kulawar yayanta, a yanzu ke kina karkashin kulawar iyayenki ne, daga lokacin da kika ce ke zaki yankewa kanki hukuncin ba tare da neman izinin miji ko iyaye ba, to kin jefa kanki a matsala kenan, kuma raina iyaye a zauna lafiya, karki yarda zuciyarki ta raya miki wani abu akan Mama Baraka, ita uwace duk yadda ta zo sai dai ki yi hakuri da ita ki yi mata biyayya ki samu aljanna, ke da yanzu Allah ya cika miki burinki? Ga iyaye ga yan'uwa? To me ya rage? Sai idan miji ko?"
Ta yi murmushi tana fahimta ko wane harafi na bayaninsa.
"Gwanin Hikima, shiyasa na yi alkawari indai har zan sake aure ba zan auri kowane namiji ba sai mai irin sifofi da halinka"
Ya bude ido.
"Allah ko?"
"Uhmm"
"Ki ce kawai idan namiji yana da irin halina ya shigo za a bude masa kofa.
"Aa fa, kai tsaye ba sai ya kasance kuma yana da irin sunanka"
Ya dauke kai yana murmushin da ya bayyana hakoransa, ita ma ta yi murmushi ta yi kasa da kanta tana wasa da yatsunta can kuma ta dago tana masa wani kallo mai tafiya ta zuciya.
"To ni wane hali ne da ni haka? Har Gimbiya da kanta tace ba zata zo kowane Yarima ba sai mai dabi'un wazirinta?"
"Ba waziri ba ne, Sarki ne, na birnin wata zuciya da ta dade da jefar da kowa da komai ta shiryawa karbar kowane kalar yaki, ta yarda ta jure ko wane mashi da hakura da tsuka, da Gwarzon ya bayyana a cikin gonarta, sai ya nome duk wata ciyawa dake hana ta sukuni, har ta kai ganin sawun dokinsa kadai ya wadatar da ita da farinciki, da ya yaye komai sai ya maida zuciyar fara da taushi kamar auduga"
"Idan kuma Jarumin ya kasance ba shi da sunana fa?"
"Sai jarumar ta kasance a raye babu igiyar aure"
"Ai mace bata iya rayuwa sai da ABOKIN RAYUWA"
Ta yi murmushi kawai ta sauke kanta kasa, shi ma yayi shiru na tsawon lokaci kowane yana nazarin dan'uwansa.
"A cikin idonki akwai wani haske dake hana mai kallonsu hango abun da ke ciki, balle ya hango ajiyar da ake, mai tafiyar yana wasiwasi, ya wuce ciki ko ya tsaya a inda aka ba shi masauki?"
"Idan idanuwan suna da raunin hango zahiri, to abar zukata su yi aikinsu mana, ba mu isa mu hana su karasa abun da suka fara ba, na gode da karatun yau"
Ta mike tsaye ta fara tafiya.
"Wai likitan yana tsoron ko zuciyar bata warke ba ne, kar garin dinki liki ya sake sabon tsagi"
Ya fada ba tare da ya juya ya kalleta ba domin shi ya bawa kofar shiga falon baya ne. Sai ta juyo ta kalleshi.
"Wai sadaukin da furucinsa kadai ya shafe duk wani tabo dake zuciya ta zama sabuwa, shi ne kuma yake tsoron tara hannu ya rike ta daga faduwa? Ko dai shi ma yana raunatata ne?"
Ya juyo da sauri.
