Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
damar da zan gyara mana, kina ina Aisha? Na ji fiye da yadda kika ji a lokacin da na barki, saboda ni a yanzu kin tafi ki bar ni da azababben Ciwon Sonki da tsananin kishinki, kin bar ni da tunaninki, ga fargabar abun da zai same ki da yadda zaki karbe ni, a yanzu ke baki jin komai saboda bana kusa da ke, amman ni ina jin duk wata azaba ta duniya saboda rashinki" Ya juya baya. "Ban san dacin rashi ba da kewa ba sai da na rasa ki, amman zan nemo ki, zan jure duk wata tsana ko tsangwama daga gareki har sai kin yarda ni ABOKIN RAYUWARKI ne, a inda na wulakanta zan daukaka darajarki wannan alkawarina ne, ki yafe min Aisha, dan Allah karki bar ni, ina da bukatarki a kusa da ni, ko da ke baki ra'ayi na na san ba zaki so ni ba, amman ni ina Sonki haka ma ya wadatar, abun nan ba shi da sauki ko kadan, ya wuce duk yadda kike tunani" Ta lumshe ido ya cije lebensa na kasa cike da kukan zuci wanda ya fi na hawaye daci. Sai a yanzu yake ta kara dorawa kansa laifin abubuwan da suka faru, yake nadamar abun da yayi mata kuma yake ganin rashin dacewa a hakan, babu komai a tare da shi a yanzu sai tsantsanar kaunar Aisha da kewarta da kuma nadamar da bata da amfani. EMILY POV. Ya aje mata tsarabar da yayi mata a gafen gado sannan ya kai hannunsa ya taba jikinta sai ya jishi da zafi kamar kullum. Taba ta da yayi ya saka ta bude ido daman idonta biyu ba bacchi take ba, ta kalleshi da idanuwanta da bata iya budewa sosai. "Babu ranar da zaki ji sauki idan ba zaki daina tunani ni ba, tunanin nan shi yake haifar miki da damuwa, ita kuma damuwa bata barin kwakwalwa ta huta, kwakwalwa kuma bata mikawa kowa matsalarta sai zuciya da jiki" "Am so fighting for peace, ina ta yin kokarin abun da zan iya, da kowane numfashi ina tunanin yata da rayuwata, na yi marmarin kurciyarta a lokacin da ban san tashin hankali ko bacin rai ba, ban san muhimmanci iyaye ko yan'uwa ba" Ya zauna gefen gadon sai ta tashi zaune ya kalleta gaba daya ta bi ta fita hayyacinta saboda tunani da damuwa, kusan tun da ta zo gidan ta gagara sakewa da kowa abinci sai dai a kawo mata a daki, sai idan yana gidan yake cilasta mata fitowa dinning ta ci abinci tare da kowa, ga ciwo kullum lafiya ta ki sama mata salama. Dr A-B yayi iya kokarinsa gurin dauke mata hankali da wasu abubuwa amman hakan be samu ba, ko Tv aka kukuna mata madadin damuwa ta ragu sai ta karu, idan ta ga yara, idan kuma wani bangare ne da ake kuka haka zata yi ta kuka kamar gaske. Idan ta auna yadda take ji a yanzu da ta san Fatima tana hannu da guri mai kyau, sai ta yi mamakin yadda mahaifiyarta ta iya jefar da ita kuma ta jure rashinta, a nan ta fahimci wasu mutanen an yi su ne kawai saboda su kaunaci mutane ba dan su samu kaunar daga gurin kowa ba. "Da nace zan saka a dauko Fatima ko? Kika ce aa kuma saboda ita kullum kike damuwa?" "Bana son kowa ya san inda nake, ina jin aminci da natsuwa a nan, kawai dai na gafara sabo wa da kowa ne, kuma ina ta guje ni bayan tsawon shekarun da muka dauka a tare, idan har zan kusance ta sai ta bukace ni, ina son na saba da rashin komai kamar yadda kaddara take koya min" Ya kai hannu ya shafa kanta cike da tausayin hawayen da take zubarwa. "Kina horar da kanki ne kawai, Fatima karamar yarinya ce bata iya gane daidai ko kuskure yara suna bin son zuciyarsu ne kawai" "Haka ne, ni ma son zuciyar na bi ya kai ni ya baro" "Wannan tunanin yake