na samu zunubi.
Haka muka raya yammacin ranar da laraba tare da yan'uwana marayu, sai da dare yai sai na nufi gurin dana saba zama na zauna karkashin wata bushiyar lemu na jingina jikina ina kallon sama, yadda taurarin suka jera abun ya burgeni sosai, sun yi ma sama ado sai sheki suke, kirgasu na fara yi da yatsana duk kuwa da kasancewar na san ba zan taba iya kirgesu su duka ba, wata maganar taurari ce dake cikin Bible ta fada min a rai.
"Sa'an nan sarki Yosiya ya umarci Hilkiya, babban firist, da firistoci masu daraja ta biyu, da masu tsaron ฦofa, su fitar da tasoshin da aka yi wa Ba'al, da Ashtoret, da dukan taurarin sama, daga cikin Haikalin Ubangiji. Sai ya ฦone su a bayan Urushalima a saurar Kidron, sa'an nan ya kwashe tokarsu zuwa Betel"
Murmushi nai ina mamakin yadda wani zai iya kona taurarin nan na samaniya har ya kwashe tokarsu. Wani lokacin bana son zufafa bincike akan addini na amman ina ganin kamar akwai gyara a litattafin bible domin kuwa wasu kalaman ko nace surorin da suke ciki sai kaji kamar abun ba zai yiyu ba wani abun ma nakanji kamar labari ne irin na shaci fadi.
"Kina nan kina aikin kallon taurari ko?"
Maganar marry ce tasa na dawo da dubana izuwa gareta, kokarin zama take kusa da ni.
"Wata rana za ki zauna tare da mijinki ku kirga taurari"
Na kalleta
"Marry kina da ban dariya"
"Miyasa na ke baki dariya idan nai maganar miji? Baki taba daukar hakan da gaske ba"
Shiru nai kamin na ce mata.
"Ina ganin wani abun kamar ba zai faru ba, akwai wadanda suka girmemu a nan gidan kuma suna nan basu yi aure ba balle kuma ni da ke, balle ma ba zamu auri mutumen da zai ga girman mu saboda ba mu da iyaye"
"Wata kila ke din kina da iyaye Emily, ina ji a raina kamar muna da iyaye yawancin mu da muke gidan marayu muna rayuwa kawai a matsayin marayu, amman wasu iyayensu sun yi cikinsu ne sun jefar da su"
"Indai har haka iyayena suka min bana kaunar ganinsu, domin sune silar shigata wannan hali"
"Idan kuma iyayenki suna tsoron ki wahala ne suka kawo ki nan fa? Ko kuma wani ne ya sace ki ya kawo ki nan?"
"Zan iya yafe musu idan wani ne ya kawo ni nan, zan yafe musu amman talauci ba hujja bace komai talaucinsu kara su yi hakuri da ni a haka mu zauna a haka, tun da suka kasa hakurin zama da ni ba zan yafe musu ba"
Na fada idanuwa na cika da kwalla, sai ta saka hannunta ta lakamoni.
"Zaki yafe mata Emily, lokacin da mijinki zai risina a gabanki ya roka mata yafiyarki ba kisan lokacin da za ki yafe ba"
"Ba zan iya yafewa ba marry, i just can't"
Dariya tai jin yadda nai maganar ina son yin kuka. Mun dade zaune a gurin sannan muka tashi muka shiga block din mu ta nufi dakinta ni ma na nufi namu. Babu wuta a dakin amman an kunna hitila kamar yadda aka saba idan ba wutar, ban kula kowa ba dukuwa da irin wasan da abokina na dakin ke jana da ita, ganin bana cikin yanayin wasan yasa suka kyaleni na hau gado na kwanta wata kofar tunanin ta bude min.
'Suwaye iyayena? Yarbawa ne, igbo ne ko ibra ko hausawa? Ban sani ba, wane addini suke? Miyasa suka jefar da ni? Basa sona ko wani dalilin ne na dabam?'
Da wannan tunanin nai bachi kuma har gari ya waye ban samu amsar tambayoyina ba. Ban farka da wuri ba kasancewar ban yi bachi da wuri ba, shiga nai bandakin mu dake can kusa da kofar shigowa dakin nai fitsari ba tare da tsarki ba na wanke bakina kuma nai wanka sannan na fito. Mai kawai na shafa, ni ma ina da kyau kamar mutumen jiya duk kuwa da kasancewarsa namiji.
