Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da kuka fito Vito na cikin gidan?" "Aa Chidimma ce kawai" Ya sake gwada kiran still switch off. A take hankalinsa ya tashi, gashi tace kar ya zo har sai ta kira be san me zai yi ba a yanzu kuma be san a wane hali take ciki ba. Sai da ya fara tuka motar yayi nisa yana ta sake sake kamin ya kama hanyar gidan Tasmia ya faka harabar sannan ya fita ya taka zuwa kofar shiga gurinta ya kwankwasa, shiru ya sake knocking nan ma shiru, wayarsa ya ciro ya shiga WhatsApp ya lalubo chat dinsa da Tasmia ya duba number ta yayi coping ya saka a dial ya kirata, ringing uku ta yi kamin ta yi na hudu ta yi picking. "Hello" Sai yayi mata sallama kamar yadda ya saba yi na kowa, ta amsa masa ta gaishe shi, bayan ya amsa ya dora mata da dalilin kiransa. "Am... Alfarma nake nema" Ta yi jimmmmm kamin ta amsa. "Fadi komai kake so Aliyu, ai ban kai matsayin da zaka nemi alfarma ba, sai dai ka yi min umarni, kuma dole na na bi ko da kuwa wuta ka ce na fada" Ta fada with excitement. "Interesting... Okay.. Anyway na zo gidanki ban same ki ba" "Allah yasa ba laifi aka ce na yi ba ba" "No ina son kije gidan Emily ne ki duba min ita, ina tare da Fatima a yanzu, bana son na je gidan har sai na yi magana da ita, kuma jikina yana ba ni ba lafiya ba" A take yanayin muryarta ya sauya saukin kiran da take ya ragu. "Ni fa bana son jefa kai a matsala, kana son shiga sha'anin Emily Aliyu kamar ka manta waye kai, musulmi kuma mai iyal..." Bata karasa ba ya yake wayar ya koma motarsa sai ga kiranta ya biyo, when he pick ya fada mata. "Kar kiran da na yi miki ya baki damar fada min magana, kuma idan kika dame ni zan bata miki rai ne" "Ka yi hakuri, ina camp ne zaka iya zuwa ka dauke ni, sai mu je na dubata" "Ba kai ki zan yi ba, ke zaki je ki dubata, duk abun da ake ciki sai ki fada min" Yana kaiwa nan ya kashe kansa wayar. "Matarka ce? Daman kana da mata?" Fatima ta tambaya tana shan ice cream. "Aa ba matata ba ce" "Toh kana son mata" Ya kalleta kawai yayi murmushi. "Kana son Momyna?" Ya sake yin murmushi. "Fatima zan tafi dake gidana na zauna a can mu huta kamin Momynki ta kira sai na maida ke" "Tohm" Taja motar suka kama hanya, tana ta masa surutu har suka isa gidan, a lokacin da ta fito motar ta kalli gidan ta ga babba ne sai ta ce. "Da zaka yarda sai mu dawo nan gidan tare da Momy da Chidimma, mu bar gidan Vito, ba za mu maka barna ba" Shi dai be ce mata komai ba ya bude motar ya dauko wasu daga cikin kayan da suka siyo ya wuce cikin gidan tana biye shi tana ta masa surutunta da fluent English dinta pure one domin bata iya hausa ba, duk wata magana da ake da ita da halshen turanci ne, hausa kadan ta iya saboda Emily bata damu ta koya mata ba, kuma bata taso a gurin da ake hausar sosai ba, ba kamar Emily ba. TASMIA POV. Da tufafinta na bautar kasa ta tafi gidan Emily fuskarta sanye da mask, bakin gate din aka ajeta, ta sallami mai okada sannan ta buga gate din mai gadin ya leko, sai ta masa karyar Emily ce ta kira ta da kanta tace tana son ganinta. "Idan ka shiga ka fada mata Tasmia tana waje" Mai gadin ya kira wayar Emily ga ji ta a kashe, sai ya shiga ciki ya kwankwansa Chidimma ta bude ya tambaya ko Emily ta san da zuwan wata kawarta, sai ta amsa masa da eh alhali bata da tabbaci. Mai gadin ya koma ya budewa Tasmia ta shigo, da yaren turanci ta tambaye Emily Chidimma ta nuna mata upstairs, har ta nufi saman sai kuma ta juyo ta saka tambayar