Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da abun karyawa ne" "Ba komai, wata magana nake son mu yi dake ta fahimta, na kira Aliyu jiya ba daga ba, wata kil yana tunanin ko saboda Kameela ne..." Mama Barakat bata karasa ba saboda saukowa Emily, daga Ummi har ita kallon Emily suke. "Na ce Nafisa ta kawo miki abun karyawa ta kawo?" Kamin Emily ta amsa tambayar Ummi Mama Barakat ta ce. "Na zo mata da abinci amman bata ci ba" Ummi ta kalleta da mamaki. "Abinci kuma? Abinci aka ce mun rasa a gidan ne da har sai an dauko daga gidanki an kawo?" "Aa na yi nufin kyautatawa ne kawai" "Gaskiya karki sake Hajiya Barakat kin ga dai daga bangaren Kameela kike, duk abun da ya faru ya faru saboda Emily kar a zo a cutartar da ita ba tare da mun sani ba" Mama Barakat na yi shiru ta sauke kai kasa, Emily ta kalli Ummi ta ce. "Ina son zan tafi gidansu Turhan ko zaki iya sakawa a kai ni?" Ummi ta kalleta cike da mamaki. "Gidansu Turhan?" Emily ta daga kai, Mama Barakat ta kalleta, Ummi was speechless for a little bit kamin ta ce. "Lafiya?" "Ummi yata tana can, zan je na yi magana da su ne" "Zazzzaki iya?" Ta daga kai with full confidence. "Amman ki bari ki yi breakfast tukuna" "Hankali ba zai kwanta ba har sai na tafi, idan na dawo zan karya" "Okay, bari na yi ma direba kwatacen gurin, ina zuwa" Ummi ta tashi rike da wayarta ta fita. "Zaki iya zuwa ke kadai ko na raka ki? Kuma tafiyarki ba zata zama da matsala ba?" Emily ta kalli Mama Barakat ya wacce ta yi maganar ta gafen ido. "Na saba rayuwa da yin abubuwa ni kadai wannan ma zan iya" Ta nufi kofa ya bude ta fita, a Entrance din ta tsaya tana sauraren Ummi dake fadawa direban inda zai kai Emily. "Number gidan dai na manta, bari na tambayi Aliyu" Ta daga wayarta a gurin ta kira Aliyu ta tambaye shi house number nawa ne gidansu Turhan, sai da ya fada mata sannan ya bukacin jin dalilin tambayar. "Za mu yi magana daga baya" Ummi ta kashe wayar ta kalli direban. "Number 7" "Tohm Hajiya" Ya juya ya sauka ya nufi wata farar mota sai da ya juyo da ita sannan ta sauka ta nufi motar ta bude gidan baya ta shiga ta zauna, direba ya dauki hanya. TURHAN POV. Be yi nisa da gida ba kiran mahaifinsa ya shigo min wayarsa direct international call from Sudan to Nigeria, cikin hanzari yayi fakin yana dan jin faduwar gaba, domin abu ne mai wahala mahaifinsa ya kira shi, idan ma wani abu ne yawanci sai dai ya bar masa sako ta whatsapp ko kuma ya sanar yace a sanar masa. Ya amsa kiran cikin ladabi mahaifin nasa be ko tsaya gaisuwa ba ya gabatar masa da dalilin kiransa. "Wani labari na ji yanzu akanka.... kuma ina fatan ba gaskiya ba ne" Ya fada da yalshen larabci, Turhan ma ya mayar masa da yaren da suka fi fahimta. "Wane labari ne?" Mahaifin yayi shiru ma tsawon lokaci. "Cewar kana da ya da wata mata da ban sani ba?" Turhan ya ji gabansa ya fadi, amman hakan be hana amsawa mahaifinsa ba. "Eh gaskiya ne, amman ni ma ban san da yar ba sai a yanzu, tana tare da ni yanzu haka" "Hmmmmmm... Shiyasa na samu kira cewar mu iyaye ya