"Waya isa duk duniyar nan ya taba Ayusher, ko da kuwa Aliyun ne da kansa? Humaira sha zamanki ki huta, babu mai tuge shukar da kika yi, zuciya tana son abin da take so"
Ta juya murmushi da farinciki sun bayyana a kowane gaba ta jikinta. Ya kwanta jikin kujera yana lilo idonsa a sama ya bude hannayensa sai murmushi yake. Ba zai karyata kansa ba, a da be sani na amman a yanzu karatun a bude yake, zuciyata tana son abun da take so, kuma take ganin ya dace da ita, ba dan kasan kadai ba, sai dan yana jin kamar idan ba shi ne ba, Emily ba zata samu farincikin da ya cancance ta ba ga waninsa, a yanzu kam baya jin saurari shawarar kowa bayan ta iyayensa duk wani abun da zai biyo bayan haka be damu ba, za a iya fadar gaskiya ko abin da ake hangowa amman be damu ba muradinsa ya samawa Emily abun da take so.
Daga lokacin da ya fara lura ya fada, sai tunanin Turhan ya bijiro masa, be sani ba ashe wanda yayi nisa baya jin kira, a yanzu baya ganin laifi ko illar hakan, domin be shiga tsakanin Emily da Turhan da nufin bata tsakaninsu ba. Ganimar da ta biyo baya tsakaninsa da Emily kuma wani nauyi ne da ba zai saukewa daga zuciyarsa ba, kamar yadda be isa ya kaucewa kaddara ba, domin haka ya shirya bawa zuciyarsa salama da abun da take laso masa da halshen wuta mai zafin gaske.
A tunaninsa kamar Emily ba zata karbe shi ba a yanzu ba ko nan gaba, be sani ba ashe ya gama cinta da yaki, a yanzu ikon garin nasa sai yadda ya juyata. Ya rike wannan a matsayin hujjar da zata hana shi cin amanar ko hana cikar burinta.
Bayan La'asar Ummi ta saka direba ya kaita gidansu Mama Baraka. Emily ta shiga tana jin bakonta domin har yanzu bata iya sake jiki kamar gidan Ummi ko gidanta. A falo ta zauna kanenta na fadar ta shiga ciki Mama Baraka tana dakinta, ita kuma ta ki ta zabi zama a falon har sai da dayar ta shiga ta sanar mata, sai gata sun sauko tare da wanda ta shiga kiranta ta karaso inda Emily take zaune tana farincikin ganinta gidan.
"Sannu da zuwa? Sun ce ki shigo ciki baki shiga ba why?"
"Zan fi jindadi idan ke kika sauko"
"Eh amman dai nan ai gidanku ne, ki sake jiki ki yi yadda kike so Aisha"
Ta daga kai sannan ta gaishe da mahaifiyarta. Mama Baraka ta rumgume tana amsawa, sannan ta tambaye ta ina su Ummi, Emily ta amsa suna lafiya.
"Ita ce mace na zo na nemi izini a gurinki, jibi za su tafi Abuja saboda can suke zama daman, ta ce na tambaya idan za ki aminta za su tafi da ni"
Mama Baraka ta kai hannu ta dafa hannun Emily tana murmushi.
"Tafiyar ta tashi ne? Ummi ta yi kokari matuka kuma ta kyautata na jidadi, sai dai hankalina zai fi kwanciya idan kina tare da ni, na yi ta son na samu lokaci na kasance da ke ban samu ba, saboda kin fi sha'awar zama a can, idan nace zan amince na barki ki tafi tare da su, na cutar da kaina, kuma babu wani lokaci da za mu samu mu kasance a tare"
Emily ta sauke kai kasa alamar bata jidadin maganar Mama Baraka ba.
"Ki yi hakuri Aisha, amman ban amince ba ina son na kasance a tare da ke, shiyasa nake shirya komai na barin gidan domin na san ba lallai zaman yayi miki dadi ba, be zama lallai ki sake jiki a nan ba saboda Kameela ko Hajiya, amman za mu koma gidana da na siya ki saba da kanenki su ma su saba da ke, ki yi hakuri dan Allah ki fahimce ni"
Emily ta daga mata kai sai ta mike tsaye a take.
"Zan koma, daman na zo na ji ta bakinki ne"
Mama Baraka ta kalleta cikin rashin jindadi sannan ta mike tsaye.
