kura min ido har na zubar da abun da na yi wahalar tafiya can wata unguwa nesa na siyo”
Nan din ma dai be jin magana ta zame masa dole dan haka ya adana kalamansa ya kalli gurin da ya bace kawai ya dauke kansa, his mind is somewhere else shi dai jin yake kamar ya taba ganinta, and he won't lie tana da masifar kyau, ta ko'ina ta kai mace, shiyasa William ya rikice jiya yana ta masa santinta. Suna isa four floor ta Elevator ya bude sai ta fita suna hada ido ta watsa masa masa wani kallo na jin haushi wanda ya fi kama da harara. Ya dauke idonsa da sauri ta har Elevator ya rufe, number 5 ya taba, ya ciro wayarsa ya kira Turhan.
“Hello Aleeyou”
Turhan ya fada da dan sautin labarancinsa kadan.
“Turhan, yarinyar nan da kake nema fara ce sosai?”
“Eh fara ce, tana da jan gashi, da blue eyes and tana kiba”
Kibar da Turhan ya fada ya saka Aliyu kwankwanto, domin ita dai wannan da ya hadu da ita daga jiya zuwa yau siririya ce.
“Tana da masifa?”
“No bata da fada ko kadan, tana da tsoro idan ma aka mata fada sai dai ta yi kuka ba zata iya maida magana ba”
“Okay, sunanta Aisha ko?”
“Eh bata da wani suna bayan wannan?”
“Ba zata rasa ba, amman na manta sai na bincika Ammy ko zata fada min”
“Ta yi dogon boko ne?”
“No bana jin ma ta gama Secondary School, ba wai na san komai ne akanta ba, amman dai zan bincika, me ya faru?”
Aliyu ya amsa masa yana ficewa daga Elevator.
“No na tambaya ne kawai saboda na taya ka nema”
“Na gode sosai Aleeyou, yau zan tafi Lagos din In Shaa Allahu, ka taya ni addu'ar Allah yasa na dace, ga matsalar masarautarmu, ga matsalar Matata ga matsalar neman yarinyar nan”
“Karka damu komai zai wuce, ita haihuwa ai lokaci ne, ita kuma za a same ta In Sha Allahu”
“Ina fatan haka”
“Okay bye Allah bada sa'a”
Ya sauke wayar yayinda yake tura office din farko ya shiga.
“Good Morning Sir”
“Morning Nick. Please inform Michael to notify our new staff members that buying food during working hours within the company premises is not allowed. They can only do so either before work begins or after closing hours, as it seems they are not familiar with our rules.
Also, remind them to sign in when they arrive and sign out when they leave”
“Okay Sir”
Ya amsa yana dan sirinawa alamar girmamawa, sai da Aliyu ya shiga office dinsa sannan Nick ya zauna ya fara cika umarnin boss dinsa da System kamar yadda aka saba, duk wani abu da za'ayi a cikin kamfanin sai dai a tura ta email, sai idan uzuri ne ko kuma wani abu ne da ya shafi mutum personally sannan ake amfani da Telphone din da aka tanadar a kowane Office.
_______
Allah yasa Aliyu ya cika alkawarin da ya dauka, domin maza sai Allah.
Anya idan Vito ya san kudurin Emily na guje duk wani abu nasa zai barta kuwa?
Kuna ganin Emily zata iya jure aiki a karkashin Amal kuwa?
Shin Turhan zai yi nasara idan ya tafi Lagos neman Aisha?
[4/20, 9:58 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
Page 6️⃣
Sai da ta sauke numfashi sannan ta tura kofar office din ta shiga, ta manta da dokar Amal na neman izini kamin shiga.
A gaban teburinta ta dora mata abun da ta siyo sannan taja ta tsaya tana jiran Amal ta gama wayar da ta shigo ta same tana yi.
Sai da Amal ta gama wayar sannan ta kalleta a fusace.
“Wai ke kam baki da tunani ne ko kuma dai rainin wayo ne yayi miki yawa? Zuwanki na farko na miki gargadin shigo min office ba tare da neman izini ba amman baki ji ba ko? Ke ba yarinya ba balle ace za'ayi ta maimaita magana”
Emily ta kalleta da kyau tana jin babu dadi domin matar dake zaune a gabanta tana mata fada bata wuce sa'arta ba, amman take kokarin wulakantata saboda kawai tana aiki a karkashinta.
