duba turaruka da suke gurin da mayuka na maza na gyara jiki, daya bayan daya ta dauka tana dubawa sannan ta aje ta nufi closet ta bude tana kallon tufafinsa talkaminsa da kuma hulluna. "Assalamu Alaikum" Sallamar Ammy ce ta saka ta juyowa ta kalli kofar sai ta maida kanta gurin kayan da take kallo ba tare da ya amsa ba. "Kina fushi da ni har yanzu, amman baki fahimce ni ba ne Aisha, bana nufin cutar da ke, daga lokacin da kika bar min wasikar nan kika gudu ba sake walwala ba, Turhan be saka samun damata ba, na yi mamakin da na ganki a cikin wannan shiga da kuma canja addinin da kika yi, wannan duk be dace da ke ba" Emily ta juyo ta kalleta. "Toh me ya dace da ni? Cigaba da zama da mutumen da na fi kaunar mutuwata a kansa? Ko kuma yarda da surukar da ta fifita farincikinta akan nawa? Ke kika fada min danki zai ba ni farinciki zai ba ni gata, sai gashi danki ya maida ni baiwa a masarautar da shi ya kamata ya ba ni gata, ya maida ni kurma alhalin ina ji, ya gabatar da ni masarautar a matsayin baiwa da kika ba shi, ko wace safiya sai na wanke bangaren matarsa, bana iya cin abincinsu a haka nake daurewa, ko da yake laifina ne, ai ya gargade ni tun kamin na aure shi, yace kar na amince, amman saboda ina son na faranta miki rai na miki sakamako da abu mai kyau na amince, ban taba son Turhan ba, kuma ba zan taba son shi ba, na aure shi saboda ke, a daren ranar da aka daura auren ya fada min bakar rana ce a gurinsa, a daren da aka samu cikin Fatima ya fada min bakar rana ce a gurinsa, ya fada min ba zai taba so na ko son abun da zai fito daga gareni ba, na azabtu a masarautar nan kyautar da ni aka yi ga wata mata matsayin baiwa da haka na zamu yanci, na raini cikin yata cikin wahala na haife ta ta girma ba tare da kulawa daga ubanta ba... Ko da yake ba zaki fahimta ba danki ne a gabanki..." Ta karasa tana girgiza ka tana share hawaye. Ammy ta kai zaune tana hawaye. "Na aura miki shi ne da tunanin ke da shi kuna son junanku, ni ma na yi makamanciyar rayuwar da kuka yi, amman ni na cutu ne saboda mahaifinsa baya so na, ban yi tunanin Turhan zai kyamace ki ba, shiyasa sai da na zaba na mika masa, ban ba shi gama garin bakar fata kamar sauran ba, ban yi nufin kulla Sheri ba Emily alheri na yi nufi" Emily ta dauke kai. Ammy ta nuna kusa da ita. "Zauna... Zauna ki fada min wane irin zama kuka yi, kuma me kike bukata a yanzu?" Emily ta kalli Ammy da idonta suke cike da hawaye sannan ta zauna tana aje numfashi mai nauyi a muhallinsa. [7/14, 6:25 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=KhadeejaCandy *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 5️⃣1️⃣ Cikin kuka da shesshekar kuka Emily ta karasawa Ammy labarin irin zaman da ta yi a Sudan da kuma rayuwar da ta biyo bayan zamanta a can, yadda ta hadu da Vito ta canja addini har zuwa haduwarta da Aliyu da irin rokon da ta yi masa na kar ya sanar da Turhan inda take, Emily bata boye mata ba, ta fada mata har auren nw ta yi ne saboda ita ba dan tana son Turhan ba. Ammy yaja numfashi da nauyi ta sauke hawaye na sauko mata kuka take sosai tata rayuwar take tunawa, yadda abubuwa ta yi zama da mahaifin Turhan. "Zuciyata ta