Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
name is Vito (King)" Ya kada min kai sai yaronsa ya bude min mota na nufi motar na shiga can baya domin mai gida uku ce, shi kuma ya zauna a tsakiya direbansa a gaba. Daga kaduna da direban yaja motar be tsaya ko'ina ba sai Abuja, muna isa ya wuce da mu Airport tun kamin mu bar garin Kaduna ya tambaye full name dina na fada masa ashe zai siya min ticket ne domin muna isa Airport din bamu wani sha wahala ba muka shiga jirgin ya daga zuwa garin da ban taba tunani ko mafarkin zuwa ba wato Part hartcour. A gidansa muka sauka akwai tsoro sosai a gidan domin a kowane lumgu da sako na gidan yaransa ne ga Camera ta ko'ina, a wani bangare na gidan ya aje shi, ya wadata ni da komai ya samo mai aikin da zata kula da yarana ya nemawa London asibiti mai kyau aka fara duba shi ya saya masa kayan wasa. A lokacin ne na ji na tsani musulmai har bana son jin labarinsu ko ganinsu. Ya kan ziyarce mu lokaci zuwa lokaci har na shekara daya a gidan ban san sana'arsa ba, amman ya wadata ni da komai na more rayuwa sai dai baya bari na tafi ko'ina kuma babu wanda yake shigo min. Da jindadin ya samu sai jikina ya dawo, wata rana ya shigo yana kallona yace yanzu me nake bukata, na fada masa da ace zan samu dama zan sha wani abun da zai rage min kiba ne domin ta fara damuna, kuma ina son wani abu da zai iya dauke min hankali domin ina yawan tunanin abubuwan da suka faru har mafarkinsu nake. Tambayar daya fara min ita ce zaki iya karatu? Nace zan iya, sai yace zai sama min duk abun da ake bukata zai fitar da ni waje na yi karatu kuma zai bincika abun da ya kamata akan rage kibata. Kamar wasa sai ga shi ya sama min takardun primary da secondary, ya zaba min London a matsayin kasar da zan tafi na yi diploma in business administration. Ya kuma fada min da yata zan tafi domin akwai gurin da ake bada ajiyar yara a can har sai idan mutum ya dawo daga aiki ko makaranta ya je ya karba. Da na yaye Fatima na bar kasar zuwa London na yi karatu acan na kan kai Fatima day care sai idan na dawo na je na karbota, gida ya kama min apartment daya, kudi kuma har ban sab me zan yi da su ba, sai da na shekara daya a can sannan ya bijiro min da zancen surgery, na ji tsoro amman likitan da zai min aikin ya kwantar min da hankali, ya fada min yadda dokikin abubuwan suke, kuma ya nuna min kudin da za a kashe a rubuce. Aiki aka min aka rage min nama jiki duk inda kitse yake a jikina suka cire min, na yi jinya na wahala ga dokoki da ka'idodin shan magani da abinci, a haka dai har aka yi nasara. Kamin na gama karatun na dawo kasar nan na zama wata kyakkyawa fari ya kara bayyana ni da turawan ba a banbance da wani, musamman idan na shiga cikin masu jan gashi irin nawa. A gida kuma mai aikin da Vito ya dauka Chidimma tana ta kula da London, shi ma kuma yana kula da shi ta wani bangaren, hakan ya saka suka shaku. Na dawo kasar a lokacin da Fatima ta yi wayo, sai ya zamana bata da wani makiyi irin Vito ba kuma dan ya mata komai ba, shi ma kuma baya wani jituwa da ita London ne na shi. A lokacin ne ya fara ba ni yancin fita yawo amman be yarda kowa ya zo gurina ba, sannu a hankali kishi ya fara shiga kamin ya sanar da ni yana so na, sai da ya fara sanar da ni asalinsa sana'arsa da komai. Ya fada min shi be taba son mace ba gaba daya aure ko soyayya basa gabansa sai da na zo rayuwarsa, kuma na yarda domin na lura da zaman dana yi a gidan ban taba ganin