miki tawa, ni da ke mun zama yan'uwa daman ni bani da kawa a nan kawata daya ce kuma sarkin kishi ce saboda mijinta bana son zuwa gidanta, ina zaune a gurin wata yayata, ke kuma daman na taba sauke ki a gidanki, amman asali ni yar Kaduna ce"
"Amman ke me ya kawo ki nan"
"Bautar kasa"
Emily ta daga mata kai alamar gamsuwa, sannan ta saka mata numberta ta karbi nata number. Ta mike tsaye
“Zan tafi wata kila yarana suna bukatar gani izuwa yanzu"
"Hakan yana da kyau, muje na rakaki"
Tamia ta rakata har gurin motarta sannan ta yi mata sallama tana daga mata hannu har ta yi nisa.
[4/26, 5:40 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
Page 1️⃣6️⃣
Yadda ta bar gidan haka ta same shi domin kusan lokaci daya Emily ta shigo gidan tare da Chidimma da London.
"Ina kokarin gyara falon ne da gidan ne yanzu sai na dora abinci"
Ta fada ganin yadda Emily take kallonta.
"Ina London"
"Tare muka dawo an sallame shi"
Har Emily ta juya sai kuma ta juyo ta kalli Chidimma.
"Baki kira ni na daukoku ba?”
"Na ga kin fita a cikin fushi ne, shi ma kuma fushi yake da ke, ina gudun bacin ransa ne, shiyasa sai na kira Sir Vito ya kawo mu gida"
Emily ta juya ba tare da ya sake cewa komai ba.
“Ki yi hakuri da abun da London yake miki, kin san yana dauke ta lalura ne, amman a hankali zai fahimta ya daina kamar yadda yake yi abaya"
Har ta ci ta cinye Emily bata sake juyowa ba haka kuma bata sake cewa komai ba ta haura sama ta shiga dakinta sai ta samu Vito zaune a ciki yana kallon kofar data shigo.
"Ina kika je?"
"Inda nake ra'ayin tafiya"
Ta amsa masa rudely, kallonta kawai yake har ta nufi closet dinta ta cire talkamin kafarta. Ta saba fada masa bakar magana but like ya tambaye ta wani abu ta amsa masa da wata maganar dabam. Wayar dake aljihunta ta yi ringing ta ciro wayar ta amsa ba tare da fargabar komai ba.
"Kin isa gida lafiya?"
"Lafiya kalau, na gode da kulawa"
Ta aje wayar a gefen closet din bayan ta amsa.
“Da wa kike waya?"
"Will you excuse me? Ina son na huta ne"
Ya sake dubanta a tsanake kamin ya mike tsaye ya fice daga dakin. Yana fita ta sauke numfashi da karfi ta lumshe ido tana sauraren yadda zuciyarta take bugawa da karfi.
Vito ya sauko yana kallon Fatima dake gabansa kadan tana saukowa, juyowa ta yi tana kallonsa har ya kawo daidai inda take tsaye.
“Vito... Kasan waye babana"
"Emily bata fada miki baki da mahaifi ba?"
"Meyasa ni kadai ce a makarantar mu ba ni da Baba? Kowa a duniyar nan yana da Baba amman ban da ni why? Meyasa sunana yake Fatima Aysha Emily?"
Ya rage tsawo ya risina daidai ita.
“Saboda ke kadai aka haife ki, you're special girl with bad attitudes"
Ya barta a gurin tana binsa da kallo cike da tsana, fasa sauka ta yi ta koma sama ta shiga dakin dan'uwanta. Wanka Emily ta yi ta fito ta shirya cikin short gown ta atamfa ta zauna gaban madubi tana kallon kanta. Maganganun Tasmia suna ta yi mata yawo akai, sai ta ji ina ma ace wani ya fada mata haka tun a baya, ko da yake a yanzu din ma lokaci be kure ba. Ta yi murmushi.
"Ina fatan yadda kalamanki da fuskarki suke, haka zuciyarki ma take"
Ta fada sai ta bude aljihun madubin dake gabanta ta dauko wani karamin box ta ciro agogon mutumen da ta kasa manta yadda ya taimaki rayuwarta har ta rayu. Ta shafa agogon tana rausayar da kanta.
"Ku biyu ne kawai musulmai masu halin kirki, kai ka bar min shigo Tasmia kuma ta bar min kalamai"
Ta karasa tana murmushi, sai kuma ta mike tsaye ta nufi jakarta ta saka agogon ciki ta nufi wayarta da sako ya shigo ta duba.
