na shayar da shi, sai da na shekara ashirin kamin na samu ganin dana a ido shi ma kuma sai da na yi fadi tashi shiga nan fita nan, daker na samu haduwa da nada na samu ana barinsa ya zo gurin ko kuma ni na tafi, bayan Turhan ban sake haihuwa ba saboda maganin da aka bani a gidan mahaifinsa, shi ma haihuwarsa ta zo ne kawai saboda Allah ya kaddara akwai da a tsakani, shiyasa a yanzu na maida shi abokin ban kalle ta sigar dan fari ba, komai a gidansu ake masa abinci da nake ci ma daker ya iya koyar cinsa, idan ya zo nan tufafi kalar da nake so yake sakawa, zamu yi wasa da dariya mu yi hira mu yu yawo kamar ni da kane na ba dana ba, matar da ya aura ma daga masarauta aka zaba masa, kuma har yau be taba kawo min ita na ganta ba, sai a waya, shiyasa ni ma na yi masa nawa tanadin na musamman kuma na san zai so ki zaki dace sosai"
Na kalleta da kamar mamaki jin ta ambace zan dace, sai na nuna kaina.
"Ni"
"Eh, ɗana nake yi ma tanadinki, na miki alkawari zai soki zai rike ki amana kuma zai so danki, a yanzu ne zaki san miye aure zaki dace, kuma na san zaki so shi domin shi ma kyakkyawa ne, kusan duk yan mata da nake hada shi da su cemin yake baya sonsu amman ke kam ba zai iya juya miki baya ba, domin kina da kyau kina da haske da gashi kamar matan garinsu, shiyasa nake ta boyonki ina fargabar kar wani yace yana sonki ki karba, kin ga idan ya aure shi zai aje ki a nan dole zai rika zuwa akai akai, kuma ni na zan samu nawa jikokin ta bangarena, idan ba haka ba ina tunani gaban kadan dauke shi zasu yi ba za su bari na zauna da shi ba"
Na sauke ajiyar zuciya ina tambayar kaina to idan kuma ya zo ya ga ban masa ba fa. Kamar tasan abun da nake sakawa sai tace.
"Karki damu da wai ba zai so ki ba, sai so ki ina mai tabbatar miki zai kaunace ki Aisha kamar zai yi hauka, ke kanki zaki yi mamaki yadda zai kula da ke, saboda ni na zaba masa ke da kaina kuma kin sha wahalar rayuwa Allah zai saka miki ta hanyarsa In Shaa Allahu, abun da na cutar da ni a zaman da muka yi da mahaifinsa shi ne shi baya so na, da ace yana so na da ba zan wahala a yadda na wahala ba, amman ke na san Turhan ba zai bari ko yatsa a nuna miki ba, dana yana da kirki sosai yana da tarbiyar kuma yana da addini daidai gwargwado na miki alkawarin Turhan ba zai taba cutar dake ba ba zai taba cin amanarki ba"
Ta yi min campaign ta gyara danta sosai da halin da ta san ba nasa ba ne, ta fada min abun da ba haka yake ba, ta lullube danta da kyawawan halayya alhalin akasin hakan ne a tare da shi. Ni dai ban iya cewa mata komai ba, domin kyautatawa tana biyo kyautatawa ne, ta ina zan iya cewa danta bana kaunarsa macen da bata san ni ba ta rike ni ta kyautata min ni da ɗana, gashi ta yi kuskure bata tambayi ra'ayi akan kudirinta ba, idonta ya rufe akan muradinta da kuma burin da take da shi. Dafa ni ta yi
"Aisha karki damu, na lura da kyakyawan halayen dana, kuma ba zan ce ni din mace ce mai nagarta 100 bisa dari ba amman dai na san na kam kamanta na kan kyautata iya yadda zan iya, ba zan yarda a cutar da wani ina gani ba sai inda karfina ya kare, Wallahi ba zan bari Turhan ya cutar da ke ba na miki alkawari, ke din abar tausayi ce Aisha baki da kowa kuma gani ba ki jidadin aure ba, duk wanda ya ji labarin ki dole ya tausaya miki, wata kila ta dalilinki zan samu aljannata gashi ina jinki kamar yata, ba zan taba bari Turhan ya cutar da ke ba"
Ba zan iya amsa mata da aa ba amman a lokacin na ji a jikina ban shirya sake wani auren ba, idan kuma nace ba zan auri danta ba a ina zan zauna? Zai kula da ni wa zai rike ni ni da ɗana? Ina cikin wannan tunanin muka ji kyallowar Ibraheem ni da ita muka tashi da sauri muka shiga cikin falon na haura sama na dauko shi ihu kawai yake na yi rarrashi na na ba shi madara be saurara, sai ya yanke shawarar na tafi da shi asibiti haka na saka hijab cikin tashin hankali muka tafi asibitin, su yi iya bincikensu sun ba mu test da hotuna kala kala amman ba a gano asalin damuwarsa ba sai da ya shekara biyu cif, suka ce min ɗana Autism ne, ga shi yana fama da sickle, daga lokacin hallayarsa ta sake yau ciwo gobe lafiya baya yarda da kowa sai ni sai kuma Ammy mai aikin Ammy ma daker yake yarda da ita, ko sallama aka yi da karfi sai ya fasa ihu jiki yayi ta rawa ya cige, tun ina jin tsoro har na saba, ɗana ya sha wahala gashi kuma yanzu be rayu ba, kuma be ji sauki ba har ya bar duniya, kuma be ga ubansa ba"
Ya rufe baki tana kuka.
