Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mata ya saka yatsansa ya share mata, ya sakar mata murmushi mai taushi ya girgiza mata kai alamar no more tears, ya kwamto da ita kirjinsa yana shinshinar gashin kanta dake kamshi. Slowly and slowly ya dago kanta ta kalli saitin idonsa ya sauko da fuskarsa sai ta lumshe ido tana jin sanyin lips dinsa a saman nata lips din, kamin ya raba lips din gida biyu ya saka nasa a tsakiya. Wani sako mai nauyi da mai wuyar dauka ya aika mata mata ta tsakanin bakinsa da nata, a lokacin da ya cire bakinsa cikin nasa sai ta kalleshi a rikice tana maida numfashi, sai kuma ta lumshe ido ta yi murmushi ta maida kanta kirjinsa tana mai jin kunya. Sun samu lokaci a haka sannan ya tashi dauro alwala ita ma ta yi suka yi sallah, yayi musu addu'a, ya dauko abun tabawa ya ciyar da matarsa, sannan sauya tufafin jikinsa zuwa ma bachi, ita ma ta sauya nata bayan ya bata guri ya fita falo har sai da ta gama sannan ya dawo. Abubuwa da Emily bata saka ran Aliyu ya sani ba, ko ya iya ta gansu, bata yi zaton zai zo mata a haka ba, saboda yadda take ganinsa da kokarin kawarda kai. Kusan duk wani abu mai sunan damuwa sai da Aliyu ya matar da ita a daren, har take jin kamar ita ce ta kwashe kason jarumin namiji, ta rika jin kamar bayan Aliyu babu wani namiji mai halayya da dabi'un da ya rage irin nasa. A kirjinsa ta kwana har safe, ba kuma a daren kadai ba, a kowane dare bayan daren tarewarta tana kwana a kirjinsa ne, idan yana gidan da rana kuma tana sarkafe cikin hannayensa, duk wani abun da zai bada space a tsakaninsu be yarda da shi ba. A nan ta gane kalmar soyayya ba a cikin kalami kadai take ba har a cikin aiki da zamantakewa. Matukar hali da hallayar da Aliyu ya sauke ta da su a gidansa zai daure, to bata jin akwai wata macen da zata fita dace ko jindadin aure a halin yanzu. Idan ya fita har kewa take, shi kan shi kamin ya dawo gareta ya yi missing dinta kamar ba a gida daya suke rayuwa ba. Awa ashirin da hudu yana jin kamar a kara musu wasu awanin domin sun masa kadan. Kusan duk wanda ya shiga gidan sai ya yaba da yadda aka gyara ko'ina kuma aka zuba kaya, sosai Mama Baraka ta yi kokari wajen ganin ta fitar da yarta kunya, kuma ta faranta mata rai, kuma kwaliyya ta biya kudin sabulu domin ta siya komai a gurin Khadeeja Candy ne. [8/31, 11:54 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 7️⃣3️⃣ 🌟✨ TALIYAR HAUSA – YAR MURJI ✨🌟 🥘 “Abinci na gargajiya, ɗanɗano na musamman, jin daɗin iyali!” 🥘 Idan kina/kanason abinci mai ɗanɗano na musamman wanda zai tunatar da kai daɗin gargajiya, to babu kamar Taliyar Hausa – Yar Murji! Wannan taliya ba wai kawai abinci bace, al’ada ce mai haɗa iyali, ƙauna da jin daɗi a teburin gida. ✨ Me yasa za ka zaɓi Taliyar Hausa – Yar Murji? • ✅ An yi ta da tsafta da inganci • ✅ Ta dace da kowanne irin miya: miya mai ƙwai, miya taushe, ko miya mai ƙyauƙyau • ✅ Sauƙin dafawa – cikin mintuna ka samu abinci mai gamsarwa • ✅ Lafiyayye, mai sauƙin narkewa, kuma ya dace ga kowa cikin gida • ✅ Za ka iya amfani da ita wajen girki na yau da kullum ko kuma na musamman 📍 Muna a Kaduna – amma ɗanɗanonmu ya zarce iyaka! 🚚 Ana kawo muku duk inda kuke a Najeriya (delivery guaranteed). 💛 Idan kana son jin daɗin abinci na gida wanda ke haɗa zuciya da iyali, to ka gwada Taliyar Hausa – Yar Murji yau! 📞 wa.me/+2347071821482 tuntube mu yanzu domin yin odar ku. 