Karamin wandon jean na saka wanda iyakar tsayinsa guiwa na saka wata t-shirt black na dauko kofina na jika gari na sha domin an san by this time an gama raba abincin safe kuma wanda be je ya karbo ba ba za a aje masa ba indai ba wani ne ya karbo masa ba. Bayan na gama sha na rufe waduruf din na saka wukata a aljihu tare da makullin lokar na dauki jacket dita na daura a kwankwaso na sannan na fito zuwa gurin gyaran mota wato gurin aikina.
Nayi ta sauri a hanya ganin na yi latti ba kasafai nake son oga na rigana zuwa gurin ba, naje latti sai dai duk da haka oga Abdulshakur be fito ba wata kila wani abun ya tsayar da shi a gida ko wani gurin, rigar aikin na dauka na dora saman tufafina na soma gyara gurin sannan fito da kayan aikin a waje, na kusan awa biyu a gurin sannan ya iso. Cikin girmamawa na gaishe shi ya amsa min da far'a kamar kullum, sannan ya shiga aikin gyara motocin da ke gurin a lokacin ne mutane suka fara zuwa ciki kuwa har da yaran da muke aikin tare da su yan gareji. Ni nake tsaye kusa da shi ina aikin miko masa abubuwan bukata kamin ya bani list din abubuwan da zan je na siyo a kasuwar da ake siyar da jarafuna a unguwar Orile Iganmu a nan lagos. Zuwa nai dakin dake garejen na cire rigar aikin na dawo ya bani kudi na saka a aljihu sannan na kama hanya. Ba mu da nisa sosai da unguwar dan tafiyar bata wuce ta awa daya da rabi ba, so i decided naje a kafa na rike kudin babur din ko wani abu zan iya siya da su. Na tafiyar minti arba'in kamin na kama hanyar da ke kusa da kasuwar, hanyar kamar unguwarmu take babu mutane sosai duk kuwa da kasancewar da rana ne. Gungun wasu mutane na hango za su kai mutum hudu zuwa biyar a tsaye gefen titin, ban ji tsoron ganin mutanen masu kama da yan ta'adda ba domin na saba ganin irinsu da ma wadanda suk fisu a lagos. Ban lura da abunda suke da niyar aikatawa ba har sai da na isa kusa da su, mutumem jiya ne suke kokarin karbewa mashin suna masa barazana da katuwar wukar da ke hannunsa.
"Bamu makulli"
Dayan ya fada da yaren turanci ni kuma na katsa masa tsawa da yaren yarbancin ganin zagen fuskarsa da yana nuna cewar shi bayarabe ne.
"Ba zai bayar ba, ku kananen yan iskane da kuke yawo da wuka, kuma duk wanda ya kuskura ya taba shi ai cikinku sai nasa an kasheshi ba kune yan apapa ba?"
Duk tsayawa sukai cirkocirko suna kallona yadda nai musu barazanar yasa sun dan tsorota, ban san su ban san yan ina ba ne amman yawacin yan iskan lagos apapa suke, sun dauka a yadda nai musu kamar na sansu ne ko kuma ina da wani mai tsaya min ne.
"Wacece ke?"
Dayan ya tambaya da yaren yarbancin kamar yadda nai masa magana dazu.
"Idan kun taba ni zaku san ko wacece ni"
Na fada ina zaro wukar dake cikin aljihuna na nuna musu ina yatsine fuska kamar yar ta'addar gaske.
"Ku wuce daga nan"
Kamar umarnina suke jira suka kama hanya suka kyaleshi suna ta waigena. Sai da suka wuce sannan ya kalleshi na ce
"Kai sakarene zaka tsaya haka a kwace maka babur?"
"Kamar ke ce yarinyar da kika taimake ni jiya"
Ya fada cike da mamaki yana nuna ni.
"Yes kuma yau ma na taimakeka ba, dan ka zama dolo"
Murmushi yai.
"No ina tsorone amman kin san su ne?"
"Ai a lagos ba dole sai ka san kowa ba, as long as kasan sana'ar mutun barazana kawai zaka masa, idan har kace kyalewa zaka yi kowa zai cuce ka ne, shiyasa na ke yawo da wukata"
Na fada ina maida wukar aljihuna sannan na kama hanya tafiya kasuwa ta ba tare da na jira abunda zai ce min ba.
