yi ba, wasu ma mazan sun fi haka munanawa, ni kam dai na sauke zancenta tun da ba yar gwal bace, an san an bata mata amman ba amfanin rike abu kayi ta jayayya ko dan yarinyar nan ba zata duba ba, amman ka tsaya tsayin daka kai dai a yanzu ita kake so wata kila kana tunanin kamar idan ba ita ba ba zaka sake samun haihuwa ba? Toh, Allah yasa ta zama alheri gareka kai ma ka zame mata"
"Aa Ammy ba haihuwar ce kawai nake dubawa ba, ina duba rashin kyautar da na yi kuma Allah ya tashi ba ni haihu sai ya ba ni da inda ban yi zato ba, ta cancanci komai a gareni saboda mahaifiyar Fatima ce, kuma...."
Yayi shiru ya sauke kansa kasa.
"Ammy ina son Aisha.. Ina sonta sosai ina sonta sai a yanzu na gano haka"
"Tohm Allah ya baka ita cikin sauƙi, ni ma ina son zamanku tare da farko, bayan abubuwan nan sun faru sai na ji ta fice min arai saboda abubuwan da ta yi kuma ta kalli tsabar idona ta fada min bata sonka, Turhan duk wanda baya sonka bana son shi Wallahi, kuma saboda Aliyu da iyayensa ina son ka maida matarka, na yi kuskure da na cilasta maka sakinta"
"Wani lokacin abubuwa sukan subuce a hannunmu, ko a halshe bama iya rike su, sai dai ki taya ni da addu'a"
"In Shaa Allahu, amman kasan akwai abubuwan da ya kamata mahaifinka ya sani a game da ita kuma baka fada masa ba"
"Bana son na sanyaya kudurinsa ne, inda Emily tana tare da ni duk abun da zai biyo baya mai sauki ne"
"Gobe zan je na yi na yi magana da ita, bana sin bata ran Mai Martaba kuma zan koma ko dan na shirya da matata, zan rika zagayowa lokaci zuwa lokaci"
Ammy ta sauke numfashi kawai bata ce komai ba.
EMILY POV.
Bayan Mama Baraka ta wuce, Emily ta haura sama ta shiga dakinta ta zauna bakin gadon dake dakin zata kishingida kenan ta jiyo sauti karatun qur'ane a wajen Window da murya mai dadi. Mikewa ta yi tsaye ta yaye labulen ta bude Windows din sai ta hango Aliyu zaune akan beach chair Fatima na zaune akan cinyoyinta hannunsa rike da waya yana karatun kur'ane.
Ba wannan ne karo na farko da ta taba jin karatun kur'ane ba, amman wannan ne karo na farko da taji kira'ar da ta yi mata dadi sosai ta tsuma jikinta ta tsara zuciyarta har ta zubar da hawaye, bata jin komai daga kalman labarancin amman jikinta da zuciyarta suna karbar sakon. Juyawa ta yi ta nufi wardrobe dinta ta dauko karamin mayafi ta rufe kanta fito dakin ta sauko kasa kuma sai ta yi sa'a babu kowa a falo, ta bude kofar ta fita ta zagaye ta kofar garden, cikin sanɗa ta bude kofar saboda kar ta yi kara, ta shiga tana takawa a hankali ta kusa isa inda yake sai ta zauna a kasa tana kallon bayansa domin ya bawa kofar shigowa baya ne.
Tagumi ta yi da hannayenta biyu tana kallonsa, hawaye take irin hawayen da suka sha banban da wadanda ta saba yi, wata kila saboda Aliyu ne yake karanta ya saka ta ji dabam, wata kila kuma a yanzu sakon yake son isa ga gabobin jikinta. Sai da ya gama karatun ya kashe wayar sannan ya sauke Fatima daga kan kafafuwansa ya mike tsaye ya rike hannunta.
"Muje ciki"
Ya juyo tare da ita, arba da Emily zaune a kasa ga fuskarta da hawaye ya daga masa hankali sosai duk kuwa da murmushin da yake gani tare da hawayen. A take ya saki hannun Fatima.
