Chidimma bata nan ki zuba min abinci"
Fatima ta fada a tsawace kamar yadda ta saba yi mata magana cike da rashin tarbiya. Sai dai ko kadan hankalin Emily baya gurinta tana gurin sakon da ta karanta, bata san waye ba, bata san sakon miye take da shi a waje ba. Kamar ya san tsoro take ji sai ya sake aiko mata da sakon sunansa.
"Aliyu ne, sakonki yana waje"
When she read the name sai ta ji she's safe ko da yake bata da tabbacin shi din ne ko Vito yake shirya mata wani abu? Ko kuma matar Aliyu dake neman rayuwarta. Ta sauka daga kan gadon da kafafuwanta dake sanye da safe ta fito dakin Fatima ta biyota bayanta. Ta isa gate din ta bude da kanta ta fita sai ta ga motar Aliyu fake nesa da gidan amman tana facing din gidan. Fatima ta janyota da karfi cikin ihu tace.
"Na ce miki yunwa nake ji yunwa nake ji baki ji ne? I hate you"
Emily ta kalleta kamar mai tsoronta.
"Okay"
Ta juya zata koma Aliyu ya bude motar ya fito ya doso inda suke tsaye, Fatima na ganinsa a take fuskarta ta cika da murmushi sai ya ware mata hannayensa ta je ta gudu ta rumgume shi ya daga ta sama.
"I miss you"
"I miss you too, ina ka tafi kwana da yawa?"
Ya sauketa kasa yana kallon Emily da ta yi rama sosai
"Ina nan, aiki ne yayi mana yawa, shiyasa na zo nace mamanki ta shirya ta koma aiki, kin ga da tana zuwa aiki ai kullum za mu rika haduwa ina siya miki chocolate da ice cream ina kaiki yawo"
"Mi kake yi a nan?"
"Na zo na fada miki ki shirya gobe ki koma aiki, office dinki yana nan yana jiranki, amman ba a karkashin Amal zaki yi aiki ba a yanzu, idan kuma baki ra'ayin aikin motarki tana nan kije gobe da kanki ki dauka karki aika kowa"
Ya rage tsawonsa ya mikawa Fatima key din motar.
"Ki bawa Momy"
Fatima ta karba ta mika mata.
"Good girl, ga ki kyakkyawa ga ki da jin magana to miyasa kike yi ma momy tsawa?"
"Na ce ta zuba min abinci bata zuba min ba"
"Okay amman ba a yi ma uwa tsawa, saboda ni da ke ai musulmai ne ko?"
Ta daga kai.
"Yauwa shiyasa kike burge ni, kina da saurin fahimta da ganewa, ga wayo"
Ta kyalkyale da dariya.
"Mu musulmai bama ma yima iyaye tsawa, muma musu ladabi da biyayya ne, idan kina son mu zama friends ni da ke toh karki sake yi ma Momy tsawa, baki ganin ke kadai kika rage mata ma? Tun da London be nan? Ki daina cewa i hate you idan wani yace miki haka zaki ji dadi?"
Ta girgiza kai ta turo baki.
"Ita ma bata sona bata min abun da nake so? Ko London ya mutu yanzu amman bata ba ni sunan Babanshi ba, yan makarantar mu suna min dariyar sunana na mata ne duka uku, ka gani Fatima Emily Aisha"
"Sunana ne kawai matsala? Idan Momynki ta dawo aiki zan dauke ki mu tafi makaranta a canja miki suna daga Fatima Emily Aisha zuwa Fatima Aliyu"
Farinciki ya cika fuskar Fatima.
"Da gaske? Ka yi alkawari"
Ya mika mata karamin yatsansa.
"Na yi ke ma ki min alkawarin ba zaki yi ma Momy tsawa ba daga yanzu, idan ma kin manta kin yi za ki bata hakuri"
Ta daga mishi kai sannan suka kulla Pinky promise.
"Okay now say sorry to your momy, ask for her forgiveness"
Fatima ta kalleta a shagwabe ta ce
"I'm sorry Momy please forgive me"
Aliyu ya kama kunnunsa yana daga kansa ya kalli Emily.
"Kin yafe mana ko Momy?"
