ciwon ba kadan nake jinsa ba, sai da na bari sawu ya dauke na tabbatar da dare yayi sosai sannan na tashi na koma inda na fito yadda na ayyana haka na samu. Mai shayin nan ya tashi ya kwashe kayansa a gurin na kwana, washe gari tun da asuba na yi sauri na tashi na koma gurin hanyar na zauna, da haske ya fito sai na shiga wani gida dake kusa na roki ruwa dattijiwar ta ba ni na yi alwala na fito nan na yi sallah.
Rayuwa ta zama min haka, da dare sai na kwana a shagon mai shayi da rana kuma na shiga gari Bara da neman taimako. Ta inda Allah ya taimake ni babu wanda ya taba cewa me nake a gurin ko ya kure ni, ko da yake bana dawowa gurin sai dare yayi, idan kuma sawu ya dauke sai na kwana a shagon mai shayin da be san ina yi ba. Ranar da na kwana uku a gurin ciwon ya matsa min sosai har na tafi yawon bara na dawo na shiga gidan matar dake bani sadakar ruwa ina ta gumi na roki ta ara min wayarta na kira wata number. Har tace min bata da waya na juya sai kuma ta kira ni ta ba ni amman tace na zauna a kusa da ita na yi wayar bata yarda na fita ba kuma ta saka wayar a speaker saboda bata yarda da ni ba.
Na warware zanena na dauko number Maman Luratu na saka a number na kirata, babu jimawa tana ringing ta daga wayar da sallama
โMaman Luratu nice Aisha ce"
"Aisha Allahu akbar sannu Aisha ya kike ina kike yanzu"
"Ina wani guri, maman luratu dan Allah ko kin san abun da zan yi na daina jin ciwon cikin da baya? Wallahi ciwon nan ya tsananta min yanzu sosai yau ma kamar bana iya tafiya"
Ina fada ina kuka.
"Toh ko haihuwarce? Amman cikin ai be isa haihuwa ba ko?"
"Eh wata bakwai ne, amman ina jin wahala sosai"
"Ko nakuda kike yi? Oh Allah gashi bana kusa, amman dai ki daina yawo nesa"
"Idan haihuwar ce me zan yi?"
"Kina tare da wa ne?"
"Babu kowa ni kadai ce"
"Ki nemi reza ki aje kusa saboda yanke ciki, kuma idan da hali ki tafi asibiti Aisha kin san baki da lafiya tun a nan ma"
"Tohm"
Na amsa sannan na kashe wayar na mikawa matar ina godiya, sai matar ta tambaye daga ina nake.
"Labarin mai tsayi ne ko na fada miki ba zaki yarda ba, na gode"
Na fice daga gidan ina ta sharar kwallah. A rabar ne zuciyata ta debeni na yanke shawarar ziyartar coci ba dan komai ba sai dan na samu kudin da zan tafi asibiti kuma na samu kulawa. Dan canjin da ya rage min na hau abun hawa bayan na tambaye shi wace coci ce a kusa na fada min, da muka isa na bashi kudinsa na doshi gurin gabana na faduwa a zuciyata ina jin kamar hakan ba daidai ba ne amman ya zan yi? Dole ce ta saka. Na isa gurin na yi magana da mai gadin coci na fada masa damuwata da abun da ke tafe da ni, sai yace na jira a gurin ya shigo ciki ya fito da wata Sister tace ba shigo ciki na shiga nayi mata bayanin damuwata sai ta kira wani pastor shi ma ya kira wani muka shiga wani office na sake karanta musu damuwata, da na yi hakan ne saboda kawai su taimaka min.
Sai dayan yace za su taimaka min da gurin zama da abinci amman sai idan zan yarda na koma gidan jiya, ma'ana na zama christen kamar baya, har ita macen take ce min ko da ace ban taba yin addinin a baya ba zan shiga a yanzu su kuma za su bani duk abun da nake bukata kuma za su shirya ni da mai rikona ma dake Lagos."
***. ****. *****.
Ta daga kanta sama, Aliyu ya tashi daga inda yake zaune ya zaro tissue ya mika mata, ta karba ta share hawayen da suka ki tsaya mata. Ta kalleshi da fuskarta da ta yi ja tsabar kukan da take.