"Yanzu zaki tafi? Na zaki tsaya ko abinci ki ci ba?"
"Bana jin yunwa"
Mama Baraka ta dan yi shiru.
"Toh jira ni ina zuwa"
Ta juya ta nufi hanyar da zata sadata da dakinta. Misra ta taso daga inda take zaune ta tsaya gaban Emily.
"Idan baki kasance da Mama ba, baki bata dama ba taya zaki fahimci tana kaunarki? Kuma ita uwace a gareki? A tsawon lokacin kullum maganarki amman saboda bata son bata miki rai ya saka ta hakura ki zauna a can, idan kika tafi Abuja abu zai bata wahala, tana shan gori a gidan nan, ga Mahaifinmu ya juya mata baya, duk abun da muka fada mata bata ji tana cikin damuwa, amman na san idan kina kusa da ita zata samu salama"
"Ni kaiwa bana son na yi nisa da Ummi ne?"
"Why? Saboda Aliyu? Kar ki yi yaƙi akan namiji, amman ki bar namiji ya yaƙi duniya akanki, ke na ki kawai kyautata ce da biyayya, ta nan ake gane namijin da yake sonka da gaske da kuma wanda a baki ne kawai, indai yana sonki ba zai yi nisa da ke ba, kuma zai fiki shiga damuwa, idan namiji yana son mace duk wani baki da bakibaki nata ba zai gani ba, ke da kika sha wahalar rayuwa, ki bar mai sonki ya nuna miki son gaskiya"
Emily ta yi shiruuu tana nazarin kalaman yar'uwarta, Mama Baraka ta sauko ta mikewa Emily waya.
"Ga waya na siya miki na zo na baki ne idan naje, amman tun da kin zo duk daya ne"
Emily ta karba da hannu daya sai Mama Baraka ta janye wayar bata bata ba.
"Saka hannu biyu ki karba shi ne biyayya, musamman ga iyaye"
Emily ta saka hannu tana jin wani abu a zuciyarta for the first time uwarta tana koya mata wani abu daga zamantakewar rayuwa.
"Allah ya miki albarka"
Mama Baraka ta fada. Emily ta mata godiya.
"Na gode"
Sannan ta juya Mama Baraka ta rakata har gurin motar da ta zo ta shiga. Direban yaja motar suka juya, sun fi to gate din kenan ta hango wata farar mota fara sol fake a can dayan bangaren dauke da bakin gilashi, slowing aka fara sauke gilashin har ta hango mutumen dake ciki, zuciyarta ta buga da karfi hankalinta ya tashi ta fara waige tana kallon motar kamar zata fita ta tafi can.
Mutumen da Aliyu yace mata ana nema taya kuma ta ganshi a nan? Hakan yana nufin Vito yana bibiyar rayuwarta kenan? Taya ya san ta zo nan? Ko dai ta cewa direban ya juya ta yi magana da shi? Idan kuma ya sace ta fa? Ya daga hankalin sauran mutane? Domin ta san ba zai iya kasheta ba.
Har suka isa gida bata samu amsa ko gamsuwa daga hasashen da take ba. Ta bude motar ta fito tana arba da Aliyu da ke tsaye da Tasmia a harabar gidan, take ta ji numfashinta ya fara gargada, kamar fa wannan tashin hankali da take gani na yanzu ya fi wacan, gaba daya sai ta manta da wacan kuma ta kasa boye hakan a zuciyarta. Tana tahowa Aliyu yana kallonta da murmushi a fuskarsa, hijab a jikin mace ba karamin kyau yake mata ba, sai a yanzu yake gane idan ya samu Emily ba karamar kyauta Allah yayi masa ba. Sai dai ga mamakinsa tana kawowa kusa da su sai ta wuce shi kamar bata gansu ba, Aliyu yayi hanzari shan gabanta.
"Ayusher baki ga Tasmia ba?"
"Na ganta?"