👉 Ka more ɗanɗanon gargajiya mai tsafta, mai daɗi, mai ɗorewa! Jin alamar mutum a bayanta ya saka ta juyo, sai suka hada ido, yana sayen da wando bachi sai farar vest dake jikinsa. Ya daga mata gira like how far, ta aika masa murmushi. "Ina kwana" Ya daga kafadunsa. "Ni ma ban san inda yake ba" "Okay good morning" "it's morning but not Good Morning?" Ta kalleshi with confuse. "Why?" Ya jingina da kofar kitchen din yana bata amsa tare da saka hannayensa aljihu. "Cox i didn't get a kiss from my wife" Ta juya ta aje wukar hannunta tana murmushi, kana ta sake juyawa ta nufi inda yake ta yi dage zata sumbance shi ya yi dage shi ma yana kauce fuskatsa. "Bana so, sai da na yi magana rike abun ki bana so" Ta zagaye hannayenta a wuyansa. "I'm sorry haba autan maza, na tuba handsome na maka kiss ma kamin na fito kitchen fa" "Aa ni ban ji ba, kuma waya ce ki bar ni ki zo kitchen? Ke dai kin dange sai kin wahalar da kanki ko?" "Babu wahalarwa a cikin hidimar miji ko wace kala ce" Ta sake kai bakinta da sauri zata masa kiss ya kauce yana dariya. "Na ce bana so" "Toh ba ni wanda na baka dazun, da kana bachi dawo min da abuna" "Kiss din?" "Eh" Yayi dariya mai sauti. "A ina kika ba ni?" "A nan" Ta tura masa bakinta. "Ni na san ba ta nan aka ba ni ba, amman tun da wayo za'ayi min a yaudarini ba matsala" Yayi mata kiss din. Ta sake shi tana ja baya cikin zolaya da muryar yaudara ta ce. "Ba a nan na yi maka ba, a nan na yi maka" Ta nuna kumatunta. Ya fusgota ya dawo da ita jikinsa. "To dawo min da abuna, na baki na ki" Ta noke kasa tana dariya. Binta yayi kasa yana mata kyaculculi sannan ya sake ta ya nufi plantain din da take yankawa tana soyawa at the same, ya dauki wukar yana yankawa ta karaso ya kwashe sannan ta dauki daya ta hura ta nufin ba shi. "Ki daina hura abun da abun da zaki ci, Annabi ya hana, hura abinci" "Na karu da wannan, amman akwai zafi fa" Ya aje wukar ya dauki daya ya bude yana riritawa a hannunsa har ta sha iska. "Bude bakin" Ta bude ya saka mata. "Kai zan bawa fa" "Kuma kuka ci?" "Kai ka ba ni ai" Ya kai hannunsa ya rikota suka fara kokawa ala dole sai ya cire wanda ya saka mata a baki, ita kuma ta yi hanzarin taunewa ta hade har tana kwarewa sai dariya take. Sai da ya ji tana dari sannan ya sake ta. "Wai Qalbin miyasa baki jin magana?" Ya nufi gurin da ruwa suke ya dauko mata ta bude bottle din ya daga kanta ya saka mata a baki, ta sha kadan tarin ya kwanta. "Kai ka koya min ai" Ya kai ruwan bakinsa ya sha kadan. "Ni din?" "Ko da aka kawo ni gidan nan har kunyarka nake ji, amman ta bi ka bala ni" Tana maganar tana dariya. Sai ya kai bakinsa yana hura amsan kanta. "Haka ake yi ma yarinya idan su ta kware" "Yarinya matar...." Ya zaro ido. "Ni din? Ni za ki duba ki cewa yaro? Gaskiya ne da sauranki" Ya aje ruwan hannunsa kamin ya juyo ta gudu daga Kitchen din, be san lokacin da dariya ta subuce masa ba, sai ya nufi kofar kitchen din ya rufe ta ciki, be bude ba sai da ya karasa aikin da take ya hada komai a ya zuba a mazubinsa sannan ya bude kitchen din ya kawo musu komai a inda suka saba karyawa. Al'ada ce ta ya sabawar kansa tun a lokacin da ya auri Kameela, idan ya rigata tashi shi yake hada musu komai na karyawa, idan kuma ita ta riga sai ta hada, sai dai ya fita kokarin hadawa domin tana yawan bachin safe shi kuma ya kan fita aiki dan haka baya jiranta yake hadawa musamman lokacin da take da ciki, har na rana ma wani lokacin girka