kamata mu tsawatar saboda a bawa kowa hakkinsa, taya abubuwa suka faru haka ban sani ba?" Cikin isa da isa da kasaita yake maganar kuma cike da zafin ran dake bayyana bacin ransa. Turhan zai yi magana ya kashe wayar sai ya maida masa kira be daga ba. Babu tantama ya san mahaifinsa yayi fushi, sai dai fushinsa ba zai hana shi bayyana gaskiyar komai a yanzu ba, ya san zai fuskanci kalubale daga gurin mahaifinsa da kuma matarsa amman ya shiryawa hakan, kuma ko za aje sama a dawo na zai saki Emily ba saboda yarsa da kuma lokarin gyara abun da ya bata, and of course Emily ta cancanci zama matarsa. Juya motar yayi ya dauki hanyar gida, ya faka harabar gidan ya fito motar zuciyarsa da kansa cike da tarin abubuwa da suke kokarin rinchabe masa, amman dai yana jin zai iya dauka ko dan bawa marasa ษ—a kunya.. Ya tura kofar falon ya shiga, sai ya hango Ammy a inda ya barta zaune a dinning tana karyawa. "Ammy Ina Fatima?" Ita ya fara tambaya domin tabbatar tana gidan ko aa what if bayan fitarsa an fita da ita and the way da ya ga Mahaifiyarsa ta dauki zafi akan Emily tsab zata iya damka mata ita ba tare da saninsa ba. Ammy ta kalli Stairs as her response, wani Sighs of relief yayi sannan ya sake kallonta ya ce. "Ammy ke kika kira Mai Martaba kika nemi ya tsawarta saboda bawa kowa hakkinsa?" Ammy ta maa kallon rashin fahimta da kuma mamaki. "Ko da mafarki kar zuciyarka ta raya maka zan iya daga waya na kira mahaifinka balle har na nemi ya shiga cikin wani lamari da ya shafe ni, ka tofar da wannan yawun, bana son shi...!!!" Ya fara takawa zai karasa inda take yana mata bayanin kiran da aka masa, aka turo kofar falon sai ya juya Ammy ma ta kalli kofar dukansu suka yi arba da Emily fuska babu annuri, juyowa Turhan yayi yana kallon Confidence din dake tare da ita wanda ya kara mata kyau da haiba, babu murmushi ko alamarsa a fuskarta amman haka be hana goga fahimtar kyaun surar da Allah ya tsaga a fuskarta da sigar jikinta ba, ga tufafin sun karbe a color kuma sun mata cif in size domin palazon irin wannan ne mai matsewa a sama ya bude a kasa. Emily ta taka ta shiga cikin falon tana wani taku dake nuna ta shiryawa duk wani hargitsu na su. Ba shiri Ammy ta mike tsaye tana kallonta sai kuma murmushi ya cika fuskarta. "Aisha kin zo? Yau kin tuna gida?" "Eh na zo na tabbatar da abun da kika min alkawari, kuma na tafi da yata" Turhan ya maida hannayensa baya ya cira kafa daga ya fara takawa har ya isa inda take tsaye ya tsaya gabanta, yana wani sham kamshi. "Wannan ba Aisha da muka sani ba ce, me yasa kika bari suka cusa miki wannan tunanin da wannan rayuwar a zuciya?" Emily ta kara ta ku biyu forward. "Sautin murya nake ji, amman bana ganin mai magana, saboda mai maganar ba mutum ba ne, kusa ce da fatar akuya" Turhan ya kalli bakinta dake motsi yana kyalli da man data shafa masa, ya hade yawu a hankali, kamin ya kalli kwayar idonta mai matukar daukar hankali. "Na yi kuskure, na bata abubuwa da yawa, amman yanzu lokaci ne da zan gyara, kina da damar ki tsane ni ko ki