Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
abun kawai sai na zabi sauwake mata domin samawa kaina salama" "Aiko gashi yanzu abun yana cinta, babu safiyar bata aiko min sako ban hak'uri, ni kuwa ko ba ni da rai Wallahi ba zaka zauna da Kameela ba, yarinya ta yi yunkurin kasheka kiri kiri sannan ga iyayenta ba son auren suke ba, tun farko ni damam na runtse ido ban ga kyau a makanta ba, domin iyayenta ba masu dattako ba ne, kai kuma ka tsaya kai da fata ai ita tana sonka tana da tarbiya, ga abun da ta haifar maka ai, daman yaushe iyaye za su bada shawara aki bi kuma a ga daidai?" Aliyu yayi dariya. "Yanzu dai ba zan sake zabar mata ba, ke zaki zabar min" "Aa kai da kanka zaka zabo, ni nawa bincika ne da duba dacewa" Ya mike tsaye ya nufi kitchen ya bude firjin ya dauko ruwa ya kafa gorar a baki ya sha, sannan ya fito rike da ita ya dawo falo ya zauna. "Ni yanzu ban san ya zan yi na shirya tsakaninsu ba" Ummi ta dauke kanta daga kan wayarta ta kalleshi. "Ina ruwanka da shirya tsakaninsu? Dan iya? Tun farko daman ai bata son Turhan din, kuma sai ga shi yayi mata abin da yayi ta ji ta tsane shi, kai kasan yadda mutum yake ji idan baya son wani kuma ya zo ya kara zalintarsa? Kai da ka gode Allah auren soyayya kuka yi da Kameela, haka din ma yanzu da ta yi maka ba daidai ba yanzu ya ka ji? Ka ce ta komawa mijinta ta ga kamar kana matsa mata? Yarinya ta sha wahala yanzu har bada son wari maza ai ta ma yi kokari da take kallonka, da ni ce ko hanya ba zan sake hadawa da namiji ba, idan ta ga wanda take so har zuciyarta ita zata yi magana, kuma ni yanzu ko mijina tace tana so ai sai na tattara ni da kai mu bar mata gidan ita ma ta samu jindadin rayuwa" Aliyu ya kyalkyale da dariya. "Ummi Allah ya bar min ke, duk matar da zata yi kishi da Ummi ai sai ta shirya, taya ma Emily zata ce ta so Daddy" Ummi ma ta yi dariya. "Aa wai a misali dan na nuna maka ta cancanci farinciki, kuma kishi da ni wata wahala ce? Ni fa ba zan cutar da kai ba, kuma ba zan zuba ido ka cuce ni ba, magana kuma a fada min daya na rama da goma" "Aa ni ba tsakaninta da Turhan zan shirya ba, tsakaninta da Ammy, tsakanin Emily da Turhan wannan wani abu ne da kowa be kamata ya saka kansa ba" "Yanzu na ji maganar hankali, Allah ya bata wanda zai riketa amana mai sonta tsakani da Allah kuma babu cutarwa" "In Shaa Allahu, daman ai bayan wuya sai dadi, kuma Allah da kansa yace dukkan tsanani yana tare da sauki" Ya sake kurba ruwan ya aje ya mike tsaye ya haura sama. EMILY POV. Tun bayan tafiyar Mama Baraka Emily bata fito ba sai da Ummi ta shiga ta lallasheta, da kalamai na karfafa guiwa ta fada mata yanzu ai komai ya wuce, be kamata ta rika tuna baya ba, kamata yayi ace ta fuskanci gaba. Da lallabawar Ummi Emily ta samu gwarin guiwar cin abinci ita da Fatima ta shiga ta yi wanka ta saka doguwar rigar Atamfa, sai Ummi tace ta fita ita da Fatima waje su bawa itatuwan gardens ruwa, daga bada ruwan ne ta fara jika Fatima tana dariya, sai Fatima ta yi mata gwalo ta boya a bayan itace ita kuma tana binta ta watsa mata ruwan, sai nishadi take kamar ba ita ce ta gama kuka dazun ba. Tana rike da tiyo ta ji kara bude karamin gate din da aka saka a gurin sai ta juya idanuwanta suka yi arba da Ammy. Emily ta dan rage murmushin da take tana kallon Ammy har ta karaso kusa da ita, Fatima ta fito daga inda ta boya da sauri ta rumgume Ammy tana mata oyoyo. "I miss you" Ammy bata