bangaren da Turhan yake da matarsa dabam, idan har na huta to dare ne yayi ya shiga turakar mijinta mu kuma sai mu samu hutu, na ga wulakanci na ga kaskanci ga yunwa ba a wani ba mu san adataccen abinci, idan ma aka kawo abinci wadanda suka manya ne suka kwashewa mu kanana a bar mana kadan, gashi ya fadawa kowa ni kurma ce ba damar na yi magana ko na nuna na ji wani abu, haka na yi rayuwa cikin tsananin azaba da azzatarwa, idan aka yi baki ni nake gyara ko'ina na gidan kuma ban isa na ce na gaji ba, gimbiyarsa kuma bayi ba su isa su daga kai su kalleta ba sai hukunci.
Wata rana na makara ban tashi ba, domin tun da asuba muke tashi mu fara aiki ga gidan da girma, kananan bayin da muke yin aikin ba mu da yawa, su kuma manyan aikinsu bangaren kula da baki ne ko abinci, sai wata babbar hidima idan ta taso. Ko da na isa na samu wata ta maye gurbina tana aikin mopping din da aka ce na rika yi kullum. Da farko na jidadi na yi zaton ko an dauke min ne na huta na wunin ranar ashe sun shirya kai karata a gurin babbar hadimar matarsa ne. Sai da aka gama komai na fito ina gyara gefen dawaki hadimar ta iso, da wani yare take min magana wanda ban iya ba, ko da ace na iya ban isa na amsata ba, saboda Turhan yace kar na sake na nuna ni ba kurma bace, ina jin tana magana amman ban waigaba, sai da aka tabo ni sai ta yi min alama da bachi da lokaci tana tambayar meyasa, ba ni da amsar bata dan haka na yi shiru sai kallonta nake tun da ban iya maganar kuramen ba balle na fada mata da kurmancin cewar ban san lokaci yayi ba, ashe hakan yayi mata ciwo, a take ta koma ciki babu jimawa wasu mata suka zo suka rika ni suka tafi da ni wani daki, tun daga yanayin dakin na san azabtar da ni za'ayi domin akwai bulala a cikin ga kuma wani namiji tunbuke da da katon rawani yana jiran shigowata.
Ba su tirsasani ba gurin shiga da kafafuwa na shiga, mutumen ya fara duka tun ina hawaye kawai ina kukan dole irin na kurame har kai ga ihu ina neman taimako, sai ga mutane an cika gurin kowa yana kallo da mamakin maganar dake fita bakina, sai da na samu sa'ida sannan na fito daga dakin na koma bangarenmu na kwanta ina jin fatata tana min zugi. Can da dare aka aiko daya daga cikin bayin da muke kwana da su ta kama hannuna ta fita da ni ina tafiya daker, daman haka suke min idan ana kirana saboda basu iya kurmanci ba ni kuma ban isa na yi magana ba. Da muka isa bakin fadar gimbiyar Turhan sai babbar hadimarsa ta yi min alama da na wuce ciki na shiga daga baki baki na zube kasa, sai ta yi tafiyarta. Na kusan awa daya a gurin sannan Turhan ya fito cikin shigarsa ta jallabiya da alkibba mai kyau hannayensa a baya ya karasa kusa da ni cikin wata irin tafiya ta kasaita ta ban taba ganin yayi irinta a gidan Ammy ba, fuskarsa babu annuri.
"An fada min kin yi magana? Saboda me?"
Maganar ma a rarrabe yayi min ita saboda kasaita ta.
"Dukan ne yayi min yawa ban san lokacin da na yi ihu ba, ka yi hakuri"
Sai a lokacin ya kalleni yana jin kansa.
"Wa yasa aka doke ki? Me kika yi?"
A tunani da sanin matarsa aka min dukan dan haka da ya tambaye ni sai na ce.
"Matarka"
Na kama hafafuwansa na rike ina kuka.
"Turhan dan Allah ka maida ni gida"
Ya ja baya.