"Na gode Emily"
Ya fada sai na juyo na kalleshi ina murmushi.
"Baka manta sunana ba?"
"Taya zan manta sunan Jaruma"
Ya fada da dariya nima dariyar nai na cigaba da tafiyata.
_________________________
Want more?
*Comment*
*Share*
*Follow* my channel https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01
[4/29, 6:17โฏPM] ๐๐ต๐ฎ๐ฑ๐ฒ๐ฒ๐ท๐ฎ ๐๐ฎ๐ป๐ฑ๐: ๐ ABOKIN RAYUWA ๐*
*ยฉ Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... โ๏ธ
Page 1๏ธโฃ9๏ธโฃ
Tun daga wacan ranar ban saka ganinsa ba, amman ban manta sunanansa ba, ban manta kyaun fuskarta domin Khaleefa yana da kyau sosai kwatankwacin yadda mutane suke baya kyauna. Kusan zan iya cewa kyaun ne abun da ya ja hankalina izuwa gareshi.
Na cigaba da rayuwata ta yau da kullum kamar yadda na saba a gidanmu na marayu, da safe zan tafi makaranta da yamma kuma na leka gurin aikina na gyaran mota wato garejen oga Shakur, idan aka samu aiki yayi kyau ko kuma muka samu customers da yawa a ranar yana min alheri kamar yadda ya saba.
Kasancewar yau assabar na tafi aikin tun safe ban tashi ba sai yamma, da zai sallame ni yayi min sallama mai kyau, ba karamin faranta min rai yayi ba hakan ya kara min karfin guiwar tafiya gida, na yi wanka na shirya na fito domin kashe kudin da aka bani, domin abu ne da kowa ya shaideni da shi alheri hali na, idan na samu kudin na kan sawo abubuwan dadi na kawo, kowa ya saka hannu ya ci, ban san na ci ni kadai ba. Na isa gurin na gaisa da shi da yaren igbo na ba shi kudi nace ya hada min kayan marmari, a nan yake fadan min domin da na taimakawa yayi siyayya ranar nan kullum sai ya zo nemana. Da mamaki na tambaye shi.
"Nema na? Me zan masa?"
Yayi murmushi ya koma cikin karamin shagonsa ya dauko farar takardar ya miko min.
"Number ce ya rubuta yace idan kika zo a baki, duk da haka kuma yana zuwa kullum da zaki iya jiran shi anjima kadan zaki ga ya zo"
"Amman yace na yi masa laifi?"
"Alamu be nuna hakan ba"
Ya miko min ladar na karba, har zan tafi sai kuma wata zuciyar ta ba ni shawarar na tsaya na jira shi mana idan ma wani abun ne ai zan ji. Haka kuwa na aikata na zauna a gurin muna ta hira da Mutumen sai ga shi ya iso da babur dinsa kamar wacan karon.
Tun kan ya sauko daga kan babur din fuskarsa ta washe da murmushi, ya karaso kusa da inda muke zaune yayi min sallama, na amsa masa kamar musulmai, sai ya washe hakora.
"Garkiwata kamar dai kin fini iya hausa"
Na yi murmushi zuciyata na bugawa da wani irin karfi, irin bugun da bata saba yi ba.
"Kana ta nemana aka ce, amman dai ba laifi na yi ba ko?"
"Laifi kika yi babba kuwa"
Ya fada yana dagawa igbon hannu tare da mika masa 2k.
"Laifin me"
"Kin san kin taimake ni a nan haduwar farko, haduwa ta biyu kuma kin ceto rayuwata kin ceto abun hawana kuma abun sanata, tun daga lokacin zuciyata bata barni na zauna laifi ba, na yi bata hakuri har na gaji amman bata bar ni ba, wata kila saboda ba ni da kowa a garin lagos ne, wata kila kuma saboda taimakon da kika yi min ne, ko kuma dai saboda kina marainiya ne amman dai kin tsaya min a rai kuma kin ba ni tausayi sosai"
"Baka da kowa a nan"
Na tambaya da mamaki fuskarsa na cika ni da kwarjini, ba dai kyaun ba kam Khaleepa akwai kyau kamar dan indiawa.