"Zaki iya zuwa office a duk lokacin da kika shirya, Office dinki yana nan yana jiranki"
"Why? Saboda kai ma ka yi amfani da wannan damar ka shimfida min dokoki ka mulke ni a yadda kake so?"
Ta yi jira har ta gaji be dawo mata da amsa ko wani sakon ba. Aje wayar ta yi ta fice daga dakin zuwa dakin da danta yake, wasa ta samu yana yi da Fatima har da dariya sai dai shigowarta ya saka dukansu su biyu yanayinsu ya sauya, Fatima ta dan hade rai, shi kuma ya juya mata baya gaba daya irin yadda yake idan yana fushi baya son kallon fuskar mutane. Ta zauna akan gadon ta kai hannu ta shafa bayansa.
"My babu, har yanzu fushi kake da Momy? Why saboda Momy ta jima bata zo ba? Me Momy ta yi ne London har kaka juya mata baya? Momy da take kaunarka? Taka siya maka abun dadi...? Ina kake son mu tafi? Kana son mu yi wasan ruwa?"
Duk rarrashin da ta yi masa da kalamai be juyo ba kuma be sauka daga fushin ba, da ta yi kokarin juyo da shi ma sai ya saka mata ihu ya ruda dakin har sai da Chidimma ta bar abun da take ta shigo ta rumgume shi. Tashi ta yi ta fice daga dakin ta sake komawa dakinta, ta kwana da tunani kala kala a ranta ta kulla wannan ta kwance wacan, daga karshe ta bi tsarin da zuciyarta ta dorata ta hau ta hakikance cewar ba zata koma aiki ba, amman zata nemi wani aikin domin cika burin da take da shi.
Washe gari ita da kanta ta shiryawa yaranta abun karyawa, ta zubawa Fatima nata a lunch box na London kuma ta bawa Chidimma ta ba shi, ita kuma ta koma ciki ta saka kanana kaya da sneakers ta fito ta shiga kitchen ta dauki water bottle ta zuba swan water sannan ta fito.
“Zaki tafi wani gurin ne Ma'am?”
"Yes zan je motsa jiki ne"
Chidimma ta dan tabe baki kadan domin ba abun da Emily ta saba yi ba, Emily ta nufi London da Chidimma ke feeding dinsa ta sumbance shi ta shafa kansa sannan ta fice tana fadawa Fatima ta yi hanzari direban dake kaita school yana jiranta.
"Yau ba zan je School ba"
"Saboda me?"
"Saboda kowa yana tsokana ta a makaranta, idan aka kira sunana"
Ta fada tana huci, Emily ta aje gorar ruwan dakin hannunta ta nufi Fatima ta kama hannunta nufi sama da ita. Ta zaunar da ita kan gado.
“Cikin masu miki dariya akwai wanda ta fiki gata? Ko ta fiki kashe kudin da kike kashewa?"
Ta girgiza kai kamar zata yi kuka.
“Toh karki sake bata ranki idan sun fada miki haka, ai su iyaye maza suke da, ke kuma kina da uwa mace jajirttaciyya mai kokarin sama miki rayuwa mai kyau, mai son abun da kika so, ba kin ce kina son mu bar gidan nan ba.?”
Ta daga mata kai.
“Duk abun da nake kokarin aikatawa a yanzu na yadda zan bar gidan nan ne, ki kwantar da hankalinki ki daina damuwa da abun da suke fada miki, kuma ki daina fadawa kowa labarin ki Fatima ke ma kina da surutu, idan suka miki dariya kice haka kike so, kuma ke baya damunki, ki min alkawari ba zaki sake damuwa da maganaer su ba, ni kuma zan miki alkawarin barin gidan nan cikin kankanen lokaci kuma na siya miki duk abun da kike so, tashin hankalinki tashin hankalina ne Fatima, karki sake min magana makamanciyar wannan“
Ta daga mata kai sannan ta kai mata yatsa.
“I promise"
"Good yanzu shiga ki wanke fuskarki idan kika yi haka kin wanke bakin ciki babu sauran damuwa sai ki fito da murmushi muje na rakaki mota"
Ta tashi da saurinta ta shiga bandaki ta wanke fuskar ta fito da murmushi Emily ta kama hannunta suka fita tana far'a kamar na ita ba. Chidimma na kallonsu har Emily ta dauki lunch Box dinsu suka fice, sannan ta kalli London da fuskar tausayi tace
“Ka gani Momy bata son London sai fatima, idan London yayi fushi Momy bata tsayawa ta rarrasheshi amman tana tsayawa ta rarrashi Fatima”
Ya bata fuska sosai yana ta yawo da idonta ta saki baki yawu na sauko masa, ta cire tissue ta goge masa bakin.