Chidimma ko Vito yana nan Chidimma tace mata baya gidan sai ta haura sama da sauri jikinta na rawa, na dan tana son faranta ran Aliyu ba da kuma yi ma kanta yaki, da babu abin da zai saka ta risking rayuwarta a gidan Emily, kiranta kawai da Aliyu yayi a karan kansa ya faranta mata rai balle kuma har ya nemi alfarma a gurinta, a ganinta hakan ma wani matakin nasara ne, domin da sannu bako ke zama dan gida. Tsabar rikicewa ma dakin Fatima ta fara shiga, ta fito da sauri ta tura dayar kofar ta leka sannan ta shiga. Sautin kukan Emily ta fara ji kamin ta hango ta kwance a kasa, ta karasa da sauri. "Lafiya me ya same ki?" Ganin Tasmia ya saka Emily ta dan ji sanyi sanyi har ta dago ta jingina jikin Tasmia tana duka tana fada mata Vito ne ya duke ta. Tasmia ta kalli kofa sannan ta rage murya. "Me kika masa?" Emily ta kasa magana sai kuka take. Tasmia ta kalli yadda fuskarta ta yi ja wani gefen ya kumbura ga kuma shatin belt a saman kafadunta, kana gani ka san dukanta aka yi, kuma ko bata fada mata ba, ta sani ba zai wuce ace saboda Aliyu ba, shiyasa shi ma ya damu ya san halin da take ciki. "Wata kila ya gaji da halinki ne Emily ta ina zaki zauna kina wahalar da shi, bayan duk hallacin da yayi min? Ko da yake ban san me ya faru ba, amman kina cin amanar mutumen nan, yana sonki kin kasa fahimta" Emily ta takaita kukan da take ta share hawayenta. "Ya aka yi kika samu shigowa nan?" "Karya na yi ma mai gadi cewar kin san da zuwa, na ce ya zo ya tambaye ki sai yace na shigo kin san da zuwa" "Be shigo nan ba, ban yi magana da shi ba" Mamaki ya cika fuskar Tasmia. "Toh taya ya bar ni na shigo, ni daman dai na zo ne kawai na duba ki" Emily ta yi shiru alamar tunanin sannan tace. "Tashi ki tafi kar Vito ya tarar da ke a nan, ransa a bace yake" Emily na rufe baki Tasmia ta zabura tsaye ko sau anjima bata cewa Emily ba ta fice gidan fuuuu kamar walkiya. Hankali be kwanta ba sai da ta isa gida, sai kuwa aka yi a daidai tana shiga gidan kiran Aliyu na shigowa wayarta domin hankalinsa ya tafi gurin son sanin halin da Emily take ciki. "Hello" Ta amsa da far'arta kamar gaske. "Assalamu Alaikum" "Wa'alaikumussalam" Ta yi shiru tana jiran sai ya tambaye ta. "Lafiya take?" "Lafiya Kalau take na same ta ma girki take yi" "Vito na gidan ko da kika je?" "A A Baya gidan mai aikinta ce kawai shiyasa ban tsaya komai na ina ganin lafiyarta sai na fito, kar ya zo ya tarar da ni a samu matsala, ba dan kai ba a yanzu da babu abun da zai kai ni gidan Emily ko dan gudun fitina" "Me yasa wayarta take a kashe" "Toh ban sani ba, wata kila tana gudun a kira ne yana nan, amman lafiyarta kalau na same ta ma ta sha ado abunta" Idan be ce mata thank you ba ai be kyauta ba ko ba komai ta cancanci godiya domin hankalinsa zai kwnata a yanzu sanin cewar Emily na cikin aminci. "Na gode" "Always Aliyu, ka aje duk wani tunani da kake, ka dauke ni a matsayin kanwarka, bayan shi babu wani ba" Ba tare da ya sake furta komai ba ya kashe wayar. [6/20, 7:25 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* SARAC STARS. C - Pen... ✍️ FOLLOW ME ON 👇🏻 FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914 TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1 INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0 CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08 Page 3️⃣7️⃣ ALIYU POV. Ya dan ji wani iri shi dai aganinsa babu abun burgewa namiji ya tare da matar da a daura musu aure ba a gida daya da sunan