haifar miki da damuwa, Momy ta fada min tun da na tafi baki fito ba, da zarar tafiya ta kama ni zuwa wani guri baki sake fitowa, kuma zuwa yanzu ya kamata ace kin sake jiki da kowa Emily" "Ka yi hakuri zan saba, amman ba lokaci daya ba, abun ba shi da sauki ko kadan" "Na sani, yanzu taso muje mu ci abinci a upstairs" Ya share mata hawayenta, ta san duk yadda zata musa masa ba zai taba barinta ta zauna a dakin ta ci abincin ba, dan haka ta sauko da kafafuwanta sai ya yaye mata bargon dake jikinta ya rika hannunta ya nufi kofa ya bude ya rike mata ta fito ta yi rama sosai kurmin idonta har ya fada, kana ganinta ka ga mace mai damuwa. A falon Momynsa yake cin abinci dan haka ya nufi upstairs watching her steps har suka haura ya shiga falon yana rike da hannunta. Tun da suka shigo akan hannunta da Dr A-B ya rike Aliyu ya sauke idonsa, kamin ya isa gurin fuskarta, for the first time ya ji kamar yaje ya da gudu ya rumgumeta ya fada mata komai zai wuce, saboda yadda yayi marmarinta da kuma damuwar da ya gani a tare da ita ga wata rama da ta yi abun tausayi. Tsayawa ta yi cak, Dr A-B ya kalli kafarta kamin ya kalli fuskarta zuwa abun da take kallo, sai ya ga mutanen da ba bakin fuska ba ne a gurinsa musamman Mama Barakat. Ya kalli mahaifiyarsa dake zaune zai yi magana ta riga shi. "Ka same ni ɗaki zamu yi magana" Ya saki hannunta. "Je dakinki" Ta juya tana jin abun some how, taya suka san tana nan? Ko dai shi ya fada musu? Ta sauka kasa tana tafiya hawaye na sauko mata har ta isa kofar dakin ta murda ta shiga ba tare da ta juyo ba balle ta rufe. "Har yaushe zaki yi ta gudu ne ke kam Emily?" Ta juyo ta kalleshi har ga Allah bayan yarta shi ne mutum na biyu da ta yi marmarin gani. "Taya ka gano ni?" Ta taka ya shiga cikin dakin. "Ta yadda mutuwa take neman rai, duk inda kika shiga zan nemo ki Emily, duk inda kika tafi zan biyo sawunki" Hawaye ya sauko mata "I don't need to do this, ban cancanci wannan sadaukarwa ba" "You just don't know what you mean to me, tabbas ban cancanci sadaukarwa daga gareki ba, alfarma nake nema, Emily ina son na maida ke gida" Ta yi baya baya ta zauna tana rumgume da hannayenta tana wasu hawaye masu zafi. Ya karasa cikin dakin yana kallonta cike da tausayi. Ya zauna nesa da ita tana kallonta shiru yatsasu na tsawon lokaci, kamin ya yanke shirun da fada mata abun da ta fi bukatar ji a yanzu. "Fatima tana lafiya, amman ta yi marmarinki sosai" Ta lumshe ido, bata da tabbaci abun da Aliyu ya fada amman dai ta ji sanyi a zuciyarta. "Why are you here?" Ta tambaya ido a lumshe, muryar a dakishe, Aliyu ya amsa mata kamar mai rada. "To take you home" Ta girgiza kai tana maida numfashi sai dai bata ce komai ba, ita a tunaninta rayuwarta ta zo karshe mutuwa kawai ya rage mata. Aliyu ya cigaba da kallonta cike da tsantsar tausayinta dake ta dawainiya da shi. "Duk lokacin da kika ji ba zaki iya ba, ina nan kusa da ke, hankalina zai fi kwanciya ace duk lokacin da kika farka, zan kasance kusa, na ga nauyin da kike ɗauka ke kaɗai yaƙin da kike yi, tabon da kika nuna" Ya hade bacin ran daya tsaya masa a wuya. "Ba sai kin ɓoye shi ba yanzu zan zama ƙarfinki, kuma na yaki baƙin cikinki, idan dare ya yi miki sanyi kuma duniya ta zama maras tausayi a gareki, ki bar ni in zama lafiya da kike nema" Yayi shiru na dan lokaci. "Zan ɗaga darajarki, zan share hawayenki zan tsaya tare da ke cikin kowane hali, farinciki bakinciki ko kuma duka, idan