Ta amsa cike da fushin da bata san na miye ba.
"Gurinki ta zo fa?"
"Kuma take tsaye tana magana da kai?"
Ya daga hannayensa sama.
"Forgive me my Lady"
Ya juya ya nufi entrance yana murmushi, ba karamin dadin ya ji ba ganin yadda Emily ta sauya fuska na ganinsa da Tasmia hakan ya kara fahimtar da shi abin da yake hange a idanuwanta, ya nufi gurin ya tsaya ya juyo tana kallonsu domin zuciyarsa bata natsu ya tafi ya barsu ba. Emily ta juya ta kalli Tasmia with so much confidence.
"Ya aka yi?"
Tasmia ta yi murmushi ta taka few steps ta isa gabanta ta tsaya.
"Bakuwar bata zafi ba ce, na san kina kallona da abubuwan da suka faru a baya, ban kyauta na gano haka daga baya, kuma na zubar da komai saboda ni ma Allah ya ba ni mai kaunata, kwanan baya Kameela ta zo gidanmu ta same ni da labarinki, Wallahi sai tausayinki ya kama ni na hango da ace ni ce a yadda kike ya zan yi? Har na ji kunyar abun da na aikata shiyasa na zabi zuwa na baki hakuri ke da Aliyu kuma na biyo ta gefensa saboda ke ba a samum wayarki ba lallai ma idan na zo kai tsaye ki saurare ni ko ki yarda da ni ba, amman dan Allah ki yi hakuri ki yafe min, ba kuma ina nufin sake alaka dake ba ne aa ina neman yafiyarki ne kawai"
Emily ta sauke ajiyar zuciya.
"Ba komai na yafe miki"
"Na gode, kuma na miki murna Aliyu ya fada min kin musulunta na jidadin haka, sai dai kuma zan baki shawara ki yi taka tsantsan da Kameela, domin tana neman hanyar da zata cutar da ke ne har yanzu, zuwan da ta yi ma ta nemi na bata hadin kai mu yi miki wata illar wai ko acid ne a watsa miki, amman ban bata hadin kai ba daga karshe ma da fada muka rabu"
Emily ta matsa baya tana kallon Tasmia da dan tsoro. Sai Tasmia ta yi murmushi.
"Ke da kike da Aliyu miye na tsoro, kamin ya yarda ya zo nan sai da na sha wahala kuma ya gargade ni, jakar nan tawa ma sai da bawa wata yarinya a gidan nan ta bincike komai a ciki saboda baya son wani abu ya same ki"
Emily ta juya ta kalli Aliyu dake tsaye hannayensa biyu a aljihu yana kallonsu kamar irin kallon nan da motsi kadan yake jira Tasmia ta yi yayi tsalle ya dira gurin. Tasmia ta ciro IV aurenta ta mikawa Emily.
"Ba dole sai kin zo ba, tabbaci nake son ki samu babu ni babu cutar da ke har abada"
Emily ta karba.
"Congratulations"
Ta juya, sai Tasmia ta kirata, ta juyo.
"Aisha ko? Haka Aliyu yace na kira ki baya son sunan Emily. Ki rike Aliyu shi ne ABOKIN RAYUWARKI, kun dace da juna, ABOKIN RAYUWA ne na gari, ke ma kuma kin dace da shi domin baki da hayaniya"
Emily ta juya tana kallon Aliyu.
"Na barki lafiya"
Har Tasmia ta fice daga gidan Emily bata sani ba domin idonta suna kan Aliyu. Ya sauko a hankali zuwa inda take tsaye.