damu da tufafin a jike ba ta daga ta sama ta hade da jikinta. "i miss you too, ya kike rabin rai na" "Lafiya lau, ina Dady" "Yana can bakin gate cikin mota gidan kin fita zaki gan shi" Ta sauke ta kasa Fatima ta zura da gudu tana murna ta fita gurin. Emily ta saki Tiyon hannunta. "Ina wuni Ammy?" Ammy ta yi murmushi. "Lafiya kalau yata, ya mai gudun uwarta, kin dawo lafiya?" Emily ta yi murmushi. "Lafiya ƙalau" "Ina kika shiga kika boya? Kin daga mana hankali, kin dagawa Turhan babu inda be shiga nemanki ba har gurin da kika zauna kamin ki haifi Fatima, ita ma Fatima bata bar mu mun huta ba" "Yanzu ai na dawo, komai ya wuce Ammy" "Haka ne sai dai a fuskanci gaba, fatan dai babu wata matsala yanzu ko?" "Babu" "Tohm Alhamdulillah haka nake son ji, yanzu hankalin Turhan zai kwanta na yarki ma ya kwanta ni ma kuma sai na samu farinciki" Emily ta yi shiru bata ce komai ba. "Jiya Turhan be yi bachi ba, gaba daya ya bi ya damu saboda ba shi ya gano inda kika shiga ba, tare da shi muka zo na ce ya jira na fara shigowa na yi magana da ke, kin san saboda Aliyu baya son shigowa gidan nan" "Ammy akwai abun da nake son na fada miki" Emily ta fada, sai Ammy ta kara matsawa kusa da ita. "Ina jinki yata" "Mu zauna a can" Suka nufi gurin da kujerun zama suke suka zauna Ammy ta dora jakarta kan teburin. "Da farko da zan fara da miki godiya, na abun da kika min ni da ɗana a shekarun baya, na rike ni ba tare da kin sani ko kin san inda na fito ba, na gode Sosai, hakan ya saka ni auren Turhan da nufin na rama alheri da kika min, har abubuwan da suka faru suka faru, kowace jarabawa a rayuwa darasi ce ta kan koyar da kai wani darasi ne da baka sani ba, na kara jirmama abun da kika min ne da sanin muhimmanci a yanzu da Mahaifiyata ta bayyana" "Mahaifiyarki?" Ammy ta katse ta sai Emily ta daga mata kai Idonta na cika da hawaye. Ta tsakura mata abubuwan da suka faru. Emily ta rika hannunta. "kin yi kokari da kika rika ni, kika taimaki ɗana, a lokacin da mutunen da ya rabo ni da inda nake samun walwala ya wulakanta ni, danginsa suka ki ni, na rasa inda zan dafa, na gode Ammy na gode" Ammy ta yi murmushin jindadi. "Alhamdulillah da kika fahimci haka, ko kadan bana nufin cutar da ke, hada aurenki da Turhan ma ban yi dan cutar da ke ba, na yi ne da nufin sama miki mafita ta mijin aure ni kuma na samu mafitar ɗana a kusa da ni, idan har ina nufin cutar da ke taya zan aura miki dan da ni na haifa da ciki? Shiyasa da na fahimci akwai matsala na sauya masa na kasa saurarensa a dolensa ya bazama nemanki, gashi yanzu har ya gane kuskurensa yayi nadama babu abun da yake nema sai hada kan iyalinsa guri daya, kuma ina fatan zaki fahimce shi zaki yafe masa, ki yarda da shi ko dan yarki" Emily ta saki hannunta. "Yara ba su kai su hana iyaye farinciki ba Ammy, su yanzu suke tasowa rayuwarsu suke ginawa, shiyasa mahaifiyata bata bar farincikinta saboda ni ba, balle kuma ni da na yi ma Fatima komai da uwa zata yi ma yarta, idan har zan yarda a yanzu farincikin Fatima ya hana nawa hakan na nufin ni ban gina rayuwata ba kenan, abubuwan da suka faru sun faru kuma na ba su baya a yanzu, amman ba zan bar farincikina saboda Fatima ba, ba zan sake kuntata ma kaina sabida kowa ba" "Hakan yana nufin babu wani gyara tsakaninki da Turhan?" "Babu Ammy, ni ban taba son Turhan ba, har yanzu ban ji wani abu akansa ba, kuma bana tunanin nan gaba zan ji, yanzu idan har nace zan sake