“I'm sorry na manta ne, zan kiyaye next time”
“Better”
Cewar Amal tana daga bubble tea din da ya zube.
“Shayewa kika yi?”
“No zubewa yayi by mistake”
“To zan fada a cire min a cikin albashinki, yanzu kuma je ki siyo min wani”
“Okay”
Emily ta amsa mata sannan ta juya ta fice jiki a sanyaye, cikin rashin jindadi da kasala ta sauka kasa ta sake komawa gurin dazun ta siyo mata wani bubble tea din ta dawo ta hauro sama ta yi knocking ta jira har sai da ta yi mata izini sannan ta tura ta shiga.
Saman teburinta ta dora mata tare da atm dinta sannan ta juyo ba tare da tace mata komai ba zata fice sai Amal ta kirata.
“Hey”
Emily ta juyo ba tare da tace komai ba, Amal ta nuna mata tulun takardun da suke zube kasa a gafen teburin.
“Ki dauki wannan ki je ki yi typing dinsu, a yadda kika gansu a papers idan kin gama ki turo min ta email dina”
“Okay”
In short sannan ta nufi tulun takardun ta dauka ta fice daga office din zuwa nata Office din, Widows din office din ta bude tana kallon titi da kasan building din, hutun minti goma ta yi sannan ta juyo ta zauna a kujerarta ta bude system din ta fara typing tana murmushi kamar ba ita ce ta gama bacin rai a dazun ba.
Sai dai abun da baka saba ba, yana da wuyar aiwatarwa musamman a karon farko, bata jima tana yi ba ta fara gajiya, haka dai ta daure ta cigaba da typing har azahar.
Bata bar office dinta ba sai 4pm domin bata yarda ta fito ba sai da ta tabbatar ta gama komai, ko da ta fito kusan wasu sun dade ta tafiya gida, few mutane ne suka rage irinta sai kuma ma'aikatan dake gyara kamfanin. Bata samu Taxi ba dan haka ta hau okada ya kaita gida, bayan ta biya shi ta kwankwasa gate din mai gadin ya bude mata ta shiga ciki cike da gajiya, jakarta kawai ta jefar ta shiga kitchen, lunch da Chidimma ta aje mata ta dauka ta fito falo ta fara ci da sauri saboda yunwa.
“Anya zan iya aikin nan? Haka aikin yake ko kuma dai...”
Sai kuma ta yi shiru ba tare da ta karasa ba ta cigaba da cin abinci, a gurin da ta ci abincin a gurin ta kwanta ta fara bachin wahala da gajiya bata farka ba sai Magariba.
“Momy...”
Ta bude idonta daker domin bachin be isheta ba, ta kalli yarta.
“Fatima”
“Momy yau kin kwanta da wuri”
Ta tashi zaune tana murmushi sai a lokacin ta tuna da yaran domin gajiya ta saka ta manta da su.
“Ina kuka tafi?”
Chimdimma ta tafi da mu park daga can muka je gidansu. Emily ta kalli Chidimma dake tsaye.
“Baki fada min ba”
“Yes saboda Oga ya zo bayan kin fita yace na rika fita da su, saboda baki da lokacinsu yanzu kar ya zama suna kadaici a gida, musamman Londom da yake ba lafiyayyen ba”
“Okay amman daga yanzu, karki sake fita da yarana ba tare da kin fada min ba”
“I'm sorry Maa”
Emily ta mike tsaye ta nufi gurin da danta yake tsaye kusa da Chidimma ta risina tana shafa fuskarsa.
“My Baby how is your day”
Ya mata murmushi kawai ya cire hannunta a fuskarshi. Chidimma ta saki hannunsa
“Sai da safe ranki ya dade”
Emily ta fahimci Chidimma fushi ta yi dan haka ba ta dakatar da ita daga tafiya ba.
“Ba zaki karanta mana story book ba?”
Fadima ta tambaya. Sai mahaifiyarta ta amsa mata.
“Zan karanta muku, ina da labari mai dadi da zan baku, and zan girka muku dinner mai dadi”
Tana maganar tana rawa da kai tana murmushi, a take farinciki ya cika fuskarsu, yadda ta fada haka ta aiwatar, tana girka musu abinci tana fada musu yadda ta sha wahalar aiki yau.
“Ma'aikatar ana aiki da yawa ne Momy?”
Fatima ta tambaya tana cin abinc.