"Wai kokari kike sai kin kure kallona kin hango muni na? Idan ma kin ga haka sai dai ki yi hakuri da ni, domin kaddara ta gina mana gida kuma dole sai mun shiga, idan za a hau sama a fado ni dai ba zan yarda ki bar ni ba, na zama karfen kafa, yanzu akan Ayusher bana jin has, ni kadai nake gane abin da nake ji, idan na mutu ke ce sanadi"
Yana maganar cikin sigar kaunar da soyayya. Murmushi ya zama matar wajib zuciyarta na lasuwa da kaunarsa. Ya ciro dayan hannunsa a aljihu tare da wata yar karamar fulawar Rose mai matukar kamshi ya shinshina sannan ya risina ya aje mata kasa a gabanta.
"Hankalina yana kwantawa idan na yi arba da murmushinki, idan kika kalleni sai na ji kamar na fi kowa farinciki. Ga tukuicin kallonki Sarauniyar abar da ban fada ba"
Ya wuce yayi gaba abunsa kamar ba daga bakinsa kalaman suka fito ba. Emily ta duka ta dauki flower ta kai hancinsa wani kamshi mai sanyi ya ratsa hancinta ya sanarwa kwakwalwarta, kwakwalwar ta sakarwar zuciyarta sakon kai tsaye. A lokacin da ta bude idon sai ta hango shi rike da kofar falon alama ita yake jiran ta fara shiga. Ta mike tsaye ta fara takawa tana kallonsa, shi kuma ya dake ya ki yarda ya hada ido ta ita wannan karon duk kuwa da ya san idanuwanta suna kansa ne. Takunta yake kallo yana kirga tazarar dake tsakaninsu har ta iso kusa da shi ta tsaya.
"Na gode da kika karbi kyautata, ina hango rayuwa ta har abada a cikin idanuwanki"
Ya kalleta suka sake sakarwa juna murmushi. A cikin wani sabon tattausan halshen ya furta.
"Lady's first..."
Yana nuna mata cikin falon da dayan hannunta, ta dauke kai ta wata zumar kauna na dibanta ta shiga falon.
[8/19, 7:16 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
Page 6️⃣9️⃣
A lokacin da ta shigo falon bata samu kowa. a cikin ba, hakan ya bata damar nufar dakinta kai tsaye ta shige ta cire hijab ta kwanta kan gado ta aje wayar Mama Baraka ta bata a gafe ta kai flower Aliyu a hanci tana shakar kashin dake jiki sai lumshe ido take fuska dauke da murmushi.
A rayuwarta bata taba haduwa da wanda ya iya sarrafa halshe ya karantar da ita sabon karatu ba kamar Aliyu, idan ta ce be tafi da zuciyarta ba ta yi karya.
"Ashe kin dawo"
Ta bude idon da sauri ta tashi zaune ta boye fulawa a bayanta, tsabar shauki ya mantar da ita yadda ake rufe kofar daki, bata san a sake kofar take na sai da Ummi ta shigo.
"Eh na shigo baki falo"
"Ina daki ne, toh ya kuka yi?"
"Bata amince ba, tace ta fi son na zauna a tare da ita"
Ummi ta sauke ajiyar zuciya.
"Daman na yi wannan tunanin, ita ma ya kamata ta samu lokaci da ke ai, kuma Abuja babu wani nisa idan kika so ganinmu za ki iya zuwa"
Ta yi shiru sai kuma ta mika hannu ta dauko wayar da Mama Baraka ta bata.
"Ta ba ni waya"
Ummi ta shigo ta zauna ta karba tana murna.
"Maa Shaa Allahu"
A nan suka bude ashe har da sim ciki ba su sani ba sai lokacin, Emily ta yi kamar ta fadawa Ummi ta ga Vito a yau sai kuma ta yi gudun kar hankalinsu ya tashi musamman idan Aliyu ya sani.
"Allah yasa alheri ya tsare, sai kin gama gani sai a saka miki numbobinmu"
"Tohm Ummi"
"Kin ga Tasmia?"
"Eh ta ba ni katin aurenta, a can ma na bar shi waje ina jin"
Ta fara duddubawa bata ga Iv ba.