Ya mike tsaye still yana kallonta.
"Please Unblock me, ina tunanin ban cancanci haka daga gurinki ba"
Ya shafa kan Fatima sannan ya nufi motarsa yana daga mata hannu, har ya wuce Emily bata motsawa daga inda take tsaye ba balle ta ce wani abu.
_______________________
Sannu ‘yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe ɗinki da kaya masu kyau, masu ƙima daga Khadeeja Candy Store
Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sauƙin sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing.
Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taɓawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet ɗinmu sun dace da ke
Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sauƙi ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko’ina!
Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1
da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0
Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame.
Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ƙayatarwa duk a farashi mai sauƙi.
Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu!
Baki da lokaci? Muna da sauƙin oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina!
To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08
Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store.
Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haɗuwa.
[5/21, 9:26 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
FOLLOW ME ON 👇🏻
FACEBOOK
https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914
TIKTOK
https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1
INSTAGRAM
https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0
CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01
KHADEEJA CANDY STORE
https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08
Page 2️⃣8️⃣
Sai da ta daina hango shi sannan ta juyo ta dawo cikin gidan rike da hannun Fatima dake ta tsalle da murna saboda Aliyu yace zai canja mata suna. Emily ta shiga falon ta nufi dining ta fara aje wayarta sannan ta zubawa Fatima abinci, ta ja kujera ta zauna ta dauki wayar ta duba number Aliyu ta yi unblocking dinsa.
"Momy ya sunan wannan oganki ma?"
Emily ta kalleta a hankali.
"Aliyu...."
Fatima ta yi dariya cikin farin cikin.
"Fatima Aliyu"
Emily ta aje wayar hannunta tana kallon Fatima, tausayinta ne ya fara zuwa a ranta ganin yadda take ta daukin samun sunan uwa ma kawai ba uban ba, to ina ga ace ubanta yana sonta yana ji da ita?
"Fatima ba zai yi ki karbi sunan wani ba"
"Saboda me?"
"Saboda baki da alaka da shi, he's just a stranger"
"He's not a stranger he's your friend, Momy ni ina son sunan"
"Na ce aa"
Fatima ta wulgar da plate din abinci kasa ta kalli mahaifiyarsa cikin kufula tana son ta yi mata tsawa tana tuna alkawarin da ta yi ma Aliyu, gashi tana tsoron kar Emily ta fada masa domin gani take kamar zata iya fada masa cewar ta yi mata tsawa, sai kawai ta fashe da kuka ta nufi dakinta, Emily ta bita da kallo kamin ta maida dubanta gurin wayarta kiran Tasmia ne ke shigowa, ta amsa kiran ta saka a Speaker.
"Hello"
"Emily ya kike?"
"Ina lafiya, kin tuna da ni yau"
"Daman kullum ina tunawa da ke, kawai ina jin tsoro ne, ina fatan kina lafiya"
"Ina lafiya Tasmia"
"Zaki iya shigowa yau mu gaisa?"
Emily ta yi shiru domin akwai abun abubuwa da yawa da take bukatar abokin tattaunawarsu.
"Eh gani zuwa"
"Amman karki bari ya san kin zo nan dan Allah"
"Okay matsoraciya"
Ta fada da murmushi sannan ta aje wayar ta mike tsaye, dakin Fatima ta fara shiga ta dagota daga kefen da take tana kuka.
"Zan fita yanzu zaki je?"
"Ba zan je ba"
"Ba zan barki ke kadai ba"
"Ni ba zan je ba"
Emily ta daga wayar kira Chidimma two miss calls bata daga ba, sai ta kira Tasmia.
"Zaki iya zuwa Tasmia ina tsoron tafiya na bar Fatima ita kadai, mai kula da ita bata nan kuma tace ba zata bi ni ba"
"Ina tsoron zuwa gidanki Emily"
"Ba abun da zai faru na miki alkawari"
Tasmia taja dogon numfashi ta sauke.