Aliyu ya mike tsaye ya nufi windows office din ya tsaya tana kallon harabar ma'aikatar, sai a yanzu na fahimci dalilin Ammy na juyawa Turhan baya, ta ki ta fahimce shi ta saurare shi.
Ya sake juyowa ya kalli Emily dake ta kuka, dawowa yayi gurin teburin ya zari tissue ya mika mata ta karba tana shaye hawayenta.
"Ba zan ce na fi sauran ba, amman dai na miki alkawari daga yanzu wani ba zai sake cutar da ke ba, sannan ina son na ja kunnenki akan Tasmia karki sake yarda da ita, abu na karshe da zan fada miki shi na har yanzu Ammy tana sonki, mace ce mai kirki kawai danta ne ya tsaba alkawari, saboda wannan ta juyawa Turhan baya, wannan dalilin ya saka yake nemanki, yanzu haka ya fada min bata da lafiya kuma yana tunanin kamar har da tunaninki ya saka ta ciwo"
Ta kalle shi tana hawaye.
"Asha ma ba nadama yayi ba, ashe ma..."
Ta kasa karasa.
"Dan Allah Aliyu ka yi min alkawari ba zaka taba fada masa inda nake ba"
Ya kalleta sai yayi shiru na dakiku kamin ya amsa mata.
"Na yi, ba zan taba bari Turhan ya san inda kike ba ta dalilina sai idan ke kika yi ra'ayi, you have my words"
Ta daga masa kai alamar gamsuwa.
"Mu je na kai ki gida"
"Zan iya tuki na zo da mota"
"No i want to take you home safely"
"Amman za a iya cewa ranar mun shiga mota daya, kuma yanzu a sake ganin mun shiga"
Ya rumgume hannayensa.
"A duk lokacin da zan aikata wani abu uku nake dubawa kuma nake jin nauyi, Ubangijina, mahaifaina, matata, Ubangijina ya san ba ni da wata mummunar manufa akanki, sai kyakkyawa, Matata ta san da ke, iyayena ne suka rage su kuma na san ba su da matsala, the rest can go to hell, let's go"
Ya fara takawa ya isa kofar ya bude ya juyo ya kalleta sai ya samu shi take kallo.
"Aliyu yana da banbanci da sauran ki saka wannan a zuciyarki, you can trust me"
Ta mike tsaye ta isa kofar ta fito sai ya janyo kofar a daidai lokacin da Amal ta fito office dinta, dan tsaye ta yi da farko irin na mutum da mamakin ganin sabon abu ya rufe shi, Aliyu yayi kamar be ganta ya jera da Emily suka wuce, a tare suka sauka kasa suka isa har gurin motarsa ta bude ta shiga, shi ma ya shiga.
"Amman lokacin tashi aikin be yi ba"
Yana yi ma motar key ya amsa mata ba tare da ya kalleta ba.
"You need to rest, labarin zaki karasa min wani lokacin, don't stress yourself"
Ya tashi motar suka kama hanya, sai ta maida dubanta gurin agogon da ya bata tana ta murza agogo a hankali. Kallo mace ya wuce sau biyu zuwa uku haramun ne a gurinsa amman Emily ya kasa dauke idonsa a kanta, musamman a yau da tausayinta ya zame masa nauyi, tukin kawai yake amman idonsa da hankali yana gurinta har ya isa gidanta, ya faka a wajen gate din gidan yana kallonta.