aiwatar da duk abun da kike so a kaina, amman Please ban da zancen rabuwa" "Kana da karfin hali, har a yanzu umarnin kake ba ni? To wacan Aisha ta mutu, wacan Aisha ita ce kaza, ni kuma Zabuwa ce fira nake, ban zo nan dan na yi musayar kalamai ga wanda be san mutunci kansa da na mahaifiyarsa ba, So...." Ta kauce gabansa ta nufi gurin da Ammy take tsaye tana kallonta rai a bace. "Taya kika sauya Haka Aisha tun daga kan sutura da hali da addini ba wanda muka san ki da shi ba ne" "Danki na daga cikin mutanen da suka sauya ni, ko dai na sake maimaita miki labarin ne?" "Wannan rashin kunyar duk na minene Aisha?" "Na neman rabuwa da mutumen da ya fifita son zuciyarsa ne akan ra'ayin mahaifiyarsa, na yi zaton kin sa ya rubuta takardar ai, kawai zan karba ne ko kuma ki kawo min domin tabbatar da furucinki" "Saki ko? Yanzu nan zai sake ki" Ammy ta nufi stairs, Turhan ya bita da kallo gabansa na faduwa wani hadarin tashin hankali yana haduwa a cikin kansa. Kasaita sarauta da isa duk ciresu yayi ya jingine ya nufi Emily ya sake tsayawa a gabanta, tana daga kai ta watsa masa wani kallo sai da gabansa ya sake bugawa da karfi, ta cika shi da kwarjini. "Dan Allah ki fahimta, na san na bata miki na kuntata na munana miki, abubuwa da yawa sun faru, na rashin jindadi da cutarwa, amman ki yi hakuri, ina son ki fahimci cewar ni dan adam ne, dole mukan yi kuskure... Ko... Ko ganganci, amman mafi girman kuskure shi ne kasa gane cewar kuskure ne, ki yi hak'uri Emily ki yafe min" Emily ta dauke kai zata matsa daga gabansa sai ya kai hannu ya rikota. Hannunsa da gurin da ya rike ta kawai ta kalla ta dago ta watsa masa wani mugun kallo, ba shiri ya dauke hannunsa a jikinta a tsorace. "Please... Kar mu dawo muna nadamar abun nan, ki duba rayuwar ki da ta Fatima, ba zata ji dadi ba bayan tsawon lokacin nan ta tashi ba tare da mu ba, abu ne mai wahala ki iya jure ziyararta a koda yaushe, idan ke baki bukatata a rayuwarki ni ina bukatarki" Emily bata ce masa uffan ba, hankalinsa be kara tashi ba sai da ya hango Ammy na saukowa rike da takardar da biro. "No no nooo Ammy ni fa ba zan sake ta ba, ke kika sa na aureta, na ji na yi kuskure to ku ba ni damar gyarawa mana, duk wata wuta da zata kunna zan iya tarar ta, amman ban da rabuwa, wannan be dace ba, na shirya fuskantar ko wanw kalubale a yanzu, And Emily na shirya gabatar da ke har a gurin mahaifina da kuma ฦดar mu Fatima, zan mu na komai a yadda ya dace" Ammy ta karaso gurin ta mika masa da biro. "Rubuta mata saki" Ya matsa baya ya girgiza ma Ammy kai. "Ammy please... Karki cilasta ni wannan, ki kan ba ni umarni na bi dan Allah kar mu samu tsabani a nan, ko sakinta na yi makiya ma dariya za su mana" "Ka dubuta mata saki Turhan" Ammy ta furta cikin kakkausan halshen. Yaja kujerar dinning ya zauna ya rufe ido yana murtuke fuska kamar mai shan wani abu marar dadi. Ya sake bude idon ya mike tsaye. "Bari na yi magana da ita" Ya karasa gaban Emily ya kama hannunta ya rike cikin yanayin dake bayyana tsakanin damuwarsa. "Dan Allah