kina buƙatar hannun da zai rika ki ya tsamo ki daga rijiyar da kika fada, zan miƙa nawa, idan kina buƙatar yin ihu, ki yi zan ji kukanki na saurareki Emily" Yayi shiru yana kallom hawayenta, hawaye take sosai har wani kololon kuka ke mata yawo a zuciya. "Duk abin da zan ɗauka don ki samu nutsuwa dauka, zan tsaya tare da ke, hakan zai samu idan kin zauna a kusa, ki bar ni in kiyaye ki lafiyarki cikin guguwar rayuwa, zan zama mafakarki zan ɗauki zuciyarki idan bazaki iya da ita ba, tare zamuyi ƙarfi, za mu fuskanci duhu, ke ce duniyata a yanzu, wata da tauraruwa da ke jagoranta ta" Ta bude ido ta kalleshi, kalamansa na ratsata da tsuma zuciyarta, ashe dai ita ma tana da muhimmamci, a yau Aliyu ya karanta mata abun da ta dade tana musunsa a zuciyarta. "Kowane hawaye da kika zubar, kowa rauni da kika bayyana zan kasance a tare da ke, abun da ke tsakaninmu a yanzu ya wuce tausayi kawai, wata katangar karfe ce da bata rusuwa, wani kololon nauyi ne wanda ni da ke muke dauka da baya zai taba yiyuwa mu aje ba, every time you fall I'm breaking too, amman ina kokarin na ga na tashi saboda ke, so I'm here to take you home karki ce min A A" [8/1, 1:58 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL?mode=ac_t *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒* *© Khadeeja Candy* Page 6️⃣0️⃣ Dr A-B ya bi bayan Momy ya shiga bedroom dinta, ya zauna cikin rashin natsuwa da kuma bacin rai. "Ya aka yi suka san nan? Kuma suka san Emily tana nan?" Momy ta dube shi. "Samu sakon neman yarinyar nan ta email, waya daga wannan yaron Aliyu, kullum da kalar magiyar da yake min da rokon na ba shi dama ya zo yayi magana da ita, ya fada min Madam Barakat ce mahaifiyarta, ita kanta ta same ni da maganar kuma na fahimce ta na karanci damuwa a tare da ita sosai saboda ni ma uwa ce, and kai kanka mafita kake nemawa yarinyar ai kuma yanzu yan'uwanta sun bayyana me zai saka mu cigaba da boyeta?" "You just don't like her Momy haka ne?" "Me zai saka na tsane ta? Me ta min? Labarinta abun tausayi kamar rayuwarta, amman ba mu da wata hujja na cigaba da rike ta, kasan mahaifiyarta tana da damar ta saka kara ma akan boye mata yarinya? Balle kuma Madam Barakat ta yi min komai? Ba zai yiyu na gagara cireta daga matsala ba" Dr A-B ya mike tsaye ya taka ya juyo. "Amman baki shawarce ni ba, ni na kawo ta gidan nan akalla ta kamata ace ina da labarin abubuwan da suke tafiya akanta" "Ba lallai ita ko kai ku aminta ba, shiyasa ban fada maka ba, kuma ai ba tafiya suka ce za su yi da ita ba, magana kawai za su yi, ni kaina na dauki tsawon lokaci kamin na amince da yaron ma, daga baya Mahaifin yaron ya tuntubi mjjina akan yarinya and i can't said NO" Ya sauke ajiyar zuciya mahaifiyarsa ce ba zai iya daga mata murya ba, sai dai sam abun da ta yi masa be masa dadu ba ko kadan. Ya fito daga dakin yana kokarin boye bacin ransa ya kalli Madam Barakat da bakuwarsa ba. "Barka da zuwa Madam ya hanya?" "Alhamdulillah" Ta amsa tana kallonsa kamin ta kalli Aliyu dake kofar shigowa falon tana takowa a nutse. Dr A-B ya kalleshi shi ma ya kalli Dr A-B kamar ba za su yi magana da juna ba, sai kuma Aliyu ya mika masa hannu. Dr A-B ma ya mika masa hannu suka gaisa, sannan ya nunawa Aliyu kujera shi ma ya zauna. "Yaya Emily take a yanzu?" Aliyu ya tambaya, Dr A-B ya fada masu yanayinta da kuma abunuwan da yake kokarin ganin ya cin ma a game da lafiyarta. "Maa Shaa Allah haka ake so, ka