"Aliyu..."
Ta kirashi da muryarta kasa kasa. Ya amsa mata yana kallonta zuciyarsa cike da tausayinta.
"Ka taba marmarin abun da baka taba samu ba?"
Ta tambaya har lokacin bata kalleshi ba.
"A'a"
Ya amsa mata bayan few seconds.
"Me kike marmari?"
Ta kalleshi tana kuka.
"Iyayena, ni uwa amman ni ma ina neman tawa uwar ina jin kewarta duk da ban taba kasancewa da ita ba, me yasa suka jefar da ni, me na yi musu? Miyasa gashin kaina yake yake da idanuwa na, ni yar asalin wace kabila ce, wa na biyo mahaifina na ko mahaifiya? Minene asalin sunana? Su waye yan'uwana? Duk ba ni da amsar ko daya"
Ya busar da iskar bakinsa.
"Emily kuka kike son na miki ne?"
Ta girgiza kai.
"Toh dan Allah ki yi daina kukan nan haka, kin cika zuciyata fal da tausayinki, a yanzu kuma bana son ganin damuwarki, ban wanzu a wacan duniyar da kika sha wahalar rayuwa ba, amman ina ta dorawa kaina laifi miyasa ban san ki tun a farko ba? Wata kila duk wannan wahalar da baki shata ba, iyayenki kuma wata kila ma sace ki aka yi aka kai a gurin ba tare da sanin iyayenki ba, domin alama suna nuna ke ruwa biyu ce, amman ki daina kukan kin ji?"
Yana mata maganar cikin sanyin murya da rarrashi. Ta share hawaye.
"Good Girl"
Ya bude motar ya fita ya zagaya bangarenta ya bude mata ta fito.
"Na san Fatima bata nan yanzu, amman anjima idan ta dawo school ta huta ni ma na tashi aiki zan zo na dauke ta mu je yawo"
Ta bata fuska kamar zata fashe masa da kuka.
"Aliyu dan Allah...."
Be bari ta karasa ba ya tare numfashi ta.
"No no no noooooo Emily ba abun da kike tunani ba ne, ina son na dandana mata dadin uba ne, tun da kin nuna mata na uwa, kuma kin wahala da yawa ya kamata ki huta, wani ya dauki responsibility, you're not alone we're Family"
Kallonsa kawai take.
"Kin min izini?"
Ta daga mishi kai.
"Thank You, ki yi hakuri da fadan da muka yi dazu ki yafe min"
Ta yi murmushi, shi ma murmushin yayi tana tsaye yana kallonta har ta shige ciki, sannan ya koma motar ya koma gurin aikinsa.
Yana shiga office abu na farko da ya fara yi shi ne kiran Ammy ya gaishe ta kuma yayi mata ya jiki domin tabbatarwa idan da gaske bata da lafiyar ko kuma fadar Turhan ne kawai.
"Alhamdulillah"
"Ammy me ke damunki?"
"Sun ce hawan jini ne da ciwon suga, amman dai Alhamdulillah sauki yana samuwa"
"Kina gida ne ko asibiti"
"Ina asibiti"
"Allah ya kara sauki, In Shaa Allahu zan shigo na dubaki"
"Aa karka damu, ba sai ka wahalar da kanka ba ina tunanin da na kara samu sauki kadan za su sallame ni"
"Allah ya kara sauki, amman dai zan shigo In Shaa Allahu"
Daga haka yayi mata sallama, after like one hour, kira ya shigo wayarsa da bakuwar number sai da ya kai karshen typing din da yake sannan ya amsa wayar.
"Assalamu Alaikum"
"Wa'alaikumussalam, Aliyu kana lafiya?"
"Lafiya kalau Alhamdulillah"
"Baka gane mai magana ba ko? Mama Baraka ce"
Ya dan yi shiru kamin ya amsa.
"Maa Shaa Allahu Mama ya gida fatan kowa lafiya"
"Alhamdulillah, Aliyu idan ka samu lokaci ina son mu yi magana ka kira ni, nasan yanzu kana kan aiki ne ko?"
"Eh gaskiya ina gurin aiki"
"Toh idan ka koma gida ko zuwa dare ne sai mu yi magana"
"Lafiya dai ko?"