zama da shi to ni ce zan cutar da shi, kuma na cutar da zuciyata to miye amfanin haka?" "Aisha ni kika kalli kwayar idona kika fada min baki son ɗana?" "Ki yi hakuri Ammy, kin san inda na fito kin rayuwar da ni, ke ma kin yi makamanciyar tafiya irin tawa, miyasa ba za ki fahimce ni ba?" "Saboda mahaifin Turhan be yi nadama ba, har yau be nemi ni ko neman afuwata ta ba, amman ke Turhan ya gane kuskurensa ya tuba kuma ya shirya faranta miki har hawaye ya zubar akanki, ya kauracewa abinci, bachi ma baya wadatarshi, da ace saboda Fatima ne kawai ai ba zai waiwaiyeki ba tun da ya same ta, amman saboda yana son ki yana son farincikinki ya kasa hakura, ki ba shi dama Aisha dan Allah" Emily ta girgiza kai. Sai Ammy ta kama hannunta ta rike. "Haba mana Aisha, ɗana na cikin mawuyacin hali saboda ke, ba shi kadai ba, Khaleefa ma ya munana miki iyayensa ma sun munana amman ni ban miki ba, miyasa ba zaki yafe masa ba, ki ma dakinki ki rumgume yarki da ke son Babanta? Duk wani sharadi da zaki gindaya mana ni na miki alkawarin za mu dauka" Emily ya sake janye hannayenta. "Ba zan iya ba Ammy ki yi hakuri, ba zan iya rayuwa da mutumen da ya shigo dakina a daren aurena ya tofa min yawu a fuska, ya kalli kwayar ido ya kira ranar da aka daura mana auren da bakar rana a gurinsa, ya shiga da ni gidansa a matsayin baiwa, yana kallo nake goge inda matarsa take takawa, yana sane ake dokana, be damu ya ba ni abincin da nake iya ci ba, ban taba dandanar dacin rashin magana ba sai da na auri Turhan, kuma ba dan bana iya maganar ba, sai dan ya gabatar da ni a matsayin kurma kuma ya saka min sharadin kar na kuskura na yi magana, a gidansa ban isa na saka kayan da nake so ba sai uniform din bayi, ban isa na kwanta a inda nake so sai tare da hadiman matarsa, ya kira ranar da ya kusance ni da bakar rana, ya fada min ba zai taba so na ko son abuj da na haifa ba, mutumen da yayi min duk wannan taya zai dauke ni a yanzu ya nunawa duniya yace ina da daraja? Ai ya gama kwance min zane a kasuwa kowa ya ga tsiraicina, Turhan ya haihu da ni kin samu jika har gobe ban isa na goge wannan ba, Ammy haka ma ya wadatar..." Ammy ya mike tsaye ba tare da ta kara cewa komai ba ta fice daga gurin. Emily ma ta mike tsaye ta nufi wani ice ta dafa shi da hannu daya dayan hannun kuma ta dafe kanta tana jin babu dadi na tunawa da rayuwarta ta baya. Tana tsaye a gurin bata motsa ba ta ji an kira sunanta "Aisha?" Ta juya ta kalli Turhan dake doso inda take tsaye hannayensa rumgume a baya yana tafiya daya bayan daya irin ta jinin sarauta. Ya tsaya gabanta yana kallonta daga sama har kasa for the first time ya ga kyauta irin kyaun da be taba ganin ta yi ba sai yau, duk kuwa da babu kwalliya a fuskarta, sai kuma kwarjininta ya kama shi gabansa har faduwa yake da take kallonsa ido cikin ido kallo irin na wanda ya tanadi amsar kowace tambaya. "Za mu iya yin magana da Allah?" "Yau kai ne kake neman izinina akan wani abu?" "Haba ki bar abin da ya wuce ya zama ya wuce mana Aisha! Na yi kuskure na sani kuma na karbi kuskurena, ke ma a yanzu kina cikin kuskure na barin wanda ba muharraminki ba yana kallon surar jikinki da kyaunki yana magana da ke yana jindadin muryarki, be ma kamata ki zauna a nan ba shiyasa duk abun da na fada ba fahimta kike ba, saboda ba zai taba bari ki fahimce ni ba, kuma ba zaki gane hakan ba sai nan gaba." "Na fada maka wani? Aliyu ya fi min kai amfani sau dubu, shi