"Ni na sani a yanzu ba akan shiriya nake ba, na sani ba akan daidai nake ba, na san addinin musulunci shi ne addinin gaskiya, a wacan lokacin ban yarda da tayinsu ba duk kuwa da kasancewar ina cikin tsananin bukatar taimako a lokacin, amman akwai wani abu da Allah yake sakawa a zuciyar wanda ya so da shirya, na musulumta saboda Khaleefa da aurensa ban san cewar ina son addinin ba sai a lokacin, sai kawai na ji raina ya bace akan me za su ce na koma addinin da bana samun natsuwar zuciya da kwanciyar hankali irin na ruhu sai da na bar shi, ni dai a lokacin na san ina son musulunci dan haka sai na ki yarda, na fada musu ni taimako kawai nake nema ba wai ina nufin barin addinin ba ne, su kuma suka ce ba za su taimaka min ba haka na taso na fito"
Ina jin kamar shi kadai ne wani hukunci da na taba yankewa kuma ban yi nadama ba, da kafa na dawo saboda ba ni da kudin da zan hau abun hawa na dawo, sai kuma na sha wahala a hanya saboda ni ba har gari bace hanya da mai achaba ya bi da ni na bi ina tafiya, idan na rikice sai na tambaya mutane da sannu har na kawo kaina unguwar da nake zaune. Na iso ban isha'i sai na samu guri na zauna ina ta jin ciwon cikin da ban gane nakuda ce ba, daker na iya roko ruwa na yi rama sallolin da ban samu yi ba, na kwanta a gurin azabar ciwo cikin bata karu ba sai da dare ya raba.
Na koma gurin da nake kwana na kwanta da ji abun ba zai daina ba na taso na fito na dawo gidan matar nan na kwankwasa mata gida sai jikanta ya bude yana haska ni da fitila.
"Dan Allah matar gidan nan nake nema"
"Lafiya wacece"
"Ni ce"
Na leka sai ta ga fuskata.
"Dan Allah ki taimaka min da ruwa na sha, kuma idan kina sa wani magani dan Allah ki taimaka min na sha, kar na mutu ciwon ciki nake da na mara"
"Ba ni da magani amman dai zan baki ruwa ki sha"
Ta shiga ta dauko min ruwa na karba da hannu biyu na sha na juya na koma shagon na zauna ina ta kuka domin ciwon ya matsa min ga kuma abu ina ji a kasana kamar zai fito, ban san lokacin da na fara ihu ina rike teburin mai shayin dake gurin ba, sai matse kafa nake ina juyawa, tsabar bala'i da azabar da ciwo har wani juri nake ji ina jin kamar ba a duniya nake ba, ashe haihuwa tana da zafi ban sani ba sai a ranar, gashi babu kowa a kusa da ni, duk zafin nan na haihuwa a haka iyayena suka wofintar da ni? Ina cikin tsananin nakudar dana na farko dan wata bakwai matar da ta taimaka min da ruwa ta iso gurin ta dafa ni, ta haska ni da fitila ina jin jikanta na fadar Gwaggo kika sani ko jikin shege ne. Sai tace.
"Ko cikin shege ne ai ba za a kyaleta ba Kabiru rayuwa ce"
Ta bude kadata ta haska sai ta saka salati.
"Haihuwa ce zaki yi kuma kafa nake gani ba kai ba subhanallahi"
Ta rika ni, da taimakon danta suka kai ni gidanta, ita tayi ta fada min yadda zan yi tana taimaka min tana danna min ciki har na haihu, amman na ji azabar da ban taba ji ba, har na ji kamar babu kasana gaba daya a lokacin. Da zanenta ta lullube dana ta yanke min cibi na sake wata nakudar sannan wani abu ya fado wai shi uwa, ta saka a leda ta kulle. Ta dauko wani zane ta lullube ni ta dora min dana a kusa da ni, ni dai ina kwance a gurin bana bachi bana farin ciki haka kuma bana kishiyarsa, hawayena kawai masu zafi suke sulalowa a idona, har ta yi zaton ko na mutu ta girgiza ni sai na kalleta.