yi kokari mun gode sosai" Mama Barakat ta fada. Dr A-B be ce komai ba ya kalli agogon hannunsa. "Momy tace kun zo nan ku ganta ne, bari na yi magana da ita sai ku shiga ku ganta" "Already na yi magana da ita, kuma mun zo nan ba dan magana da ita kawai ba, maganar gaskiya mun zo nan ne saboda mu tafi da ita gida" Aliyu ya amsa masa, Dr A-B ya kalli Aliyu. "Bana tunanin tana bukatar tafiya wani guri yanzu, domin abun da Emily take bukata a yanzu shi ne kulawa da kwanciyar hankali" "Zamu bata fiye da abun da kake tunani Dr already mun yi booking flight in the next 40 to 1h zamu juya In Shaa Allahu" Dr A-B yayi kokarin mikewa tsaye sai ga Momy ta fito dakin ta dawo falon tana zaunawa Emily ma ta shigo falon tana tafiya a hankali. EMILY POV Mikewa yayi tsaye. "Jirgin da za mu bi zai tashi nan da awa daya, ban sani ba ko rayuwa zata ba ni aron lokaci na dawo gareki, wata kila kuma sa'a ce zata rabe ni ta saki ki bi ni, duk wannan ba ni da ilimi akai, sai abun da zuciyarki ta gamsu da shi" Ya juya ya fice daga dakin. Emily ta bishi da kallo har ya fita yaja mata kofar, sai ta lumshe ido murmushi kadan ya bayyana a fuskarta dake dauke da hawaye. Nemanta kawai da ya bata lokaci yayi abun farinciki ne a gurinta, gashi kuma a yanzu ya daureta da kalaman da wani be taba mata ba, ko da karya Aliyu yayi mata a yau ta jidadi domin ya nuna mata tana da muhimmanci, da ace zata iya da ta zauna Aliyu yayi ta zuwa yana dawowa ba dan komai ba sai dan waken da daya rare mata mai dadi a yau ya karanta mata shi a kullum ya zo neman Alfarma. Ta mike tsaye ta share hawayenta ta nufi kofar dakin ta bude ta fita tana tana takawa a hankali kamar mai tsoron bayyana sautin takun kafarta haka ta haura sama ta shiga falon Momy, sai kuma ta yi tsaye bata karasa kusa da kowa ba. "Emily kin yi magana da wannan" Dr A-B ya nuna mata Aliyu ta kalli Aliyu da be kalli inda take ba tun da ta shigo, ta daga kai. "Ya fada miki sun zo man ne saboda su tafi da ke?" Ta daga kai. "Za ki bisu?" Ta dubi Aliyu har lokacin be kalleta ba idonsa yana kan wayarsa. Ta daga kai "Kin tabbatar kin shirya komawa?" Ta yi shiru na lokaci kamin ta daga kai. Dr A-B ya mike tsaye daman tun dazun yake da shirin tashi ya nufi kofar fita ya raba gefen Emily ya fice ba tare da yace komai ba. Aliyu na ganin haka ya san Emily ta amincewa bukatar da ya zo da ita sai ya hade yawun farinciki ya gyara zamansa ya daga ido kadan ya kalli Emily. Emily ta ji babu dadi ficewar da Dr A-B yayi domin haka ya nuna be yi maraba da tafiyar tata ba. Ta juya ta bi bayansa ko da ta shiga dakinsa Already ya zauna akan kujera and to her wannan ne karo na farko data taba shigowa dakinsa. Ta karasa inda yake zaune ta risina kasa ta dafa hannun kujera. "Ka yi fushi da ni?" Ta tambaya da wata murya gwanin tausayi. "No bani da hujjar yin fushi dake akan abun da ke kika yanka da kanki, kawai dai abun da nake tsoro ya zamana cilasta miki yayi ko kuma yayi miki barazana" "Ba ko daya, kawai ya yi rubutu a kwakwalwata ne, ya karanta min da halshen da da zan fahimta" "Kuma bana fatar ki koma ki sake fuskantar wata matsala" "Ni ma bana fatan haka" "Ko ma dai miya faru ki sani you're always welcome here" Ya mike tsaye ya nufi gurin da yake aje kayansa ya dauko card din ya nufota ya kama hannunta ya mikar da ita tsaye ya danka mata. "In case of.., kuma ba lallai sai kina cikin matsala ba ya kamata ace ko da yaushe ina jin duriyarki