"Lafiya amman ba kalau ba, akan matarka ne bata fada mana abun da ya hada ku ba, kai kuma baka biyo sawunta ba, ta zo mana nan duk ta rikice ta zama abar tausayi, sai dai ka samu lokaci za mu yi magana"
"Okay Mama"
Ya sauke wayar ya cigaba da aikinsa. Sai 4pm ya tashi aikin a hanya yayi sallah la'asar ya isa gida ya dafa ma kansa indomie ya ci sannan yayi wanka ya shirya cikin wani voile lace na maza black color mai kyau, ya saka bakar hulla ya sha turare da bakaken talkama kamar wanda za shi zance, ya cika aljihunsw da sabbin kudi sannan ya fito ya shiga motarsa ya dauki hanya sai gidan Emily, da ya isa unguwar be karasa gidan kai tsaye ba gudun kar ya janyo mata matsala, sai ya faka gida uku kamin nata, sannan ya kirata a waya.
"Hello"
"Assalamu Alaikum"
Ta amsa, sai kuma ta yi shiru.
"Gimbiyar tawa ta shirya ne?"
"Oh oh oh Fatima?"
"Yeah"
"Eh ta shirya"
"Toh a fito min da ita, ina waje nesa da ku sai kin saka ido sosai zaki iya ganina gida na uku kamin na ku, bana son na zo kusa ne ban san ko Vito yana ciki ba kar yace zai miki fada ko ya dake ki, kin san ni kuwa a yanzu ba zan saka ido ko yatsa wani ya nuna miki ba"
Ta yi murmushi mai sauki tana jindadi tare da sauke numfashin da ya ji shi har cikin zuciyarsa. Ya zauna a motar na tsawon mintuna goma sannan ya hango ta ta fito sanye da bakar abaya ta rolling dankwalin abayar ta rufe kanta kai kace musulma ce, ta yi kwalliya sosai har da jan baki, tun daga nesa Aliyu yake kallon fuskarta tafiyarta da yadda bakar abayar ta yi mata shegen kyau ko kyaltawa baya yi gaba daya ta dauke hankalinsa ko Fatima da ya zo domin ita be gani ba sai Emily, da ta iso gurin motar sai ya sauke gilashin ya jingina da kujerar motar yana kallonta kamar wanda ya zauce.
"Sannu"
Ta fada ta muryar mai dadi idonta suna jan hankalinsa ga wani tsadadden murmushi a fuskarta. Yayi murmushi ya sauke kansa kasa.
"Emily ashe kina da kyau, na gode da kika karramani, wannan shigar ta dace da kyau, kin yi ma abayar kyau sosai"
Ta yi murmushi ita kanta ta san ta yi kyau.
"Wata kila da zaki rika suturta jikinki haka da manyan kaya masu sauko miki su rufe tsiraicinki da zan yi ta kula ina fahimtar kyaunki ne, kuma zan fi sake jiki na jidadi, kin san ban taba kula da kina da kyau ba sai yanzu?"
"Saboda na saka abaya?"
Ya girgiza yana kallonta da murmushi.
"Aa saboda kin rufe jiki, kin dace da sunan Aisha, daga yau ba zan sake kiranki da Emily ba, sai Aisha"
A bakin gaskiyarsa yake fada mata tufafin yayi mata kyau domin yayi mata kyau babu karya, sai dai yana karfafa mata guiwa ne saboda ya dawo mata da sha'awar saka tufafin da musulunci ya yarda mace ta saka, so yake ta ji wannan alfarma yaja hankali da abun da yake gani da jin shi ya dace da ita. Fatima ta daga masa hannu tana masa waving domin ta lura be ganta ba, bayan kuma Emily ta fada mata ita ya zo dauka za su tafi yawo.
Ku yi hakuri dan ni dan Allah Wallahi uzuri ne yake rike ni.
[6/17, 9:33 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_writing
🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
Page 3️⃣6️⃣
"Hey Fatima ya kike?"
Ya fada yana kallonta sai ta amsa cike da far'a da zumudi.
"Fine"
Aliyu ya kalli Emily.
"Ni fa ba ke na zo dauka ba, Fatima kawai nace zan dauka"
"Ni ma ka ji nace ka tafi da ni ne?"
"Ina karantar abun da yake cikin zuciyarki a fuskarki da idonki shiyasa kika yi anko da ni, ni bakin voile ke bakin abaya"
"Saboda an rubuta a fuskata ina son ka tafi da ni?"