musu yake ko yayi musu takeaway. A yanzu kuma ya dora daga inda ya tsaya da Emily, banbancin Emily da Kameela shi ne, Emily tana son girkawa Aliyu abinci saboda tana son yi masa hidima tana son ta yi masa abu na faranta rai, abun da zai yaba mata. Tana gwada new recipe wani yayi dadi Wani kuma yayi ba lada ba la'ada, shi kuma da yake gwanin zama da mace ne, be taba kin yaba mata ba. Ko be yi dadi ba yabawa yake ya gode mata, sai dai ya fara mata inda za ta gyara ko su sake yi tare. Kusan inda ba shi da wani aiki a waje to yana gida kusa da matarsa. Ita vata yarda ta yi nisa da shi, shi ma kuma be koya mata ba. Idan ya fita har kewar dawowarsa take, takan tanadi labarai kala kala da take ba shi, kama daga na littafi zuwa na mutane da take ganina kafafin sada zumunta, wani lokacin har kudi yake sakawa idan labarinta yafi na shi armashi zai biya, idan kuma nata ya fi armashi zata biya, ita ta kan biya ta wata sigar ne, shi kuma ya biya da kudi. Zamantakewa suke kamar daman can ita ce matarsa ta farko, ita ma shi ne mijinta na farko, ko da yake masu iya magana sun ce macen da miji ke so kullum yar gata ce. Tun bikin su da sati biyu Ummi ta bar su a garin Kaduna ta koma Abuja gurin mijinta daman can take zama dawowarsa, abubuwan da suka faru ne suka saka ta dawo Kaduna da zama, a yanzu kuma tun da sun kamalla komai cikin aminci da farinciki sai ta koma gurin tata ibadar ta aure. Kamin ta tafi sai da ta yi musu huduba sosai, musamman Aliyu, saboda tana ganin Emily kamar bata da matsala. Ta gargadi Aliyu ta yi mata uzuri da kuma taka tsantsan akan zamantakewarsu, ya rufe ido kuma ya toshe kunnuwansa daga masu suka ko gulma, ita kuma ta yi biyayya ga mijinta ta gujewa bacin ransa, sannan ta toshe kunnu daga wasu kannan maganganu. Ummi ta roki Emily karta zafafa akan zaman Fatima a hannunta, domin abu ne da dukansu suka sani Turhan ba zai yarda Fatima ta zauna tare da su ba, ko da kuwa tana son haka. "Ki daurewa zuciyarki ko babu dadi ki masa uzuri, saboda ya so ki be samu ba yanzu kuma yana da yarki, to ki masa hakuri ya ji sanyi ko ta nan, kuma karki bude hanyar da zata kawo baraka da mijinki akan yarki, sannan karki yarda mijinki ya raina yarki ko ya kaskantar da ita, kuma ko da tana can ki rika kula da ita akai kai, dan Allah ku bawa marada kunya, kar a ji kanku, idan sulhu ya gafara da mijinki, akwai mahaifiyarki idan abun ya ci tura, ina nan kuma mahaifinsa na nan, ba fata muke ba, amman dai kar aji a waje" Nasihar Ummi ta saka Emily ta dauke kai daga damuwa da rashin Fatima a kusa da ita, domin washe garin ranar da aka daura musu aure Ammy ta aiko aka dauki Fatima, har yau Fatima bata san ya dakin Emily yake ba, saboda ta ki kawota ita kuma bata son ta matsa abun ya zame musu matsala. Dan haka ta saka musu ido, Fatima na garin nan bata nan bata da labarinta almost 3 months da bikin babu amo babu labari. KAMEELA POV. "Ko da mafarki ban dauka Aliyu zai iya juya min baya har haka ba, kusan duka kawayena na bata da kowa saboda da shi, gaba daya rayuwata ta ta'allaka ne akansa" Kanwarta Farida ta dafata. "Kameela ke kika dauki Aliyu wani shege fa, tun farko be dace da ke ba" Kameela ta dube ta. "Zaki iya fada min illar Aliyu daya?" "Zan fada miki da yawa ma, kin ga dai akwai masu sonki masu kudi amman kin nace sai shi, kuma ɗan makiyinmu ne" Ta yi murmushi. "Ba zaki gane ba, wannan ba illa ba ce, kuma na gujewa duk sauran ne