domin sanin halin da kike ciki" "Na gode na jidadin haduwa da kai, ka taimaka min gashi ba ni da wani abu da zan biyaka" "Zaki biya idan lokacin biya yayi" Ta yi murmushi tana hawaye sai ya rumgumeta yana jin babu dadi domin zaman da ta yi a gidan ya saba da ita. "Idan kin tafi karki fasa shan maganinki, kuma ki guje duk wani abu da zai saka miki bacin rai ko damuwa" Ta amsa masa da kai tana kallon katon hoton dake tsaye gefen mirror sa kamar na cikin hoton zai yi magana. Ta dago daga jikinsa tana cigaba da kallon hoton. "Mahaifina ne" Ya amsa mata tun gabanin ta yi masa tambayar. Sai ta juyo ta kalleshi da mamaki ta sake kallon hoton amman bata ce komai ba. "Kina mamaki ne? Ni ma haka nake mamakin jin cewar Madam Barakat ita ce mahaifiyarki" Ta share hawayenta ta yi "Shiyasa nake son tafiya, akwai tambayoyin da ita kadai zata iya amsa min su. "Fatan alheri" Yayi fada da murmushi sai ta saki hannunsa tana jin kewarsa tun kamin ma ta bar gidan. Ta fito dakin sai ta sake dawowa falon Momy ta samu mai aikin gidan ta hado mata kayanta a akwaiti har hudu domin Dr A-B ya wadata da tufafi a gidan daidai gwargwado. A sanyaye ta karasa kusa da Momy ta risina kasa "Na gode da karbata da ka yi, na gode da masauki da hidima da kika yi da ni, na gode Sosai" "You're Welcome, kina jin kina son tafiya Emily?" Ta daga kai. "Okay, ga kayanki an hado, ki shiga ki duba idan baki manta komai ba" Emily ta girgiza kai domin bata son komawa dakin, ji take kamar ta yi kuka ita ma ta saba da su musamman ma DR AB dake shiga mata gaba a komai na gidan. Duk abun da ake Emily bata kalli gefen da Mama Barakat take ba ita ma kuma bata yi saka bakinta ba sai bin Emilyn take da kallo cikin yanayi marar dadi. Mai aikince ta saukar da kayan kasa aka saka a motar da suka zo da ita Aliyu yayi ma Momy godiya sannan ya mike tsaye yana kallon Emily. "Zamu iya tafiya?" Ta kalleshi sannan ta fara takawa ta wuce ya bi bayanta, da suka zo gurin sauka stairs sai ya cira kafa ya rigata sauka just to watching her steps kar ta fadi domin benen mai hawa biyu ne ba daya ba gashi hawaye take ba lallai tana gani da kyau ba. Da suka sauka kasa gaba daya sai ya bude mata kofar falon ta fita Mama Barakat ma ta fita sannan ya fita, sai da Emily ta sauka entrance din sannan ta juyo ta kalli kofar falo, bata sani ba ko zata dawo ko kuma tafiya ce ta har abada, domin kaddara tana hadata da mutane kala kala kuma ta rayu a gida mabanbanta, sai dai a wannan gidan ta hadu da mutane masu karamci da girmamawa. Aliyu ya bude mata back Seat yana tsaye yana kallonta sai ga kira ya shigo wayarsa ya dayan wayarsa, yana ganin haka ya san Fatima ce domin har yanzu wayarsa dayar tana hannun Fatima, kusan kullum sai ta kira shi tace ya bata Momy zata yi magana da ita ko ta ce ya fadawa Momy ta zo, wani lokacin zai ce Momy ta yi bachi, ko kuma yace ta yi tafiya, ta ce ya turo number ya tura mata idan ta kira ta ji kashe. Shi kanshi fargabar kiranta yake domin kuka take masa sosai idan yace Momy bata nan, wani lokacin ta kan ce shi ya zo amman ba zai tafi ba, idan ta bukaci akaita gurinsa Turhan ba zai yarda ba. "Hello" "Bana fadi miki idan kin kira ki rika sallama ba?" Sai ta yi sallamar cikin kuka. "Waya taba ki?" "Momy ce, har yanzu bata zo ba? I miss her i want to see her" "Bari na kira ki FaceTime" Ya yanke wayar ya kirata FaceTime yana kallon fuskarta hawaye shabe shabe sai yayi murmushi ya rage volume