Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
baku bincika ba kuka barta ta fita, yanzu da wani ne da zai cutar da ita fa? Da yanzu ni za a bari a matsala" "Na yi zaton ko tana son magana da ita ne Private, ita ma da ta fita ta ga ba ita ba ce ai sai ta dawo" "To ina zata san wannan idan tana son magana da ita ai ga dakuna ko kuma ta aiko a dauketa, amman sai a bari ta fita a bincika ba kuma ba a bi bayanta" "Aisha ce ba zata san ta dawo ba?" "Eh mana, duka duka nawa Ayusher take? Wannan tunanin ba zai zo mata ba, yanzu ne fa kwakwalwata take girma" Ummi ta saki baki tana kallon Aliyu da a bakin gaskiyarsa yake maganar. "Toh za a kula next time, yanzu dai ka dawo da ita ko yaya?" "Ai ba zan bar yarinya karama a waje ba" Ummi ta yi murmushi kawai ta nufi kofa ya biyo bayanta. A falo suka rabu ta nufi bangaren Daddy shi kuma ya nufi dinning din da matarsa take zaune tare da Nafeesa. Nafeesa na gaishe shi ta mike tsaye ta fice dinning din domin ba su damar karyawa su kadai ba tare da takura ba. "Kika yi serving kanki? Baki bari na zuba miki ba?" Ta mike tsaye. "Bari na zuba maka" "No it's my duty to feed you, zauna zan zuba da kaina" Ta koma ta zauna tana murmushi. Ya zuba ma kansa tana cin abincin yana kallonta har ta aje spoon. "Kin koshi?" Ta daga mishi kai. "Ba ki ci da yawa ba, ko wani abun kike so dabam?" "Aa" Ta amsa, ganin Nafeesa ya saka ta jin kunya sai ta mike tsaye. "Bari na dauko wayata" Aliyu ya juya ya kalli Nafeesa. "Idan kika aje plate din ki dauko mata wayarta" Nafeesa ta amsa da tohm. Emily ta koma ta zauna tana dan jin kunya. Nafeesa ta dauko mata wayar ta kawo tana mata wani kallo na zolaya. Emily ta karba ta rike "Thank you" Nafeesa ta yi murmushi kawai ta koma ciki, sai a lokacin Aliyu ya sake kallonta ya ce. "Kamata yayi ta ce you're welcome Mrs Aliyu ko?" "Idan Ummi ta zo ta same ni a nan zata ce ba ni da kunya" "Haka fa, ke ce mai kunya ni ne marar kunya ko?" Ta yi dariyar da bata shirya ba ta sauke kanta kasa tana taba wayar. A nan ta yi arba da sakon da ya sauya murmushin fuskarta zuwa tashin hankali. Tuna Aliyu na gabanta ya saka ta yi kokarin boyewa da murmushin dole. "Miye?" "Ba komai" "Vito ne? Ko Kameela?" "Miyasa ka zarge su?" "Saboda Turhan be jima da barin gidan nan ba, ba zai yiyu ya miki wani sako na tashin hankali da zai bayyana a fuskarki ba, ko mutuwa yayi ba ke za a sanarwa ba, amman Kameela zata iya aiko miki da sako marar kyau, haka ma Vito, cikin biyu dole a samu daya" "Vito ne" Ta fada kamar zata yi kuka. Aliyu ya tashi daga inda yake zaune ya zagaya gefenta ya karbi wayar. "Congratulations kin yi aure ko? Kin yi min butulci Emily kuma dole ki dandana dacin hakan, ke da wannan Balaraben da ya aure ki, ke da fitinanniyar yarki" Aliyu ya ciro wayarsa ya kwafi number ya saka a wayarsa bayan ya gama karanta sakon, sannan ya tura masa da sako da wayarsa. "Ba Balarabe ne ya aureta ba, ni ne na aureta mutumen da ya janyo ta daga PH zuwa Kd, mutumen da suka yi aiki tare, wawa ka zo ka tare ni mana, miyasa kake tsoro?" Ya kalleta. "Daman na yi tunanin zai samu number duk da yake sabuwar number ce, amman mai son abun ka ya fika dabara, kuma zuciyata ta raya min yana bibiyar rayuwarki, amman yanzu an zo karshe da yardar Allah, tun da har giyar hauka ta dauke shi ya turo wannan sakon za a gano inda yake" Emily ta mike tsaye. "Kashe shi za'ayi?" A kokarin Aliyu na kwantar mata da hankali ya ce. "Aa za a dai kama shi, sai a