"Ba ni da kowa, kawai na biyo abokina ne da yake achaba a Lagos saboda ance yafi arewa samun kudi, sai na zo ni ma nake yin achaba, ban san kowa ba sai ke sai abokin nan nawa, sai kuma mutumen igbo"
"Interesting"
Na furta not knowing what to say next, yayi tagumi yana kallona.
"Ashe dai zan sake ganinki, na ji kamar na yi hauka, kullum sai na zo nan neman kyakkyawar fuskar nan"
"Amman ya kan yi ka iya magana da igbo nan bayan baka jin yarensa"
"Wani na samu yake rubuta min duk abun da nake so na tambaye shi idan na zo, sai shi ma ya rubuta min idan na tafi gurin wacan sai a fassara min"
Na yi murmushi ina yaba karfin halinsa, amman fa ya burge ni, neman ganina kawai zai saka shi wannan hidimar.
"Ni zan tafi"
"Haba ban gama kallonki ba fa, kuma kin san yaushe nake bata lokaci ina zuwa nan nemanki"
"Idan na dade ban dawo ba kawaye za su neme ni, kuma ba a son muna fita muna dadewa a waje ba tare da wani dalili ba"
"Shikenan muje na rakanki, akwai abubuwa da yawa da nake son sani akanki, kamar yadda aka yi kike jin hausa, kuma kike da kirki da kulawa, kuma gashi kina da kamun kai, dan na yi mamakin yadda na baki kudi baki karba ba, kuma gaki kyakkyawa"
Duk yadda na so na tafi ni kadai be yarda ba sai da ya goyani da babur dinsa ya kai ni kusa da gidanmu na marayu, a boye na sauka domin bana son kowa ya gan ni, idan aka gani ma za'ayi min fada. Ya sake rubuta number shi ya ba ni ya bani kudi a nan din ma ban karba ba, be tafi ba sai da na masa alkawarin zan kira shi mu gaisa da wata wayar.
A ranar kasa cin abincin dare na yi, na gagara cin kayan marmarin da na siyo sai tunaninsa nake, a wacan lokacin akwai kurciya sosai a tare da ni, domin ina da shekara goma sha biyar ne, a lokacin ina sss1, gashi kuma wani be taba nuna min kulawa kamar yadda shi ya nuna min ba, ina da kyau wannan abu ne da ni kaina na sani, amman kyaun nawa be taba sakawa wani be taba nuna min kulawa mai kama da soyayya kamar shi ba, sai dai mutane su na haba haba da ni, wata kila suna gani ko tunanin ni na yi karama ne.
Abu kamar wasa muka fara shakuwa da juna, da wayar mai dafa mana abinci a gidan nake amfani ina kiransa mu gaisa, wani lokacin har cin hanci nake bata, shi kuma da zarar ya ga flashing dina zai kira mu dade muna yawa, idan yana son ganina kuma zan boya na tafi nesa da gidanmu na hadu da shi mu ga juna, a gaskiya na so Khaleepa a wacan lokacin irin son da idan ina tunaninsa bana iya bacci, idan ban yi waya da shi sai na wuni cikin wani yanayi na rashin dadi, a makaranta gurin aiki bana da komai sai tunaninsa.
Wani lokacin zai yi min siyayya sai na boya na shigo da ita ba zan fadawa kowa ba, ranar da Marry wacce take kasan gadona ta gane ina soyayya ta tsare ni da tambaya har sai da na fada mata shi ne mutumen da muka hadu kuma na fada mata shi musulmi ni, sai ta fusata kuma ta tsorata ni cewar ai su musulmai basa auren kafirai, kuma a arewa ba a son wanda ba bahaushe ba, arna suke kiranmu, a madadin na yi nazarin kalamanta sai soyayya ta rufe min ido na fara gaba da ita. Na same shi da maganar tabbas a lokacin, sai ya karyata abun da ta fada, a nan yake fada min asalinsa da gidansu da garinsu da yake kauyen Kaduna. Ya nuna min fargabarsa ta daga gurin inda nake zaune ne, yana ganin kamar ba za a yarda a aura masada ni ba, a lokacin ni ma hankalina ya tashi domin na san ba za su yarda ba.