"Sannu"
Na daga mata kai, da safe sai jikina yayi tsami sosai, ta taimaka min da tsumma na tare jini ta gyara dakinta tace na wanke kayan jinina haka na daure da ciwon jiki na da kasa na wanke kayana da kaina na zauna ina jin kamar fata ce kawai ta rage min a jiki, ta kawo min dumame na ci na sha ruwa sannan ta tambayi labari. Na fada mata komai sai ta tausaya min amman ta fada min ba zata iya ba ni gurin zama ba saboda zargi. Kuma ban ga laifinta ba tana da gaskiya ba kowa zai iya rike ni ba, dawainiyar ma ai sai ta yi masa yawa.
Ta fada min idan mace ta haihu a musulunci akan yanka mata rago idan yayi kwana bakwai, kuma uba yana yi ma dansa huduba a kunne, amman ni daya be samu ko daya ba, hakan ya saka ni kuka sosai. A lokacin na saka masa suna Ibraheem ba dan na san ma'anar sunan ba, kawai dai na saka masa haka ne.
Da dare yayi matar bata bari na kwana a nan ba saboda kukan da London yake ba ji rarrashi ga shi kuma nono na babu komai a ciki, na kwana a ashagon mai shayi kamin lokacin tashina yayi sai ga mutane na gani har hudu ciki har da mai shagon da abun dukansu, suka ce an fada musu a nan nake kwana kar na sake kwana a gurin su yanka ni, dayan ya so ya mare ni wai dan na raina musu wayo wato har haihuwa na yi a gurin. A daren suka kore ni na goya daya da zanen matar na kama hanya ina ta tafiya har gari ya fara haske gashi ko'ina na bi sai an kalleni saboda kukan da London yake domin ba lafiyayyen ฤana na haifa ba, gashi dan tsito ba shi da girma, ni kaina tafiyar ma daker nake yi ina ta raba kafa saboda zabar da nake ji a kasana.
A haka na rika raba manyan gidaje ina yin Bara wani gidan masu gadi basa bari na karasa ba suke korata wasu kuma basa ma bude gate din. Har na fada gidan wata mata mai farar zuciya mai tausayi mai jinkai, da alama da saba taimakon domin na tarar da gate din gidan a bude kuma da na fadawa mai gadin taimako nake nema sai yace min na wuce ciki.
Na shiga sai na zauna daga bakin kofar falon ina jiran fitowarta, na dade a gurin sannan aka bude kofar falon, wata matashiyar yarinya ce ta bude kofar ganina kamar tana mamaki ta tambaye ni lafiya. Nace mata taimako nake nema sai ta tambaye ni wane iri na furta abinci domin shi na fi bukata a lokaci, yarinyar ta juya ta shiga ciki bata jima ba ta fito da plate din shimkafa irin wanda aka ci aka rage tace ba a gama shirya mana abun karyawa ba amman ga ragowar shimkafar jiya idan zaki iya ce. Na karba jiki na rawa na fara ci hannu baka hannu kwarya kamin na kwance dana dake ta ihu ga wani zafi da jikinsa yayi na rumgume shi na gyara zama na fara saka masa shimkafar a baki tana kaiwa makoshinsa sai ya dauke numfashi...
***. ***. ***. ***.
Ta aje zaren zancen tana neman nata numfashin dake kokarin daukewa saboda kuka na tuna rayuwar da ta dade da rufe shafinta. Aliyu ya matsa baya yana kallonta cikin tashin hankali, a lokacin ne ta fara zaga office din tana neman numfashinta kamar zata mutu, da sauri ya fita Office din ya fadawa Nick ya nema masa wata mace da take kusa ya dawo ya nufi fridge dinsa ta dauko ruwa ya nufeta hankali a tashe, wata mace ce ta shigo dakin tana sanye da suit.
"Rikata dan Allah zaunar da ita ki rumgume ta"
Ya nuna mata Emily a take ta nufi Emily ta aikata abun da ya fada sai ya miko mata ruwa yace ta bata. Matar ta karba ta kai mata ruwan a baki Emily na shan ruwan ta fara amai babu kakkautawa bata tsaya ba sai da ta amayar da komai na cikinta, matar na rike da ita har ta fara dawowa hayyacinta sai dai kuma jiki babu kwari.