be taba fada min magana marar dadi ba, be muzantani ya fada min magana marar dadi ba, be doke ko ya saka a doke ni ba, be kira ni fasika ba, da na ba shi labarina be musa ba, ban roke shi alfarma ya gagara yi min ba, be yarda an wulakanta ni ba, ne gan ni a cikin damuwa ya bar ni balle har ya jefani a ciki, dan haka ba zan yarda wani ya fadi wata magana marar dadi akansa ba" Turhan ya hade wani abu mai daci da tsayawa rai yayi murmushi. "Ban zo nan saboda wani da be kamata ko sunansa na furta ba, na zo ne nan ne saboda ni da ke" "Babu wani abu tsakanin ni da kai, zama ne dai ada mun yi yanzu kuma ya kare, idan har zaka zo mu tattauna wani abu to ya kasance akan Fatima and Only Fatima" "Aisha miyasa idonki ya rufe har haka ne? Mu fa iyaline be kamata kina haka ba, ki yi hakuri da duk abubuwan da suka faru na san ban kyauta ba ina neman afuwarki ki yafe min dan Allah, Wallahi na yi nadama, kuma na yi bakinciki abubuwa na da na yi miki, ina neman afuwa, kuma na miki alkawari hakan ba zai sake faruwa ba" Ya bata fuska sosai kamar zai mata kuka. "Na yafe Turhan, that's okay zaka iya tafiya ka yi rayuwarka" Ya kalleta da sauri domin be yi tsammanin zata yafe masa haka da sauri ba. "Kin yafe min Emily? Zaki koma zama da ni kenan?" "I forgive, never forget ba za mu sake zaman aure ba Turhan, na kasa manta abubuwan da ka yi min, ka fada min ba zaka taba kaunata ba wannan ya zauna a kaina" "Baki yafe min ba kenan, indai kin yafe min to zaki yarda ki zauna da ni ne Aisha, Fatima ma zata yi farinciki, idan har baki yarda kin aureni ba zan shiga mummuna hali Aisha, Wallahi ba ina fada miki haka saboda kan karya ba ne, har cikin raina ina kaunarki Aisha, kuma ina son zama da ke, idan kika guje min ban san iya halin da zan shiga ba, Wallahi ba dan ke ba, ba zan taba tako kafata a cikin gidan nan ba, ni yanzu damuwata ki amince da ni ban damu ko kina so na ko baki so na ba! Zan iya zama da ke a kowane hali, Aisha karki ba ni kunya a gaban makiya dan Allah, don't break my heart please" "You broke me first.... Shin baka yi tunanin ya abun yake da zafi ba? Ni ma a yanzu ban damu da duk wani zafi da zaka ji ba, ka tafi ni dai na yafe maka amman zama a tsakaninmu ya kare" Ya lumshe ido ya rasa ina zai saka kansa ya zai yi Emily ta fahimceshi. Emily ta wuce shi ta fice daga gurin, tana shiga falon ta samu Ammy zaune ita kadai a falon Fatima na saman jikinta, kallo daya Ammy ta yi mata ta san ɗanta be samu nasara ba. "Momy nace dady ya dawo nan mu zauna tare gaba daya, ya fi dadi kina nan Ammy ma ta zo ga Uncle Aliyu ga Dady ko?" Emily ta girgiza mata kai. "Aa Dady zai zauna gurin Ammy, idan kina so zaki je ki gan shi" Sannan ta kalli Ammy ta ce. "Ammy na gode da ziyara, zan haura sama" Ta nufi stairs, Ammy ta bita da kallo har ta haura sannan ta sauke fatima a jikinta ta kama hannunta. "Fatima muje ko?" "Aa ki tafi sai gobe zan zo" "Baki son gurin Daddynki?" "Ina so gobe zan zo tare da Momy" Ammy ta saki hannunta ta fice rai a bace. [8/6, 11:10 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *©️ Khadeeja Candy* Page 6️⃣4️⃣ Ammy ta same shi zaune a motar cikin wani yanayi marar dadi. Bata ce masa uffan ba shi ma be furta komai ba yaja motar suka kama hanya sai da suka isa gida ta bude motar ta fita sai ya ji shi ya kasa fita, yana mamakin yadda Aliyu ya shige masa hanci, haka zai zura ido wani katon banza yana kallon masa mata? Yana jindadin