Haka dai muka cigaba da soyayya, yana fada min idan ya aure ni, zamu yi rayuwar aure mai kyau, zai nuna min soyayya zamu rika cin abinci a tare wanka kwana komai kamar na masoya, ashe karya yake amman ni ban gane ba, kawai abun da ke daukar hankali kyaunsa da kuma yadda be taba yarda ko da wasa ya taba nuna son taba jikina ba, har ta kai yana kiran mahaifiyarsa ya ba ni mu gaisa, be min karya ba ya fada min sana'arsa kuma ya fada min shi dan kaduna ne, amman a kauye suke zaune tare da iyayensa. Soyayya da muka fara da Khaleepa kusan kamar ta budewa maza kofa ne, domin babu ranar da zan fita wani be nuna yana so na ba, amman bana sauraren kowa sai shi, idan naje church kullum addu'ata na yadda kowa zai amince na aureshi ne.
Ana haka wata rana aka shigo kirana tare da sauran yan mata sa'anin na, muka tafi sai muka samu wasu manyan mutane ne suka zo neman ya da zasu rike kamar su suka haifeta. Daman akan yi hakan wasu jarirai suke so, wasu kuma wadanda suka dan tasa, amman ita tace tana son matashiyar buduwarwa, domin ta taba daukar jaririya kuma ta reneta tana can hannunta a gurinta ta girma. Matar tana yin arba da ni, sai ta zabe ni, suka ba ni damar tafiya na shirya domin a ranar zan tafi bayan ta yi duk abun da ya kamata, a ranar na sha kuka sosai a gurin abokan zamana na gidan, domin tun muna yara muka taso tare, har na ji kamar kar na bita, sai dai kuma ina son tafiya ni na shiga family na samu wanda zata rike ni a matsayin ina son na rumgumeta na ji yadda ake ji.
Gidanta babba gida ne a lagos tana da masu kyau, ga manyan motoci da ac abinci sai wanda na zaba nake ci, tun a ranar da aka kawo ni ta fada min ita bata taba haihuwa ba, tana da jiki sosai likitoci sun ce kitse yayi mata yawa ba zai barta ta haihu ba, hakan ya saka take son rike yara kamar yaranta. Ta nuna min kauna tace zata rike ni kamar yarta, ban maida sati a gidan ba aka canja min makarantar da nake zuwa makarantar masu kudi makaranta mai kyau. Mukan zauna musha hira da ita idan na dora kaina a jikinta sai na yi ta kuka, ashe dai ni ma wata rana zan samu masu sona.
Ta tambaye ni a ina na iya duka yaruka hudu da nake ji, na fada mata yaren Igbo da yarbanci daman kowa ya iya a Lagos domin mun tashi mun ga su ake amfani da su, turanci kuma ba iya a makaranta, hausa kuma na koya a gurin Oga Shakur da yaronsa da ya kasance bahaushe.
Kwakwalwata tana da saurin fahimtar abu, kusan duk abun da na sakawa raina zan iya na kan iya cikin kankanen lokaci, haka ya saka tun ina primary har secondary school ni nake dauko ta daya aji.
Sai da na yi wata biyu a gidan sannan na samu damar aron wayar mai aikin Momy kamar yadda muke kiranta na kira number Khaleepa da tuni na haddaceta, da na kira shi kamar zai yi karamar hauka saboda yadda nake ta jiran kirana a koda yaushe, ni kaina sai da na yi kuka, daman dauriya kawai nake amman duk tsawon kwananki da na yi a gidan da jindadin da nake samu bana jin farinciki saboda bana jin muryar Khaleefa.
A ranar be iya bachi ba sai da na fita na tambayi mai gadin gidan ya fada min yadda zan masa kwatance ya zo ya same ni a gidan muka gaisa, a nan kam ban da fargaba duk kuwa da kasancewar ban gama sanin halin matar ba, amman dai da alama tana da fahimta kuma tana da kirki ina ganin kamar da alama zata bar ni na auri Khaleepa, ya kawo min waya a ranar keypad da sabon layi saboda ba zai iya jure rashin jina ba, ba tare da fargabar komai ba na karba na shiga da ita gida, ban boye mata ba na nuna mata wayar na fada manta wanda ya kawo min.
"Saurayinki ne"
Na daga mata kai ina murmushi ita ma ta yi murmushi.