saboda suna da aure, Aliyu kuma saurayi ne, Aliyu ba shi da wata illa da za a dube shi da ita a hana shi aure, amman ya ci amanata" "Ko yanzu fa kin ki bawa sauran dama ne, mutane na nuna suna sonki" "Farida ba zan iya zama da mai mata ba" "Ko da Aliyun ne ya dawo?" Ta yi shiru domin bata da amsar tambayar a yanzu. "Dan Allah karki bari son Aliyu ko abun da yayi miki ya hanaki kula wasu mazan, ki duba fa da zai yi aure ma be zauna a gidan da kuka zauna ba sai ya zabi zama a wani gidan kuma ya kwaso kayanki ya aiko miki, da kin mana yadda muke so ai da yanzu kin riga shi aure" "Ba auren ba ai mazan ne, yanzu duk namijin da zaka ce ya saki matarsa ya aureka ba zai yarda ba, ni kawai sai idan na samu saurayi zan yi aure" Farida ta gwalo ido. "Eyyy sai kice ya saki matarsa ya aure ki? Tsakani da Allah Kameela ki aje wannan tunanin a gafe, yanzu fa gasar kudi ake ba ta kishi ba, kishi da hauka na talaka ne, indai mutum yana da yan kudadensa iya ruwansa da wani kishi, kuma duk manyan mutanan da ke sonki kowa da matarsa da yara ta ina zai saki matarsa ya aureki? Wani ma mata biyu" "Ki daina zancen manyan mutane, na auri wanda ya kusa haihuwa da majina zan ji ko da kishi ko yayansa? Ko kuma so kike na sake auren na fito?" "Aa amman mai kudi wake zancen majinarsa? Murar ma ai sai talaka, da kudinsu wa zai kula wannan kuma mataki suke dauka, ni Wallahi kawai ki yarda hannu ya koma miya bawan Allah nan yana aurenki first lady zai maidaki, daman yana neman yar boko kuma wayayen kyakkyawa ta nuna mai dan jiki fit haka dai kamar ke" Kameela ta ja tsaki ta tashi ta fice ta bar mata dakin. Ta yi ma kanta alkawarin ba zata sake waiwayar Aliyu, ta riga da ta aje shi a gafe yanzu saboda ya yi aure. Abu kamar wasa kamar gaske, Kameela ta kasa kula kowa, idan ta ji labarin kana da aure da iyali sai ta aje ka a lissafi. Mahaifiyarta da iyayenta suna kokari sosai gurin lurar da ita abubuwan da ya kama ta dauka da muhimmanci a aure amman ta kasa domin ba wai iya rabuwa da mata ba, ita ko mai yayan wata bata so. Burinta ace ita kadai ce agidanta sai yayanta. Saurayin da take ta jira ya ki samuwa, akan nuna ana sonta, wasu da yawa da suka nemeta lokacin da tana budurwa ba su samu ba, sun dawo amman ta gagara kula ko daya saboda dukansu suna da aure, jiran take sai ta samu marar mata kuma wanda zai fara gina iyali da ita. Ta kasa karyata zuciyarta ta kasa yarda da kaddararta tana da wasa da lokacinta, zuciyarta na ta yi mata hange hange marasa amfani. Kuma ta kasa cire Aliyu a ranta, kawai ta hakura da shi ne, amman sonsa ya ki barinta, kishinta ya ki ya tafi, kusan kullum idan ta kwanta da tunaninsa ai ta tuna a yanzu wata macen ce a kirjinsa ba ita ba, wata macen ce take kula da shi ba ita ba. Wasa wasa Kameela ta fara nisa cikin burin da zuciyarta ta dora nata, na yaki da umarnin Allah, madadin hakuri da hukuncinsa. Ba iyayenta kadai ba ita kanta abun yana damunta, ta kasa focusing a kan rayuwarta, ta kasa manta Aliyu da zamantakewarsu, ta kasa bawa wasu mazan dama. Tun yan'uwanta suna lallabata mata har lamarin ya fara ba su haushi suna fita sabgarta. Ta kai ita kadai take iya fahimtar kanta, ta kan kebe ta yi ma kanta tambayoyin da ba su da amfani da kuma nadamar da bata haifar mata da komai ba sai bakinciki. A yanzu ta gane ta inda matsalar ta bullo, sanadin zafin kishinta ne, ya kaita ga kokarin halaka mijinta, domin ita ce babbar damuwarta