"Fatima tafi ciki zan yi magana da Momy"
"Miyasa take kuka"
"Shi nake son na ji"
Fatima ta fice gurin tana yi tana waigen Emily. Sai da ta fice sannan Aliyu ya karasa ya ɗurkusa gaban Emily.
"Lafiya? Me ya faru? Mama Baraka ta yi wani abun ne?"
"Hawayen ba na tsakanin mutum da mutum ba ne, tsakanin Rai da Mahaliccinta ne, Wallahi na dade da gamsuwa Allah ɗaya ne, wannan dalilin ne ya saka karbar musulunci ya zama abu mai sauki a gurina, ban sani ba ashe ma a musulma aka haife ni. A yau na ji karatun nan dabam, ban taba jin karatun da yayi min dadi ya tsuma jikina irin naka ba"
Aliyu ya sauke ajiyar zuciya sannan ya yi murmushi ya zauna a gurin.
"Shi Alkur'ane abinci ne ga ruhi, waraka ce ga ko wace cuta, kuma tsira ce ga kowane rai, ga dadin karantawa, ga dadin sauraro ke ma wata rana zan so na ji yadda ta ki kira'ar take"
"Anya zan iya?"
"Idan kina tare da ni akwai abun da ba zaki iya ba?"
"Ta ko'ina Aliyu kai ZaKi ne, ka tare duk wata kofa da zata nuna gazawata"
"Saboda babu gazawa a tare da ke, na yarda da ke fiye da yadda na yarda da kaina, miyasa kike kwankwanto akan abun da ni na hango shi tun kamin ki fada"
Ta share hawayenta tana murmushi.
"Ta ko'ina fari kake Aliyu, har yanzu na kasa ganin dogon bakin a tare da kai, na kasa ganin abun da ake ta nuna min akanka"
"Ke ce mace ta biyu bayan mahaifiyata wanda ta yarda ba ni da aibu kuma bana yin mata laifi, hakika Emily ke ta musammance"
"Kai din gwanin magana ne, ka iya kalami, kowane harafi yana ratsa cikin jikina ya fahimtar da ni abun da da ban fahimta ba"
"Saboda kin iya saurare ne, kusan ni bawa ne duk wani abun da sarauniya take son ta ji, halshe ne yake sarrafawa ya fada ba tare da neman izinina ba, jindadin yadda kike ba ni lokacinki, alfarma kike min na san ai ban cancanta ba, na gode da karramawa"
"Sai ka rika yin abu kamar ni din wata ce Aliyu"
Ta fada a shagwabe kamar mai shirin yin kuka. Ya duba ko'ina ya ga babu mai ganinsu.
"Ni na taba fada? Sam sam sam ke din ai ba wata ce ba, ke Emily ce mace mai kyakkyawar zuciya, ga hakuri da juriya, macen da data sha wahalar rayuwa kuma ta cancanci girmamawa d soyayya daga gurin kowa, ba zaki taba zama wata ba, wata yana nufin wata wanda ba kowa ba, ke kuwa mutum ce har da rabinsa"
Ta yi murmushi ta sauke kanta kasa.
"Idan an min izini, ina son zan shiga ciki kin san ke ba muharramata ba ce, kuma a musulunci babu kyau mace da namiji su kebe su kadai"
"A har a nan da yake fili kuma da rana?"
"Ai bana iya banbance dare ko rana idan kika tsare ni da idonki, kwarjini kike min komai girman guri sai inji kamar muna a cikin karamin daki ne, shiyasa nake ta taka tsantsan kar na bata miki rai, Emily, au Aisha yau kin yi shiga ta mutumci na jidadin laifinsu ne basa fada miki yadda kike musu kyau shiyasa baki damuwa ki rufe kanki da jiki"
"Su wa?"