"Karki sake taba kafata, tashi ki fice, kuma na fada miki ke kurma ce karki sake ki sake yin magana"
Na tashi daker na koma bangarenmu, na samu tufafin wata na dora kaina akai domin ni Turhan be bani nawa tufafin da Ammy ta hado ni da su ba, kuma bata kira ta ce a bani ba, kowa yana ta tufafi daga kala biyar zuwa sama ni kuwa kala biyu ne daga tufafin da yake a matsayin uniform dinmu sai tufafin da na cire. Ina dakin aka sake zuwa aka dauke ni hadimar Gimbiyar tana ta masifa sai dai ban san me take fada ba. Wacan dakin aka sake maida ni aka sake zaneni sai dai wannan karon ban yarda na yi uhu ba saboda Turhan ya gargade ni.
Dukan ne ya zama silar rashin lafiyata a masarautar har na tsawon sati gashi babu kyakkyawar kulawa babu maganin kirki, rayuwar bauta rayuwa ce ta kaskanci da wulakanci Aliyu, wanda ba zan yi ma kowa fatanta.
Da na fara jin sauki sai na koma kan aikina tun daga lokacin bana bari ma asuba ta yi ina bachi, da zarar karfe uku ta yi na dare na farka ba zan sake komawa bachi ba. Zamani ya waye duniya ta canja ban taba tunanin har a lokacin akwai sarakunan da suke mulkin bayin ba sai da na ga masarautarsu Turhan. Gashi basa ganin kimar bakar fata, domin a duka bayin babu larabawa sai yan wasu yarukan ko kabila, ni kaina sai su yi ta kallona wasu har taba gashin kaina suke suna yaren da bana ji, wani lokacin kuma a daga fatar idona a kalli idon.
A ranar da Allah ya kaddara za a samu cikin Fatima, da safe ne sosai ina goge fadar Hadimar Gimbiyar ta zo ta kama hannuna ta shiga da ni can ciki sannan ta saki hannuna ta fice, ina tsaye a gurin Turhan ya fito sai na yi hanzarin zubewa kasa na maida idanuwa kasa.
"Biyo ni"
Ya fada sai na mike tsaye na bi bayansa, da halshen larabci ya sallami masu saka turaren dakin sai daya daya umarci ta ba ni turaren na karba na bi bayansa har muka shiga bangarensa. Muna shiga ya nuna min inda zan aje turaren ya ce.
"Shiga wacan dakin akwai bandaki a ciki ki yi wanka, ki cire tufafin ki daura tawul"
Yana min maganar yana kallo da kyama da kuma dan bacin rai kamar wanda baya cikin yanayi mai dadi.
Na aje turaren na nufi dakin da ya nuna min na shiga, na cire tufafin jikina kenan ban kai ga shiga bandakin na ji shigowarsa.
"Dole ce kawai saboda kin min karya kince matata ce ta saka aka duke ki alhalin ba ita ta saka ba, kin saka ta kaurace min na tsawon lokacin nan"
Wata kila yana cikin uzurin da ba zai iya jira na yi wankan ba, ko kuma yana tsoron ta shigo ta tarar da mu ne sai ya yi abun da zai yi cikin gaggawa, bayan ya gama yana ta tsaki da tofar da yawu.
"Wannan ce bakar rana ta biyu a gurina bayan ranar da na aureki, kuma karki sake na ji maganar nan kin shigo dakina a gurin kowa ko kuma wata alama"
"Dan Allah Turhan ka maida ni gida"
Na roka ina jin kaina a cikin wani irin kaskanci da ban taba samun kaina a ciki ba.