mace ko daya ba, kuma be taba nuna min son taba jikina ko yin wata mu'amala da banza da ni ba. Har sai da ya fara nuna min yana kaunata, ya cancanci na ba shi kauna amman zuciyata ta yi firrr ta ki karbarsa, na kan duba alherinsa da kyautatawa amman soyayyarsa ta ki zama a zuciyata wata kila saboda basa jituwa da Fatima ne, wata kila kuma saboda zuciyar tawa ta mutu ne bana jin son namiji a zuciyata. Da fatima ta shekara biyar sai kiyayyarta ga Vito, domin Fatima tana da wani irin hali na kafiya da rashin jin magana,karamar yarinya ce amman ta iya muguyen kalamai. Ko kadan Fatima bata dauko daga hali da kamanin na ba, a duk lokacin da kowa zai kalleta Turhan zai gani kamar an tsaga kara. Gashi da ta yi wayo sai ta tashi da son addinin musulunci ta hanyar CHANNEL din da muke kallo, daga ranar dana fada mata asalin sunanta Fatima ne bata sake amsa sunan Lisa ba, ni kuma bana iya hana ta abun da take so, shiyasa idan Vito ya fita sai na kama mata channel din tana koyon abubuwa na addinin musulunci har ta fara iyawa, domin Fatima tana da wayo sosai da basira ga bakinta a bude yake kamar na babba. Tun tana da shekara daya da wata hudu ta fara kiran Dady ba tare da kowa ya fada mata, sai na hana ta, a lokacin da ta yi wato sai ma fada mata ita bata da mahaifi, shiyasana hade mata suna uku Fatima Emily Aisha. Ko kadan jininta be hadu da na Vito ba har ta kai yayi tsanani har ya kan gwada dukanta ni kuma na nuna masa ba zan lamunta ba, ga shi kuma yana shan kayan maye ni kuma bana son yarana su taso suna sha, ko suna kallon abun, sai na fada masa ina bukatar gurin zama na wa ni kadai, be musa ba ya sama min gida na koma ya cigaba da kula da rayuwata da ta yarana, ni kuma sai na yi amfani da wannan damar na saka Fatima makarantar Islamiya dake garin ta kan je a duk lokacin da ta ji tana bukatar zuwa, a ranar da Vito ya gane dai da yayi min duka, daman ya saba idan na bata masa rai duka yake min tun ban saba ba har na fahimci haka halinsa yake. Vito yayi min komai Aliyu kuma ya cancanci komai daga gareni, a yanzu ma ya fada min ya gaji, kuma na san yayi kokari yana da gaskiya, yana tsananin kishina yana so na kuma ya kyautata min fiye da Turhan fiye da Khaleefa fiye da kowa, kokarinsa da hakurinsa kullum na jiran lokacin da zan amince da kaunarsa ne kuma na aure shi. Wannan ce Emily Aliyu wannan ne tarihin rayuwata, wannan dalilin ne ya saka na tsani musulmai kuma ya saka ba zan taba yarda Turhan ya ga Fatima ba, ba kuma zan taba sha'awar arba da Khaleefa ba, na san idan Turhan ya san da Fatima zai karbe ta ko dan ya kuntata min, ba dan yana sonta ba a yanzu kuma bani da kowa sai ita... Na wahala a lokacin da kowa yake bachi akan tasa rayuwar, na shiga taskun rayuwa a lokacin da babu ni da kowa, na kwankwasa kofofi da yawa ba su bude min ba, a duk inda na saka kafa sai na tarar rame ne na shiga ukuna Aliyu a yanzu ina kokarin gina kaina ne na zama kamar kowa, ni ma na samu yanci ni ma na jidadin da kowa yake ji. Har yanzu abubuwan da suka faru suna ruda kwakwalwata, abu kadan ya kan tuna min da baya, bana nufin cuta ma kowa miyasa ni ake cutar da ni? Shim ko dai ban cancanci farinciki ba? I'm so fighting for peace kwanciyar hankali nake bukata a yanzu, abu kadan zai iya buga kwakwalwata i have done enough i have done everything i can.. I deserve happiness too ko ba haka ba? ****. ****. *** "Kin cancanci, da ace zan iya dawo da lokaci baya Emily da na gyara