gabatar da shi gaban kuliya saboda kar ya cutar da kowa, haka yayi miki?" Ta daga kai. "Zauna kin ji yan matana, bari na nunawa Daddy wannan sakon, kuma zan sanar da Ammy halin da ake ciki, ba lallai idan na yi magana da Turhan ya saurare ni ba, amman na san Ammy zata dauki abun serious" Ta koma ta zauna ya nufi hanyar da zata sadashi da bangaren Daddy, sai kuma ya juyo ba shi da nutsuwar barinta a falon jin yake kamar wani abu zai same ta. "Shiga dakin Nafeesa ki zauna, kuma kar kowa ya sake sallama miki ki fito ko ni ne, mai son ganinki ya zo ya same a nan" Ta sake tashi, zuciyarsa bata bar shi ba sai da ya rakata har bakin kofar dakin Nafeesa ya bude mata ta shiga. "Karki bar yarinyar nan ta fito, idan ta bata ke na sani" Ya bugawa Nafeesa warning, sannan yaja kofar ya rufe ya nufi bangaren Mahaifinsa. TURHAN POV. Ammy bata yi mamakin ganin ya dawo da Fatima ba, daman ta lura tun kamin su tafi bata son tafiyar, tun jiya tana jikin ubanta tana taya shi jimami ko abinci sai da ta ga yana ci sannan ta ci. "Shiga ciki ki yi kallo" "Dady ba zai tafi ba?" Ta tambayi Ammy dake bata umarnin. "Eh" Tohm" Ta amsa sannan ta nufi hanyar dakinta. "Fatima" Turhan ya kirata sai ta juyo, ya tafi inda take ya rumgumeta sosai yayi kissing dinta ita ma ta yi masa kiss. "I love you" "I love you Too Dady" Ya sake ta yana murmushi, ya bita da kallo har ta shige sannan ya dawo kusa da Ammy. "Bata yarda ta zauna can, ko magana bata yi da Emily ba" "Daman na ga alamar ba zata zauna ba" "Ni zan tafi Ammy, anjima kadan jirgimu zai ta shi" "Ba zaka bari sai next week ba" "Garin ne baya min dadi gara dai na tafi kawai, ko zan samu salama" Ammy ta mike tsaye ta bude masa hannayenta sai ta matsa kusa da ita ta rumgume uwarsa. "Jikinka da zafi sosai Turhan, baka da lafiya ne?" "Zazzabi ne kadan na ke ji" Ta sake shi tana taba fuskarsa da jikinsa. "Ba kadan ba ne, ko'ina ya maka zafi fa, gaskiya ba zaka yi tafiyar nan a yau ba" Turhan ya zube kasa ya rike kafafuwan Ammy yana kuka kamar ba shi ba. "Ammy dan Allah ki yafe min, bijirewa umarninki ne ya jefani a halin da nake a yau, da ace na bi yadda kika tsara, da yanzu ban shiga wannan damuwar ba, da yanzu ban shiga wannan bakincikin ba" "Na yafe maka duniya da lahira, kuma damuwa Allah zai maka maganinta, Emily ba ita kadai ce mace a duniya ba" Ta daga shi ya zauna kan kujera ya rike kansa dake tsarawa. "Ba zaka tafi yau ba" Ya sauka kasa ya zauna ya dora kansa akan cinyar Ammy. Sun dade a haka kamin ya ciro wayarsa yayi canceling flight din, ko kadan a yanzu baya son ya sabawa Ammy domin ya ga illar hakan. "Zan bari sai next week" "Allah ya maka albarka, bari na dauko waya na kira Likitana" Ammy ta tashi ta fice daga falon ta shiga dakinta, tana daukar wayarta ta ci karo da sakon Aliyu daga numbersa da tuni ta goge ta a wayarta. [8/27, 11:03 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 7️⃣2️⃣ 🌟✨ TALIYAR HAUSA – YAR MURJI ✨🌟 🥘 “Abinci na gargajiya, ɗanɗano na musamman, jin daɗin iyali!” 🥘 Idan kina/kanason abinci mai ɗanɗano na musamman wanda zai tunatar da kai daɗin gargajiya, to babu kamar Taliyar Hausa – Yar Murji! Wannan taliya ba wai kawai abinci bace, al’ada ce mai haɗa iyali, ƙauna da jin daɗi a teburin gida. ✨ Me yasa za ka zaɓi Taliyar Hausa – Yar Murji? • ✅ An yi ta da tsafta da inganci • ✅ Ta dace da kowanne irin miya: miya mai ƙwai, miya taushe, ko miya mai ƙyauƙyau • ✅ Sauƙin dafawa – cikin mintuna ka samu abinci mai gamsarwa • ✅ Lafiyayye, mai sauƙin narkewa, kuma ya dace ga kowa cikin gida • ✅ Za ka iya amfani da ita wajen girki na yau da kullum ko kuma na musamman 📍 Muna a Kaduna – amma ɗanɗanonmu ya zarce iyaka! 