"Ashe na kai ga buduwar, bari na fara shirin aure"
Na rufe ido ina dariya, ta tambaye ni sunansa da kuma inda muka hadu na fada mata komai, a take yanayinta ya sauya, sai ta karbi wayar hannuna tace zata aje sai idan mai gidanta ya dawo kasancewarsa matafiyi, idan sun tattauna abun da ya dace zata ba ni wayar, ban jidadi ba amman haka na daure na cigaba da waya da Khaleepa da wayar mai aikinta. Wata rana sai ta kira ni tare da mijinta suka zauna da ni suka fada min ilolin da suke cikin auren musulmi, ta yi ta fada min kalamai marasa dadi akan musulmai da kuma yan arewa, ita da mijinta burinta su cusa min kyamar musulmi kamar yadda ake yi sauran yara, ta fada min na yi kankanta da fara soyayya a yanzu, kuma Khaleepa ba ajina ba ne domin shi achaba yake yi, ni kuma a yanzu na kalli irin gidan da nake rayuwa.
Soyayya bata da hankali bata ji bata gani, duk ban ji abun da suka fada min ba, a haka na nuna musu ni dai ina son Khaleepa ba zan rabu da shi ba, sai suka saka min dokar ba zai sake zuwa na fita ba, kuma ba zan sake waya da shi ba, haka kuma ba zan ma taba aurensa ba, idan ma ina wannan tunanin na aje. Suka saka min kulli mai tsanani bana zuwa koma'ina daga gida sai makaranta sai kuma idan mun fita siyaya, ko kuma ranar Sunday muna fita zuwa church. Sun min gata sun nuna min soyayya suna kashe min kudi amman duk bana gani saboda Khaleefa ne a rayuwata, kullum cikin kuka da damuwar rashinsa nake, ban sani ba a lokacin ashe hawaye ba su cancanci zuba saboda shi ba.
Wata rana mun je Church, na sulale na ari wayar wata mata na kira shi na fada masa dokokin da Momy ta saka min ita da mijinta kuma sun ce ba zan aure shi ba, a wayar ya rika kuka yana fadin Innalillahi idan na rabu da shi zai halaka zai mutu, ni ma na rika kuka ina jin kamar ma na kashe kaina domin ban taba soyayya da kowa ba sai da shi.
"Emily zaki iya aurena a kowane hali?"
Na rasa taya zan amsa masa.
"Amman ba addininmu daya ba Khaleepa"
"Karki damu da wannan addinin musulunci ya yarda mu auri wanda ba addininmu daya ba, kuma na san idan kina so na zaki musulunta domin ki aure ni"
"Zan iya ina kaunarka sosai Khaleepa"
"Emily zaki iya bina mu gudu? Idan ba haka ba ban san wata mafita da nake da ita ba, daga wannan wayar ma ban san ta ina zan sake jin muryarki ba, kuma muna nan ba za su bari mu kasance da juna ba"
"Idan mun guda ina zamu je"
"zan gudu dake mu koma kaduna gurin iyayena, zaki zauna a can a daura mana aure mu zauna a can"
"Ina tsoro ba zan iya ba Khaleepa"
Duk wata kalma da zata raunata ni ta sanyaya min guiwa da zuciya sai da ya nemo ta ya fada, amman ban yarda be shi ba. Na koma gida ina ta tunanin mafita amman ban samu ba sai wanda ya kawo, gashi kaunarsa sai kara ruruwa take a zuciyata, da kaina na samu Momy a dakinta ina kuka na fada mata ina son Khaleepa ta bar ni na aureshi, madadin ta tausaya min sai tace idan na sake mata maganarsa sai ta min duka kuma ko zan mutu ba zata taba bari na auri musulmi ba. Ranar mutuwa ce kawai ban yi ba tsabar bakinciki da nadamar kin bin shawarar Khaleepa na bishi mu gudu. Da sati ya zagayo muka je church Momy ta saka pastor ya dafa kaina ya rufe ido yayi min addu'a, bayan an zauna zaman church ana tsaka da wakar church na saci kafa na fice daga cikin church din daman Momy tana zama a gaba ne mu muna zama baya. Na fito na ari wayar mai gadin church din na kira Khaleefa na fada masa yanzu na amince zan bishi mu gudu.
Sai ya fada min inda zan je na jira shi, haka kuwa aka yi ba bawa mutumen wayarsa na fice daga church din na tari okada na fada masa inda zai kai ni, ko da na isa na samu Khaleepa a gurin tsabtsab da shi kamar kullum, yana
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 63