"Tufafin mana? Ita mace ai tsada ne da ita, shiyasa idan suka killace a jikinta suke yin kyau, basa son rabo da ita"
"Haka suke fada maka?"
"Haka na gani rubuce a fuskarki, ki daina musu da abun da baki iya canjawa Aisha kina yi ma tufafi kyau"
Ya mike tsaye ya fice gurin ya barta a nan zaune a gurin fuska da murmushi, zuciya da annuri. Tunanin Aliyu ne raya daren Emily, tana ta tunanin da be ma kamata ta fara shi yanzu ba, ba zata iya cewa son Aliyu take ba bata shiryawa ma wannan ba, amman tabbas shi din na musamman ne a gurinta yana da wani mukami mai girma a zuciyarta a idonta kuma yana da nauyin kimar da ba zata iya aunawa ba.
Sautin karatun Kur'ane ya tashe ta daga bacci ta bude ido ta juya ta kalli Blue-Tooth din dake aje kusa da kunnenta na dama, sannan ta juyo ta kalli Fatima dake zaune tana kallonta.
"Momy kowa ya tashi tun dazun ke ce kawai baki tashi ba, har Uncle Aliyu ya zo ma, shi ne yace na kawo wannan redio mai magana amman kar na tashe ki"
Emily ta yi murmushi ta janyo yarta jikinta.
"Hmmm ban kwanta da wuri ba shiyasa na ke bachin safe"
"Uncle Aliyu yace na rika kunna miki karatun kina sauraro idan an je na saka carji yace zai rika biyana kudi idan ina haka"
Ya shafa fuskar Fatima.
"Fatima kina son Aliyu ko?"
Ta daga kai.
"Yes"
"Sosai?"
Ta daga kai.
"Shi da Dady wa kika fi so?"
Sai ta rake murya kamar mai rada tana zare ido.
"Dady, amman karki fada masa"
Emily ta yi murmushi.
"Momy ke har yanzu baki yin sallah? Kowa yayi sallah da safe, ke har yanzu ba zaki yi sallah ba? Gidan Ammy ana sallah nan ana sallah miyasa baki yi? VITO baya nan babu wanda zai dake ki"
Tana maganar tana yatsina fuska. Emily ta tashi zaune.
"Kin fara dawowa da halinki ne Fatima? Fada min magana any how?"
Fatima ta yatsina fuska ta sauka kan gadon ta fice. Emily ta juya rai a ba ce tana sake arba da Blue-Tooth din da Aliyu ya aiko mata sai bacin ran ya gushe murmushi ya cika fuskarka, ya matsa ta kai hannu tana shafa Blue-Tooth din. Sai kuma ta sauka daga kan gadon ta shiga bandaki ta wanke bakinta da fuskarta ta fito, sleeping dress din da suke jikinta masu kama jiki ne, saboda ta girmama Aliyu ta dauko daya daga cikin hijab din da Ummi ta aje mata green ta saka sannan ta fita.
Aliyu na tsaye yana magana da Nafisa Fatima na rike da kafarsa tana lilo, Emily ta fara saukowa sai duk suka kalleta.
"Wow kin ga yadda kika yi kyau?"
Cewar Nafisa, Aliyu ya kalleta daga sama har kasa ya sauke kansa kasa be sake kallonta ba har ta sauko, be kuma fasa murmushin da yake ba annuri ya cika fuskarsa.
"Ina kwana Emily"
"Lafiya kalau"
Ta amsawa Nafisa sannan ta kalli Aliyu da already ya juya.
"Ina kwana"
"Lafiya ƙalau, kin tashi lafiya?"
"Alhamdulillah"
Ya juyo da sauri ya kalleta murmushin dake fuskarsa ya fadada, sai dai be ce mata komai ba sai da Nafisa ta shiga dakin kasa.
"Alhamdulillah.... Baki taba fadin wani abu mai dadi irin wannan ba, musulunci zai miki kyau Emily sosai"
Yaja mata kujera.
"Bismillah zo ki karya"
Ta nufi dinning din ta zauna tana tambayar ina Ummi.