Emily ki yi hakuri ki yafe min, ki ba ni dama na gyara kuskuren da na aikata, ki yi hakuri Emily zan canja, na ma manja ba yadda kike tunani ba ne, zan baki duk wata kulawa da kike bukata" Ko kallonsa bata yi balle ta yi wani reaction da zai nuna ta fahimci kalamansa. "Ka sake ta na ce" Ya kalli Ammy kamar ba shi ba. "Ammy dan Allah karki cilasta ni aikata abun da ban yi niya ba, ba daidai ba ne... I... I... I love her... Ina son... Matata, rabuwarmu zata kara bata abubuwa ne kawai, ya kamata mu fahimce ta zafin zuciya ne yake debanta take kalamai marasa dad..." "Zaka sake ta, ko sai na barranta ka daga gani ni" Ya kalli Ammy babu shiri sai ta sake nanata masa. "Ka sake ta yanzu nan" Kamar wanda aka yi ma shocking haka ya rumgume Emily da sauri ya matse ta a jikinsa ya runtse ido, ya dauki dakiku a haka Emily bata motsa ba sai ya sake ta koma ya zauna ya Ammy ya dora masa takardar a dinning da pen. "Idan baka sake ta ba, ban yafe haihuwar da na yi maka ba Turhan...!!!" Ya kalleta cikin tashin hankali da rashin madafa. "Ammy...." Ya masa cewa komai hannu na rawa ya dauka ya dora a takardar ya kama biron baya ko iya rubutawa har sai da ya saka dayan hannunsa ya rikw hannunsa na dama, ya sake dagowa ya kalli Emily. "Ba zaki ce komai ba Aisha? I'm sorry i Love you, idan ba zaki yi dan ni ba ko dan Fatima" Emily ta ki ta kalle shi. Sai ya kalli Ammy idona na zubar da hawaye ya ce. "A koda yaushe ni mai biyayya ne a gareki, da dadi ko ba dadi, zan saki Aisha, amman ba dan raina na so ba, sai dan ba zan iya jure tsinuwarki ba, amman dai ba haka raina ya so ba" Ya maida hannunsa yayi rubutun da larabci hannunsa na rawa, sannan ya dago takardar ya mikawa Emily, sai a lokacin ta kalle shi tana jin wani sanyi a ranta. "Ashe kana iya kuka Turhan, ko kuma na munafunci ne irin yadda ka yi a lokacin da za mu bar Kasar nan zuwa Sudan" Ta fisgi takardar daga hannunsa, sannan ta juya ta kalli Ammy. "Ina yata?" "An dai baki takardar da kika bukata, kuma na fada miki za a tabbatar miki an kuma yi haka, takardar ita ce wajibi" Emily ta daga kai ta kalli stairs da nufin kiran Fatima sai ta hangota tsaye tana kallonsu tana kuka, bata fahimci me kai da kawo ba ita dai kawai abin da ta gane mahaifinta na kuka Emily ta ki jin tausayinsa. Emily ta mata murmushi ta mika mata hannu. "Fatima zo mu tafi" Fatima ta sauko da gudu Ammy ta juya da nufin idan Emily ta yi yunkurin rikonta ta hana, Turhan kuma hankalinsa ya kara tashi ganin zai yi 2 - 0. Fatima na saukowa ya nufi Turhan ta rumgume shi. "I love you Daddy, stop crying" Emily ta kira sunanta da karfi. "Fatima wannan mutumen da kike gani, ba mutunen kirki ba ne, shi ya bar mu a tsawon shekarun nan, baya son ki ya cutar da ni" "Be cutar da ke ba, na ga yana kuka yana cewa yana sonki, me ya kika min karya Momy miyasa baki son na samu Baba? Kowa yana da baba amman ni ba ni da shi?" Turhan ya dauke ta ya dora a kafada ya rumgume yana jin sanyi a ransa. "Fatima wannan mutunen ya cutar da ni ya wofintar da ke" "Duk abun da ya