“Ina tunanin haka, amman akwai wahala wata zan saba zuwa gaba”
Ta busar da iskar bakinta, tana shafa kanta.
“Momy can i ask you something?”
“Yes My Love”
“Me yasa ake sunana ya kasance Fadima Aisha Emily, not Fadima Hamza like London”
A take Emily ta ji wani kunci da bacin rai ya tunkarota da kamar fada ta ce.
“Again? Ina tunanin mun gama wannan maganar tuntuni?”
“Momy kowa yana using sunan babanshi, amman ni sai dai na yi using sunanki? Why? Even London ana kiransa London Hamza, why not London Aisha Emily?”
Emily ta aje spoon din dake hannunta ta mike tsaye.
“Time to bed”
“I need to know Mom kullum yan makarantarmu sai sun min dariya, Yau ma da nafi gidansu Chidimma an tambaye ni sunana na ce Fadima Aisha Emily sun min dariya”
“Ba na sha fada miki ba ki da Baba ba?”
“London me yasa yake da Baba, Me yasa ake ce masa London Hamza?”
“How many time do i have to told you Babansa ya mutu, ke kuma ban haife ki da ubana ba, haka nan na haife ki”
“But-”
“But, if you ask me one more Question zan doke ki da daren nan”
Ta fada mata a tsawace.
“But kin taba cewa Babana musulmi ne, amman ban taba jin sunansa ba”
Da sauri Emily ta bar dinning din domin ta san idan ta kara minti daya a gurin zata doki Fatima ne, gidan ya rikice mata domin tun a yanzu London ya fara rikicewa yana kuka. Dakinta ta shiga ta zauna bakin gado ta rike kanta tana shafa goshinta a hankali idonta a rufe sai numfashi take maidawa da karfi. Ta kwashe minti talatin a haka sannan ta mike tsaye ta cire rigar jikinta ta shiga bathroom ta yi wanka ta fito ta saka fajamas sannan ta sake dawowa falon ta nufi London da har lokacin kuka yake ta rumgume shi.
“Ya isa haka ya isa haka gani a nan”
Jikinsa yayi zafi sosai alamar fever, rage tsayi ta yi ta dago shi daga jikinta ta kalleshi.
“London saurareni, kukan ya isa haka kaga jikinka ya fara zafi, Fatima London yayi wasa da ruwa?”
Fatima ta juyar da kai ta rumgume hannayenta ta turo baki gaba tana cigaba da kallon tv ta ba tare da ta amsa mata ba, ita ala dole fushi take.
“Fatima I'm talking to you...!”
Emily ta daka mata tsawa har sai da London din ya zabura ya kara fashewa da kuka.
“Yayi wasa da ruwa”
Ta amsa mata a dikile sannan ta mike tsaye ta haura sama tana wani halba kafa kamar wata babba. Emily ta rumgume London tana jin kamar ta fashe da kuka, domin babu abun da yake firgitata a yanzu kamar rashin danta, He's not just an autisms yana fama da sickle tana yawan tashin masa lokaci zuwa lokaci, abu kadan yana iya saka ciwon nasa tashi, kusan ta fi wahalar da shi fiye da Autisms domin yana a cikin jikinsa ya zama rayuwarsa da hallintarsa ce a haka, wannan kuma a cikin jininsa take.
Daukarsa ta yi ta koma saman cushion ta zauna tana rumgume da shi tana juyawa a hankali, kamin ta aje shi ta tashi ta haura sama ta shiga dakinsa, maganin ta dauko ta sauko ta bude ta bashi sannan ta tallaba shi daker ta haura sama, suna shiga dakinta ya fara kwara amai a jikin sai ta sauke shi da sauri ta rike shi. A nan fa hankalinta ya tashi da sauri ta sake shi ta nufi gurin da ta adana keys din motarta ta dauka da nufo shi ta dauke shi saman duk wani nauyinsa sai ta daina jinsa a lokacin. Kamar ba ita ba haka ta saukowa downstairs din da sauri ta nufi kofar falon ta bude ta shimfidashi a balcony ta nufi gurin da jerin motocin uku na gidan suke ta matsa remote din hannunta domin gane keys din wace motar ce ta dauko.