budurwarsa ko wadda zai aura, hakan sai ya saka ya ji addinin musulunci ya kara burge shi domin addinin Musulunci be yarda da wannan ba, a ta dayan bangaren kuma yana tambayar kansa anyaba shi da zunubi na aje mata ya a nan a can kuma ya bata damar shakatawa da yi yadda take so da mutumen da ba muharraminta ba? Ya kalli Fatima dake ta ciye ciyen kayan dadinta hankali kwance. "Fatima mu tafi gida haka nan?" A take ta bata fuska. "No bana so mu tafi yanzu" Ya mike tsaye ya nufi Kitchen, ruwa ya dauko ya sha ya dawo falon ya zauna. "Kai ma baka da kowa kamar Momy na?" Ya dubeta. "Waya ce miki bata da kowa?" "Bata da kowa sai ni kadai" "Sai Vito" Ta girgiza masa kai. "Aa i hate him" "Why do you hate him? Me kake miki ne?" "Baya dariya, kuma yana da fada yana duka, kuma ba ya bari kowa ya zo gurinmu" "Toh mamanki tana da ni yanzu" "Yeehhhhhh" Sai yayi murmushi ya shafa kanta, sai ya ji duk ta burge shi. "Mun zama mu uku ko?" "Yes, zaka zama Babana? Ni kadai ce ba ni da Baba a duniyar nan kowa yana da Baba amman kace zaka maida sunana Fatima Aliyu amman baka yi ba, har yanxu ana kirana Fatima Aisha Emily...." "Ke ma kina da mahaifi Fatima, kuma na san da zai ganki zai kaunace ki sosai zaki ji dadi, da ace mahaifiyarki zata aje abun da ke zuciyarta ta dubi maslaharki da kin yi farinciki sosai, kina da uba sunanshi Turhan" Ta dafa shi, hakan ya farfado da shi daga guntun tunanin da yake. "Ka ji" Ya lumshe ya bude sannan ya daga taya matsa da ita saman jikinsa ya rumgume ta, ba dan ya ji abun da take tambayarsa ba sai dan tausayinta da ya kama shi. Kiran Emily be shigo wayarsa ba sai kusan Isha'i a lokacin da yayi alwala yana warwarar hannun rigarsa Fatima ta shigo masa da wayar da ya bari a falo, har dakin da yake ta mika masa. Ya karba ya kara a kunne, for the first time sai ya ji nauyi fara yi mata sallama. "Salam alaikum" Ta masa sallamar sai yayi murmushi ba tare da ya amsa ba ya ce. "Yau dai kina da nuna min hallayarki na kwarai ashe kin iya sallama" "Na iya mana, ni da na zauna da musulmai kuma Hausawa" "Kina lafiya Emily?" Ya tambaya, sai ta lumshe ido hawaye na sauko mata, ta girgiza kai kamar yana gabanta tana jin kamar ta fada masa ba lafiya ba, amman tana gudun abun da zai je ya dawo. "Anyways na kira wayarki a kashe, saboda hankali na be kwanta ba da yanayin da na barki, kuma da na ji wayar kashe na damu sai na saka Tasmia ta bincika min ke" Da ya kai iya nan sai ya yanke maganar saboda yana son ya gano idan Tasmia gaskiya ta fada masa ko akasin haka. Emily ta hade kukanta ba tare data bude ido ba ta ce. "Me tace maka?" "Me kika ce tace min?" "Ban fada mata komai ba, bata ma min maganarka ba" "Okay, ta fada min ta same ki kin yi ado kina yi ma Vito girki, nace toh ina nan na damu ita kuma tana can tana girki ma wanda ba mijinta ba, Allah yasa dai kar na samu zunubi" Ta cige baki hawaye na sauko mata kana ta bude ta sauke numfashi a hankali. "Ado tun wanda ka tarar na yi ne, ban sake wani ado ba, ina Fatima tana tare da kai" Ya kalli Fatima dake cin apple. "Yeah, amman Aisha na tambaye ki mana" "Uhmmm, ku haka addininku ya yardar ku zauna da mutane musamman namiji kuna tarayya ko daba muharraminku ba ne...? Mu a gurinmu hakan ba abu ne mai kyau ba" "Ban taba tarayya da Vito ba, wani abu be taba shiga tsakaninmu ba, a tsawon zaman da muka yi, yana jiran sai na aminta da soyayyarsa ne, ni kuma zuciyarta ta kasa fahimtarsa, wannan abun yana wahalar da rayuwata