miki komai, but it's not too late i Will make things right da yardar Allah Emily sai kin yarda musulmai akwai na gari kuma sai kin dauwama a cikin addinin da ke baki natsuwa har abada" Yayi furucin ne a daidai lokacin da jirgin ya sauka garin Kaduna, Fatima kuma take bachi. ______ Toh fa masu karatu kun ji tarihin Emily. [7/1, 9:53 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 4️⃣4️⃣ Aliyu yayi hanzarin saka wayarsa aljihu tun kamin Turhan din ya karaso inda yake, ya zaro handkerchief ya lullubawa fuskar Fatima duk da ya san ba lallai ne a ganin farko Turhan ya gane fatima tana da alaka da shi domin ba zai yi tunanin Emily zata samu ta bangaren Aliyu ba, and he would never think Aliyu zai iya boye masa babban abu kamar wannan. "Abun mamaki, Aliyu kai ne a nan?" Aliyu yayi murmushin karfin hali yana ala ala kar Fatima ta farka, domin ya san karamin aikinta ne ta labarta masa waye ita ko be tambaya ba. "Ni ne, Turhan taya muka hadu?" Turhan yayi murmushin kasaita yaje zai rumgume abokinsa daman al'adar larabawa ce rumgume juna da sumbanta idan suka hadu da wanda suke so, haka Turhan yayi yunkurin aikatawa cikin murna da farincikin ganin abokinsa sai dai babu dama saboda babyn dake hannun Aliyu. "Ohhh Baby waye haka ta hana ni rumgumar abokina, ban jidadi ba" Aliyu ya fadada murmushinsa abubuwa biyu suka zagaye shi, yadda Turhan yake murnar ganinsa ya saka shi jin wani iri na gaskiyar daya boye masa gashi kuma yana fargabar kar Fatima ta farka. "Baka santa ba, daman wai tun da muka yi waya kace min zaka zo baka zo ba?" "Ban samu zuwa ba, daman na so mu zo tare da Reem ne amman haka be samu ba" Ya fada cikin wani yanayi na rashin jindadi. "Toh ya jikin Ammy?" "Da sauki take cewa sai dai naje na gani, muje ma tare ai sai ka duba ta ko? Daman ina neman mai raka ni kasan kullum idan zan je gurin Ammy tsoronta sabo yake zame min, saboda maganganu da kuma fuskar da take karba ta da ita, ta daina murna da zuwa na yanzu" Aliyu can't say no to his friend kuma ya san ba zai yiyu ya tafi tare da Fatima gidan ba hatsari ne ma babba ya tafi da ita gidan. "Yeah amman na yi waya da direba na ce ya zo ya dauki a nan" "Malam ba wani babban abu ba ne direbanka ne fa, karkashinka yake ai zaka iya fada masa ya koma kawai, direban da zai dauke ni yana waje yana jirana mu je kawai kasan dai ba zan barka Airport din nan ba" "Bata zan yi?" "Aa amman dai ba zan barka ba i miss you Aliyu sosai fa" "Okay fine mu jira Direban ya karaso sai ya tafi da wannan yarinyar kar mahaifiyarta ta damu, ni kuma sai na bika mu kaika gida tun da ka zama amarya" Yayi dariya tare da kai hannu ya taba Fatima dake ta bachinta cike da sha'awar yara. "Yar waye wai" Hannunsa na kaiwa a jikin Fatima ta zabura da karfi ta sauke ajiyar zuciya a cikin bachin da take. "Oh Sorry" Turhan ya fada yana dauke hannunsa da sauri gudun kar ya tasheta, Aliyu ya kalleshi jiki a sanyeye ya juya yana fadin. "Mu tafi waje mu jira shi" Turhan ya jera tare da shi suka fito suna dan taba hira, sun tsaya harabar for like 10min direban Aliyu ya kira Aliyu ya kwatanta masa inda yake direban na isowa Aliyu yayi hanzarin nufar motar ya bude baya ya kwantar da Fatima a hankali bachi take sosai kamar wanda ta yi wani katon aiki, Aliyu ya rufe motar a hankali be taba jin ya aikata wani abu na rashin kyautata kamar kin fadawa Turhan Fatima yarsa ce a yanzu ba. Sai yake jin kamar ya ci amanar abokinsa duk da yake yana