“Amman Chidimma tana son London sosai bata masa fada, Sir Vito ma yana son London amman Momy bata son London"
Ta matsar da kujerar ta kusa da tashi ta rumfume shi tana murmushi tare da shafa bayansa alamar rarrashi. Sai da Emily ta ga wucewar motar da aka dauki Fatima zuwa makaranta sannan ta fara tafiya da sassafar, tafiya ta yi mai nisa har ta fita daga unguwar daga daya, daman manufar fitar ba domin motsa jikin ba ne kawai. Unguwar dake kusa da ta su ta shiga tana kallon shagunan da suka gurin wanda ta ga alamar babban shago ne ko super market sai ta dauki hoton gurin saboda kar ta manta. Kusan duk inda ta bi kallonta ake saboda yanayinta, kusan kowa kallon baturiya yake mata saboda yanayin shigarta idonta da kuma gashin kanta dake bude.
Taxi ta hau a lokacin da zata dawo gida saboda gajiya da ta yi, cikin gidan ta shiga ta dauko masa kudinsa ta ba shi sannan ta koma ciki ta yi wanka ta karya ta haura sama domin bawa gado hakkinsa.
KAMEELA POV.
"Na jidadi sosai ko da na iso na tarar an kawo min komai na gode Honey"
"You deserve it, Allah ya kara miki lafiya"
"Ameen, yaushe zaka zo?"
"Soon dear"
"Ka kula min da kanka"
"I will"
Ta sauke wayar tana kallon kanwarta dake tabe baki, Anty Shafa data doro alwala ta tana yarfar da ruwa ta ce.
“Kina godiya akan abun da kin fi karfinsa, dole ne daman yayi miki hidima tun da haihuwa kika yi kuma dansa kika haifa ba dan wani ba"
"Hmmm Anty Kameela da yanzu ke matar Governor ce, da yanzu ke ce first lady, amman kika ki yarda kika watsa mana kasa a ido kika zabi dan makiyinmu"
Ta sauke numfashi.
“Siyasa ce fa, saboda Baba ya rasa kujerar Senator mahaifinsa ya samu ba wani abun ba ne, kowa rabonsa yake ci, kuma zamansu yar jam'iyar hamayya wannan siyace, daman ta gaji haka, ni ba zan iya zaman kishi da sa'anin mahaifiyata ba akan zama first Lady, kuma yadda nake da kishin nan ba zan iya raba kwana da wata mace ba, kuma ba zan iya auren dan siyasa, dan haka ku bar ki na zauna da mijina muna son junanmu"
"Ga ki gashi ai idan namiji ne, har da wani yarda da alkawarin da yayi miki saboda baki da tunani, mahaifiyarsa har magana ta fada min wai ban yi aure ba"
Cewar Anty Shafa again tana kokarin saka hijab.
"Aliyu ya san ni ya san halina kuma ya san suwaye iyayena ba zai taba yarda ya karya alkawarin da ya daukar min ba, domin ya san yadda zan hana shi zaman lafiya"
Anty Shafa ta tabe baki ta kabbatar sallah, Farida kuma ta yi dan tsaki.
“Har abada dai Wallahi bana son Aliyu bana son iyayensa, domin shi ne silar bakincikin mahaifinmu"
"Sai ki kashe shi idan baki son shi"
Kameela na rufe baki aka turo kofar dakin, Mama Barakat ce ta shigo dakin da far'arta.
“Maa Shaa Allah, Kameela jiki yayi kyau"
Kameela ta wani hade rai ta juyar da fuska kamar ba ita ake yi ma maganar ba. Farida ta amsa.
“Eh jiki yayi kyau sosai Mama Barakat"
"Sannu Kameela ashe kuma dan be zo da rai Allah ya baki lafiya ya bada na aikawa yace shi din kuma mai ceto ne"
"Ameen"
Ta amsa daker kamar an mata dole.
"Ayi ma Aliyu gaisuwa"
"In shaa Allahu zai ji Mama Barakat an gode"
Farida ce kawai take amsa mata Kameela kam ko gafen da da take bata kalla ba kai kace ba ita ta shigo ta yi ma sannu ba, Mama Barakat na fita Kameela ta ja tsaki.