"Ta tafi dubiya, tace ba zata dade ba, bari na duba waje"
Fatima ta amsa sannan ta fita da gudun wajen. Aliyu ya zuba duk wani abu da yake son karyawa da shi ya dauki plate din.
"Zan shiga ciki na karya, ni ma yanzu na shigo"
"Har a cin abinci nan din ya mana kadan ne?"
Ya kalli gurin kamar wani bakonsa.
"Kin manta karatun jiya ne?"
"Aa da dare ma da shi na kwanta ina ta bita"
"Allah yasa dai kin haddace"
"Ido ma suka haddace abun da suka gani, balle abun da kunnen ya ji, ya ratsa kwakwalwa ya zauna a zuciya?"
Aliyu ya sake dubanta da kyau ita da shi suka sakarwa juna murmushi.
"Da alama dai ba zan sha wahala ba gurin taya hajarna"
"Ai tuni aka siyar maka farashi daidai da aljihunka"
Ya sauke yin murmushi amman wannan karon mai sauti, ya juya rike da plate dinsa ya haura sama. Sai da ya shiga dakinsa ya zauna sai wani tunanin ya fado masa, a take murmushin dake fuskarsa ya gushe yanayinsa ya sauya, abincin ma kasa ci yayi sai ruwan Tea kawai ya sha.
Emily na fara cin abinci sai ga Fatima ta turo kofar falon ta shigo da gudu.
"Momy Dady ya zo tun dazun yace na kira ki"
Emily ta aje spoon din hannunta, har ta yi kamar ba zata fita ba, sai kuma ta mike tsaye ganin yadda Fatima take ta rawar jiki. Ta nufi kofar da Fatima ta bude ta fita. Turhan na zaune cikin motarsa dake bude kafarsa daya tana waje, fitowa, tun da ta fito ya daga kai yana kallon be sauke ba be kuma kyabta ba har ta iso inda yake, idan yace a cikin hayyacinsa ya fito cikin motar ya tsaya a gabanta yayi karya, domin giyar kaunarta ce ta rinjaye ta hankalinsa.
"Abun bakinciki ace idan kika tashi da safe, wani ne zai yi arba da kyakkyawar fuskarki ba ni ba"
Fuska babu yabo ba fallasa ta ce.
"Na yi tunanin wani abu mai muhimmanci ne ya kawo ka"
"Duk wani abu da ya shafe ki mai muhimmanci ne a gurina Aisha"
"A yanzu ko?"
Ya sauke kansa kasa yana jin nauyinta.
"Har yanzu kina kallon abun da ya faru baya, kin kasa fahimtata Aisha, wasu na shirya min gadar zare wasu kuma sun gagara gane lissafina da abun da nake ji a zuciyata, ki yi hakuri dan Allah ki yafe min"
"Ina tunanin mun kai karshen wannan tuntuni, na yafe maka Turhan"
Ya kalleta.
"Zaki yarda ki sake zama da ni?"
"Aa"
Ya dauke wuta na dakiku.
"Na zo ne na jaddada miki cewar ina kaunarki Aisha, kuma zan tafi Sudan na san ba za ki so na tafi da Fatima, zan barta a nan saboda jindadinki, amman na zan dade ba zan dawo, kuma ina son na tafi da Fatima a yau ta ga mahaifina"
"Yayi kyau, idan ka dawo idan ba wani abu ne da ya shafi Fatima ba toh ba dole sai ka zo ka gan ni ba"
Yayi murmushi yana jin zafi a zuciyarsa ko kadan be yi zaton duniya zata juyo masa dayan shafinta ba, be yi tunanin zai zo yana rokon mace watan ma Aisha, sai kuma rayuwa ta kawo shi nan. A ka'ida be kamata ace yana zuwa gidan makiyinsa ba, mutumen da ya shirya masa zagon kasa kuma yayi masa gadar zare, amman yana zuwa saboda Emily.