"Shiga da ita ciki ki wanke mata baki"
"Okay Sir"
Matar ta rika Emily suka shiga bathroom dinsa dake office din ta taimaka mata ta wanke baki da fuskarta sannan suka fito, Aliyu ya mikawa Emily Tissue da hannunsa.
"I'm sorry"
Ta karba kawai tana kallonsa da idonta da suka kumbura fuskarta da hancinta suka yi ja.
"Anna ki rikota ku fito ku same ni gurin mota"
Ya fice yana fadawa Nick ya sa a gyara masa office dinsa. Anna din ta taimaka mata suka sauka kasa suka isa har gurin motar da Aliyu take ya bude backseat Anna ta shigar da Emily ta rufe sannan ya shiga gaba yaja motar suka fice. Madubin gaban motar ya saita saitin da Emily take jingine da motar tana hawaye kana ganinta kasan tana cikin bakin ciki da rashin kuzari.
"Kina da likitan da yake dubaku?"
Bata amsa masa ba tana ta kallon gefen titi ta yi samo kamar ba ita ba. Shi kuma be fasa kallonta ba har ya isa bakin gate din gidan yayi horn mai gadin ya leko ya kalleshi... Sai ya sauke gilashin ta gefen da Emily take.
"Ba sai ka shiga ciki ba"
Ta bude motar ta fito da kafafuwanta ta yi tsaye kamar zata fadi, Aliyu ma ya bude ya fito ya zagayo inda take. Tasmia dake zaune a can gefe cikin mota ta bude motar ta fito da mamakinta tana kallonsu, tun kamin ta kawo Emily ta mika mata hannu domin jin take kamar zata fadi, Tasmia ta karaso da sauri ta rikata, ta kalli Aliyu.
"Me ya same ta? Wani abun ka yi mata"
"Eh fyade na yi mata"
Ta amsa mata da gatse, sannan ya rufe gefen da Emily take tsaye ya zagaya ya shiga motarsa yayi reverse. Tasmia ta bishi da kallo mamaki domin ta gane waye shi. Emily ta dafata suka shiga cikin gidan ta zaunar da ita falonta.
"Emily kin san wannan mutumen da ya kawo ki ne?"
Emily ta kalleta hawaye na sauko mata.
"Dan Allah karki tambaye ni komai a yanzu, ki tafi gida ki bari sai gobe zamu yi magana"
"Shikenan amman ki yi ma maigadinki magana domin yanzu da na zo hana ni shiga yayi wai babu kowa a gidan alhalin na san a nan na taba sauke ki"
Emily ta daga mata kai domin shi ne kawai abun da take iya yi. Tasmia ta tashi ta fice har lokacin mamakin mijin kawarta take tana jinjina halin maza duk kuwa da kasancewar bata san me yake faruwa ba. Bayan Tasmia ta fice Emily ta rumgume kanta ta fashe da wani irin kuka mai karfi sosai daker ta iya rarrashi kanta ta mike tsaye ta haura staircase din ta doshi dakin da London yake a hankali ta tura ta shiga ciki, bashi a dakin ta nufi bandaki slowly ta bude nan ma be ciki, ta fito ta janyo kofar dakin ta shiga dakinta ta zauna kan tool tana kallon kanta. Ji tana bukatar ganin danta ya saka ta nufi gurin da dayar wayarta take ta dauka ta kira Chidimma a zatonta London yana tare da ita ne.
"Kina ina"
Ta tambaya bayan Chidimma ta dauka.
"Ina gurin kawata"
"Ina London?"
"Ba da shi na fita ba, na bar shi a gurin Sir Vito kamin na fita"
Emily ta kashe wayar ta kira wayar Vito ringing daya ya daga.
"Ina London?"
"Na bar shi a dakinsa yana bachi, Ina kika je?"
Bata amsa tambayarsa ba ta kashe wayar ta fito ta sake komawa dakin London din ta duba ko'ina har kasan gado bata ganshi ba, ta fito falo tana dubawa nan ma baya nan, ta fara duba lungu da sako na falon wai ko ya boya domin dabi'arsa boya a wani gurin musamman idan yana fushi, a nan ma bata ganshi ba.