"Ni ban san abun da Abbah ya gani a jikin matar ba ya aurota, gashi nan ta zo ta tsika mana zuri'a da yarbawa, sai bakin munafurci da iyayi, Wallahi na tsaneta kamar mutuwa"
"Saboda me?“
Farida ta tambaya. Kameela ta watsa mata harara.
“Ke har sai an fada miki? Wake son kishiya sai kin yi aure zaki gane kan gari, duk wani abu mai alaka da kishi ko kishiya ni bana ciki, gashi nan ta zo ta tsirka mana da nata jinin a gida"
Anty Shafa da ta sallame sallah ta jefa nata baki.
"Ai ba laifinta ba ne Wallahi laifin Abbah ne duk matan duniyar nan ya rasa wa zai aura sai bayarabiya"
"Wallahi na rantse da nice Hajiyarmu ba zan yarda mijina ya kara aure ba, bayan duk wahalar da aka Sha an samu kudi yanzu sai kawai ya karo aure, tab ai sai dai a mutu"
Kameela ta fada. Farida ta kallesu da mamaki.
"Yanzu fa ana maganar shekara goma sha biyar da auren nan, toh miye amfanin yin maganar yanzu, tun da har yara ta haifa da ai sai hakuri"
"Ke dalla gafara can baki san ma duniya ba"
Anty shafa ta karasa tare da jan taja tsaki ta fice daga dakin.
EMILY POV.
Bata farka ba sai karfe biyu da rabi na rana wani wanka ta sake yi ta yi kwalliya cikin wata shigar ta kananan kaya ta canjan sarkar cross din dake wuyanta zuwa dabam wanda ita ta siya da kanta ba wanda Vito ya siya mata ba, even though da kudinsa ta siya but not t like wanda ya bata da hannunsa, jakarta ta nufa ya dauko agogon mutumen nan ta saka a hannunta sai dai yayi mata yawa yana zubo mata a hannu.
Ta zabi haka ne domin ta shiryawa amsawa Vito ko wace kalar tambaya da zai mata a duk lokacin da yayi arba da sarkar wuyanta ko kuma agogon mutumen da baya fatan ta hadu da shi yanzu ko nan gaba.
Ta saka turare sosai sannan ta fito daga dakinta tana sanye da fararen flat shoes. Babu karya duk wanda ya kalleta zai san ta yi kyau domin red dress din yayi mata kyau ya karbi farin fatarta, ga gashinta data sako a gaba ta kulle sauran a bayan kanta. Chidimma ma da take mace kallonta take ta ko'ina Emily ta hadu kuma ta kai mace, wata kila shiyasa Vito yake sonta baya sauraren ko wace mata sai ita, sam baya kallon yaranta data haifa ma da kuma yadda yarta take yarfashi a gaban kowa, haka ma yake ta wahala da danta marar lafiya amman ita ma bata gani, idan ba shi ba wake wannan wahalar yanzu...
"Are you okay"
Emily ta tambaye ganin yadda take kallonta har ta sauko bata san ta iso kusa da ita. Da sauri Chidimma ta sauke kai kasa jikinta ya dan yi rawa.
“Ina tunani ne"
"Kina cikin wata matsala ne?"
"Aa babu komai Ma'am karki damu"
Emily ta daga kafadunta ta duba agogon da yayi mata yawo.
"Yanzu na san Fatima tana kusan da dawowa, idan zata je makaranta islamiya fine idan kuma ba zata je ba, kar a barta taje ko'ina, zan fita maybe sai dare zan dawo, ki shafa min kan London kuma ki fada masa ina kaunarsa"
"Tohm ranki ya dade"
Ta amsa Emily ta kalli dinning ta dauke idonta ta nufi kofar fita falon ta fice. Gudun abun da zai je ya dawo ya hanata fita da motarta sai ta zabi tafiya a kafa, haka ta bi shagunan da ta gani dazun da safe ta gabatar musu da kanta ta kuma tallata kanta a matsayin ma'aikaciya idan suna bukata, sai dai ta manta bata dauko cv dinta ba sai a waya take nuna musu ko ta karbi number mai gurin ta tura masa.
Kusan kowane shago kallonta ake domin bata yi kama da wanda zata iya aikin siyar abu a duka shaguna nan ba, dan haka wasu a take suke fada mata basa bukata, wasu kuma su yi tunani ko dai an turo ta ne, ko kuma an shirya yi musu wani zagon kasa ne, kadan ne suke bata tabbaci za su tuntube ta idan bukatar hakan ta taso.