raya min dole akwai abin da yake faruwa da ya saka kika gudu kuma kika bar min wannan sakon, amman ban taba tambayarsa wane irin zama kuka yi da juna ba, ni dai damuwata na yadda za a gano ki ne, wannan dalilin ya saka na daga hankalin Turhan na sauya masa fuska, na yi duk yadda uwa zata yi idan ta rasa yarsa, kin san saboda me? Saboda na gane shim Turhan mai biyayya ne a gareni? Kuma saboda ya nemo ki, ban manta lokacin da kika fada min baki da kowa ba, ina yawan tuna wannan, kuma ina jin wata kila idan na taimake ki zan iya samu aljannata ta nan, ashe ma akwai jinina a tare da ke, na aura miki Turhan ne saboda ni da ke mu samu mafita, ke ki samu miji mai nagarta mai kulawa, ni kuma na samu ɗana da zuri'arsa a kusa da ni, amman na yi kuskure, na jahilci ɗana, na yi zaton zai riritaki ne, ashe yayi miki rikon da kadan ya banbanta da wanda mahaifinsa yayi min" Ammy ta kai hannu zata taba Emily sai Emily ta matsa tana hawaye. "Baki fahimce ni ba ne Aisha, amman har gobe baki da wata uwa sai ni, ban yi nufin cutar da ke ba, na hada aurenki da Turhan ne saboda ina tunanin zai so ki, na duba kyanki a lokaci da yadda siffarki ta banbanta da yayan hausawa, wai ina zaton haka zai daga kimarki a gurinsa, sama da ace bakar fata na aura masa, na so ki kamar yar da na haifa a cikina, har gobe ni uwarki ce" Emily ta kalleta. "Zan tabbatar da hakan ne kadai idan kika saka ɗanki ya sake ni!!! Idan kika yi haka zan tabbatar kin dauke a matsayin Ƴa!" Ammy ta hade yawu da karfi ta yi jimmm na dan lokaci kamin ta sake hade yawun a karo na biyu ta daga kai. "Zan tabbatar miki da haka Aisha, ba zan so yarki ta tashi da iyaye a rabe ba, ke kin san zafin haka, haka kuma na so ki da jinina na yi nufin yanzu mu kyautata gareki, amman zan shure komai saboda farincikinki zan miki yadda kike bukata" Ammy ta mike tsaye ta dauki jakar har ta fara tafiya sai kuma ta juyo. "Zan roki alfarma daya, karki cusa tsanarmu a zuciyar Fatima, haka kuma ba zan iya shiga tsakanin uwa da ƴa ba, ba zan iya yanke hukunci akan Fatima ko Turhan ba, amman dai a tsakaninku ni na hada kuma zan raba, na barki lafiya" Ta juya ta cigaba da tafiyarta har ta isa bakin kofar ta bude ta fice, ta sauko kasa kenan ta hadu da Ummi da zata hauro sama. "Kin fito?" Ammy ta kalli Ummi ido cikin ido. "Eh na fito, Turhan zai saki Aisha zan tabbatar mata da cewar tabbas a ya na dauke ta, idan ya sake ta sai Aliyu ya aureta, na barki cikin amincin Allah" Ammy ta nufi kofa ta bar Ummi tsaye da mamaki tana kallonta har ta fice. Ummi ta haura sama ta tura dakin Aliyu da Emily take ta leka sai ta hangota tana kuka. "Ke haka zaki zauna kullum kuka kuka? Shiga ki wanke fuskarki ki fito muje kitchen" Emily ta mike tsaye ta shiga bandakin ta wanke fuskarta ta fito Ummi ta rike mata kofa ta fito suka sauka kasa, Kitchen din suka nufa ba dan ran Emily ya so ba sai dan Ummi ta bukata, a tare suka karasa aikin sai da suka jera komai a dinning sannan Ummi ta kalleta ta ce. "Kina fifita farincikin wasu akan naki, kina fargaba tunkarar wasu da abun da yake zuciyarki, shiyasa kika cutar da kanki, ko da yake ta wani bangaren ba laifin ba ne, kin tashi ba