Ya bita da kallo har ta koma ciki sannan ya kurdusa ya rumgume yarsa, sannan ya kama hannunta ya saka ta mota shi ma ya shiga suka bar gidan.
Ta dawo ta zauna tana cin abincin zuciyarta nata tunanin kalaman Aliyu, shi fa ba saurayinta ba ne amman kalamansa sun ratsa ko wane ɓar go na jikinta, ko Khaleefa da ta san asalin soyayayya suka yi kamin aure be zuba mata baiwarsa kamar haka ba. Ta ko'ina Aliyu ya kai namiji, yana da kyau ga siffar irin ta mazan da suka amsa sunan maza ga addini da dabi'a mai kyau, ga tausayi da kulawa, yana taka tsantsan da ita da bacin ranta, yana kokarin ganin ba su wuce gona da iri ba, ba kamar Turhan da yake sonta a yanzu da ta zama mutum ba kuma ta haifa masa yarinya, ba kamar Vito dake kokarin taba jikinta ko dukanta ba kuma ya tsani yarta, ko da yake shi din ma bata gama sanin waye shi ba, kuma be zama lallai yana sonta ba, ta kan iya yiyuwa ita din ma ba tsarinsa ba ce. Kuma anya ta shirya a yanzu?
Bata hankara cewar ta yi nisa ba sai da karar aje plate a dinning din ta dawo da ita duniyar hankalinta, ashe Aliyun ne tsaye a gabanta take kallo bata sani ba, zabura ta yi sai ta lumshe ido tana murmushi.
"Kina nan kina lissafina a zuciyarki ko? Kaman ni na, dabi'una siffofina, da kuma tunanin ko haka nake ko zan canja a gaba?"
Ta bude ido mamaki ya cika ta.
"Ta ya ka sani?"
Ya dauki plate ya rufe abincin da be ci ba.
"Zuciyata bata karya akan duk wani abu da ya shafe ki, ita take ayyana min abubuwa akanki, shiyasa da kika gudu ta hararon inda kike boya, da kika bar min wasiyar rike Fatima ita ta fada min kina kokarin giving up ne, ta haka nake iya hango hasken dake zuciyarki a game da addinin Musulunci tun kamin na ji labarinki, ita ta taimaka min gurin gasgata gaskiyarki tun gabanin tafi da ni a duniyar tarihinki"
Ta lankwafar da kai kamar zata yi kuka ido cike da shagwaba.
"Wai kai wane irin mutum ne Aliyu?"
Ya nuna kansa.
"Wai ni? Mutum ne kawai"
"Na musamman?"
Ta fada a sigar tambaya. Sai ya dan sirinar da kai kadan ya cire facing cap din dake kansa.
"Eh, ga ta musamman..."
Ta dauke kai tana murmushin da be taba ziyarta ba, shi ma ya dauke kai yana maida hullarsa hakoransa a bude.
Bayan sallah azahar tana Kitchen ita da Ummi suna hada lunch ma Aliyu da be iya cin tuwo miyar kubewa da mai aikin Ummi ta girka ba, sakamakon fitar da Ummi ta yi bata dawo da wuri ba sai ta kira waya cewar mai aikin ta girka. Shi kuma ya ji ba zai iya ci ba saboda be ci wani abin kirki ba da safe ba cikin ya zama empty be shirya sabunta shi da tuwo ba.
Ummi na mata zancen komawarsu Abuja a satin da zai shigo, da kuma yadda take ganin kamar Ammy ba zata yarda a tafi da Fatima ba. Emily kuma tana wata duniyar bata ma san me Ummi take fada ba bata komai sai murmushi ta kallon wani gurin alamar hankalinta baya jikinta. Ummi ta taba ta.
"Ke... Lafiya?"
Emily ta zabura sai kuma ta fashe da siririyar dariya.
"Ba komai Ummi"
Gogan kamar ya san wainar da ake soyawa, sai ga shi ya shigo kitchen din dubawa idan abinci ya dahu cause he's starving, be ma san da Emily ake girkin ba, sai dai ganin bakin Ummi sake da mamaki jin Emily da fitar da sautin dariya. Ya saka shi tambayar mamakin da ke fuskar Ummi.