a yanzu, wata kila da bata yi kokarin kashe su ba, da Ummi ba zata hana su zauna ba, duk abubuwan nan da suka faru da yanzu ba su kawo nan ba. Wata kila kuma da ta daure ta hana zuciyarta daukar Fatima ta kai ga Turhan mai yiyuwa da yanzu Aliyu be sake ta ba domin ne mafarin tonon asirinta kuma mafarin rabuwarsu. Idan ta so samawa kanta sassauci kuma sai ta tuna ai Aliyun ne ya fara kula Emily bayan kuma yayi mata alkawarin babu karin aure sai kuma ya zagaya yana bibiyar Emily. Ba ita kadai ba kowace mace ba zata dauka ba balle kuma ita dake da zafin kishi. Wani alkawari da ta daukarwa kanta kuma take da yakinin zata iya cikawa shi ne, hakura da zaman aure da Aliyu, ko da kuwa zai dawo ya ce zai maida ita a yanzu, bibiyar da ta yi masa a baya ma nadama take yanzu, domin ta san ba ajinta ba ne, namiji ya sake ta akan abun da ta fishi gaskiya kuma ta bibiyeshi ya kasa saurarenta. Ita sam bata ma amfanin zama da mutumen da ya nuna wata macen ta matarsa ta gida muhimmanci ba, ba dan haka ba babu abun da zai saka ba zai aje lamarinta a gafe ta kula Emily ba. Idan yan'uwanta suka so kara mata bakinciki sai su ce "Ai daman can Aliyun ba wani sonki yake ba. Ke ce kika makale masa, uwarsa ma ba sonki take ba" Zata iya yarda Ummi bata sonta even though bata mata wani abun dake nuna tsantsar kiyayya ba, sai dai kuma bata taba nuna mata tsantsan soyayya ba, bata yi mata gatan da ta yi ma Emily ba, bata kulata kamar yadda take samun labarin tana kula Emily ba. Kuma a yanzu ma ita ce ta cilastawa Aliyu juya mata baya bayan ta wulakanta a gidanta. Amman zancen Aliyu be sonta, sam hankalinta ba zai dauka ba, ta san mijinta yana sonta, domin mai ɗaki shi ya san inda yake masa yoyo, ta san waye Aliyu ta san irin zaman da ta yi da shi, ta san rigimarta da yadda take kureshi kuma duk ya daga mata kafa, ta san yadda yake nuna mata soyayya ciki da waje. Wannan na daya daga cikin dalilin da ya saka take hango yadda zata yi rayuwa da wani wanda ba shi ba. Yan'uwanta a kullum cikin nuna mata yadda zata walwala su ninka arziki da karfi a siyasa suke idan ta yarda ta auri abokin mahaifinsu. "Ni gaskiya ya min tsufa ga mata ga yara, ni ba ta siyasar ko kudinsa nake ba" "Matsalata da ke baki iya daukar shawara ba, ga kuma rashin hangen nesa, ai ko dan ki bawa Aliyun da uwarsa haush da ma matar ya kamata ki aure shi, kullum su yi ta ganinki gaban tv komai za'ayi sai da ke, idan kika yi hakuri ma kina gidan sai ya sake su ki koma ke kadai sai yayan da za ki haifa, ke yanzu ni ban isheki ishara ba? Yau ina Baraka ina Yayanta suke? Sai dai idan ubansu yayi marmarin ganinsu ya je ya gansu ko ya aika musu da sako, ni ko ganinsu ma bana jin yana zuwa yi, domin ko jiya da na masa maganarta cewa yayi na daina tuna masa da ita, na ce ranka ya dade ai dole na tuna maka saboda akwai yaya a tsakanin sai ya ce yara idan suka so ganinsa sun san inda yake ai, shi dai hakkin dake tsakaninsa da su ya kula da cinsu shansu da kuma sauran hidindimun rayuwa, ke har cewa yayi ba dan kar dawowar nan ya zama matsala a gareni da su ba sai ya karbe yaransa sun dawo nan, ni kuwa na yi karaf na ce a'a ya bar mata yaranta ta rike, toh ina zan iya da rikon balagagun yaya?" Tana magana tana tsire baki dadin ya isheta, yanzu Mama Baraka da yayanta basa gidan. Ta shafa kanta yarta. " Shiyasa nake son ki fitar da miji ki yi aurenki ki manta da wani Ali, daman can ba ku dace da