Ita kam a bakin gaskiyarta take neman gurin da zata iya tallafawa kanta, domin samun aiki na gobnati ko kamfani ba karamin abu ba ne ta san irin gwagwarmayar da ta yi kamin ta samu aikin da Amal ta yi mata sanadin barinsa yanzu kuma Aliyu yake son ta dawo saboda ya mulketa.
Wani babban shago siyar da talkamin maza dake cikin quarters din dake kusa da unguwarsu ta shiga, sai suka yi mata maraba bayan security ya bude mata kofar shop din, kai tsaye ta tambaye manajan gurin sai da ta basu tabbacin babu wata matsala kawai tana son ganinsa ne sannan aka nuna mata shi. Ta doshi gurin da yake zaune tare da wani.
"Ssnnu kai ne manaja a nan?"
Ta tambaya mutumen ya kalleta Aliyu ma dake zaune ana sanya masa talkami a kafa ya juyo ya kalleta daga sama har kasa.
"Eh sannu da zuwa fatan dai babu wata matsala ko?"
Arba da ta yi da Aliyu ya saka duk wani hanzari da confidence nata yankewa, wani abu mai kamar fargaba kamar tsoro ya lullubeta, har take ji da ace ta san shi ne yake zaune a gurin ba zata karaso ba, gashi ta kasa sake hada ido ta shi kuma ta kasa cewa komai, ta jimke agogon hannunta dake kokarin zubewa dayan hannunta kuma ta rike jakarta.
"Lafiya dai?"
Mutumen ya tambaya, Aliyu ya sake juyowa a kallo na biyu sai dai wannan karon ya sauke idonsa ne akan agogon dake hannunta, fuska ba yabo ba fallasa ya mike tsaye.
"Kala hudu nan sun isa for now"
Ya saka talkamin da ya zo da su, ya ciro katinsa ya aje akan babban table din dake gabansa.
"A kai min a wannan addireshin"
Manajan ya kalleshi da mamaki domin be taba siye abu yace a kai masa gida ba sai dai a saka masa mota ya tafi da shi.
"Okay ranka ya dade"
Ya nufi gurin biyan kudi ya biya da amt dinsa har kudin kaiwar sannan ya nufi kofar fita, sai a lokaci Emily ta jiya juyawa tana kallon bayansa har ya fice. Sai kuma ta ji haushi kanta meyasa be mata magana ba ko ya nuna ya santa, and why ita ta kasa yin magana a gabansa.
"Akwai abun da zan iya taimaka miki da shi"
Ta karkarto hankalinta gurin manajan.
"Eh, ina neman aiki ne a nan idan da hali"
Manajan ya kalleta saka da sama domin bata yi masa kama da mai neman aiki ba. Ta gabatar masa da kanta kamar yadda take a sauran guraren ta karbi number wayarsa ta tura masa cv ta sannan ta fita jikinta na raya mata abu ne mai wahala ta samu aiki a gurin duba da wanda ta tarar da kuma irin kallon da mutumen yake mata kamar be yarda da ita ba.
[4/27, 4:43 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01
🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
Page 1️⃣7️⃣
Yadda ta tafi a kafa haka ta dawo a haka feeling so lonely and hopeless. Ta kwankwasa gate din aka bude mata ta shiga, ganin bakuwar mota ya saka ta juyo ta kalli mai gadinta kamar zata tambaya waye sai kuma ta fasa, ta nufi main door din da sauri zuciyarta na raya mata wata kila Aliyu ne ya rigata iso gidan, sai dai hango direban Vito da ta yi a gaban motar ya sauya tunani, ta tura kofar falon ta shiga, sai ta samu babu kowa a falon sai wata bakuwar fuska da ta yi arba da ita a zahiri, a badini kuma mace ce da ta sha ganin hotonta a wayar Vito da kuma gidansa.
"Da alama ke ce Emily"
Matar dake tsaye a dinning din falon ta fada tana kallon Emily da murmushi a fuskarta.
"Barka da sauka Mrs Gloria"
Cewar Emily tana kallomta fuska babu yabo ba fallasa.
"Vito ya fada miki wacece ni a gurinsa kenan"
"Na sha ganin hotunanki a wayarsa da gidansa"
"Kamar yadda ya cika ni da labarinki"
Tana maganar tana nufo gurin da Emily take tsaye, ta kama hannunta suka zauna.