yayi nasara akansa? Miyasa wai tun farko be yarda girmama zabin mahaifiyarsa da yanzu duk be samu wannan matsalar ba. Ya dade a zaune a cikin motar sannan ya fita ya shiga falon ya zauna, Ammy ta kalleshi cikin tausayi da kuma bacin rai ta ce. "Turhan ka hakura da yarinyar nan, tun da ba mata suka kare duniya ba, ka nemi yafiyarta kuma ka kwatanta kyautata mata Alhamdulillah, a haka ma Allah ya maka albarka, kana da mata ka rike aurenka ka koma a can ka cigaba da harkokinka idan kana bukatar ganin Fatima ka dawo ka ganta" Turhan yayi shiru na lokaci kamin ya ce. "Ammy kin cire rai da dawowar Aisha ne?" "Babu amfanin mu yi ta bibiyarta tana wulakanta mu, sai kace kanta farau wulakancin ɗa namiji na ga mazan da suka fika wulakanta matansu kuma matan ne ma suke neman mazan su zauna da su balle kai da har ka gane kuskurenka kuma ka nemi yafiya? Wai yau ni Aisha zata kalli kwayar idona ta fada min bata sonka. Sai binta muka tana da juya mana baya kamar autar mata" "Aisha fa bata da laifi, laifin Aliyu ne, saboda shi ya fara ganin ta kuma ya shirya mata abun da ba gaskiya ba ya dorata a kai, gashi kuma yanzu tana gidansu su suke kitsa mata komai" "Idan da su har da ita, ai ba jaririya bace balle ace saka mata magana ake a bakinta" "Wallahi Ammy Aisha bata da laifi, laifin duk na shegen katon banzan nan ne Aliyu, kuma da yarda Allah sai na ba shi mamaki" Ammy ta sauke dogon numfashi. "Da zaka hakura da ita da zai fi, tun farko rashin daukar shawara ne ya jefaka a cikin halin da kake ciki ai, da na aura maka ita miyasa baka rike ta ba ka bi son zuciyarka? Da duk haka bata faru ba kuma da yanzu Allah kadai yasan yara nawa ta haifa maka, yanzu kuma idonta ya bushe bata ganin kowa kai kuma ka dage sai ka zauna da ita, ko zaman kuka yi auren ba zai muku dadi ba saboda bata ganin mutuncinka yanzu bata ganin girmanka" "Ni ne mai laifin ai na sani, shiyasa yanzu nake kokarin ganin na gyara laifina, ko na yi kamar zan hakura idan na tuna da Aliyu ba zan iya hakura ba Ammy, hankali ba zai kwanta ba sai idan na ga ta yi aure kuma ba shi ta aura ba, shi ma kuma idan ba zata dawo min ba" "Ai Aliyun ma da wuya ya aureta, kawai dai kai suke son gasawa aya, shi da yake da matarsa ma, dole shiryawa za su yi, idan ka yi hakuri kana nan Aisha zata nemeka, ni na san Ummi ba zata yarda Aliyu ya auri wannan yarinyar ba, ita hauka ce take dibanta" "Ammy saboda kina mace ne, ba zaki gane ba, Aisha ta kai duk inda mace ta kai babu wanda zai ganta be ji yana sonta ba" "Tohm sai ka gwada naka kokari, ni dai daga bakin nan na cire hannuna" Turhan ya ji babu dadi. "Wani abu Aisha ta fada miki ne Ammy? Kamata yayi ki goya min baya, duba yadda Ummi tana bin bayan danta duk kuwa da cin amanar da yayi, na tabbatar da ni ce ba zaki yarda na dauko Kameela matar Aliyu na aje a nan ba" "To me zai saka ka yi haka? Ka nemi wata ka aura idan har kana son auren ne" "Aa Aisha dai, idan ba ita ba..." Yayi shiru takaici ya saka Ammy tashi ta bar masa falon. "Aifa sai dai a mutu, amman ba zan taba yarda Aliyu yayi min wannan cin kashin ba, bayan ya gama da ni ya rabi matata Allah kadai ya san abun da ya faru kuma yanzu yace wai zai aureta saboda kawai bakar kiyayya ba tare da na masa komai ba" Ta juya fuska. "Ita ma dai wani lokacin da matsalarta da gaskiyar Ammy, ni ban ce ta raga min ba, amman ta daina sake jiki mana da wannan katon kwarton, ji yadda ta kyau dan Allah haka