"Kin san fa har gargadi yayi min"
"Baya ma garin nan ya tafi gurin kasuwancinsa"
"Shi kenan, amman idan wani abu ya same ni, ke ce da alhaki"
"Na yarda"
"Idan na iso zan kira ki kin san mai gadinki be bari a shiga ciki"
"Okay"
Emily ta tashi ta koma falo ta zauna, after like 40min Tasmia ta kira wayarta ta sanar mata tana waje, Emily da kanta ta fita ta shigo da Tasmia suka shigo har cikin falon ta dauko mata ruwa da drinks.
"Kin yi rama sosai"
"Ba ni da kwanciyar hankali a yanzu ko kadan"
"Rasuwar danki, da kuma wannan mai gidan naki ko?"
Emily ta zauna kusa da ita.
"Kullum ina tuna London, ga kuma damuwar yadda gobe na zata kasance"
Tasmia ta dauke idonta.
"Aliyu yayi magana da ke kuwa?"
"Eh, na tarar da sakonsa na kira shi ban san wayar tana gurin matarsa ba, abubuwa sun faru"
Tasmia ta yi fuskar mamaki ta gyara zama.
"Ban fahimta ba, kamar ya?"
Emily ta fada mata abubuwan da faru daga lokacin da ta kira Aliyu zuwa yau da ya zo gidan.
"Amman ke yanzu kina ganin zaki koma aikin ne?"
"Ina da bukatar aikin Tasmia amman ina tsoron yadda zai kasance min domin a can din na akwai wanda ta tsane ni"
"Mu ga sakon da ta turo miki"
Emily ta cire password din wayarta ta mikawa Tasmia wayar.
"Ni dai a tawa shawarar karki koma aiki a gurin nan, saboda zaki haifar masa da matsala tsakaninsa da Matarsa, kuma tun da kika ji tana barazana zata iya miki komai ko ta yi ma yarki, idan ma aiki kike so ki nema a wani gurin kawai zai fi, tsakani da Allah ke kanki ba zaki so wata ta zo ta ruguza farincikinki da mijinki ba"
"Baki fahimta ba, ni fa ba soyayya ce tsakanina da Aliyu ba, ko ranar da kika ji yace miki rape dina yayi yana miki bakar magana ne kawai"
Tasmia ta dauki ruwan ta sha ta aje.
"Na sani, ai a yadda na san Aliyu ba zai taba iya auren..."
Sai kuma ta yi shiru.
"Mutum ne mai addini sosai, kuma kin ga ke a yanzu baki san ma halinsa ba, be kamata ki sake da shi ba, be kamata ki ba shi fuska ba, ni musulma ce amman ina miki tsoron wasu daga cikinmu, ke kina ganin haka nan kawai wani zan ganki da rana tsaka yace zai dauki sunansa ya lakawa yarki daga baya kuma ya zo ya miki gori ko wani abun ya biyo baya? Emily kina da kyau fa, kyaun ki nan yana jan hankalin maza akanki, ba zaki iya gane mai kaunarki da gaskiya ba sai wanda ya so ki ko ya taimakeki a lokacin da kike tsananin bukatar taimako"
Emily ta sauke ajiyar zuciya.
"Bana nufin kulla alakar komai da Aliyu, ni a yanzu ba ta wannan nake ba, ina girmamashi ne saboda abun da yayi min ba zan manta ba, kuma a yanzu ma ya taimake ni gurin rufe London, na lura yana da kirki kawai"
"Yanzu ke micece babbar matsalarki?"
"Vito, kuma ina son na dogara da kaina"
"Da alama baya son ki rabi kowa ko kuma kowa ya rabe ki?"
"Haka ne"
"Me zai saka ba zaki yi masa abun da yake so ba"
Kallon rashin fahimta.
"Ba sonki yake ba?"
"Eh"
"Toh me zai saka ba zaki aure shi ba?"
Emily ta sakar mata ido tana kallonta.