[5/8, 8:18โฏPM] ๐๐ต๐ฎ๐ฑ๐ฒ๐ฒ๐ท๐ฎ ๐๐ฎ๐ป๐ฑ๐: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL
*๐ ABOKIN RAYUWA ๐*
*ยฉ Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... โ๏ธ
FOLLOW ME ON ๐๐ป
FACEBOOK
https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914
TIKTOK
https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1
INSTAGRAM
https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0
CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01
KHADEEJA CANDY STORE
https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08
Page 2๏ธโฃ3๏ธโฃ
Ta dauki wayarta da sauri ta kira Vito.
"Ban ga London ba ko'ina na duba baya nan, kuma na yi waya da Chidimma tace ta bar shi gurinka ta fita"
"Ina Lisa?"
Fatima yake nufi domin haka yake kiranta wani sa'in saboda ya tsani sunan hausawa da aka saka mata.
"Tana.... Fatima tana...."
Ta juya ta kalli agogon falonta lokacin dawowarta daga makaranta har ya gota.
"Ina kika je? Jiya ma kin fita ina kika je?"
Ta kashe wayar ba tare da ta ba shi amsa ba. Vito ya kalli wayar har ya aje sai kuma ya dauka ya kira Chidimma.
"Hello ranka ya dade"
Ta amsa da nishadi da girmamawa.
"London yana gurinki?"
"Aa ai tare na barku da shi da zan fita"
"Baki koma gidan ba? An duba ba a ganshi ba"
"Wata kila ko yaji muryar mahaifiyarsa ne ya boya, dan yanzu rashin kulawar da take ba shi ya saka baya son zama kusa da ita, madam bata kula da shi yadda ya kamata"
"Chidimma ki yi hankali da bakinki, ki daina fada min laifin Emily, idan ma wani abu take marar kyau ki bari na gani da kaina, karki sake fada min tana gida ko bata nan sai idan na tambaye ki, madadin na ga laifinta ke zan tsane ki ne"
Yana kaiwa nan ya kashe wayar ya dauki rigarsa dake aje kan gadon ya saka ya fito dakinsa sai ya samu mahaifiyarsa a falo tana hira da mai dafa masa abinci.
"Fita zaka yi"
"Eh"
Ya amsa a takaice sannan ya dauki daya daga cikin keys din da suke lake a kofar fita falon ya fice. Ta dayam bangaren kuma Emily na aje wayar ta nufi harabar gidan tana tambayar mai gadi ko Fatima ta dawo? Sai ya fada mata bata dawo ba amman direban dake daukota daga school ya fita da mota tun dazun.
"Amman ka ga London ya fita?"
"Aa be fita ba indai ba Oga ne ya fita da shi ba a mota a kafa kam be fita ba wani kuma be fita da shi ba"
"Ya bata ban ganshi ba"
"Kin duba ko'ina?"
"Eh"
Ta amsa masa sai ta nufi kofar gate din ta bude ta sauri ta fita tana ta kalle kalle bata yarda yana cikin gidan ba domin ta duba ko'ina bata ganshi ba, haka ta fi hanya ko talkami babu a kafarta tana tafiya tana kalle kalle idan ta ga mutane sai ta tambaya ko sun ga wani yaro, kowa yace mata a'a.
"Yaro ne sosai fari yana ihu idan ya ga mutane wani lokacin yana da jin tsoro kuma yana yin abu kamar marar hankali amman ba mahaukaci ba ne Autism ne, yana da matsalar data shafi kwakwalwa"
"Ba mu ganshi ba"
Gungun mashayan sun fada suna kallon cinyoyinta dake waje. Ta dora hannu akai har zata fasa kuka sai kuma ta karfafawa kanta guiwa ta kara gaba tana nemansa. Sai da ta kusa kai karshen unguwar tana duba kwararo ko lungu bata ganshi ba kuma kowa ta tambaya sai yace be ganshi ba. Can wata zuciyar ta raya mata ko ya bi direban da zai dauko Fatima makaranta gashi bata fito da waya ba balle ta kira, ta juya ta koma da sauri duk nisan hanyar bata gani ba cikin mintuna ta dawo gidan ta buga gate din da karfi mai gadin ya bude yana kallonta sai dai be ce komai ba ita ma bata bi ta kansa ba ta nufi cikin gidan da gudu sai ta samu kofar falon a bude Fatima na zaune rike da jakarta ta makaranta tana kallon mahaifiyarta a tsorace.