faru ya faru ne saboda be san an haife ta, kin samu abun da kike so dan Allah ki tafi" Ammy ta fada. "Ba zan tafi ba sai da yata, daman mun saba rayuwarmu ba da ku ba, da Fatima zan tafi" Emily ta fada sai ta nufi Fatima ta riko hannunta zata rabata da jikin Turhan, a take Fatima ta fisge hannunta. "Bana son na tafi tare da ke, ina son babana i hate you" Emily ta fisgota da karfi, sai Fatima ta saka mata ihu tana kuka. "Bana son na tafi da ki, Babana nake so" Emily ta kalli Turhan. "Na rainin cikin yarinyar na haife na raine ta har ta kawo yanzu, ba tare da kai ba, a yau ka bayyana a rayuwarta ka cusa mata kiyayyata alhalin kai ne makiyinta, hakika kai azzalumi Turhan" Turhan ya girgiza mata kai alamar ba shi da laifi, Emily ta juya ta nufi kofar fita, zai yi magana Ammy ta rike hannunsa ta girgiza masa kai. Emily ta fita falon tana zubar da hawaye ta nufi motar da aka kawota ta shiga tana kuka, har direban ya isa gida kuka take, haka ta motar ta nufi entrance din taka ta isa bakin kofar falon, a kokarinta na saita kanta ya jingina da window falon tana maida numfashi. "Ki taimaka min dan Allah, ban san ta ina zan tunkareta ba, ba lallai ta fahimta ba, amman ina son Emily fiye da sauran yayana kuma tsawon lokacin nan Wallahi ban san inda take ba, ban ma san yadda abubuwan nan suka faru ba..." Ta ji muryar Mama Barakat tana maganar cikin kuka, Emily ta dago daga jikin window falon tana jin wani jiri yana debanta, kawai sai ta ji mafarki take ta girgiza kai ta juyo rike da takardar da kuma wayar, ta nufi gate mai gadi ya bude mata ta fice, haka ta kama hanyar titi, ta taba fuskarta sai ta ji kamar ba tata ba, idonta har wani rufewa suke suna budewa hawaye suka fara mata kwarara. Tsayawa ta yi cak ta kalli gabas ta kalli yamma, ta kalli kudu ta kalli arewa, ta kalli sama ta kalli kasa sai ta rasa a ina take. Babu wanda ya fado mata a kwakwalwa sai Dr A-B, ta share hawayen ta dago wayarta ta kalli screen din ta bude ta shiga ciki, one by one ta rika bin number har ta isa gurin number Dr A-B ta danna masa kira. Ta yi ringing uku ya daga. "Hello..." "Emily ce i need your help, ina tunanin kwakwalwata ta samu matsala" "Daman na san zaki kira, a ina kike?" "A inda nake" "Zaune ko a tsaye?" "A tsaye nake" "Samu guri ki zauna ki bawa wani na kusa da ke wayar" Ta mika wayar a iska ta sake ta, sannan ta zauna a kasa, tana bin ko'ina da kallo kawai rayuwar mafarki take ganinta.... [7/19, 5:10โ€ฏPM] ๐—ž๐—ต๐—ฎ๐—ฑ๐—ฒ๐—ฒ๐—ท๐—ฎ ๐—–๐—ฎ๐—ป๐—ฑ๐˜†: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=KhadeejaCandy *๐Ÿ’ ABOKIN RAYUWA ๐Ÿ’* *ยฉ Khadeeja Candy* Page 5๏ธโƒฃ4๏ธโƒฃ Sai da Emily ta fice daga gidan sannan Ammy ta saki hannunsa, ta juya ta nufi stairs ranta a bace zuciya kuma ta yi mata nauyi, bata yi zaton abubuwa za zo a haka, ko ba komai kyautatarwa da ta yi ma Emily bata cancani yi mata hakan ba, and ba ita kadai ce mace da za'ace an fara sakawa a damuwar ษ—a namiji ba, balle ace ita ce ta karshe, mata da yawa an yi musu abun da ya fi nata ciwo da kuna wasu