"Idan kika sake fadin sunana ko daga ido ki kalleni sai na saka an miki illar da zai lalata miki idon, ko baki in yaso sai ki zama kurma da gaske, tashi ki bace min da gani"
Ya daka min tsawa rai a bace, a cikin rakunan bakincikina, ranar da Khaleefa ya sake ni ba zan manta da ita ba, ba zan manta da furucin da Turhan yayi a gareni ba na kiran ranar aure da kuma ranar da ya tara da ni a matsayin bakar rana ba, haka ba zan manta da ranar da na rasa ɗana ba. Na kimtsa kaina na fito ina jin jikina yana min wani iri domin na dade irin wannan alakar bata hada ni da kowa ba bayan na fito daga gidan Khaleepa. Na cigaba da aikina ina hawaye har na gama, sai rayuwa ta ci gaba tun ina saka ran Ammy zata zo ko kuma ta kira amman babu ko daya, gashi ni kuma ban taba rike waya ba tun bayan dana zauna a gidanta ban san ma ta ina zan same ta ba.
A haka na sake shafe wata biyu a gidan, kuncin da na shiga sai yafi na baya saboda matarsa da hadimarsa sun tsane ni a yanzu ba tare da na san laifin da na yi aikata a agaresu ba. Ga kuma lailayin da nake ta yi a boye.
Muna cikin wannan halin wata rana sai fadar sarkin ta yi babban bako. Wani babban mai kudi kuma dan kasuwa ya sauka masarautar tare da rakiyar manyan mutane daga Nigeria. Aka saka mu yi wanka muka fito tsaba saboda zamu tarbi bakon tare da tawagarsa. Sai kuma aka yi dace Turhan da matarsa sun tsallaka sun bar kasar zuwa gurin da be fada min ba, na fahimcin hakan ne ta hanyar rufe wani bangare da aka yi a part dinsu aka hanani shiga na gyara kamar yadda nake, kuma aikin da ake yawan sakani ya ragu ba ma ni kadai ba har da sauran bayin.
Wasu kuma na daina ganinsu wata kila har da su aka yi tafiyar.
Matar Sarkin wanda take zaman step mother din Turhan ta tarbi matar dan kasuwar da ba zan iya fadar dalilinsa na zuwa garin a lokacin ba. Ni da mutum uku aka zaba mu yi Serving din matar dake wanye da abaya kanta da wings ta nada gyalen abayar a wuyanta ga bakin gilashi, da alama dai ba musulma bace shiyasa ta kasa rufe kanta. Kusan shi ne karo na farko da na bar garen Turhan zuwa wani bangare na gidan, wata kila babu wata adatattun bayi ne a lokacin wata kila kuma Allah yayi nufin kubutar da ni ne, shiyasa abun da duk ya faru ya faru.
Muna jera abincin a madaidaicin falon da aka ware mata ina satar kallonta zuciya nata yi min sake sake, yadda zan samawa kaina mafita, domin tun da muka shigo naji tana waya da yaren igbo. Sai da muka gama jera abincin tsab sannan na kalli matar cikin karfin hali da nemawa kai masifa na soma mata magana da yaren na Igbo.
"Dan Allah ina neman taimakonki, na ga ke ma igbo ce yar'uwata dan Allah ki taimaka min"
Sauran bayin da muke tare da su suka kalleni kamar a firgice sai dayar ta fice da sauri. Matar ta kalleni tana mamaki ta ba ni amsa da yaren na Igbo.
"Kina jin igbo ne? Daga ina kike?"
"Daga Nigeria, ki taimaka ki maida ni gida dan Allah, ni yar kabilar igbo ce, daga Lagos na zo aiki gurin wata mata a kaduna sai ta hada baki da wani suka siyar da ni a matsayin baiwa a gurin dan sarkin garin nan, ina zaune a nan ne a matsayin kurma wahala nake sha sosai a nan, gashi na baro ɗana kuma ba shi da lafiya, yanzu kuma idan baki taimaka min ba kashe ni za su yi saboda sun ji na yi magana ba su taba jin na yi magana ba"
Ina maganar da yaren na Igbo ina kuka.