Sai da ta fito da motar sannan ta nufo shi ta dauke shi har lokacin amai yake ta saka shi motar, gaba daya ta gama fita hayyacinta, ko kadan bata son wani abu ya sami yaranta sai take ganin zata ragu ne, domin a halin yanzu bata da wasu family bayan Fatima sa London, kuma ta tabbatar ba zata sami wasu ba, domin alkawarin da ta daukarwa kanta abu ne da take jin babu wani abu da ya isa ya saka zuciyarta kusantar kofar da zata karyashi.
Yadda ta ja motar ta fice daga gidan kai kace koyon tuki take bata kware ba, domin jikinta rawa yake ta ko'ina irin rawar nan na wanda ke tsoron faruwar wani abu, each and every second sai ta juya ta kalli danta dake gidan baya tana kiran sunansa, kamin ta isa asibitin gaba daya ta fita hayyacinta, domin bata taba ganin danta yayi amai mai yawa haka kamar yau ba. Babbar asibitin kudi ce da aka saba kwantar da London a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, ba London kadai ba har Fatima da ita kanta Vito ya dauki nauyin a duba su asibitin ta kudi.
Ta karbi kati shiga asibitin suka duba bayan motarta sannan ta tuka da karfi ta isa Emergency ta fito a firgice ta tare da ta kashe motar ba haka kuma tashin hankali be barta ta rufe motar ba, ta bude back seat da sauri ta fara janyo danta sai ta ji karfinta ya kare ta gagara fitowa da shi, sai kawai ta fashe da kuka ta saka ihu, securities din da suke tsaye a emergency din suka nufota da sauri suka fito da London da har lokacin amai yake ta shekawa. Nurse suka fito da gado aka dora shi.
“Dan Allah ku taimaka min kar ya mutu, ku taimaka kar ya mutu”
Shi ne abun da take ta fada da halshe Ibo tana kuka ta bi bayansu, daya daga cikin security ne ya shiga motarsa ya faka a gurin da aka tana domin aje motoci, ya shiga mata da key din. Tana ta zarya ta kasa tsaye ta kasa zaune, kafarta babu talkami kanta a yamutsa fajamas din dake jikinta ma kadan wandon ya wuce mazaunanta be gama sauka a cinyarta ba, rigar kuma bata da kauri sosai. Kusan kowace fatar jikinta a bude take, ban da kirjinta zuwa kasan cibiyarta.
“Ga keys din motarki”
Ta kalli key din sannan ta karba ta rike ta cigaba da zirya kafarta babu talkami, kana kallonta kasan a firgice take, hankalinta kuma be kwanta ba sai da London ya samu saukin aman da yake yayi bachi a dakin da aka sauke shi, Likitan da ya karbe shi ya kalleta yana murmushi.
“Da sauki ma fa sosai kawai ke ce kika daga hankalinki”
“Be saka yin amai irin wannan mai yawa ba, kuma zafin jikinsa ya wuce kima”
Ta fada hawaye na sauko mata.
“Eh amman da sauki sosai, kuma ina son na baki shawara ya kamata ace kuna da likitan dake zuwa yana duba shi akai akai, kin ga kamar irin yanzu, da ace akwai likitan dake duba shi ba sai kin yi wahalar zuwa ba, sai idan abun ya gagara, yana da ki samu likitan da zai duba shi koda yaushe, yadda kike daga hankalinki wata rana ba zaki iya kawoshi asibiti ba”
Ta daga masa kai, sai ya daga kafadarta alamar karfafa guiwa ya wuce, ita kanta zata so ace akwai likitan dake duba danta duk lokaci, sai dai tasan Vito ba zai yarda ba, domin baya yarda da kowa ya shiga gidanta balle kuma rayuwarta ko ta yaranta, ta yi ta kokarin yin haka yin haka ba sau daya ba amman be amince mata ba. Ta shiga dakin ta rufe kofar a hankali ta karasa kusa da shi tana kallon fuskarsa.
Rayuwarta take tunawa a wani dare makamancin wannan da rashin lafiya ta kamata, ita kan ta fishi wahala kwananta uku tana ciwon ciki kamin akaita asibitin, sai kuma aka rasa mai jinyarta domin bata da kowa sai gamon tsintsiya da ragga wato mutanen da aka raine ta a tare da su a gidan marayu.