🚚 Ana kawo muku duk inda kuke a Najeriya (delivery guaranteed). 💛 Idan kana son jin daɗin abinci na gida wanda ke haɗa zuciya da iyali, to ka gwada Taliyar Hausa – Yar Murji yau! 📞 wa.me/+2347071821482 tuntube mu yanzu domin yin odar ku. 👉 Ka more ɗanɗanon gargajiya mai tsafta, mai daɗi, mai ɗorewa! TWO MONTHS LATER... "Ah gaskiya an gyara gidan sosai, Aliyu yayi kokari, iyayenta ma sun yi, ko ku kuka mata kayan daƙin" Ummi ta yi dariya tana kallon kanwarta Hajiya Larai. "Hajiya Larai, ba mu muka mata ba, mahaifiyarta ta karbe ragamar komai daga hannunmu, ita ta yi mata komai, da kam har na yi magana da Khadeeja Candy za mu siya kayan Kitchen ta mana breaking down na komai sai gashi ita mahaifiyar tace dan Allah kar mu yi komai mu bar ta ta yi, sai muka cire hannunmu, lefe kawai ta hada mana, sai na yi ma Hajiya Baraka Recommending dinta, indai ba ta canja ba ina tunanin gurin Khadeeja Candy aka siya komai na kayan Kitchen da bedsheet da curtain har frames ma domin komai saidawa take" "Mhn idan ba ke ba Ummi yaushe za ayi ma yarinya miji kuma ayi mata kayan dakin? Wannan ai shi ke nuna kin an bata sadakar Aliyu kenan, wannan uban lefe da aka zuba ai kam dole uwarta ta dafe ka cire ta a kunya" "Daman shi lefe idan namiji yayi ai kansa yayi ma, tun da shi za'ayi ma kwalliya, ba faduwa ba ce" "Haka ne, ta yi kokari gaskiya, dan kan an zuba kaya komai yayi gwanin sha'awa kam, kai kace ma dauko komai aka yi aka zuba kawai a ciki" "Ai Khadeeja Candy ce ba daga baya ba indai kaya ne, gurinta nake siyan tufafi Laces shadda, Atamfa abaya shoes kai komai fa, har adashe ma na ga tana yi, kuma a kawo maka komai cikin aminci da salama, facebook na fara haduwa da kayanta na gwada saya yanzu kam har mun zama regular customer" "Ikon Allah wasu fa suna da zafin nema, toh ita kuma a facebook take siyar da kayanta ne? Zan so na gwada dan gaskiya kayan nan sun burge ni" "Aa fa kin ji Hajiya Larai da wani zance, a ko'ina kika searching dinta za ki same ta, a TikTok ne, ko Instagram har Snapchat, ko a WhatsApp, amman fa ki tabbatar kin shirya siya" "Hajiya Larai ta yi murmushi, ta dauko wayarta Ummi na karanta mata number Khadeeja Candy wanda take whatsapp chat da ita. "0 8 0 3 6 1 2 6 6 6 0" "Zan dubata ta WhatsApp In Shaa Allahu, auren Maimuna da za'ayi sai mu siya mata komai a can ma, tana dai siyar da manyan kaya ko?" "Sosai, cooler daga 12k har ta dubu tari taskwas za ki samu a gurinta, ya danganta da abun da kike so" "Aiko zan gwada da yardar Allah" "Tohm Allah ya amice, ba da ke za a tafi karbar garar ba ne? Ko da yake kin ga dakin amarya har kin gaji" "Da ni mana, ina za a barku a baya, mun bada sadakar ango kuma ace ba za mu karbo gara ba?" "Wane irin sadaka Hajiya Larai?" "Ah yo sadaka mana mai sunan Mama, ke kin san idan ba Aliyu ba babu wanda zai kwashi wannan yarinyar nan haka, a aje zancen kyau a gafe a kalli asalinta" "Kin gani Hajiya Larai karki bar Aliyu ya ji zancen nan na ki, domin yana son matarsa idan kika fadi wani abu marar dadi akanta karamin abu ne ki ga ya sauya miki fuska, su shegu ba sa da zafi ko gata ne? Miye na su a ciki? Wannan zancen na cikin gidana ne, ni ban san miya ja ni na fada miki ba" "Aiko dai kin san ni bana barin ta kwana, amman ai ba nuna mata zan yi