"Fatan na same ki lafiya, ya yaranki"
"Duk muna lafiya"
Ta kai hannu ta rike fuskar Emily.
"Ke kyakkyawa ce, kina da aji amman ba irin kyaun da za'a ce babu wata macen bayan ke ba, ďana yana kaunarki sosai kin jama lu'u-lu'u a zuciyarsa, a duniyarsa kuma kin zama numfashinsa wanda yake jin kamar idan ya rasa ki ya rasa rayuwarsa gaba daya"
Ta shafa fuskar Emily.
"Kin canja rayuwar ďana, a da babu ruwansa da mace ko wace kala ce, be taba min zancen budurwa ba, ban taba ganinsa da wata ba, idan ma na yi masa ransa baci yake, be taba soyayya sai akanki, ada baya tsoron aikata kowane kalar aiki ko jefe kansa a hatsari, amman sanadin ki a yanzu yana tsoron shiga matsala, ya kan ce min idan wani abu ya faru da shi ya zaki yi? Wa zai kula da ke da yayanki?"
Emily ta sauke kanta kasa tana hade yawu.
"Amman kin san danki yana siyar da kwayoyi? Drugs"
Mrs Gloria ta yi murmushi.
"Na sani, wannan sana'ace da ya gada tun daga gurin mahaifinsa, kamin a kashe shi, kar hakan ya dame ki, amman ki yi taka tsantsan da zuciyarsa, ba saboda ke ba saboda wadanda suke tare da ke"
Ta mike tsaye.
"Be san na zo nan ba, karki sanar masa. Na barki lafiya"
Emily ta bita da kallo har ta fice, ta sauke ajiyar zuciya ta jingina da kujerar, ta daga hannunta tana kallon agogon dake hannunta ta lumshe ido ta bude ta maida dubanta gurin Jakarta da wayarta dake ciki ke sanar da ita isowar sako. Ta ciro wayar ta duba sakon da shigo daga number Aliyu even though bata yi saving number ba, amman ta gane number shi ce domin sakon yana a saman wacan sakon da ya turo mata a ranar da suka hadu asibiti.
"Mahaifina dan siyasa ne, sau hudu yana tsaya takarar dan sanata amman be taba yin nasarar ba sai bana"
Ta karanta sakon ta sake karanta sai ta aika masa da quation marks, like why are you telling me this?
Ta tashi ta nufi dakin da danta yake tana ta mamakin dalikinsa na bata tarihim mahaifinsa ba ma nata ba, tana tura kofar dakin sai ta same shi tare da Fatima da Chidimma suna ta wasan doki cikin far'a da sakewa, sai da ta fara kawata fuskarta da murmushi sannan ta karasa cikin dakin ta shafa kan London a take ya hade rai ya matsa gefe, bata damu ba ta shafa na Fatima sannan ta karasa kusa da shi ta zauna a kasa.
"My handsome Man"
Kamar jira yake ta rufe baki sai ya saka mata ihu da sauri ta tashi daga gurin ta matsa.
"Baya bukatar ganinki ne a yanzu, da dai zaki yi hakuri ki fita saboda muna wasa a yanzu kar a bata masa rai, mu wuni a damuwa"
Ta daga ma Chidimma kai cikin rashin jindadi ta fice daga dakin, ta shiga nata dakin ta aje jakarta da duk wani abu da yake hannunta ban da wayarta da yake karanta sakon Aliyu da ya shigo mata yanzu.
"Wata rana a Kaduna ranar 20 ga watan march 2020 aka ina tare da friends dina a inda muka saba haduwa mu yi shawara ko wani abu mai amfani, a ranar muna kallon tv ne a lokacin ake sanar da sakamakon zabe wanda mahaifina ya tsaya a karo na hudun kuma karo na karshe a rashin nasararsa, aka sanar cewar ya fadi kamar kowace shekara abokin hamayyarsa yayi nasara a karo na hudu, daman shi ya saba yi nasara a duk zabe"
"Miye alakata da zaben mahaifinka?"
Ta aika masa da tambayar domin har yanzu bata fahimci inda ya dosa ba, ya aiko mata da murmushi sai kuma wani sakon.
"Na ji babu dadi sosai, abokaina suka karfafa min guiwa, muna haka sai ga mahaifiyata ta kira ni cewar mahaifina yana ciki wani hali na damuwa saboda faduwa zaben da yayi, na yi hanzarin barin abokaina na shiga motata domin tafiya karfafawa mahaifina guiwa kasancewata namiji daya tilo
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 63