tare da kowa ba, duk wanda ya rasa iyaye ko ya tashi a maraya farincikinsa ragagge ne, a kullum yana tsoro ko fargabar rasa farincikin wani fiye da nasa, ko da yaushe kina jin ke baki da amfani wasu ne masu amfani, karki sake tsorata ko cilasta kanki abun da ba shi kike bukata ba, aikim nan da muka yi ranki be so ba ni na sani, amman kin kasa fada saboda kar raina ya bace" Emily bata ce komai ba idonta dai ya cika da hawaye. Ummi ta dauki cup ta zuba ruwa "Shiga dakin ki wanka, Nafisa zata kawo miki wasu tufafin ki saka kamin a siyo miki irin wadanda kika saba sakawa, idan kin ci abinci sai ki kwanta ki huta" Emily ta juyo ta fara tafiya, sai Ummi ta aje cup din hannunta ta fasa shan ruwa ta kira sunan Emily. "Emily" Ta sake juyowa, Ummi ta karasa kusa da ita ta rumgumeta, sai Emily ta rike ta fashe da kuka sosai, Ummi ta rika shafa bayanta tana jin tausayinta sosai karamar uwa ce da takw bukatar uwa a kusa da ita, kuka sosai Emily ta yi har ta karya zuciyar Ummi da tausayinta, Ummi ta zubar da hawaye tana mamakim yadda wasu uwa ko yan'uwan suke juyawa abun da aka haifa baya har ya rasa gata, alhalin ba su san halin da yaran suke samun kansu ba. Sai da Emily ta samu natsuwa a kafadar Ummi sannan Ummi ta share mata hawayenta. "Shiga ki huta, za a kawo miki abinci" Ta daga kai ta fice daga Kitchen din ta haura sama, Ummi ta kalli Nafisa daya daga cikin yan matan da take riko ta ce. "Ki zuba abinci ki kai mata, a fadawa Kulu ta shirya mata wani abu mai ruwa ruwa ko zata iya sha, wacan abincin kuma ki kaiwa Aliyu idan kin je ki fada masa sai Daddynsa ya iso za mu zo" "Tohm Ummi" Daga haka ta haura sama, Nafisa ta debi abincin ta kai dakin Emily sannan ta sauko ta fita harabar gidan neman Kulu, bayan ta sanar mata umarnin Ummi ta sake dawowa falon sai ta samu Ummi na jiranta. "Ungo ga wannan tufafin shigar mata da shi, ki je ki kaiwa Aliyu abinci yanzu nan" "Tohm" Ta karbi tufafin ta shigar da shi dakin Emily sannan ta fito ta saka mayafinta ta dauki abinci ta fice, Direban da ya kawo Ummi ne ya dauke ta zuwa asibitin bayan sun isa ya rika mata kayan har gurin dakin da Aliyu yake ba abar shi ya shiga ba dan haka yace ta fadawa Aliyu yana gaishe shi, ta amsa da Toh ta shiga ciki. Ta shiga ciki sai ta same shi zaune akan kujera yana tasbihi da alama sallah ya gama. "Sannu Yaya Aliyu ya jikin?" Ya daga mata kai sai da ya shafa addu'a sannan ya amsa. "Alhamdulillah" "Ga abincin ka, Ummi tace na kawo" "Ni zan iya cin abinci yanzu na sha tea ma babu jimawa, maybe zuwa anjima zan iya ci" "Tace a fada maka sai Daddy ya iso za su tare" "Okay, Ina Emily?" "Tana can gida tare da ita aka maka girkin ai" Aliyu ya kalli cooler abinci mai kyau da tsada da Ummi ta siya gurin Khadeeja Candy. "Zuba min abinci" Nafisa ta bude Warmers din ta fara zuba masa soyayyar shimkafa da kaza sai kamshi take. "Yauwa Khaleefa yace yana maka sannu da jiki" "Wane Khaleefa?" "Direba?" "Da shi aka zo daga Abuja?" "Eh shi ya kawo ni yanzu" Ya karbi abincin ya fara ci yana taunawa a hankali. "Idan kin tafi ki fadawa Khaleefa nace ya je kauyensu ya huta na kwana biyu har sai an neme shi, ita kuma Ummi ki fada mata