zai sakata gaba yayi ta kallo, macuci" Ya hade yawu da karfi, ya saka hannunsa yana karawa rigar wuyansa fadi kokarin yagata take, yana jin kamar numfashinsa na danne, bani irin kishin Emily yake ji har na bala'i EMILY POV. Misalin karfe 9pm tana zaune falo Ummi na kara mata wasu darussan na rayuwa, Aliyu ya sauko Fatima na janye da hannunsa. Da suka kawo kasa sai Fatima ta sake shi ta nufi Emily ta kama gashinta tana yaryadawa a bayanata. "Momy Dady yace in dinga rufe miki jiki" Emily ta juyo ta kalleta, Ummi ta yi murmushi bata ce komai ba, Aliyu kuma ya kalli Emily kadan ya dauke kai. "Uncle Aliyu yace zai koma gidansa gobe, Momy zaki je? Zamu koma can ne kuma? Miyasa ba zamu zauna gidan Dady ba, Ammy tana sonki da Dady sai mu koma can har Uncle Aliyu ko?" Ummi ta kalli Aliyu dake gefenta. "Ina zaka koma" "Gidana dake nan Ummi, zan fi jindadi, kuma yana da kyau mu kiyaye dokokin ubangiji" "Hankalina zai fi kwanciya ka zauna a nan, kwantarka ake ne zaka koma can? Ina jin nan da sati biyu ma za mu koma Abuja gaba daya" "Aa Ummi indai kika ce zaki sama min masu tsoro zan yarda shi ma saboda ki zamu kwanciyar hankali ne, amman Addu'a ta ashe ni, zan koma can In Shaa Allahu" Emily ma ta kalleshi tana jin babu dadi ganin take kamar idan baya cikin gidan ba zata sake sosai ba, yanayin ya sauya har ta kasa boyewa ta cire gashinta dake hannun Fatima ta mike tsaye ta bar falon. ONE WEEK... Ba banza aka bar Aliyu ba, daman fa yarbawa sun iya mugun abu, idan ba haka ba taya Aliyu zai sake ta, daga kawai ta kai yarinya gurin Babanta, gashi har ya fadawa Ummi ta saka guba a abinci, ko Ummi bata nuna mata bata son zuwanta gidan ba ta san ba zata sake aminta da ita ba, gashi yanzu ko zuwa gidan bata son ta yi. "Kai gaskiya ba banza ba, kalli ko Bakar Barakar nan dan ba zan ce Mama ba ni bata haife ni ba, kamata yayi abbah ya koreta gaba daya daga gidan nan kamar kare, amman be yi ba sai saki daya yayi mata har da cewa wani wai baya son kowa ya fitar da maganar ta yi zaman yayanta, yana nufin zai maida ita kenan, shiyasa take ta shige min tana kiran Aliyu tana wani bani shawarar munafukai, ashe ta san Emily yarta ce shi take hangowa" Magana take da kanta tana ta safa da marwa tana dora hannu a kai tana saukewa, ita a yanzu babu tashin hankalinta kamar yadda Aliyu ya juya mata baya, sakonta be reply ya bi yayi blocking din number ta ma, Ummi ma bata amsa mata idan ta kira kuma bata maida mata da amsar sako, gashi yanzu Aliyu gida daya suke rayuwa da Emily. "Wai to shi wannan Turhan din in ban da sakarai ne shi haka zai zuba ido wani ya karbe masa mata? Ayi mutum kamar dusa, wannan bakin ciki ina zan kai shi? Wallahi Aliyu be ma dace da yarinyar nan ba, ga kafirci ga shi bata hanyar aure aka aureta ba" Ta fashe da kuka ta sauke hannu ta sake dorawa, haka take kowace rana ta saka wannan ta kwance waccan ita kadai domin yan'uwanta babu mai tayata gaba daya ma basa son zancen Aliyu, su sun ji dadin haka daman ba sa son aurenta da Aliyu gashi yanzu an rabu kuma sanadin haka Abbah ta saki Mama Baraka, Hajiya sai shiga da ita take na balmar baka tana son mijinta ya kori Mama Baraka daga gidan gaba daya. Kuka Kameela ta ci sosai ta rasa ina zata saka kanta, ko ba Emily ba ba zata so Aliyu ya so wata ba balle kuma Emily, mace da ita kadai ce ta hana ta walwala ta kuma rabata da mijinta, kuma sanadinta ta sakawa mijinta guba gashi

Chapter 51 of 63