yana jefani a matsala, ni ban taba mu'amala da kowa ba sai Khaleepa da Turhan, shi ma Turhan ya fada min kan kuskure ne, kuma bakar rana ta biyu a gurinsa bayan ranar da aka daura mana aure, yana daga cikin dalilin da ya saka nake son gina rayuwata ni kadai ina son na zama mai ikon kaina" Jin cewar bata taba zina ba ya burge shi, haka kuma jin cewa Turhan ya kira ranar da ya aure da bakar rana a gurinsa ya saka shi kara dora ayar tambaya akan zamantakewar aurensu. "Fahimta, I'm sorry for misunderstanding you" "Dan Allah ka bar Fatima ta kwana a gurinka, gobe sai a kawota" "Okay" Ta bukataci hakan ne gudun kar ya zo kawo Fatima ya hadu da Vito ko kuma ya ga dukan da Vito yayi mata yace zai dauki mataki ya jefa kansa a matsala. Falo Fatima ta koma tana kallo, shi kuma ya tsaya a dakin yayi sallah, be dago daga sujudarsa ta karshe ba sai da yayi ma Emily addu'a, bayan ya gama ya sauko falon ya umarce tayi alwala ta yi sallah, ba musu ta tashi zuwa jnda ta yi alwalar magariba ta yi ta dawo falon ta dauki hijab din Kameela daya dauko mata a dazun ta saka ta fara sallah, shi kuma ya shiga Kitchen ya fara gyara tattasai da attarugu da albarba ya kunna gas ya dora nama akai, ya fara yanka vegetables, sai ga Fatima ta shigo Kitchen tana tambayar me yake yi. "Jallof zan girka kina ci?" "Ka iya girki?" "Sosai ma" Ita ta yi ta taya shi hira yana girkin, duk abun da ya zuba sai ya daga ta ta gani da ya gaji sai ya goyata a bayansa ta leko kanta ta saman wuyansa tana kallon yadda yake girki, idan yayi abun da bata saba gani ba sai tace masa ba a haka ake yi ba, shi dai dariya kawai yake ya cigaba, da ya gama hada komai sai ya koma tare da ita falon suka zauna sai da ya nuna sannan ya koma ya zubo musu a plate daya shi da ita. "Kai kadai zaka ci?" "Aa ni da ke" "A plate daya" "eh ko baki cin abinci a plate daya da wani?" Ta yi dariyar jindadi "A gida raba mana ake kowa plate dinsa dabam, amman ina so" Ya zauna ya sake komawa ya dauko ruwa da lemu, sannan yace ta zo su ci, madadin ta zauna a gefensa ko gabansa sai ta tsallake abinci ta zauna a kan ciyarsa, yana ganin haka sai ya aje Spoon daya ya dauki dayan yana ciyar da ita da shi shi ma sai ya ci, ko loma nawa yayi sai ta kirga tun be hankara ba har ya fara dariya, ita da shi suka ci abinci cikin nishadi, har wayarsa ya dauko yayi mata hoto yayi mata video, kusan a lokacin ne ya ji yana matukar kaunar samun nasa yaran, Fatima kuma ta yi enjoying moment din tana jinsa kamar mahaifinta. Bayan sun gama ya bude quran app din wayarsa ya tana karanta dan abun da ta iya yana mata gyara, har bachi ya dauke ta, daukar ta yayi ya haura da ita sama ya kwantar da ita kan gadonsa ya lullubeta ya zauna gafen gadon ya karanta mata addu'a ya tofa mata sai ta bude ido ta kalleshi. "Meyasa kake watsa min yawu" "Addu'a ce ta tsari idan aka karanta ma yara ko suka karanta babu abun da zai same su har safe, Momy ki bata miki idan zaki kwanga bachi?" "Aa" "Toh ki koya ki rika yi ma kanki kin ji?" Ta taso daga kwance da take ta rumgume shi. "Da nan nake zaune tare da momy da mun rika jindadi, kowa yana son ace yana da ba Baba, momy ta maka girma amman zamu iya zama yayanka mu duka biyu" Yayi murmushi ya shafa bayanta a haka ta sake yin bachi sai ya kwantar da ita ya fito falon, ya dauki wayarsa ya kira Mama Baraka, sai dai bata daga kiran nasa ba har ya yanke, aje wayar yayi a tunaninsa ta yi bachi domin tara da rabi har ta gota, yana dauke