din ya juya camera from font to back ya nuna mata Emily dake tsaye tana kallon gidan bata san wainar da ake toyawa ba. Wani irin tsalle Fatima ta yi ta fashe da kuka. "Hi Momy Hi Hi Hi Hi Momy Momy Momy I'm sorry" Aliyu ya juyo da front camera yana murmushi ya kara volume din. "Muna Abuja yanzu tare da Momynki, za mu dawo idan muka dawo zata zo ta ganki" "Okay..." Ta daga mishi kai tana dariya sosai tana daga mishi hannu alamar bye bye, sai duk ta ba shi tausayi, shi ma ya daga mata hannu ta kashe wayar ya kira sunan Emily. "Emily" Ta juyo sai ta kalli motar daya bude ta fara takawa ta nufi motar ta shiga tana ta kallon kofa wai ko Dr A-B zai fito ko Momy sai dai rashin jindadin tafiyarta ya hana Dr A-B fitowa because he don't want to say good bye to her, Momy kuma tana jin kanta ba kasafai take saukowa kasa ba, ba kuma dan wulakanci ba domin bata da wulakanci ko kadan sai dan isa ta naira. Ta shiga ta zauna Aliyu ya rufe motar Mama Barakat ta bude dayan gefen ta shiga ta zauna Aliyu ya shiga front seat sai da suka fice daga gidan sannan Aliyu ya tambaya ko dai su tsaya su kwana Abuja domin to him Abuja gida ce no need to rush, Ummi ma a nan take zauna ba dan abun da ya faru ba da yanzu bata je Kaduna ba. "Aa mu tafi kawai" Mama Barakat ta fada, a nan Emily ta kalleta. "Da gaske ke kika haife ni?" Mama Barakat ta kalleta jiki a sanyeye. "Ni ce?" "Taya? Meyasa kika jefar da ni? Me na yi?" "Baki yi komai ba, na haife kyakkyawa cikin koshin lafiya, na aje ki a inda na bar ki ne saboda na haife ki ba da aure ba, kuma baki yi kala da ni ba, ina jin tsoron irin kallon da duniya zata min a wacan lokaci ne" "Amman kin san ina gurin kuma a gurin na rayu? Kin taba tunanin nemana? Ko sanin halin da nake ciki?" Mama Barakat ta girgiza kai. "Ban taba ba, saboda ina tunanin kamar abun da na aikata shi ne mafita a gareki da ni, ban taba sha'awar na san wane kike ciki ko rayuwa kike yi ba, tun da na aje ki na rufe shafinki, ban sake ganinki ba sai wacan ranar da kika labarta min labarinki, dana kalleki kuma sai na ga siffarki da yanayinki be sauya ba daga na mahaifinki, kuma sai kika gudu saboda neman mafita, sai n aji tsoron nemanki saboda yarana da aurena da kuma ke taya zan fuskance ki?" Emily ta yi juyar da kanta ta jinginar jikin mota tana hawaye, hawayen da ba su tsaya mata ba har suka shiga jirgi. A guri daya suka zauna da Mama Barakat a first class, Aliyu kuma ya zauna wani guri dabam ba kusa da su ba. TURHAN POV "Momy zata dawo na ganta" Turhan yayi mata murmushin zahiri badini kuma wata wuce ta ce take cin ransa. "Wow zata dawo I'm happy, to yanzu sai kije ki ci abinci kar Momy ta ga kin rame ko?" Ammy ta fada, Fatima ta daga kai har ta fara tafiya sai kuma ta juyo. "Idan ta dawo zata zauna a nan? Zamu zauna tare? Bana son wani ya sake tafiya kuma" Ammy ta daga mata kai, sai ta dawo da gudu ta rumgume Turhan. "Ina son haka" Ta fada da hausa domin zamanta gidan ta fara tsintar wasu kalamai na hausa, Ammy ta kan gwada mata magana da hausa ta koya mata wasu abubuwa, idan kuma ta ji ana hira aka fadi wani abu sai ta tambaya me aka ce ko me ake nufi har rubutawa take idan yan kwaran suna bisa kai, idan kuma rigimar neman Momy ya tashi bata kula kowa. Sai da ta fita dakin sannan Ammy ta kalli Turhan ta ce. "Abuja Ummi take zaune, amman a yanzu ance tana gidanta na Kaduna yanzu kuma Aliyu yace suna Abuja za su dawo Kaduna yau,

Chapter 48 of 63