"A duk duniyar nan ban san wani mutum mai sonki ba kamar Vito, ban san yadda ya hadu da ke ba, amman alamu ya nuna yana kaunarki sosai, yana kaunar yayanki, idan ma kina son sauyawa yarki suna ki bata sunan Vito mana, kuma gashi yana da kudi yanzu an daina auren kyau ko wani abu auren kudi ake, gashi kuma addininku daya"
"Amman Fatima bata son shi"
"Fatima bata son shi ko kuma dai ke din ce baki gama gamsuwa da shi ba? Ai Fatima yarki ce zaki iya cusa mata abun da bata yi niya ba, haka kuma zaki iya nuna mata alfanun da yake cikin auren Vito, kuma idan kika aure shi hankalinki zai kwanta na shi ma zai kwanta duk wannan takurar da yake miki zai daina yinta"
Emily ta hade yawun bakinta ta wani bangaren Tasmia tana da gaskiya, sai dai kuma ta wani bangaren bata ra'ayin auren Vito saboda yarta Fatima da kuma halinsa da sana'arsa sai dai ba zata iya fadawa Tasmia bata son sana'arsa ba gudun kar ta bukaci jin wace sana'a yake yi.
"Idan har kika koma karkashin Aliyu kika yi aiki shi ma juyaki zai yi kamar yadda Vito ma yake yi a yanzu, kuma kin ga yana da iyali be kamata ki shiga tsakaninsa da matarsa ba, ko wace mace zata yi kishin ace namiji yana hulda da wata mace ko da ta gaisuwa ce, na san kin san yadda farinciki yake da tsada ba zaki so rusa na wasu ba"
Emily ta sauke ajiyar zuciya a karo na uku, tana jin gamsuwa da kalaman sabuwar kawarta Tasmia.
"Ki yi blocking dinsa, idan har ya damu yayi magana dake to ki ba shi number, yayi magana da ke ta hanyata, saboda gujewa wata rana kar Vito ya dauki wayarki ya gani, ko kuma shi Aliyun yayi miki abun da ba ki yi tsammani ba"
Emily ta dubeta.
"Miye banbanci magana da shi a wayarki da kuma tawa? Ina da iko da wayata, Vito be san password dina ba, kuma ke kika fada min idan ina son na canja dole sai na yi pushing idan na nuna masa har a waya ina tsoron ya ga wani abu ai zai zama abun kamar yayi min yawa"
"Eh toh haka ne, amman dai karki zake, kuma karki kuskura ki karbi aikin nan, karki sake bawa wani namiji damar da zai juyaki yadda yake so"
"Aikin aiki akwai abun da ya saka na ke sauraren Aliyu, shi ma akwai dalilin da ya saka yake neman sanin abubuwa akaina, baki san miye ba wata kila sai nan gaba?"
Tasmia ta dan yi jimm tana kallon Emily.
"Minene? Soyayya?"
"Aa..."
Turo kofar falon ya saka daga Tasmia har Emily suka juya sai suka yi arba da Chidimma.
"Sannu Ma'am, Oga Vito ne yace na dawo na shirya masa wani abu baya son abincin da aka girka yau"
Emily bata ce komai ba ta dauke ido, Chidimma ta wuce Kitchen Tasmia ta kalli Emily.
"Ba ke kike masa girki ba?"
"Da can na kan yi dan kaina ko yarana, amman yanzu ita take yin komai har abinci a guri daya yake ci da ita a yanzu, ina jin kamar yana son yayi replace dina ne da Ita ko kuma me ban gani ba"
"No ba zai taba son yar aikinki ba, bayan ma kin fita komai, kuma ai ta yi masa kaskanci ace ya so ta"
"Ni kin san yadda na ganki? Kin san yadda ya dauko ni? Shi ya mayar da ni yadda nake a yanzu har ake gani a yaba kyauna, shi ne kadai mutumen da ya so ni ba tare da duba asalina ko halitta ba, kuma har yanzu be taba nuna min jikina yake so ba, be taba min gorin komai ba, be taba nuna min gajiya akan kula da ni ba"
Tasmia ta dafa kafadarta.
"Irin wannan ne kike neman rabuwa da shi? Ai shi ya fi kowa cancantarki Emily, babu wani sakamako da zaki masa sai na aurensa, akasin hakan kamar kin butulce masa ne, kuma ina tabbacin amana ba zata barki ba, ki yi tunani akai"
Emily ta daga mata kai tana hade abun da ya tsaya mata a makoshi.
"Amman dawowa zai yi ne da ya ce ta zo ta girka masa abinci?"