"Ai kara da kika jefar babu amfanin tafiya bikin ai, kawai dai saboda ta matsa ne yasa na ce Aliyu ya hakura ya barta ta zo, ai neman yafiya ne ba wani abu ba, amman kin san yaron nan ba shi da ta ido fa ta zo sai da ya saka Nafeesa ya bincike ta? Baiwar Allah har tausayi ta ba ni"
Emily ta yi dariya kamar yadda Ummi ma take dariya.
"Haka ta fada min"
"Kin san Aliyu be son abun da zai same ki, be yarda da ita ba ne gaba daya"
Ummi ta sauka kan gadon ta mike tsaye.
"Bari na barki ki huta sai kin fito"
"Tohm Ummi"
Emily ta bita da kallo har ta fice tare da ja mata kofar dakin. Downstairs Ummi ta sauko.
"Ta fada maka Hajiya Baraka bata barta tafi tare da mu ba?"
Aliyu ya aje red apple din hannunsa.
"Ban tambaye ta ba"
"Daman na yi wannan tunanin shiyasa ban kwallafa rai akan tafiya da ita ba, idan ma Hajiya Baraka ta yarda ba lallai ne Ammy ta yarda a tafi da Fatima ba? Ka duba ka ga gaba daya ta dauke hankalin yarinyar nan daga gidan nan, ba dan ma Aisha tana da hakuri da kai zuciya nesa ba da Allah kadai ya san damuwar da zata shiga ko matsala"
"Ummi ni bana ganin laifin Ammy fa, tsakani da Allah ke kanki kina son jikoki balle ita da Turhan kadai ta haifa, kuma an dade babu abun nan, sannan a inda take ma ita kadai take zaune, taya son abokin hira ai"
"Haka ne kuma, Allah ya kyauta"
"Ameen, yanzu tafiyar ke kadai zaki yi ta kenan?"
Ummi har ta wuce ta juyo.
"Ban gane ni kadai zan tafi ba? Ga Nafisa ga ka"
"Aa ni ba zan tafi ba, ni da ke koyawa Ayusher karatu? Bata gane karatun kowa sai nawa, idan na tafi wa zai koya mata?"
Ummi ta tabe baki tana murmushi. 'Yanzu na yi magana yace ba sonta yake ba, kake koya mata karatu ko dai kake koya mata soyayya'
Ta fada a ranta a fili kuma sai ta ce.
"Kadai tsoron kake ka tafi wani ya rutsa dan ginin da ka fara ko?"
Yayi murmushi
"Ai ni idan na yi gini a filin da yake nawa babu mai iya rusa shi Wallahi, bana bada kofa balle ma kuma wannan yarinyar Ummi?"
Ummi ta kara tabe baki.
"Uhm uhm ɗan duniya hayaƙin taba, Allah ya baka ikon cigaba da tausayinta kamar yadda ka fada"
Ta mike tsaye yana dariya ya fice falon. Ummi ta girgiza kai ta nufi Kitchen.
"Daman ai na fada idan ta yi tsami ma ji, kullum idan aka yi magana sai kace tausayinta kake, kai ba zaka iya aurenta ba ko Turhan ya mutum yanzu me aka yi? Hmmm yaran zamani ana hango musu abu suna kaucewa, su karyataka"
TURHAN POV.
Duk wata hanya da zai bi ya fahimtar da mahaifinsa yadda yake son Emily da kuma yadda kasancewa da ita zai kwantar masa da hankali ya hada kan iyalinsa guri daya, ta hanyar auren Emily a karo na biyu ne kawai yake jin zai mallaka masa Fatima a kusa da shi, abu ne mai wahala Ammy ta yarda ya zauna da Fatima a Sudan, amman idan da Emily ba ba shi da haufi, baya ga haka kuma baya ra'ayin wani ya kasance da matarsa sai shi kadai.