hannunsa daga mazaunin wayar sai ga kiranta ya biyo baya, sai ya sake dauka ya amsa, tare da sallama ta amsa masa suka gaisa sannan ta tambaye shi. "Aliyu me yake faruwa tsakaninka da matarka?" "Mama Me ta fada muku" "Bata fada mana komai ba, an yi anyi da ita ta ki ta yi magana ba, sai kuka da damuwa abinci ma bata iya ci, gaba daya ta fita hayyacinta" Yayi shiru na dan lokaci tare da tunanin alfanu da kuma rashin sa da zai haifar idan har ya fadi dalilin da ya saka ya turata gida, ba dan Ummynsa ba da babu abun da zai hana ya fadawa kowa abun da ta yi masa ko dan ta shiga taitaiyinta ta hankalta. "Babu komai Mama" "Aa mu fa iyayene, babu komai zaka turo ta gida ko sakinta ka yi?" "Aa" "Toh me ke faruwa tsakaninku? Aliyu ita rayuwar aure sai da hakuri na san ka yi ne, amman ka kara, na san idan ba kai ba ne ba zaka iya zama da Kameela ba, sai dai bana son kana duba sherinta ka rika duba alherinta ko dan ku bawa marasa da kunya, kaga yanzu dawowar da ta yi nan iyayen sun nuna babu ruwansu da ita yan'uwa kuma sai dariya suke mata, dan Allah ina rokon alfarma Aliyu ba dan na isa ba, sai dan na san ka da biyayya da kawar da ido da kuma hakuri da tunani, dan Allah ka yi hakuri ka zo ko kuma ka aiko daukar maka matarka ka bata hakuri ka bawa iyayenta, ku shirya tsakaninku" Ya sauke ajiyar zuciya. "Shikenan zan yi tunani Mama" "Aa ba tunani nake son ka yi ba, idan ka tsaya tunani ai sai shedan ya samu damar baka wata gugurwar shawara, domin shi kullum burinsa ya lalata rayuwar aure, dan Allah ya shirya cikin weekend din nan ka zo ka dauki matarka, gobe friday zuwa assabar ko lahadi sai ka shigo ka koma, ka turo min number Mahaifiyarka na kira ita ma na bata hakuri" "Aa ba sai kin kira ba, bata ma san abun da ya faru tsakaninmu ba" "Tohm ai haka ake so, ana son ma'aurata su zama masu sirri, Allah ya hada kanku ya baka hakuri da wuyan dauka, kuma maganar nan ta tsaya daga ni sai kai dan Allah, domin Kameela da iyayenta ba su san na kira ba, ni ce kawai na damu da halin data shiga shiyasa na kiraka mu yi magana, number ka ma a boye nasa yara suka dauko min, ba tare da sanin Kameela ko iyayenta ba" "Na gode Mama" "Toh Allah ya maka albarka, kuma ka kara hakuri domin matarka tana kaunarka sosai" "In Shaa Allahu" "Na gode" Ya sauke wayar, ya amsa mata ne kawai saboda yana jin nauyin ce mata aa ba zai iya ba, haka kuma yana tsoron matsalar da fadin gaskiyar abun da Kameela ta yi masa zai janyo, ita yake tausayi ba kansa ba, domin ya san tana son shi, kuma ya san irin gwagwarmayar da suka sha kamin aure, kana ya san idan har aka ji abun da ta yi abu ne mai wahala wani namiji ya sake aurenta, shi kansa ya san auren Kameela jarabawa ne a gurinsa ba dan baya kaunarta ba sai dan zafin kishinta da kuma halin da take kokarin jefashi kuma ta jefa kanta. EMILY POV. Bata farka ba sai karfe takwas na safe, saboda tunani da kuma dukan da Vito yayi mata be barta ta sami bachi da wuri ba, daker ta iya saukowa daga kan gado saboda tsamin da jikinta yayi ko'ina ciwo yake mata. Bathroom ta fara shiga ta wanke bakinta ta yi wanka da ruwa mai zafi sosai saboda ta gasa jikin sannan ta fito daure da tawul, rass gabanta ya yanke ya fadi ganin Vito tsaye a dakin yana jiran fitowarta. Tsayawa ta yi cak a jikin kofar bata karasa fita ba kuma bata koma ciki ba sai kallonsa take. "Good Morning" Ya tako zuwa inda take sai ta yi baya baya zata koma ciki, ta bata fuska sosai alamar zata yi kuka. "Tsorona