Da sauri ta nufeta ta dafa ta.
"Fatima kin dawo? Da direba zai je daukarki a school tare da London aka je? Ya bata ban ganshi ba"
"Be bata ba, ruwa ya fada Vito ya zo nan ya tsamo London a swimming pool ya tafi ya kai shi asibiti"
Emily ta fadi zaune idonta na cika da hawaye wata sabuwar fargaba na tunkarota, tunaninta be bata zai tafi can ba even though ta leka bata ganshi ba amman bata saka ran zai fada ruwa ba. Ta saki Fatima ta nufi staircase ta haura sama zuwa dakinta ta dauko wani makullin motar domin wacan motar data fita da ita da safe tana can gurin aikin su Aliyu ta baro.
Ta sauko da sauri tana jin numfashi na sama kamar zai dauke gudu take amman kamar ana daure mata kafafuwa haka take ji, rashin kuzarin nan da ya same ta a office din Aliyu a dazun bayan ta gama gutsura masa labarinta ya dawo mata a yanzu.
Gurin shiga motar ma sai da ta yi da gaske sannan ta iya bude motar ta shiga, cikin karfin hali ta yi ma Motar key ta yi reverse, a hanya ma tana jan motar motar na janta sai ta taka burki ta tafi sai kuma ta tsaya ko ta yi baya kamar wanda ta sha wani abu haka ta samu kanta duk wanda ya ganta sai yayi zaton ko ta sha wani abu ne, fakawa ta yi gefen hanya ta dora kanta a sitiyarin motar tana ta sauke ajiyar zuciya ta rufe ido tana maida numfashi, ta yi hakan ya fi a kirga sannan ta samu kuzari ya dan zo mata, ta sake tuka motar ta nufi asibitin da aka saba kai shi a duk lokacin da bashi da lafiya.
Ta faka motarta a emergency ta fito ta rufe motar, ta nufi entrance din Emergency din tana kokarin daga kafarta ta taka gurin gabanta ya fada ras ras ras dudududummmm har sau uku, kamar wadda ta tuna wani abu sai ta fasa bata dora kafar, ta ja baya ta tsaya tana kallon Kofar Emergency din dake can ciki wato second door da mutane suke fitowa, ta kasa shiga ta gagara komawa ta tsaya a gurin har na tsawon minti 5. Tana tsaye a gurin sai ga Vito ya fito tare da wani yana hangota sai ya tsaya da sauri kamar mai jin tsoro, sai kuma ya taka ya karasa inda take tsaye.
"Mu tafi gida"
"Dana ya mutu ko? London ya mutu?"
Vito ya dafata kamin ya sake cewa komai ta ce
"Na jiya a jikina, an sanar min saboda ni ma uwace, ban taba samu kaina a irin yanayin da na samu kaina a yau ba, ban taba jin abu makamancin wannan ba, saboda ban taba rasa makusanci na jini ba sai yau, na ji abun da ake ji, na ragu yau na koma daga ni sai Fatima"
Tana maganar wasu masu tsananin zafi suna sauko mata.
"I'm sorry, zan kasance a tare da ke a cikin kowane irin hali Emily"
Ta fasa wani irin ihu kamar mahaukaciya Vito ya rike kamin ta kai kasa, wani irin kuka take daya saka hankalin kowa dawowa gareta, bata san yadda ake ji idan an rasa wani ba sai a ranar domin bata taba rasa kowa ba sai yau.
Shi ya saka ta mota ya tuko zuwa gida wanda suke tare kuma ya taho da gawar London, ta shiga falonta tana kuka Fatima ta tarbeta ita ma tana Kukan domin tun a dazun jikin yayi sanyi saboda yanayin yadda ta ga an ciro dan'uwanta a ruwan kamar tsumma.
"Ya mutu Momi"
Emily ta kasa magana ta rumgumeta tana ta kuka. Vito ya nemi guri ya zauna ya dafe kansa ya runfe ido, domin ba kadan yake son London ba, dama Fatima ce wata kila ba zai ji damuwa da bakinciki kamar haka ba, amman London yana son yaron yaron ma yana sonsa, shi ya canja masa suna Ibraheem zuwa London ya canja masa addinin kuma ya yarda,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 63