Da mahaifinsa ya fahimci abun da zuciyarsa take muradi sai ya karbawa bukatarsa. Ya fahimcin hankalin dansa baya a tare da su a yanzu, domin an maido masa matarsa an shirya tsakaninsu ya fahimtar da ita kuma ta yi masa uzuri, amman tunaninsa fa hashensa kullum yana gurin wacan matar ne da be da tabbacin zata dawo gareshi.
Ya saka mahaifinsa a gaba ne, da neman yayi masa ruwa da tsaki saboda yana ganin idan mahaifinsa ya wuce masa gaba Emily zata samu, yadda yake gani za a bullo ma lamarin abu ne mai wahala Emily ta tsallake tarkonsa.
Kamin su bar kasar Sudan sai da mahaifinsa ya kira Alhaji Bello ya fada masa bukatarsa da kuma rakiyar da yake son yayi masa, Turhan ma da kansa ya sanar da Dr Adam yadda suka shirya komai, ya fada masa yayi hakan ne saboda neman yafiyar Emily wata kila idan yayi wannan zata yafe masa. Dr A-B ya ba shi goyon baya dari bisa dari kuma ya tabbatar masa da cewar tare da shi za'ayi tafiyar.
Sosai kaunar Emily ta kama Turhan kusan da ya ji labarin musuluntarta ta gurin Fatima yayi murna yayi farinciki sosai. Sati daya da yayi a garin sai yake jinsa kamar shekara, tunaninsa yana kan Emily ne, har ta kai idan ya kalli matarsa sai ayyana da ma ace Emily ce, ko kuma idan Emily ce ga yarsu ga ta farincikinsa ya cika. Idan kuwa zuciyar ta tuna masa Aliyu yana can yana kalla masa mata sai ya ji kamar ya hade zuciyar ya mutu saboda kishi da bakinciki. Babu daren da baya mafarkin kasancewa da Emily, idan ya zauna shi kadai shiru baya tunanin komai sai nata, idan ya fita aiki tana nan a ransa, wasan dokin da yake idan yana yi sai yayi ta ayyana yadda zai koya mata wasan idan ta kasance matarsa.
Be fadawa Mahaifinsa cewar ba da aure aka haifi Emily ba saboda baya son mahaifinsa ya yanke kudurinsa ko ya ki goya masa baya, ya fada masa mahaifinta Bature ne kuma ba a kasar yake ba, mahaifiyarta kuma tana auren wani yaron abokinsa wato Bulama Bello step father din Dr A-B, ya fada masa uba daya suke da Dr A-B, ya kuma fada masa a yanzu tana zaune idansu Aliyu ne, sun yi makirci sun zaunar da ita gidan saboda ya kar ta koma gurinsa.
"Za mu nema maka yafiyarta da kuma aurenta gurin Ahji Mudallab, ba zan yi zuwa biyu ba"
Da mahaifinsa ya fada masa haka ba karamin dadi ya ji ba, domin hakarsa ta cin ma ruwa daman abun da yake nema kenan
Shi ma mahaifinsa ya gama sallamawa da fahimtar irin son da dansa yake yi ma wata mace da ba jintsi da jinin larabawa ba.
Turhan kam yana ganin ta ko'ina an daure Aliyu da iyayensa kuma an saka Emily a tsakiya ba zata iya cewa a a ba. Ta waya yake labartawa Ammy komai idan kuma yana video call da yarsa sai ya fada mata yana dawowa zai je ya dauko Emily za su dawo su zauna guri daya.
Sarkin Sudan da kansa ya daga waya ya kira Mahaifin Aliyu ya sanar masa za su neman yafiyar Emily a gidansa, a ciki satin nan da zai shigo. Saboda ya kyautata musu ya aje uzurinsa ya sanar da Ummi cewar ta daga zancen komawarta Abuja a satin zuwa Next week saboda zai dawo Kaduna a satin, sai dai be yarda ya fada mata ko Aliyu cewar iyayen Turhan ne za su zo ba, yayi hakan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 55 Chapter of 63