"Amman baki yi kama da mutanen Nigeria ba"
"Wallahi daga Nijeriya nake, a gidan marayu na tashi ban san kowa na wa ba, idan mum tafi zan kai ki har gurin domin ki tabbatar dan Allah ki ceto rayuwata"
Na yi mata karyar an siyar da ni ne domin ba lallai ta yarda ba idan na fada mata dan sarkin garin ne ya auro ni ya mayar da ni haka. Daya daga cikin manyan hidiman bangaren Turhan ne ta shigo ta kama hannuna zata fice sai na cigaba da rokon matar.
"Na yi kasada na jefa kaina a matsala na yi magana idan baki taimake ni ba, shi kenan na rasa rayuwata kuma ɗana ya rasa ni, ke fa uwa ce ki taimake ni dan Allah"
Bata ce min komai ba, a lokacin ne na gane na yi kuskure na jefa kaina a babbar matsala domin ban samu biyan bukata ba. Waje aka fitar da ni can bangaren Turhan aka bar ni tsaye a rana a lokacin har na sadakar na san hadimar zata min hukuncinta ne kuma idan Turhan ya dawo shi ma yayi min na shi. Tsawon awa uku na yi tsaye a ranar kamin hadimar da kanta ta sake zuwa ta kama hannuna muka koma bangaren na Sarkin da sai a lokacin na taba ganinsa ido da ido a cikin fadarsa.
Matar ta nuna ni tana murmushi tana fadar nice da yaren turanci, mai fassarawa sarkin yayi Larabci sai sarki ya daga kai da hannunsa kadan wani na kusa da shi yayi magana sai aka fassara ma matar a nan ni ma na ji yana fadar.
"Sarki yace ya baki ita kyauta"
Matar ta yi godiya sosai sai aka fitar da ni waje, a nan sai da suka dade cikin sannan suka fito fadawan sarkin suka yi ma mutumen rakiya tare da matarsa ni kuma na shiga a tawagar masu rakiyar dan kasuwar a wata mota ta dabam. Hankali be kwanta ba sai da muka bar fadar da muka isa filin jirgi na yi zaton za'ayi mana irin na farko ne, ashe shi saboda isa da jirginsa yake yawo, sai dai hakan be hana a tantance mutanen da suke tare da shi ba, ni kuma bi ta wata hanyar dabam da ni bata hanyar da kowa yake bi ba, sai da aka isa gurin jirgin aka fito da ni daga motar na shiga aka zaunar da ni can baya nesa da mutane. A lokacin ne abubuwa suka fara yi min gizo ina ganinsu kamar mafarki.
Tun da muka tashi ba mu sauka ko'ina ba sai Abuja Nigeria. Da muka sauka jirgin ne matar tasa aka matso da ni kusa da ita ta gargade ni da halshen igbo.
"Ina fatan ba karya kike min ba, domin idan ya zama tsabanin abun da kika fada min toh zaki hadu da mummunan hukunci kuma zan saka a nemoki a ko'ina kika a kasar nan"
Na ce mata na amince, suka shiga motar alfarma mu kuma aka saka ni a wata motar, ina ta kallon gari da titunan Abuja da tunanin dan yancin da na samu har muka isa gidan mijin matar mai kama da wata babbar fadar Sarki, mutanen da suka tarbeta ita da mijinta ma abun kallo ne, a nan na kara gane kudi suna da muhimmanci sosai a rayuwar dan'adan. Da muka sauka gidan sai ta hannata ni a hannun wata mata yar Kaduna tace mata wai ina da zan je na dauko ɗana tana son kar a barni na tafi ni kadai na tafi tare da rakiyar wasu saboda tana son ta gano gaskiya ta, ni dai an kira ni kawai aka nuna min matar da za mu tafi tare, ta hanyar wayar da matar take da yaren yarbanci, na fahimci kudin wacan matar da ta ceto ni wanda ko sunanta ban sani ba. Komai aka bani kasa ci na yi ina ta zumudin ganin ɗana ga kuma tsoro ya cika zuciya gani nake kamar Turhan zai aiko a tafi da ni ne. Hankali be kwanta ba sai da muka bar garin Abuja tare da matar da mijinta da nake kyautata zaton dan siyasa ne.