"Bana bukatar a rubuta, saboda ina iya karanta rubutun da alkalin zuciyarki ya ayyana ko babu tawada"
Ta bude baki zata yi magana ya tare numfashinta.
"Ki cigaba da musawa daman ai kin saba"
Sai ta yi murmushi ta sauke kanta kasa, shi ma murmushin yayi ya mika hannu ya bude gaban motar, Fatima bata jira yace ta shiga ba ta shige front seat. Emily ta duba wayarta ganin kiran Vito na shigowa wayarta ya daga mata hankali sai ta yi hanzarin kallon Aliyu.
"Ku yi hanzari ku tafi"
"Ke fa?"
Ta girgiza kai ta rufe motar.
"Ba zan je ba"
Aliyu ya kalli wayar dake hannunta da yadda hankalinta ya tashi a take sai ya kashe motar.
"Dan Allah ka tafi kuma karka dawo da ita sai idan na kiraka"
"Idan baki ra'ayin tafiya yawon da ni ba zan cilasta miki ba, amman ke ki fara tafiya gidan tukuna"
"Aa sai ka wuce hankali zai fi kwanciya idan ka tafi"
"I'm your boss ni zan baki umarni ba ke zaki ba ni ba"
Ta kalli titin ta sake kallonsa cikin tashin hankalin da take boyewa.
"Amman kace baka son bacin raina, dan Allah ka tafi"
Tana fadar hakan ya murzawa motar key cikin wani yanayi na am masa dole ya hau titi, bata bar gurin ba sai da ta daina hango su, sannan ta koma cikin gidan da sauri, ta shiga falon cikin tsoro sannan ta haura sama zuwa dakinta wayarta ta fara kashewa ta boyewa tana dagowa sai ga Vito ya shigo fuska kamar bakin maciji, wani irin cin burki yayi ya tsaya kallonta daga sama zuwa kasa, ganinta da Abaya ya ninka masa bacin rai.
"Miye wannan a jikinki?"
Ta yi shiru bata amsa masa ba. Sai yayi cikinta mayafin abayar ya fara fisgewa ya jefar ya rike wuyanta da karfi.
"Ina Fatima take? Ina kika je? Meyasa kika saka wannan kayan?"
Ta ture shi da karfi ta fara magana cikin tsawa.
"Saboda ina ra'ayin sakawa, na gaji da abun da kake min Vito komai na rayuwar duniya sai ka zaba min zan yi? Tufafi sai wanda kake so? Bana mu'alama da kowa sai wanda ka yarda da shi? Yar aiki mai gadi duk sai wanda ka zaba?"
"No ba zaba miki tufafi ba, ki saka duk wanda kika so, amman ban da wannan! Ke yanzu ba abun kunya ba ne a gurinki ki yi koyi da musulmai? Ina hankalinki ya tafi? Me kike son zama Emily? Zan amince miki ki yi komai zan baki gata amman ban da canja addini Emily ba zan taba yarda da wannan ba"
"Bana son zama da kai, ina son na bar gidan nan na yi rayuwata ni kadai"
"Baki da wannan ikon, wane yake hure miki kunne ko? Ina kika tafi? Ina Fatima?"
"Ba ruwanka da wannan"
Ta sake riko wuyanta.
"Miye bana miki Emily? Wane irin gata ne ban baki ba? Wane irin jira ne ban yi ba akanki? A duk lokacin da na miki maganar aure hankalinki wani gurin yake tafiya, gaba daya ba nine a gabanki, na gaji yanzu, waya zo gurinki ko kuma gurin wa kika tafi?"
Ta ki ta yi magana, a take ya wulgar da ita kasa da dukannin karfinsa, sai kuma ya bita ta kama abayar jikinta daga saman gurin v shafe dake gaban rigar ya yaga daga sama har kasa.
"Ba zaki sake saka wannan tufafin ba, ba zaki sake kula kowa ba, you already know yadda raina yake baci idan kika kula wani miyasa kika yi? Me yasa kika kasa karbata har yanzu?"
Ta dauke ta da mari, ya kai mata duka a fuska kamin ya mike tsaye ya cire belt din jikinsa ya fara dukanta tana ihu, and he keep questioning her. Sai da yayi mata duka sosai irin dukan da be taba yi mata ba sannan ya jefar da belt din ya zauna kan kujera tana kallon yadda take murza jikinta tana kuka, a yanzu kuma sai ya ji ransa ya fi baci akan duka da yayi mata fiye da laifin da ta aikata. Bedsheet din kan gadon ya yaye ya lulluba mata a jikinta da babu komai sai underwears, ya zauna a gurin ya rike kansa.