juna ba, balle kuma yanzu da ya auri shegiya, kuma yar Baraka, ko dan ke na san dole ta aura masa ita, kuma abun kamar ba na banza ba, kin san lamarin yarbawa fa, in ba shi ba yaushe Aliyu zai auri shegiya? Ko da tana da kyau ai Asali wani abu ne mai girma, ko dan yayan mutum" "Daman ita ta lalata komai gurinta nake tafiya neman shawara lokacin da muna samun tsabani kuma ba ta ba ni shawarar kwarai har cewa take ba laifin yarinyar ba ne, ashe saboda ta san yarta ce" "Eh mana, dan Allah ki bawa maraɗa kunya, ki zabi mijinki ki yi aurenki ga ki tsaye da kyau zaune da kyau son kowa kin wanda ya rasa, idan ma ba ki som shi His Excellency ki zaba cikin masu son ki mana, daman Alhaji yace tun da yayi maganar be sake ba, be zama lallai sai shi ba, ki zaba wanda kike so ki ba shi dama idan vaki bada daman ba baza ki iya kawar da tunani da damuwa a ranki ba, amman fa karki dauko ɗan makiyinmu kuma, karki mana na Aliyu, yanzu kam ba za mu bari ba ma" Ta kwnatar da kanta a cinyar mahaifiyarta. "Ki taya ni da addu'a Hajiya Allah ya sauya abun da nake ji a zuciyata kuma ya zaba min inda zan samu kwanciyar hankali da zaman lafiya, duk masu mata ne, samarin sun ki zuwa wai ko dai dan na yi aure ne?" "Aa ina ruwan aure da samarin, ke yanzu baki san an fi son zaurawan ba? Kuma saurayin zai iya zuwa, amman dai mun fi son mai kunbar susa, kin san logi be kin dadi, ba mu ki ace surukanmu duk manyan mutane ne ba, su kuma samari nan wasu ba rikon aure ba wasu kansu babu komai ciki sai tunanin abubuwan da ba su za su gina gobensu ba, kadan kake samu na kwarai, yanzu ba ga Aliyu ba? Amman da ace wanda ya san ciwon kansa kika aura inda ba shegen zamani ba ne, babu ruwansa da wani hango wata sai hada hadar kudi, ina za su shigo ina suka fita, daman duk abun da iyaye ba so babu albarka a cikinsa, shiyasa Aliyu ya zama haka" Hausawa suka ce wanda ya cika da yaƙi ya mallakeka har ƴaƴanka, babu yadda Kameela iya bayan bin shawarar mahaifiyarta da yan'uwanta matukar tana son zama lafiya da su, kuma ta shirya samawa zuciyarta salama. Abun babu dadi kam amman dole ta daure a haka ta budewa masu kwankwaso kofarta dama, ko labarin zai sauya. Tun da wadanda take dakon zuwa sun manta hanya, wato marar mata da yaya ko kuma saurayi, har yau bata samu ko daya ba, masu matan ne dai suke ta kawo mata hari, daga mai daya, sai biyu har da mai uku yana nema ta hudu da ita tsabar sun raina mata wayo. [8/31, 11:54 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 7️⃣4️⃣ 🌟✨ TALIYAR HAUSA – YAR MURJI ✨🌟 🥘 “Abinci na gargajiya, ɗanɗano na musamman, jin daɗin iyali!” 🥘 Idan kina/kanason abinci mai ɗanɗano na musamman wanda zai tunatar da kai daɗin gargajiya, to babu kamar Taliyar Hausa – Yar Murji! Wannan taliya ba wai kawai abinci bace, al’ada ce mai haɗa iyali, ƙauna da jin daɗi a teburin gida. ✨ Me yasa za ka zaɓi Taliyar Hausa – Yar Murji? • ✅ An yi ta da tsafta da inganci • ✅ Ta dace da kowanne irin miya: miya mai ƙwai, miya taushe, ko miya mai ƙyauƙyau • ✅ Sauƙin dafawa – cikin mintuna ka samu abinci mai gamsarwa • ✅ Lafiyayye, mai sauƙin narkewa, kuma ya dace ga kowa cikin gida • ✅ Za ka iya amfani da ita wajen girki na yau da kullum ko kuma na musamman 📍 Muna a Kaduna – amma ɗanɗanonmu ya zarce iyaka! 🚚 Ana kawo muku duk inda kuke a Najeriya (delivery guaranteed). 💛 Idan kana son jin daɗin abinci na gida wanda ke haɗa zuciya da iyali, to

Chapter 59 of 63