da laifi. "Ka tafi da ita gida ka shiga da ita ciki ka kwantar da ita" Ya saka hannunsa alijihu ya ciro keys ya mika masa. "Toh ranka ya dade" Ya karbi keys din sannan ya dauki kayan da Aliyu ya zo da su ya saka bayan mota, sai a lokacin Aliyu ya sami relief ya nufi gurin da Turhan yake tsaye jikin motar da za su shiga, yana isowa Turhan ya ware hannu Aliyu ya ware suka rumgume juna. "Na jidadin zuwan nan yaushe rabon da na saka ka ido Aliyu" "Ni ma na yi marmarin ganinka, fatan kana lafiya" "Da sauki dai ina lafiya ga mutumen da uwarsa ke fushi da shi?" Ya bude motar ya shiga baya Aliyu ma ya zagaya ya shiga baya, mutumen da suke tareda Turhan ya shiga front seat direba yaja motar suka fara tafiya, suna taba hira har suka isa gidan. Turhan da Aliyu a tare suka fito motar Aliyu ya wuce gaba ya shiga cikin falon Turhan na bayansa, Mai aikin Ammy ta amsa musu ta gaishesu, Aliyu ya karasa gurin da Ammy take zaune ya zube kasa yana gaisawa da ita Turhan ma ya karasa ya zauna kusa da Aliyu. Cikin murna da farinciki take kallon Aliyu. "Madallah Aliyu ne a gidan na mu yau?" "Ni ne Ammy ya jikin na ki" "Jiki Alhamdulillah Aliyu ina samun sauki, ashe ka samu shigowa" "Eh kin san daman na ce zan shigo na duba ki, sai gashi kuma wani uzurin ya taso aka yi daidai, a airport na hadu da Turhan ai sai muka zo tare" "Maa Shaa Allah, haka fa ka fada min zaka zo ai ka huta baka tsaba alkawari uwarka ta yi farar haihuwa Aliyu" Ammy ta fada har lokacin bata kalli inda Turhan yake ba. Turhan ya sauke kansa kasa yana jin wani iri, Aliyu ma ya ji babu dadi domin Ammy tana kokarin muzanta abokinsa ne a gabansa which it's not fair. "Amman dai jikin da sauki sosai ko Ammy?" "Na samu sauki Alhamdulillah, ai na ma fadawa abokinka ba sai ya zo ba, kawai be ji magana ta ba ne daman be saba ji ba" "Haba Ammy taya baki da lafiya kuma ki ce kar ya zo? Ai ba zai yiyuwa ba, ke fa mahaifiyarsa ce Ammy ki rika duba wannan" "Zuwansa ba zai rage ni da komai ba balle ya kara ni, rabin ciwon nan ba shi ne silarsa ba? idan ya zo ai ba da lafiya zai zo min ba, kuma ina da masu kula da ni nan yayan yan'uwa sun ce wadatar, idan za amin allura kullum sai Nurse ta zo, Likita kuma kullum yana zuwa duba ni, saboda na fada masa ni bana son asibiti ko da mutuwa ce a bar ni na mutu a gida, kaga shi kenan abokinka ya huta ba sai ya sake zuwa kasar nan ba sai yayi zamansa a can daman haka ubansa yake so" Turhan ya kalleta felling hopeless cikin murya mai rauni ya ce. "Wani dan kirki ne zai yi fatan mahaifiyarsa ta mutu ya huta? Ammy ya kike magana haka kamar mai magana da makiyinta? Danki ne fa ni jininki, na rasa ya zan yi na kawar da wannan bakin shatin dake a tsakaninmu, Ammy kina tunanin all this while abun nan dade yake min? Ko tafiya kika yi kika bar ni wannan abun ba zai barni na samu salama ba, Ammy ni ma ina cikin damuwa gaba daya yanzu bana jindadin rayuwar da nake, abun da a aikata kuskure ne kuma ni dan'adam ne aziji" Ammy ta girgiza kai. "Aa abun da ka aikata ganganci ne ba kuskure ba, da gangan ka aikata, saboda baka kallo da daraja irin ta uwa, kuma abun da ka yi min ai ka kyauta tun da ka samu tukuici, Allah ya maka albarka Turhan na gode" Aliyu ya ce. "Ammy ki yi hakuri dan Allah ki yafe masa abun nan ya wuce" "Na yafe masa, amman wucewar wannan abun? Sai na koma ga Ubangijina, ni kadai na san me nake ji, yaron nan shi kadai Allah ya ba ni, idan kai ka manta mahaifiyarka ba zata