na bawa Khaleefa hutu" "Ka kore shi kenan?" "Aa ai ba zan hana shi hanyar cin abincinsa ba, but for now bana son Emily ta ganshi ranta ya bace, yaje ya huta za a rika biyansa har sai idan Ummi ta bukaci a daina tun da Direban ta ne ba nawa ba" "Okay" "Idan kin koma ki shiga gurin Emily make sure ta ci abinci please, kuma ku rika janta da hira kar a wareta, ko nuna mata banbanci ku rika janta a jiki Please" "Okay" Ya kalli wayarsa dake kan gado tana ringing, Nafisa ta dauko ta miko masa ganin sunan Mama Baraka ya saka shi kallon Nafisa ya ce. "Zaki iya tafiya, Muktar yana nan zai min komai idan ina bukata" "Okay Allah ya baka lafiya" "Ameen" Ya amsa ya aje wayar kan cinyarsa ya cigaba da cin abincin a hankali. TURHAN POV Yana harabar gidan yana video call Fatima a hannunsa sai waving take yi ta gaban wayar, ganin direban Ammy ya saka shi sauke wayar ya nufeta Fatima na hannunsa. Ammy ta fito motar cikin wani yanayi da ke bayyana damuwarta amman hakan be hana da ta kalli Fatima ta yi murmushi ba, ta kai hannu ta karbeta daga Turhan kamar wata yar jaririya, Turhan ya karbi jakar Ammy ya bi bayanta suka shiga falon. Sai da ta fara zama sannan ya zauna Ammy ta sumbanci goshin Fatima ta sumbanci hannunta ta shafa kanta tana murmushi. "Tafi can dakina dake sama ko kuma gurin wayar da Aliyu ya baki zan yi magana da Dadynki" Fatima ta juya ta kalli Turhan dake murmushi ita ma ta yi murmushin jindadi ambatar daddynta da Ammy ta yi ta sauka kan cinyar Ammy ta nufi upstairs, daga Ammy har Turhan binta suka yi da kallo sai da ta haura, sannan Ammy ta kalli Turhan. "Kana kama da mahaifinka sosai, ko kadan ba ka yi kamada ni ba, a kamanni da hali duk baka rago shi ba" Turhan ya fadada murmushinsa yana zaton Ammy zata yabi mahaifinsa ne. "Shi ma ya mu'amalance ni kamar yadda ka yi ma Aisha" A take murmushin dake fuskar Turhan ya gushe. "Ta inda ya dara ka, shi be gabatar da ni a matsayin baiwa ba a gidansa, na shiga a matsayin mata, amman boye ni yake bana fita idan yayi baki saboda kar a gan ni, matansa duka biyu basa bukatar ganina dan haka ban isa na chudanya da su ba, shi kansa auren ya zamo masa dole ne kawai a haka yake zaune da ni, da aka samu cikinka sai ya ji tsoro kar na fara yin zuri'a da shi alhalin baya bukatar wani jinsa a cikin familynsa sai nasa, be yarda na shayar da kaiwa, ina haihuwarka aka karbe aka bawa wata balaraba ita take shayar da kai take maka hidima, da ya ga baka yi kama da ni ba har dadi ya ji, shiyasa bayan na haife ka sai aka hada kai da hadimata aka ba ni maganin hana haihuwa na sha ba tare da na sani ba, da maganin ya zauna a cikina sai ya haifar min da rashin lafiya, a dole yake bani kulawa saboda kar na fadawa mahaifin ya wufintar da kyautar da yayi masa, sai da ya ji ya gani da wahala da ni sai wata rana ya saka na shirya masa abinci, ban san ya aka yi ba amman dai bayan ya ci abinci ya kamu da ciwon ciki aka je asibiti suka tabbatar guba ce, abun da har na kasa ganewa shi ne shi ya saka gubar da kansa ko kuma hada baki yayi da likitan saboda ya fadi hakan? Daga gidan sarauta aka wuce da ni gidan yari wai ina son kashe sarki, mahaifina ya shiga ya fita