"Yana nan daman, na boye miki ne saboda ki zo"
Tasmia ta ji yan hanjinta sun kaɗa ta mike tsaye da sauri gumi na karto mata, bata ko tsaya yi ma Emily sallama ba ta rumgumi jakarta ta nufi kofar falon ta bude Emily na mata magana bata kulata ba, da sassarfa ta isa gate tana samun ficewa sai ta ranta a na kare ta aina da gudu tana yi tana waiwaye har sai da ta yi nisa da gidan sannan hankalinta ya kwanta.
Emily ta dauki shawarar Tasmia na cewar kar ra koma aiki, duk kuwa da irin kyautatawa Aliyu zato da take, amman zai iya amfani da damar ya dawo da Turhan a rayuwarta ita kuwa a yanzu bata bukatar kowa, sai dai ta dayan bangaren ta san taba bukatar aikin haka ta kwana da tunanin yi ko bari har garin Allah ya waye bata samu matsaya ba.
Bayan Fatima ta wuce school, Emily ta shirya ta sauko rike da jakarta da wayarta, kallo daya ta yi ma Vito dake zaune yana karyawa ta dauke ido ta nufi kofa.
"Zaki je neman aiki ne? Har shaguna nawa zaki rika bi kina neman su dauke ki aikin da ke kanki zaki iya daukarsu? Idan har baki son kudi da nake aje miki ne toh a shagon siyar da talkami da kika nemi aiki ne, shi ma nawa ne, kudin dai still daga karkashina za su fito"
Ta juyo ta kalleshi ta dauke ido ta yi ficewarta. Da gaske gurin nasa ne ko kuma dai ya san mai gurin wata kila kuma yana mata barazana ne kawai saboda ya daureta a guri daya, har ta isa gurin aikin na su Aliyu bata daina tunanin maganar Vito da kuma Tasmia ba, ta duk inda zata auna Vito ya cancanci zama da ita, kuma sakamakon da zata masa na mallaka masa zuciyarta ne da yake bukata kamar yadda Tasmia ta fada, wata kila zata iya shawo kan Fatima ta amince da shi. Ta shiga gurin da ake aje motocin kamfanin tana duba motarta domin ta manta gurin da ta faka ta a wacan karon.
Sai da ta yi rabin gurin sannan ta ga motarta ta matsa key din hannunta ta bude motar a gurin da zata zauna ta yi arba da wata farar takardar dauke ta rubutu, hannu ta kai ta dauki takardar sannan ta shiga ta zauna.
"Idan kin riske sakon nan, ki shiga office dinki ki yi signing cewar kin bar aikin a hukumance kamar yadda kika karba a hukunce"
Ta daga kai ta kalli harabar sannan ta aje takardar ta fito motar ta rufe ta nufi cikin ma'aikatar, bata sha wahala gurin haura sama ba domin ba wannan ne zuwanta na farko ba, ta shiga Elevator har hawa na 4 ta fita ta doshi hanyar da office dinta yake, kallo daya ta yi ma kofar office din Amal ta dauke kai ta murda office din da yake zaman nata a da ta shiga.
Ga mamakinta sai ta sami Aliyu tsaye a gaban teburinta yana saka two cube of sugar a tea dake kan teburinta.
"Babu gaisuwa?"
Ya fada ba tare da ya kalleta ba.
"Ina kwana"
"Lafiya kalau"
Ya saka Tea spoon ya motsa tea.
"Zauna"
Babu musu ta nufi kujera dake facing din gefen teburin ta zauna, ya dauki tea din ya aje a gabanta.
"Na san baki karya ba, dauki ki sha"
Nan ma kasa musa masa ta yi, sai ta saka hannu biyu ta dauki cup din ta kai baki ta fara sha.
"Sai kawai kika ji kira daga sama ko? Ana zaginki?"
Ta sauke tea din ta rike a hannunta.
"Ki yi hakuri laifina ne, ya kamata na fada miki waye ni tun farko, ko da yake baki bukaci jin haka ba"
Ta dora idonta akan ragowar tea din dake hannunta.
"Amman kamin wannan fada min miye aikin Vito?"
Ta kalleshi da kyawawan idanuwanta ta sauke kai kasa, ba tare da ta amsa masa ba, domin ba zata iya tonawa Vito asiri agurin kowa ba.