manta ba Aliyu, irin fadi tashin da na yi akan na samu ganin yaron nan, na wahala a gidan mahaifinsa kuma na wahala kamin a bar shi ya zo gurina, na dauki yar mutane na aura masa da tunanin hakan zai saka na samu dana da zuri'arsa a kusa da ni, amman ya watsar ya karyata duk wata halayya tasa dana fadawa yarinyar nan, marainiya ba uwa ba uba, yanzu Allah kadai ya san halin da take ciki idan ma tana raye, bata da kowa sai Allah bata da wani wanda zai nemi ya san halin da take ciki tun da bata da dangi, yarinyar nan ta yarda da ni amman Turhan ya rusa duk wannan ya nuna ba ni da muhimmanci a garesa kamar yadda ubansa ya nuna min" Ammy tana maganar hawaye ya sauko idonta, Turhan yayi kasa da kansa ya saka hannunsa ya rike goshinsa idonsa suka cika da hawaye, ba na tausayin Emily ba na bakinciki daya saka mahaifiyarsa har ta zubar da hawaye akansa gaban abokinsa. "Wane irin muhimmanci Aisha take da shi a gurinki har haka Ammy? Da har zaki zubar da hawaye akan abun da ya faru?" "Irin muhimmanci da baka da shi" Ta amsa masa kai tsaye da kakkaurar murya. "Indai saboda ni ka zo, toh ka hada kayanka ka koma bana bukata, ka bari idan na mutu sai ka zo jana'iza" "Subhanallahi Subhanallahi" Ya maimaita har sau uku sai Aliyu ya dafa shi. "Turhan fita waje ka jira ni" Ya tashi cikin wani irin yanayi na bakinciki da ya fice falon, sai da ya fita sannan Aliyu ya ce da Ammy. "Ammy bana son na tunatar da ke abun da kika riga kika sani, na san kin so Emily da Turhan kin tsara zamansu, amman haka be samu ba baki tunanin wata su din ba alheri ba ne ga junansu? Kuma haka Allah ya tsara shi da ita babu dogon zama, kuma Ammy karki manta duk yadda zaki so Emily Turhan danki ne, na san be kyauta ba amman fushinki a kanki da damuwarki zai iya janyo masa matsala a rayuwa ko ba yanzu ba a nan gaba, kuma Ammy Turhan yayi nadama sosai yanzu haka zancen da yake min yana son ya saka kudi mai kauri akan nemo Emily, abun ya dame shi ma, ki yi hakuri Ammy" Ammy ta yi murmushi. "Allah ya maka albarka Aliyu, ka san muhimmanci uwa shiyasa ka fadi haka, tafi ka tafi na gode" "Shi kenan Ammy Allah ya kara sauki ya baki lafiya" "Ameen Allah ya maka barka" Ya mata sallama ya fito falon a jikin motar da suka shigo ya samu Turhan ya jingina fuskarsa dauke da damuwa. Aliyu ya saka hannayensa aljihu yana sauke ajiyar zuciya ta dayan bangaren abokinsa ya ba shi tausayi, sai dai kuma idan ya tuna labarin da Emily ta ba shi sai ya ji kamar be tausaya masa ba. "Turhan am sorry iyaye sai lallabawa" "Haka take fada min maganganu marasa dadi a duk lokacin da na zo, kuma ta sani na yi iya kokarina gurin neman yarinyar nan, ban same ta ba toh ya zan yi? Kana jin tana fadin bata san halin da Aisha take ciki ba, ni kuma da nake cikin wannan halin bata jin tausayina na rasa ya zan yi" "Da sannu komai zai zama daidai In Shaa Allah, wai taya ka yi Aisha ta subuce maka.?" Madadin ya amsawa abokinsa sai ya ce "Ita ma fa yarinyar ta jefa ni a matsala, miyasa ta amince da auren nan tun farko fisabilillahi" "Allah ya kawo sauki, ni zan wuce abun da zan fada maka shi ne ka yi hakuri da mahaifiyarka kuma ka yi ta addu'a" "In Shaa Allahu, ma gode Aliyu, bari na yi ma direban magana sai ya kaika gida" Aliyu ya shiga motar Direban yaja shi zuwa gidansa, a mota Aliyu ya gwada kiran Number Emily ya jita a kashe sai ya aika mata sako. "Are you okay?" Domin ya san ya kamata ace ta kira shi bayan riskar sakonsa, and maganar