"Lafiya?"
"Aa dariya take yi?"
Ya kalli Emily?
"Are you okay?"
Da Emily ta san Ummi ba ita take kallo ba sai ya turo baki gaba tana murmushi mai dauke da shagwaba ta girgiza masa, ya san kan garin ya fahimcin karatun tun ba a biya masa aya ba, yana son yayi murmushi ba dama saboda Ummi tana Kitchen sai kawai ya dauke kansa ya nufi fridge, a yayin da idon Ummi ya dawo kan Emily sai ta yi hanzarin sauke kanta kasa kamar ba komai. Aliyu ya dauki ruwan da ba su ya shigo sha ba ya fice gonar annashuwa ta yaɗu a kirjinsa. Sai da ya fice suka kammala shirya komai sannan Emily ta kalli Ummi ta ce
"Ummi yanzu idan ina son, na sake zama musulma zan cigaba da ibada ne kawai? Kuma kina ganin Allah zai karbe ni? Zai yafe min barin addinin da na yi a baya?"
Ummi ta aje cup din hannunta tana kallon Emily da mamakin abun da ba su yi zatonsa yanzu ba.
"Kina son ki dawo musulunci ne?"
Emily ta daga kai with so emotional. Numfashin Ummi ya fara rawa saboda farinciki.
"Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah"
Ta juya ta fice Kitchen din da sauri jikinta har mazari yake. A falo ta samu Aliyu zaune yana durawa cikin ruwa.
"Zan fada maka wata magana amman sai ka ba ni tukuici"
Ya kalli Ummi gabansa ya dan fadi ba dan tsoro ba sai dan abun da be san miye ba.
"Toh Ummi haka nan zan bada tukuici ban san girman albishir din ba? Idan aka min wayo fa?"
"Wannan mai nauyi ne, Emily tana son ta musulunta"
Ummi ta fada idonta fal da kwalla, Aliyu ya mike tsaye babu shiri ya leka Emily take tsaye bayan Ummi.
"Seee.... Riiii.. Seriously?"
Emily ta daga mishi kai, ya juya ya juyo ya daga hannunsa sama ya sauke kasa ya jimke.
"Yes.... Yes... ALHAMDULILLAH YA ALLAH"
Ya saka hannunsa aljihu ya ciro keys din ya bude hannu Ummi ya saka mata ya ciro Atm dinsa ya danka mata.
"Ga tukuicinki nan Ummi"
Ya rumgume Ummi cikin farinciki da emotional domim babu halin rumgume Emily dake tsaye hannayenta a baya tana lilo da su hawaye na sauko mata. Ya saki Ummi ya karasa gurin da Emily take tsaye.
"Da gaske kin shiryawa wannan?"
Ta daga kai.
"Ba dan cilastawa ko tsana ba?"
Ta daga kai.
"Karki yi musulunci saboda farantawa kowa, ki yi musulunci da gaskiya da mana da kaunar Allah ta tsoron azabarsa da kwadayin rahamarsa, saboda mutane suna canjawa suna gushewa, Allah baya taba sauyawa yana tare da bawayinsa na gari a kowane irin hali"
"Ina son Allah Aliyu, saboda shi zan yi na san shi ya saka min gamsuwar da nake ji, na shirya ko da zan sake shiga halin da na ninki wanda na shiga a baya, ba zan sake kuskuren barin addinin aminci da salama ba"
"Ina son zan musuluntar da ke Emily ki min wannan alfarmar"
Ta daga mishi kai.
"Zan fadi wasu kalmomi ki maimaita da su ake shiga musulunci, saboda shi addini ne mai tsari da dokoki"
Ta daga mishi kai tana hawaye.
"Ash-hadu an lā ilāha illallāh, wa ash-hadu anna Muhammadan rasūlullāh"
Yana fada tana maimaita da larabci da suka gama ya maimaita mata da hausa.
"Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma na shaida cewa Annabi Muhammadu Manzon Allah ne"
Ta maimaita kowace kalmar cikin kuka da aminci da rahama da narkewar zuciya. Aliyu ya duka gabanta ya rike kansa, Ummi ta rumgume ta tana kuka kamar yadda Emily ma take kuka.
[8/19, 7:16 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
Page 6️⃣8️⃣
Aliyu da kansa ya daga waya ya kira Mama Baraka ya yi mata albishir da labari mai dadi, sai gata ta dira gidan cikin farinciki ita da duka yaranta suka wuni gidan har dare sannan suka tafi. Washe gari Mama Baraka ta yi waina ta yi sadaka kuma ta aiko musu da ita a nan tace su yi sadaka. Kwanakin da suka rage ma Aliyu na bin Ummi Abuja da su yayi amfani yana ta koyawa Emily addinin musamman karatu da bata iya ba, da kuma wadansu hukunce hukunce wasu baki ne a gurinta wasu kuma ta taba saninsu saboda ta taba kasancewa a cikin addinin a baya.
Ana sauran kwana biyu Ummi ta tafi Ummi ta umarce Emily ta tafi gidan Mama Baraka ta fada mata zancen tafiyarsu kuma ta tafi gidan Ammy ma ta sanar saboda Fatima dake can hannun Ammy tsawon lokacin nan da Turhan yayi sati daya da barin garin Kaduna, Emily bata wani damu ba saboda ta yankewa kanta hukuncin zata bi Ummi ba kuma dan komai ba sai dan bata son ta yi nisa da Aliyu, dan haka bata damu ta sanar da Mama Baraka ko Ammy ba a ganinta kamar ita take da ikon kanta, saboda rayuwar ta da saba yi a baya, haka kuma take ganin idan ta tashi tafiyar da Fatima zata tafi ne kawai ta dauko ta a gidan Ammy.
Ba Aliyu kadai ba Ummi ma tana taba mata wani bangare na karatun, Nafeesa ma haka Mama Baraka ma ta yi maganar daukar mata malamin islamiya da zai rika zuwa yana koya mata a gida, Emily ta nuna bata so wai ai Aliyu ya ishata, kuma bata yi karya ba, domin karatun da yake koya mata kawai take ganewa saboda yana mata komai daki daki, yana mata bayani ta irin sigar da take so shiyasa idan karatun ya shiga kanta baya fita, amman sauran sai dai ta yi ta tunanin me aka ce a nan ma. Idan Aliyu ne yake koyarda ita tana maida hankali ta iya waninsa kuma karatun wahala yake mata.
Shi kanshi da ya fahimci hakan sai ya zama kullum a gidan indai ba wani abun ya fita ba, ko ya bijiro masa, a gidan yake karyawa yayi mata karatu idan ya fita ya dawo da rana su dorada dare ma kamin ya tafi gidansa sai ya fada mata. A yau bayan Aliyu ya gama koya mata karatun Sallah wanda shi yafi kowane muhimmanci yake tambayarta.
"Kin yi magana da Mama Baraka? Akan tafiyarki?"
Ta fara lilo da kafafuwanta kasancewa tana zaune kan kujera ne can kusa da motocin da suke aje a gidan.
"Aa sai idan za mu tafi zan mata bankawana"
"Kamar ya? Ta amince ki tafi ne?"
"Sai ta amince? Na saba yin komai bana jiran umarnin kowa"
Aliyu yayi murmushi ya aje littafin akan teburin dake tsakaninsu.
"Da kika ce, yanzu ke ai yar gata ce ba ke zaki yi ma kanki hange ba, yi miki za'ayi, a musulunci mace ita ta ko'ina yar gata ce, idan tana yarinya tana karkashin kulawar iyayenta ne, idan ta girma tana karkashin kulawar mijinta, idan ta tsufa tana karkashin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 54 Chapter of 63