"Dialer ne na Drugs?"
Ta sake dubansa.
"Ba fashi yake ba, da boyo zai rika yi ke ma ya boye ki, ba zai iya shiga ciki mutane kamar yadda yake yi a yanzu ba, kuma ba matsafi ba ne da yanzu ya bada ke ko kuma ya mallake ki sai yadda yayi da ke, idan kuwa baya duka biyun nan to yana siyar da kwaya, shiyasa yake samun mahaukanta kudi ko? Kuma shiyasa ya mallaki bindiga ta hanyar da be dace ba, saboda shirin ko ta kwana, domin ya san a tsakaninsu ma suna iya samun matsala da junansu, kin san sana'ar da yake ba sana'a ce mai kyau ba, shiyasa kike kokarin gina kanki kina son ki bar karkashinsa? Siyar da kwana ya kara masa karfi sosai da mutane ko? Da kuma jami'an tsaro shiyasa yake yadda ya ga gama? Kuma yana sha shiyasa bakinsa yake baki idonsa yake da ja kuma yake saurin fusata idan kika masa laifi sai kwakwalwarsa ta nuna masa dukanki ne kawai mafita"
Kallonsa kawai Emily take tana mamakin yadda yake cankar abubuwa line by line a daidai.
"Na zo nan ne saboda mu yi maganar Vito?"
"Aa kin zo nan ne saboda mu yi maganar ki da kuma tawa"
Ya zauna.
"Mutane za su yi mamaki idan suka tarar da ni a office dinki, na sakan shiga office kowa na so karbar abu ko hannatawa da kaina idan bana bukatar wani ya shiga tsakani, amman ban taba zama office din kowa ba sai Emily"
Ya duba agogo hannunsa.
"Da farko zan fara da baki hakurin abubuwan da suka faru, matata bata fahimce ki kuma tana da zafin kishi"
Yayi shiru na wasu dakiku sannan ya cigaba.
_______________________
Sannu ‘yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe ɗinki da kaya masu kyau, masu ƙima daga Khadeeja Candy Store
Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sauƙin sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing.
Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taɓawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet ɗinmu sun dace da ke
Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sauƙi ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko’ina!
Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1
da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0
Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame.
Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ƙayatarwa duk a farashi mai sauƙi.
Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu!
Baki da lokaci? Muna da sauƙin oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina!
To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08
Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store.
Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haɗuwa.
[5/22, 7:54 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
FOLLOW ME ON 👇🏻
FACEBOOK
https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914
TIKTOK
https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1
INSTAGRAM
https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0
CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01
KHADEEJA CANDY STORE
https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08
Page 2️⃣9️⃣
"Sunana Aliyu Aliyu AA Bappa Mudallab, sunan mahaifina Aliyu Mudallab amman ana kiransa da Bappa Mudallab kasancewarsa da na farko a gurin mahaifinsa, mahaifina dan siyasa amman a baya yayi aikin gobnati kamin ya sinci kansa a siyasa, ya fara da commissioner kamin yayi dan majalisar hijar kaduna har sau uku daga baya ya tsallaka zuwa tarayya neman sanata, mahaifina manomi ne sosai, kusan siyasar ta karbe shi ne kawai har yayi suna a ciki, amman abun da ya dogara da shi muma muka jingina, ni kaina na kam taba noman a lokacin damina, mahaifina kuma yana nema a rana da damina da baraza, yana da gonaki da gidajen shanu da ake saffara Madara da Fresh kirdirmo, da manshanu, haka kuma mahaifina yana kiwon fili da kaji.
Mahaifiyata kuma mace ce da bata komai sai rainon yayanta uku da Allah ya bata, Ummi bata sana'ar fari balle na baki, mu uku kawai ta haifa Yayana Yusuf, sai kuma ni Aliyu sai kanwarmu da ta zo bayan an fidda rai da samuwarta wato Ramla. Ummi ita kadai ce a gurin Mahaifinmu bayan ita be sake auren wata matarba, kuma har yanzu ba mu taba jin wani abu tsakaninsu ba, ko da yake ita da shi yayan wa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 23 Chapter of 63