ma sukan yafe tun gabannin a nemi yafiyar balle ita da har an jefa kai a kasa saboda ita, ga kuma yarinya me yasa ba zata kalli wannan ba? Ai ta san yadda rashin uba yake da ciwo me zasa ba zata yi ma yarta fatan rayuwa a karkashin inuwar uba ba? Ta zauna bakin gado, wani bangare na zuciyarta yana raya mata wata kila ba laifin Emily ba ne, domin gaba daya wannan ba rayuwarta ba ce, ba mamaki zugata aka yi, indai har zata iya amincewa ta auri Turhan saboda Ammy to taya zata iya kallon idonta ta fada mata magana kuma ta tsaya tsayin daka a cikin gidanta akan lallai sai Turhan ya sake ta, idan an ciza ai hurawa ake, ta san danta be kyauta ba, amman a yanzu yayi nadama, kuma idan danta be yi daidai ba me yasa ita zata saka ta a ciki? "Lallai makashinka yana tare da kai" Ta furta tana jinjina kai, Aliyu da Ummi take hararowa, ba iya alakarta da Ummi ba, daman gaisuwa ai ba sosai suke ba, amman Aliyu da Turhan abokai ne be kamata Aliyu yayi ma Turhan haka ba, ko dan abotarsu da kuma ganin idonta, ta yarda da zancen Emily cewar ta roke shi kar ya fada saboda bata son suna san rana raye, amman bata gamsu wannan ce kadai hujjar da Aliyu zai rike ya ki fadawa Turhan inda Emily take ba bayan kuma ya san har da ya a tsakaninsu, wannan rashin kunyar da da dagiyar ma saka mata su aka yi akai ba nata ba ne. Sai dai dalilin da zai saka Aliyu ya aikata hakan ne bata gano ba har yanzu, sonta yake mana, daman can Emily tana da kyau balle kuma yanzu, amman abun kunya ne ace Ummi ta goya masa baya, idan ba haka ba ai matarsada ba zata yi kishi ba. Ta dago ta kalli kofar dakin Fatima ta turo ta shigo tana rike da teddy. "Dadyna ya ce na shigo zai tafi ya dawo, yace na zo gurinki" Ammy ta yi murmushi ta bude mata hannayenta, Fatima ta tafi ta shiga jikinta, Ammy ta rungume ta sosai tana sauke ajiyar zuciya har tana jin kanta na ciwo, burinta ta yi zuriya ta samu rayuwa mai kyau ta gurin danta domin ita tata rayuwar ta lalace, amman hakan ya gagara. "Ina son ki sosai Fatima, ina son ki saka wannan a ranki, ni da Mahaifin ki muna matukar kaunarki" Fatima ta dago ta kalleta. "Ke ce kika haifi Daddyna?" Ammy ta daga mata kai. "Kin san waya haifi Momy na?" Ammy ta girgiza kai. Sai ta maida kanta ta kwanta jikin Ammy. Ammy ta sauke numfashi a hankali, tana kallon kofar dakin zuciyarta na raya mata Turhan ya bi bayan Emily ne. "Ina son Dadyna, ba zan bi Momy ba ba zan tafi gurin Vito ba, i hate him" Fatima ta fada ta daga kai ta kalli Ammy. "Momy zata zauna a nan ai ko?" "Haka muke fata, abun da ni da Mahaifin ki muke ta kokarin yin kenan" Ammy ta amsa mata yanayin fuskarta na sauyawa, tana mamakin Emily ta dayan bangaren kuma ta yi mamakin Aliyu, ta kara rumgume Fatima... TURHAN POV. Sai da Ammy ta yi minti talatin a dakin sannan Sauke Fatima ya nuna nata teddy dake kan kujera. "Dauki Teddy dinki, ki tafi gurin Ammy ni zan fita na dawo" Ya fada mata da hausa yana mata na kurame domin ita ba fahimtar hausa take ba, shi kuma be gwane a turancin ba, ya sumbance ta ya nuna mata