ya samu daker aka fitar da ni, a wacan lokacin sun yi nufin kashe ni saboda su share labarina. Da aka dawo da ni kasar nan sai ya aiko da min da takardar da saki, wannan maganin da aka ba ni ya zama sanadin da ban samu lafiya ba sai da aka yi min aiki aka cire min mahaifa gaba daya" Ammy tana labarin tana zubar da hawaye, ta kalli Turhan. "Kasan me yasa na fada maka duk wannan?" Ya girgiza kai alamar a a jiki a mace ido na zubda hawaye. "Saboda na fahimci na yi kuskure na hada aurenka da Aisha, balaraben asali be son bakar fata, balaraben mutum yana da dagawa, ina tuna yadda na yi ta yaki na yi ta fadi ta shi na ganin hankalin mahaifinka ya dawo gareni amman hakan be samu ba, indai akan auratayya ne balarabe be taba karbar bakar fata. Gaba daya sun ture karantarwa da koyarwa Ma'aiki da yace wani be fi wani ba sai wanda ya fi jin tsoron Allah" Ya share hawayensa. "Ammy me ya kawo wannan maganar?" "A yanzu da na fada maka ka ji dadin abun da mahaifinka yayi min?" Ya girgiza kai. "Taya kake tunanin Fatima zata ji? Ya zaka ji idan wani yayi ma yarka haka? Da ace ba mahaifinka ne ya aikata min haka ba me zaka yi?" "Ba zan bar shi da rai ba?" Ammy ta daka masa tsawa hawaye na sauko mata. "To kai ba zuciya ce a kirjinka ba? Me yasa baka ji haka lokacin da kake cutatawa amanar da na baka ba? Aisha nan uwar wasu ce ai gashi nan ta haifa maka ƴa, yar wasu ce ita ma yar adam ce idan aka munana mata tana jin zafi kamar yadda zaka ji" "Ban san... San... Iya abun da ta fada miki ba, amman Wallahi ban taba dukanta ba, kuma ba a taba dukanta na kyale ba, ban tana hana mata abinci ba, a lokacin da kika aura min ita na yi kuskuren na kin karbarta ne saboda ina tsoron yadda zan gabatar da ita a matsayin mata a masarautar Mahaifina ba lallai ya karbeta ba, matata ma haka kuma wacan lokacin ina jin kamar darajarta bata kai ba, amman yanzu duk na gane kuskuren hakan" "Ta fada min irin zaman da kuka yi, kuma ta fada min a yanzu saki take so" Turhan ya ji zuciyarsa ta buga da karfi ransa ya bace sosai. "Idan tana son saki zata iya fadar tana son saki ba sai ta saka kin tuna da abun da be kamata ki tuna da shi ba" "Ni na hada auren yanzu kuma zan raba, ka rubuta takardarta ka ba ni zan kai mata" "Zan sake ta, amman ba zan bata Fatima ba" "Tsakanin kai da yarka babu ruwana a ciki, amman tsakanin kai da ita ni na hada yanzu kuma zan raba" Ya hade rai sosai ya tashi ya haura sama gurin da yarsa take. Ammy ta dade zaune a gurin zuciyarta na mata turkuki sannan ta tashi ta shiga dakin, a daren kwana ta yi da bakinciki tuna baya da kuma bakinciki abubuwan da suke faruwa a yanzu. Turhan kuma ya kwana tare da yarsa da tunanin abubuwan da yayi Emily, motsi kadan idan Fatima ta yi sai ya farka domin a kirjinsa ta kwana har safe. Washe gari suka hadu gurin karyawa, Ammy ta juye halshe ta gudun kar Fatima ta fahimci me suke magana akai, da yaren Larabcin Sudan ta ce. "Idan ka rubuta takadar ka ba ni da kaina zan tafi na kai mata" Ya tsayar da cin abinci da yake ya kalli Ammy da babu fuskar wasa a maganarta ya ce. "Da gaske kike yi Ammy? Wai da gaske kike na saki AISHA?" "Na taba maka wasa

Chapter 41 of 63