Guri daya na zauna da matar, da alama ticket din da aka saya min na kusa da ita ne. A nan ta gabatar min da kanta ta fada min sunananta Barakat amman yaranta suna kiranta da Mama Barakat ta fada min ita bayarabiya ce, sannan ta tambayi labarina, ita kan ban boye mata komai ba na fada mata labarina tun daga tashina zuwa auren Khaleepa da kuma Turhan, gaba daya sai ta sauya ta rika kallona har sai da na tsorota, har muka isa Kaduna hawaye ke cika mata ido tana sharewa. Mun sauka Airport din idanuwa a zare kamar wata marar hankali ga rama na yi gaba daya ba ni da natsuwa. Mota daya aka zo daukarmu na shiga gaba ita da mijinta suka shiga baya, duk maganar da mijin yake bata amsawa har ya tambaya lafiya? Tace babu komai. Mun sauka gidanta ba laifi gida ne mai kyau amman ko kadan be kamo gidan wacan matar ta Abuja ba, kuma ita wannan da alama tana da abokiyar zama domin gidan bangare biyu ne, sai da muka fara shiga bangaren na farko ta shiga ita da mijin sai ta fito ita kadai ta shiga motar aka karasa da mu bangarenta.
Na sauko motar ina jin kamar na yi tsuntsuwa na gan ni gaban ɗana, haka dai na daure muka shiga ciki, ta nuna min dakin da zan zauna sannan ta haura sama har lokacin hawaye take hawan ma tana yi tana waigena har ta haura stairs din. Ina ganin ta shige na juya ya saci kafa na fice daga bangaren, da kaina na gate din gidan na fice, tafiya kadan na tari abun hawa na hau na fada masa ya kai ni cocin da take kusa a nan garin Kaduna, babu wata daguwar tafiya sai gamu gaban cocin, na gaishe da mai gadin na fada masa ina tafe da matsala ne amman ina son ya bani kudi na sallami mai achaba tukuna babu musu ya biya mai babur din, sannan ya shiga da ni ciki a tunani idan na je ma Ammy kai tsaye ba zata ba ni ɗana ba dan haka na zabi neman taimakon mutanen cocin bayan na fada musu ina ra'ayin komawa alnahin addinina na Christianity.
Sai suka ba ni shawara na fara tafiya dauko yaron har sai idan ta hana tukuna za su shigo ciki, na ba su addireshin gidanta sannan na cire takardar na rubutawa Ammy martanin karyar da ta yi min cewar danta na kirki ne ya banbanta da sauran, domin na san ba lallai na samu tsayawa na fada mata baki da baki ba, amman idan na bata wasikar zata karanta. Su suka ba ni kudin abun hawa na hau achaba na isa unguwar a lokacin ne tsoro ya yaye min saboda ina son ganin ɗana ta kowane irin hadi, da Allah yayi nufin ba ni nasara ina buga gate din mai gadi ya bude sai da ya dade yana kallona sannan ya gane ni, ya bar ni na shiga ciki na samu falon babu kowa sai ɗana shi kadai yana kallon Cartoon, na karasa da zafin nama na dauke ɗana na aje mata takarda a gurin da na dauke shi na fito yana ihu domin shi ma be gane ni ba, mai gadin ya tsaya tambayar ina zan je da yaro na kai masa mugun halbi a gurin da ya fi komai muhimmanci a jikinsa, ba shiri yaja baya na bude gate din na fice da gudu kai kace sato yaron na yi.
Ina tafe ina waije ko za'a biya ni amman ban ga sawun kowa ba sai da na samu Achaba na hau sannan Ammy ta biyo ni da motarta tana cewa na tsaya na cewa mai Achaba kar ya tsaya, be tsaya ba sai da muka isa cocin na sauka da guduna na tsaya layin mutanen da cocin ke rabawa tallafi. Ammy ta dade tana kallona har sai da mai gadin ya bude min na shige.
TIRKASHI....!!!
A tunaninku tsakanin Auren Khaleepa da Turhan a ina Emily ta fi shan wahala? Waya ya fi gallaza mata?