Ta zauna a kujerar dake kusa da gadonta ta kama hannunsa ta rike, jininta ne wannan shi ne kadai zata iya shaidawa duniya cewar ita din daga gareta yake, kuma shi din nata ne, bayan wannan da kanwarsa bata da wani abun tunkaho, da ace ta rasa shi a yau da daren yau ya fi kowane dare muni a gareta. Hannu ta saka ta share hawayen idonta tana tunanin Fatima ta san zata ji tsoron zama ita kadai a gidan gashi bata fito da waya ba balle ta kira Chidimma tace ta shiga ta kwana tare da ita, haka kuma ba zata iya barin ďanta shi kadai a irin wannan lokacin da bata san karfe nawa ba ta tafi gida.
Bachi rabi da rabi ta yi saboda tunanin Fatima, da kuma danta dake tsare da shi, sanyin asuba na fara saukowa ta mike tsaye daga kan kujerar yana mika, kamin ta sirina ta sumbanci danta dake bachi ta shafa kansa zuwa fuskarsa, tana matukar tausayin rayuwarsa saboda yadda tasa kaddarar ta zo, shi din ba kamar sauran yara ba ne, gashi kuma ciwon sickle be barshi yayi walwala ba. Ta dago ta nufi kofar ta bude a hankali ta fice ta rufe, haka ta taka har gurin motarta babu talkamin domin bata zo da su ba, sai da ta yi ta dubawa sannan ta gane gurin da aka aje mata motar.
Ta tuka motar cikin natsuwa ta isa gida, sai dai ta yi horn ya kai goma kamin mai gadin ya taso ya bude mata, ta faka a gurin da ta dauki motar ta bude ta fito tana amsa tambayar jikin London da mai gadin yake domin ya ga yadda aka fita da shi.
“Ya ji sauki”
Ta amsa a gajiye sannan ta nufi cikin gidan ta bude ta shiga, sama ta haura da sauri ta shiga dakin Fatima, ba karamin dadi ta ji ba ganin Chidimma na rumgume da ita suna bachi, ta yi murmushi kadan sannan ta juya ta fice daga dakin ta shiga nata dakin, tufafin jikinta ta cire ta shiga bandaki ta yi wanka ta fito daure da bathrobe ta daure kanta da tawul.
Kitchen ta nufa tana hamma ta kunna gas ta shirya abun karyawa, sannan ta fito a daidai lokacin da Chidimma ta sauko kasa.
“Good Morning Maa”
“Morning Chi”
“I'm sorry na kwana a nan ne saboda Fatima ta same ni tana ta kuka wai ba zata iya kwana ita kadai ba”
“Kin kyauta na jidadin haka, ga abun karyawa nan na shirya ki shirya yanzu ki tafi asibiti gurin London, saboda zan tafi gurin aiki yanzu, ki fadawa direban Fatima idan ya daukota daga school ya kirani zan fada masa inda nake aiki sai ya kaita saboda kar dawainiyar ta miki yawa, idan na tashi zan biyo asibitin idan sun ba mu sallama sai mu dawo tare”
“Okay Maa”
Emily ta ratsa gafenta ta haura sama, cikin kankanen lokaci ta shirya ta fito dakinta ta leka dakin Fatima sai ta same ta a bandaki tana wanke bakinta
“Good Morning My Love”
Fatima ta juyar da fuska, cikin rashin jindadin abun da ta yi Emily tace
“Idan kin tashi daga School ki fadawa direbanki ya kira ni, zai kawo ki gurin da nake aiki idan ban tashi ba a lokacin, saboda Chidimma zata tafi asibiti gurin London, ni kuma zan tafi aiki”
Tana fadar hakan ta ja mata kofar bandakin ta rufe ta fito daga dakin ta sauko kasa tana jin zuciyarta na mata babu dadi, ta karasa dinning wayarta na ringing a karo na uku, tea ta zuba ta daga cup din ta sha rabi sannan ta nufi kofar falon ta bude ta fice.
A road din unguwarsu ta amsa kiran Vito dake ta shigowa wayarta, ta sani ba dan baya garin ba da yanzu ya karaso gidanta, domin a ka'ida idan yayi mata kira uku bata daga ba to ba zai yi na hudu ba, zata ganshi gidan ne.
“Hello”
“Are you okay? Lafiya kike?”
Ta ji kamar ta ce masa aa ina cikin damuwa kuma ta fada masa London yana asibiti amman bata son daga masa hankali, haka kuma bata son yana shiga al'amurranta kokarin jenye shi take daga jikinta.
“Yeah I'm fine”
Dakikun da ta dauka bata ba shi amsa ba ya saka shi fahimtar tana cikin damuwa, daman kuma ya karanci muryarta.