ba, ko shi ta kasa dai tana saka, tun da ke ma kin bi ina ni ina juya baya?" "Kawai ki musu fatan alheri, domin babu abun da zai raba su sai mutuwa da yardar Allah" "Tohm Allah ya sanya alheri, mu din ai sai da hakuri, ko'ina akwai mu, dangin miji ba, mu ga fari mu ga baki, mu koma gefe mu yi magana" Ummi ta tabe baki tana dariya. "Wanda be iya zama da ku ba kuke wahalarwa, wanda kuwa ya san ku ya karanci komai ya huta" "Heeeee Ummi.. Kuma fa haka ne..." Hajiya Larai ta kyalkyale da dariya ta mikawa Ummi hannu suka tabe. Sannan ta sauke kafa daya kan daya ta mike tsaye. "Bari na fita waje mu zauna kamin su iso" "Hajiya Larai jibila da cincin kawai za a kawo mana, kayan masarufi a kai ma angon abun sa" "Toh mu karba ne kawai na mu, ba za a raba ba sai kin ga komai" "Tohm shikenan" Ummi ta amsa tana Hamma, kusan tun da aka daura auren na Aliyu da Aisha Ummi bata huta ba, bata wannan bata wacan har aka yi wunin biki da walimar dare domin ya ki yarda ayi kida, haka yayi ko a aurensa na farko, Ummi ta yi zaton a wacan saboda fadi babu dadin da aka yi ta yi ne da family Kameela ya saka yace ba zai yi biki ba, domin su suka yi komai da ake na hidamar kida da raye raye kuma be halarta ba. A yanzu kuma ta gane haline na gujewa tsabawa Allah, ya fada mata ya sake jadada mata cewar Manzon Allah S. A. W ya ce Allah ya tsinewa duk wata ni'ima da Allah yayi ma bawa aka taru aka yi raye raye aka chakudu maza da mata, auren Emily na daga cikin ni'imomin da Allah ya yi masa dan haka na zai yarda ya rayu da ita a karkashin tsunuwar Allah ba, sai dai ba zai hana ta yi nata taron da mata yan'uwanta ba domin addnin ba haramta ba, matukar maza ba su gani ba kuma ba su chakudu ba. EMILY POV. Bata san miye auren gata ba sai da ta zama karkashin inuwar kulawar Aliyu. Daga ranar da aka saka musu rana tana karbar kyaututukan kauna da soyayya daga mijinta danginsa da kuma danginta. Sabon gidan da ya siya ma sai da ya dauke ta ya tafi ta ita ta duba komai ta fadi inda be mata ba aka canja, komai zai siya mata sai ya nemi zabinta, abun da take so shi za'ayi, bata taba auren wani ya lalaba kamar yadda Aliyu yake mata ba. Ko a lokacin da zai fada mata ba shi da ra'ayin yin biki ta sigar lalama ya biyo mata yana lallabata yadda zata fahimta kar ranta ya bace. Sai kuma aka yi sa'a ita ma bata da bukatar bikin saboda bata da wasu kawaye da zata gayyata idan ma za'ayi sai dai Mama Baraka ta yi na ta gayyatar. Haka kuma aka yi, Mama Baraka ta aikawa kowa katin gayyata da wuri, domin Emily ta dawo a sabon gidanta ne ana sauran wata daya biki. Danginta har wadanda suke nesa sai da suka halarcin biki. Emily ta ji wannan auren a dabam kuma ta kara fahimtar yadda rayuwa take tafiya, a wannan auren ne aka yi mata wankan lalle wanda ake yi ma ko wace budurwa a aurenta na farko, sai dai ita bata samu wannan damar ba sai a yanzu, ba taba shafa mata lalle ba sai a wannan karon, yan'uwanta mata da kawayensu ka shirya henna day wanda Aliyu ya dauki nauyi, domin bikin na duka mata ne babu maza. Anyi Walimar dare walimar data samu halarta manyan mutane daga bangaren Mahaifiyarta da kuma iyayen Aliyu da abokan arzikin Ummi. Ranar wunin biki Mama Baraka ta dauko masu masu kudin kwarya da kuma yarbawa suka kayatar da wunin. A gurin Khadeeja Candy ta siya duka kayan Kitchen din da aka sakawa Emily bayan, Ummi ta hadasu da ta bincika kuma ta ga akwai abubuwan da take bukata sai kawai ta zaba ta tura kudi aka hada komai