Team Turhan kuna da katon aiki a gabanku😢 indai kuna son Emily da Turhan sai kun tanadi makaman sallama 🤗
_______________________
Sannu ‘yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe ɗinki da kaya masu kyau, masu ƙima daga Khadeeja Candy Store
Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sauƙin sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing.
Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taɓawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet ɗinmu sun dace da ke
Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sauƙi ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko’ina!
Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1
da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0
Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame.
Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ƙayatarwa duk a farashi mai sauƙi.
Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu!
Baki da lokaci? Muna da sauƙin oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina!
To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08
Ba kawai kaya ba ne salo ne, ƙima ce. A Khadeeja Candy Store.
Ki zo yau, ki ɗanɗani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haɗuwa.
[6/26, 9:29 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL
🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
Page 4️⃣1️⃣
Sai da ta bar gurin sannan na fito na sallami mai achaba na koma ciki na rika ɗana dake ta ihu, gaba daya ya ki yarda da ni saboda be gane ni ba. Kansa na rike na saita shi ya fuskanci sai na koma kiransa da sunanyen da nake masa ina hadawa da Momy, a take ya tsagaita kukan da yake ya kalleni sai na yi masa dariyar dake tafe da hawaye na rungume shi ina jin kamar za a sake raba ni da shi ne.
Kwana na uku a coci, a tsawon kwanakin nan bana sallah bana saka hijab duk wani abun da ya danganci musulunci bana yinsa, saboda na fada musu zan koma addinin Christianity, sai dai a can kasa zuciyata na ni na san ban shirya barin addinin musulunci ba, ba dan mutanen cikinsa sun yi min gata ba sai dan ina jin natsuwa da addinin a cikin zuciyata, domin addinin musulunci addinin mai tsari da tsabta da dokoki, ni kuma mace ce mai son zaman lafiya mai son natsuwa. Sun mutunta ni sosai a cocin domin gidan wani pastor aka kai ni, abinci sai na ture gurin kwanciya mai kyau, matarsa tana ta nanata min halayyen musulmai basa da kyau kuma daman su basa son kafirai, har take cewa na yi kuskure da na bar addinin da ace ban gane gaskiya na dawo ba da Yesu yayi fushi da ni kuma ya kona ni.
Kusan duk wa'azinta jinsa kawai nake, amman a zuciya ina kyamar abun, ana gobe Lahadi wanda ta kama ranar coci a ranar za a min wanka da ruwa mai tsarki kuma a maida ni addinin kirista a ba ni bibles kamar yadda na sani yake a hukunce kuma matar ta jaddda min, sai na dauki London na goya ma sanya hijab dina cikin giyon na fito da sunan zagayawa harabar cocin, na nufi gate da yi ma mai gadin karya cewar zan fita naje na dawo kuma sun san da fita ta, domin an fada masa duk wanda ya zo nemana kar ya bar mutum ya shiga sai an sanar saboda ni da su muna tunanin Ammy zata dawo nemana.
Salin salin na fice daga gidan, ba kuma dan na san inda zan je ba sai dan ban shirya komawa addinin ba, na hau achaba na tambaye shi dan Allah wace umguwa ce nesa sosai da cikin gari, unguwar da san yi tafiya sosai sannan a isa gurin, ya fada min sai na ce ya kai ni can, mun yi tafiya sosao kamin muka isa unguwar dake kama da sabuwar unguwa ma sauka na ba shi kudinsa na nisa cikin unguwar ina ta kallon yadda tsare tsarenta yake, har na hango wani gida dake da fanfo da kwararo a ciki, na dauki leda na tara ruwan na fara sha sannan na shayar da ɗana na yi alwala sallah na fara yi na rama duka wandada aka biyo ni har na ji na gaji, a lokacin kuma wata zuciyar take ta fadan min na koma dai domin wannan addinin be karbe ni ba, amman dayar data ci karfina ta hana ni komawa na zauna a gurin har
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 33 Chapter of 63