kumatunsa ta sumbance shi tana jin dadi. "I love you" "I love you Too" Ta mayar masa sannan ta yi masa bye bye, tana hawa tana daga masa hannu har sai da ya fice sannan ta haura sama gaba daya rike da Teddy. Motarsa ya nufa ya bude ya shiga yayi mata key, ya bi bayan Emily, shi kansa ya san be kyautu ace ya sake ta ba, amman saboda Ammy ya aikata, sai dai sakin ba yana nufin ya barta ta cigaba da rayuwa a gidansu Aliyu ba, kattan banza suna kallon matarsa ba, gashi ba wani suturta masa jikin take ba, kuma ta tafi da fushisa yana bukatar ya same ta su tattauna mafita, domin shi kam a yanzu be hangowa kansa rayuwa babu ita ba, ko ba komai ta ba bashi abun da kudi ba sai siya ba, ita ce mace ta farko da ta maida shi uba wannan farinciki da jindadin da alfaharin ba zai taba gushewa a gurinsa ba, kuma a yanzu ya shirya gabatar da ita a gaban kowa, gashi ma har mahaifinsa ya sani which be san ta iya ya ji haka ba... He can risk anything to be with Emily yanzu kam, abubuwan daya bata sai ya gyarasu sannan hankalinsa zai kwanta, idan ya gabatar da ita a matsayin baiwa a yanzu yana son ya gabatar da ita masarautar a matsayin mace mai tsada kuma mai cikakke ikon a gurinsa, domin Emily ta gama masa komai a yanzu, ta haifa masa ya, kuma ita ce macen da mahaifiyarsa take so. Farat daya tunanin abubuwan da yayi mata suka fado masa a rai sai ya rasa ina zai saka kansa, yana tunkin yana kawar da da wasu wata zuciyar na ba shi shawarar yadda zai gyara wasu. Ya karasa gidan Aliyu sai da ya tsaya a gurin gate din sannan ya tuna Aliyu ma ai baya nan kuma Ammy ta fada masa a gidansu Aliyu ta samu Emily, a take ya juya Motarsa ya dauki hanyar gidansu Ummi daman babu wani tazara sosai. "Kina takurawa kanki ne kawai Aisha, duk wani abun da za su fada miki ko su nuna miki na karya ne, hakika ba ki dace da kowa sai ni" Ya fada yana tuka motar, ko kadan be so sakinta sai dan babu yadda zai yi ne, wani nauyi yake ji a kansa kamar shi aka saka ba wai shi yayi sakin ba. Daf da zai karasa gidan wayarsa ta yi kara alamar kira, ya duba sai ya sake arba da number mahaifinsa a nan ma sai da ya faka sannan ya amsa wayar ba tare da ya kashe motar ba. "Hello Abie" "Ka bar duk abun da kake ka dawo gobe ina nemanka" Ya fada masa da larabci kamin ya amsa masa ya kashe wayar. Turhan ya kifa kansa da sitarin motar ya cije baki, yana jin bakin cikin yadda aka yi mahaifinsa ya sani ma, waya fada masa me yasa aka fada masa a yanzu, yana da shirin gabatar ma mahaifinsa da komai amman ba a irin wannan yanayin ba, yayi nufin sai idan abubuwa sun gyaru shi da Emily ga kuma yarsa. Yanzu be isa ya ki tafiyar ba, alhalin kuma be shirya mata ba, domin a yanzu baya son abun da zai saka shi yin nisa da Emily. Ya dago cikin damuwa ya cigaba da tukin har ya isa bakin gate din gidan yayi horn mai gadin ya tambaya ya fada masa ciki zai shiga gurin Ummi sai ya bude masa gate, Turhan ya shiga ya faka harabar gidan ya fito yana wani shan kamshi ya doshi Entrance din da Ummi take tsaye tare

Chapter 43 of 63