ta aika da mota aka dauko mata, wasu kuma daga baya ta kara aka aiko mata ta hannun Driver. Mama Baraka ta shiga ta tsayarwa yarta tun daga gyaran jiki karbar lefe da kayan saka rana har kayan daki da gara bata bar kowa yayi mata ba. Dr A-B ma da so ya dauki wani abu bata ba shiyasa dama ba, sai kudi mai kauri ya turawa Emily ta hanyar Mama Baraka yace a aje mata idan bukatar wani abun ya tashi. A auren Aliyu Emily ta san miye gata a aure, ta san dadin yan'uwa da iyaye, ta san wasu abubuwan da suke na daga al'adar hausawa da kuma yarbawa. A wannan auren an yi mata gara an yi mata kayan daki da komai da mace take bukata daga iyaye, ga yan'uwanta a kusa da ita komai zata yi su suke shigewa gaba, su bata shawara ko ma su aiwatar ba tare da jiranta ba, yan'uwan Mama Baraka na nesa da na kusa duk an sadata da su wasu ta waya wasu kuma sun zo bikin. Bata kara gode Allah ba sai a daren da Aliyu ya aiko da manyan motoci zuwa daukarta tare da abokansa da wasu daga gwaggonninsa da iyaye. Mama Baraka da yan'uwanta suka yi mata nasiha suka mata kuduba da uwa ke yi ma kowace ƴa, aka dauke ta tana lullube da zane bayan ta saka tsadadden lace na al'adar yarbawa, Tana sanye da sakarta ta zinari da aka saka mata a lefe, wuyanta da murjani da ya sauko mata har gaban kirjinta, haka ma hannayenta, kafafuwanta da suka sha bakin lallen suna sanye da iborun, tana ta kamshin turare sai guɗa ake masu, suka ta saka mata albarka da yaren na yarbanci. Aka fada mata idan zata shiga gidan ta shiga da kafar dama kuma ta yi addu'a da Bismillah. Tana zaune falon mahaifiyarta Fatima ta shigo ta ratsa mutane ta zauna kusa da ita tana ta kallon mutane, Emily ta miko hannunta a hankali ta kama hannun Fatima ta rike, idan suka yi magana da yarbanci tana jin duk abun da suke fada saboda tana jin yaren yarbanci da igbo tun a zamansu na can. Can kuma ta juya ta daga mayafin mahaifiyarta ta leka fuskarta. "Momy kin yi kyau" Ta fada tana shafa fuskarta tana murmushi, hawayen dake makale a idon Emily ya zubo mata. "Kin fi kowace rana kyau, har da lalle fa da sarka har biyu, da makeup" Emily ta lumshe ido tana murmushi, ko kadan bata yi tsammanin jin haka daga bakin yarta ba, ko da yake tun da Turhan ya saka kafa ya bar garin Fatima ta dawo gurinta daker da sudin goshi sai ta waye cikin mutane, musamman da kannen Emily suke janta a jiki. Da kuma aka fara hidimar auren sai ya zama abun ya burgeta, domin bata taba gani irin wannan auren ba, komai a gurinta sabo ne, duk abun da za'ayi ana yi da ita yana gaba gaba. Aliyu idan ya zo gidan zai zo mata da kayan dadi, ko be zo ba zai aiko a kawo mata, wani lokacin idan ya zo ita yake sakawa a sallamo yayi hira da ita ya bata tsaraba ya tafi. Yana iya kar kokarinsa wajen ganin Fatima ta sake jiki da shi kuma ta kwantar da hankalinta dan kar damuwarta ta jefa Emily a damuwa. Kusan kuma kwalliya ta biya kudin sabulu domin ya samu fiye da rabin abun da yake nema a gurin Fatima. Wadanda suka kasance iyaye ga Emily ne suka bukaci kanen su daukewa Fatima hankali ta yadda za a fita da Emily ba tare da ta sani ba. Domin suna jin lokacin da take tambayar Emily yau sabon gida za su tafi ko? Da wayo aka fitar da ita, sannan aka fita da Emily, a nan ma ta ga wata al'ada da a bata kyauta a karbi Amarya. Emily ta shiga motar tana hawayen da a yau ta tabbatar na farinciki ne. Tana zaune shiru tana saurari tafiyar har suka isa gidan masoyinta kuma Abokin Rayuwarta. An riko hannunta