Ammy ta taba shi na cewa bata da wanda zai damu ya san halin da take ciki tun da bata da kowa. Bayan direban ya aje shi ya juya shi kuma ya shiga gidan da yayi datti yana mamakin taya haka ta faru domin yana da mai gyara masa gidan every week. A falo ya samu Fatima na ta bachi har lokaci akan kujera hannu ya kai ya taba jikinta yana mamakin wane irin bachi ne take haka, sai ya ji shi da dan zafi kadan. Mai kula da harabar gidan ya shigo yana masa sannu da zuwa Aliyu ya amsa yana tambayar ina mai gyara gidan. "Tun da ta tafi bata dawo ba, bata fada maka komai ba tace dai zata je ganin gida ta bada keys a aje maka" Ya saka hannunsa aljihu ya ciro keys din ya bawa Aliyu da hannu biyu. Aliyu ya mika masa Atm dinsa ya fada masa code sannan ya fada masa inda zai tafi ya samo musu abinci mai kyau... Sorry ku yi hak'uri gobe zan yi long page in Shaa Allahu. [7/2, 6:50 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 4️⃣5️⃣ Kamin yaron daya aika ya dawo Aliyu ya shiga ciki yayi wanka ya canja tufafi sannan ya dauki wayarsa ya kira Mama Barakat ya tambaya ko tana gida. "Eh ina gida Aliyu ko ka shigo garin ne?" "Eh na shigo kuma yau nake son na shigo gurinki saboda ina son komawa gobe kin san aikin na mu babu daga kafa" "Haka ne to sai ka shigo" Ya sauke kiran sannan ya fito falo yayi sallah yana sallamewa aka yi knocking, knocking din da ya tashi Fatima ta farka idonta har sun yi ja tsabar bachi, Aliyu ya karba ya rufe kofar. "Yaushe muka zo nan?" "Kina bachi little princess" Ta yi mika "Kai ka dauko ni?" Ya risina inda take zaune yana kallonta da murmushi a fuskarsa. "Eh kin tashi lafiya?" Ta kalli falon. "Nan gidanka ne?" Ya daga mata kai. "Ashe kana da wani gida Vito ma gida biyu yake da shi" "Good taso ki wanke baki ki yi wanka sai ki ci abinci ki yi sallah" Ta kalli shaddar dake jikinsa. "Kai ka yi?" "Eh" Ya kama hannunta suka sauka tana fada masa kanta na ciwo, ya shiga da ita dakinsa ya nuna mata bandaki da yadda zata yi komai sannan ya fito ya dawo falon ya zauna yana taba wayarsa, har a lokacin sai da ya gwada kiran Number Emily ya ji ta a kashe. Yana ta nazarin abun da zai saka ta kashe wayarta kuma ta dauki lokaci har haka bata kira ba bayan sakon da ya tura mata, duniyar tunani ta dauko shi daga can bangaren Emily zuwa na Turhan idan ya ce be ji tausayin abokinsa ba yayi karya, ya san da zarar Emily ta bayyana a rayuwarsa komai zai zame masa daidai, sai dai kalamansa na dazun cewar da laifin Emily na amincewa ta aure shi ya sanyaya masa guiwa, jikinsa kuma yana ba shi cewar Emily ta yi gaskiya ko Ammy ta san da Fatima a matsayin jikarta abu ne mai wahala ta bar mata ita balle kuma Turhan, hakan ya saka shi ya ji lallai ya kamata ya bar garin Kaduna gobe gudun kar makamancin abun da ya faru a Airport ya sake faruwa, gashi kuma yana son ya san halin da Emily take ciki domin rashin samun wayarta da kuma maido masa da amsar sakonta ya saka shi a damuwa. A tare suka ci abincin da Fatima tana ta fada masa mafarkin da ta yi, ya rigata koshi a dole ya jira sai da ta koshi ita ma sannan ya kwashe kayan ta bishi Kitchen tana kallo komai ta gani sai ta taba ta tambaya, ko ta fadi Momy na irinsa. "Fatima Zaki iya zama a gidan nan ke kadai naje wani guri na dawo?" Ta lake kafada "Aa ba zan zauna nan ba, sai dai mu tafi tare" "Ba zan dade ba kuma zan iya bar miki wayata ki yi game ki yi kallo" "Duka na kalli komai na cikin wayar ni

Chapter 35 of 63