kike ji? I'm so sorry i didn't mean to hurt you ke kika janyo, jiya ban yi bachi ba saboda tunanin abun da na yi miki" Ya karasa ya rikota ya fito da ita sai ya rumgume ta a kirjinsa. "I'm sorry" Sun dade a haka kamin ta dago daga jikinsa ta nufi kujera ta zauna. "Jikinki da zafi zan kira Likita ya zo ya duba ki" "Bana bukata" "I'm sorry Emily am sorry" Ya karasa kusa da ita sai ya zauna a kasa ya kama hannunta ya rike. "I'm really sorry, zuciya ce ta rufe ni" "Wannan ba shi ne karon farko ba" "Na sani, kuma ba zai zama karon karshe ba matukar baki daina kula wasu mazan ba, kuma baki cire ranki akan addinin nan ba" Ta fisge hannunta daga rikon da yayi mata ta mika tsaye, short gown ta dauko ta saka ta daure kanta da ribbon tana kokarin juyowa ta ji shi bayanta tsaye. "I'm sorry Emily I'm sorry, i didn't mean to hurt you" Ya juyo da ita yana kallon fuskarta dake zubar da hawaye. "But you already hurt me, baka da banbanci da Khaleefa shi ma dukana yake, Turhan ma ya dukene, kowanenku yana juyani ne son ransa, idan kuka gaji da ni sai ku watsar, ina ta fadawa hannun mutanenda babu komai a gabansu sai son zuciya, na tabbatar da ace ni kanwarka ce, ba zaka yarda wani yayi mata wannan dukan ba, jiya ban iya bachi da wuri ba saboda radadin dukan da ka yi min, takamarka kawai saboda ina karkashinka ne, saboda kana ganin ba ni da kowa, da ace ina da gata ba zaka min wannan dukan ba Vito" Ta wuce shi ta fice daga dakin, zaunawa yayi a kujerar data tashi dazun ya dafe kansa, babu abun da ya tsana kamar ganin hawayen Emily, a yau da ace wani ne yayi mata abun da yayi ba zai kwana duniya ba, but still yana jin babu dadi meyasa ba shi da hakuri why yake da saurin hannu? Yana son Emily yana mutuwar sonta yana kishinta wannan ne abun ne ya ci shi da yaki ya gagara fin karfin zuciyarsa har gobe... Tana fita dakin ta nufi downstairs, sai kuma ta fasa sauka ta dawo saman ta nufi dakin London ta shiga, saboda tana bukatar gurin da zata kebe ta tausayawa kanta. Sai dai kuma shiga dakin ya dawo mata da tunanin danta da kewarsa, dakin yana nan yadda ya bar shi babu abun da aka cire ko aka sauya, sai datti da yayi domin Chidimma ta daina share dakin. Kwalliyar dakin ta fara kallo sannan ta sauke idonta gurin hotonsa ta karasa gurin gadon ta zauna a kasa ta dora kanta akan gadon tana hawaye. Can kuma ta dago tana kallon study table dinsa dake gefe daya, ta tashi ta koma kan teburin ta zauna saman kujera tana duba takardun da yake zane da su da rubutu, wani gurin ya zana ta ya zana kansa da Vito da Fatima da Chidimma ya rubuta sunan kowa, ta kai hannu tana shafa zanen, ta bude wasu takardu ta dauko tana dubawa, wani gurin ya rubuta, na yi fushi wani gurin ya rubuta i hate Momy, wani gurin ya rubuta I'm sick har ta kai gurin da ya rubuta. "Chidimma tace Momy bata so na, bata so na bata so na bata so na, tana son Fatima Fatima bata son London, Chidimma tace Momy bata son London, Momy bata son London Momy ta tsani London" Tana karantawa hawaye na sauko mata kamar ruwa, ta girgiza kai da sauri. "Ina son ka dana, ka fi soyuwa a raina fiye da Fatima, baka fahimce ni ba ne" Ta kwala wani uban ihu cikin kuka, ta mike tsaye da fito dakin da gudu kamin ta sauka kasa Vito ya fito dakinta ya biyo bayanta Chidimma dake mopping ma ta tsaya tana kallon Emily dake saukowa tana kuka rike da takardun. "Meyasa kika saka dana ya tsane ne? Me na miki? Me yasa kika tsane ni? Me na miki?

Chapter 30 of 63