ta sauko motar kanta a kasa aka shiga da ita gidan da duk wanda ya ga tsarinsa da kayan da aka zuba a ciki sai ya yaba da kokari mijinta da kuma iyayenta. Bayan iyaye sun fita aka barta da kanenta da wasu daga familyn Mama Baraka da suka zama kawayenta na short period of time. Abokan Aliyu suka rako shi ya shigo falon da manyan tufafi babbar riga har da hula. Kowane yana rike da babbar leda suka cikin big center table din da kayan taba ka lashe da suka shigo da su. A nan ta san wani abu siyen bakin amarya, abokan Aliyu suka siye bakinta da kudi mai kauri da siyayya da, sun yi farinciki sosai domin ba su bar gurin ba sai da kowa ya ji saukar alert. Sai da kowa ya watse Aliyu ya rufe kofar sannan ya yarda ya bude fuskar matarsa, sannan a hankali ya yaye duk wani abu dake jikinta ya rage daga dankwalinta sai lace ne kadai, har sarkar cire mata yayi saboda yana ganin kamar sun mata nauyi, ya kama hannayenta duka biyu ya sumbanta sannan ya cire abun hannun ya aje, ya sauko kasa ta zauna ya daga kafarta abun adon dake kafarta ya cire bayan ya sumbanci kafar sannan ya aje ta a hankali, ya dago dayar ya cire ya sumbance ta ya aje kasa. Ita kanta ta ji a jikinta jumma'ar da zata yi kyau, tun daga laraba ake ganewa, Aliyu ne kadai Jarumin dake tsoron tana jikinta saboda gujewa tsallake iyakokin da musulunci ya gindaya musu. Har bayan aurensu, be taba kokarin taba jikinta ko wuce gona da iri saboda ta zama mallakinsa ba, kamin ranar yau idan ya rumgume ta ko ya sumbance to ya fahimci tana cikin damuwa ne sai yayi mata haka saboda ya kwantar mata da hankali, shi ma yana kokarin ganin be tsallake iyakoki ba duk kuwa da ya san halalinsa ce tun da an daura musu aure. "Abar kauna? Komai na ki yayi kyau" Ya fada yana kallon kyakkyawar fuskarta, kunyarsa da take ji a yanzu ta fi wanda ta ji a washe garin ranar da aka daura musu aure. Kafarta daya ya daga a hankali yayi mata chakulkuli, ta motsa kafarta murmushi ya cika fuskarta kunya ta saka ta rufe idonta. Yatsansa ya saka yana bin layin lallen da aka zana mata a kafa a hankali kamar mai zanen yana kallon kai kace be taba gani lalle a kafar mace ba. Har sai da ta kasa jurewa ta hanye kafarta. Sai yayi murmushi ya mike tsaye ya cire babbar rigarsa ya aje ya zauna kusa da ita, ya juyo da fuskarta ta fuskance shi. "Qalbi, bude idonki ki kalli mijinki, masoyinki, mallakinki abokin rayuwarki na har abada, mijin da yake jin ya fi kowa sa'a da rabo saboda ya same ki" Ya kara matsawa kusa da ita sosai har jikinta yana taba na shi. "Kin san me, uwar ƴaƴa? Tun daga ranar da kika shigo rayuwata, komai ya canja. Na rasa yadda zan bayyana, amma ke ce farin cikin zuciyata. A duk Lokacin da na gaji, sai murmushinki ya bani ƙarfi. A duk lokacin da na shiga damuwa, sai kalamanki su zama shauki da nutsuwa a raina." Ya ɗan janyo hannunta ya riƙe, yana tana saman yatsunya, ya ci gaba da cewa "Kin fi zinari daraja a wurina, kin fi dukiya ƙima. Wallahi idan na dubi idanuwanki, ina jin kamar na mallaki duniya baki ɗaya. Ke ce zuciyata, ke ce abokiyar tafiyata har ƙarshen rayuwata." Emily ta bude ido tana jin daɗin maganganun a zuciya, kowane harafi yana tsarata ya isar mata da sako. Ya saka karamin yatsansa cikin nata irin yadda yara suke yi. "Na yi alkawari ba zan taɓa barin ki, ki ji kaɗaici ba. Zan kasance tare da ke cikin farin ciki da bakin ciki. Domin soyayyarki ita ce hasken zuciyata, kuma ke ce sarauniyar gidana" Hawaye ya sauko

Chapter 58 of 63