“Don't lie to me, me ya faru bayan bana nan?”
“Fatima ce kawai bata jin magana”
Yayi shiru ba tare da ya ce komai ba, sannan ya kashe wayar, ita kuma ta sauke ajiyar zuciya ta tari okada ta hau ta, be sauketa ko'ina ba sai gurin aikinta.
ALIYU POV.
8:36pm...
Gaba daya yanayinsa ya canja zuciyarta ta sosu kuma ransa ya bace sosai saboda abun da yayi arba da shi a wayar matarsa. Sai dai a cikin sharudansa akwai kokarin kwantar da hankali da kuma yin uzuri a duk lokacin da wani abun bacin rai ko tashin hankali ya same shi, ya sani ya dara matarsa Aisha Ilmi da goge, kamar yadda ya fita shekaru haka ya fita hankali da zurfin tunani domin hankalin namiji ba daya yake da na mace ba. Ba da'asar bace bincikar wayar matarsa domin ya yarda da ita 100% ko da yake ita bata yi masa irin wannan yarda ba saboda kishi, a duk lokacin da ta samu dama sai ta bincike wayarsa, sai dai tana daga masa kafa domin bata taba daukar wayarsa ta bincika ta same shi yana chatting da mata ba, ko wani abu makamancin wannan, abu ne da ya daukarwa kanta nisanta wayarsa da duk wani abu da zai dauki hankalinsa daga matarsa a lokacin da tafi bukatarsa a kusa da ita. Ya haddace password din wayarta, ita ma ta haddace masa saboda yarda da suka yi da junansu.
Ya aje wayar yana kokarin saita kansa, domin be kamata ya nuna mata bacin ransa a yanzu ba, ko ba komai tana dauke da juna biyu zata iya damuwa, haka kuma ba zama lallai abun da yayi arba da shi a wayarta ya zama wata illa ko laifi a idonta ba. Ta kalleshi bayan ta sallame sallar Isha'i tana murmushi.
“Ki yi min addu'a”
“Ai kullum ina maka addu'a amman cewa nake Allah yasa daga ni babu kari”
Ya daga kafadunsa yana murmushi mai sauti.
“Daman ai daga ke babu kari, wai baki yarda da alkawarin da na yi miki ba?”
“Na yarda mana, amman matan yanzu fa shaidanu ne, kai dai Allah dai ya tsare kawai kuma ya kawar da idonka”
“Ameen”
Ya girgiza kai ya kai hannu ya dauki dabinon ajwa ya kai bakinsa, sai da ta kammala addu'ar sannan ta dawo kusa da shi ta zauna ta cire hijab din. Janta yayi a hankali ya kwantar jikinsa.
“My one and only ina bukatar tuna miki wani abu, kuma ina son ki dauke shi serious”
Ta dago kadan ta kalleshi.
“Minene?”
“Sirrinmu sirrinmu ne, be kamata wani ya ji ba, musamman na auratayya, yadda muke mu'amala da duk wani abu da ya shafi gonarmu be kamata wani ya sani ba”
Gabanta ya fadi, domin ta fahimci kalamansa sai dai kunya irin na wanda aka tsinkawa zane a kasuwa ba zai barta ta nuna masa ta fahimci nufinsa ba.
“Ni bana gane yarenka ka fito fili ka fada min abun da kake nufi”
Ya tashi zaune da kyau ya fuskanceta.
“I'm sorry na shi whatsapp dinki na san be kamata na shiga ba wata kila akwai sirrinki da yan'uwanki da be kamata na ji ba ko na sani, akan hakan ina baki hakuri, wani sako ya shigo ta sama kuma na bude na gani, wata kila saboda na samu damar tunatarki me Allah ya nuna min sakon”
“Kana ta jan sakon da tsaye please minene?”
Ya aje numfashi a hankali.
“Na ga wani chat da kike da kawarki Huda, ban san iya aminci ko yardar dake tsakaninku ba, amman Aisha ban jidadin yadda kike fada mata sirrin shimfidarmu ba, ko a musulunci babu kyau, kuma maganganun ne da basu dace ba”
Ta dan wara ido tana murmushin da ya kusa zame mata dariya.
“Haba dai, wannan fa duk zancenmu ne na mata, kuma ita da ba ganinka take ba ma”
“Ko dai minene tun da kika ga musulunci ya hana be
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 63