"I'm sorry"
"Ka kashe ni kawai, na gaji"
"Ba zan kashe ki ba, amman zan kashe mutumen da yake ziga ki, na san ba zai wuce wannan dan iskan yaron na gurin aikinku, ba mamaki shi ya turo NDELA har gida na"
Emily na jin haka ta yi karfin halin tashi zaune.
"ba shi ba ne, karka dauki alhakinsa, mutumen da nake aiki a tare da shi shi ne mutumen da ya taimaki ni lokacin da na kusa rasa rayuwata da cikin Fatima, shi ne mutumen da nake ta ajiyar agogonsa, he has nothing to do with this, karka cutar da shi Vito, idan wani abu ya same shi ba zan taba yafe maka ba, kuma ba zan taba yafewa kaina ba"
Ta karasa daker tana kuka, ya kalleta ya sake kallonta ya sake kallonta a karo na uku, ya rasa me yasa ta kasa kaunarsa ta kasa bashi hadin kan da yake bukata, bayan duk abun da yayi mata, bayan duk tsawon shekarun nan da suka dauka tare bayan dubun kyautatawa. Mikewa yayi tsaye ya fice daga dakin ya dawo falo ya zauna ya saka hannunsa aljihu ya ciro wani karamin kwalba mai kamar akwati ta zuba wata farar hoda a hannunsa ta shaka da karfi ya rufe ido yana juya kai na dan lokaci, sannan ya tashi ya fice daga gidan gaba daya.
ALIYU POV.
Da farko yawo ya so yayi da Fatima sosai kuma yayi mata siyayya amman halin da ya bar Emily ya tsaya masa a zuciya, hakan ya saka shi canja kudirinsa na kai Fatima park da guraren shakatawa ya tafi da ita super market kawai ya siya mata kayan wasa da na ciye ciye, tana zabar abun da take so yana tambayarta sallah nawa ake a wuni, me ake karantawa da wane lokaci ake yi, kuma ita tana yi ta bashi amsa daidai ban da yin sallah, tana yi sallah ne a duk lokacin da take sha'awar yin sallah, sai da suka shiga mota ya kama hannunta yana murmushi yace.
"Yanzu ki min alkawari kullum zaki yi kowace sallah babu fashi, kuma komai kike zaki aje ki yi sallah"
"Wata rana ina gajiya fa"
"Eh ko kin gaji ki yi a haka, ai ba zaki so idan kin mutu a kona ki ba ko?"
"Eh"
"Good kina son idan kin mutum na musance a aljanna ko? Guri mai kyau da ni'ima kuma komai ake so za a samu a ciki"
"Har da kayan wasa"
"Sosai da kayan dadi kala kala, amman sai idan mutum yana yin sallah, kin ga ina son ki ba zan so ki shiga wuta ba"
"Eh ba zan shiga ba wuta ba, Momy ce zata shiga wuta ita ce bata sallah, kuma ita ce kafira"
Aliyu yayi murmushi mai sauti.
"Toh a duk lokacin da kika yi sallah ki rika rokon Allah yasa Momy ta dawo hanyar musulunci, ai ba zaki so a kone ta ba ko?"
"Eh amman wata rana ina son a kone ta sai a cireta"
"Aa babu kyau Momyki tana sonki ita ma ba zata so ki kone a wuta ba, duk wanda kake so ba zaka so ya shiga wuta ba"
"Sai wanda baka so? Toh Vito ina son ya kone a wuta yayi baki ya soyu"
Nan ma Aliyu dariya yayi
"Aa shi ma ki masa addu'a Allah ya shirya shi ya dawo musulunci"
Ta lake kafada ta turo baki gaba.
"No bana son shi ba zan yi ba"
"Zan rika biyanki idan kina musu addu'a"
"Noooooo bana son shi i hate him ni bana son shi"
"Da alama kina da kafiya Fatima ki daina ba shi da kyau kinji don't be a stubborn girl"
Ta makale kafada ta juya masa, murmushi kawai yayi ya daga wayarsa ya kira number Emily sai ya ji ta a rufe hakan ya dan kara masa damuwa.
"Fatima
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 29 Chapter of 63